Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 57 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya baka umarnin da zuciyarka bata so, abin
akwai ciwon da sai mai juriya zai iya dannewa, dan haka shi ya gagara dannewa
saboda zafin zuciya.

Gudun kada ya ɓata ran mahaifiyarsa yasa yana shiga bedroom ɗinsa ya ɗauki wayarsa
da key ɗin motar da Jaish ya ɗaukosa daga airport ya fito, suna parlon har lokacin
momma tana bawa su Akka hakuri ya zo ya capki hannun Auta dake tsaye kusa da
Pretty, sun rike hannun juna suna kallan wannan tashin hankali da yake faruwa, bai
sake yin magana da kowa ba kuma bai bi ta kan kowa ba ya ja hannun Auta suka fice
daga parlourn.

Allah sarki zuciya, a gaggauce King ya bi bayansa domin ya ji ina zai je a wannan
daren haka shi da bai san ko'ina a ƙasar ba?. Momma ta yi mamakin ganin King ya bi
bayansa, bata yi zatan zai yi saurin nuna zallar soyayyar da yake yiwa ɗan nasa a
fili a cikin ƙankanin lokaci haka ba, ta manta da cewa ita zuciya bata da ƙashi,
idan ta so abu dole a bata ko a samu matsala.

Ko da King ya fito bai same shi a wajen ba, a hanzarce ya nufi parking space ko
zai same shi, sai dai kafin ya isa parking space ɗin sai ya hango ɗaya daga cikin
motocin Jaish ta kutsa waje warriors sun buɗe mashi gate. Sosai King ya shiga
damuwa, da sauri ya koma ciki domin ya sa momma ta kira mashi shi ya dawo gida kada
ya ja mota yana cikin fushi a samu matsala.
To a tinaninku ina Smart zai tafi a cikin wannan dare? To mu je zuwa dai.

••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A ɓangaren Dubai kuma, Ramish ya aminta ya baiwa Leesharh jini bisa umarnin Smart,
dan ya yi mashi massage kamar yadda ya saba yi mashi, ya umarcesa da ya bata jini
kuma ya kula da ita sosai har ta samu lafiya, domin da ita kaɗai zasu yi amfani
wajen kama masu nikaf, ita ce kaɗai zata zama sanadiyar kamasu, dan tasan komai
kuma tana da hujjijo a kansu, komai yana da sanadi, dan haka ita Leesharh ita ce
sanadin da zasu yi amfani da ita wajen kamasu cikin ruwan sanyi, dan mutanen shegun
kai ne, dole a kara masu tarko.

Wannan dalilin yasa Ramish ya aminta ya bada jininsa, (sorry ranan a wajen rubuta
jinin Leesharh zan rubuta O negative na rubuta O positive, typing errors aka samu,
sai daga baya da ina sake duba page ɗin na gani, so O negative take.)

Yanzu yana kula da lafiyarta sosai, a rana yana daurewa ya leƙa in da take sau
ɗaya ya tabbatar tana cikin kulawa mai kyau, kwanaki sun suɗe amma har yanzu bata
farfaɗo ba, sai dai jikin nata yana ta kara kyau tana samun lafiya yadda yakamata.

Wannan kenan abin da yake faruwa a Dubai, mun ɗan ji halin da suke ciki, bari mu
leƙa wani ɓangaren ma mu san a wani hali suke ciki, dan na lura rikicin dake cikin
kingdom of power ba zai kare ba, yanzu ma wasan zai fara, so dole in rinƙa
takaitawa muna laƙa wasu ɓangarori dan jin yadda ake ciki.

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Bayan wasu ƴan kwanaki.

Abubuwa masu ɗan yawa sun fara a cikin waɗan nan kwanaki da suka shuɗe wanda suka
haɗa da jinyar da Sweetie ta sha bayan dawowarta daga wajen wutar can da Black
Tiger ya so konata Allah ya nufa tana da sauran shan ruwa a gaba, Allah ya ɗaurata
a kansa ya sanya mashi ɗigon tausayinta a ransa, ba komai yasa ya tausaya mata ya
barta ba kuma face yadda ta tuna mashi da akwai ranar da zai faɗi abin da ya aikata
wato ranar lahira kenan, waɗan nan kalaman nata sun sa ya ɗan ji kamar zuciyarsa ta
ɗan yi sanyi wanda hakan ya ja ya kyaleta.

