Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taɓa ganin bakin
bakiri irin King Abdul Mutallab ba, shi ma bai sha ta daɗi a hannunsu ba bare King
Al-Mustapah ba.

Cike da isa da izza ta ce.
"Umarni nike baku ba shawara ba! Ku yi gaggawar barin nan tin kafin rai'na
ya ɓaci, ka dai san ba zamu karɓi wani risinawarku ba, dan bamu da buƙata!".

Zai sake yin magana ta ɗaga mashi hannun alamar bata da buƙatar sake jin ko uppan
daga gare shi, daga haka ta ce.
"Commander nan da mintuna 5 idan basu bar nan ba ku yi masu zobe ku yakesu!".

Ta yi maganar a dake ba tare da ta kalli in da commander yake ba, yana kai karshen
maganar kuma ta juya cikin zafa ta bar wajen.

Har ta ɗan yi nisa a tafiyar tata sai kuma ta juyo, cikin kakkausar murya ta ce.
"Babu sulhu a tsakaninmu da ku har abada, ayi ta yaki daga nan har illah Masha
Allah, muddin ba zaku daina zalinci ba, mu kuma ba zamu ɗaga kafa ba, babu wani
sauran azzalumi da zamu bari ya sarara!".

Tana kai karshen maganar ta wuce abinta, a hanzarce warrios goma suka rufa mata
baya, warrios goma kuma suka tsaya a tare da commander Zafar dan su kori su King
Al-Mustapah!.

========After some hour=========💘

King Al-Mustapah ya juya ya koma Daularsa, su commander an dawo cikin gida dan
cigaba da shagalin biki, hankalin kowa a kwance, sai kaiwa da komawa ake yi, ana ta
hidima, abubuwa sun kara tsananta, haɗuwa iya haɗuwa.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••💘🔥

Waje ya yi waje, cikin katafaren hall dake cikin kingdom ɗin aka shirya wanna
gagarumim taro domin dinner bikin, haɗuwa iya haɗuwa wanna waje ya yi, an zuba
sabin furniture da komai da komai, zayyana maku ƙawatuwar wannan waje ma ai ba zai
yi wu ba, dan ya zarce tinaninku.

An ƙawata kujerar zaman amarya da ango sosai, gabaɗaya cikin hall ɗin matasan ƴaƴan
manya manyan sarakuna da shuwagabani masu ji da kansu ne a ciki, iyaye basu halarci
wajen ba, saboda abu ne na yara matasa, Auntynsu Jawad ita ce a gaba wajen kawatawa
gimbiya Chuchu kwalliya, har yanzu bata san cewa Jawad aka aurawa Chuchu ba Rizwan
ba, King ya bar abin sai bayan komai ya lafa za'a yi maganar, iya momma ce kawai ta
san a matansa ma.

Abu fa ya yi abu, sai dai ango Jawad dik a susuce yake, bashi da kuzari ko kaɗan,
hankalinsa dik ya karkata a kan Rizwan yanzu, amma ba karya kwalliyarsa da ya sha
ta yi kyau over, dik da akwai ɗan rama a tattare da shi, hakan bai hana haiba da
kalama tasa ta bayyana ba, ya fito a jikin Akka ɗinsa, zallar madarar kyau.

Sai shirye shirye ake yi da misalin karfe 11 na dare za'a fara gudanar da dinner
ɗin.

To bari mu garzaya wani part kafin lokacin yin dinner ya cika sai mu dawo dan ganin
yadda komai zai gudana.


=======BLACK 🌑 WORLD🪐========

Today part in this Black world is the best part amount the previous part's!! I
really like this part more than your expectations 💘 because I really like islam, am
very very proud to be a Muslim💘 a kullum burina in ga ina magana a kan addinina
tare da manya manyan hujoji, ina faɗar niimomin addinina da fifikonsa da kowani
addini, kai ba zan iya gaya maku yadda nike kaunar musulmai da musulci ba wlh,
Allah dai ka kara mana soyayyar Manzon Allah, amma muna alfahari da musulunci kam
ba karya!!.

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

Karfe 7 dai'dai Ronnie suka dawo daga church, yana san zuwa ya ga Sweetie
amma ya fi san ya kai ga yayansa a farko, dan haka a bakin kofar room ɗinsa suka
rabu da Floris, ita ta shiga ciki shi kuma ya wuce part na Black Tiger.

