Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 95 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shiga bashi kafin ya ce bari ya kira
Smart ɗin. Da ya kirasa sai dai a maimakon ya yi mashi faɗa sai ya ce. "Son me kaje
kake yi wa tsoffin nan ka tunzurasu har haka ne? Daddynka ya kirani last week, yau
kuma kakanku ya kirani, ka je kana goda masu iko ko? Kasan fa su sarauta ne, babu
mai nuna iko a gabansu".

Kai tsaye ya amsa da. "Daddy tsoffin ne basa a kan hanyar da ta dace shiyasa nike
mayar da su kan hanya, kasan ba zan yi abu mara kyau ba ai ko my lovely dad?".
Kamar mai shagwaɓa haka ya yi maganar, ALLAH ya gani yana kaunar daddynsa over.

Murmushi daddyn nasa ya yi. "That's my son, nasan gyara kake yi shiyasa ma da
daddynka ya kirani ban kiraka ba, dik yadda aka yi nasan basu aikata dai'dai,
cigaba da dawo da su kan hanya my son, zan yi alfahari da kai, amma ka yi sauri ka
dawo ka ji? Ina kewarka over"...... Da okey kawai ya amsa tare da cewa i love you
dad, love you too shi ma ya ce, daga haka suka yi sallama. NA CE YANZU KUN GANE MAI
KARA SANGARTAR DA SMART KO? KUN JI UNCLE MUHAMMAD WAI YA CIGABA DA DAWO DA SU
HANYA, KAI WATO ALLAH KA BARMU DA IYAYENMU!!.

---------------------------------------🔥🔥🔥

Baki a ɗauke da sallama dattijuwar nan ta shigo room na Auta, irin dogayen rigunar
shan iskan nan ne a jikin Auta ɗin, rigar tana da ɗan siririn hannu, while a
dai'dai gwiwarta ta tsaya mata, tana gajin dattijuwar ta yi gaggawar saukowa ƙasa
daga saman bed ɗinta ta nufeta da sauri, kwandon mai shake da kayan fruits dake
hannunta Autar ta karɓa tana faɗin. "Mama ai da baki wahalar da kanki ba, sai in zo
in ɗauka da kai'na". Ta yi maganar tana kallon kayan fruits ɗin kafin ta ɗago da
kallanta a kan tsohuwar, yau shi ne kallonta na farko da fuskar dattijuwar.

Wani irin faɗuwar gaba ta ji dan taga wannan kamar ba tsohuwar gaske bace, kada ku
manta yaran Momma they're gifted!. Amma sai ta kawar da tinanin nata tare da juyawa
ta koma wajen bed ɗinta, a saman bedside drawer ta ɗaura kwandon tana cigaba da
kallon dattijuwa ta kasan ido, juyawa ta yi tana tafiya har da ɗan ɗingisawa irin
na tsoffi............... Yanzu Fisabilillah my people's ku faɗa mun mutum mai irin
zuciyar Auta meyasa zaka so kasheta? Yarinyar da babu ruwanta, bata da girman kai,
ga girmama manya, bata duba da talaucinsu ko aiki a karkashinsu da suke yi, da
zarar mutum ya girmeta zata bashi girma koma wanene!.

Komawa saman bed ɗinta ta yi ta zauna tare da ɗauko wayarta tana duba sakon
mutuminta, dan koba komai a yanzu kalamansa suka sanyata farinciki, tana samun
annashuwa. ..............Wai ina mijinta Abdussalam ne? Allah sarki ya dawo Dubai,
dan a tinaninsa ta mutu, har ya cire rai da ita, sai dai kuma har yau har gobe
sonta yana a cikin zuciyarsa, kullum sai ya yi mata addu'ar samun rahama, ita kuwa
tana nan ta mance da wani Abdussalam, dan Smart ya ce mata kada ta damu Abdussalam
ya saketa, yanzu ita ba matar kowa bace, so dan haka ta mance da wani Abdussalam ta
fara sabuwar rayuwa!. Amma fa dan ta yi farinciki Smart ya faɗa mata haka, ba wai
dan Abdussalam ɗin ya saketa ba!!!.

