Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 89 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi dan ya fitar
da kalmar da Smart ya faɗa ba mutuwa ba, wai irin zai ce wata kalma mai kama da
mutu kenan sai ya ce haka Smart yake son cewa ya manta ya ce mutuwa. Da haka suka
isa gida, tin bai gana kashe motar ba Smart ya fito ya buɗe gidan baya, ko kaɗan
bai bi ta kan Leesharh ba ya ɗauki Auta ya nufi cikin gida kamar gidansa.

A gaggauce Ramish ya kashe motar ya bi bayansa, ita ma Leesharh da gudu ta rufa
masu baya. A parlour saman kujera ya shinfiɗe Auta, sannan ya ciro wayarsa ya
dannawa number Zash kira, yana ɗagawa ya ce mashi. "Mun iso everything is ready".
Yana kai karshen maganar ya katse kiran. Dai'dai lokacin Ramish ya shigo ciki, har
tsoron sake tambayar yayan nasa yake yi, dan zuciyarsa ba zata iya ɗaukar jaddada
mashi mutuwar Auta ba, a bakin kofa ya tsaya ya ƙasa ƙarisowa ciki.

Binsa da kallo mai ɗauke da fassara kala kala Smart ya yi kafin ya ce. "Zoka zauna
mu yi magana akwai in da nike san zuwa". Kai ya ɗan girgiza yana kallon gawar Auta
ya sake kallan Smart, alamar ba zai iya ƙarisowa ciki ba. Nisawa Smart ya ɗan yi
kafin ya ce. "Zunaira bata mutu ba, shikenan zo ka zauna".

Wani irin dogon numfashi da Ramish ya ja tare da dafe saitin zuciyarsa shi zai
tabbatar maka da suna bala'in kaunar Auta fiye da kawunansu, sonta a cikin jinin
jikinsu yake!!. A hankali ya karisa ya zauna kusa da ita, dai'dai lokacin ita ma
Leesharh ta shigo.

"Zunaira bata mutu ba, ta shiga doguwar suma ne, Zash zai kawo likitocin da zasu
lura da ita, zan barta a nan a hannunka, ka bata kulawa sosai wanda nasan ba sai na
faɗa maka ba zaka yi hakan, kada ka bari kowa yasan tana raye, ina san dad ya
ɗanɗani azabar da ta ji a zuciyarta lokacin da ya yi mata sanadiyar mutuwar wanda
take so, ko mijin nata kada ka bari yasan tana raye, zamu bari a matsayin ta mutu,
sai ta samu lafiya sosai, idan tana san zama da Abdussalam ɗin sai a barsu, idan
kuma bata so sai a raba auren". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a
kanta. Yau tin da ya ɗaura idanunsa a kan Ramish yake yi mashi wani irin kammani
kamar Hoorain haka! Shi da yake yasan kamannin Hoorain tin yana Paris, akwai
hotunansa ma dayawa a wayarsa wanda shi Hoorain ɗin yake turawa Auta a lokacin da
suke soyayya!.

"Yah Omerish amma me yake faruwa ne? Dama bata san Abdussalam ɗin ne aka yi
auren?". Ramish ya tambaya!. Jinjina mashi kai Smart ya yi kafin ya faɗa mashi dik
abubuwan da suka faru na yadda King ya hanata Hoorain har hakan ya yi sanadiyar
mutuwar Hoorain ɗin, da ta ji Hoorain ɗin ya mutu shi ne ta shiga doguwar sumar
nan! Sosai Ramish ya ji ɗacin abin da dad ɗin nasu ya yi, tsabar ɓacin rai bai san
lokacin da ya ce. "To shi dad ɗin akwai wanda ya taɓa hanashi san ransa ne? Amma me
Hoorain ya yi mashi bayan soyayya da Zunaira? Hukuncin ya yi tsauri".

