Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 24 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gashin kanta, Floris tana
daga zaune a bakin bed tana yi mata bayanin yadda zata gyara da kanta, ita ta ce a
koya mata ta yi da kanta ba sai ta rinƙa jira ana yi mata ba.

Sai santin kyanta da kyan gashinta Floris take yi, ba shakka kayan barcin sun zauna
a jikinta, bakara mun kyau ta yi masu ba, yanayin idanun Sweetie idan ta kalleka
sai ka ji tsikar jikinka ya mimmike, shiyasa fa Kamran baya yarda ya kalli cikin
idanunsu ita da Pretty.

Ta cikin mirror gabanta fararen idanun nata suka walwalo mata jarumin nasu tsaye a
bakin kofa, sam basu ji shigowarsa ba, a yanayin tsarin kofarsa irin na yayansa ne,
zaka iya saitawa kofar sillent, idan ka shigar mata da sillent ko ka buɗe ba za'a
san ka buɗe ba, saboda ba zata yi kara komai ƙanƙantarta ba.

Sai da Ronnie ya ji wani irin faɗuwar baba, a take tsikar jikinsa ta mimmiƙe
lokacin da ya ga walwalin fararen idanunta ta wurga mashi kallo da su, ga shi ta
cikin mirror ne, abin sai da ya ɗan razana zuciyarsa.

"Ronnie yaushe ka shigo?". Ta jefa mashi tambayar ta zage tana ta ƙoƙari dole sai
ta kama gashinta mai bala'in tsantsin da yaki kamuwar nan ta ɗaure, gashin yaki
kamuwa ta samu ta ɗaure shi, har wani nishi take yi wajen ƙoƙarin kama shi, sai
dariya Floris take yi mata tana tsokanarta da raguwa bata iya komai ba.

Jin ta ambaci Ronnie yasa Floris ta yi saurin kai kallonta a wajen kofar, yana
tsaye cikin kayan barcinsa sak irin na jikinsu ita da Floris, sai dai na shi ash
colar ne, na Sweetie milk color, na Floris black color, ya harɗe hannnu a kirji
yana kallansu.

"Beb yaushe ka shigo bamu sani ba?". Floris ta jefa mashi tambaya. Yana ta kallan
kayan jikin Sweetie bai amsa masu ba, sosai Floris ta ji wani abin ya soki ranta,
kamar ta ji zafin kallon Sweetie da yake yi har ya kasa iya amsa mata maganarta.

Abin ya sosa mata zuciya, sai ta miƙe da nufin ta fita ta basu waje,
tin da ta kalli yanzu shi idan yana tare da Sweetie baya kallan kowa bare har ya
gansa da daraja!!.

"Floris ina zaki je?". SweetiE ta faɗa itama kallanta a kan Ronnie, ita tana kallan
face ɗinsa shi kuma yana kallan zubin kyakkyawar halittarta mai tafiya da imanin
namiji mai lafiya.

Rai a ɓace a ɗan kule ta ce. "In da ya dace da ni zan je Sweetie".

Gashin kanta ya ki ɗauruwa ne ta sakesa ya watse a gadan bayanta dan ta gaji, sai
faman haki take yi ta ce. "To ki dawo da wuri"................... Sweetie duniya,
sarai tasan ran Floris ya ɓaci ne, amma da yake ta san ta kan tsiya dik yadda suka
zo mata a haka take binsu, wasa wasa ita ma ta iya tsiya sosai, sai ta nuna bata
san ma Floris ta yi fushi ba, ta nuna abin bai dameta ba har da cewa ta dawo da
wuri.

Kin amsa mata Floris ta yi, ranta ne ma ya kara ɓaci, wato ko hakuri ba zasu
bata ba, sai ma suka nuna kamar basu san tana ɓacin rai ba, lallai dole ta san
matakin da zata ɗauka a kansu, ba zata zuba masu idanu su rinƙa kunsa mata
bakinciki ba.

Da ta zo wucewa a kofar ɗakin, matsa mata hanya Ronnie ya yi, kallansa a kan
Sweetie ya ce. "Dama Angela tana nemanki".

