Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 21 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sam basa san datti, basa san kazanta, dole Jaish ya gansu a matsayin
datti, saboda kayan jikinsu dik a koɗe sosai suke, gara ma ita Mahnoor doguwar
rigar bikinta ta saka, shi yana da ɗan kyan gani.

Da gudu Mahnoor ta kwace hannunta daga rikon da momma ta yi mata, ta kariso
cikin parlourn ta rungumi Mahreen dake ihu ta ji azabar wurgar da ita da Jaish ya
yi, ta bugu sosai.

Kwace rikon da Jawad ya yi mashi ya yi, da sauri ya nufi hanyar fita waje dan ya
je ya cire kayan jikinsa dan ta taɓa, in baku manta ba mugun kyama Jaish yake da
shi, kun tuna farkon zuwansa garinsu yadda ya rinƙa kwarara amai saboda bappa ya
taɓa shi? To yanzu ma hakance.

Akwai tashin hankali, my people's kuna tinanin Jaish zai yarda da Mahnoor a
matsayin mata kuwa? Akwai fa matsala. Amma my people's nace ba, who noticed that
Jaish and Jawad shekarunsu ɗaya kuma shekarun mstansu ma ɗaya?........ 🤔 A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA.............. MUJE ZUWA AKWAI ABUBUWA A GABA MASU
BAN MAMAKI, KUN SAN INA SAN IN YI TA SURPRISING ƊINKU AI.

•••••••••••••••••FOREST••••••••••••••••🔥



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




•••••••••••••••••FOREST••••••••••••••••🔥


••••••••••••••••AFTER SOME TIMES🔥

Zaune Pretty take a kasan wani bishiyar zaitin mai bala'in tsayin gaske. Tana zaune
suna fuskantar juna ita da Zunaira, ta yi shiru tamkar mai tinanin wani abin, ga
dikkan alamu akwai damuwa a tattare da Zunaira sosai, sai dai ita Pretty a yau babu
alamar damuwa a tattare da ita.

Meya haɗa Zunaira da ta mutu kuma da Pretty? Muje zuwa. Kada ku manta alkalamina
ɗan alkawari ne, dan haka ya yi maku alkawarin samun surprise dayawa a cikin
labarin nan, so yanzu haka mun fara buɗe babin surprise ne, Princess Teema taku ta
amana Queen of surprises. Muje zuwa dan jin me ya haɗa Auta da Pretty kuma? Ina
Team Zunaira? Princess Teema tana tayaku murna Zunaira is alive.
Auta tana sanye da kayan Pretty a jikinta, ta yi rama sosai, ta sha jinya ta
sha bakar wahala baiwar Allah, har ta fita a hanyacinta, idan kuka ganta yanzu ba
zaku taɓa yin zatan ita bace, saboda wahala da ta sha, har duhu sai da hasken
fatarta ya yi, idanun nan nata sun kara girma saboda rama.

Fuskarta ya ƙanƙance, ita ma yanzu ta zama irin Pretty babu ɗaura ɗan'kwali
sai dai su saki gashi har baya, coz ita Zunaira gashin nata ma in ka gani sai ka
san ta ci uwar wahala, dik ya cukurkuɗe kamar ba ita ba.

Wasu irin fresh fruits ne a gabansu cikin kwanto irin wanda Mammar kamran take
amfani da su, wato kwanton da ake zuba timatir. Ba cin fruits ɗin suke yi ba, Auta
tana tinanin gida da su Chuchu yanzu tsawon lokaci bata a tare da su, ita kuma
Pretty Allah ne kaɗai yasan me a cikin zuciyarta, dan bata bada daman ya fito fili
a san halin da take ciki ba.

Har yanzu akwai ɗan sauran magani manne a cikin Zunaira in da Hoorain ya caka mata
wuƙa, wajen ya warke alhamdulillah, dan har tana iya tafiya da kafafunta.

"Alhamdulillah my Queen ta samu lafiya".......... Daga bayansu suka ji wannan
murya wanda ko basu juyo ba sun san shi ne, dan shi kaɗai ne garesu a cikin wannan
forest ɗin.

