Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 19 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanan
bakinciki, tana tsoron dawowa kuma saboda tasan aika aikan da ta yi, tana san
dawowa kuma saboda ta hana su bappa kwanan farinciki shi da Mairo.

Haka dai ta daure ta kwana a gidan Arɗo, da asuban fari sai da ta daidai ci lokacin
da maza gabaɗaya suka tafi masallaci, sai ta sato hanya ta dawo gida.

Nan ta isko Mairo saman dadduma tana addu'a, bata ce mata ko uppan ba ta wuce izuwa
ɗakinsu Mahnoor.

Tabbas Mahnoor ta ji shigowarta, amma da yake barci ya ci karfinta sai ta kasa
motsawa, daren jiya bata yi barci ba, ta kwana kukan rashin mijinta, barci ya
kauracewa idanunta, sai yanzu gabanin asuba ɗin nan ne barci ya ɗauketa, da kyar ta
iya gabatar da sallah.

Ganin Mahnoor tana barci Mahreen kuma tana cikin ɗakinta ne yasa Nenne ta fito ta
shiga kitchen, a dai'dai lokacin ita ma Mairo ta fito domin ta hura wuta, karo suka
yi a cikin kitchen Mairo ta ɗaga mata gaisuwa.

Ai yadda kuka san bango Mairo ta yi wa magana ba ita ba, ta yi banza da ita. Ita ma
Mairo sai ta wuce ta ɗauki bokiti zata ɗebo ruwa. Kwace bokitin Nenne ta yi ta ɗebi
ruwa a ciki ta wuce fuuuu sai ɗakin Mahnoor.

Ita kuwa Mairo baiwar Allah sai ta koma cikin ɗakinta ta ɗauko wani bokitin mai
ragowar ruwan da ta shiga da shi daren jiya dan kada ya yi sanyi sosai idan zasu yi
alwala, dama suna shiga da ruwa a bikiti su ajiye a cikin ɗakinsu, da asuba da shi
suke yin alwala, ruwan cikin kitchen iska na bugasa ya yi sanyin da in suka zo yin
alwala zasu wahala, so yanzu da asuba ita da bappa sun yi alwala sun bar ragowar,
sai ya ɗaukosa ta nufo waje.

Tana sako kai zata fito waje ta ji ihun Mahnoor.

Da gudu ta karisa fitowa, ita ma Mahnoor da gudu ta fito daga cikin ɗakin nata
jikinta sharkaf da ruwa. Bayanta Nenne ta biyo da sauri, sai huci take yi

Kamar aljanna haka Mahreen ta fito da gudu daga ɗakinta ita ma. Tana ɗaura
idanunta da suke gani dishi dishi a kan Nemne ta san cewa ita ce nan ta jiƙa mata
ƴar uwa.

Nenne zata fara surfa bala'i kenan bappa ya yi sallama, hakan yasa ta haɗiye
maganar da take san yi.

Da mamaki bappa ya fara binsu da kallo. Tin bai yi magana ba Nenne ta yi saurin
cewa. "Wlh Mairo kin ji kunya, yanzu fisabilillah me Mahnoor ta yi maki a cikin
sanyin nan zaki jikata da ruwa fisabilillahi?".

A hanzarce bappa ya dawo da kallonsa a kan Mairo wadda ta zaro idanu tana al'ajabin
maganar Nenne.

"Nenne ki ji tsoron Allah, ni yaushe na jiƙa Mahnoor?". Baiwar Allah maganata
sanyi sanyi kamar na Mahnoor ɗin.

"Oh karya kenan zan yi maki? Wlh idan kika sake ina magana kina magana sai na dirje
maki baki".
Shiru babba ya yi yana binsu da kallo. Mairo ta buɗe baki zata yi magana kenan
Nenne ta sake cewa.

"Idan har mace ta kai mace to wlh ta furta uppan taga idan ban dirje bakin hegiya
ba! Ni saarki ce?". Tana magana tana girgiza sak dai yadda Mahreen take yi idan
tana masifa, ashe gado ta yi.

Ita dai Mahnoor baiwar Allah da sai rawan sanyi take yi ta takure waje guda ko ɗaga
idanu ta kasa yi bare ma har ta kallesu, sai kerma jikinta yake yi saboda iskar
dake kaɗata, ga jikinta sai ɗigar ruwa yake yi.

