Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 27 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bismilla babu ita babu rabarinta, ta ɓace a wajen.

Sannan ya yi amfani da magic ɗinsa wajen dakatar da bugawar numfashin Ronnie, ya yi
kamar ya sumar da shi, dan in ba haka ya yi ba yau zai iya kashe Ronnie dan ɓacin
rai, saboda yasan ba zai bar shi ya kwana lafiya ba, a kanta zai hana kowa barci ya
yi ta kuka, so gara ya yi mashi haka zuwa da safe ya tashesa, kafin nan kuma zai yi
ƙoƙarin ganin ya shafe mashi tinaninta a babin rayuwarsa gabaɗaya, e lallai akwai
aiki babba.

Team Ronnie ina kuke, me kuke tinanin zai faru? Za'a shafe kwakwalwar Ronnie,
damuwata ɗaya shi ne ya batun musuluntar da ya yi? Kenan zai koma krista?😥

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, wannan yafi komai ɗaga mun hankali, bana san ya
koma krista wlh............😥

To bari dai mu leƙa Dubai kila kafin mu dawo abubuwa zasu ɗan yi sassauci.

••••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••🔥

Zaune Sharifat take a bakin bed ɗin dake cikin A&E room ɗinsu, ta buga uban tagumi
tare da zubawa Leesharh dake kwnace a saman bed ɗin idanu tana kallonta, yau tsawon
kwana uku kenan da Ramish yasa hannu aka saketa saboda ba wayarta bace, Bilal ne ya
ɗaukota ya dawo da ita, Dr Raj yana kula da ita, shi ne Dr ɗinta, shi ma sai da
Bilal ya sanya baki ne ya yarda yake dubata, da farko ya ce shi ba zai iya duba
lafiyar wadda ba'a san asalinta ba, infact shi baya ma san ganinta, sai da Bilal ya
umarcesa a kan hakan sannan ne ya yarda ba dan ya so ba!.

Tsawon wannan kwanaki ukun Leesharh bata san in da kanta yake ba, da farko ma Dr
Raj ya ce ta mutu, sai daga baya suka iya jiyo sautin bugawar zuciyarta can ƙasa
ƙasa kamar yana san dakatawa ya dai'na aiki.

Allah sarki ta ji horon manyan kai, sai da ta zaɓi mutuwa a kan hakan, a gaskiya
Ramish mugu ne bashi da imani wlh, dama ga shi kullum yana maganar kada daddynsa ya
yarda da kowa, kai gaskiya guy ɗin nan Ramish bashi da daɗi, ya azabtar da ita
over.

Dikkan jikinta bandeji, an mammanneta ta ko'ina kamar wata pacin tayar mota,
hannunta na dama ma ya samu karaya, wai a haka ma fa dan Bilal yana dakatar da
Ramish ɗin, da ya jima da kasheta.

Sai kuka shafiat take yi hawaye bibbiyu, kwanaki uku Leesharhnta taki motsawa, tin
tana sa rai har ta fara karaya, jikinta dik ya mutu ta fara tinanin ko dai mutuwa
da gaske Leesharh ta yi basu sani ba?.

Yanzu kun gano daga in da Omaid and Obaid suka gado mugunta da iya horor da mutane
ko?

Shi kansa Abu Abdussalam sai da ya razana a lokacin da Bilal ya dawo da ita, sosai
ya yi wa Ramish faɗa a kan yi wa mutum ɗan adam irin wannan horo babu daɗi, ya ce
ko namiji bai yarda ya sake hora shi kamar haka ba ballanta mace wadda ita sam babu
gurbin wahalarwa a jikinta, ya rinƙa sassauta zuciyarsa gudun yin danasani gaba.

A ɗan fusace ya ce da Abbie. "Abbie danasani fa ka ce?!". "Kwarai danasani My son".

Kara ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. "Babu wata danasanin da zan yi a rayuwata, dan
haka ni ka dai'na faɗa mun hakan".

Da yake Abbie yasan halin kayansa sai ya koma sigar rarrashi. "Haka ne son, bana
fatar ka yi danasanin nima, amma please ka rinƙa sassautawa, kaga macece fa ita,
amma haka ka horata kamar ka riki kartin maza ƴan ta'adda".