Ya ɗauki a kallah 30 mins a ciki, can ya fito sanye da hoodies masu balai'n tsada a
jikinsa, ya yi matuƙar kyau, da alama a part ɗin ya yi wanka, da yake yana da
hasken fata sosai sai black color tana bala'in yi mashi kyau launin kayan kenan.

Dab zai shiga room ɗinsa ya tsinkayo muryar Floris da Sweetie suna magana, ɗan
dakatawa ya yi dan ya ji me suke faɗa.

"Kina nufin kin san Jesus?". Cewar Floris. Ta yi maganar mamaki sosai a saman
face ɗinta, dan suna dawowa daga church ta yi saurin karisawa wajen Sweetie, a
shirmenta wai bari ta yi saurin fara koyawa Sweetie addininta dan ta rinjayeta, shi
ne da ta fara magana a kan Annabi Isa (A.S) sai Sweetie ta ce mata ta san shi ai,
abin ya bata mamaki matuƙa. Sai ta samu wajen a bakin bed ta zauna dan ta ji daga
ina Sweetie ta san Jesus?!.

Jinjina kai Sweetie ta yi tare da amsa mata da. "I think mu musulmai ma mun fi ku
sanin wanene shi! Kai bama i think ba, mun fi ku sanin wanene shi menene tarihinsa
na hakika!".

Sanya password Ronnie ya yi a kofar ya buɗe, dan yana san ya ji hujjojin da
Sweetie take da shi da har take magana with full confidence a kan addinin nan nata
yana san kureta.

A tare suka dawo da kallonsu a kansa tin da ya shigo, zama ya yi saman egg-s
chair dake fuskantarsu, ya harɗe hannaye a saman kirjinsa yana binsu da kallo.

"Beb ka ji Sweetie wai ta san Jesus fa!". Cewar Floris da bata yarda Sweetie ta
san Annabi Isa or ta fita saninsa ba!.

Kallonsa a kan Sweetie da ita ma take kallonsa. "A ina kika san Jesus bayan ba
addinin nin mu kike ba?".

Kamar baya san yin magana ya yi ta, kuma shi ma yanzu yana san kure
Sweetie ne, saboda ya ga confidence ɗinta ya yi yawa, gara su kureta su gani.

"A malamullah mai tsarki wato Alqur'ani, a nan nasan shi, shi ya zo mana da
tarihinsa gabaɗaya har ta dalilin da yasa kuke ce mashi Allah, wasunku su ce mashi
ɗan Allah".
Ta bashi amsa cikin halin ko in kula bare har ta wani damu.

"Wanene Jesus?". Ronnie ya wurga mata tambayar dan ya kureta, su ji shin da gaske
ta san shi ne ko dai cika baki ne kawai, basu yarda da ana yin karya a duniya ba,
dan basa yi, amma a kan wanan magana sun fara tunanin kamar san zuciyarta kawai
Sweetie take faɗa, sunga kamar tana san janyesu izuwa addininta ne ba tare da wani
hujja ba!.

Miƙewa tsaye ta yi cike da jin daɗin tambayoyinsu a gareta, dan dama so take su
bata dama ta yi masu bayani game da hujoji domin ta samu Allah ya taimaketa ta
tsiratar da su daga duhun kafurci izuwa haske da rahma. Tambayar Ronnie ya yi mata
matuƙar daɗi sosai, sai ta ji tamkar ice block ya manna mata a kirjinta.

Jingina da jikin wall ta yi tare da harɗe hannayenta a kirji, dikkansu idanunsu a
kanta suna jiran bayaninta.

A nitse ta fara magana one by one with full confidence.
"Jesus wato Annabi Isa manzon Allah ne, yana ɗaya daga cikin manya manyan
manzanin da Allah ya turo masu riƙe da litafi, shi ne annabin da aka turowa bani
Israela wato yahudawa, shi ne ya zo da littafin injila wanda a yau kuke kiranta da
Bible domin isar da saƙon Allah zuwa ga bani Isra'ila................"

