Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 81 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi sabo sosai da sosai, sai dai dik zaman da suke yi su
uku a cikin gidan da iya Smart kawai Pretty take magana, bata taɓa cewa su Bobo ko
sannu ba, har ranar da zasu tafi kingdom of power sannu bai haɗata da su Bobo ba,
kuma a tare suke zaune, nan suke kwana, amma yarinyar nan tamkar bata san da su a
gidan ba....... Dole in ɗan taƙaita wasu gurare domin manyan gurare da suka fi
mahimmanci suna gaba, so dan haka mu je zuwa!!. Mu je ga kingdom of power.
Su uku suka shirya tafiya kingdom of power, suka bar su Bobo su kaɗai a gida cike
da kewarsu, Auta baki har kunne zata je ta ga Hoorain, ita dai Pretty koma ina zasu
je bata da matsala, bama ta san ina suka nufa ba, kawai tana rike da hannun Auta
har Bobo and Zash suka kaisu airport, har suka shiga cikin jirgi suna manne da
juna!!.


(STOP MY PEOPLE'S!! Na ce stop!!. Yaseen irin ƙwaƙwalwar mutane ne da ni! Wlh irin
ƙwaƙwalwarku nike da shi!! Ta ya za'ayi ku rinƙa ce mun kamar ba ƙwaƙwalwar mutane
irin naku nike da shi ba wai?! To irin naku ce da ni, kawai dai abin da na sani shi
ne kowa da irin girman ƙwaƙwalwarsa, kun gane ai?. Masu mamakin yadda na haɗe
masarautu biyar dikka nike story a kansu, kuma kowanne da cakwakiyar, dik yawan
mutanen ciki bana mance ko mutum ɗaya ko na ɗauki sunan wanna na bama wannan kuma
stop na ce yauwa kuna ganewa ko? Tabbas ku zaku ga akwai wahala, amma ni a wajena
Allah ba wani abin bane, dik suna a cikin kwakwalwata ne shiyasa bana mantawa, kuma
batu na gaskiya ni ina rubutu da zuciya da ƙwaƙwalwata ne shiyasa, idan na sanyawa
zuciyata zan yi abu to is very very hardly na kasa yi! To paka paka kwakwalwarmu
iri ɗaya ne kun ji? And amsar last tambaya shi ne e ni ina karanta Bibles sosai
gaskiya, tin ina primary school na fara karatunsa, a hannun wata friend ɗina mai
suna Rejoice James na fara karɓa na fara karantawa, kuma har yau idan na yi ra'ayi
ina karantawa, so karatun Bible ba haramun bane ba!. Daga ƙarshe kuma ita rubutu
baiwace sosai wlh da Allah yake bawa bayinsa, ina kuma miƙa ɗinbin godiyata a
garesa da ni'imar da ya yi mun, ina alfahari da ilimin addinin dana zamani ya bani,
ka zalika ina farinciki da ni'imar rubuce rubuce da ya yi mun, bugu da kari ina
godiya da basira game da falalar ƙwaƙwalwa mai girma da ya bani, alhamdulillah,
babu abin da zan iya biyan Allah da shi face godiya game da bauta bisa ƙaida, wlh
ina matuƙar alfahari da farincikin da dik wani littafin da na rubuta da kuma wanda
zan rubuta a gaba, dan dik littafan da na rubuta alhamdulillah na samu abin da
nikeso. Dan wlh dikkansu sun faɗakar, sun wa'azantar kai babu ma kamar wannan
RAWANIN ZALINCI, littafin nan ya fita daban sosai, tin ban kammala shi ba na samu
sakonni da dama a kan yadda mutane suka karu da shi matuƙa, gaskiya I really
appreciate that!! And really like you guy's. Much love...💘
🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥


Tin kafin jirginsu ya yi landing airport ta cika da shirga shirgan sabbin motocin
da King ya sayo dan wannan biki. Jaish ne ya jagoranta tawagar zuwa ɗaukarsu, Jawad
and uncle Jahiz dik suna tare, guyson ma ya je, amma su Omaid sun ki zuwa.

Jirginsu na sauka ba tare da ɓata lokaci ba suka fito, Auta na rike da hannun
Pretty, while shi kuma yana bayansu. Jaish da Jawad ne suka fara nufarsu, fuskar
Smart tamkar wanda aka aikowa da saƙon cewa wutar jahannama zai shiga, shi kansa
Jaish sai da ya ji gabansa ya faɗi ganin face ɗin yayan nasa. Sannu da zuwa suka
haɗe baki wajen yi mashi shi da Jawad, sai dai bai amsa ba, ko kallon in da suke
bai yi ba, burinsa kawai ya isa gida su yi ido biyu da King, yau sai ya sanar da
shi dalilinsa na hana Auta wanda take so, ya sanar da shi dalilinsa da yasa yake
san lalatawa yarinya rayuwarta....... KAI YA AKA YI SMART DA AKA ƁOYEWA BATUN AUREN
YA SAN DA ZA'AYI BIKIN? WA KUKE TUNANIN YA FAƊA MASHI?.