Ya ilahi, wani irin bakin bargon bakinciki ne ya kara lulluɓe zuciyar Floris, wato
har da Ronnie ma faɗi yake ta je bai wani damu da ranta a ɓace ba ko? Lallai ma sun
walaƙantata, dole ta nemi hanyar ɗaukar mataki.

Bata bashi amsa ba shima tasa kai ta fice da sauri, tana fita ta rushe da kuka mai
taɓa zuciya, da gudu ta biyo ta saman escletor, bata ma jira ya yi kasa da ita ba
ta taka stairs ɗin da gudu ta sauko ƙasa.

A babban parlour ta wuce master Devil dake zaune saman sofa tana jiran Jack akwai
aikin da Black Tiger ya basu, so yana zaune yana jiransa ta zo da gudu tana kuka ta
wuce, da kallo ya bita yana mamakin meyasakata kuka kuma? Ya dai san ita ce sanyin
idaniyar Ronnie, in ka taɓata to ka taɓo karar kwanarka, amma yau take kuka da
hawayenta kuma Ronnie yana cikin gidan nan? Anya lafiya kuwa? Ya jefawa kansa
tambaya.

Ɗayar bakar zuciyarsa ce ta amsa mashi da kila Ronnie ɗin ne ya bakanta mata rai,
kila da shi suka samu saɓani, in kuwa haka ne kana da damar shiga jikinta ko dan
fansar da kake san ɗauka a kan Ronnie. Jinjina kai ya yi tamkar yana magana da
mutum mai rai, sai ya ji ya yi na'am da wannan shawara da zuciyar tasa ta bashi, a
hankali cikin zuciyarsa ya furta................ "Now is my time Ronnie, wait for
me am coming".

Shi kuwa Ronnie tana fita ya tako izuwa in da Sweetie take, hannu yasa a nitse ya
fara tayata tattara gashin nata ta ɗaure, yana jin wani love period a tattare da
shi mai matuƙar nishaɗantarwa.

"Ronnie meyasa ka kori Floris?". Sweetie ta jefa mashi tambaya.

"Very very sharp brain, kai Sweetie ke karshe ce, yanzu waye ya faɗa maki na koreta
ne da gangan?". Ya kai karshen maganar tare da tsai da idanunsa a kan ɗan bakinta
ta cikin mirror dake gabansu.

Kunga yadda suke tsaye a gaban mirror nan suke kallan kansu, haka Black Tiger
yake tsaye a gaban nasa mirrorn yake kallan dik abin da yake faruwa a gabaɗaya
faɗin birnin Black world.

"Ai daga ganin yadda ka yi mata na fahimci da gangan ka yi hakan dan ta fita,
akwai wani abin special da zaka faɗa mun baka san ta ji ne?". Cewar Sweetie.

Jinjina mata kai ya yi, tamkar wanda yake a cikin maye, rage tsawonsa kaɗan ya yi,
a dai'dai kunnenta ya saita ɗan bakinsa.................. "So special sosai ma zan
faɗa maki, haƙiƙa ke yar baiwar ce Sweetie, Allah ya yi maki baiwar kaifin
ƙwaƙwalwa ga iya magana mai daɗi, ga fahimtar halin da mutum yake a cikin cikin
ƙanƙanin lokaci, kin cancanci a yaba maki, ba zan taɓa bari wannan kaifin ƙwaƙwalwa
taki ta salwanta a banza ba, tabbas idan kika yi karatu jama'a da dama zasu ci riba
a tare da ke, al'umma guda zasu karu da iliminki".

Tin da ya fara magana idanunta a kanta tana jin tamkar gizo ko mafarki take yi,
hakan yasa ta ɗan zaro mashi ido ta cikin mirror, ba zai iya ganin cikin kwanciyar
idanunta ba sai ya lumshe nasa yana cigaba da jawabi.

Sai da ya kai aya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin matsuwa da jin me yake
nufi ta ce.
"Ronnie to me kake nufi da kalamanka?".

"Zan faɗa maki wani lokaci, yanzu dai ba shi ne a gaba ba".

"Menene a gaba to?". A matse da san jin komai dallah dallah ta jefa mashi tambayar.