Auta ce ta juyo haɗe da kai kallonta a kansa, ita kam Pretty bata juya ba,
kamar fushi take yi da shi........... Kamar dai kullum yana nan cikin wannan shiga
tasa, ga dikkan alamu su Pretty har yau basu san ya kamannin face ɗinsa take ba.

Ɗan yake Auta ta yi mashi, baiwar Allah ko tana cikin damuwa murmushi baya ɓata
daga kan face ɗinta, murmushi sadakace in ji Manzon Allah (S.A.W)

"Na ji sauki Alhdulillah".......... Ta bashi amsa tana ƙoƙarin faɗaɗa
murmushinta da dole.
Tsareta da idanu ya yi tamkar zai cinyeta, bai sake yin magana ba, ita ma
bata sake yin magana ba, ta dai kawar da kallonta daga kansa, tsoronsa take ji
sosai, saboda yanayinsa, amma hakan baya hana ta yi mashi murmushi ta kuma yi mashi
magana idan ya zo, saboda shi da Pretty su suka ceci rayuwarta, da yanzu babu ita a
doran duniya.

Ba komai yasa take tsoronsa ba kuma face zubin halittarsa, cikakken sadaukin
warrior ne sosai da sosai, and wani lokaci yanayi mata yanayi da Hoorain da ba zata
taɓa iya mantawa da shi a rayuwarta ba, ta in da kuma yake yi mata yanayi da
Hoorain shi ne rashin yarda ya buɗe fuskarsa a garesu, tin da ta fara samu sauki ta
fara magana in ya zo tana rokansa da ya buɗe fuska su ga juna, sai ya ce mata sai
wani lokaci, yana yawan zama a tare da ita lokacin da take jinya, suna hira dik da
ba sosai ba, amma baya yarda idan ta kawo zancen buɗe fuska, wannan dalili ya ɗarsa
mata tsoronsa a ranta, tana tsoron waɗan da basa buɗe fuska a yanzu.

Batu na gaskiya wannan ba Hoorain bane, basu ma da haɗi, Hoorain yana Daular Queen
Zarina, sai dai shi ma wannan yana da nashi dalilin da yasa baya san buɗe fuakarsa
a garesu ne kamar yadda shi ma Hoorain yake da nashi dalilin, amma ba mutum ɗaya
bane sam, ita dai Auta tana tsorace da masu rufe face ɗinsu ne kawai wanda dani da
ku kuma dik mun san dalilin tsoronta a kansu.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Omnish yau ba zaki yi mun magana bane?". ........... Ya yi maganar yana zagowa
ta gabansu.

Turɓune fuska ta yi, tana turo baki ta ce. "Yau ba zan yi magana da kai
ba". ........ "But why?"....... Ya yi maganar dai'dai lokacin da yake tsugunnawa a
gabansu. Hannu ya kai ya ɗauki lemu mai ɓawo guda ɗaya daga cikin kwandon gabansu.
Cikin nitsuwa ya fara ɓare lemun yana satar kallon Auta ta wutsiyar ido.

"Ba kai ne kace ba zaka sake wuce kwana ɗaya baka zo garemu ba, amma yau ka kai
kwana biyar baka zo ba". Cewar Pretty sarkin mita da raki. Kamar zata yi kuka ta
kai karshen maganar. Tana kai karshen kuma ta miƙe da sauri ita a dole ta yi fushi
zata tafi ta basu waje. Sak dai yadda take yi wa Kamran idan ya ɓata mata rai ta yi
fushi.

Cikin zafa ya yi saurin riko hannunta, Pretty tana bashi ciwon kai da shegen
shagwaɓa da saurin kukan nan nata, ga shi bata jin lallashi da wuri.............
"Haba my baby, to ki yi hakuri ba zan sake ba, kuma nima ai ba dan san raina nike
rabuwa da ku ba, idan da dan san raina ne ba zan rabu da ku ba ai, ina san
kasancewa daku sosai, amma bani da damar yin hakan, kiyi hakuri kinji rigimammiya
kawai"................. Dik maganganun da yake yi idanunsa a kan Auta da take ta
binsu da kallo, ita dai Pretty ta shiga ranta sosai, tana burgeta bare ma idan tana
yi wa wannan sadauki shagwaɓa, sosai take jin daɗin kallonsu a tare.