Kansa a ƙasa ya jinjina tare da cewa. "Amma menene banbancin wanda ya so tasan bomb
a wannan hall ɗin da ƴan ta'adda?".

Shiru Abbie ya yi, dan babu banbanci, gara ma ƴan ta'adda da sauki a kan wanda zai
tashi bomb cikin wannan taro da sama da mutum 1000 zasu rasa rayukansu, har da
makotan hall ɗin dik zasu iya kamawa da wuta su haɗa da mutanen dake ciki.

Miƙewa tsaye ya yi ganin Abbie ya rasa bakin magana. "Good night Abbie". Ya
faɗa ba tare da jiran abin da zai ce ba yasa kai ya nufi waje. Da kallo Abu
Abdussalam ya bisa har ya fice, ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaga hannu ya furta
zafafan addu'oi kamar haka.
"Ya Allah ka shirya mun my son ɗina, Allah ka sassauta mashi wannan zafin zuciya
tasa, Allah ka kara kare mun shi daga dik wata sharri, daga karshe Allah ƙasa ya
kara zamtowa mai son na gasken gaske wato Allah ka haɗa zuƙansu shi da Sharifat na
yi masu aure".

Shi kuwa Ramish, bedroom ɗinsa ya wuce, white jallabiyar jikinsa ya cire, ya rage
daga shi sai sexy short and singlet............ My people's wai meyasa Yah Ramish
yake san sexy kaya kamar wani mai aure ne?...🤔

Short ɗin ta kama shi sosai, dai'dai irin........ Na dai yi shiru kada ace na cika
saka ido.

Toilet ya nufa dan ya yi wanka ya yi shirin yin barci. Bilal kuwa baya nan ya fita.

After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi
masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsadaya shafa. Yana tsaka da gyara
gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face ɗinta t............


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




E..…...............17


After some minutes ya fito sanye da sexy bathrobe milk color a jikinsa, ya yi
masifar kyau sosai. Mayukansa masu kyau da tsada ya shafa. Yana tsaka da gyara
gashinsa ta cikin mirror ya yi arba da face ɗinta tana tsaye a bakin kofar shigowa,
ta kasa gaba ta shigo ciki ta kuma kasa yin baya ta fita waje.

Kamar bai ganta ba haka ya yi, ya cigaba da abin da yake yi har ya kammala, bakin
bed ya wuce ya zauna, cike da class ya ɗauko wayarsa, number da yake san kira ya
shigar, babu suna number, hakan na nufin ba'ayi saving ɗinta ba.

Kira ya danna tare da kara wayar a kunnensa, bugu ɗaya aka ɗaga call ɗin cikin
sauri. Daga ɗayan side ɗin Sharifat ta ce. "Hello wanenen?".

Wannan wayar tasa Bilal, Dr Raj, Rizwan sune kawai suke da phone number, shiyasa
Sharifat bata ma san wanene bane, wayarta kuma ba irin nasu bane da in sun kira zai
baka suna da location ɗin in da mai kira ya kiraka haɗe da gajeran bayanai a kan
mai kiran.

Shiru ya yi kamar na minti ɗaya. Yana jinta ta kara faɗin wanene? Bai yi kamar
zai amsa ba, ta sake tambaya na uku, nan ma shiru. Ranta ne ya ɓaci, dama ga
damuwar rashin lafiyar Leesharh, sai abin ya kara yi mata yawa, dan haka cikin faɗa
ta ce. "Wannan wani irin iskanci ne a kira mutum kuma ba za'ayi magana ba? To koma
wanenen kada a kara kirana".

Sai da ta kai aya a zazzaga masifar tata zata katse kiran ne ta tsinkayo sexy voice
ɗinsa cikin nitsuwa ya ce. "Ki kawo mun cappuccino yanzu".