Abu na biyu da ya faru a kwanakin da suka shuɗe sun haɗa da rokar Black Tiger da
Ronnie ya yi a kan ya sanya Sweetie makaranta tun da tana da ilimi kuma tana da san
karatu ga ƙwaƙwalwa. Da yake shi Black Tiger idan ba aikinsa bane ya biyo ta kanka
sam bashi da mugunta, sai ya aminta a kan Ronnie ya yi mata komai da ya dace.

Hakan kuwa aka yi, Ronnie ya shige gaba wajen yi mata komai yadda yakamata.

A ɓangaren ita kuma Sweetie, sabon walaƙanci yarinyar nan ta karo, bare ma yanzu da
Ronnie ya koya mata yadda zata yi amfani da magic ɗinta, ohohoho, yanzu tana bawa
Black Tiger ciwon kai, ga shi ba yadda ya iya da ita, idan ya yi mata magic ita ma
ta yi mashi, ta saka shi a gaba bata san ta barshi ya zauna lafiya, yana aikin
neman Pretty dan yasan Spender yana hannunta a yanzu, ita kuma Sweetie tana
distracting ɗinsa a nan, tin ranar da Sweetie ta ƙalubalancesa a kan ya nemo
Spender da kansa daga lokacin ya shiga nema, a nan ne ya gano yana hannun wata
yarinya mai kama da Sweetie wato Pretty kenan.

Yanzu haukar neman Pretty yake yi, ya fita harkar Sweetie dan yanzu bata da amfani
a wajensa, ba dan Ronnie bama ai da Black Tiger ya jima da kasheta an rufe babinta
ya nemo Pretty ya karɓi Spender, so Ronnie ya ce yana santa, kunsan shi ya nuna
yana san su Floris ma yasa aka kawosu empire ɗin, a takaice dai yanzu Sweetie zaman
Ronnie take yi a birnin, amma ta takurawa Black Tiger dan tana san ya musulunta,
tana san kuma ta shiga jikinsa sosai ta yadda ko da ta kuresa ta ja yasa a kureta a
gari to da kansa zai sa a dawo da ita.

Kun san idan mutum yana yawan shiga harkarka ko baka so ko kana so, to dik ranar da
aka ce babu wannan mutumi sai ka ji wani irin a cikin ranka, irin abin da take san
yi wa Black Tiger kenan. Kuma dayawan lokuta Allah yana ɗaurata a kansa tana tsira
ba tare da ya yi mata hukunci ba.

••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

Zaune Ronnie yake a bakin bed ɗinsa yana kallan kyakkyawar fuskar Sweetie dake zuba
barci, tana shirya cikin wani kyakkyawan sleeping dress, tin da ta yi sallar asuba
take zuba barci saboda gajiya da ta yi, daren jiya bata yi barci ba, ta bi Ronnie
wajen casunsu da suka saba, har karfe 1 na dare suka dawo, da suka dawo kuma sai
suka zauna zaman karatu har karfe 3, tana koya mashi karatun addini da dik abin da
yakamata ace musulmi ya iya.

Abin da yasa yanzu take yarda ta bi Ronnie ko'ina har church ɗinsu, saboda tana san
ta shiga jikin mutanen birnin sosai, ta ga yanayinsu, ta san karfin tsaurinsu a kan
addininsu, ta san zasu iya karɓar musulunci cikin sauki ne ko kuma sai an sha
wahala, wannan dalilin yasa take yarda ta je ko'ina dan da'awarta.

Yanzu haka wajen casun da suka je jiya ta yi nasarar jan ra'ayin wasu ƴanmata guda
biyu da suka yaba da kyan halinta har suka ce suna san kulla abota da ita, da
taimakon Ronnie ta samu suka amsa zasu musulunta a sirrance suma, kunga kuwa ashe
shiga cikinsu da take yi babban nasara ne.