Kuka Pretty ta saka mashi wai dan ya ce mata rigimammiya a karshen maganarsa,
shikenan ya sake jijjigo wata rigimar............ Dan dolensa ya gyara zama a kasan
wannan bishiya, ya ɗaura Pretty a saman laps ɗinsa ya hau rarrashi.

A saman kirjinsa ta kwantar da kanta tana turo baki ita a dole ranta ya
ɓaci........ Cigaba da ɓare lemun hannunsa ya yi yana satar kallon Auta, da yake
face ɗinsa a rufe sai iya idanunsa ne kawai a buɗe, idan ka gansa zaka yi zaton
lemun yake gani, amma Zunaira yake gani, ita kuma tana ta kallon Pretty da ta gama
tafiya da imaninta.

Shiru wajen ya ɗan yi na ƴan sakanni da ya kammala ɓare lamun, sai ya rabata
kashi huɗu, Pretty dake zaune saman laps ɗinsa ya ɗauki ɗaya ya sanya mata a baki
yana dawo da ainahin kallonsa a kan face ɗinta.

Buɗe bakinma Pretty sai ta ja mashi aji sai kuma ta yi shagwaɓa, amma haka ya
jirata ta gama shan kamshinta kafin ta ɗan buɗe mashi bakin nata, shi ma kaɗan ta
ɗan buɗe.

Tura mata lemun ya yi yana dawo da kallonsa a kan Auta, ta sunkuyar da kanta ƙasa,
wasu zafafan hawaye suka fara bin ƙuncinta, ba komai ya ja hakan ba face abin da
yake yi wa Pretty ya tuna mata da ita da guyson, ta yi kewan ƴan uwanta sosai, ba
dan sadauki yana kula da ita yana rarrashinta haɗe da kawar mata da damuwar da take
ciki ba wlh da bata san ina zata sanya rayuwarta ta ji sanyi ba, bata taɓa rabuwa
da ƴan uwanta ko nan da can ba sai a dalilin Hoorain, wannan abin ba zai taɓa
gogewa a ranta ba har abada.

Kanta a ƙasa, bai san hawaye take yi ba, sai ya ɗauki lemu guda ɗaya cikin wanda
ya raba, bata yi zato ba sai ganin hannunsa ta yi yana ƙoƙarin cusa mata lemun a
bakinta. Da sauri ta ɗago kanta, karap suka haɗa ido, ya ɗan yi mamakin ganinta
tana kuka, ita kanta Pretty ta yi mamakin hakan.

Tashi ta yi daga saman laps ɗinta ta koma kusa da Auta, ɗan rungumota ta yi tana
faɗin............ "Allah sarki meyasa kike kuka kuma ƴar uwa?".

Shiru bata amsa masu ba, ita kaɗai tasan me take tinani, ita kaɗai tasan raɗaɗin da
yake cikin ranta.

"Omnish jeki ki kawo mun maganinta kin ji?"............ A faɗa a sanyaye. Ɗan
zaro idanu Pretty ta yi, a ɗan tsorace ta ce. "Ciwonta ne yake yi mata zafi?".
Kai ya gyaɗa mata a alamar e, hawayenta Pretty ta fara share mata, cike da
tausayawa ta ce. "Ki yi shiru ki dai'na kuka, In Sha Allah ciwonki zai yi sauki,
yanzu zan kawo maki maganinki, amma ki dai'na kuka, bana san ganin kina
kuka"......... Oh Pretty sarkin iya tsara zance idan ta yi ra'ayi, in bata yi ba
kuma sai ka yi zatan wawuya ce ko kurma.

Jinjina mata kai kawai Auta ta yi ba tare da ta yi magana ba, goge mata hawayen da
ƴan hannayenta Pretty ta yi kafin ta miƙe da sauri ta nufi makwancinsu dan ta ɗauko
maganin.

