Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 79 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗan saussauta rikon da ya yi mata, word in out
of control ya shiga yi. "Please Aesh believe that zan dawo maki da dikkan
farincikinki da ya gushe, ki yarda mu yi aure, i promised you that ba zan taɓa bari
ki yi kunci ba, you will never regret kasancewarmu a ma'aurata, please Aesh trust
me"...... Cikin wata iriyar murya tamkar wadda take a buge, kamar bata cikin
hayyacinta ta ce. "Yah Ramish zaka aureni ne kawai ba dan kana sona ba, sai dai
kana tausayina kuma kana san rufe ɓarnar da ka aikata a gareni, baka san familynka
su san cewa ga abin da ya faru, na san halin larabawa sosai, na zauna da su tin ina
karama, wlh dan ka rufe ɓarnarka yasa ka aminta zaka aureni, na tabbata baka sona,
saboda ko a ƴar aikin gidanku ban kai na zo ba, tsautsayi da rufe maku gaskiya yasa
na shigo cikin familynku, masu aikin gidanku dik mutane ne da suka kammala diploma,
baku ɗaukar jahilai a masu aiki, amma ni jahila ce da ko secondary ban kammala ba,
babu wani ilimi a kai na, amma an rufe maku hakan ta hanyar kirkirar mun takardu na
karya wanda ke nuna na yi karatu, bayan ko kusa ko alama ban yi ba, kaga kai ba
saa'ata bane, ba zaka taɓa san jahila wadda bata da gata ba, wacce kuma aka ɗauki
hayarta domin ta kasheka, ko ka manta ni ɗin na shigo gidanku dan in kasheka ne? Ka
mance da cewa na taɓa poisoning ɗinka? Ka manta da cewa na taɓa zama silar da aka
harbeka da gun? Ka manta da cewa na yi maka abubuwa dayawa dan ganin ka mutu?". Ta
kai karshen maganar tana ruwan hawaye.

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Dik nasan da hakan, amma ina san ki san cewa in har
zan ki ki saboda wannan dalilin, to tabbas zan ki Bilal, saboda dik abin da yake
faruwa da sa hannunsa a ciki dik da bani da cikakkiyar hujja mai karfi sosai a kan
hakan, dik hujjojin da nike da su a kansa basu da karfi sosai, amma suna tabbatar
mun da yana da sa hannu a ciki, ki sani ni ba dan na rufe abin da na aikata a
gareki yasa zan aureki ba, sonki nike yi Aesh". Babbar magana, kenan Ramish yasan
da sa hannun Bilal a yunƙurin kashe shi da ake yi? Shiyasa ya juya masu baya kenan?
To mu je zuwa. Wlh Ramish karya yake yi mata, bawani yana sonta ne, batu na gaskiya
yana tinanin tana da ciki shiyasa yake san ta yarda su yi aure dan kada su haifi
cikin a waje, ta yadda Allah ya tashi kama shi kuma sai ya sanya mashi kaunar yara
ta yadda baya jin zai iya zubar da ciki, yana san ta haifa mashi, kamar yadda
Leesharh ta yi hasashe hakan ce, ba wai dan hana sonta zai aureta ba ɗan rainin
wayo. Amma kuma dani da ku dik mun san akwai son nata a zuciyarsa, sai dai shi ɗin
ne bai yarda da hakan ba, baku jin baya wani magana sai su yi sauri su yi aure ne?
Idan da ya yardanwa kansa sonta yake yi, to da tabbas zai rinƙa yi mata abubuwa na
masoya, amma a'a, shi damuwarsa kawai su yi aure.

"No Yah Ramish, na tabbata baka sona, nafa san halin larabawa, tin ina karama na
tashi a cikinku, nasan dik wani hali naku, kuna da kishin zubewar mutumcinku, bare
ma kai da ka fito daga cikin babban family masu karfin faɗa aji a kasar, dole ka yi
komai dan mutumcin gidanku". Ta kai karshen maganar tana tari mara sauti sosai.
"Aesh yanzu baki yarda da maganata ba kenan?". Shiru bata iya amsa mashi ba. Kara
matsawa jikinta sosai ya yi, cikin sigar rarrashi ya fara yi mata dabara dan ta
yarda. Ko da sunan wasa ba ya san abin da ya aikata ta fita, ko dan kakansu King
Badeen, and ace ɗa ga King Zuhair yana da ɗan shege? Kai ai abin babba ne.