Kai tsaye Smart ya ce. "I think Hoorain ɗansa ne ko kuma suna da wani kwakkwarar
alaƙa a tsakaninsu"............ Wata uwar zabura Ramish ya yi, with harsh voice ya
ce. "Ɗansa kuma? How comes?".......... Dan furzar da iska mai tsananin zafi daga
bakinsa Smart ya yi kafin ya ce. "Dik ajiye waɗan nan batutuwa, yanzu dai zan turo
jami'ai guda goma su yi tsaron gidan nan, zan turo wasu biyu daban kuma su yi
tsaron Zunaira sosai, ban yarda a bata komai daga wani waje ba ba tare da sanin
jami'an dana wakilta ba, ban yarda ta ci wani abinci ba face wanda waɗan nan
jami'ai zasu girka mata, sannan su zasu rinƙa yi mata komai, kai dai ka saka idanu
a kansu, kuma zata so ganinka a kusa da ita. Idan na gama bincike a kan koma menene
you will get the result, maybe zan dawo gareku cikin satin nan, maybe kuma zan iya
fin hakan".

Tashin sense, shiru Ramish ya yi yana mamakin abubuwan da suka faru, wannan wace
iriyar musifa ce? Ya jefawa kansa tambayar. Zuba mashi idanu Smart ya yi yana
kallan face ɗinsa, dik yadda aka yi Smart yana hasashen Ramish ɗan waye, tausayinsa
ne sosai ya kama shi, ya zai ji idan aka toni asalinsa? Gaskiya King bai yi mashi
adalci ba sam sam.

"Don't trust anybody my brother, idan da dama kanka ma kada ka yarda da shi
gabaɗaya, ka kula sosai". Cewar Ramish.............Jin jina kai Ramish ya yi kafin
ya ce. "Yah Omerish ina jin kamar Raj ba kanina bane, saboda abubuwan da suka
faru".

Tausayinsa ne ya sake kama Smart, kamar kuwa yasan gaskiya. "Kaninka ne, ka dai'na
barin shaiɗan yana sanya maka banzan tinani a ranka, keep praying, everything will
came and end"........ Shiru ya ɗan yi, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin
zuciyarsa. Smart zai sake yin magana idanunsa suka sauka a kan Leesharh dake manne
da jikin bango tana binsu da kallo. Ɗan zaro idanu Smart ya yi, saboda tsantsar
kamanninta da Zash da ya gani, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa.

Dai'dai lokacin Zash ɗin ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama, ga wasu shahararrun
Drs guda uku biye da shi a baya. Miƙewa tsaye Ramish ya yi yana faɗin. "Zash wanene
ya faɗa maka ina nan?". Harara ya wurga mashi kafin ya ce. "Awww our bro ka ɗauka
sai ka faɗa mun in da kake ko?". Ɗan ɗaure fuska ya yi tare da cewa. "Stop please,
wai ya aka yi kasan gidana?"....... "Kana mamaki ne?". Smart ya katsesu. Da sauri
Ramish ya juyo da kallonsa a kan Smart ɗin. "E Yah Omerish, friend ɗina ne fa, kuma
ni ban taɓa zuwa da shi nan ba, ban san ya aka yi yasan nan ba".

Miƙewa tsaye Smart ya yi. "Ni na turo shi wajenka domin in san dikkan ƴan uwana, ba
jami'i kasa da kai bane kamar yadda kake tunani, shi bama SWAT bane, ya shiga
jikinka ne kawai bisa umarnina, assistant ɗina ne a wajen aiki, jajirtaccen jami'i
fiye da tinaninka, yanzu kuma ni na ce ya zo nan da Drs dan su duba Zunaira".

Mamaki ne ya kama Ramish, dama ya yi mamaki a lokacin da Zash ya shiga hukumar
SWAT, dan da kallo ɗaya ya yi mashi yasan wannan kwararren jami'i ne sosai, amma
sai ya bar abin a ransa, suka cigaba da kasancewa a tare, ashe kuwa hakan ce,
jami'i ne. Yana can yana mamaki har su Drs sun dukufa a kan Auta dan jadada
aikinsu. Smart bai jira ba ya wuce haɗe da yi masu sallama, haka ya zo ya wuce
Leesharh ba tare da ya sake ɗaga idanu ya kalleta ba. Mayar da hankalinsu su Ramish
suka yi kan samawa Auta lafiya, babu wanda ya damu ko ya mayar da hankali kan
kamannin Leesharh da Zash bare har su yi bincike!!.