Tana tafiya ya matsa kusa da Auta sosai, dama wayo ya yi wa Pretty ta tafi shiyasa
ya ce ta je ta ɗauko mashi magani, idan ya matso ya ce zai ɗaura Zunaira a kan
cinyarsa ko wani abin makamancin haka kuka Pretty take yi ta ce ai kafarsa nata ne
ita kaɗai shiyasa ya yi mata wayau ta tafi.

Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta, shi kansa sai da ya ji wani irin abu ya tsaya mashi
a makoshinsa mai wuyar haɗiyewa. Kallanta ya yi ido cikin ido, gabansa ne ya ji ya
fada dum dum haka. Ɗayan hannunsa yasa ya fara goge mata sauran guntun hawayen dake
face ɗinta, cikin sanyin murya can ƙasa ƙasa ya ce.

"Kin manta cewa kin mun alkawarin ba zaki sake zub da hawayenki a banza ba
ne?".

Shiru bata iya amsa mashi ba, sai ma ji da ta yi kamar ta tashi ta gudu a wajen,
dan dai yana da girma da kima a idanunta wanda ba zata iya yi mashi abin da zai
ɓata mashi rai ba ne yasa ta danne, ba za kuma ta taɓa manta halaccinsa a gareta
ba. Ƴar Halak kenan.

Ganin bata yi magana bane yasa ya sake matsawa kusa da ita sosai, a hankali ya ɗan
rungumota da nufin ya yi mata rarrashi irin wanda yake yi wa Pretty. Dik da yake
sadauki sai da ya ji wani irin shock a jikinsa, kamar wanda aka jonawa lantarki,
har sai da ya ɗan saketa jin abin da bai taɓa ji ba. Amma kuma yana san ta yi shiru
kuma ta yi mashi magana, dan haka sai ya daure ya sake rungumota a jikinsa, yana
jin wani irin bakon yanayi haka ya daure ya fara rarrashinta tare da tuna mata da
alkawarin da ta yi mashi a kan ba zata sake yin kuka ba.

Dan dole ta haɗiyi kukan nata, saboda ya iya rarrashi sosai, ko da yake dik wanda
zai rarrashi Pretty ta yi shiru lallai ba shakka ya iya rarrashi, dan Pretty sai
Allah.

Murya can ƙasa ƙasa haɗe da kuka ta ce.
"Ka yi hakuri ba zan sake ba". Da yake tana kuka sai voice ɗin nata
ya yi tamkar a shagwaɓe ta yi maganar, ba ƙaramin ɗarsa wani abin a ransa wannan
magana tata ya yi ba.

Ƙasa sake yin magana ya yi, wannan sadauki ya shiga yanayi, abin ku da ba'a saba
ba, an saba da datse kan mutane da takoba, ba'a saba shukan fure ba, sai ya zamana
kaman wani ɗan fari a gabanta, ya hau aikin binta da ido kawai, daga ta yi mashi
shagwaɓa sau ɗaya shikenan ya birkice.

(Anya ba zamu kai sadauki wajen Yah Jawad ya koya mashi karatun shuka flowers
😅
ba kuwa my people's?)

Jin ya yi shiru bai amsa taba yasa ta yi tinanin ko dai ransa ne ya ɓaci yaki sake
kulata, dan haka sai ta kara marairace murya, a wannan karon cikin shagwaɓar gaske
ta ce......... "Na yi alkawarin ba zan sake ba, dan Allah kayi hakuri, kaga ma na
goge hawayena". Ta kai karshen maganar tana kai hannunta saman fuskarta.

Haba tuni sadaukinmu ya kara shiga yanayi, kamar ba shi ba, sai ya ji kamar
an canza shi ne lokaci guda, ya kasa iya yin magana.

Allah sarki ta zaci fushi yake yi, sai ta kai hannunta ta riko nasa hannun, kamar
zata saka kuka ta shiga bashi hakuri. Dik sai kara rikita shi take yi, da kyar ya
iya samu ya juya hannunta ya koma cikin nasa, a hankali ya furta ta yi shiru dan
Allah ta dai'na magana, dan tana kure tinaninsa.

