Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 80 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hakan yasa ya
kira Smart a waya ya sanar da shi ga halin da yake a ciki, ashe dama sarautarsu ba
ta Allah da annabi bace, sosai Smart ya yi mamakin jin hakan, a lokacin suna a tare
da Zash, dan su ukun a tare suka yi karatu.

In short dai Smart ya ce da Bobo ya ɗauki ƴan uwan nasa ya bar ƙasar, dan faɗa fito
na fito da su lokaci guda ba zai yiwu ba, dole sai sun yi shiri, idan kuma ya ce
zai zauna a tare da su har su yi shiru zasu iya matsa mashi, idan bai biya masu
buƙatarsu ba zasu iya kashe shi, dan ya rigada ya san sirrin RAWANIN JINI. Wannan
dalilin yasa Bobo ya shirya makirci cikin dare ya ɗauke mom ɗinsa da kannen nasa
dikka biyu ya gudu da su zuwa kasar France, Smart ne ya tsaya mashi tsayin daka
sosai, mom ɗinsa dama a tsananin tsorace take, hankalinta a mugun tashe, tana cike
da fargabar waye ɗanta zai zaɓa ya fiso, tsoronta kada ace ita ce, kun san wanda
baya tsoron Allah da shegen tsoron mutuwa, wlh billahi dik wanda baya tafarkin
Allah shegen tsoron mutuwa ne da shi kamar me, dik wanda yake da karfin imani baya
tsoron mutuwa, dan already yasan sai ya mutu, kuma idan na kwarai ne shi yasan
lahira ta fi mashi duniya sau miliyoyin miliyoyi, dan haka zai so ya tafi lahira ma
sai ta fi mashi.

Mom ɗinsa tana tsorace, dan ita tasan wannan al'ada, amma kannensa mata basu san
wannan al'adar ba. Lokacin da ya shirya ya ɗaukesu daga kasar ba karamar daɗi mom
ɗinsa ta ji ba, sai dai kuma taki ta musulunta har wa yau, ba yadda bai yi da ita
ba, har ya faɗa mata cewa saboda addinin musulunci yasa bai yi sadaukarwar jini ba,
musulunci yasa bai zaɓeta an kasheta ba, dan haka ta musulumta shi ne addinin
gaskiya, amma matar nan ta ce babu wannan magana, ba zata musulunta ba, har da cewa
Allah ya yi wa Musulunci albarka da ya kuɓutar da su, amma dai ita ba zata
musulunta ba, Smart ya ce mashi ya cigaba da binta a hankali kamar yadda shi ma
yake lallaɓa mom ɗinsa ta musulunta, idan suna da rabo watarana za'a dace, to haka
dai suka yi, kunji kaɗan daga tarihin Bobo. Amma fa har yau har gobe neman Bobo
suke yi dan su kashe shi, ya karya alkawari da dokokin BLOOD CROWN, suna nemansa
kamar hauka, yanzu an dai'na tinanin ya hau mulki ma, tinanin kashe shi kawai ake
yi, jininsa za'a baiwa BLOOD CROWN! Tashin sense, kai akwai cakwakiya fa, bamu fara
wasan ba, ku jira bayan bikin Auta balbalin kura zai taso daga sararin samaniya,
gobara zata taso daga kogi, wanda kwantar da wannan bala'i sai Allah kawai!!.

Kada ku ga laifin mahaifiyar Bobo na kin musulunta, saboda mijinta ya taɓa hawa
gadan mulkin BLOOD CROWN, kamar yadda mijinta ya sanya wannan RAWANI imani da
tausayi ya fita a ransa, haka zalika ita ma majalisar dokokin masarautar masu
alhajin kula da BLOOD CROWN suka cire mata dik wani tausayi da imani, shiyasa bata
yi wa su Bobo da sauki, wlh barema Bobo, yana shan wahala a hannunta, tana tauye
masu hakkinsu, bata san barinsu su sarara, harta ƴaƴanta mata, tana da bakar zuciya
na mugunta sosai, kafin su iya samu ta dawo na kwarai to fa sai ranar da aka ruguje
BLOOD CROWN!!. UHM AKWAI RINA A KABA!!.