Bappa dai ya rasa wanene mai gaskiya a cikinsu, domin kuwa dikkansu ga bokiti a
hannunsu, kuma dik bokitin da ragowar ruwa a ciki, to wacece ta watsa Mahnoor ruwa
kenan? Ya kasa gane gaskiya, ga shi Nenne ta fi uban kowa baki a wajen, dole ka
yarda da ita ce mai gaskiya.
Mahreen da idanunta ke ganin mata dishi dishi saboda barci ne ta fara magana
kamar wata ƴar maye.
"Bappa wlh dik in da za'a je a dawo ni nasan Nenne ce ta daki Adda Mahnoor
kuma ta zuba mata ruwa, dan ita ce bata sonta, Diddi Mairo kam nasan tana sonmu
wlh".

Mairo da tin da Nenne ta buga mata warning bakinta ya mutu ne ta sauke nannauyar
ajiyar zuciya jin cewa Mahreen ƴar cikin Nenne ta yarda da ita, sai dai ita yanzu
ta zama ƴar kallo, saboda wlh munafurcin Nenne da iya lauye zancenta ya sha tunanin
Mairo. Balai'n Nenne ya wuci yadda ake tunani, zata aikata abu amma cikin second
zata mayar da laifin kan Mairo tare da hujojin da dole ka yarda Mairo ta aikata,
baiwar Allah Mairo bata da hanyar wanke kanta sai dai Mahreeh ta shigar mata ta
faɗi gaskiya, ita yanzu Nenne ta dai'na bata mamaki.

Kuma a al'adarsu idan babba yana magana yaro baya saka baki kome zai faru, shiyasa
kuma ji Nenne ta dakawa Mairo warning a kan kada ta sake saka mata baki a magana.

"Kai makahone baka ganin bokiti da ruwa a hannunta? Ai ruwan dake ciki ne ta
jiƙa Mahnoor da ita, tsawon shekara nawa muke tare da kai? Tin Mahnoor tana
jaririya na riketa, ban taɓa zuba mata ruwa na sai yau? Meyasa zan yi mata hakan?
Meyasa ban yi mata a baya ba sai yanzu?". Cewar Nenne kenan.

Kunsan dik abin da take yi wa Mahnoor bappa bai sani ba, bai taɓa sanin tana
azabtar mashi da ƴar marainiyarsa ba, so ya ɗauka tsakani da Allah take rike da
ita, wannan dalilin yasa ya fara zargin da gaske Mairo ce ta zuba mata ruwa, saboda
tsawon shekaru bai taɓa ganin Nenne ta musguna mata ba!.

E kam akwai cakwakiya Mairo ta faɗa kaidin Nemne, to ni dai ina bayan fage.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




12


"Allah bappa ba Daddi Mairo bace, ni nasan Nenne ce". Cewar Mahreen.

Bappa da ya gama sanin Mahreen bata karya ne ya jinjina kai, ya ji kuma zuciyarsa
ta yarda da Mahreen ɗin, dan balai'n Nenne sai ita, Allah mai sakayya a lokacin da
bawa bai zata ba, shi ya kasance masifaffe kuma bala'i ga mahaifiyar Mahnoor, shi
kuma Nenne ta kasance kwatankwacin hakan a garesa, shiyasa dayawan lokuta baya kula
Nenne idan tana yin wannan abin nata, yana kallan hakan a matsayin shi da maman
Mahnoor.

A kan Mairo ya tsayar da kallonsa, cikin nitsuwa ya ce. "Taimaka mata ta canza
kaya".

Yana gama faɗar hakan ya wuce ɗaki ba tare da ya sake bi ta kan Nenne ba, ba komai
ya sa bai kulata a yanzu fa face dan su Mahreen suna wajen, baya san su rinƙa samun
saɓani har suna sa in sa a idanun su Mahreen, hakan zai gurɓata tarbiyar da suke da
shi sosai, kuma hakan yanasakawa yara su rage ganin girman iyayen nasu, idan baku
dai'na ba a hankali hankali dik wani mutunci da girma ƴaƴan zasu dai'na ganinku da
shi.

