Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 11 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da abin tsoro, gabaɗaya bishiyoyin cikin forest ɗin suma jikinsu ya yi
bakin kirin, ga wasu irin kawunan mutane, ga kasusuwan kwarangwal, abin dai sai
wanda ya gani, ga wasu irin inuwa dake gilmawa ta gaban idanunta tamkar na wasu
gungun aljanu, a gabaɗaya dajin nan babu wani abu mai ɗan dama dama da zaka iya
gani, sai zallar madarar abin tsoro mai firgita kwakwalwa.

Dik tsananin karfin hali irin nata sai da ta yi balai'n rasaza, ta kasa iya furta
ko uppan, jikinta har kerma ya fara yi, sai ta fara danasanin meya kawota.

A hankali wani irin inuwar wani dogon halitta mai tsayin gaske ya fara nufo in da
take tsaye, sam bata iya ganin wanna halitta, inuwarsa ne kawai zaka gani.

Da kyar ta iya ɗaga kafarta da ya yi mata bala'in nauyi, a hankali ta fara ja da
baya, inuwar yana kara tinkarota, jininta sai rawa yake yi, ta kasa iya furta sunan
Allah da ya kawo mata ɗauki.

Ganin da gaske wannan halitta ita yake nufowa yasa ta zage da iya karfinta na
karshe ta tattare karfinta dikka ta juya da karfin gaske dan ta gudu ta fita waje,
sai dai kash tana juyowa kofar ɗakin ya rufe kansa da wasu irin mahaukatan locks
masu ban mamaki wanda bata san da su a jikin kofar ba sai a yanzu.

Nan take gabaɗaya empire ɗin Black Tiger ya ɓacewa ganinta, ya zamana iya dajin ne
kawai a wajen, kasar dajin in da take takawa kenan bakin kirin yake kamar gawayi.

Tashin sense, wani irin dukan tara tara kirjinta ya yi, da karfi ta wage baki ta
kurma ihu, sai dai sam voice ɗinta baya fita, kamar ma bata yi ihun ba.

Cike da fargabar abin da zata gani a hankali ta juyo kirjinta na dikan uku uku
jikinta na kara tsananta kerma.

Wani irin mahaukacin ihu ta saki lokacin da ta gama juyowa ga wannan halitta
dake nufota. Tin daga wanna ihu kuma bata sake iya ji ko ganin wani abin ba, ido da
ido da ta yi da halittar yasa idanunta suka makance ta dai'na ganin komai,
kunnuwanta suka kuramce ta dai'na jiyo sautin komai.

Me kuke tinanin ta gani ya makantar da ita? Me kuke tinanin zai faru da ta
kurmance?

Yanzu wasansu zai fara, shin kuna tunanin dama zasu zubawa Sweetie ido ta
musuluntar da su Ronnie ne? Su da jininsu na tsanar musulinci ce? Akwai matsala fa!
Sweetie ta taro yakin da a yanzu dai ba iya shi zata yi ba! Saboda a yanzu ita
kanta bata san wacece ita ba, bata san baiwar dake gareta ba bare ta yi amfani da
shi wajen yakarsu ita ma dan ta taimakawa kanta da mutanen da zasu yarda da ita!
Bata san ina ta dosa ba a halin yanzu, fatana dai Allah yasa kada su wujijjiga mana
rayuwarta ko ma su shafe babinta a doran duniya!!.

===========================💘

DUBAI.🔥
Al'umma dai sun ki nutsuwa su kwantar da hankalinsu, saboda suna ganin mutuwa zasu
yi, jami'an nan sun yi iya ka bakin ƙoƙarinsu kowa ya nutsu dan ma su iya gane kila
makiyan suna a tare da su, amma ina kowa neman hanyar fita yake yi, dik da an rufe
gates ɗin amma sun ki tsayuwa waje guda.

Gungun jami'ai ne suka yi wa ahalin Abu Abdussalam zobe domin su tabbatar da
sun fitar da su lafiya lou.

Sai dai fa Ramish da aka hara yaki motsawa daga in da yake bare har ya bi ayarin
Abu Abdussalam su koma gida.