Uhm aka ce maka namiji a fagen kalaman yaudara to fa an rufe kofa, dan kuwa Ramish
sai da yasa ta yarda da cewa da gaske yake sonta, amma taki yarda ta amsa zata
auresa, sai ta ce ta yarda da yana sonta, amma dan Allah ya kyaleta haka nan, idan
ma saboda ciki ne ya mayar da ita Nigeria in da babu wanda ya sansa bare har
mutumcinsa ya zube, zata reni cikinta a can ta haifesa ta kuma rike kayanta, ba
zata taɓa kama sunansa a bakinta ba.
Kai kawai ya girgiza, lallai yau ya yarda Leesharh yarinya ce sosai mai
ƙaramin tinani, wai ba zata taɓa ambatar sunansa ba, tab bata san me haihuwar bane,
ai wlh time da yaron zai titsiyeta a kan ina ubanta san da zata ji takura ta faɗa
mashi ma babu wanda ya sani, kuma dik bama wannan ba, a Nigeria tasan ƴan uwanta
ne? Sannan shi dik bama wannan ba, yana bala'in san yara, bare kuma ace jininsa, a
gaskiya yana son kayansa, dole idan akwai cikin nan ta haifa mashi kayansa ta bashi
ko me zai faru sai dai ya faru, babu wani Nigeria da zai maida ta da ɗansa!!.
Babbar magana, ya kuke ganin wanna cakwakiya zata kaya?. Bala'in can, ya mama uwar
jiji da kai zata ji a lokacin da Ramish zai kawo mata bastard matsayin jika? Tab ya
King zai yi?.

Shiru ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi a hankali hankali. Tamkar a mafarki
suka ga wutar gidan ta ɗauke gabaɗaya, a ɗan razane ta yunkura zata bar jikinsa, ta
ɗago kai tana kallan saman ɗakin. Tin da ya ga hakan yasan akwai matsala, dan wuta
bata taɓa ɗaukewa haka nan. Tana ƙoƙarin barin jikinsa ya yi saurin rikota, kamar
mai raɗa ya ce mata. "Yi shiru kada ki motsa". Muryarta a dashe ta ce. "Yah Ramish
meyasa wutar ta ɗauke? Ni dai nasan tsawon shekaru ba'a ɗauke wuta a kasar nan! Ko
dai kai ka kashe ne?............"

Yatsa ya ɗaura mata a saman lips ɗinta. "Kada ki sake yin magana, yi shiru, and ki
zauna a nan ina zuwa, kome zai faru kada ki motsa daga nan". Ya kai karshen maganar
tare da saketa. Tana san tambayarsa ina zai je, tana tsoron ya ce ta yi shiru kada
ta yi magana, wayarsa na aljihinsa, amma bai kunna ligh ɗinta ba, cikin sanɗa ya
nufi waje. Yana fitowa ya ji takun tafiyar kartin mutane suna haurowa saman stair
case ɗin, shiru ya ɗan yi yana mamakin yadda suke da karfin hali da dabarar iya
kashe wutar gidan dan kada camera ta ɗaukesu, dama shi yasan zasu biyosu, saboda
dama bai yarda mota ɗaya ce ta bi bayan Leesharh ba, dole sun saka masu ido, sai
dai bai sa a ransa zasu yi saurin biyosu ba, ya yi zatan zasu ɗan kwana biyu su yi
shiri, fatansa a nan yanzu shi ne Allah ya bashi sa'ar kama ko mutum ɗaya ne da
ransa, dan samu amsoshin wasu tambayoyi nasa.

Yana tsaye yana tinani sai ji ya yi an bangajesa za'a wuce, har sun iso in da yake
ba tare da ya farga ba. Wanda ya bangajesa ɗin ya yi gaggawar fitar da light mai
bala'in haske ya dalle mashi fuska da shi, hakan yasa ya kashe mashi kwayar
idanunsa baya iya ganin su waye ne. Ya yi ƙoƙarin kwace hasken, amma ina ba zai
yiwu ba, dan baya iya ganinsu ma bare har yasan waye ya rike hasken ya kwace.