Ɗan siririn murmushin da tsawon watanni bai samu gurbi a face ɗinta bane ya
bayyana a fuskarta a lokacin da take karanta saƙon guy ɗin can, hannu ta miƙa ta
ɗauki apple a cikin kwadon fruits da dattijuwa ta kawo mata, wato tana shan fruits
tana karanta saƙonsa abin zai fi sugar. Bakinta kai tsaye ta kai apple ɗin zata
gatsa kenan unexpected taga harbi da kifiya an harbi apple ɗin hannun nata ya faɗi
ƙasa tare da kifiyar. Zabura ta yi ta miƙe tsaye tare da gefar da wayar hannunta
dan ta tsorata sosai.

Cikin natsuwa ya tako izuwa cikin ɗakin, sanye yake da security uniform, wlh
kayan sun yi bala'in yi mashi kyau matuƙa, tamkar dam shi aka yi, uniform ɗin su
Smart ne, ƙasa ya yi da kansa cikin girmamawa ya ce. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe,
ban yarda da inganci apple ɗin bane shiyasa na dakatar dake daga sha, sannan a doka
sai na bincike abinci kafin ki ci, ban bincike bane shiyasa na hanaki ci!". Da kyar
ya iya kai karshen maganar saboda yadda words ɗinsa suke sarkewa, da alama hakan
yana da nasaba da yanayin shigarta, ɗaya ne daga cikin jami'an dake kula da
lafiyarta, mai kawo masu abinci ne!. Ya kai karshen maganar tare da mayar da kwari
da bakarsa ya maƙala a bayansa kamar wani warriors!.

A wani irin slow ta ɗago idanunta ta sauke a kansu. Murya tamkar a mafarki ta ce.
"Ina ainahin mai kawo mana abinci?". Nisawa ya yi, har yanzu kaifin ƙwaƙwalwarta
yana nan bai ragu ba, dik da ciwon da ta sha, tsawon wata uku tana jinya, amma babu
abin da ya sauya!.

Ta yi mashi tambayar ne dan tana son ya sake yin magana ta tabbatar da abin da take
zargi!. "Baya nan, an canzasa da ni ne, daga yau nine zan rinƙa kawo maku abinci".
Cikin wannan sanyin murya tasa dai ya yi maganar!. Kurawa fuskarsa idanu sosai ta
yi, yana sanye da mask a face ɗinsa, iya idanu kawai zaka gani a waje. Ya ɗauki
tsawon wata ukun nan a tare da su, amma yana tare ne da securitys da suke bakin
gate, baya daga ta ciki, shiyasa bata san shi ba, yau ne ganinta na farko da shi da
Smart ya canza shi ya ce ya dawo ciki ya zama mai kula da ita sosai!.

"Ban taɓa tinanin zaka yi mun wasa da hankali ka yi tinanin ba zan iya ganeka
ba! Dik duniya My hero ne kawai zai iya irin wannan harbin da ka yi, saboda shi ɗin
bahago ne, da hagu yake harbi, da hagu yake faɗa, da hagu yake komai, kuma nasan da
cewa tabbas kai ne shi, dan kana shigowa nan zuciyata ta amsa, ta bada bugun da
tsawon wata uku bata buga haka ba, a kansa kawai zuciyata take yin irin wannan
bugu". Ta kai karshen maganar idanunta sun cicciko da kwallah sosai.

"Ranki ya daɗe ban gane a kan me kike magana ba!". Ya faɗa can ƙasa, cikin wannan
sanyin murya tasa dai. Zafafan hawaye ne suka fara bin kuncinta, rasa me zata ce
mashi ta yi yasa ta durkushe gwiwowinta a saman mattress ɗin tare da rushewa da
wani irin kuka mai tsananin taɓa zuciya, kukan da ta ɗauki sama da wata uku yana
cinta a zuciya ta kasa samun damar yin sa sai yau.

Har cikin ransa ya ji tsananin zafin kukan nata, amma sai dai Smart bai bashi damar
ya kusanceta ba, bashi da ikon rarrashinta a yanzu, dole ya daure ya juya zai fita
cikin zafa sabo kukan nata yana taɓa shi, idanunsa a kanta sosai.