INTERMISSION. NAN SHI NE TAAKIYAR LITTAFIN RAWANIN ZALINCI.🔥♥️

--------------------------------🔥♥️

To fa, mun zo dai'dai wani gaɓar da dikka masarautu biyar na RAWANIN ZALINCI suka
gama bayyana, zan lissafo maku su sai in baku aikin zaƙulo stars ɗinku daga kowacce
masarauta. Na farko akwai KINGDOM OF POWER, na biyu CROWN OF INJUSTICE wato BLACK
WORLD, na uku akwai KINGDOM OF JUSTICE, masarautar Queen Zarina kenan, na huɗu
akwai EVIL KINGDOM, masarautar su Yusuf, na biyar akwai, BLOOD CROWN, masarautar su
Bobo, dama na ce maku masarautu biyar ne, kuma dik mugan abokan gabane da basa
shiri kwata kwata, kuna dai gani yakar juna suke yi, RAWANIN ZALINCI ya zo da
sabbin salo na daban, stars na littafin nan su bakwai ne zuwa takwas, kowanne kuma
zai fito daga ɗaya daga cikin masarautun nan, KINGDOM OF POWER ce kawai take bada
stars guda biyu, yanzu aiki ya ragunmaku, dikka masarautu biyar sun bayyana, saura
a fara ainahin yakin bayan bikin Auta kenan, dama in da nike ta fatan in iso kenan,
kuma Allah ya kawo mu!. A yanzu ba zan kira maku Stars da kowacce masarauta zata
bayar ba, daga matansu har mazansu, saboda kuna tare da dayawansu ne baku san daga
ina suke ba, idan kuka san daga in da suka fito a nan ne zan bayyana maku kowani
masarauta da stars ɗin da ta bayar, amma ku cigaba da canki cankanku...... 😅

(Kam bala'i, gaskiya RAWANIN ZALINCI ya zo da salo na daban, wai har yanzu laluɓar
stars ake yi! Tab to akwai show a nan gaba, ku mu je dai zuwa, zaku sha mamaki
fa.😅 To amma a Black world dai mutum biyu muke da su da zasu iya zama star, akwai
Ronnie da King Lucian, amma bamu sani ba ko wani zai bayyana a gaba, sannan a
masarautar Queen Zarina akwai Rishan ko kuma Ude, na gaba, a masarautar evil
kingdom akwai Yusuf da Adam.😅Masarautarsu Bobo wannan kun rigada kun sani na faɗa
maku cewa Bobo na daga cikin stars guda shiddan nan, a kingdom of power kuma waye
kuka zaɓa a matsayin star? Wannan fa ba zaɓina bane, zaɓin ƴan special grp ne, ni
tukun nan ban zaɓa maku stars ɗin ba, ku jirani bayan bikin Auta da Abdussalam
akwai tada tarzoma, dan lallai kwakwalwarku zata yi caji fiye da tinaninku, muje
zuwa cikin labari my people's)

----------------------------------------🔥🔥🔥

Kwanciya Bobo ya yi a saman sofa yana kallan Zash dake latsa waya, shi ma Smart
Zash ɗin yake kallo, kamar suna zargin ya ɓoye masu wani abin ne. Shi kuwa
hankalinsa gabaɗaya a kan wayarsa. Bobo zai yi magana phone ɗinsa ta gara ringing.
Cikin natsuwa ya cirota daga aljihunsa yana ɗan lumshe Amber eyes ɗinsa kamar yana
jin barci, lovely sis shi ne sunan dake yawo a saman screen ɗin, picking ya yi tare
da matsar da wayar can gaba domin su ji daɗin ganin juna da kyau, video call ta
kirasa. Wata kyakkyawar yarinya ce mai kama da shi sosai, idanunta starry Eyes ne
masu bala'in kyau, kwayar idanunta Jade ne, suna wani walkiya kamar ruwan hawaye ne
kwance a cikinsu, kuma haka suke, shi kuma Bobo phoenix Amber eyes yake da shi, shi
ne ya banbanta shi da ita!, hancinta sharp nose take da shi, ga yawan eyebrows very
thick dark brown.