A dai'dai lokacin Pretty ta dawo hannunta ɗauke da sak irin kwaryar da aka basu
magani a lokacin da suke jarirai, ganinta yasa ya yi saurin sake Zunaira ya ɗan ja
baya kaɗan.

Karɓar maganin ya yi Pretty ta zauna kusa da shi, a gefensu ya ajiye ba tare da ya
bawa Auta ba, Pretty bata nemi jin meyasa bai bawa Autan ba, sai ta kwanto jikinsa
ta fara aikin zuba mashi shagwaɓa da ta saba.

Haka suka kasance cikin farinciki suna hira yana satar kallon Auta na tsawon
lokaci, har sun shagala sun mance da zai tafi sannan ya kawo masu batun lokacin
tafiyarsa ya yi. Kuka suka saka mashi su biyun dikka, Allah sarki wlh basa san zama
su biyu a cikin wannan kungurmin dajin, amma to ya zasu yi? Dole su hakura dan
sadauki dai bai san ƙasarsu Gimbiya Zunaira ba, ita ma bata san ta ina take bama
bare tasan in da garinsu yake, ba hanyar komawa.

Hakuri ya rinƙa basu yana rarrashinsu har sai da ya samu suka ɗan nitsu, sannan ya
rakasu har sabon bakwancin da ya yi masu ya kuma ƙawata masu shi, bai mayar da
Pretty ainahi in da suka taso a tare da mom ɗinsu ba, ya canza mata waje, har yau
har gobe kuma yana wahalar neman Sweetie, ba dare ba rana, dayawan lokuta idan ya
shigo forest ɗin kafin ya je in da su ke sai ya yi ta kewaye a cikin dajin yana
neman Sweetie, kun san na gaya maku kungurmin daji ne mai girman gaske, yana da
ɓangarori da dama, idan kana wannan ɓangere ba zaka taɓa zatan akwai mutane a wani
ɓangare ba saboda nisan dake tsakani.

So kullum a cikin daji yake yawon neman Sweetie, bai taɓa kawowa ransa bata a
wannan dajin ba.

Har ciki ya rakasu, ya kuma gargaɗi Pretty a kan kada su yarda su fito waje, dan
yasan halinta sarai da shegen san zama wajen ruwa, kullum sai ya gargaɗeta a kan
fitowa waje, amma kuma kullun idan ya kawo masu ziyara a waje yake samunta, shegen
san zama wajen koramu dake aman ruwa ne da ita. Kamar wata ƴar ruwa!.

Da kansa ya rufe masu kofar ramin nasu dan ma kada su fito, sai dai kash yana
tafiya Pretty ta ce da Auta ta zo su je wajen korama su zauna hai, ita bata san
zaman cikin nan, ta fi san waje. Auta kuwa ta bita suka fita, wajen wata korama mai
aman ruwa suka je suka zauna suna kallan ruwa......... Pretty sai shirin Allah.

•••••••••••••••••••DUBAI••••••••••••••••••🔥

Kwance Sharifat take a saman bed ɗinta, ta ci kuka har ta godewa Allah, yau tsawon
kwanaki tara kenan ba tare da Leesharh ba, tana cikin damuwa da alhinin hakan sosai
sun rigada sun saba.

Gobe zata koma school, dama rashin Leesharh ya ja mata zazzaɓi har na tsawon
kwanakin nan bata je school ba, idan kuka ganta sai kun tausaya mata, da alama ba'a
taɓa breaking heart ɗinta ba sai a wannan karon baiwar Allah.

Miƙewa ta yi zaune, tinanin guyson ne ya faɗo mata a ranta, ta tina kullum
sai ya tambayeta ina Leesharh, Allah sarki yakamata ta sanar da shi kalar cin
amanar da Leesharh ta yi masu. Can tinanin maganganun su Omaid a kan Leesharh ya
faɗo mata ranta, kenan ya tabbata su Omaid suna da gaskiya, dama tin da suka ɗaura
idanunsu a kanta suka ce she looks like a criminal, Guyson ya yi ta yi masu faɗa,
ashe kuwa zancensu haka ne.