HOORAIN!! Ba shakka shi ne, Auta bata yi karya ba, kuma zuciyarta bai buga a karya
ba, soyayyarta a garesa gaskiyace, dole idan ya kusantota ta ji hakan a ranta.
QUEEN OF SURPRISE na ce ku karɓi wannan yau kuma!!.

Tabbas Hoorain yana a tare da ita a cikin wannan gida, kuma Smart ya ɗaukesa daga
kingdom of power tun lokacin da Dr ya ce zuciyarsa ta dai'na harbawa, ya umarci su
Ansar da su yi shiru kada su faɗawa kowa. To bama shi ne surprise ɗin da QUEEN OF
SURPRISE na zo baku ba, babban surprise ɗin shi ne kun san da cewa Zunaira matar
Hoorain ce? A rana ɗaya aka ɗaura auren Smart and Pretty, Zunaira and Hoorain, da
sa bakin Abbonsa kuma, shi ya yi mashi waliyi, kamar yadda uncle Muhammad ya zama
waliyin Auta. Idan baku manta ba Smart ya ce mata ya yi mata alkawarin zata mallaki
Hoorain, a lokacin da King ya ce mashi ya kawo mashi Zunaira, suka ɓoye batun aurar
da ita zasu yi, basu san dik abin da suke yi a gidan Smart yana sane ba, tuni yasan
aurenta za'ayi, wannan dalilin yasa ya ɗaura mata aure da Hoorain tin kafin su dawo
kingdom of power, ita kanta bata san da wannan aure ba, shi kansa Hoorain ɗin bai
sani ba, iya Abbonsa ne kawai ya sani.

Shiyasa kuka ga da ana ta batun bikinta da Abdussalam ya yi banza da su , dan yasan
me ya aikata, ya so sanar da su cewa Auta matar aure ce a ranar da za'a ɗaura aure,
amma lura da ya yi da irin tsanar da King ya gwadawa haɗin Auta da Hoorain yasa ya
dakata da sanar da su ya shiga wani bincike, dan haka a kan auren Hoorain aka ɗaura
na Abdussalam, yanzu Hoorain ne mai mata ba Abdussalam ba, abubuwa sun yi wa Smart
yawa sosai ne a lokacin da Hoorain ya mutu a idon duniya shiyasa ya ja gefe yana
kallonsu yana wani aikin na daban, a nan ne ya fara binciko tarihin maman Hoorain
da King, wannan dalilin yasa ya dakata da barin Hoorain da Auta su yi zaman aure,
sai ya bar Hoorain a Paris ya bar Auta a kingdom of power.

Time da ta ji labarin Hoorain ya mutu ta suma ya dawo da ita Dubai, da ya sanar da
Hoorain hankalinsa ya tashi sosai, har kuka ya yi mashi a kan ya barshi ya zo ya
ganta, wannan dalilin yasa ya sanya shi ya yi shiga irin na jami'ansu dan ya biyosu
su zo wajenta ya ganta, da ya zo kuma ya rinƙa haɗa Smart da Allah a kan ya barshi
ya kasance a gidan, ya yi mashi alkawarin ba zai taɓa bari ta ganesa ba, sanin irin
karfin son da yake yi mashi yasa Smart ya ce Hoorain ya kasance da securitys dake
bakin gate kada ya zo ciki, dan kada a samu matsala, a hana Hoorain yana samun
damar ganinta daga nesa, sau da dama tana tsayawa a jikin window tana kallan
harabar gidan, ta nan yake ganinta.

Yau kawai da safe Smart ya ce Hoorain ya koma mai kula da ita a cikin gida, wancan
jam'i dake kula da ita kuma y koma bakin gate, har yanzu da nike yi maku magana
Hoorain bai san Auta matarsa bace, kamar yadda ita ma bata san shi ne ainahin
mijinta ba, sannan bayan Smart, commander, uncle Muhammad babu wanda ya san da
wannan magana.