Yana picking kuka ta saka mashi cikin shagwaɓa har sai da tasa Zash da Smart suka
juyo da kallonsu a kan Bobo ɗin. Shiru ya ɗan zuba mata ido yana kallan yadda take
kukan, kamar wacce aka sanya dole ta yi kuka. A tausashe sosai ya ce. "Pinkish
lafiya kike kuka?".

Da sauri wata kyakkyawar yarinya kamanninsu ɗaya kamar tagwaye ta kwace wayar tare
da faɗin. "Bro wai kuka take a kan kewarka". Ta faɗa tana kallansa. Juyar da kansa
Smart ya yi ya cigaba da yin abin da yake yi, miƙa mashi hannu Zash ya yi a kan ya
bashi wayar. Ba musu ya miƙa mashi yana kallansu da ido. "Beauty ina babyn take
bata bari in faɗa mata yaushe Bobo zai dawo". Cewar Zash.
Baki beauty ta washe kafin ta ce. "Laaaa Yah Zash dama kuna tare? Shi ne baka
nemanku ko? Kullun zamu kira Bro amma bama sanin kuna tare". Ta faɗa tana ɗan
zaroviolet eyes ɗinta...... "Sorry aiki ne suka yi mun yawa, amma a mun afuwa,
yanzu dai bawa wancan rigimammiyar da kullum idan ta kirasa sai ta yi mashi kuka".

Maman Sultan saboda ke da Aisha Jajeri na kara yawan page ɗin nan. Dan haɗani da
Allah da kuka yi!!!.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



53


Miƙawa Pinkish wayar ta yi, har lokacin tana kuka hawaye bibbyu ta karɓa, idanunta
a tsaitsaye, gashin idanun nata a tsaitsaye alamar bata da kunya ko kaɗan. Zuba
mata idanu ya yi yana kallan yadda take kuka bilhakki da gaskiyarta, kai abin ma
dariya ya so bashi, ta wani zage, taki ɗago kai ta kallesa, tana kallan ƙasa, a
tinaninta Bobo ne, wai ita nan zata gwada mashi ranta a ɓace yake sosai dan ya yi
maza ya dawo!. "Bana ce ki rinƙa rufe kanki kuma ki rinƙa sanya sutura masu rufe
jiki ba?". Shi ne abin da Zash ya faɗa cikin sanyin murya.

Ai tana jin voice ɗinsa a miliyan ta ɗago da kanta, tana sauke kallanta a kansa
bata san time da ta waro idanu waje ba, wani irin walwali Zash ya gani na idanunta
kamar in an haska madubi a rana, tana ganin shi ne ta yi gaggawar miƙewa zaune, yau
babu shagwaɓa sam sam, cike da mamaki ta ce. "Yah Zash dama kai ne? Amma ai kaman
Yah Bobo na gani, ko dai numberka na kira ne dama? Kuma dai Yah Bobo na kira fa". A
dibirbirce take maganar, tana wani kame kame. Zuba mata idanu ya yi yana kallan
yadda take wani muzurai kamar maras gaskiya, tasan sun yi alkawarin zata rinƙa
sanya ɗankwali da sutura ta kwarai, bata san shi ya karɓi wayar ba da ba zata taɓa
yarda ya ganta a haka ba, kuma wlh tana rufe jikin nata dan cika alkawarin da ta
ɗaukar mashi, yau ne kawai aka samu matsala bata rufe ba, tashinta daga barci
kenan, yanzu tasan kome zata ce ba zai taɓa yarda tana rufe jikinta ba!.

"Yah Zash ina rufewa fa, kuma yau ɗin ne na manta ban rufe ba, ka tambayi Aunty
beauty zata faɗa maka". A dibirbirce yanzu ma ta yi maganar, word ɗin suna sarke
mata. Shiru dai bai amsa mata ba, hakan ya kara dibirbirtar da ita ya yi, tana san
ya yi magana dan ta san ransa ya ɓaci ne ko bai ɓaci ba,.amma ya yi shiru. "To Yah
Zash bari in ɗauko kayan in saka ka ji?". Ta faɗa tana kallan cikin idonsa zat tana
jiran me zai ce, ko kunyarsa bata ji ba. Kuma fa zata kai irin 15 years haka, amma
babu ko kunya, ga shi kayan barcin jikinta irin riga mai ɗan siririn hannun nan ne,
ga cup na breast, ya fitar da gabaɗaya shatin nipples ɗinta, ga tudun breast ɗin
nata ma dikka a waje.