Ya dai ce Bilal ya kasance a tare da Abbie ɗin nasu, shi yana nan bari ya tabbatar
da dik wanda ya zo nan dominsu ya koma gida lafiya ba tare da kwarzani ba, ba yadda
Abu Abdussalam bai yi da shi a kan yazo su tafi ba amma yaki yarda.

Hankalin Abu Abdussalam a tsananin tashe, saboda yasan Ramish ɗin aka hara kunga
bai kamata ya tsaya a wajen ba, amma yaki tafiya, burinsa ya kama wanda ya yi
wannan harbin.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

Kaiwa suke suna sake komawa, suna safa da marwa a tsakiyar katafaren parlournsu,
gabaɗaya zufa ce take ta keto masu, ta wanke fuskokinsu tamkar waɗan da aka watsawa
ruwa, gabaɗaya parlourn da suke ɗin A.c ne a kewaye ta ko'ina, amma a haka suke
haɗa wannan zuba saboda bala'in zilmi da fargaba da suke ciki, fatansu ɗaya shi ne
Leesharh ta ɗauki wanna call ɗin, saboda wannan shi ne kawai damar da suke da shi,
in har wanna dama ya kubce masu to abubuwa biyu dole su faru, na farko dole za'a
kara tsananta tsaro a gidan Abu Abdussalam wanda ba zasu sake samun irin makamancin
wanan dama ba, sannan dole su Ramish zasu shiga binciken wanenen yake yi masu
wannan aiki?.

Sun san wanene Ramish tsab zai iya kamasu, dan kwararrene a aikinsa, dole su shiga
tsananin tashin hankali.

Sai kiran wayar hannun Leesharh suke yi babu kakkautawa.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Call ɗin farkon ne ya katse na biyu ya sake shiga, Sharifat tana rike da hannunta
ɗaya, call ɗin yana gab da katsewa ta sanya babban yatsarta zata ɗauka.

Kamar daga sama aka bugeta ɗaya daga cikin jami'an da suka yi masu zobe, jama'a
ne suka ture shi by mistake ya yi baya baya, to da yake ita da Sharifat ce a kusa
da shi sai ya bugeta, ta ɗan yi baya ta bugi Sharifat wayar hannun nata ya faɗi
ƙasa.

Ina cikin cunkosan jama'ar nan ba ta yadda za'ayi ta tsugunna dan ta ɗauki
wayar, tashin hankali iya tashin hankali ta shiga, ta rasa ya zatayi, ga shi wannan
ɗauka call ɗin da zata yi shi ne aiki na karshe da zata yi wa masu nikaf a
shirmenta wai sai su bata babanta.

Sosai ta shiga tashin hankalin da har bata san lokacin da hawaye suka fara wanke
mata fuska ba.

A tunanin Sharifat saboda tashin hankalin da suka shiga a yanzu ne yasa take kuka,
dan haka sai ta shiga bata hakuri tana gaya mata babu abin da zai samesu lafiya lou
zasu koma gida.

Ina ai ita tasan me take tunawa, cigaba da kukanta kawai ta rinƙa yi tana jin
zuciyarta tana yi mata zafi.

A haka aka fita dasu ta baya, babban tashin hankalinta na biyu bata taho da wayar
ba, a tunaninta ta ina zata yi magana da masu nikaf ta ji ta gama aikin ne ko da
saura?.

Tun da suka dawo gida take kuka ta ki ta yi shiru, Sharifat ta yi lallashi har ta
gaji amma ina taki ta yi shiru.

Dan dole Sharifat ta rabu da ita ta je ta yi wanka tare da zuwa ta shirya cikin
female arabs jallabiya, ta yi kyau sosai.

Wayarta ta zo ta ɗauka domin ta kira number yayanta, dan hankalinta yaki kwanciya
ganin ba'a tare da shi suka dawo ba, ta shiga damuwa sosai, dan dai kawai ba yadda
zata yi ne.

Numbersa ta shigar ta fara kira. Wayar ta yi ringing har ta katse ba'a ɗauka ba,
Leesharh na kwance saman gado har lokacin tana murzan kukanta.