Tamkar saukar aradu haka ya ji saukar wani irin karfe a kansa, sun kashe mashi ido
da haske baya ganinsu sun dakesa da wani katan karfe a kai, take wani irin jiri mai
karfin gaske ta ɗebesa, dik hasken dake haska shi duhu yake gani a wannan lokaci,
kan ka ce me ya zube ƙasa baya numfashi. Kawar da light ɗin daga kansa suka yi zuwa
kan wasu dake bayan mai rike da light ɗin, wasu irin shirga shirgan mutane ne masu
sanye da bakaken kaya haɗi da manya manyan boots a kafafunsu, ga hands gloves,
mask, baka iya ganin komai a jikinsu sai jajayen idanun da suka yi ja saboda kayan
maye!!.

"Ku shiga ku ɗauko mun ita, shi wanna angama da shi!". Wanda ya rike light. Wucewa
karti uku suka yi izuwa cikin ɗakin, saura suka tsaya a tare da ogan nasu mai rike
da light ɗin.

My people's me kuke tinanin zai faru ne? Ni kaina page ɗin yau sai dai in kora
Maltina and exotic kawai in yi shiru, mu leƙa Paris mu dawo!!.


🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥


Smart ya ɗauki a kallah 10 mins suna tattaunawa da King, da alamar rashin jituwa
kuma a maganganun nasu, dan yadda Smart yake maganar zaka fahimci dikkansu ransu a
ɓace yake. Daga karshe cikin fushi ya katse kiran, sannan ya yi off na wayar
gabaɗaya tare da miƙewa ya nufi cikin ɗakin, haka ya rinƙa rarrashin Auta har
tsawon kwanaki.

Yau takama weekend, Saturday, Smart yana tare da su a gida, bai je ko'ina ba, a ƴan
kwanakin nan ya yi matuƙar sabo da su Pretty, tin tana bakanta mashi rai har ta
dawo tana burgesa a dik abin da take yi, ba abin da ya fi ɗaukar hankalinsa a
tattare da ita sai olive eyes ɗinta da kuma shegen shariyarta na jinin sarauta,
tana bala'in burgesa yadda bata daga idanu ta kalli mutum, sannan tana matuƙar
burgesa yadda take da tsoro, idan ta tsorata ba ƙaramin kyau take mashi tana tafiya
da imaninsa ba, wani lokaci da gangan yake tafiya waje filin dolphins na Auta ya
barsu a ciki, idan ta farga da baya kusa da su ta tsorata ta fara kuka kyau matuƙa
take yi mashi.

Sanye yake da pj a jikinsa, suna sama gabaɗayansu, Auta tana gyarawa Pretty gashin
kanta suna ta hira, shi kuma ya tasa laptop a gabansa yana ta aiki dangane da
bincikensa. Auta da Pretty suna sanye da hoodies na mata a jikunansu, Auta ta sanya
hular kayan a kanta, ita kuwa Pretty daman kun san ba sanya ɗankwaki take ba koda
ba gyaran gashi ake yi mata ba!.

"Yah Omerish me kake yi ne haka? Naga kamar zanen kunnan mutum da ido?". Cewar
Auta, ta yi maganar idanunta a kan laptop dake gabansa, da yake suna kusa da shi
sosai, a saman duguwar sofa set guda suke.

Hankalinsa a kan aikinsa ya amsa mata da. "Ina san kirkirar karfin ji ne fiye da
komai, abin da zai iya dauko sauti tin daga nisan kilomita 10 a tafiya da ƙafa".
Cike da mamaki ta sake cewa. "Yah Omerish to naga hoton kunne, me kake yi da
shi?"........ "Kwaikwayon halittar Allah zan yi! Kamar yadda muka kwaikwayi
halittar idanun mutum muka fidda camera haka nike san kwaikwayar halittar kunne dan
in samu majiya mai karfi".

Ai Auta bata san time ɗin da ta saki Pretty ta miƙe ta dawo kusa da shi sosai ba,
cike da mamaki ta ce. "Yah Omerish dama Camera idanun mutum aka kwaikwaya ne?"....
Kai ya jinjina mata kafin ya amsa da. "Komai da kimiya take kirkira ai kwaikwayo
muke daga halittar Allah, babu wanda ya isa ya kirkiro wani sabon abu a duniya, sai
dai ya kwaikwayi wanda Allah ya yi, Ubangiji ya rigada ya halicci komai, kawai dai
mu muna zamanantar da shi ne"..... Kara shiga mamaki sosai Auta ta yi, ita kuwa
Pretty bama su isheta kallo ba, mashirmaciya, kwanciya ta yi tana kallan sama kamar
wata dake da motsi a kai, babu ruwanta da tattaunawarsu.