Yau zata fara zuwa school, amma ta kwanta sai barci take zubawa. Ronnie yana san
tashinta kuma yana san barinta ta huta.

Zuba mata idanu sosai ya yi yana kallanta, sai yaga alamar kamar zara zaran
eyelashes ɗinta suna motsawa, ɗan blinking eyes ɗinsa sau biyu ya yi ya sake kafesu
a kanta, a nan ne ya fahimci idanunta biyu bata yi barci ba. Wani irin cool
murmushi ya saki kafin ya ce. "Maza tashi ki shirya zuwa school".

Miƙa ta ɗan yi tare da waro kyawawan fararen idanunta, ganin yana murmushi ya
sanyata sakin cute smile ita ma wanda sai da tasa Black Tiger dake kallansu ya ji
murmushin nata ya burgesa. Hannunta ta kai ta saƙalo wuyan Ronnie kafin ta miƙe
zaunta.

"My brother waye ya faɗa maka ba barci nike yi ba?". Ta jefa mashi tambayar tana
kai hannunta saman kumatunta, irin mutum ya ɗan tallabo kumatunsa haka.

Miƙewa tsaye ya yi tare da riko hannunta. "Tashi ki shirya, idan kin gama shiri zan
faɗa maki ya aka yi nasan idanunki biyu". Ya kai karshen maganar tare da janyota,
tana yi mashi yauki da yanga ta sauko kasa, a hankali ta fara turo baki tana gallah
mashi hararar wasa, bai wani damu ba ya ja hannunta izuwa toilet. Fitowa ya yi ya
kyaleta domin ta yi wanka.

Shi yanzu ba school yake zuwa ba, dan ya gama saura bautar ƙasa, sannan kuma
akwai partyn da zasu yi wanda aka ɗaga, da last week zasu yi sai aka ɗaga sai next
week. Da kansa ya fitar mata da uniform ɗin nata, har bakin toilet ya je ya tsaya
tare da yi mata knocking, kanta ta ɗan leƙo hannunta dik kumfa. Miƙa mata uniform
ɗin ya yi an hi iron ɗinsu sun yi kyau. A maimakon ta karɓi uniform ɗin sai ta
shafa mashi kumfar dake hannunta a face ɗinsa, siririn murmushi ya saki, da a baya
ne lokacin da yake krista da ya shiga cikin toilet ɗin, amma yanzu Alhdulillah
yasan wasu hukunce hukuncen na muslunci, sai kawai ya yi murmushi yana faɗin zaki
fito ne ai.
Da biyu Sweetie ta yi mashi hakan, dan ta tabbatar karatun da take karantar da shi
ya nutsa cikin kwakwalwarsa ne ko dai ɓata lokacinta take yi, ashe kuwa ya nutsa
yadda yakamata kuma yana amfani da abin da ya karanta.

Karɓar uniform ɗin ta yi ta koma ciki tana cigaba da murmushin ta yi nasara ita
ma. Shi ma komawa bakin bed ya yi yana murmushi haɗe da jinta a ransa tamkar ƴar
uwarsa na jini.

Wlh yadda suke gudanar da rayuwa ita da Ronnie haƙiƙa yana matuƙar burge Black
Tiger, Ronnie bai taɓa kawo yarinyar da suka shaku suke wasa tamkar yaya da kanwa
ba irin Sweetie, ga shi yanayin face ɗinsu yana shege, wani irin farinciki na
musamman Ronnie yake yi idan yana tare da ita, hakan yasa Black Tiger yake raga
mata sosai, saboda tana sanya ɗan ƙaninsa a cikin farinciki.

Wayarsa Ronnie ya ɗauko da nufin ya fara latsawa kenan dan ya gaji da zama shiru,
sai ya ji an turo kofar toilet. Da sauri ya kai kallonsa wajen. Ai bai san time ɗin
da ya miƙe tsaye ba. Ya ilahi Sweetie ta yi masifar kyau a cikin wannan uniform
ɗin. Mini skirt ne da bai gama rufe mata santala santalan cinyoyinta ba launin ash
colar, sai riga mai dogon hannu launin white color, ta ɗaure gashin a tsakiya ta
saki jelar har baya, yau bata wanke kanta na dan daren jiya ta wanke.