5 miss calls Sharifat ta yi wa Ramish amma bai ɗaga ba, hakan ba ƙaramin ɗaga mata
hankali ya yi ba, dik sai ta ji kanta yana jujjuya mata, addu'a ta fara yi Allah
Ubangiji yasa yana lafiya.

Miƙewa ta yi ta shiga toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shinfiɗa dadduma,
sallar mangariba ta gabatar tare da nafilfili ta shiga yi mashi domin Allah ya kare
mata shi, wlh Sharrifat tana kaunar Ramish sosai.

Addu'oi sosai ta rinƙa yi mashi a cikin sujjada. Ta ɗauki almost 4 hours a saman
dadduma tana karatu da addu'oi bayan idar da sallah isha'i da ta yi, har kwallah
sai da ta yi mashi!.

Abin ya yi matuƙar ɗaga mata hankali.

Daga karshe bayan ta kammala ne ta miƙe ta dawo wajen gadon, a lokacin Leesharh ta
dai'na kuka sai ajiyar zuciya take saukewa.

Wayarta Sharifat ta ɗauka, number Abbie ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka. Kamar zata yi
kuka ta ce.

"Abbie kana gida ne?".

Abu Abdussalam dake kishingiɗe a saman wani shinfiɗa tasa ta alfarma mai kama da
shinfiɗar sarakuna a cikin rest part ɗinsa ne ya amsa mata da yana gida kuma yana
wajen hutawarsa.

"To Abbie gani nan zuwa".

Da okey ya amsa mata. Katse kiran ta yi tare da fara matsawa Leesharh a kan ta
tashi zu je wajen Abbie.

Har da ce mata. "Tin da ni kin ki ki ji rarrashina zaki ji na Abbie ai, sarkin
tsoro kawai, ke daga jin anyi harbi da bullet zaki wani fara kuka! A haka kuma zaki
auri Yah Bilal kenan?".

Allah sarki Sharifat har ta bani tausayi, bata san cewa ba wannan ne a gaban
Leesharh ba, hmmm wanna shi ne Sharifat tana goya yar kunama.

"Ni Sharifat ki tafi kawai babu in da zan je". Da kyar voice ɗinta yake fita
saboda kuka.
"Allah babu in da zan je ba tare da ke ba, kawai ki tashi mu tafi".

Make kafaɗa ta yi haɗe da tirjewa ita lallai ba zata je ba. Matsa mata Sharrifat
ta cigaba da yi dan ba zata iya ganinta a cikin damuwa ta kyaleta ba.

Hannu ta kai ta riƙo hannunta tana ƙoƙarin janta ta mikar da ita tsaye dan dole.

Cikin ɗaga murya Leesharh da ranta ya gama ɓaci ta ce.
"Ki sakeni babu in da zanje nace maki! Wai ana dole ne?!"

Sam Leesharh bata san ta daka mata tsawa haka ba, ranta ne ya kai ƙololuwa wajen
ɓaci.

Zaro idanu Sharifat ta yi ba tare da ta saketa ɗin ba, nan take kuma sai ta ji
zuciyarta ya tsorata da Leesharh, a take ta fara tunanin anya kukan tsoro Leesharh
take yi kuwa? Anya babu wani abin a kasa kuwa? Kukan ne ya wuci na hankali yanzu
kam.

Ganin Sharifat ta zaro idanu ne yasa ta fahimci abin da ta aikata, dan haka sai ta
yi kasa da kantah haɗe da riƙo hannayen sharifat cikin nata.

"Ki yi hakuri sister, ban san na yi hakan ba".

Kamar wadda aka sanyawa battery Sharifat ta ce. "Leesharh kukan me kike
yi?".............. Ta yi maganar idanunta a kan Leesharh babu ko kyaftawa!.

Nan fa Leesharh ta fara zazzare ido tana ƴan kame kame, ta rasa me zata ce, ita
da kanta tana neman tonawa kanta asiri.

"Am....... Ba........... Ba........ Babu komai". Ta faɗa murya a sarke.

"Tun da ni ba zaki faɗa mun ba tashi mu je wajen Abbie sai ki faɗa mashi". Cewar
Sharifat.