Kara yin kasa da kansa ya yi, ya manna ɗan bakinsa da kunnenta, ya yi ƙasa da murya
matuƙa yadda sai shi da yake furta maganar da kuma ita da ake yi a kunnenta ne
kawai zasu iya jin me suke ciki, with his full confidence ya fara magana kamar
haka.

"Ina yi maki albishir da ina san shiga addininki dan kuwa shi ne na gaskiya na
yarda d.........."

Katse shi ta yi ta hanyar juyowa da karfi garesa, she was so surprised over, she
didn't expect that wonderful word from him, she can't forget this days in her life
koma da wasa ya yi mata!.

Zata yi ihun ban mamaki ya yi sauri rufe mata baki, ƙasa sosai ya kara yi da
murya. "Kada ki kuskura ki yi hakan, ina san ki sani dik abin da muke yi yaya yana
kallanmu, kuma yana jinmu, raɗa a kunne ne kawai ba zai ji me na faɗa ba, dan haka
ki kiyaye, ki yi shiru ki saurareni".

Wani irin tsuma ta ji jikinta yana yi, tamkar ana mincininta, burinta kawai ta daka
tsalle ta yi murnar ta yi nasara, amma ya zata yi? Dole ta yi shiru ta danne kada
murna ya koma ciki idan Black Tiger ya jiyosu, har wani ciza laɓɓanta ta yi saboda
irin tsananin farincikin da yake ratsa mata zuciya, tamkar mai jin sanyi haka take
jin jikinta yana yi mata.

Sarai ya lura da tsananin farincikin da ta shiga, hakan ba karamun kara mashi
kwarin gwiwa ya yi ba, ya yi farinciki matuƙa shi ma, kuma tin da ya yardanwa kansa
zai shiga addinin Musulunci ya fara jin kansa a wani irin ni'ima, nishaɗi da
farinciki na ban mamaki, yana jinsa tamkar ba shi ba, wani irin sakayau yake jin
jikinsa yadda kuka san wanda ya kwashi shekaru yana ɗauke da wani kungurmin dutse
mai nauyin gaske sai yau aka sauke mashi shi, ya ji komai tana yi mashi daɗi, shi
kaɗai idan ya zauna sai ya tsinci kansa da sakin murmushi, wannan ne ya kara bashi
kwarin gwiwa ya yarda da babu abin bauta da gaskiya sai Allah, lallai suratul iklas
gaskiya ce, lallai ne Allah shi ne kaɗai abin bauta na gaskiya. My best part
again!! Lallai ne Allah shi ne abin bauta na gaskiya, ka bisa ka more, akasin haka
ka ɗanɗani madarar azaba!!.

Cigaba ya yi da cewa. "Zan karɓi addininki saboda na yarda shi ne na gaskiya, na
yarda Allah shi ne abin bauta ba Yesu ba! Sannan na yarda da dik abin da kika faɗa
mun hakan ne, sai dai ina neman wata alfarma guda ɗaya a gareki".

A hanzarce ta yi yunkurin yi mashi magana, hannunsa na saman bakinta tin da ya rufe
mata ɗazun, tana san amsa mashi da wace alfarma ce wannan, sai ya yi saurin kara
rufe mata baki da kyau.

"Kada ki damu, ba sai kin amsa mun ba, nasan so kike ki ji wace alfarma ce, ko
baki amsa ba zan sanar dake, ni dai ki yi shiru ki saurareni kada ki yi wata
magana".

Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sai kara tsuma jikinta yake yi, tana jin tamkar
ta rumgume shi da karfi saboda daɗi, tabbas idan Ronnie ya musulunta zasu iya cin
karfin wannan yakin, shi kaɗai kusan kaso 40 ne cikin ɗari na wannan fafutukar.

"Wannan alfarma ba komai bace face ki taimaka mun mu canza yayana, mu yi ƙoƙari ya
shiga addinin Musulunci, tabbas yayana yana da zuciya mai kyau, kema idan kika ji
tarihin tasowarsa zaki yarda da hakan, yana da san taimakawa mutane, sai dai yana
da wata ɗabi'a ɗaya wadda ita ta haifar mashi da bakar zuciya a cikin kirjinsa!!".