Daga nan sai raini ya shigo tsakani, kana yi wa yaro magana yana kallanka yana
cigaba da abin da yake yi, kunga ai hakan ba daɗi, to sai ku kiyaye, faɗar iyaye a
gaban yara bama iya rai'nin kawai yake haifarwa ba, zaku saka mashi sha'awar faɗar,
idan macece ba zata rinƙa jin shakkar ta gaggayawa mijinta maganganun ba idan ta yi
aure, in namiji ne ba zai rinƙa shakkar zagin mata kai har da duka ba idan ya yi
aure, akwai abubuwa da dama wanda faɗar iyaye a gaban ƴaƴansu yake haifarwa, kome
za'ayi maki ki danne a gaban yara sai kun keɓe nan kam in kin ga dama ɗaga shi ki
maka da kasa..........................😒😅

Ajiye bokitin hannunta Mairo ta yi, ta karisa in da Mahnoor take sanyi ya gama
lallasata, hannunta ta riko suka koma cikin ɗakin nata, Nenne muguwa ta jiƙa mata
mattress ɗinta sosai.

Bayansu Mahreen ta bi, Nenne na kiranta ta bawa banza ajiyarta ta shige ɗakin
Mahnoor.

Bokitin ta ajiye kamar zata bi bayansu, sai kuma ta fasa ta wuce cikin ɗakinta rai
a matuƙar ɓace, da ta so ne bappa ya ci mutuncin Mairo, ya yi mata tas, amma bata
samu hakan ba.

After some minutes.

Mairo ta fito daga ɗakin Mahnoor ta wuce cikin kitchen dan yin abin da ya fito da
ita dama, ƙoƙarin fara hura wuta ta yi, sannan ta ɗauko bokitin ta cika shi da ruwa
ta kawo kusa da murhu, tana ƙoƙarin ɗaura sabon tukunyarta a wuta sai ga Mahnoor ta
shigo cikin kitchen ɗin.

Ta canza kaya izuwa dogon rigar da bappa ya saya mata a lokacin bikinta. Tana sanye
da hujabinta kamar kullum.

Cikin girmamawa ta ce. "Daddi ina kwana".

Fuska ɗauke da fara'a Mairo ta amsa mata da lafiya ta tashi lafiya. Ita ma da
lafiya ta amsa kafin ta ɗaura da cewa.
"Bari in tayaki Daddi".

"A'a Mahnoor, jeki ki kwanta kawai, ba sai kin tayani ba, ai ba wani aiki mai
wahala bane, tuwo zan yi sai sanya maku ruwan wanka".

"Ayya Daddi ki bari in tayaki kin ji?". Yadda ta yi magana murya a marairace, Allah
sarki barci fa take ji, amma kuma ba zata iya kwanciya ta yi ɗin ba, dan yanzu tana
jin tsoron Nennen ta sake zuwa ta jiƙata da ruwa.

Da kyar Mairo ta yarda ta tayata ɗin, dan haka sai ta ce to ta yi shara ita
kuma bari ta ɗaura ruwa sai ta haɗa kayan wanke wanke kafin nan Mahnoor ta gama
shara sai su yi wanke wanke a tare.

A bisa ka'ida yau Nenne ce zata yi abinci ba amarya ba, amma da yake bappa yasan
bata kwana a gidan ba sai ya ce da Mairo ta ɗaura mashi girkin kawai, kunji dalilin
fitowarta da sassafe kenan.

Tsintsiya Mahnoor ta je ta ɗauko, cikin nitsuwa ta fara shara hankalinta gabaɗaya
yana a kan tinanin mijinta, Allah sarki yau ta kai kololuwa a kewarsa, ji take
kamar ta yi ta kuka babu dakatawa, yau da yana nan yanzu warhaka tana kwnace a
jikinsa bata fito ba, a gaskiya ta yarda ta yi babban rashi a rayuwarta wanda ba
zata taɓa manta shi ba har abada.

Dai'dai wannan lokacin da take shara tana tinaninsa.......... Shi kuma yana tsaye a
jikin window ɗin ɗakinsa, ya yaye labulen tamkar mai kallan wani abin a harabar
kingdom ɗin, a zahiri babu abin da yake kallo, tinani kawai yake yi, tinanin ma
wanda bai san namenene ba, kawai a ransa ne yana jin tamkar akwai wani gurbi a
ransa da yakamata ya cike wannan gurbin, ya rasa ganewa zuciyarsa, tana yi mashi
babu daɗi, kamar akwai abin da ya rasa haka.