Jinjina kai ta yi kafin ta amsa da. "Okey bari in yi wanka sai mu je".

Kamar zata ce mata su je kawai, sai kuma ta ce bari ta kyaleta ta yi wankan zai fi.

Toilet ta miƙe ta shiga dan ta yi wanka. Sharifat ta zauna a bakin bed tana jiran
fitowarta.

A bakin wash hand base ta tsaya tana kallon kanta a cikin mirror, Allah sarki har
idanunta sun kumbura saboda kuka, haƙiƙa Leesharh tana cikin tsaka mai wuya baiwar
Allah, daga gidan yari ta wuce wannan ukubar kuma, Allah dai ya bata ikon cin
jarabawarta.

Ta jima sosai tsaye tana kallon kanta kafin daga bisani ta wuce wajen haɗa ruwan
wanka, dik jikinta a mace kamar anzare mata laƙa.

Sharifat na zaune tana ta istigifari tana rokan Allah da yasa Ramish ɗinta yana nan
lafiya, har Leesharh ta fito ɗaure da towel ta sameta.

"Kisaka irin jallabiyata mu yi iri ɗaya Abbie zai ji daɗin hakan". Cewar
Sharifat, ta yi maganar dai'dai lokacin da Leesharh zata shiga dressing room ɗinsu
dan shiryawa.

Jinjina kai ta yi haɗe da amsawa da okey sannan ta sa kai ta wuce.
In short a shirye Leesharh ta fito cikin kaya irin na Sharifat, tin bata karisa in
da Sharifat take ba ta miƙe ta nufeta.

Hannunta ta rike suka nufi waje. Kai tsaye wajen Abu Abdussalam suka nufa.

Yana kishingiɗe saman shinfiɗar ga kayan marmari a gabansa, yana sanye da white
arabs jallabiya, dattijon arziki kenan.

Yana ganinsu ya miƙe zaune, a saman shinfiɗar suka zauna, Leesharh ta gefen
damarsa Sharifat ta gefen hagunsa.

Sharifat tana rike da wayarta irin na Leesharh a hannunta.

"Barka da dare Abbie". Sharifat ta faɗa.

Bai kai ga amsawa ba Leesharh ma ta faɗi hakan. Cikin muryar dattaku ya ce.
"Yauwa ƴaƴana.............. Leesharh menene ya sami idanunki?"

Kasa ta yi da kai tana ƙoƙarin fara ƴan kame kame.

"Abbie tin daga wajen taron nan da taga anyi harbi ta fara kuka, nayi ta
rarrashinta ina faɗa mata babu abin da zai sameta amma taki yin shiru har sai da
muka dawo gida".

Tin da Sharifat ta fara magana kallonsa yake a kanta har ta dire, sannan ya dawo da
kallonsa a kan Leesharh.

Yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi maganar Ramish ya shigo wajen bakinsa a ɗauke da
sallama.

A miliyan Sharifat ta kai kallonta a kansa, shi kuwa hankalinsa sam baya a kansu,
yana sanye da sleeping dress riga da wando milk color masu bala'in kyau, ya yi kyau
sosai, dik da bashi da fara'a kullum fuska a ɗaure, amma da kallo ɗaya zaka yi
mashi ka fahimci yana cikin damuwa, ya ƙara tsuke fuskarsa sosai, ya haɗe gerar
kasa da ta sama.

Saman sofas dake wajen ya zauna, sai wani kara tsare gida yake yi yana cin
magani.

Wani irin mummunar razanannen faɗuwar gaba Leesharh ta ji a lokacin da ta ɗaura
idanunta a kan wayar dake hannunsa, tabbas wayarta ce da masu nikaf suka bata, to
ya aka yi wayar ta zo hannunsa?. Ta jefawa kanta tambayar.

Dakatawa da yiwa Leesharh magana Abu Abdussalam ya yi tare da mayar da kallonsa
a kan Ramish.

"My son ka dawo?".
Cike da ƙaguwa da san jin amsar da Ramish zai bashi ya yi tambayar, cike kuma da
tsananin fargabar abin da zai ji.