Katseta Ronnie ya yi da cewa. "Ta yaya Jesus ya zo duniya? And yana da baba ko
bashi da shi?".
All his though ya ɗaureta a wanna tambaya, dan da wanna suke amfani a koda
yaushe su danganta annabi Isa a matsayin ɗan Allah, idan ta bashi amsar Annabi Isa
bai da baba kunga ya samu damar kara karfafa cewa ɗan Allah ne shi.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Da ga kai har Floris kada wanda ya sake
katse mun maganata, zan yi maku bayani a kan wanene annabi Isa (A.S) dallah dallah,
dan da alama ku baku san ainahin wanene shi bama, so yakamata ku san shi da kyau ku
kuma san in da kuka dosa!!"......... Tashin sense.

Ko tsoronsu bata ji ba ta gaya masu hakan, idanunta a kan Ronnie da yanayin face
ɗinsa ta fara canzawa izuwa na ɓacin rai, ita kam Floris tuni dama ranta ya gama
ɓaci, ta ya Sweetie zata ce masu basu san Jesus ba? Wannan ma ai rainin wayo ne!.

Ko kaɗan bata damu da ganin sun ɓata rai ba, ko a gefen takalmarta, cike da kwarin
gwiwa da yakinin in ta yi masu bayani zasu fahimta ta fara magana kamar haka.

"Annabi Isa (A.S.), wanda ake kira Yesu Almasihu a Kiristanci, yana daga cikin
manyan annabawan Allah da Musulmai da Kiristoci ke girmamawa, kowane yana da
fahimtarsa kan tarihinsa da matsayinsa".

"Tarihin Annabi Isa (A.S.) a Musulunci". Idanunta a kan Ronnie take wannan magana
ko shakkarsa babu bare tsoronsa.

"An haifi Annabi Isa ta mu’ujizar Allah ba tare da uba ba, mahaifiyarsa Nana
Maryam tana cikin tsarkaka. Wannan lamari ya faru ne saboda umarnin Allah don ya
zama alama ga duniya a cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya ta 16 zuwa 34 a nan
wannan bayani yake!"

"Annabi Isa ya zo da sakon tauhidi, yana kira mutane su bauta wa Allah shi kaɗai,
ya kuma tabbatar da shari'ar Annabi Musa (A.S.). Ya kuma kawo mu’ujizai da suka
haɗa da warkar da kurma da makafi da maido da matattu bisa iznin Allah".

"Matsayinsa a Musulunci. Musulmai ba su dauki Isa (A.S.) a matsayin Allah ba, sai
dai matsayin annabi kuma manzon Allah. A Musulunci annabi Isa ba kasheshi aka yi
kamar yadda kiristoci suke tunani ba! Allah ya ɗaukaka shi zuwa gareshi wato sama,
cikin Suratul An-Nisa shafi na 4 aya ta 157-158 Allah ya yi magana akan hakan!"

____________________🪐💘

"Dalilin Da Yasa Wasu Suke Bauta Masa a Kiristanci. A cikin Kiristanci, Yesu ana
ɗaukarsa Ɗan Allah, kuma Kiristoci suna ganin shi a matsayin cikar alkawarin Allah
ga ƴan Adam don cetonsu daga zunubi ya kaisu ga rahma!. Kiristoci suna ganin
nassoshi da aka rubuta a Littafinsu suna nuna cewa Yesu shi ne Ɗan Allah wanda aka
aiko domin ya mutu don zunuban duniya, sannan ya tashi daga matattu, malamansu sun
gaya masu irin mu'ujizozinsa hakan yasa suke ganin ya kai ya zama ɗan Allah, saboda
ya tada matattu ya kuma warkar da marasa lafiya bisa umarnin Allah. Wannan shine
tushen imaninsu kiristoci".

"Wasu Kiristoci suna daukar Yesu a matsayin wani bangare na Ubangiji. Wannan
akidar ta samo asali daga fahimtar su game da littattafan Injila ko in ce Bible
ɗinsu na yanzu!".

"Nasan zaku yi mamaki idan nace maku Bible da kuke karantawa a yanzu ba shi ne
wanda Annabi Isa ya zo maku da shi ba, and canza maku shi tsawon dubbanin shekaru,
amma bari in yi maku bayani yadda zasu fi fahimta da kyau, bari in banbance maku
Alqur'ani mai girma da kuma injila haɗe da Bible ɗinku na yanzu, bari ku ga
banbancin sai ku fidda na gaskiya".