Hannunsa rike da cup mai ɗauke da cappuccino, yana sha a hankali hankali yana
tunane tunane, yanzu ba jimawa suka dawo saga masallaci sallar asuba, sanye yake da
kayan barci masu bala'in kyau a jikinsa, sun haɗu da Jawad, amma a hospital ya je
ya ga Jawad ɗin.

Allah sarki tamkar su cinye junansu saboda so, sai dai Jawad bai faɗa mashi cewa ya
yi aure ba, ya dai ce mashi Jannat ce bata da lafiya yake jinyarta.

And bai san guyson yana hospital ɗin ba, Jawad kawai ya je dubawa, yana duba shi
kuma ya dawo, dan dik baya jin daɗin jikinsa, baya san fita daga cikin ɗakinsa,
dama shi ba mai san fita bane sai idan ya zame mashi dole.
Yana cikin kuncin da ya rasa me dalili, while ita kuma tana cikin kuncin da ta
san dalili. A haka ta gama sharan nan tas, suka yi wanke wanke a tare da Mairo,
Mairo na wankewa ita kuma tana ɗaurayewa ta sanya cikin baf, tas suka gama gwanin
birgewa sannan Mairo ta kwashe tuwo a kwanikan.

Mahreen kuwa tuni ta kwnata a mattress na Mahnoor ta mayar da barci abinta.

Bayan Mairo ta sauke ruwan wanka, ta sirkawa bappa ta kai mashi banɗaki, sai ta
fito ta shiga ɗaki domin ta faɗa mashi, ita kuma Mahnoor ta fara kwasan kayan
abincin ta fara kaiwa kowa ɗakinsa.

Tamkar wadda aka koro haka Nenne ta fito daga cikin ɗakinta, tamkar wata ɓarauniya
haka ta fara sanɗo, a haka ta nufi cikin toilet ɗin.

Jim kaɗan ta fito sai muzurai take yi tamkar an kama ɓera a tarko, dik alamar
rashin gaskiya ne a tattare da ita, da alama wani mugun abin ta kullah.

Da gudu ta shige cikin ɗakinta, kamar ba ita ta fito yanzu ba, har da kwanciya ta
lulluɓa da zaninta.

Bappa kuwa ya fito ya shiga banɗaki dan yin wanka. Ita kuma Mairo ta hau sharan
ɗakin, da alama Mairo tana da tsabta sosai.

Mahnoor kuwa bayan ta gama, a kusa da Mahreen ta zo ta zauna tare da buga uban
tagumi, a hankali ta fara jin faɗuwar gaba kaɗan kaɗan kamar wani abin yana shirin
faruwa da ita, jingina bayanta da jikin bango ta yi, a hankali ta fara maimaita
Hasbunallahu wani'imal wakil domin Allah ya saukaka mata koma menene yake shirin
faruwa da ita!.

A wani irin haukace bappa ya fito daga cikin toilet ɗin nan, ihun da yake kurmawa
da karfi sai ya razana dik wanda kunnuwansa zasu saurara. Cike da tashin hankali da
firgici ya faɗo tsakar gidan yana ihu.

Mahnoor tamkar bata ji su ba, sam bata fito ba, dan tasan shi da matansa ne, sai ma
kifa kanta ta yi a saman gwiwowinta ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar
mai sauraro.

Da gudu Mairo ta fito daga cikin ɗakin dan taga menene yake faruwa, Nenne kuwa sam
taki fitowa tana ciki kamar bata ji shi ba, sai dai tana can tana zuba uban dariya
kamar wata zararriya.Ta toshe baki da pillow dan kada sautinta ya fita tana ta
tikar dariya.

Mario tana fitowa ta iskosa kwance rashe rashe a kasa yana ta birgima yana ihu
kamar wani zararre, daga shi sai kajeran wando a jikinsa, ita ma bai gama sanyata
da kyau ba, ga kuma ruwa a jikinsa, da alama ya fara wanka ne ya fito, dik kasa ta
buɗe shi saboda ruwan dake jikinsa.

Ganin haka yasa Mairo ta fita waje da gudu neman taimako dan taga kamar wani
mai ciwon aljanu ko farfaɗiya haka, so ba zata iya ba sai ta yi waje dan neman
taimako.