"Yah Zash ka yi magana mana". Tamkar zata sanya kuka ta yi maganar. Siririn
harara ya bita da shi kafin ya ce. "Sai da kika ganni ɗin ne zaki ce bari ki je ki
saka kaya? Ya muka yi dake time da na zo gida last?"...... A word ɗinsa ta fahimci
bai ji haushi ba, ransa bai ɓaci ba kenan, dan haka sai ta saka mashi shagwaɓa,
tana turo baki ta ce. "Da gaske Yah Zash ina saka kaya manya, wai baka ga yanzu na
tashi daga barci bane?". Harara ya sake binta da shi kafin ya buɗi baki da nufin
magana sallamar Auta ta karaɗe kunnuwansu.

Gabaɗaya kai kallansu suka yi a kansu. Ai Smart bai san time da ya zaro idanu yana
kallan Pretty ba, ta yi masifar kyau cikin English wears ɗin nan, ya ilahi kowa ya
ganta sai ya sake waigawa, Auta ta kasheta da haɗuwa, madarar kyanta ya kara
bayyana. A ransa ya ce kaga yarinya kamar ita ta yi kanta, ƴar karama sai shegen
kyau da shegen miskilanci.
Pretty ba hankali, ko sannu bata cewa su Bobo ba, ta wuce ta yi zamanta saman sofa,
ko kallan in da suke ma bata yi ba, kamar bata san da halittarsu a wajen ba. Ita
kuwa Auta cike da zumuɗi ta ƙarisa wajensu, wajen Zash ta fara nufa tana faɗin.
"Yah Zash tin da nazo nike tambayar Yah Omerish ina kake? Sai ya ce mun ka tafi
Dubai".

Hannu ya miƙa mata ta bashi nata tana murmushi, zaunar da ita kusa da shi ya yi
kafin ya amsa mata da. "E jiya na dawo, na yi kewarki sosai my sweetheart".....
"Nima na yi kewarka sosai, kullum sai na tinaka". A shagwaɓe ta faɗa. Cike da
zolaya ya ce. "Da gaske anyi kewata ɗin nan kuwa?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e da
gaske. Wani irin kallo ya wurga mata mai kama da hararar wasa yana faɗin. "To
meyasa ba'a kirani ba tin da an yi kewata?". Zata yi magana ta ji murya cikin harsh
voice ance. "Yah Zash wacece kuma wannan?!". Bawan Allah shi ya ɗan manta ma waya
yake yi!.

Dawo da kallonsa a kan wayar ya yi kafin ya amsa masu da. "She's my sweetheart". Ya
faɗa yana ɗan riko shoulder ɗinta, ya matsar da ita jikinsa kafin ya ɗan sauko da
wayar dan su samu damar ganinta sosai. Cool murmushi ta sakarwa Pinkish kafin ta
ce. "Sannunki".

Ɗaure fuska sosai Pinkish ta yi, sai ma da ta ɓalla mata harara kafin ta amsa da.
"Yauwa". Saura kaɗan su saka Zash murmushi, Pinkish bata da hali mai kyau, ita sam
sam bata san mutane, ji yadda ta haɗe rai fa, amma fa a ganin Zash ne bata san
mutane shiyasa ta ɗaure fuska dan taga Auta, ku fa a ganinku me yasa ta yi hakan?.

"Yah Zash she looks like Yah Bobo". Cewar Auta kenan. Jinjina mata kai ya yi kafin
ya sanar da ita kannen Bobo ne, kara faɗaɗa murmushinta ta yi baiwar Allah, sannan
ta kara ce masu sannu. Fuska a ɗaure tamau ta ce. "Wacece ke kuma?".

Tana ta fara'a ta amsa da. "Sister Yah Omerish ce ni". Bata ƙarisa maganar ba
beauty ta leƙo da kanta ta cikin wayar, wani irin haɗaɗɗen murmushi ta sakarwa Auta
kafin ta ce. "Wow they looks alikes, you're so cute, pretty and beauty like him, i
like you!".