A can kingdom of power kuwa, lokacin da King ya tabbatar da Zunaira fa mutuwa ta yi
ta bakin Jaish, wlh yanke jiki ya yi ya faɗi, sai dai suka kwashesa zuwa hospital,
doguwar suma ya yi, sai da ya shafe kwana biyu a sume likitoci suna ta kokarin a
kansa, daga bisani aka dawo jinyarsa a gida bayan ya farfaɗo, sai da ya ɗauki good
3 weeks yana jinya, baya furta komai sai dai ya yi ta binsu da kallo, kuma dik da
haka bai yi danasanin hana aurenta da Hoorain da ya yi ba, ya dai yi fatan da wani
take so ba Hoorain ba ba shakka da zai bata shi ko da ba jinin sarauta bane,
Hoorain ne dai baya kaunar haɗa jini da shi.

Momma bata san Auta ta rasu ba, sun ɓoye mata, ko da ta dawo daga Dubai sai ce mata
suka yi tana wajen uncle Muhammad na France, wato daddyn Smart kenan, hakan yasa
bata wani damu ba. King dai ya sha jinya, dan wlh har Auta ta farfaɗo ta fara samun
lafiya sosai shi bai koma dai'dai ba, kuma kusan kamar commander ya zama, dan wani
lokaci sai ya rinƙa magana kamar Auta tana kusa da shi, kamar yana tare da ita suna
hira. Abin ya tada hankula matuƙa, yanzu uncle Abbas shi ne yake kula da mulkin
kingdom of power, King yana jinya.

Gudun kada guyson ya samu taɓin hankali yasa Smart ya sanar da shi Auta bata mutu
ba tana raye, ya kuma sanya Ramish ya haɗasu suka ga juna, ranan sun sha kuka
sosai, tin da Auta ta farfaɗo bata yi magana ba sai ranar da guyson ya zo wajenta,
a nan ne ta yi magana, ta yi kuka, ta kuma yi wa Hoorain addu'a, daga nan Ramish ya
ce tun da ana hutun school a bar guyson ya kasance a tare da ita, dan a dalilin
zuwansa wajenta sauki ya kara samuwa har tana magana, Smart ya yi na'am da hakan,
shi kuma yana kingdom of power, rashin lafiyar da King yake ciki yasa bai tada
balli a kan amsoshin da yake so ba, ya ɗaga kafa zuwa dad ɗin nasa ya samu lafiya.

RAMADAN KAREEM!!.

Ana gobe za'a ɗauki azumi, sai shirye shirye ake ta yi na tarar wata mai falala mai
albarka, unexpected Smart ya ga diran mom ɗinsa a kingdom of power, ta ce ba zata
iya zama ba tare da shi bane, tin da yaki dawowa shi ne ta biyo bayansa, ya ji
matuƙar daɗin ganinta, ya kuma jin babu daɗi yadda ya bari ta yi kewarsa, matar da
tin da ya taso fara'a kawai yake gani a face ɗinta, ta so shi fiye da yadda take
san kanta, macen kirki adala, ya yi mata addu'ar samun haihuwa sau ba iyaka, ya ji
dama ace yana da damar sama mata aihuwa da sai ta gaji da ƴaƴa.

Sosai su momma suka karɓeta hannu bibbiyu, momma ma ai sai zama yar kallo ta yi a
tsakanin Smart da mom ɗinsa, dan kuwa ya tare a wajenta abinsa, kafin ya je wajen
momma sau ɗaya ya je wajenta sau uku, kun san zuciya bata da ƙashi, sai momma ta
fara danasanin kai mashi su da ta yi, tana ganin kamar ya fi son mom ɗin tasa a kan
ita da ta haifesa, bata san ba haka bane, shaƙuwa ce kawai, kada ku manta tun yana
jajiriri fa, mom ɗinsa ita ta yi mashi komai, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da ita,
momma fa time to time take zuwa wajensa, a shekara sau ɗaya take zuwa idan ta samu
damar zuwa Dubai gaisuwar azumi, kunga kuwa dole ya fi shaƙuwa da mom ɗinsa, amma
batu na so da kauna ai baya haɗa momma da kowa, it kaɗai ce babu ta biyunta!!.

Zaune suke a parlourn momma, da momma da mom ɗin nasa suna hira, nan momma take
cewa mom ta yi wa ɗan nata magana ya yi aure mata. Murmushi mom ta yi kafin ta ce.
"Ai baya son yi, ta kyalesa sai time da ya yi ra'ayi, ga shi nan Heleena tana can
tana haukar sonsa amma yaki kulata".