Abin da Smart yake gudu shi yake son faruwa ga shi da kallo guda Auta ta gane
heronta, wai a hakan ma ya ja mashi kunne a kan kada ya yi wani motsin da zai sa ta
gane shi, kada kuma ya yi mata magana, sannan idan ta kama dole ya yi magana to ya
canza murya yadda ba zata gane ba....... Smart yana so ne ya gama bincike, ya
tabbatar da Hoorain ɗan waye ne a tsakanin King and commander kafin ya basu damar
sanin sun mallaki juna, shiyasa yake yi masu iyaka a yanzu. KAI JAMA'A KU TAFAWA
SMART, YA CIKAWA AUTA ALKAWARINTA YA TSAYA MASU SUN MALLAKI JUNA, SAI DAI KWAI
CAKWAKIYA MAI GIRMA A GABA, YANZU HOORAIN DAN WAYE NE? SHI NE BABBAN TASHIN
HANKALIN, KADA AZO YAZAMANA YAYANTA! DOLE SMART YA NESANTASU DA SANIN CEWA
MA'AURATA NE SU, SANNAN KUMA YA SU KING ZASU JI, BA SHAKKA SMART YA CIKA ƊAN HALAK.

(Wai an ce maku a banza na bar Hoorain ya shanyewa Auta baki ne?🥱 To matarsa ce
halacɗinsa, a book ɗina ai ba'a taɓara kun gane ai? Sai idan akasi aka samu misali
kamar Leesharh da Ramish wanda su kunga kaddara ce ta afka masu, amma haka kawai a
book ɗina ba'a lalata gaskiya, ina ƙoƙarin tsayawa tsayin daka wajen ganin na
tsabtace rubutuna, yauwa idan da aurene a sha shagali!.)

A gaggauce ya fice daga ɗakin. Tana ɗago kai taga baya nan ta yi saurin dirowa
kasan bed ɗin, a lokacin har anfara kiraye kirayen sallar isha'i, waje ta nufo da
gudu dan ta bi bayansa, saboda wlh tasan shi ne, heronta ne. Shi kuwa yasan zata
biyosu dama, sai ya ɓuya mata a in da ba zata gansa ba, dan kada ta ganesa ya karya
alkawarin da ya ɗaukawa Smart yaja Smart ɗin ya mayar da shi Paris ya sake
nesantasu, gara mashi a nan koba komai yana samun damar ganinta bawan Allah, shi ma
fa ya sha jinya, almost 1 month yana fama, sai dai Smart ya ce mashi ya yi hakuri
Zunaira bata yi aure ba, an warware auren, dan haka ya kwantar da hankalinsa, sai a
sannan ne ya samu natsuwa!!. QUEEN OF SURPRISE ina miƙo gaisuwar gareku my
people's.....….. 🙌💘🔥


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬
63

Waje ta nufa da gudu domin ta duba shi, tamkar wadda bata a cikin hayyacinta, dik
ta firgice tana wani irin kuka mai tsuma rai, dama a kusa zuciyar take, kiris take
nema!.

Daga in da yake laɓe ya ji ba zai iya barinta ta fita waje da irin wannan shiga
dake jikinta ta nufi securitys ɗin nan ba, kun san shi da shegen kishi, ina ai ba
zai iya daurewa ba. Kasa cigaba da ɓuya ya yi, tana dab da buɗe kofar parlour ta
fita ya yi gaggawar nufarta. Ta baya ya sanya hannu ya toshe mata baki game da rufe
mata idanun da ɗayan hannun nasa. Baya ya yi da ita kai tsaye sai bedroom ɗinta.
Ciki ya mayar da ita, bai saketa ba har suka kai wajen bed, yana zuwa ya zaunar da
ita tare da zame hannunsa, sannan cikin sanyin muryan nan yasa dai ya ce. "Kada ki
sake fita ko parlour ne!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa zai fita.

Cikin zafa ta miƙe tsaye, hawaye tamkar an buɗe tap an kure mashi gudu, da kyar
voice ɗinta yake fita ta ce. "In dai baka son in fita waje to ka bayyana mun kanka
matsayinka na herona, in kuma ba haka ba ka cigaba da ɓuya to tabbas ba iya waje
ba, gidan dikka zan bari koma duniyar bakiɗaya, dan ban ga amfani zamana a raye
bama, ace kana numfashi kuma muna waje ɗaya sannan kana guduna! For what reason?"
Ta jefa mashi tambayar a yayin da zuciyarta tamkar zai yi bindiga saboda tsananin
tashin hankali da damuwar abin.