Ta kai karshen maganar tana sauke ajiyar zuciya. Daga Ronnie har Floris babu wanda
ya sake tofa ko uppan, sun tsareta da idanu, sai dai dikkansu ransu ya sosu na
yadda take ƙoƙarin karyata malamansu da kuma littafinsu, amma sun kasa kunne dan su
ji hujojinta.

Cigaba da yin maganar ta yi cikin tsanaki yadda komai doɗewar kwakwalwar mutum sai
ya fahimci zancenta tsaɓ!.


"Bambanci Tsakanin Injila da Al-Qur'ani Mai Girma, and Bible".

"Injila wanda Annabi Isa (A.S.) ya kawo shi ne wahayi daga Allah, wanda aka
yi niyya ga bani Isra'ila a lokacin. A Musulunci, an san wannan da Injil, amma ba
wannan ba ne Littafin Bible da Kiristoci ke amfani da shi a yau. Littafin da
Kiristoci ke kira Bible an haɗa shi ne daga rubuce-rubuce daban-daban, ciki har da
Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali, wanda yawanci ya ƙunshi tarihin Annabi Isa da
wasikun manzanni, ba asalin Injila da Allah ya saukar ba, tarihin mu'ujizar Annabi
Isa ne suka cika cikin Bible na yanzu, shiyasa kiristoci suka zage a kan lallai
Annabi Isa Allah ne tun da zai iya raya matattu, ina da yakinin da anbawa kiristoci
ainahin littafin da Annabi Isa ya kawo masu domin su san girman Allah to da tabbas
yau za'a wayi gari babu Christians ko ɗaya a duniya, da zasu san girman Allah su
san kuma dik abin da Annabi Isa ya aikata dan gane da mu'ujizarsa to Allah ne ya
umarcesa ya kuma yassare mashi yin hakan, amma an ɓoye masu gaskiya an barsu cikin
ɓata!".

Ɗan dakatawa ta yi da maganar tana jan numfashi, tabbas ta lura ran Ronnie ya kara
ɓaci. Amma ko kaɗan bata damu ba!.

Kasa jurewa Ronnie ya yi har sai da ya ce. "Menene hujjarki na cewa an canza mana
littafi ne ba wanda Jesus ya zo da shi muke amfani da shi ba?!". Da ɗan daga murya
ya yi maganar.

"Amma ai nace kada ku saka mun baki a magana ko ku katseni ko?".

Mamakin jin furusinta suka yi, yadda ta yi masu magana kamar tana basu umarni,
kallon mamaki Ronnie ya bita da shi ita kuma Floris kallan takaici! Sai dai basu
furta uppan ba, ita kuma ko a jikinta.

"Idan na gama bayanai da nike son yi sai ku tambayeni in kuna da tambaya, amma
yanzu ku yi shiru ku saurareni tukun nan, zan gaya maku komai game da hujoji!".

Kasa yin magana Ronnie ya yi, amma ba karya ransa ya sosu, ta wani ajisu kamar wasu
ƴaƴanta tana kora masu kashedi, wlh Sweetie akwai balai'n karfin hali yarinyar
nan!.

Sai a lokacin Ronnie ya kula da kamar wani abin ya faru a room ɗinsa bayan
tafiyarsu church, amma bai yi magana ba, ya yi shiru bisa umarnin hajiya Sweetie!.

Mirrornsa da ya fashe Black Tiger ya mayar da shi yadda yake, chandelier ta koma
mazauninta tamkar bata taɓa motsawa ba, amma a haka Ronnie ya fahimci akwai abin da
ya faru a ɗakin!.

Cigaba da bayani Sweetie ta yi kamar haka. "Al-Qur'ani littafi ne wanda Allah ya
saukar wa Annabi Muhammad (SAW) ta wurin Mala'ika Jibril. Shi ne kalmar Allah
tsarkakakke ba tare da canji ba tun lokacin da aka saukar da shi, kuma ya kasance
jagora ga dukan al'umma".

"Injila. Asalin Injila da Annabi Isa ya kawo an saukar da ita ne da harshen
Aramaic, wanda shine yaren Annabi Isa. Amma Bible na yau an rubuta shi ne da Greek
da Latin kafin a fassara shi zuwa wasu harsuna. Wannan ya haifar da bambance-
bambance masu yawa da kara tsaurara banbanjin tsakanin injila da Bible".