Dakatawa ya yi da yin maganar yana kallan yadda ta zaro ido tamkar wadda ta yi
mutuwar tsaye, babbar magana, wai ta taimaka mashi su musulunta da Black Tiger?
Wannan bakin mugu mai bakar zuciyar da babu imani bare tausayi a cikinta ɗin ne
zasu musuluntar? Ita ko da take san kowa ba cikin birnin ya musulunta bata taɓa
sanya shi a lissafia ba, dan tasan sai dai ta mutu kamar kare ba dai wannan ya
musulunta ba, sai dai jikinta ya ɗanɗani azaba da ukubarsa har ya kai ga hallakata,
lallai ne yau Ronnie ya zo mata da sabon zance mai haɗarin gaske wanda babban
barazana ce ga rayuwarta. TASHIN HANKALI!!!!.

Sai dai kuma ta matsu da ta ji wace iriyar dabi'a ce wannan wadda ta canza
zuciyarsa izuwa Black HEART?.

Dik da ganin tashin hankali ta damuwa haɗe da ruɗani a saman face ɗinta na jin
bukatarsa hakan bai hana shi cigaba da cewa.

"Zallar san mulkar duniya ce a ran yayana shiyasa yake da bakar zuciya, zai
iya yin komai a kan burinsa, kuma wasiya ce daga gabanmu kafin ya mutu, ya umarcesa
da lallai ya mulki duniya, ya cika mashi burinsa ya riga Duniyar shaiɗanu yin
hakan, mulki ita ce nan tasa yaya ya zama bakin mugu, zaki iya taimaka mun mu jawo
shi cikin addinin musulunci, na tabbata in ya musulunta zai ji irin daɗi da sanyin
zuciya da nike ji, tabbas dik wani black heart dake cikin kirjinsa zata washe izuwa
fara tas, tabbas musulunci alkhairi ce, nima daga yarda zan shiga dik zafin
zuciyata na ji ta sanyaya".

Allah mai iko da hikima, tabbas hakane, Allah ya nunawa Ronnie aya ta hanyar
sanyaya mashi zuciya daga yarda zai shiga musulunci, Allah yana sansa da rahma
shiyasa ya kara sanya mashi ni'ima da kaunar addinin a ransa, tabbas musulunci
duniya ce kuma gaskiya ce, hanya fara da babu ɗigon baki a kanta, hanyar riskar
tsira da nasara.


Girgiza mashi kai ta fara yi a kan ita ba zata iya taimaka mashi wajen jawo Black
Tiger addinin Musulunci ba, dan ita gaskiya bata shirya mutuwa ba tare da sake
haɗuwa da Pretty and mom ɗinsu ba, tana san ƴar uwarta.

Kara yin ƙasa da murya sosai ya yi, sannan ya cigaba da cewa............ "Na san
damuwarki da abin da kike jin wa tsoro, rasa ranki kike tsoro ko?". Ya jefa mata
tambaya.

Kai ta gyaɗa mashi alamar hakan ne, ranta take tsoron rasawa, yar kaniya ta ji
wahala shakar da ya yi mata a cikin ruwa, daga nan ta fara tsoronsa da shakkarsa.

"To ina san ki daina tsoro, ki sani da wata ce ko wani ko minti ɗaya ba zai
karaba a duniya idan ya kalli fuskar yayana, amma ke kin kallesa ido cikin ido,
kuma baki tsorata ba, daga nan yakamata ki sani cewa yaya ba zai iya kashe ki ba,
sai dai ya azabtar dake, na san zaki sha wahala matuƙa, amma banda batun mutuwa".

Wani irin kallo ta wurga mashi wanda za'a iya fassara shi da me kake nufi da kace
zan sha wahala amma ban da batun mutuwa?.

Ya fahimci abin da take san karin bayani a kai, dan haka sai ya ce......... "Tabbas
sai dai yaya ya gana maki azaba, amma ba zai iya kashe ki ba, ke ɗin ƙaddararsa ce,
dalilina a nan kuma shi ne Spender yana tare da ke, saboda Spender ne yaya ba zai
kashe ki ba, da wannan dama zamu yi amfani wajen taimakawa mu juya black heart
izuwa white, amma sai kin jure, zaki azabtu matuƙar, idan kuma kika jure har muka
yi nasa tabbas sai mun fi kowa jin daɗi".
Ɗan dakatawa ya yi yana kallan face ɗinta, yaga alamar ta ɗan sauko jin
maganganunsa na karshen nan, kwarin gwiwa ya samu wajen cigaba da ce mata.