Jinjina kai Ramish ya yi ba tare da ya yi magana ba.

"To meyafaru and kiran me suka yi maka?". Cewar Abu Abdussalam.
Ya jefa mashi tambaya cike da damuwa, dama tun ɗazun Ramish ya dawo daga wajen
taron suna tattaunawa da Abbie ɗin nasu, yanzu ba jimawa jami'ansa suka kirasa a
waya shi ne ya tashi ya tafi, ya ce da Abbie yana zuwa yanzun nan, dawowarsa kenan.

Wayar Leesharh dake a hannunsa ya miƙewa Abu Abdussalam.
Karɓa Abbie ya yi yana jiran a kora mashi bayani, shiru Ramish bai yi magana ba,
kamar wanda baya san motsa lips ɗinsa, ya yi kasa da kai kamar mai tinanin wani
abin.

Gajiya da ƙaguwa da Abbie ya yi da san jin bayani ne yasa ya ce. "My son meyake
faruwa ne?".

Shiru Ramish ya kara yi har na tsawon good 2 mins.

Sai kallansa Leesharh take sata kirjinta na dukan uku uku, ji take yi tamkar zata
mutu, gabanta sai mummunar faɗuwa yake yi, alamar rashin gaskiya ne karara ya
bayyana a saman face ɗinta, har wani zufa take ji yana keto mata.

Ita ma Sharifat sai satar kallonsa take amma ita kallon soyayya take yi mashi ba ta
wata manufa ba, dan ma dai tasan baya san yawan kallo ne yasa take kallonsa a sace,
da a sarari zata gansa.

Sarai Abbie ya gane cewa ƴarsa ta kamu da san Ramish da jimawa, amma ya zuba masu
idanu yana ganin gudun ruwansu, baya san kuma ya faɗawa Ramish Sharifat tana sansa,
ya fi san Ramish da kansa ta gane hakan ya kuma faɗa santa da kansa ba tare da an
haɗa su ba.

Sai dai Abbie abin ya fara damunsa yanda har yanzu babu wani canji a tattare da
Ramish, ko kallo baya ɗaga idanun ya yi wa Sharifat, abin ya tsayawa Abbie a wuya,
ba shi kuma da burin da ya wuce ya ga wannan haɗin ta yiwu, yana ji da ƴar nan tasa
matuƙa.

Sai da Ramish ya gama hatsewa da jan ajinsa, sannan ya ɗan gyara zamansa, ba
tare da ya ɗago ya kalli ko mutum ɗaya daga cikinsu ba ya fara yin magana kamar
haka, cikin sanyi murya haɗe da nutsuwa ya ce.

"Wannan waya da na baka makunnine na tashi nakiya".

Ɗan zaro ido Abbie ya yi, matsalarsa da Ramish kiwiya wajen yin magana, sam baya
san buɗe baki ya yi magana yadda ya dace, sai dai ya yi wa mutun in short a
dunkule, in ka gane kai ka sani, in ma baka gane ba nan ma kai kasani, kamar wani
mai ciwon baki.

"My son wai ba zaka bar wanan halin naka ba ko?". Cewar Abbie da ƙaguwa kamar ta
kashe shi, yana bala'in san jin karin bayani!.

Sai a lokacin ya ɗago da kallonsa a kan Abbie. Yasan a kan me Abbie yake magana, a
kan rashin maganarsa ne, dan haka sai bai wani kula shi ba, alamar ba dainawa ɗin
zai yi ba kenan!.

"Bomb ne a kewaye da hall ɗin nan, wanna wayar ita ce matashin bomb ɗin, shi ne
dalilin fitana yanzu". Cewar Ramish.

Kallon Abu Abdussalam a kansa ya kara zaro idanu sosai, a hanzarce ya ce.
"Bayan harin da aka kawo maka bai yi masu ba shi ne suka kewaye mu da bomb?
To su wanene? Wai me ka tsarewa mutane ne?".
Cike da tashin hankali Abbie ya yi maganar.

Tamkar babu Ramish a wajen, bai sake cewa ko uppan ba.