Kai tsaye gidansu Arɗo Mairo ta nufa, ko mayafi bata ɗauka ba, hankalinta ne a
tashe.

Takuwa yi sa'a Ibrahim kawun Mahnoor yana nan, dan haka sai suka taho a tare
da shi da Arɗo.

Dik ƙasa ya farfasa fatan jikin bappa, saboda yadda yake ta dirza jikinsa a kasa
yana ihu, kafin Mairo ta dawo wlh har jiki ne yake fitowa daga fatar tasa, bawan
Allah.

Ashe ƙarara Nenne ta je ta zuba mashi a cikin ruwan wanka, muguwa saboda tasan
Mairo ce ta kai mashi ruwan wankan, kunga yanzu zai ce Mairo ce ta yi mashi
mugunta, Allah sarki daga zuwan amarya bappa zai fara ganin laifinta. Wato wlh
Nenne da gwaggo anya akwai shaiɗanu irinsu kuwa? Dik abin da Nenne take yi gwaggo
take shirya mata shi dallah dallah yadda zata yi komai, shiyasa kuka ga ta dawo
gidan bappa da confidence ɗinta.

Sun lura aikin bokaye baya kama bappa, shi ne suka dawo ta munafurci da kisisina,
komai Mairo ta yi su ɓata, tin bappa baya ganin laifinta har ya zo ya fara gani ya
fara jin haushinta, har ma ya saketa, shi ne burinsu, to yanzu Nenne ta fara fito
da makaman yakinta, muje zuwa dan ganin yadda wannan wasa zata kaya.

Ƙoƙarin kama shi Arɗo dattijon arziki da Ibrahim suka yi dan su kai shi ko da ɗaki
ne kada ƙasa ta cigaba da fasa fatarsa. Sai dai ina, sun kasa kama shi, saboda wani
irin zillo da yake yi, burinsa kawai a sosa mashi jikinsa, wani irin bala'in
kaikayi na musamman yake ji, Allah sarki bawan Allah.

Ga shi kararar ta damuna ce ba ta rani ba, irinta ta fi bala'in zafi, kaikayi kamar
zai kashe mutum, ga zafi idan ka sosa, wlh Nenne muguwa ce ta karshe, tana ɗaki
tana ta dariyar mugunta hegiya.

Mairo kuwa kuka kawai take yi da hawaye bibbiyu, Mahnoor ma tana jin dik abin da
yake faruwa, amma taki leƙowa, saboda bata san ganin wani tashin hankali a kan
wanda take ciki a halin yanzu.

Sai da Ibrahim ya fita ya samo wasu manyan maza su biyu, sannan suka zo da kyar
suka iya kama bappa. Allah sarki abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya,
dan yadda yake birgima sai ya baka dariya, hannunsa dikka biyu a kansa, dan daga
kai ya zuba ruwan, tamkar zai ɗaye fatar kansa saboda sosawa, ji yake yi kawai ya
yi ta dirje kan nasa a ƙasa ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji.

A yanzu ma bai san su wanenen a kansa ba, wlh kuka yake yi sosai, hawaye dik ta
wanke mashi fuska. Mairo dik tinaninta yana da wani ciwo ne da bata sani ba.

Arɗo da ya gane menene sai ya ce da Ibrahim a kawo mashi ɗanyar kashin shanu, dan
shi ne maganinsa.

Jin Arɗo ya ce a kawo ɗanyar kashin shanu yasa Ibrahim ya fahimci karatun, ransa ne
ya yi mummunar ɓaci, a kule ya ce. "Waye ya saka mashi karara kenan?". Ya yi
maganar yana kallon Mairo, da yake akwai zuciya da saurin fushi sai nan take
idanunsa suka yi ja ransa ya ɓaci.

Mairo da hawaye sun gama wanke mata fuska ne ta fara girgiza mashi kai tana faɗin
wlh ba ita bace kuma bata san wacece bace. Ibrahim zai sake yin magana Arɗo ya
umarcesa da ya yi sauri ya kawo ɗayar kashin shanun nan da wuri kada su rasa
bappan.