"Tabbas yana haukar neman Spender, a da na yi niyar yi maki dabara in shiga
jikinki dan ki bamu Spender, amma a yau ni nike tsaye a kan kafafuna ina mai
umartarki da dik azabar da zai gana maki kada ki kuskura ki bashi Spender har sai
mun yi nasara, zan yi ta razanaki dan ki bashi, kada ki yarda ki bashi".

A daidai lokacin da ya ce a da can baya ya yi niyar shiga jikinta ya mannu da ita
dan ya kwatawa yayansa Spender daga hannunta ba karamun zaro idanu ta yi ba, dan
bata taɓa expecting haka daga garesa ba, ya bata mamaki matuƙa.

Sarai ya lura da maganar ya girgizata, amma sai ya basar, ya cigaba da karfafa mata
gwiwa a kan zata iya, dik da cewa ba lallai ne su yi nasara ba, amma zasu jarraba,
kuma yana da yakinin ko basu yi nasara ba zasu samu cigaba sosai, zasu iya canza
wasu abubuwa, kuma shi burinsa kenan.

Sosai ta ji kwarin gwiwa jin cewa ba zai kasheta ba, dama ita batun kisan ne a
ranta, tin da kuwa babu kisa tabbas zata jure dik wata wahala, tabbas zata iya,
dama ita burinta su yarda da ita su musulunta.

Katse mata tunaninta ya yi da cewa. "Yaya zai yi wuyar musulunta, amma ki sani idan
muka yi sa'a ya musulunta to fa tabbas Birnin nan dikka zasu musulunta".

Wani irin sanyi ta ji a ranta, nan take ta fara hasko kanta a cikin al'ummar birnin
nan tana koya masu karatun addini, nan take ta fara hasaso kalar ladar da zata samu
idan suka musulunta, tuni ta mance da wahalar da za'a sha kafin ayi nasara, tin da
dikka birnin zasu musulunta idan ya musulunta ai ita ko zai kasheta kafin ya
musulunta in dai zai musulunta ɗin wlh a yanzu kam ta yarda, ko zata mutu ba gudu
ba ja da baya. Tuni ta saki ranta, cike da kwarin gwiwa ta girgizawa Ronnie kai
alamar ta yarda ta amince zata yi dik abin da ya ce.

Sosai ya ji sanyi a ransa, sannan ya yi mata raɗar yadda zasu fara tsara plan ɗin
nasu, daga karshe ya buƙaci da ta shigar da shi addininta wato ta bashi kalmar
shahada. Yana kai karshen maganar ya zame hannunsa daga ɗan bakinta domin ta bashi
shahada.

Haka kuwa aka yi, a hanzarce ta juyo ta fara yi mashi raɗa ta kalmar shahada a
kunne yana maimaitawa a hankali yadda kowa ba zai ji ba, har lokacin yana rankwafe
a kanta, ko gaji bai yi ba bawan Allah.

Sai da ta kai har karshe, sannan ta matsa baya da shi like three step, sai ta fara
binsa da kallo mai cike da kauna da farinciki, tana yi mashi kallon cikakken
musulmi a yau.

Ya yi shiru yana kallanta yana jiran ya ji me next, sai kawai yaga ta daka tsalle
ta faɗo jikinsa tana dariya kamar wadda ta zare.

Rungumeta kam ya yi a jikinsa yana jin wani irin farinciki na musamman, ya ɗagata
sama ya manneta da kirjinsa suna ta sakin murmushi wa junansu.

A kunne ta raɗa mashi. "Is time, get ready to fight my Ronnie, da izinin Allah zamu
yi nasara, zamu cetosu daga halaka zuwa tsira".

Juyowa ya ɗan yi shi ma ya fara yi mata nasa raɗan. "Kada ki bari yaya yasan da
cewa na musulunta fa, zai kasheni dik san da yake yi mun, ko Floris kada ki bari ya
sani".
Jinjina mashi kai ta yi kafin ta ce. "To taya za'ayi ka yi sallah?".