Ai tana daga zaune a bakin bed ɗin Leesharh bata san time da ta miƙe tsaye haɗe da
ciro wayar daga kunnenta ba, bata taɓa zaton Yah Ramish bane. Innalilahi wa inna
ilahir rajiun shi word ɗin da ta rinƙa maimaitawa babu kakkautawa, gabanta sai
faɗuwa yake yi, ƙoƙarin tinano abubuwan da ta faɗa cikin masifar da ta zazzaga ta
fara yi ko Allah zai sa ta tina komai ta ji ta yi zagi a ciki ko bata yi ba, yau ta
shiga uku shi ne abin da zuciyarta yake faɗe.

Shi kuwa yana gama faɗar abin da ya yi niya ya katse kiran, a hankali ya maido
da kallonsa a kan Ummie dake tsayen mashi a bakin kofa, kamar dai akwai muhimmin
abin da ya kawota ɗakinsa, dan bata zuwa part ɗinsu sai dole.

"Zan iya sanin abin da ya kawoki nan?". Ya jefa mata tambayar tare da kawar da
kallansa daga kanta.

"Da gaske ne wai ka saki Leesharh? And da gaske ne wai ba ita ta yi maka laifi
ba?". Shi ne tambayar da Ummie ta jefa mashi, daga ganin face ɗinta kasan bata ji
daɗin dawowar Leesharh ba, ta haɗe rai kamar hadari, ranta a ɓace matiƙa. Ta tsani
Leesharh, bata so ace sun saketa ba, ta so ne su kasheta, amma sai Sharifat ta ce
mata an dawo da ita, ta tambayi Dr Raj meyasa aka dawo da ita ya ce mata ta tambayi
Yah Ramish, tana shakkar tinkararsa saboda baya ba da fuska, hakan yasa ta tambayi
Bilal, shi ma ya ce ta samu Yah Ramish a wajensa zata samu amsa, tin jiya take san
tamnayarsa, amma tana tsoron tinkararsa, da kyar yau ma ta samu kwarin gwiwar zuwa
garesa da abin ya dameta, wannan ma sai da wannan friend ɗinta mai kibar nan ta
kara mata kwarin gwiwar a kan ta je ta tambaya kada ta damu.

Idan baku manta ba a baya ita da kawar tata sun haɗa baki zasu kashe Leesharh ai,
to shi ne da Ramish ya kamata sai suka ce ya hutasshesu, sai murna suke yi, rana
tsaka kawai murna ta koma ciki, gaza jurar hakan suka yi har sai da suka zo dan
tabbatarwa.

"Abin da kika zo tambaya kenan?". Ya jefa mata tambaua.
Wlh Ramish ya tsani Ummie kamar me, babu abin da ta yi mashi kuma, haka
kawai bai yarda da ita ba wai.

"Shi ne abin da ya kawoni". Ta bashi amsa.............. Gyarawa ya yi ya kwanta
abinsa, ya janyo bargo har zuwa saman jikinsa. "Zaki iya tafiya dan bani da alaƙa
da wannan magana da kika zo mun da ita". Shi ne amsar da ya bata, yana gama maganar
kuma ya jawo remote ya kashe wutar ɗakin tare da kunna lamps, sannan ya kara gudun
Ac.

Tsaye ta yi tana kallansa, ta ƙasa tafiya. A hankali ya lumshe idanunsa kamar mai
barci, zubawa face ɗinsa idanu ta yi tana kallo, nan take shaiɗan bakin azzalumi ya
fara ƙawata mata kyansa da surarsa, take a wajen ta ji ta kamu da muguwar
sha'awarsa. Tashin hankali!!.

Zuciyarta ne ya fara azalzalarta, kun san mutumin fa ba dai kyau ba, jinin
Zuhair ai ba wasa ba, ƙasa kawar da kallanta a kansa ta yi, ji take yi kamar ta
tafi ta faɗa jikinsa, shaiɗan sai kara rura wutar wannan bakin al'amari yake yi a
ranta, ta yi matuƙar kwaɗaituwa da surarsa a wannan dare, dama ita ma idan ba
iskanci ba me zai kawota ɗakin santalelen saurayi a cikin wannan dare? Bayan kuma
shaiɗan yana nan a tsakani yana yawo tsakanin karya da gaskiya tsinanne.