A fusace ya fice daga gidan, a ransa ya kudurta babu abin da zai hana shi cin uban
koma wanene ya saka wa bappa wannan abin........... Lallai Nenne zata sha duka a
hannun yayanta kenan.

Da kyar suka kama bappa suka kaisa ɗaki, a saman batarman amarya Mairo suka
kwantar da shi.
Sanya waɗan nan maza biyun Arɗo ya yi da su danne mashi bappan da karfi,
haka suka danne hannunsa da ƙafafunsa, Allah sarki yana jin kaikayi sosai hakan
yasa da suka danne shi babu halin sosawa sai ya fara zaro idanunsa da suke jajir
kamar wuta yana wani irin miƙa yana san kwace kansa, azaba yake ji Allah sarki, wlh
dik wanda ya gansa a wannan hali sai ya tausaya mashi, abin akwai azaba ne sosai.

Wlh ko leƙowa Nenne taki yi, tamkar bata a cikin gidan. Suna ɗauke bappa izuwa
cikin ɗaki ta samu hanya ta fita gidan a miliyan sai gidan Arɗo. Ta je gwaggonta ta
ɓoyeta a cikin ɗakin, wato waɗan nan biyun anyi mugaye, kamar waɗan da suka fita
daga tsatson Black Tiger............🤔

Da kyar su Arɗo suka iya ceto bappa ta hanyar yi mashi wanka da ɗanyar kashin
shanu, suna tsaka da yin wannan aikin ne tamkar saukar aradu suka fara jin kukan
jirage a sararin samaniya.

Ai a miliyan Mahnoor ta fito waje daga cikin ɗakinta, dan tasan waɗan nan jirage su
suka rabata da mijinta, ta manta ma bata goge hawayen fuskarta ba, dama Mahreen ma
ta tashi daga barci tin lokacin da bappa yake ihu, Mahnoor ɗin ce ta hanata fita,
so yanzu sai suka fita waje da gudu a tare.

Tamkar dai a baya yadda suka zo suka ɗauki Jaish, haka yanzu ma jirage ta sama
motoci ta ƙasa, kuma a kusa da kofar gidan bappa suka faka motocin.

Waje Mahnoor da Mahreen suka fita, yau Mahnoor babu tsoro, dan zuciyarta mijinta
kawai yake san gani, burinta ta sanya idanunta a kansa, shiyasa bata tsorata da
jirage da motocin ba.

Gabaɗaya mutanen kauyen a wannan karon ma fitowa waje suka yi dan ganin su wanene
suka zo. A lokacin su Arɗo sun kammala shafe bappa da kashin, hakan yasa bappa ya
nitsu tsit kamar wanda ya yi barci, tabarman Mairo kam ya lalace da kashin shanu.

Fitowa Arɗo suka yi, dan suma su je suga su wenene?. Kowa a kauyen sai rarraba
idanu suke yi, yau shine ganin motonci na biyu a kauyen.

Manya manyan bodyguards ne suka fara fitowa daga cikin motocin, da yake dikkansu
larabawa ne, sai su Mahreen suka yi masu kallon mutane guda, wai suna kama sosai.

Gabaɗaya yan kauyen sai da suka ja da baya lokacin da bodyguards ɗin nan suka
bayyana, wasu jiga jigai da su.

Bubbuɗe kofofin motocin suka yi gabaɗaya. A hankali uncle Jahiz ya fara fitowa daga
cikin motar. Ya zo ya tsaya a kusa da ɗaya daga cikin motocin, yau yana shirye
cikin Arabs dressing, har da alkyabbarsa ya ɗaura saman shigar tasa, ya fito a
balarabensa sak.

Like wow unexpected momma ta fito daga cikin ɗaya daga cikin motocin wanda uncle
Jahiz yake tsaye a kusa da shi, tana fitowa guyson ya biyo bayanta, da kallo ɗaya
zaka yi mashi in dai kasan shi ka gane bashi da cikakken lafiya sosai.

Mahnoor tana ɗaura idnaunta a kan momma da guyson nan take ta gane dik yadda aka
yi ƴan uwan Jaish ne, dan jini ba wasa ba, ita kuwa Mahreen da hankali bai gama
isarta ba kallon Jaish ta yi wa guyson, kun san na gaya maku guyson yana da tsawo
sosai, amma bai kai Jaish ba, kuma Jaish ya fisa cika gaskiya, amma ita kallon
Hamma Jaish ta yi mashi.