"Yanzu kun cire bombs ɗin ne?".
Abbie ya sake jefa mashi tambaya. Wato idan baka da hakuri sosai ba zaka iya
zama inuwa guda da Ramish ba, dan zai kasheka da takaici ne, sai ayi mashi magana
goma bai amsa ɗaya ba, to in ba mai hakuri ba waye zai iya jure wannan walaƙanci
fisabilillahi?.

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Abbie Yah Ramish wannan ai wayar Leesharh
ne!".
Sharifat ta katsesu da faɗar hakan, ta yi maganar cike da tashin hankali
maras misiltuwa, sannan ta yi maganar tana miƙewa tsaye haɗe da dafe saitin
zuciyarta.

Ramish and Abu Abdussalam har suna rige rigen kai kallonsu a kanta.

A miliyan ita ma Leesharh ta miƙe tsaye.............. Wani irin zufa yana kara
tsananta a saman face ɗinta, hankalinta idan ya kai dubu to ya tashi, jikinta sai
wani irin kermar wahala yake yi. Da kyar ta haɗiyi wani irin azabbabben wahalallen
yawu mai wuyar wuce maƙogwaranta.

Miƙewa tsaye shima Abu Abdussalam ya yi kallonsa a kan Sharifat da kwayar
idanunta tamkar zasu faɗi ƙasa saboda zarosu da ta yi!.
Baiwar Allah jikinta har kerma yake yi, bata taɓa tsammanin makamancin hakan
ba ko a mafarki.

Ramish kam yana zaune bai miƙe ba, idan ka kallesa in the first place zaka yi zaton
Sharifat yake kallah, amma kuma Leesharh yake kallo saboda ya gano abin da yake san
ganewa, dama shi tin ainahi bata kwanta mashi a ransa bane yasa ya ce kada ta sake
zuwa part ɗinsu, sai ga shi an kamata red handed.

My people's me kuke tinanin zai faru a wannan waje? Akwai tashin hankali
kuwa!!. Rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya

===========================🔥

••••••••••••••••JIMETA🔥••••••••••••••••

Tsawon kwanaki biyu babu Jaish babu labarinsa, tin bappa yana sa tsammanin zai
waiwayesu har ya dai'na, yanzu har ya fara rage damuwansa a kan haka, bawan Allah
sai dai har ƴar rama ya yi saboda damuwa.

A ɓangaren Nenne kuwa farinciki kamar ba zata mutu ba, burinta ya gama cika rayuwar
Mahnoor ya lalace, ta zama karamar bazawara, bata wuce 15 years ba amma ta zama
bazawara, abin ya yi wa Nenne da gwaggo mugu mugun daɗi.

Shi kam hamma Faisal ya kafe a kan lallai tin da Jaish ya koma in da ya fito to
shikenan a mayar mashi da matarsa Mahnoor, har da cewa dama ai Jaish aljani ne ba
mutum ba, dan haka tin da ya koma duniyarsu na aljanu ai ba dawowa zai yi ba, so
shi yana nan a kan bakarsa na zancen Mahnoor.

Ya bi ya tayarwa da kowa hankali, shi lallai a yanke auren Mahnoor da aljani Jaish
a bashi ita ya aura.

Tin bappa yana kallan hakan a matsayin shirme har ya fara yarda da hakan ce
kawai mafita, in ba haka ba Mahnoor ta shiga uku a wannan ƙauye, abin ku da
ƙarancin wayewa da rashin ilimi, zasu sakota ne a gaba da zage zage da kananan
manganganu kamar ita ta ɗaurawa kanta, barema da abin ya haɗu da bappa ya hana nasu
ya baiwa bare, to wlh ba zasu barta ta yi zaman lafiya har ta ji daɗi a ranta ba,
zata kai ta kawo fita ma sai ta gagara yi.

So gudun takura mata yasa bappa ya fara tunanin Arɗo ya kashe aurenta da Jaish
kawai a ɗaura aurenta da Faisal hakan zai sa ta samu sanyi da rayuwar farinciki.