"Al-Qur'ani an saukar da shi da harshen Larabci na asali, kuma har yanzu yana nan
daidai kamar yadda aka saukar. Wannan yana tabbatar da tsaronsa ba tare da canji
ba!".

"Injila ta kunshi wa'azi na Annabi Isa, da alheri, da darussan soyayya, da
imani, da sanin girman Allah da ranar kiyama. Amma rubuce-rubucen Bible na yanzu
sun haɗa tarihin Annabi Musa, annabawan da suka gabata, da wasikun manzanni da su
irin su Bulus, wanda ba sahabi ba ne na Annabi Isa (A.S.) Wannan ya sanya kiristoci
suna samun akida mai ɗan rikitarwa".

"Al-Qur'ani ba wai wa'azi kawai ba ne, cikakken tsarin rayuwa ne wanda ke
jagorantar Musulmi wajen ibada, mu'amala, siyasa, dokokin shari'a, da zamantakewa,
hukunci kan lahira, mutuwa haɗe da kwamciyar kabari, hisabi da dai sauransu. Ya
kunshi hukunci masu ma’ana da shawarwari kan dukkan bangarori na rayuwa, Alqur'ani
mai girma ya haɗe komai da komai".
"Injila ta asali (Injil) an yi mata canje-canje da yawa bayan Annabi Isa.
Bible na yanzu an rubuta shi shekaru da dama bayan barin Annabi Isa duniya, kuma
kiristoci suna da nau'o'i daban-daban na Bible, misali, Catholic Bible da
Protestant Bible, wanda ya nuna rashin tabbaci kan ainihin littafin, Alqur'ani mai
girma shi kaɗai ne babu wani kala daban daban, kai ko suna ba'a sake mashi ba, yana
nan a Alqur'aninsa kamar yadda ya sauka!".

"Al-Qur'ani ya kasance tsarkakakke tun lokacin da aka saukar da shi har yanzu,
ba tare da wani canji ba. An adana shi a kwakwalwa da rubuce-rubuce daga lokacin
Annabi Muhammad (SAW). Wannan ya tabbatar da tsaronsa daga duk wani ruɗani".

"Annabi Isa ya kira mutane zuwa tauhidi, wato bauta wa Allah shi kaɗai a cikin
injila ta ainahi Mark 12 verses 29. Amma a cikin Bible na yanzu akwai akidun
Triniti (Trinity) da suka bayyana Yesu a matsayin Ɗan Allah ko wani ɓangare na
Ubangiji. Wannan yana da saɓani da asalin saƙon Annabi Isa a Musulunci!!".

"Al-Qur'ani yana nan daidai da saƙon tauhidi na Annabawan da suka gabata, yana
tabbatar da cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Suratul Al-Ikhlas 112. Ya
kuma kawo bayani kan matsayin Annabi Isa da sauran annabawa".

"Injila sakon tauhidi ne ga bani Isra'ila daga Annabi Isa, amma Bible na yanzu
ya haɗa da bayanan da suka sha bamban da asalin saƙon Allah".

"WANNAN SHI NE BANBANCIN ALQUR'ANI DA INJILA DA KUMA BIBLE INA FATAN KUN GAMSU
SOSAI?".

Ta yi tambayar tana rarraba idanunta a kansu. Babu wanda ya iya furta uppan a
cikinsu.

Sai dai a lokacin da ta zo wannan gaɓar Ronnie ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi,
saboda shi kansa yasan suna da Bible kala daban daban wanda rubuce rubucen cikinsu
ma yake kala daban daban! Kamar yadda ta ce akwai Catholic Bible da Protestant
Bible, yasan da hakan, so sai ya ji kamar ta ɗan faɗi gaskiya a wannan gaɓar.

Ganin kamar zuciyar Ronnie ta ɗan sanyaya ne yasa ta kara jin kwarin gwiwar zata
iya cin nasara a kansu, dan haka sai ta cigaba da bayaninta.

Tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Ronnie ya katseta da cewa. "Shekara nawa ne
tsakanin rasuwar annabi isa da kuma bayyanar Bibles na yanzu da kiristoci suka
kaddamar a matsayin injila?".

Zaro idanun Floris ta yi haɗe da mamakin Ronnie, ta ji kamar ya gamsu da zancen
Sweetie ne.

Sosai Sweetie ta ji daɗin wanna tambaya da Ronnie ya yi mata, dan tana ganin kamar
ta fara cin nasara ne, dan haka cikin farinciki da zumuɗi ta amsa mashi da.