Dik abin da suke yi Smart yana kallansu, dan idan baku manta ba ya zuba secret
cameras sosai a gidan ta in da babu wanda zai san da su, so dik abin da yake faruwa
yana gani. A lokacin ya kammala zubawa Pretty iskancinsa son ransa, ya kwanta yana
jinta tana kuka ƙasa ƙasa, ya ce idan ya ji bakinta tana kuka sai ya sanya wuta ya
konasa, shi ne yasa take kuka ƙasa ƙasa dan kada ya ji!.

Banza da ita Hoorain ya yi ya cigaba da tafiyarsa, zuciyarsa tamkar zata yi
bindiga shi ma.
"My Hero". Ta ambata cikin wani irin murya mai matuƙar raunin da komai taurin
zuciyarka sai ka ji ta ratsaka, shi kansa Smart wani irin tausayinta ne ya kama shi
sosai, hakan yasa ya fita daga side na camerar tasu ya shiga massage na wayarsa,
dama da phone ɗinsa ya yi connected na cameras ɗin.

Cak ya dakata da tafiyar da yake yi jin sunansa da ta kira. Saukowa kasan bed ɗin
ta yi, ta tsaya a wajen, cikin rawar murya ta ce. "Dama akwai ranar da zata zo kana
raye ina kuka ka nuna baka san ina yi ba? Dama dik alkawarin da ka mun ba gaske
bane? Dama wasa kawai kake yi mun? In kuwa haka ne meyasa ka bari na kamu da sanka
har haka? Meyasa ka cutar da zuciyar da bata san komai ba face kaunarka? Meyasa a
dik duniya ni kaɗai ka zaɓi ka cutar? Menayi maka my Hero? Wannan shi ne sakamakon
son da na nuna maka kenan? Abin da zaka saka mun da shi..............". Kasa ƙarisa
maganar ta yi saboda wani irin kululun bakinciki da ya toshe maƙoshinta, cikin wani
irin tari mai sauti ta fara ƙoƙarin cigaba da maganarta, sai dai ina, ta gagara yin
hakan, sam sam voice ɗinta yaki fita, hannu tasa ta dafe saitin wuyarta tana cigaba
da tari mai sauti wanda sai da ta sanya shi juyowa babu shiri.

A dai'dai wannan lokacin wayarsa ta yi kasa alamar shigowar sako. Hannu yasa cikin
aljihunsa ya ciro wayar, ganin message na Smart da ya yi saving numbersa da babban
yaya ne yasa ya yi gaggawar buɗe sakon.
"Ka rarrasheta kawai tin da ta rigada ta ganeka, but kada ka yi crossing line
dana ja maka!". Smart ba zai iya jure ganin ta a irin wannan hali ba, shiyasa ya
ce ya rarrasheta kawai!.

Shi ne abin da saƙon ya ƙuntsa, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a
hankali, dama ko Smart bai yi mashi massage ba, ba zai taɓa tafiya ya kyaleta a
wannan hali da take a ciki ba, dama dole zai tsaya ya rarrasheta, dan zuciyarsa ba
zata iya jura ba, yanzu ma da kyar ya danne. Tin da yake a rayuwarsa bai taɓa danne
wani abu mai tsananin azaba ba irin wannan tashin hankali da ta shiga! Idanunsa sun
kaɗa sun yi jajir kamar wuta!.

Cikin natsuwa ya taka ya nufi in da take, mayar da wayarsa a cikin aljihunsa ya yi,
a gabanta ya tsaya tare da yin ƙasa da kai, cikin natsuwa ya ce. "Am so so sorry
Hoonaira, ba zan sake kwantanta makamancin hakan a gareki ba, dan Allah stop all
this, please kin ji?". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa ya riko nata
dake wuyarta tana tari. Kara jaddada mata da tuba yake yi ya yi. Ina ai babu bakin
magana, ta rigada ta kure maganarta, yanzu idan ta buɗe baki zata iya haɗiyar
zuciya!.