"Yah Omerish to tayaya kuka kwaikwayi ido? Tayaya Camera yake kama da shi?". Cike
da zaƙuwa da san jin amsa ta tambayesa. Dakatawa da aikin da yake yi ya yi, sannan
ya juyo da kallonsa game da hankalinsa a kanta, cikin sanyin murya ya fara bata
ilimi kamar haka!.

"Abubuwa da dama muka kwaikwaya daga idon mutum muka kirkiro Camera, cikin abubuwan
da muka kwaikwaya sun haɗa da. Lens da Focusing wato mayar da hankali. Kamar yadda
ruwan ido wato lens yake daidaita haske domin samar da kallo mai kyau, ya iya
fahimtar menene a gabansa, haka ma camera ke amfani da lens dan mayar da hankali
wato focus ga abubuwan da take ɗauka, kin ga a nan mun kwaikwayi ido".

"Abu na gaba shi ne. Aperture wato kofar shigar hasken shiga. Ido yana da wani
ɓangare da ake kira da pupil, wanda ke buɗewa ko rufewa don daidaita adadin hasken
da ke shiga. To haka camera ma, tana amfani da aperture wanda ke sarrafa yawan
hasken da ke shiga camerar, nan ma kinga idanu muka kwaikwaya".

"Na uku shi ne. Retina da image sensor, wato fuskar karɓar hoto. A cikin idon
mutum, retina ce ke ɗaukar hoton da haske ya samar, sai ta aika wa kwakwalwa ta
hanyar jijiyoyin gani, ƙwaƙwalwa itake tantance menene a wajen ba ido ba!. To haka
a camera ma, akwai image sensor, wato kamar CMOS ko CCD wanda ke ɗaukar hoton da
haske ya samar sannan ya juya shi zuwa hoto har ma a iya adanawa kamar yadda
ƙwaƙwalwa take adana hoton da ido ya gani, in kaga abu ai ka rigada ka gani ne, ya
zauna a kwakwalenka".


"Na huɗu shi ne Autofocus, wato daidaita tsawo. Kamar yadda idon mutum ke daidaita
mayar da hankali kan wani abu cikin sauri. To haka camera ma tana amfani da
autofocus system dan tabbatar da cewa hoton yana cikin sharp. Abu na biyar shi ne
HDR, wato high dynamic range da Contrast Perception. Ido yana iya bambanta haske da
inuwa fiye da yawancin Cameras. Dan haka an ƙirƙiri HDR technology a camera ne dan
taimakawa wajen ɗaukar hotuna masu daidaiton haske da duhu sosai, kuma har yanzu
mun ƙasa iya kirkirar camerar da zata iya daidaita abu sak yadda ido zata iya yi,
dik da kullum muna cikin kara faɗaɗa bincike ne dan gano manyan abubuwa masu amfani
da zasu daidaita komai, shiyasa zaki ga duniya tana kara gaba Camerori masu karfin
ɗauka suna kara fitowa, har yanzu ƙoƙari muke yi muga camera ta yi karfin ɗauka
kamar ido dik da mun san babu wanda ya isa ya yi abu dai'dai da Allah, muna dai
kwatantawa ne iya baiwar da Allah ya yi mana!".

"Dik da cewa camera ta zamani tana da fasahar da ke kama da yadda idon mutum
ke aiki ko in ce maki mun kwaikwayi ido mun kirkireta, to har yanzu idon ɗan adam
ya fi ƙarfi wajen fahimtar launi, haske, da zurfin hotuna fiye da kowace camera da
muka ƙirƙira a duniya, muna dai iyaka bakin ƙoƙarinmu, amma Allah ya wuci tinanin
mutum, babu wanda ya isa ya yi dai'dai da shi, sai dai mu yi ta kwaikwayo dan
samawa al'umma saukin abubuwa!". Ya kai karshen maganar yana ɗan jan lallausan
kumatunta, ta wani natsu tana suararonsa.