"Tarihin rubutun Bible, musamman Sabon Alkawali (New Testament), yana nuna cewa
akwai babban tazara tsakanin lokacin da Annabi Isa (A.S.) ya bar duniya da lokacin
da aka rubuta kuma aka tattara wannan littafi. Bari dai na yi maku dallah dallah
dan ku fahimta".

Kara nutsuwa Ronnie ya yi dan ya saurareta da kyau, da alama zuciyarsa ta fara
yarda da maganganunta, dan komai ta faɗa tana kawo hujja mai karfi wanda dole ka
yarda, kamar a baya yadda ta faɗi ayayon Alqur'ani da za'a je a duba dan tabbatar
da gaskiyarta, hakan yasa ya fara gasgatata.

"A tarihin Kiristanci, ana tsammanin Annabi Isa ya bar duniya, daga hangen nasu
an ce an kashe shi, amma a Musulunci ba a kashe shi ba, Allah ya ɗaukaka shi zuwa
sama kamar yadda na faɗa a baya. Wannan lamarin ya faru kimanin shekarar 30-33 AD".

AD wato Anno Domini yana nufin bayan haihuwar Annabi Isa ne, BC wato before Charist
yana nufin kafin zuwan Annabi isa duniya kenan, to shekarun ake kira da BC, bayan
zuwansa kuma AD.

Cigaba da bayani Sweetie ta yi cikin sani da kuma kwarin gwiwa. "Bayyanar Sabon
Alkawali (New Testament). Rubuce-rubucen farko na Sabon Alkawali, waɗanda aka ce
wasikun Bulus ne (Paul), sun fara bayyana kusan shekaru 20-30 bayan ɗauke Annabi
Isa daga duniya da Allah ya yi, kimanin shekarar 50 AD bayan zuwansa duniya kenan".

"Injiloli guda huɗu ko in ce Bible ɗinkuna yanzu guda huɗu wato Matthew,
Mark, Luke, John. An rubuta su kusan daga 60 AD zuwa 110 AD. Injila na Markus wato
Bible mark ana ɗaukar shi mafi tsufa, an rubuta shi kusan shekarar 60-70 AD. Sauran
injiloli (Bibles) suna tafe daga bayansa".

Izuwa yanzu jikin Ronnie ya yi sanyi, saboda jin yadda take zayyano tsawon shekaru
baya, ko mai san zuciyar mutum ya ji wanna bayanai nata dallah dallah sai ya san
gaskiya take faɗi, sai dai idan yaki aminta da hakan dan san zuciyarsa ne! Amma
irin wanna shekaru da take ambata ai babu karya!.

"A lokacin shekaru 325 AD bayan haifar Annabi Isa kenan, a taron Council of
Nicaea, a karkashin Sarki Constantine, aka fara tsara da tantance irin waɗanda za
su shiga cikin Bible na yanzu, kuma wannan ya ƙarfafa canje-canje na ra'ayi da
tsarin Kiristanci, kun dai ji Bible naku na yanzu sarakunar da ne suka shirya
abubuwan da za'a rubuta a ciki, so ni nasan ba laifinku bane zamanku kiristoci,
laifinku a nan shi ne rashin faɗaɗa bincike da neman sanin gaskiya bayan Allah ya
baku dama da baku yi na shi ne laifi, kun dogara da littafi guda ɗaya wanda tsara
maku shi aka yi ba zancen Allah bane!".

"Injila ta gaskiya da Annabi Isa ya kawo ta ɓace na tsawon lokaci, hakan yasa
saƙon Allah bai isa ga mutanen yadda yakamata ba. Wannan ne yasa Allah ya saukar da
Al-Qur'ani Mai Girma don ya zama tabbataccen jagora wanda ba zai taɓa sauyawa ba,
wasu gungun kafurai sun jima suna shuka tsiya da rashin son gaskiya a duniya, amma
Allah ba'a yi mashi wayo, da suka ɓatar da injila ta gaskiya sai ya sauko da
Alqur'ani wanda wane mutun ya iya canza rubutun cikinsa, karya mutum yake, tsawon
shekaru har yau yana nan yadda aka sauke shi!!".

Ta kai karahen maganar idanunta a kan Ronnie tana kuma sauke nannauyar ajiyar
zuciya, sai fatan take yi Allah yasa su gane gaskiya.