Wlh ta ƙasa juyawa ta bar ɗakin, infact ta ƙasa iya dai'na kallansa, ga shi lamps
suna haska fuskarsa da kyau, dan ta bakin bed ya kwanta, cikin dare ga fara
kyakkyawar fuska haske na haskata ai kyau iya kyau, ni kuma na ce dik jarabarki
wannan handsome guy na King ya fi karfinki In Sha Allah.

Sallamar da aka yi daga bayanta ne yasa ta yi wani irin razana tare da zare
kallanta daga kan Ramish, jikinta har wani tsuma yake yi da sha'awarsa. Wajen da
take tsaye a kwai ɗan duhu hakan yasa Sharifat bata gane wacece ne a wajen ba, ta
dai ga mutum, sai ta yi tinanin ko Yah Bilal ne, dan haka sai ta ce. "Yah Bilal
good evening".

Shiru Ummie ta ƙasa iya amsa mata, sai ma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin tana
haɗiyar yawun kyan Ramish.

Sam Sharifat bata kawo komai a ranta ba, bata san wacece bace, kawai ta wuce ciki
dan ta kai mashi cappuccinon da ya buƙata.

A gaban bed ta durkushe gwiwowinta, kamar zata saka mashi kuka, murya a raunace
ta ce. "Good evening Yah Ramish".

Sam bai amsa mata ba, bai ma motsa ba kamar ya yi barci, ita kuma tasan sarai bai
yi barci ba, ga zara zaran eyelashes ɗinsa suna ɗan motsawa alamar bai yi barci ba
amsawa ce kawai ba zai yi ba, dan haka sai ta ɗaura da cewa. "Yah Ramish dan Allah
ka yi hakuri ka ji? Wlh ban san kai bane ka kirani a waya shiyasa na yi zafafan
furuci".

Nan ma bai motsa ba, kamar babu shi a ɗakin. Miƙewa ta yi ta ɗaura mashi
cappuccinon a saman table dake tsakanin sofar a cikin ɗakin, sannan ta nufi waje,
dan tasan ko kwana zata yi ba zai amsa mata ba sai time da ya yi niya, gara mata ma
ta tafi zai fi mata.

Tana tafiya tana waigosa cike da tsantsar kaunarsa, sansa ne yake kara ratsa
zuciyarta, tana san cigaba da kallansa amma babu dama, dan haka ta wuce waje da
sauri idanunta suna ƙoƙarin cikowa da kwallah.

Tana fitowa parlon ta ci karo da Yah Rizwan ya fito daga bedroom ɗinsa rike da cup
a hannunsa, yana sanye da white arabs jallabiya, ya yi wani irin rama sosai, da
alama daga jinya ya tashi, Allah sarki yana jinyar san Chuchu shi ma kuma Aneesa
tana jinyar sansa.

"Lil daga ina kike a cikin wannan daren?". Cewar Rizwan.

Dakatawa ta yi da nufar waje, da sauri ta juyo garesa, bata yi zaton ya dawo gidan
ba, dan bata gansa ba, rabonta da shi tin a kingdom of power ranar bikinsa, dik
jinyar da ya sha bata sani ba, ba komai yasa hakan ba kuma face in dai ba wajen
Ramish ba bata zuwa wajen kowannensu a part ɗin, ɗan gara ma shi Rizwan ɗin da yana
sakar mata fuska wani lokaci idan ta rasa abokin hira tana zuwa bedroom ɗinsa su
zauna.

"Wajen Yah Ramish na je kai mashi cappuccinon". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.
Gyara tsayuwarsa da kyau Rizwan ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Yah Ramish ɗin ya
yi maki wani abin ne naga kamar kina kuka?".

Kai ta girgiza alamar a'a tana ƙoƙarin shanye hawayen dake san zubo mata. "Mayasaki
kuka to?".
"Babu komai Yah Rizwan...........". Tana kai karshen maganar ta rushe da kukan
da bata san daga ina ya fito ba, da karfi kukan ya kubce mata.

Da mamaki Rizwan yake binta da kallo, Sharifat kenan sarkin saurin kuka ga raunin
zuciya. Da yaga da gaske take kukan sai ya matsa kusa da ita, a saman table na
wajen ya ajiye cup ɗin hannunsa, sannan ya janyota jikinsa ya rungumeta.