Sosai Auta ta ji daɗin kalamanta, tana murmushi sosai ta ce. "Same, I like more,
and you're very beauty more than me". Girgiza kai ta ɗan yi. "Not more than your,
lest than your okey?"........ Zata yi magana harsh voice ɗin baby ya katsesu da
cewa. "Then so what if she's beauty? Am also beauty more than........".

Zash ne ya katse mata maganar bata karisa ba ta hanyar zaro almond eyes ɗinsa, ya
yi mamakin jin yadda take faɗa, dik da yasan dama mafaɗaciya ce kamar mom ɗinsu,
ba'a taɓata ta yi shiru, to amma me Auta ta yi mata da zata fara faɗa da ita kawai
ba gaira babu dalili?.
"Pinkish are you hard what you're saying?". Cewar Zash. Shi dai Smart ya koma
kan aikin da yake yi, yana yi yana satar kallan Pretty da ta kwanta tana kallan
sama kamar mai motsi a kai, ta yi shiru kamar dai bata tare da su haka. While shi
kuma Bobo hankalinsa na'a kan tiger dake kwance a can kusa da pool dake wajen.
Pretty bata san da tiger a wajen ba.

Ganin Pinkish bata nuna mata so ba yasa ta tashi daga wajen, dan bata san mutum ya
nuna mata kiyayya. Kusa da Smart ta zauna hankalinta a kan Bobo ta ce. "Yah Bobo
sannu da zuwa". Hararar ya wurga mata kafin ya ce. "Sai yanzu kika ganni?". "Sorry
Yah Bobo waya nike yi fa". Dawo da kallansa a kanta ya yi kafin ya ce. "A'a kin
dai'na san Yah Bobo yanzu, Yah Zash ya fini"....... "Yah Omerish ka faɗawa Yah Bobo
ban fi san kowa ba, dikkanku ina sanku kamar rai'na". Ta faɗa kamar zata yi kuka.

Hannunsa Smart yasa ya janyota jikinsa, can ƙasa cikin sigar rarrashi ya ce.
"Kyale Bobo, yana cikin damuwa ne zai sauke mana a kanki, bashi hai"..... Take ta
ji tausayin Bobo ya mamaye zuciyarta, cike da alhini ta ce. "Yah Omerish meyasa me
shi?". "Matsala ce ta gida shi da mom".

Kamar zata yi kuka ta dawo da kallonta a kansa. "Sorry Yah Bobo ka ji? Believe
Allah Everything it will come to and end". Jinjina kai ya yi kafin ya ce. "In Sha
Allah our sweetheart"..... Shi kuwa Zash ya zage sai bawa Pinkish hakuri yake yi,
ita kuma ta kafe a kan bafa zata hakura ba, dan ranta ya ɓaci, daga karshe ma kashe
wayar ta yi tana kuka, ya rasa me ya yi mata ya bakanta mata rai har haka. Pinkish
manyan ƙasa!.

"Yah Omerish mu tafi to". Cewar Auta. "No my sweetheart, baki ga su Bobo sun zo
ba, mun fasa fita, sai gobe". Take fuskarta ta nuna rashin jin daɗin hakan, ta so
yau tun da sun samu dama su fita, amma kash hakan ba zai yiwu ba, miƙewa ta yi jiki
ba kwari ta nufi barin wajen. Har cikin ransa ya ji cewan bata ji daɗi ba, amma ya
yi kamar bai gane ba, hannun Pretty ta riƙo tare da cewa. "Pretty zomu je bedroom
ɗinmu mu kwanta mu yi hira". A miliyan Pretty ta ɗago da kanta. "Fitar fa?". Ta
jefa mata tambayar tana kallanta, yarinyar nan tamkar bata san da halittar mutane a
wajen ba, wlh da a gidan sarauta cikin gata Pretty ta tashi za'ayi bala'i, wato dik
miskilanci mutum sai ya sarara mata, wannan ma ba wayewa ne da ita ba, da yake dai
a jininsu abin yake ne sai gata tana dakonsa.