Jim momma ta ɗan yi, dan tasan Heleena da ake magana a kai, sai bata ce komai ba,
dan kada ta ce wani abu mom ta ce bata son familynta.
A can gefe kuma King ya gama sanar da uncle Abbas cewa yana nemanwa Smart
auren Sareena, dan sun dace, uncle Abbas kuma ya ce Allah ya basu zaman lafiya,
wato ya bashi kenan, uhm yau ake yinta. SAREENA ZAƁIN KING GA SMART, HELEENA ZAƁIN
MOM ƊINSA, PRETTY ZAƁIN MOMMA, wa kuke tinani zata zama zaɓin Smart kuma?........

Suna tsaka da hiran sai ga Sareena ta shigo cikin part ɗin, tana san ganin Smart
ɗin ne, ta jima tana san ganinsa bata samu dama ba, shi ne ta daure ta zo part ɗin
momma ko yana ciki, tana tsoron zuwa room ɗina. Yau dai tana sanye da abaya har
ƙasa, sai dai da alama shegen shigar tata ta yi daga ta ciki.

A saman carpet ta zauna tare da ɗagawa su momma gaisuwa kamar wata ta Allah. Fuska
ba ya bo ba fallasa momma ta amsa. Shiru ta yi tana tinanin me zata ce ne ta samu
bayani a kan Smart, shin yana gidan ne ma ko baya nan, ta ƙosa ta ji. A daidai
wannan lokaci mama Haulat ta shigo ɗauke da abincin Smart cikin wani luxury tray na
alfarma.

Duba time momma ta yi, karfe 8:30 na dare, kallon mama Haulat ɗin ta yi. "Lokacin
cin abincin nasa ma ya yi, bari mutuniyar tasa ta zo ta kai mashi"....... A saman
table mama Haulat ta ajiye abincin tare da juyawa ta nufi waje. Jiki na ɓari
Sareena ta ce. "Momma abincin Yah Omerish ne?". Kai Momma ta gyaɗa mata alamar e. A
hanzarce ta miƙe, jiki na ɓari ta ce. "To bari in kai mashi momma". Oh ta samu
dalilin zuwa in da yake!.

"A'a Sareena, Omerish bai aminta da kowa ya kai mashi abinci ba face Pretty, ko su
Jaish ya ce baya so, ita kaɗai ya yardanwa, kuma kin san dokace ma ta wannan gidan
ba kowa yake kaiwa Prince abinci ba sai wanda ya naɗa da kansa kuma ya amincewa".
HAKIKA DOKARSU CE HAKA, BAMA ABINCI BA, BABU WANDA YA ISA ZUWA KUSA DA SMART A
MATSAYINSA NA PRINCE MAGAJIN MULKI IDAN BA WANDA SHI DA KANSA YA YARDANWA BA KUMA
KO ABINCIN DA ZAI CI SAI AN TANTACETA SOSAI, KO ITA PRETTY DA YA AMINTA TA RINƘA
KAI MASHI ABINCI BA TA ISA TA KAI ABINCIN KAI TSAYE BA, DAGA KITCHEN SAI AN TANTACE
KOMAI TSAB AN TABBATAR BABU WANI ABIN CUTARWA SANNAN TA WUCE TA KAI MASHI.

Shi da kansa ya ce wa momma bayan Pretty bai yarda da kowa ya taɓa abincinsa da
sunan zai kawo mashi ba, yana jin daɗin cin abinci da ita shiyasa ya ce ita zata
rinƙa kawo mashi, saboda su ci a tare, kun san Pretty da shiririta da sakalci, idan
suna cin abinci tana sanya shi nishaɗi da har ya ci abinci sosai ba tare da ya sani
ba, yana mugu mugun son kasancewa a tare da ita, sai ta kai karfe 1 na dare a
ɗakinsa, yana aikin bincikensa a kan familynsa, ita kuma tana zuba mashi shirme
tana bashi nishaɗi, wani lokaci sai ta yi barci a bedroom ɗin nasa, sai ya kammala
abin da yake yi zai mayar da ita nata ɗakin, a tare suke kwana da Mahreen a part na
momma, to nan yake kaita idan ya tashi kwanciya barci.