Ita ma rungunesa ta yi tana kara rushewa da kuka. Baya cikin yanayi mai daɗi sam,
amma haka ya daure ya shiga rarrashinta yana bata baki.

A haka Dr Raj ya zo ya wucesu ya shiga ɗakin Yah Bilal dan ya sanar da shi
condition da Leesharh take ciki a yanzu, dama tin safe Bilal ɗin yake jiran wannan
amsa daga garesa.

"Ki yi shiru kinji our lil, kinga fa ke kaɗai ce sistermu a cikin gidan nan,
bai kamata ace wani abin zai sanya manake kwallah ba".

Kun san Yah Rizwan Allah ya yi mashi baiwar iya kalamai masu kwantar da hankali,
dan haka koma yaya mutum ya kai ga ɗaukar zafi ko ɓacin rai cikin ƴan mintuna zai
rarrashesa.

Haka ita ma Sharifat cikin ƙanƙanin lokaci ya rarrasheta har sai da ta yi shiru,
sannan ya sanyata murmushi kafin ya raba jikinsa da nata, ya riki hannunta suka
nufi bedroom ɗinta.

Sai da ya tabbatar ta kwanta tana farinciki sannan ya juya ya fito, kai tsaye ya
koma bedroom ɗinsa shi ma.

A ɓangaren Ramish kuwa, sai da ya gama shan kamshinsa, ya gama jan ajinsa sannan ya
tashi ya ɗauki cappuccinonsa ya fara sha cike da class. Kaɗan ya sha ya ajiye
sauran, ya miƙe ya nufi prayer mad set. Dadduma ya ɗauko, already ya ɗauro
alwalarsa tin ɗazun, salloli ya zo ya fara gabatarwa yana neman Allah da ya dafa
mashi ya saukaka mashi binciken nan da suke yi a kan masu nikaf, nan da next month
akwai wani taro da zasu sake yi, baya fatan har a kai ranar wannan taron bai kama
masu kawo mashi hari ba, idan bai yi hakan ba za'a iya samu gagarumin matsala su
sake kai mashi hari cikin taron kamar yadda suka yi a farko, za'a iya rasa rayuka,
waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya mutuwa, idan hakan ta faru ranza zai
kuntata sosai, saboda dalilinsa ne mutane zasu mutu.

So sai addu'a yake yi da Allah ya taimakesa kafin next month. Dai'dai lokacin da
yake kwarara wannan addu'a a dai'dai lokacin Leesharh ra farka bayan kwanaki uku
tana sume kenan.

Dr Raj ya yi namijin ƙoƙari wajen kula da lafiyarta, ya nuna cikakkiyar kwarewa a
ɓangaren aikinsa wanda hakan yasa ta farka a cikin hayyacinta. Hannunta da ya samu
matsala ma ya sha ɗauri kuma ya sha kula sosai, haƙiƙa Bilal ya yi kokarin a wannan
ɓangaren kam dik da bamu san menene ainahin abin da yake a cikin zuciyarsa ba.
Ta yi babban sa'a kafin ta farka daga doguwar sumar nan dik wasu raɗaɗin ciwo dake
jikinta sun kau, dan haka bata ji wani azaba da ta farka ba, sai da ta zo motsawa
dan ta miƙe ne gaɓɓan jikinta suka ce ina ai basu san wannan ba, dole ta koma ta yi
lamo a gadan tana kallan saman celling tana ƙoƙarin fahimtar a wace duniya take ma
tukun nan, dan ita dai tasan ta baro kanta a hannun Yah Ramish ya danki gashin
kanta yana bugata da jikin bangon ɗakin da suke horas da masu laifi, tin wani buga
mata kai da bango da karfi da ya yi har ta fara ganin dishi dishi, daga nan bata
sake sanin a wani hali take a ciki ba.

Sai a yau da taga alamar kamar a gidan Abu Abdussalam take, amma ba halin tashi ta
duba, dan haka sai ta mayar da idanunta da suke yi mata zafi ya lumshesu tana furta
istigifari a cikin ranta.