Kowa ya zaro idanu waje yana kallon waɗan nan kyawawan taurarin, barema guyson da
kusan rabin ƴan kauyen suke yi mashi kallon Jaish, har sun fara manta yadda Jaish
yake. Dik hankalin kowa a tashe, wasu sai kuskus suke yi suna gulmar bappa, wai
bappa ne dik ya fara ɗauko masu wannan annoba dangin aljanun ya kawo masu kauye, da
bai ɗauko Jaish ba ai da hankalinsu a kwance, yanzu ga shi sai zirya motoci suke yi
a kauyensu suna ɗaga masu hankali.

Wasu kuwa addu'a suke yi Allah yasa bappa aka zo kashewa tin da shi bashi da aiki
sai yayuɓo mutane ya kawosu gidansa ya ajiye. Sai mugun fata suke yi mashi.

Jama'a ku tafawa mata......... Meya kawo Momma Jimeta? Mu koma baya mu leƙa KINGDOM
OF POWER mu ji ta ya aka yi suka zo kafin mu dawo muji dame suke tafe.

Jama'a nace ku kara tafawa mata........

Bayan dawowar Jaish da kwana biyu, sai da suka barshi ya huta, sannan ne momma ta
buƙaci da tana san sanin in da ya afka tsawon wannan watanni da ba'a gansa ba, King
ne ya ce mata e gaskiya hakan kam yakamata, yakamata su san in da ya je.

A lokacin su commander Zafar sun shirya tsab zasu tafi yaki, ba yadda Aunty MieMie
bata yi ba a kan King ya dakatar da wannan yakin su yi tsastsauran bincike tukun
nan, amma ina ransa a ɓace, zuciyarsa taki sauƙa, hankalinsa baya jikinsa, ya ce
babu ja da baya, umarni yake badawa ba shawara ba, kada ya sake jin bakinta a cikin
wannan magana, hakan yasa ta ja gefe ta yi shiru, amma wa King kawai, ta nuna mashi
ta bar zancen, amma bata bari ba, ta dai umarci su commander Zafar a kan ta basu
nan da kwana biyu dik in da Zunaira take su nemota, idan ba haka ba kada su dawo
kingdom ɗin nan, shi ne abin da ya faru.

A tinanin king umarninsa suka tafi aiwatarwa, amma neman Zunaira suka tafi, saboda
dama dan Zunaira za'a je yakin ai, idan aka dawo da ita ba shikenana ba zance ya
mutu, idan kun lura ita Aunty MieMie bata san yaki sam sai in ya zama dole, dik da
taurin zuciyarta akwai imani da tausayi a cikinsa, tasan yaki yana haifar da
matsaloli sosai, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa rayukansu.

Guyson ya farfaɗo daga doguwar sumar da ya shiga, sai dai baya magana, dik
yadda suka so ɓoyewa Momma rashin lafiyarsa sai da ta gane, dan ta rasa sukuninta,
ta shiga damuwa, hakan yasa King ya sanar da ita cikin nitsuwa ta hanyar da yasan
ba zata ji raɗaɗi sosai ba.

Aikuwa faɗa mata ɗin ya yi amfani, ta buƙaci a dawo mata da shi gida ta yi
jinyarsa, a turo nurse su zo su rinƙa kula da shi a gabanta tun da ita babu halin
ta je hospital. Hakan aka yi, dan dik abin da zai faranta mata shi King yake yi a
yanzu, baya san ganinta a cikin damuwa, dan ma dawowar Jaish ya rage mata abin da
take ji a ranta sosai.

Jinyar guyson da ta fara yi ne tana faɗa mashi kalmomi masu karfi dan nuna
tawakkali da godiya ga Allah, sai Allah ya taimaketa ta fara shawo kansa, kunga
kuwa faɗa mata rashin lafiyarsa ya yi amfani, tin da ga shi ta dalilinta ya ɗan
samu lafiya har yana iya yin magana.

A daren rana na huɗu da dawowa Jaish Tunisia, dama ya yi kwana ɗaya a Nigeria, so a
rana ta huɗu da dawowarsa momma ta buƙaci da su zauna su yi magana a kan daga ina
su uncle Jahiz suka

Please Login or Register in order to submit comment