"Yah Omerish ya ce ba zamu fita yau ba sai dai gobe". Auta ta bata amsa tamkar
zata yi kuka. Girgiza kai Pretty ta fara yi kafin ta ce. "A'a ni ba zan yarda da
hakan ba, tin da ya ce zai kaimu yawo to sai ya kaimu!". Cike da gadara ta yi
maganar, sak dai yadda shi yake magana da gadara kamar kowa mallakinsa ne a
karkashinsa yake, ashe ba laifinsa bane, sarauta ke ɗawainiya da shi, to yau dai ya
samu dai'dai da shi.........😅

Da mamaki gabaɗayayansu suka ɗago da kallonsu a kanta, sai a yanzu Zash ya san da
ita a wajen, shi ma Bobo dik da ta zo ta wucesa bai ɗago ya kalleta ba, hankalinsa
a can duniyar tinani, sai a yanzu ya ganta. Shi kan Smart wlh burgesa take yi, sai
ma idan tana magana, a yanayin yadda yake kallan abin nata kamar yarinya irin ce
mai cike da class da ji da kanta, zaku iya zama da Pretty tsawon wuni a waje guda
word ɗaya bai haɗaku ba, in baka mata magana bata yi wa mutum, idan ma ka yi mata
ɗin ma sai ta yi niyya zata amsa, kamar wata mai aljanu.

A ɗan rikice Auta ta ce. "Pretty Yah Omerish ne fa, meyasa zaki ce haka? Shin ba
yayanki bane shi?". Ɗan turo baki ta yi, kuma dik maganar da take yi kallanta a
ƙasa, bata ɗago kai ba bare ta haɗa ido da kowa. "To shi Yah Omerish ɗin ba shi ya
yi mana alkawarin zai kai mu ya wo ba? Waye ya ce mashi ana saɓa alkawari? Ko bashi
da ilimi ne? Kuma shi ɗin waye ne shi da ba za'a faɗa mashi gaskiya ba? Dole ya
cika alkawari ya fita da mu!". Babbar magana, mai ilimi tana magana, wai Pretty ce
zata cewa wani bai da ilimi, ita da lokacin da mamansu ke karantar da su tana
karkashin korama tana shakar iska mai ni'ima, Sweetie na kwasan ilimi, amma da ɗan
guntun karatunta da bai wuce primary 3 ɗin bane zata ce wai wani bai da ilimi, kai
Pretty ƴar duniya ce wlh.

Zash da Bobo kallan Smart suka yi, har suna haɗa baki wajen tambayarsa wacece
Pretty. Mayar da kansa a kan laptop ɗinsa ya yi, bashi da amsar da zai basu, dan
shi ma bai san wacece ita ba. A karo na biyu suka sake tambayarsa, kawai sai ya ce
masu sistersa ce. Da mamaki suka sake binta da kallo, kwata kwata bata yi kala da
ƴan gidansu ba, kalarta daban, ko iya kyakkyawan eyesball ɗinta kawai ya isa ya
fahimtar da mutane ba zubin larabawa gareta ba, amma sai basu yi wani dogon tinani
a kan komai ba, suka yi shiru kawai.

Auta na kokarin yi mata magana ta wuce izuwa in da Smart yake zaune, ƴar rainin
wayo bata ganin mutane ashe tasan in da kowa yake zaune. A kusa da shi ta tsaya,
tana zuwa ta riko hannunsa a cikin nata, cikin shagwaɓar da take yi wa Kamran,
without respect ta ce. "Ka tashi ka kaimu yawo ka cika alkawarinka!". Kamar Momma
ke bashi umarni, ba abin ya maketa ta mutum mashi a wajen ya yi kisan kai
ba............ Shi yanzu ya fara yi mata kallan mai matsala a ƙwaƙwalwa, har ya
fara tinanin yin scanning na brain ɗinta.

Tsawa Auta ta daka mata a kan bata da hankali ne? Ita bata san babba bane?. Kuka ta
saka tare da faɗawa jikinsa, ita ba ruwanta da wani babba, bata ma nemi sanin ko
waye shi ba ato, kawai tin da ya yi alkawari bai isa ya karya ba, dole ya cika
mata. Babbar magana, ai rasa abin faɗe ya yi, su Zash sun tsaresa da ido kawai suna
binsu da kallon mamaki, yau sun ga wadda Smart yake ragawa,.abin wlh ya yi mugu
mugun basu mamaki.