•••••••••••KINGDOM OF POWER•••••••••••🔥

Baki ɗauke da sallama Momma ta shiga master room ɗin dearlyn love ɗinta, baya a
cikin bedroom ɗin, zubar ruwa da ta jiyo a toilet yasa ta fahimci yana ciki, dan
haka sai ta kwantar da babyn Khadija a saman bed ɗinsa, ta ɗauki wayarsa domin ta
kira uncle Jahiz.

11:00 a lokacin, dare ya yi, sai ta mayar da wayar ta ajiye a zuwan sai da safe
kawai su haɗu. Tana ajiyewa King yana fitowa ɗaure da towel a waist ɗinsa.

Da sauri ta miƙe ta nufesa, ƙayataccen murmushi ya sakar mata, da alama ya yi
farincikin dawowarta sosai. Tana zuwa ta karɓi ƙaramar towel dake hannunsa ta hau
taya shi goge jiki tana yi mashi barka da dare.

"Kin dawo lafiya?". Ya faɗa fuska ba yabo ba fallasa, yana ta kallanta cike da
tsananin kauna mai zafi. "Lafiya lou na dawo har ma da tsaraba". Ita ma tana
magana tana kallansa cike da kauna.

Kara sakar mata murmushi ya yi kafin ya ɗaura hannayensa a saman lallausan
kumatunta. "Tsarabar me kika dawo mun da shi". Ya yi maganar ba tare da ya lura da
babyn dake kwance a gadansa ba.

"Kamata ya yi ka tambayi ya na sami mutanen ya kuma na barosu kafin ka tambayi
tsarabar ko?". Ta kai karshen maganar tare da manna mashi towel ɗin hannunta a face
ɗinsa tana ɗan jan dogon hancinsa cikin salo na soyayya.

"To ni Rahilarh menene ya dameni da su da zan tambayi ya suke?"....
Ɗan ɗaure fuska kaɗan ta yi. "Kai ko kake da damuwa da su".

"Kamar yaya kenan?". Da ɗan mamaki ya yi tambayar.
"E kai kake da damuwa da su tin da sun baka suruka sun kuma bawa ɗanka mata".

"What?". Ya faɗa da ɗan ɗaga murya. Jinjina mashi kai ta yi alamar kwarai kuwa,
sannan ta ɗaura da cewa. "Muje in saka maka kaya sai ka zo mu yi magana........."

A hanzarce ya katseta da cewa. "A'a Rahilarh, ki faɗa mun wasa kike mun kawai a
yanzu ba sai na je ko'ina ba".

Ganin da gaske yake yi yasa ta amsa mashi da e wasa ne, dan tasan halinsa, dama
tasan zasu kai ruwa rana kafin ya aminta da Mahnoor idan ya aminta ɗin ma kenan, ba
zai yarda ƴaƴansa su auri wasu ba idan ba larabawa jinin sarauta ba, shi ma yana da
kabilanci sosai kamar dai Akka, basa san wasu bare a cikinsu, a hakan ma dai ɗan
gara shi a kan su Akka, shi kabilanci nasa a kan ƴaƴansa ne kawai!.

Har wani ajiyar zuciya ya sauke jin ta ambaci wasa take yi mashi, hannunta ya ja
suka wuce dressing room dan ta taya shi shiryawa, suna tafiya yana yi mata gargaɗin
a kan kada ta sake yi mashi irin wannan wasa baya so, shi ƴaƴansa ba zasu yi aure
daga waje ba, a cikin gida zasu yi aure kuma ƴaƴan sarakuna kamarsa zasu aura.

Da okey kawai ta bisa har suka shiga cikin room ɗin. Soyayya mai tsabta suka shiga
zubawa kafin ta fito mashi da kayan barci, kwana biyun nan ya yi kewarta saboda
damuwowi da suke a ciki, daga wannan sai wannan, sai yau ne ya damu damar samunta
tana farinciki, ba komai ya sakata a farinciki ba kuma face auren Jaish, ta ji
daɗin wannan lamari kuma zuciyarta ta kaunaci Mahnoor fiye da tinanin mai tinani,
dik wasu qualities da ake san mace ta haɗa Mahnoor ta haɗa shi, tana da tabbacin
idan King ya ganta shi ma ba zai yi ja in ja da zancen ba, wuyarta ya yarda ta
ganta ɗin ne kawai.