"Kada ki damu da wannan, a ɗakin yaya zamuna yi, dan yana kallan komai dake cikin
birnin nan amma banda ɗakinsa, dan haka tin da ya fara shiga fada a nan zamu rinƙa
yi".

Wani irin daɗi ta ji ya kara lulluɓeta, da karfi ta kara kankamesa kamar zata mayar
da shi jikinta, shi ma wani irin daɗi yake ji na musamman.

Black Tiger dake ganin me suke aikatawa ya zaci soyayya Ronnien nasa ya fara yi,
hakan yasa ma ya kawar da kallonsa a kansu, ya shiga kallan sauran wurare a cikin
birnin.

Sake Ronnie ta yi, shi ma sauketa ya yi, cikin farinciki ta ce. "Muje ka rakani
ɗakin yayanka yanzu!".

A ɗan rikice ya ce. "Me zaki je yi a can?".

"Kai dai muje zaka gani"........... Bai musa mata ba, ta wuce gaba ya rufa mata
baya.

Me kuke tinanin zai kaita room na Black karfe a daren nan?.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬
"Kai dai muje zaka gani"........... Bai musa mata ba, ta wuce gaba ya rufa mata
baya.

Me kuke tinanin zai kaita room na Black Tiger a daren nan?.

Sun zo zasu fita daga room ɗin kofar taki buɗewa, yanzu ta san password na kofar,
dan haka ta yi ta yi yaki buɗewa, da ta gwada sau uku ma sai kofar ya fara karar
jiniyar motar ƴan'sanda, alamar ansaka mashi wrong password kenan.

Da sauri ta juyo da kallonta a kansa, yana tsaye ya harɗe hannaye a saman kirjinsa,
sai kallanta kawai yake yi.

"Ronnie meyasa kofar taki buɗewa? Kuma ka ji tana wata iriyar kasa!".

Ƙasa ƙasa ya furta. "Saboda yaya bai yarda mu fito yanzu ba, shi ya hana kofar
buɗewa, mu koma kawai".

Ranta bai so haka ba, ta juya da nufin su koma kenan sai suka ji alamar ana taɓa
kofar, da sauri ta juyo da kallonta a kan kofar. Kamar mai raɗa a ɗan tsorace ta
ce. "WANENEN?". Ta tsorata jin ana taɓa kofar ne.

Gaba ya wuce ya koma cikin ɗakin, a bakin bed ya zauna, ta tsaya tana kallonsa tana
jiran amsa. Murya a kasalance ya ce. "Robbot ɗin da suke aiki a cikin empeir ɗin
nan ne, baki ji kofar ya yi karar an saka mashi wrong password bane? Shi ne suka zo
dubawa, rabu da su ki zo ki bani tarihin yesu da Imam Madih, zasu tafi idan suka
gama bincike suka tabbatar da babu wata matsala".

Tin da ya fara magana ta shiga mamaki jin kamalansa, lallai akwai tsaro mai karfi a
empeir ɗin nan, tabɗijam.

Sai da ta ji ya ce ta zo ta bashi tarihin Imam Madih ne ta ɗan saki ranta, cike da
fara'a ta ce. "Ba ranar na baka ba?".

Kai ya girgiza kafin ya ce. "Ranar tarihin yesu kika bani, kika ce zaki faɗa mun
wanene Imam Madih, amma baki faɗa mun ba, kuma ni ina san Yesu sosai, bana gajiya
da jin tarihinsa na gaskiya".

Shiru ta ɗan yi, ya zuba mata ido cike da kauna yana jiran ya ji me zata ce, kamar
wadda aka sakawa battery ta ninka murmushin dake saman face ɗinta, cikin jin daɗin
san samun iliminsa da yake yi ta fara faɗin.

"Ba iya Yesu yakamata ka mutu a kansa ba, ka mutu a kan fiyayyen halitta
manzon rahma manzon tsira zaka ji matuƙar daɗi fiye da tinaninka a yanzu".