"To shi ne yanzu Yah Omerish kake kwaikwayon kunne?". Like wow ta yi tambayar,
abin ya bata mamaki ne sosai, wato dai dik wani kimiya kwaikwayo ne daga Allah, sai
dai su Allah ya basu baiwar iya zaƙulo halittun da idan sun kwaikwaya sun yi wani
fasahar da shi zai taimakawa al'umma sosai, lallai su ƴan baiwa ne sosai!!......
Jinjina mata kai ya yi alamar e yana kirkiro naura mai karfin ji sosai ne, zubawa
laptop ɗin nasa idanu ta yi tana kallan yadda yake ta ƙoƙarin faɗaɗa bincikensa, ya
zuba tsantsar basira a kan aikinsa.

Suna a haka tiger ɗinsa ya shigo wajen da gudu yana gurnani. Ai daga Auta har
Prettyn dikka haukace mashi suka yi, gabaɗaya suka rungumesa suna ihu. Sai suka sa
ma ya rasa me zai yi, saura kaɗan su jefar mashi da laptop a ƙasa Allah yasa ya
tare. Ya ƙasa yin komai dan sun nukunkume shi, ga ihun da suke yi. Cikin harcen
farasanci ya rinƙa cewa damisan ya tafi, amma shi ma yaki tafiya, dan iskanci, sai
ma tsalle da ya yi zai haye jikinsa. Ai wani ihun da Auta ta kurma sai da ta sanya
damisan dakatawa. Daga bisani ya juya da gudu ya bar wajen, ajiyar zuciya Smart ya
sauke kafin ya ce. "To sarakan tsoro, sai ku sakeni ai tin da ya tafi". Auta ce ta
fara cewa. "Yah Omerish ka leƙa tukun nan ka tabbatar da ya tafi ko yana nan".
"Matsoraciya kawai, ya tafi, kuje ku shirya ma ku zo mu je in kaiku yawo tin da
weekend ne".

Ai da jin haka Auta ta yi gaggawar sakinsa, dama ta jima tana rokon ya fita da su,
sai ya ce masu yana busy, to yau dai zasu fita, cike da ɗauki ta ja hannun Pretty
suka nufi stair case dan su je su shirya. Da kyar Pretty ta yarda ta bita, sai da
ta ce mata tiger fa ya sauka ƙasa gabaɗaya, yana harabar gidan, sannan ne ta yarda
ta bita, suna shiga bedroom ɗinsu suka garƙame da key wai dan ma kada tiger ya
biyosu ciki.

Shi kuwa komawa ya yi ya zauna yana jiran ya ga wanenen zai auro saman, dan zuwan
da damisan nan ya yi wajensa labari ya kawo mashi a kan ya yi baƙi, yana fahimtar
dabbobin nasa, kun san idan ka zauna tsawon shekaru da dabba kuka saba to fa zaka
iya fahimtar dik abin da take ciki. Yana zama sai ga wasu zaƙwaƙuran matasa biyu
sun hauro saman, ɗaya fari tas kaman madara, ɗayan kuma chocolate color, kusan
kansu ɗaya, and ɗaya farin kaman bature ne, ɗayan kuma Africans ne, dikkansu
kyawawan gaske ne, tsayayyun maza, dik in da ake neman namiji to sun kai, ko da
yake tin da kuka gansu a tare da Smart kun san suma ba baya ba, dan baya abota da
marasa fasali marasa ilimi.

Kai tsaye suka nufosa, da ido ya bisu har suka iso shi, hannu ya miƙa masu suka yi
musabaha kafin su samu waje saman sofa suka zazzauna. Cigaba ya yi da aikin da yake
yi tare da faɗin. "Zash yaush ka dawo?". Wannan handsome chocolate guy ɗin ne ya
amsa mashi da. "Yesternigh". Jinjina kai ya ɗan yi kafin ya juyo da kallansa a kan
ɗaya farin. "Bobo is there anything problem?".

Fuska ɗauke da damuwa Bobo ya amsa mashi da. "Yeah". Zuba mashi idanun suka yi suna
sauraransa. Cigaba ya yi da cewa. "My baby, yau da kewarta na tashi sosai". Ɗan
kawar da kansa Smart ya yi. "Sorry, komai zai wuce, abu kaɗan ya rage mana"....
Nisawa Smart ya ɗan yi kafin ya kawar da kallansa daga kansu, a ransa yake faɗi shi
bai ga amfanin damuwar da bobo yake yi a kan wani abin bama, yakama ne ma a ce ya
manta da kowa da komai na rayuwarsa ta baya tin da yanzu komai ya canza.