Shi kuwa banza da ita ya yi, kamar bai san tana yi ba, ta rinƙa kuka kamar wadda
aka saukarwa da wahayin yinsa, Auta dai sake baki ta yi ta rasa abin faɗe. Cigaba
da aikinsa ya yi yana tinanin tafiyarsu kingdom of power jibi da za su yi, zasu je
su amsa kiran King. Ya yi nisa cikin tinanin da yake yi sai ji ya yi tamkar wanda
aka tsayarwa da gabaɗaya jinin jikinsa, cak ya ji kowani kofa na jininsa ya dakata
da yin aiki, lokaci guda ya jisa a duniyar mercury. Slowly ya dawo da kallonsa a
kanta. Tana kuka tana yi mashi wasa da cibiyarsa kamar ya sakata, sam bai ji
lokacin da ta ɗaga mashi riga ba, sai jin ɗan yatsarta ya yi a cikin cibiyarsa.

Ai wani irin shocked da ya yi sai da yasa su Zash hankalinsu ya dawo kansa, amma
basu fahimci dalilin shocked ɗin ba, saboda basu iya ganin me Pretty ɗin take mashi
ba, dik da haka sai suka tambayi dalili. Kai kawai ya iya girgiza masu, Pretty na
nema kiran ruwa, dama yaya, su da suka yi gadan abin, lallaɓa rayuwarsa yake yi
amma yarinyar nan zata jefa shi cikin bala'i. Da kyar ya iya riƙo hannunta a cikin
nasa, a take ya ɗaure fuska wai irin ta zaci ba wasa yake yi ɗin nan ba.

Sai dai tana ɗago kanta suka kalli juna ido cikin ido sai ya nemi dik wani zafin da
ya ɗauka ya rasa, kwayar idanunta sun sanyaya mashi rai lokaci guda. "Tashi muje
to". Shi ne kawai abin da ya iya faɗa mata. Ba musu ta miƙe daga jikinsa...........
"Zash muje yawo". Ya faɗa yana kallonsu. Miƙewa Bobo ya yi ya kwanta yana faɗin sai
sun dawo shi babu in da zai je. Shi kuwa Zash ya miƙe tsaye yana faɗin su je zai
samesu a can bari ya je gidansu Bobo ya ɗauki Pinkish and beauty sai su je a tare
daga nan sai su wuni a nan a tare. Sosai Bobo ya ji daɗin wannan al'amari, saboda
ko ba komai yau zasu huta da masifar mom ɗinsu. Haka kuwa aka yi.

Smart dan dolensa ya ɗaukesu suka fita, in ba haka ba Pretty ba zata barshi ya
zauna lafiya ba, sai dai kuma ko da suka fita ɗin ma bai tsira ba, dan tana manne
da shi, dik in da zai shiga taki rabuwa da shi saboda shegen tsoro. Sai ma da suka
shiga katafaren wajen shaƙatawa dake ƙarƙashin teku, wajen ne na glass da kana ciki
kana iya kallan yadda manya da ƙananan kifaye da sauran halittun ruwa suke shawagi.
Ita dai Auta ta saki jiki sai kallo take yi tana ɗaukar hotuna kala kala, kai tsaye
tana turawa Hoorain ɗinta. Ita kuwa sarkin tsoro ta ƙanƙame shi dan dole ya
rungumeta suka rinƙa yawo a ciki. Da suka je restaurant na cikin wajen, dik san
abinci irin nata a wannan rana dai ta ce ba zata ci wannan abincinba, ba yadda
Smart bai yi ba taki, har ce mata ya yi zai bata a baki, amma taki yarda, ba komai
yasa taki ci ba face abincin ruwa ne, a wajen basa sayar da komai sai namomin cikin
ruwa, gani ta yi sun bata kyama sosai wasu halittun, sai daga baya Smart ya fahimci
tana da kyankyani ne, dan haka sai ya ce a kawo mata kifi wanda aka cire kayarsa
tsab, dan yasan halinta, ba iya gyarawa zata yi ba, ta ci kaya ta barshi da wahala.

Da aka kawo mata ta ji daɗi sosai ta kuma ci, dan shi wannan ta saba ci a wajen
Kamran!. In short yau dai sun sha yawo sosai yadda yakamata, a taƙaice dai kafin su
koma kingdom of power sun

Please Login or Register in order to submit comment