"Wanenen shi manzon tsira ɗin?". Ya jefa mata tambaya........... Cikin nitsuwa ta
tako ta zo kusa da shi, a saman bedside drawer ɗinsa ta zauna, gyara zamansa ya yi
ya zamana suna fuskantar juna, dik a matse yake da san jin yadda zata bayyana mashi
manzon tsira, jikinsa har tsuma yake yi, shi yanzu yana bala'in san jin tarihin
annabawa da Sahabbai da yadda suka rinƙa sadaukar da rayukansu dan mu a yanzu mu ji
daɗi.

Cikin nitsuwa ta fara kora bayanai masu cike da ilimi da hujjoji masu karfi........
"Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) shi ne manzon Allah na karshe kuma
mafificin halitta. Shi ne aka aiko domin ya shiryar da mutane gabaɗaya zuwa ga
addinin gaskiya, wato Musulunci, musulunci shi ne yake bayyana mabiya Allah guda
ɗaya tak ba Allah biyu ko uku kamar yadda yahudu da nasara suke faɗi ba, musulunci
Allah ɗaya ne tak cikin Tauhidi hakan ta bayyana. An haife Manzon Allah a garin
Makka a shekara ta 570 Miladiyya, a wani gida na kabilar Quraysh, kuma ya fito daga
zuriyar Annabi Ibrahim (Alaihissalam) ta hanyar Annabi Isma'il (Alaihissalam)".

Tun daga farkon bata tarihinsa Ronnie ya ji wani irin kaunarsa tana ratsa shi, sai
ya ji kamar ta cigaba da bashi tarihinsa har illah Masha Allah.

"A cikin Alqur'ani mai girma, cikin Suratul Ahzab sura ta 30 aya ta 40 Allah ya
bayyana Manzon Allah a matsayin annabin karshe wanda babu wani annabi da zai sake
zuwa bayansa".

"Cikin Suratul Anbiya, sura ta 21 aya ta 107, Allah ya ce ba mu aiko ka ba sai
domin ka zama rahama ga talikai. Suratul Najm, sura ta 53, aya ta 3 da na 4, Allah
ya ce Manzon Allah bai faɗi Al-Qur'ani daga son zuciyarsa ba. Ba komai ba ne sai
wahayi da na yi masa, cikin Suratul Ahzab, sura ta 33 aya ta 21, Allah ya ce lallai
a gare ku akwai kyakkyawan misali a wajen Manzon Allah, ga wanda ya ke fatan Allah
ya cecesa a ranar lahira, to ya ambaci Allah da Manzonsa da yawa".

A cikin sunanun tirmidhi, hadisi mai lamba 3148, manzon Allah ya ce lallai ni ne
shugaban ƴaƴan Annabi Adam, kuma ba na yin alfahari ko fariya a kan hakan".

"Ni ne rahamar da aka bayar." Cikin Sunan Ad-Darimi. Wasu daga cikin ayyukan Annabi
Muhammad (SAW) Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi kuma ya yaƙi bautar gumaka. Ya kafa
gwamnatin Musulunci a Madina bisa gaskiya da adalci. Ya yaɗa ilimi da hikima.Ya
kyautata zamantakewa da zamantakewar aure da rayuwar jama’a gabaɗaya".

"Allah ya umarci musulmi da su koyi dabi'un Manzon Allah (SAW), domin duk abin da
ya koyar da al'umma ya kasance bisa umarnin Allah ne. Wannan yana cikin abin da ke
tabbatar da cewa ya kasance tsarkakakke kuma cikakken misali ga dukkan al’umma".

Ronnie ya gama tsumuwa da san Manzon Allah, dan ma Sweetie bata bashi kaso ɗaya
cikin dubu na kyawawan halayen manzon rahma ba.

Ganin ya tsareta da ido ne yasa ta dakata da yin maganar. "Ronnie lafiya?". Ta
jefa mashi tambayar cike da matsuwa da son jin amsa.

Girgiza mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, fuskarsa ɗauke da
ƙayatattcen murmushi mai kwantar da hankali.

"Ni dai ka faɗa mun menene in ba haka ba in fasa baka tarihin Imam Madih".

Ƙasa ƙasa kamar mai raɗa ya ce. "Kaunar manzon

Please Login or Register in order to submit comment