Uhm wanenen bobo da ake so ya manta da komai na rayuwarsa ta baya? Mu ji tarihinsa
kaɗan, dan shi ma yana daga cikin manyan stars na RAWANIN ZALINCI. RAWANIN ZALINCI
labarine a kan ɓangarori biyar, dan haka manyan jaruman cikin littafin zasu iya
kasancewa su bakwai ne, amma idan kuka san wanenen Bobo zan banbanta maku sani
abin.

-------------------------------------🔥♥️

BLOOD CROWN. shi ne sunan masarautar su Bobo, masarauta ce da aka kafata a kan jini
tin zamanin kakanni. A cikin masarautar BLOOD CROWN, a dokance dik wani sarki ko
sarauniya da zai hau karagar mulki sai an zub da jinin wani a matsayin hadaya. Ana
kiran wannan al'ada da suna kariya wacce suke ganin ita ce take kare masarautar
daga lalacewa ko hare hare daga masarautu, ita ce take hana kowa iya tinkararsu,
kuma suna ganin hakance ma ta hana King Zuhair yakarsu, a cewarsu sun rufe mashi
ido da baki ba zai iya yin komai a kansu ba, dan suna sadaukarwar jini!!.

Bobo shi ne babban Prince na wannan masarauta, yana da kanne mata ƙanana guda biyu,
ya shaƙu da kannen nasa matukar shaƙuwa, yana bala'in sansu fiye da kansa, sun taso
cikin gata da kula, a lokacin da ya kai shekaru 22 sai mahaifinsu ya fara shirye-
shiryen yadda za'a fara koya mashi sarauta, dan shi ne kawai magaji. Sam sam
mahaifiyarsa bata so ba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa mutanen garin basa
san haihuwar ƴaƴa maza, dan za'ace za'a basu mulki, kuma kafin su hau mulki sai sun
zub da jinin wanda suka fi kauna. Shiyasa suke san haihuwar ƴaƴa mata, har murna
suke su shirya shagali idan suka haifi mace, amma in suka haifi namiji, wlh kuka
suke yi yadda kuka san gidan makoki, gidan suna sai ya koma gidan mutuwa!!.

Mahaifinsa jarumin gaske ne na bugawa ga jarida, kazalika mahaifiyarsa, zakanya ce
sosai!. Sai dai masarautar tasu ƙazantar dake cikinta ya zarce tinanin mai tinani,
suna bautar da mata, suna wahalar da su, sun ɗauki mace a matsayin abar sauke
sha'awarsu kuma baiwa a garesu, mata basu da wani galihu basu da gata, dik wani
aikin karfi mata ne ke yi, dik wani zalunci suna yi masu, a dik time da suka ga
dama ko a cikin daji ne zasu haiƙewa matansu su biya buƙatarsu, noma mata ne suke
yi, kai komai da maza zasu yi matan ke yi, a cewarsu ai mata bayinsu ne, babu
tausayi babu imani, fyaɗe da zinace zinace ya yi over, ba zaku so tona ɓarnar da
suke aikatawa ba wlh, amma a hankali idan tafiya ta yi nisa zaku ji komai!.

--------------------------------🔥🔥

Bobo ya fara karɓar dik wani horo da ya danganci mulki salum alum, sai dai a
lokacin da aka zo kan batun sadaukar da jini kafin ya ɗale kan kujerar mulki, aka
sanar mashi cewa dole sai ya kashe wanda yake tsananin so kafin ya hau gadon
sarauta. Wannan ita ce hanyar tabbatar da biyayyarsa ga mulkin da aka gina a kan
jini!. Tashin Hankali. Nan fa Bobo ya ce babu wannan magana, dan dik duniya mutum
huɗu yake so, daga kannensa mata guda biyun nan, sai mahaifiyarsu da kuma
mahaifinsu, dan haka ko mutum ɗaya ba zai iya kashewa ba, babban abin takaicin ma
wai shi da kansa zai kashe mutumin da yake kauna, sannan ya lashi jininsa a kan
harshensa, dik dan ya nuna zallar rashin imani, a cewarsu ta hakance kawai zasu iya
gamsuwa da cewa namiji mai dakakkiyar zuciya ce yake mulkarsu. Sai dai kuma ba zai
iya bada wanda ya taɓa yin mulki ba, misali ace ya bada mahaifinsa, hakan ba zai
yiwu ba, dan already babansa yana da tsari ya ɗale dangerous seat kuma ya ɗaura
blood crown a kansa.