Ganin hakan yasa ya saki hannun nata tare da nufer dispenser ya ɗebo mata ruwa mai
sanyi sosai a cikin cup, sannan ya dawo in da take a tsaye. Miƙe mata ruwan ya yi a
kan ta sha, sam baya son taɓa jikinta saboda yasan ba matarsa bace, shiyasa yake
yin ɗan nesa nesa da ita. Karɓar ruwan ta kawo hannunta zata yi, sai dai ina,
kakkarwa sosai hannunta yake yi wanda yasan ba zata iya rike cup ɗin ba, hakan yasa
ya matsa dap da ita tare da sanya mata cup ɗin a baki a kan ta sha!.
A hankali ta fara karɓar ruwan tana sauke wani irin ajiyar zuciya mai ɗauke da
sirrika dayawan da take buƙatar lokacinsa domin buɗe mashi waɗan nan sirrika.
Lokacin guda Smart ya ji soyayyarsu ya yi matuƙar birgesa, take ya ji gabaɗaya
jikinsa ta motsa, har ɗan lumshe idanunsa ya yi irin abin ta shigesa yadda yakamata
ɗin nan.

Tana gama shan ruwan ta faɗo saman massive chest ɗinsa tare da rushe mashi da
wani sabon kukan. Ai ɗauke wuta ya yi na wasu ƴan sakanni, lokaci guda ya jisa a
duniyar mercury, ƙasa motsawa ya yi bare ya rabata da jikinsa, wani irin azabbabben
shock ya ji tin daga tsakiyar kansa har izuwa tafun kafarsa, uhm abin ba'a magana.

"Why? Why zaka mun haka? Wani laifi na yi da na cancanci irin wannan hukunci?
Meyasa? Meyasa?". Daddaɗar muryarta ne ya daki dodan kunnensa yasa ya farfaɗo daga
duniyar tinanin da ya afaka. Ta yi maganar kuma tana riko rigarsa wajen massive
chest ɗinsa. Kasa magana ya yi, sai dai ya kai hannunsa ya riƙo hannunta dake a
saman kirjin nasa, gam ya damke hannun nata tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita!
Shiru dai bai iya yin magana ba!!.

Lokaci guda Smart ya ji sa a duniyar samar iska, juyo da kallonsa a kan Pretty dake
kwance tana kuka ya yi, shaukin soyayyar su Auta ya ɗebesa har bai san lokacin da
ya janyota jikinsa ba, wai shi ma zai yi irin na Hoorain ya rarrasheta, sai ya
shiga ce mata. "Ya isa haka, ki yi shiru." Daga haka bai san me zai sake cewa a
gaban ba, sai ya yi shiru yana kallan face ɗinta, cigaba da kukanta ta yi tana
shessheƙa. A ransa ya ce ko kukan ma take yi kara kyau take yi, tamkar ita ta yi
kanta. Ya kai karshen zancen zucin nasa tare da kai hannunsa ya shafi lallausan
lips ɗinsa da suka tura pink sosai saboda kukan, sai wani ɓari suke yi tamkar mai
jin sanyi, hancinta ya yi jajir, kazalika kumatunta ma ya yi jajir.

Ɗan jan dogon numfashi ya yi tare da saukewa a hankali kafin yasa hannu ya ɗan
shafi lallausan kumatunta!. Cigaba ta yi da kukanta tamkar bata san yanayi ba, haka
ya bi ya rinƙa tattaɓara har lokacin da barci ya ɗauketa a jikinsa, ajiyar zuciya
ya sauke a fili ya ce dai gobe zaki yi azumi dik rigimarki!.

Shi kuwa Hoorain yana san ya yi mata rarrashi mai kyau, amma yana jin tsoro saboda
da kunnuwansa kuma da idanunsa ya gani kuma ya shaida ita matar Abdussalam ne, dan
haka sai ya rabata da jikinsa ba dan ya so ba, ya rarrasheta tare da ce mata ta
zauna kada ta sake fita yana zuwa. Yana fita Smart ya yi mashi sakon a kan ya
shirya kayansa yau zai dawo kingdom of power, saboda Auta ta rigada ta ganesa, kada
azo a samu matsala, kar su jiƙa mashi aiki ba tare da ya gama bincikensa ba, su yi
abin kunya, ai kunga da kunya idan bincike ya bada cewa yaya da kanwa ce su ɗin, so
dole ya rabasu.