Sai kyalli gashin nata yake yi sosai, abinku da golden white, kun san yana kyalli
sosai. Ga sock ɗinta white color sosai. Haba ai Ronnie bai san time ɗin da ya fara
santin kyan da ta yi yana yabawa ba. Kashe mashi idanu ɗaya ta yi kamar yadda yake
yi mata, sannan ta kariso gabansa tana tambayar ta yi kyau?.

Wlh Black Tiger yana iya ɓata awa guda yana kallan rayuwar Sweetie da Ronnie,
gwanin ban sha'awa da burgewa, yanzu ma haka zuba masu idanu ya yi yana kallansu.

"Haba my lovely sis, ai faɗe ma ɓatawa, kinsan ke makurar kyau ce". Ya faɗa yana
buɗe mata tafin hannunsa. Buɗe nata tafin hannun ta yi kafin ta ce. "Ban mu sha my
brother".

Tafa hannu suka yi kafin su kai tafin hannunsu saman ɗan bakinsu suka manna mashi
sumbata sannan suka hurawa juna, lokaci guda suka saki ƙayatattcen murmushi kafin
su rungumi juna, abin gwanin birgewa, na tabbata ba iya Black Tiger kawai ba, dik
wanda ya gansu ba zai so ya dai'na ganinsu ba, saboda sun haɗu, idan suna tare suna
bata show.

"Bro bari in je wajen big bro ina zuwa". Ta faɗa tana raba jijinta da nasa,
yanayin tattarar skirt ɗinta gwanin birgewa, ya sha tattare sosai har ya ɗan yi
kamar umbrella.

Bai tambayeta me zata je yi a part na Black Tiger ba, sai kawai ya bita da to, dan
yasan ko ya tambaya ba faɗa mashi zata yi ba. Da sauri ta nufi waje, shi kuma ya
shiga dressing room dan ya ɗauko mata school back ɗin nata da dik abin da ya dace.

Nima na haɗa kayana na tafi shan maltina.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Yanzu ita ma ta gama iya buɗe kofar Black Tiger, ko ya rufe da magic sai ta buɗe ta
shiga, shiyasa ya daina wahalar da kansa dan rufewa ma, ya kyale masu kofar a buɗe
kawai.

Ciki ta shigo yana dai tsaye a gaban mirror bai motsa daga in da yake ba, a
tsakiyar ɗakin ta tsaya tana kallansa yadda ya yi kyau cikin wani irin shiga na
musamman, ga wani zazzafar long coat da ya ɗaura a saman kayansa saboda sanyin da
aka tashi da shi yau, ya yi kyau matuƙa.

A dik lokacin da ta kalli Black Tiger jaruminta na farko wato Kamran shi kawai
take tinawa, a kullum tana tinaninsa fin sau a kirga, da shi take kwana take kuma
tashi, burinta ɗaya ta gansa, a kullum sai ta yi wa kanta wasu tambayoyi kamar
haka, a ina yake? A ina zata gansa? Yakamanninsa suke? Shin yana tinata ne ko ya
manta da ita? Meyake yi a halin yanzu? A koda yaushe sai ta yi wa kanta waɗan nan
tambayoyin da bata da amsarsu bata kuma da in da zata sami amsarsu, wata rana har
kuka take yi idan ta tunasa. Amma har yau bata iya sanar da Ronnie soyayyar Kamran
dake ranta ba, tabar sirrin a ranta.

Meyasa idan taga Black Tiger take tina Kamran? Shin suna da wata alaƙa ne ko
dai kawai a ranta ne take jin kamar girma da cikar Kamran ya kai Black Tiger dan
bata taɓa ganinsa ba?.