Floris ta rasa abin faɗe, sai idanu kawai take binsu da shi, ta ji abin da ya
girmewa shekarunta.

"Shin kana da wata tambaya dan kara tabbatar da gaskiya ta da gaskiyar
addinanina ne ko dai ya isa haka?".

Ta jefawa Ronnie tambaya idanunta a kansa.

Zuciyarsa ta gama yarda da zancenta dikka, amma dik da haka dan kara tabbatarwa sai
ya ce.
"Shekara nawa Annabi isa ya yi a duniya.............. and tare da
mahaifiyarsa ya yi rayuwa? Sannan akwai wani dalilin da yasa bai yi aure bane?. And
ya rayuwarsa ta kasance a cikin al'umma a lokacin da ya bayyana bai da uba? Ya
fisakanci kyara ko tsangwama ne daga mutane? Ko dai a addininki Annabi isa yana da
baba ne ɓoye mana aka yi kamar yadda aka canza mana komai?".

Ta ji matuƙar daɗin jin wanna tambaya tasa, ranta ya yi sanyi sosai.
With full confidence ta ce. "Tarihin Musulunci da Kiristanci ya nuna cewa Annabi
Isa (A.S.) ya rayu a duniya na kimanin shekaru 33 zuwa 34 kafin Allah ya ɗaukaka
shi zuwa sama. Wannan yana nufin bai mutu ba a hannun mutane, kamar yadda Musulunci
ya bayyana Surat An-Nisa shafi na 4 aya na 157-158 Allah ya yi wanna bayani".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗaura da cewa.
"Annabi Isa ya taso ne a ƙarƙashin kulawar mahaifiyarsa, Nana Maryam, wacce
Allah ya zaɓa kuma ya tsarkake ta daga zunubi. Ya zauna tare da ita yayin
ƙuruciyarsa har lokacin da ya fara wa'azinsa. Mahaifiyarsa ta kasance ginshiƙi da
gatansa, musamman ganin cewa ba shi da uba".

Ronnie fa ya ji abin da bai taɓa ji ba, ga shi maganganunta dai ba zasu karyatu
ba, shi kansa yasan gaskiyar take faɗe, saboda idan ba gaskiya bane taya tana
karamarta haka ace zata tsara irin wanna dogon karya? Ai ba zata taɓa yiwuwa ba.

Cigaba da bayani ta yi. "Dalilin da yasa bai yi aure ba, Allah ya aiko Annabi Isa
(A.S.) da takamaiman manufa, isar da saƙon tauhidi ga Bani Isra'ila da warkar da
zukatansu daga zalunci da ruɗi. Rashin yin aurensa ba tare da shakka ba ya haɗu da
wannan manufar, don ya mai da hankali kan aikin annabci ba tare da wata tangarda
ba!".

"Al'ummar da Annabi Isa ya fito daga cikinta tana cike da tsangwama da adawa
ga saƙon Allah, kuma rayuwarsa ta kasance cike da ƙalubale. A irin wannan yanayi,
yin aure ba zai yiwu ba, domin tsangwamar mutane za ta iya shafar iyalinsa idan ya
kasance da su".

"Allah yana aikawa da annabawa tare da yanayi daban-daban, don su zama abin
koyi ga al’umma. Rashin aurensa wata hanya ce ta nuna cewa rayuwa mai cike da ibada
da sadaukarwa na yiwuwa ba tare da iyali ba, musamman idan mutum yana da babban
aiki na isar da saƙon Allah".

A dai'dai wanna gaɓa Ronnie ya samu karin haske sosai, wato hikima ta Allah tana da
yawa, rashin yin auren Annabi Isa wani haske ne ga al'umma. Nan take ya kara jin
lallai wannan Allah da Sweetie take magana a kansa shi ne Ubangiji na gaskiya.

Cigaba da bayani Hajiya Sweetie tamu yarinya ƴar baiwa mai cike da ababen ban
mamaki ta yi.

"Rayuwarsa a cikin al’umma lokacin da ya bayyana ba tare da uba ba. Fitowarsa
ta musamman ce, Annabi Isa ya fito cikin mu'ujiza rashin uba........ Wannan lamari
ya haifar da jita-jita daga wasu mutane,

Please Login or Register in order to submit comment