Tun da aka kama Leesharh bata yi waya da kowa ba, wayarta ma a cikin jakarta da
suka je taron nan da shi ta barshi, dan haka sai ta sauko kasa daga saman gadon.
Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi bags rack ɗinsu. Tana sanye da
Pakistan a jikinta, ta ɗaura gyalen kayan a matsayin ɗan'kwali.

Wani irin jiri ne taji yana ƙoƙarin kayar da ita, da kyar ta iya kame kanta ta
tsaya da kafafunta. A hankali ta zuge zip ɗin jakar ta buɗe.

A miliyan ɗari ta kai hannunta ta murza idanunta tana kara zarosu waje, sam
bata san lokacin da bakinta ta furta what!! Ba, da karfi ta yi maganar. Nan take
jikinta ya fara kerma, a hanzarce ta zira hannunta a cikin jakar ta fito da
wayoyinsu. Wayarta ce da na Leesharh. Da karfi ta furta. "Kenan da gaske kamar
yadda Yah Bilal ya ce mun Leesharh ta ce wancan wayar ba nata bane kenan hakan ce?
Kenan tana da gaskiya ba wayarta bace wancan?".

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, Allah sarki su Yah
Ramish sun azabtar da baiwar Allah a banza!".

Cikin ɗaga murya ta yi maganar. Jikinta har tsuma ya fara yi, burinta ta ganta a
gaban Ramish ta sanar da shi wancan waya da gaske ba na Leesharh bane, tabbas
Leesharh ba muguwa bace, dama ta kafe a kan wayar ba tata bace, ashe tana da
gaskiya.

Nan take ta ji karfi ya zo mata, dik wani kasala ya gudu. Da gudu ta juya ta nufi
hanyar fita daga ɗakin. A dab kofar fita suka yi karo da Ummie zata shigo ta
dubata. Ai tsabar farincikin da zumuɗin ta isa ga Ramish bata tsaya bin ta kan
Ummie ba ta yi waje a miliyan.

Bata zame ko'ina ba sai part ɗinsu Bilal, Ummie na kiranta amma ina bata saurara
ba, wasu irin zafafan hawayen farinciki ne ya rinƙa tsere a saman face ɗinta, ji
take kamar ta ɗaura hannu bisa kai ta yi ta zunduma ihu mai sautin gaske ko zata
ɗan samu sassauci.

Dr Raj kawai ta iso a cikin parlournsu, yana zaune ya tasa laptop a gaba yana
bincike a kan wata cuta da ake yawan korafi a kanta a hospital ɗinsu, kamar sabuwar
cuta ce da ta keta tsaron likitoci, so a matsayinsa na babban likita ya dukufu a
kan neman maganinta babu dare babu rana.

Ko sallama babu ta afko masu cikin parlon, a yadda ta shigo da wani ne zai razana
sosai, amma da yake jinin Modarawa ne shi ɗin ko kaɗan bai razana ba, sai da ma ya
ɗauki 1 min kafin ya ɗago da kallonsa a kanta, izzar sarauta ta motsa.

Kallo mai wuyar fassaruwa ya wurga mata, ta wani shigo kamar wadda aka koro,
ko sallama babu. Nan take ta sha jinin jikinta, dama idan ba Yah Rizwan ba babu mai
sakar mata fuska a cikinsu, shiyasa sam bata wani yinsu sosai.

Bai ce mata ko uppan ba ta fara ƴan kame kame tana ɗan juye juye, still dai bai ce
ko sannu ba, ya mayar da kansa a kan laptop ɗinsa ya cigaba da aikin dake gabansa.

Tsabar tsarguwa da tsorata bai tambayeta ba ta fara magana a rikice tana haɗe
word....... "Yah Raj dama Yah Ramish nike nema, dama zan bashi wayar Leesharh ce
wlh ba ita ta..............".