Bobo ya shiga ruɗani da tashin hankali a in da ya fara bincike a kan masarautar
tasu, gadan gadan ya shiga wannan bincike. A nan ne fa ya gano wani sirri mai ban
tsoro, wato sarautar BLOOD CROWN tana da asirin duhu. Ba wai kawai ana kashe mutane
ne dan cimma muradi ba, rawanin da kowani sarki yake sakawa a yayin hawa mulkinsa
rawani ne da yake da wata asiri mai kyaucewa hankali. Dik wanda ya sanya rawanin
nan a kansa, zuciyarsa ba ta ƙara jin tausayin mutum, daga nan ya rabu da imani da
tausayi.

Bobo ya gano cewa dik sarakunan da suka gabace sa, rawanin ya mai da su masu
mugunta, yana rage musu tausayi kuma yana ƙarfafa su su yi zalunci ba tare da
rashin jin daɗi ko kunya ba. Wannan yana nufin idan har shi ma ya sanya rawanin to
zai zama azzalumi kamar su. Babbar magana! Ya shiga ruɗani mai girma gano cewa yana
da yaya namiji da mahaifinsa ya kashe domin ɗale kan kujerar mulki, ya sadaukar da
jininsa ga BLOOD CROWN kenan, bala'i iya bala'i Bobo ya shiga a wannan lokaci, nan
fa ya fara tinanin mafita a garesa dama ƴan uwansa bakiɗaya, dan ba zai taɓa iya
bada ko mutum ɗaya daga cikin huɗun nan ba, ba kuma zai iya bari a cigaba da wannan
ɓarna ba, saboda a lokacin shi ya musulunta ba tare da saninsu ba, a makarantarsu
ya karɓi musulunci daga abokinsa wato Smart, tare suka yi karatu a ƙasar France, a
lokacin da aka ce ya karɓi mulkinma hutun school ya dawo, daga nan suka rikesa wai
karatun ya isa haka, lokacin hawansa gadan mulki ya yi! Dama shi ya matsa yana san
karatun!.

Daga nan Bobo ya fara shirin wargaza mulkin zalunci. Sai dai hakan yana da
gagarumin hatsari da barazana ga rayuwarsa da ƴan uwansa. Sama da sau goma ƴan
majalisar masarauta tana yin zama a kansa, sun tursasa mahaifinsa a kan ya sanya
shi dole ya ya zaɓi wadda ya fi kauna ya kasheta a karawa CROWN ɗinsu karfi, dan da
alama zasu iya fuskantar marazana daga wasu masarautun idan basu yi gaggawar bada
jini sun karawa RAWANIN karfi ba. Sai dai dik yadda za'ayi da Bobo anyi yaki buɗar
baki ya ce ga wadda ya fi so, da zarar an yi mashi magana sai ya ce su ɗan kara
mashi lokacin. Ya yi kokarin canza dokokin masarautar, amma ƴan majalisar masarauta
sun dakatar da shi game da daka mashi zazzafar warning a kan zai iya rasa ransa
idan ya yi kuskuren taɓa doka guda ɗaya daga littafan dokokinsu, dole ya bi komai
kamar yadda ya ganta a rubuce, tsawon shekaru suke a kan wannan tsari. UHM ABIN
TAKAICIN MA WAI WANDA YA FI KAUNA ITA ZA'A KASHE, WLH BASU DA IMANI KO KAƊAN
MUTANEN NAN!!.

Bobo ya yi iya tinanin da zai yi, amma ya kasa samawa kansa mafita, saboda sun fi
karfinsa, bai isa ya yi fito na fito da su ba, sun fishi yawa, hakan tasa ya koma
gefe ya yi shiru dan tinani a natse ko za'a samu mafita. Daga karshe ya yanke
shawarar fitar da sirrin familynsa ga abokai ko zai samu maslaha,

Please Login or Register in order to submit comment