Cikin sanyin murya ta ce. "Big bro good morning".
Shiru bai amsa mata ba, bai ma yi kamar zai amsa ba, yana cigaba da dudduba
abin da yake ra'ayi zai fita zuwa fada, anjuma za'a buɗe katafaren hospital da ya
ginawa Ronnie, za'ayi taran partyn buɗe hospital ɗin, ba ƙaramin dukiya Black Tiger
ya zubar a wannan taron ba, an shirya abubuwa sosai, and dik a cikin Daularsa
za'ayi, kuma hospital ɗin ma a cikin Daular tasa take.

So yana da abin yi sosai yau, shiyasa ma yau dressing ɗinsa ta fita daban da
kowacce rana, yau ranar Ronniensa ne.

Bata damu dan bai amsa maganarta ba, sai ta sake cewa. "Big bro na yi kyau?". Tana
magana kirjinta na harbawa da karfi karfi, dan tasan bata taɓa zuwa wajensa ta fita
lafiya ba, kullum sai sun yi dirama ɓatacciya kaman wasu tom and Jerry.

Nan ma shiru bai amsa ta ba, kuma dama tasan hakance zata biyo bayan, dan sai ka yi
mashi magana sama da guda uku bai amsa ko ɗaya ba, ba wanda yake sanya shi yin
magana sai time da ya yi ra'ayi.

Cikin natsuwa ta tako ta nufi in da yake tsaye, jingina bayanta da jikin drawer
mirror ta yi, yazamana suna fuskantar juna, kallansa gabaɗaya yana a kan mirrorsa
tamkar bai san da wata halitta a wajen ba. Shiru ta ɗan zuba mashi idanu na ƴan
sakanni kafin ta sanya hannunta cike da tsoro ta shafi kyakkyawan bakin gashin dake
kwance a gefe fuskarsa. Hannun nata har yana kerma saboda tsoro.

Hakan yasa dan dole ya dawo da kallonsa a kanta, wannan yarinya ta zame mashi
kashin wuya, ya faɗa a ransa yana kallonta. Wlh Sweetie ta san kan duniya, ido ɗaya
ta kashe mashi kafin ta ce. "Big bro na yi kyau?".

Zaman lafiya yau yake so, dan yana da abin yi masu muhimmanci a gabansa, dan haka
sai ya ɗaga mata gerarsa guda ɗaya alamar yes ta yi kyau. Ajiyar zuciya ta sauke
yau karo na farko ya amsata dik da bai buɗi baki ya yi magana ba, amma ta ji daɗin
abin da ya yi.

Ita ma ta fahimci yau ya yi so sillent over, da alama akwai abin da yake gabansa
sosai, dan haka ba zata ja tsokana sosai ba, saboda idan ta ce zata ja sosai zai
iya yi mata illah dan yana aiki, yanzu tagama karatarsa tsab, tasan lokacin da zata
ja shi da tsokana ba zai cutar da ita ba, wato idan ta same shi baya yin aikin
komai, nan kam sakan jiki take yi ta hakura mashi.

Hannu ta sake kaiwa zata shafi sajensa da nufin ta yi mashi bye bye. Carap
ya capki hannun nata da hannunsa ɗaya, dan idan tana taɓa shi ɗin nan tana sanya
mashi kasala. Kallon juna ido cikin ido suka yi ba tare da kowannansu ya furta word
ba. A hankali ya saki hannun nata tare da yin ƙoƙarin juyawa ya cigaba da abin da
yake yi.

Ita kuwa a ranta ta ji lallai kafin ta tafi sai ta sake taɓa sajensa, dan
haka yana saketa ta sake kai hannun zata taɓa sajen nasa. A wannan gaɓan wuyarta ya
damko da hannunsa tare da janyota ta matso dap da shi har suna iya jiyo sautin
numfashin juna.

Dik da ya shake mata wuya bata damu ba, dan ta samu abin da take so ne, wato ya
matsar da ita dab da jikinsa kenan. Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman lion chest
ɗinsa, ɗayan hannun nata kuma ta shafi gefen face ɗin nasa. Tabbas ta ji shakar da
ya yi mata, amma ta daure bata nuna alamar ta ji ba.

Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Ke bakya da tsoro ne?". Cike da mamakinta ya yi
maganar, har ga Allah tana bashi mamaki yadda bata nuna tsoro, kun san irin haka
dole ya bawa mutum mamaki, wannan rashin tsoron da take nunawa yasa har yana jin
kamar tana burgesa, yana san mutum mai confidence.

Ɗan ɗaga idanunta sama ta yi ta yi fari da su, hakan ba ƙaramin kyau ya kara yi
mata ba, ga shi ya tsareta da idanu, shi kansa yasan ta kara kyau matuƙa yadda ta
yi da idanun nan nata, amma bai nuna alamar yaga ta yi hakan ba, sai ya kara ɗaure
fuska sosai.

Cikin wani irin sexy voice ta ce. "E to ban taɓa yin tinani a kan jin
tsoron ba, amma tin da ka yi magana yanzu zan yi tinani in ga ko ina ji ko bana
ji". Tana magana tana jujjuya idanu kyanta na kara bayyana matuƙa, ga shi suna
kurkusa da juna sosai
Ya fahimci iyashege ya yi wa yarinyar nan yawa, dan haka sai ya zare hannunsa
daga wuyarta yana kawar da kallonsa daga kanta.
"Big bro do you know something?". Ta faɗa tana cigaba da shafa kyakkyawan
sajensa da hannunta ɗaya. Bai kulata ba ya mayar da hannunsa a saman mirrorsa yana
ƙoƙarin bincikar in da Pretty take a halin yanzu. Kun dai san kingdom of power
masarauta ce ta mahaddara Alqur'ani mai girma, King mahaddaci ne, ba karamar abu
bane Black Tiger ya iya laluɓar Pretty a cikinta, sai in ta fito daga wajen da
mahaddata suke ta kutsa ko ta irin part ɗin uncle Abbas da sauransu haka.

So Black Tiger ganin Pretty zai yi mashi wahala matuƙa a cikin kingdom ɗin, sai ya
zage.

"Sau da dama ina challenging ɗinka da ka yarda mu yi muhawara kaki ko? Why? Ko kana
tsoron zan kayar da kai ne?". Ta kai karshen maganar tana ɗaga mashi gera guda.
Burinta kawai ya yarda rana ɗaya ya bata dama, idan ta fara faɗa mashi girman
Allah, da niimomin Allah sai ya musulunta ba tare da ya shirya ba, idan kuwa bai
musulunta ba to tabbas ta cire ran zai iya musulunta a duniya.

Shiru dai bai kulata ba, kamar bai san da ita a wajen ba. Ƙasa ta yi da
kafafunta da ta ɗaga, ta gaji har sun fara yi mata zafi, a hankali ta zame hannunta
daga lion chest ɗinsa, kallan kofar fita ta yi, ta yi readyn guduwa sannan ta yi
wasu maganganu ƙasa kasa kamar word biyu haka wanda bata bawa kowa damar jin me ta
faɗa ba. Tana kai karshen maganar ta yanka a guje zata yi waje.

Quickly ya juyo magic eyes ɗinsa, with his magic ya janyota ta dawo gabansa.
Capka ya kai hannunsa zai yi wa wuyarta, zulle mashi ta yi ta faɗa kirjinsa tana
sauke ajiyar zuciya. Hannunsa yasa cikin zafa zai ɓanɓareta daga jikinsa, ina ai
kin yarda ta yi, sai tasa magic ɗinta ta taresa.

Me kuke tinanin ta faɗa mashi tasa ya harzuƙa lokaci guda haka?. Wlh Sweetie sai
shirin Allah, dama masu shiru shirun nan basu iya fallewa da rashin kunya ba, ku
duba lokacin da take forest tare da su Kamran, salihar yarinya mai natsuwa, yanzu
gabaɗaya Ronnie ya wayar da ita sai kuma ta zama tantiriya a rashin jin magana ga
tsokanar bala'i.