A ɓangaren ita kuwa Mahnoor, kwananta biyu a gidan Arɗo wajen kakarta Inna, kullun
ɓuya take yi ta yi ta zuba kuka babu kakkautawa, tana tsananin san mijinta, sai ma
yanzu da ya yi mata nisa ta gane ashe shi ne farincikinta.

Wlh cikin ƙanƙanin lokaci ta yi wani irin zabgewa ta rame, harta wannan gurun wuyar
tata da Jaish yake gani ya burgesa yanzu tsokar wajen ta zabge saura kashi.

Mahreen da Jaish yake ba mijinta bama ta rame saboda damuwa da kukan bappa ya dawo
mata da Hammanta, kunsan ta saba da shi, bare kuma Mahnoor da ita kaɗai tasan ya
take ji a ranta, ya saba da yi mata abubuwa dayawa, yanzu har kasa yin barci take
yi.

Hankalin bappa ya gaza kwanciya na komawarta gidan Arɗo, dan haka yau ya shirya
tsab zai je ya ɗauko. Ba zai iya yin nisa da ita ba.

Zaune take a tsakar gida ta buga uban tagumi, tana sanye da kayan fulani, ta yi
wanka tsab, sai dai da ganinta zaka san bata cikin walwala, fuska babu annuri, ta
buga uban tagumi.

Idan ka kalleta zaka yi zatan tana kallan Inna dake ta faman shanya masara a tsakar
gidan ne, amma kuma ba haka bane, ta luluƙa duniyar tunani ne.

Sallamar bappanta ya dawo da ita cikin hayyacinta. Tana ɗaura idanu a kansa bata
san lokacin da ta rushe da kuka ba.

Da gudu ta tashi ta nufesa, dik kunya irin tata yau bata san lokacin da ta ce
mashi. "Bappa tare da hamma kuka zo?"

Miƙewa tsaye Inna ta yi daga duken da take tana shanyar masara, tsakanin
tausayin jikar tata ce ya kara kamata. Shiru ta zuba kasu idanu yana kallonsu, ji
take yi kamar ta matsa masu kwallah.

Bappa ya rasa abin faɗe, bashi da kwarin gwiwar iya sanar da Mahnoor ba tare da
Jaish yake ba, dama ya zo da kwarin gwiwarsa ne zai sanar da Inna za'a mayarwa da
Faisal matarsa tun yadda yaga sun ɗauki Jaish da wuya ya waiwayesu, sai kuma ya
cikaro da wannan kuka da take yi na neman Jaish, anya zai iya sanar da ita wannan
magana kuwa?.

Ya jefawa kansa tambayar, jikinsa dik ya yi mugun sanyi. Mahnoor ta rungume shi
tana ta kuka.

Da gudu Mahreen ta fito daga ɗakin Inna, kai tsaye da gudu ta nufi bappa tana
faɗin. "Bappa ina Hammanu yake?".

Ta ƙarisa maganar idanunta cike tab da kwallah. Riƙota ya yi kawai ya runguma bai
iya furta ko kala ba.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Ta ƙarisa maganar idanunta cike tab da kwallah. Riƙota ya yi kawai ya runguma bai
iya furta ko kala ba.

Inna da sun gama jikata da tausayi ne ta juya zata nufi ɗakinta dan ba zata iya
ganinsu ba. Katseta bappa ya yi ta hanyar ɗaga mata gaisuwa.

A daddafe ta amsa mashi tare da wucewa cikin ɗaki da sauri. Tana shiga ta zauna
bakin gado tana addu'ar Allah Ubangiji ya sa kada Mahnoor ta gajesu, dan tun
tasowar Inna a cikin kalubalen rayuwa take har Allah yasa ta auri Arɗo, ta taso ne
a hannun kanin mahaifinta, ta fuskanci wahala wajen matarsa, shiyasa kuka ga tana
da hakuri, baiwar Allah ta wahala ne, ta sha fama a gidan.

Bayan aurenta da Arɗo ma bata huta ba, gwaggon Nenne har kusan haukatata ta yi
a kan kishi a cikin wannan gidan, har yau har gobe kuma basu barta ta huta ba, suna
bibiyar rayuwarta da sharri, dan ta tsaya da addu'a

Please Login or Register in order to submit comment