Da momma ta ce to ya auri Pretty ɗin mana kawai sai abin ya fi bada armashi, sai
cewa ya yi shi bai ce yana sonta ba ai, kawai dai yana jin daɗin kasancewa da ita
ne, tana ɗebe mashi kewar Zunaira tana kuma saka shi nishaɗi.

My people's anya kuwa kun yarda da Smart? Wai tana saka shi nishaɗi! Ina team ɗin
Pretty, kada ku yarda zai lallata maku ɗiya, in ba iskanci ba ka aureta ɗin mana,
zaka wani ce nishaɗi take baka!.

Wani irin ɗaure fuska Sareena ta yi, ranta ne ya yi maki, kamar zata sake yin
magana sai kuma ta yi shiru, ta zauna tana jin tamkar ta haɗiyi zuciyarta.........
Tsabar sakalci irin na Pretty ko sallama bata yi ba ta afko cikin parlourn, tana
sanye da sleeping dress white color, riga ne da wando dogo, ta saki gashin nan har
baya, Momma ta yi ta yi da ita ta rinƙa ɗaura ɗankwali amma yarinyar nan taki fir.
Tana turo baki ta zo ta zauna kusa da momma, sarkin son jiki har da kwantowa a
jikinta tana shagwaɓe fuska. Momma tasan halinta sai cewa ta yi. "Yunwa kike ji
ko?".

Kamar zata yi kuka ta amsa da e yunwa take ji!. "To ai ga abincin yayan naku, tashi
ki je ki kai mashi sai kuci kamar da kuka saba". Cewar momma.. ita dai mom da bata
jin larabci sai binsu da ido kawai take yi bata san me aka faɗa ba. Jin momma ta ce
ta tashi ya ɗauki abincin Smart ne yasa Sareena ta gane e lallai wannan ita ce
Pretty da ake ta magana, binta da kallo ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, saboda
tsantsar madarar kyau da ta kallah, tasan babu abin da zata gwadawa Pretty sai
rashin kunya wanda bata san cewa shi ma Pretty number ɗaya bace, sai dai idan ba'a
zo ɓangaren ba!.

Ziciyarta ne ya cigaba da kara ƙawata mata kyan Pretty, tinani ta fara yi a kan me
zata yi mata ta rabata da Smart, ya zamana ma ko inuwarsa ba zata sake gani ba,
bama ta san wacece Pretty ko yar wacece ba, ita dai tin da ta ganta a part ɗin
momma sai ta zaci ko daga cikin ƴan uwan momma na Dubai take!. Tana can tana tinane
tinane bata san lokacin da Pretty ta ɗauki abincin Smart ta fita abinta ba, sai
waigawa ta yi taga babu abincin kuma babu ita ma Prettyn. Siririn tsaki ta ja wanda
ta manta a gaban momma take.

Miƙewa ta yi ta nufi waje, a cikin ranta tana faɗin lallata kyan Pretty kawai zata
yi shi ne mafitarta, zata ɓata mata fuska kaca kaca ya yi damage ta yadda kowa zai
ji kyamarta. Tana fita ta nufi part ɗinsu Omaid dan su shirya wannan mugunta a
tare, dan ta rantse ba zata bar Pretty ba.

Ita kuwa Pretty kai tsaye ta wuce bedroom ɗinsa, babu ko sallama ta afka ciki
abinta, yana zaune a saman bed ɗinsa sanye da sleeping dress kalar na jikinta sak,
dama shi ya saya mata tin a France, so su uku suka yi ankonsu, shi da ita da Auta,
yana rike da wayarsa suna chat da Ramish yana jin ya lafiyar Auta a yanzu. Ta
wutsiyar ido ya kalleta, tin ɗazun tinaninta ne a ransa, yana tina yadda zata kare
da azumi gobe, anya zata iya yi kuwa? Bata fa shiri da yunwa, ga shi gaskiya girma
ya fara zuwa, kirjinta sun cicciko, period kawai ya rage ta fara yi, dole ma ai ta
yi azumi, sai dai za'a sha fama kam, bala'i tab zai fi kowa fama da ita, dan daga
shi sai momma take jin maganarsu. Tin ɗazun yake ta tinanin mafita a kan azumin.