Sosai Hoorain ya ji zafin hakan, amma bashi da zaɓi, dole ya bi maganar babban yaya
idan yana son cigaba da kasancewa cikin farinciki. Dole ya haɗa kayansa a ranar ya
koma kingdom of power, ita kuma Auta Smart ya sanar da ita ta yi hakuri Hoorain zai
dawo gareta nan da ɗan lokaci, ta kasance cikin farinciki, kuma ya basu dama su
rinƙa yin waya da juna.

Uhm lokacin da Hoorain ya dira a kingdom of power babu wanda bai girgiza ba,
musamman ma King da shi ya gama saddakarwa Hoorain ya mutu, ya ji zafin cetan ransa
da Smart ya yi, hakan yasa ransa ya ɓaci matuƙa da har ya fusata ya ce Smart ya
wuce ya koma Paris, shi kuma Smart ya ce sai ya gama abin da ya kawosa, dama shi
bai zo zama a kingdom ɗin ba, dan haka idan ya kammala dole zai koma in da ya fito,
dan a can ya fi wayo.

A wannan dare dai King da uncle Abbas game da Akka suka yi zaman meeting su uku
wanda babu uncle Jahiz a ciki, a nan ne Akka ta ce. "Idan muka aura mashi Sareena
ina da yakinin zata iya mantar da shi dik wannan bincike da yake son yi, kuma ina
da tabbacin zata iya sauya shi ta yadda zai dawo yana jin maganarmu".

Uncle Abbas ne ya karɓi zancen da cewa. "Ina fatan hakan ya kasance, in ba haka
ba tabbas zamu shiga bala'in da gara mutuwa a kanta, zai zama dik abin da muka yi a
baya ya tashi a banza".......... Shi dai King ya yi ƙasa da kansa bai iya sake cewa
komai ba! Kun san wani irin zulumi King yake a ciki? Batu ne a kan Hoorain! Kun san
da cewa su Akka basu san alaƙar dake a tsakaninsa da matar commander ba? Shi ne
tashin hankalinsa na biyu bayan batu kan Ramish, yana tsoron gaskiya ta bayyana,
mutumcinsa zata zube, kuma ai yanzu ya tuba.

Su Akka kuma suna cikin zulumi ne a kan batun Ramish, suna tsoron Smart ya bankaɗo
gaskiya, dan dikkansu abin ya shafa!! Shi ne fa suke san aura mashi Sareena wai dan
su rufe mashi baki..... KAI SMART ƊAN DUNIYA NE, YA HANA SU AKKA SAKAT YA TAFI YANA
SOYAYYARSA DA PRETTY!! WATO DIK SUN SAN KOMAI DAKE FARUWA! UHM AKWAI KALLO A GABA
WLH!.

Ganin King ya yi shiru yasa Akka ta ce. "Zuhair lafiya kuwa?". A hanzarce ya
girgiza mata kai alamar babu komai, shiru suka zuba mashi idanun suna kallonsa, da
yake sun san halin da suke a ciki sai suka ce kila shi ma fargabar abin da Smart
zai iya tonowa ne yasaka shi a cikin damuwa, hakan yasa suka hau rarrashinsa suka
tausansa tare da cewa kada ya damu da Smart ya auri Sareena komai zai canza, ita
Sareena tana jin maganarsu, dan haka zata zama wadda Smart yake jin maganarta In
Sha Allah!.... My people's kuna ganin haƙarsu zai cinwa ruwa kuwa? Anya zasu iya
sanya Sareena ta zama wacce Smart yake jin maganarta kuwa? Muje dai zuwa.

Haka suka yi wannan zaman meeting suka tashi ba tare da kwakkwarar mafita ba, da
alama uncle Jahiz bai san me yake faruwa bane yasa babu shi a wannan zama.

Ita kuwa Mammie tana can tana shirya yadda zata ɗauki Fanan daga gidan ba tare da
kowa ya nemeta ba,

Please Login or Register in order to submit comment