A miliyan ta haɗiye sauran maganganun a cikinta bata kai karshe ba saboda sauka da
idanunta ya yi a kan Ramish dake tsaye bakin kofar shigowa cikin parlourn daga
bedroom side ɗinsu.
Ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, Bluetooth mai kyau da tsada ce manne
a kunnensa, da alama waya yake yi, amma saboda tsabar nitsuwa irin nasa daga
sharifat har Dr Raj babu wanda ya iya jin abin da yake faɗe, ƙasa ƙasa cike da
class da nitsuwa yake wayar.

Yana sanye da sexy sleeping dress a jikinsa, tamkar wani mai aure, ga idonsa kamar
dai, to na dai yi shiru, amma da alamar tambaya fa a tattare da shi, sai tashin
kamshi yake yi, da alama bai jima da farkawa daga barci ba, yanayin kayan barcin
nasa idan ka gansa sai gabanka ya faɗi, shiyasa nace kamar wani mai aure, da alama
wlh Yah Ramish ɗan duniya ne sosai, gabaɗaya gaban rigar a buɗe take, faffaɗar
kirjinsa a waje, dik macen da ta gansa haka sai kirjinta ya buga, kai ko namiji ya
gansa a haka sai kirjinsa ya buga bare mace, ka gansa cikin full kaya ya rufe
ko'ina nasa ma sai ka ji ka faɗa da shi bare kuma ya buɗewa mutane gaban kirjinsa
dan iya hege.

Sharifat da ta zama kamar wadda aka sassaƙa a waje ya wurgawa hegun sexy eyes
ɗin nan nasa yana cigaba da magana da wanda suke waya. Yadda kuka san idanunsa
allura suka yi mata, wani irin zabura ta yi da ya kalleta, da karfi ta furta.
"WAYYO ALLAH". Ta yi maganar tare da juya mashi baya.

Allah sarki a take ta birkice kamar wadda aka zarewa kaso hamsin cikin ɗari na
hankalinta.

Dr Raj da ya ji ta furta wayyo Allah ta, sai ya ɗago da kallonsa a kanta, dai'dai
lokacin ta juyawa Ramish baya hannayenta sai kerma suke yi. Ganin yadda ta juya
baya da sauri yasa ya juya ya kai kallansa a kan kofar da zata sadaka da bedrooms
side ɗinsu, dama tin da yaga ta yi irin wannan juyi ya yi tinanin Ramish ta gani,
dan shi kaɗai take yi wa irin wannan abin.

Ganinsa a tsaye yasa ya mayar da kallonsa a kan laptop ɗinsa, dan a cewarsa sun fi
kusa, baya shiga shirginsu. Tana san gudu ta bar part ɗin, tana kuma san yi mashi
magana dan ta ceto ƴar uwarta Leesharh, sai dai ba zata iya juyowa ta sake kallansa
a irin wannan shiga ba, yana ɗaga mata hankali kuma yana rikitata, ga shi wandon
sleeping dress ɗin ma sai wanda ya gani, ku baku ji sunan kayan bane ma, sexy
sleeping dress, ai daga nan zaku gane ba kayan arziki bane, na masu aure ne, shi
kuma shirgegen gwauro da shi ya zo ya wani saka su.

(Sai su Yah Rizwan sun yi mashi fyaɗe da tsakar dare kila zai dai'na saka kayan
ma'aurata 😅😅😅😅😅 na faɗa a saka mun gas😅ni bana tsoron Ramish da💪🌝 )

Dr Raj ya cigaba da aikin gabansa, shi ma Ramish juyawa ya yi ya koma cikin
room ɗinsa, saboda dama ya leƙo parlourn ne dan ya duba Bilal yana nan ko baya nan.

Jin alamar ya bar wajen yasa ta wani sauke nannauyar ajiyar zuciya wanda har sai da
Dr Raj ya jiyota, amma ko a gefen takalmarsa ya cigaba da abin da yake yi.

A hanzarce ta juyo, kirjinta na dukan uku uku ta bi bayan Ramish da kallo, har ya
kurewa ganinta, komai nasa abin burgewa ne. Wani irin ta ji a ranta, wani ɓangare
na zuciyarta yana ce mata ta bi bayansa, wani kuma yana ce mata

Please Login or Register in order to submit comment