Ajiye masu abincin ta yi a saman carpet ta nufo shi, a gefen bed ɗin ta zauna tana
tura baki.
"Bana ce ki rinƙa yin sallama ba? Kuma bana ce idan kin zo ki rinƙa gaishe ni
ba?". Ya gefa mata tambayar yana cigaba da katsa wayansa.

Unexpected ta faɗo jikinsa tare da sanya mashi kuka tana faɗin. "Yah Omerish wai
mama Haulat ta ce gobe za'a fara azumi babu ni babu cin abinci sai dare?". Tana
kukan kuma dan iyashege tana tura hannunta a cikin rigarsa ta kasa, so take ta taɓa
cibiyarsa, wai ita da yake yi wa faɗa a kan saka ɗankwali da yin sallama, shi ne ta
kwanta a jikinsa take yi mashi wannan sakalci da iyashegen, Pretty sai shirin Allah
wlh, dama abin da take ta yi wa kuncin rai kenan, shi ne taki faɗawa momma ta zo
tana juyeshi a nan, dan tasan ya fi kowa biye mata a gidan!

My people's me kuke tinani idan Sareena ta zubawa Pretty acid a fuska? Dan dai kun
san su Omaid zasu bata goyan baya, uhm




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

58


Tsaye yake cikin arabs jallabiya milk color, ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa
yana aikin kai komo a cikin bedroom ɗinsa, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana
cikin tsananin tashin hankali gane da ciwo, tamkar ba King ɗinmu ba, ya rame
matuƙa, ya yi wani irin haske sosai, sai idanu kwala kwala farare tas zaka gani,
gabaɗaya a dabaybaye yake da damuwa.

Tsayawa ya yi a gaban windown room ɗinsa dake fuskantar harabar family part,
kalaman Smart ne kawai suke yi mashi yawo a ransa, ta wani ɓangare na zuciyarsa
kuma rashin Zunaira, ta ko'ina ba sauki, babban abin da ya fi ɗaga mashi hankali
shi ne kamar yadda Smart ya ce sai ya faɗa mashi uwar Ramish, to abin tashin
hankalin a nan ne shi ne allura ce take shirin tono jibgegiyar garma mai girman
gaske, domin kuwa ba faɗar uwar Ramish ɗin ne matsala ba, matslar shi ne ya aka yi
ya baiwa mama Ramish a matsayin ɗanta ita kuma bata san ba nata bane? Wannan shi ne
ainahin tashin hankali da yake ciki, dan tono yadda aka yi ya bata Ramish babban
bala'i ne ga gabaɗaya kingdom ɗin wanda sai ta shafi kowa da kowa, idan Smart ɗin
ma bai yi hankali ba zata zama sanadiyar mutuwarsa ko na mommarsa or guyson, dama
shi guyson a kan hanya yake, taimakon Allah yasa bai mutu ba yake fama da ciwon
ciki mai zuwa dik shekara kenan, wannan ba karamar bala'i bace, gara ma sanin me
yake a tsakaninsa da matar commander a kan wancan bala'i na Ramish, siririn da a ka
rufe tsawon shekaru 30 amma Smart ko daga ina ya jiyo sirrin har ya bankaɗo shi?.
WANNAN SMART SAI DAI SHIRIN ALLAH, YA TAYARWA DA DATTIJO HANKALI YA BARSA CIKIN
CIWO DA AZABA!!

Haƙiƙa King ya shiga tashin hankalin da bai san ranar fita ba. Batu a kan maman
Hoorain wato matar commander wannan tabbas suna da alaƙa, kai tin ba yau ba, tin
kafin King ya yi aure suke tare, bari in maku tarihin, sun sha soyayya nakin
karawa, saboda matar commander uwarta baturiya ce ubanta balarabe, shiyasa ta fita
daban a masarautar, sai dai kuma tana matsayin baiwarsu, King Zuhair ya kamu da
sonta sosai, yadda kuka ga Auta ta so Hoorain, haka suma suka so juna, sai dai
kash, King Abdul Malik ya ce ko mutuwa King yake yi ba zai taɓa aurar baiwa ba, ya
haramta masu mallakan juna, wannan dalilin yasa suka kasance a tare a bayan fage,
suka rinƙa sheke ayarsu har King Abdul Malik ya fitar mashi da mata, wato da Mummyn
Chuchu da Mamansu Aneesa, bai yi gardama dik da cewa baya sonsu ba, dan shi ai yana
tare da wacce yake so a ɓoye.