Ganin ba zata sake shi bane yasa ya juya tare da ɗagata da kyau mai gabaɗayanta
ya ɗaurata a saman lion chest ɗinsa, sannan ya nufi balconynsa da ita, magic walk
ya yi hakan yasa ya isa da wuri. Tin da Sweetie take bata taɓa sanin a wani hawa
yake ba, bata san yana da nisa da ƙasa sosai ba, da yake da elvator ko escalator
suke haura sama sai bata ganin nisansa.

Yana fita balconynsa ya tsaya a dab glass dake wajen. Sai kallan face ɗinsa take
yi tana yi mashi tsiya na sambatu kamar haka. "Big bro kana da kyau fa, amma
matsalar baka murmushi, dik da hakan kuma kyanka bai ɓaci ba". Cike da zolaya ta yi
maganar.

Hannunsa ya kawo saitin face ɗinta, kyawawan yatsunsa ya kyasta mata a saitin
face ɗin nata, da sauri ta kai kallanta a kan ƴatsun nasa, kasa ya nuna mata a kan
ta kalli wajen. Da yake bata san in da suke ba sai ta kai kallanta wajen with her
full confidence.

Ai tana ganin nisan kasa wani irin ihu ta kurma, a miliyan tasa hannunta ta saƙalo
wuyarsa ta ƙanƙamesa sosai. Ihu take yi tana faɗin dan Allah ya yi hakuri ya riketa
kada ta faɗi kasa. Kun san idan kana sama ka kalli kasa mai nisa har wani irin jiri
zaka ji yana ɗebanka, ka ji kanka yana juyawa.

Ganin ta tsorata sosai yasa tsabar mugunta irin nasa sai ya sa hannunsa da karfi ya
ɓanɓarota daga jikinsa, tana ihu tana ƙoƙarin riƙesa ya jefata kasan kamar wata
kayan wanki yana kallan face ɗinta.
Datse idanunta gam ta yi tana ihu tana kalmar shahada, ta gama saddakarwa mutuwa
zata yi, tin da take da shi bai taɓa yi mata abin da ya razanata har hanjin cikinta
suka kaɗa ba irin wannan. Gabaɗaya komai na jikinta sai da ya girgiza, cikinta ya
kaɗa matuƙa. Juyawa ya yi ya koma cikin bedroom ɗinsa ransa fes, a cewarsa ko ba
komai yau ya yi maganin yar ƙaniya.

Ita kuwa tana tsaka da kurma wannan ihu sai jinta ta yi a saman wani abin
tattausa, a tinaninta dik kasa zata faɗa. A zabure ta waro idanunta waje tare da
wani irin yunkurawa da karfi sabowa amai da ya zo mata da karfi.

Wato Black Tiger ɗan duniya ne, da magic nasa ya yi amfani ya dawo da ita saman bed
ɗinsa, ya jinjiga mata yayan hanji a banza kawai. Amma kuma ya ɗarsa mata tsoro
sosai a ranta, ya nuna mata mutuwa kusa da kusa, ba ta ce mashi bata san tsoro ba?
To da alama yanzu kam ta sani.

Kasan bed ɗin ta sauko tare da durkushe gwiwowinta a ƙasa tana tari da karfi
karfi ta dafe kirjinta da hannunta ɗaya, dan tsananin wahala da ta sha. Ƙoƙarin yin
amai a wajen ta yi, amma ta kasa, dan aman yaki fitowa. Kamar ta fita a hayyacinta.

A hankali Ronnie da ya shigo tun ɗazun ya matsa kusa da ita, shoulders ɗinta ya
tallabo yana ce mata sorry. Tana jin voice ɗinsa ta yi saurin miƙewa tsaye tare da
kai kallanta a kansa, sai dai tana miƙewa jiri ya kwasheta, dan har yanzu
ƙwaƙwalwarta yana nuna mata tana faɗuwa ƙasa ne, a fili ta zame zata faɗi Ronnie ya
riketa da kyau yana kara faɗa mata sorry.

Shiru ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi ƴar ƙaniya, dama bata taɓa haɗa
inuwa da Black Tiger ta sha lafiya ba na faɗa maku. Rikota da kyau Ronnie ya yi
suka

Please Login or Register in order to submit comment