Sun ɗauki a kallah 30 mins a cikin ɗakin suna zuba love ɗinsu suna soyewa kafin ya
sanya sleeping dress ɗinsa su fito rungume da juna.

A bakin bed suka zauna, sai a lokacin ya lura da babyn dake kwance a saman bed ɗin,
cike da mamaki ya jefa mata tambayar babyn waye? Daga ina ta ɗauko shi?.

Gyara zama ta yi suna fuskantar juna, cikin nitsuwa ta fara zayyane mashi komai da
komai har da zuwanta gidan bappa da abin da ya faru zuwa ga kawo mata baby da uncle
Jahiz ya yi.

Girgiza kai King ya fara yi kafin ya ce. "Hakan ba zai taɓa yiwu ba! Jaish bai kai
yin aure yanzu ba, kuma koda ya kai ɗaya daga cikin ƴaƴan uncle Rahab nike san ya
aura, babu ɗana da zai auro mun mace daga waje, dik cikin gida zasu koma su yi
aure, dan haka wannan aure ban aminta da shi ba, yazama dole a kwancesa.

Shiru momma ta yi tana sauraransa har ya gama faɗarsa, sannan a nitse ta ce. "Dik
hukuncin da ka yanke dai'dai ne bana da ja a kan hakan, dan nasan ba zaka taɓa san
abin da zai cutar da ƴaƴanka ba, dan gobensu ya yi kyau zaka zaɓa masu mata masu
inganci, amma ina san ka mun wata alfarma"......... Ta kai karshen maganar idanunta
a kan face ɗinsa.

A taƙaice ya ce. "Wace alfarma kenan". Fuska a ɗaure ya yi maganar.

"Ina san ka bani sati guda, ka yi shiru a kan maganar har na tsawon sati
guda, sannan sai na gabatar maka da matar tasa, idan har bata da qualities da kake
buƙata a tattare da matan da kake san ƴaƴanka su mallaka to zan aminta da ka
warware auren a mayar da ita kasarsu!".

Momma mace mai hikima da dabara, ko me zata kulla masu ta buƙaci sati guda kuma? Mu
je dai zuwa.

"Rahilarh bafa zan yarda da batun auren nan ba, ni bana ma san ganinta, ban buƙatar
hakan kawai a mayar da ita kasarsu a raba wannan aure, dan bana da buƙata".

Ganin da gaske yake yi babu wasa kuma babu alamar zai yarda da Mahnoor gaskiya, sai
ta fito mashi ta wata hanyar daban.

Matsawa ta yi kusa da shi, a saman jikinsa ta kwanta, cikin salon kauna ta fara
jansa da wasa, sam bata nuna ta damu da kalamansa ba, dik da ta damu ɗin a cikin
ranta, tana kaunar Mahnoor tin daga kallon farko, ba zata taɓa bari a raba wannan
aure ba.

King sai wani ɓata rai yake yi yana wani ɗaure fuska, cigaba da yi mashi wasanni
momma ta yi tana ɓalle botiran rigan jikinsa cikin salo mai jan hankali. Ai bai san
time da ya saki face ɗinsa ya fara biye mata ba, dan dama ya kwana biyu yana
dakonta kawai dannewa yake yi, ta ji matuƙar daɗin hakan, dama buƙatarta kenan, dan
haka sai ta kara zagewa sosai wajen ganin tasa ya shiga wani irin yanayi kafin ta
zuba kalaman da suke cikin ranta.

Sai da suka yi nisa King ya afka duniyar sama jannati har da yi mata rumfa da
faffaɗar kirjinsa yana zuba mata kalamai, yana sarrafata cikin kwarewa. Sai da ta
fahimci an kai point ɗin da ba zai iya yi mata gardama ba, a wannan gaɓa komai ta
ce zai amsa ne kawai, sai ta ce. "Ban tari numfashinka ba a ɗazun, kuma bana ja da
hukuncinka a garemu gabaɗaya, amma dai

Please Login or Register in order to submit comment