Aka aura mashi su, ya cigaba da kasancewa da matar commander har ita ma ta yi aure,
tsantsar soyayyar da suke yi wa junansu yasa suka gagara rabuwa dik da suka yi
aure, haka suka cigaba da rayuwa har shigowar momma rayuwarsa a wani zuwa Dubai da
ya yi, already Mummyn Chuchu and maman Aneesa ba zaɓinsa bane, shiyasa kuka ga ya
fin san momma sama da su, dan ita ce zaɓinsa ta biyu bayan maman Hoorain. Maman
Hoorain da suka yi aure ba'a cikin kingdom of power suke zaune da commander ba,
amma dik da haka suna da wajen da suka ware wanda suke haɗuwa ita da King dan
holewarsu.

A takaice lokacin da ya auri momma ta fahimci yana daga cikin sarakuna masu tarewa
da kuyangunsu, shiyasa ta yi ƙoƙarin canzasa, kuma ta yi nasara, dan ta canzasa a
lokacin da bai taɓa zata ba, a lokacin momma har ta haifi Jaish, lokacin ita kuma
matar commander ta haifi Hoorain bai wuci 2 years ba a duniya, a ranar da za'a
haifi Hoorain anyi gagarumin yakin da a ranar ne aka kashe King Abdul Malik,
lokacin da maman Hoorain da maman Aneesa suna naƙuda, ranar anyi tashin hankali
sosai. Bayan komai ya lafa aka yi jana'izar King Abdul Malik kamar yadda yake a
dokar sarauta, daga nan King Zuhair ya karɓi karagar mulki, momma ta yi nasarar
raba shi da matar commander, tin daga lokacin kuma ya tuba ya zama adalin sarki mai
mulki tsakani da Allah, sai dai matsalar da aka sake samu a ɗan gaba kaɗan kafin
matar commander ta ɓata da kuma bayan ta ɓata, wannan matsala lokacin da zaku san
shi bai ba, dan wannan matsala shi ne yake da alaƙa da Ramish da kuma yaudarar mama
da King ya yi, WANNAN SHI NE GASKIYAR ABIN DA YAKE A TSAKANIN KING AND MATAR
COMMANDER ZAFAR, TO YANZU A TSAKANIN KING DA COMMANDER WANENE AINAHIN UBAN MARIGAYI
HOORAIN? KAM BALA'IN CAN!! UHM WANNAN CAKWAKIYA SAI SMART YA WARWARE MANA! DAN KO
SHI KANSA KING ƊIN BAN JIN YANA DA TABBACIN HOORAIN ƊANSA NE KO NA COMMANDER, ITA
KANTA MATAR COMMANDER ƊIN BANA JIN TASAN AINAHIN UBANSA, WANNAN SHI NE KWAMACALA.
KU DAI MU CIGABA DA ZUWA, AI KWAMACALA MA TANA CAN GABA!!

Hege Smart ya jefa King da kansa a cikin zulumi da tashin hankali shi kuwa yana can
yana more rayuwarsa da Pretty, sai nishaɗi suke yi, ga King ya ƙasa zaune ya kasa
tsaye, wlh tin da kuka ga King ya girgiza a kan batun Ramish, ba shakka ba karamar
ɓarna bace zata bayyana, babban bala'i Smart yake son jijjigo mana wanda gara
kowani irin cakwakiyar a littafin nan a kan wannan, tabbas King Zuhair and King
Abdul Malik sun bar baya da kura, abin sai shiru, sai lokaci ya nuna mana kawai!!.
ZAN BAKU MAMAKI FA, DAMA SUNANANE QUEEN OF SURPRISE, KU YI FATAN BAYYANAR KAMRAN
LAFIYA KU DAI!!

----------------------------------------------🔥🔥🔥

"Azumi fa akwai lada, idan kika yi zaki samu lada sosai, kuma waye ya ce maki ana
wahala a azumi?". Ya yi tambayar yana ajiye wayarsa a gefe, sannan yasa hannu ya
rungumota da kyau. Kai ta shiga

Please Login or Register in order to submit comment