Kai tsaye mota ya nufa, da sauri suka rufa mashi baya, bai ce da su ko uppan ba ya
shiga mota, sai huci yake yi, ita kuma Auta da bata san me yake faruwa ba, sai
murna take yau zata sanya Hoorain a idanunta, bata sanar da shi zata dawo ba, wai
surprise take san yi mashi. Dik ta ƙosa su isa gida, ga shi dare ne, daɗin satar
hanya ta je wajensa kenan.

Jaish yana san tambayar yayan nasa me yake faruwa, amma yana fargabar amsar da
zai iya bashi, dan haka sai ya danne har suka isa gida. Motocinsu na dakatawa ya
juyo da nufin ya tambayesa, sai dai ina, kafin ya yunkura tuni Smart ya yi waje,
kafin ya fito ya bi bayansa ma har ya shiga elvator ya yi sama abinsa. A gaggauce
Jaish ya bi bayansa dan jin meyakefaruwa. Ita kuma Auta ita da Pretty suka biyo Yah
Jawad zuwa cikin gida, Auta ta yi mamakin ganin cikar jama'a a gidan nasu, amma
bata kawo cewa batun aurenta ake yi ba, hankalinta ma baya a kansu, burinta kawai
ta je ta yi wanka ta isa ga abin kaunarta su ga juna, ta yi kewarsa sosai.

Kai tsaye part na King Smart ya nufa, sallamar ma a cikin zuciyarsa ya yi, ya
kuwa yi sa'ar samun momma a ciki, yana shiga ya tsaya a bakin door tare da harɗe
hannayensa a saman kirjinsa yana bin King da momma da kallo, suna zaune saman bed,
suna duba jadawalin yadda taron zai kasance, da kuma ɗinbin dukiyar da suka ware
dan yi kyaututtuka. Jin motsin shigowa yasa suka yi gaggawar kai kallansu kan door.
Wlh dikkansu sai da gabansu ya faɗi time da suka ɗaura idanunsu a kansa. Muryar
momma har rawa yake yi wajen cewa. "Omerish har kun iso ne?"

Idanunsa a kan King ya yi shiru bai amsa mata ba, aka ce ɗan na gada ya fi ɗan na
koya, dik jaruntakar King sai da ya ji ya sha jinin jikinsa, saboda wani irin
kallon da Smart yake binsa da shi, kuma kun san idan mutum bai yi adalci ba to fa
shi kaɗai ya rinƙa tsarguwa kenan yana jin kamar ba daɗi.

"Omerish lafiya kuwa?". Momma ta faɗa a dame, ta yi maganar tare da saukowa
kasan bed ɗin da nufin ta nufesa. Sai dai bata kai ga nufarsa ɗin ba ya ɗaga mata
hannu kallansa a kan King. With harsh voice ya ce. "Why? Metayi maka da ka rantse
dole sai ka kuntatawa rayuwarta? Shin kai akwai wanda ya yi maka irin hakan ne?!".
Ya maganar ko kaɗan bai kyafta idanunsa daga kallon da yake yi wa King ba.

Momma zata yi magana ya yi saurin cewa. "Momma please let me ask him first, ya
faɗa mun dalilinsa na san sanyamu cikin bakinciki".
Cikin natsuwa King ya ajiye file na hannunsa a saman bedside drawer, sannan
ya sauko ƙasa, idanunsa a kan ɗan nasa ya amsa da. "Saboda na hanata auren mutumin
da da shi da gawa dik ɗaya ne shi ne kake ganin na kuntatawa rayuwarta?".
Kai tsaye Smart ya amsa da. "Ba wai gani nike ka kuntatawa rayuwarta
ba, kai tsaye na tabbatar da ka kuntatawa rayuwarta!". Babbar magana!!.

"Zunaira ba zata auri mayakin can ba, saboda da shi da gawa dik ɗaya ne, daga yanzu
zuwa kowani lokaci a kan hanyar mutu yake, kobama haka ba, Zunaira jinin sarauta
zata aura kamar ita, wannan shi ne gata a gare ta!....." "Gata!". Smart ya maimaita
kalmar kafin ya ce. "Dad kowa ma a kan hanyar mutuwarsa yake, ba abin mamaki bane a
wajen Allah ka mutu ka bar mayakin da kake ikirarin shi gawa ne, and koma menene
shi waye ya mayar da shi hakan? Ba kai bane? Ai bai cancanci haka daga gareku ba,
kada ka manta rayuwarsa ya saka dan cetar taku da kula da dukiyarku, me aibunsa?
Shin ba irinsu nema yakamata ku sakawa da kyakkyawar alkhairi ba?!". Cikin harsh
voice ya yi maganar, dan ya fahimci sankai ne kawai yake ɗawainiya da daddyn nasu.
"Omerish yana da kyau ka san cewa ni fa daddynku ne, ba zan taɓa yin abin da
zai cutar da ku ba, kuma yakamata ka koyi magana da ni cikin girmamawa, saboda
gidan sarauta kake, baya ga ni mahaifinka ne ni sarki ne mai jagorantar al'umma
guda!!".

"Dad a haka na iya magana, da kowa a haka nike yi!!".
Ran King ne ya kara ɓaci sosai, dama tin ɗazun danne ɓacin ran nasa yake yi
saboda baya san su samu saɓani da ɗan nasa.

"Okey, to Hoorain bawane, kare ne mai tsaronmu, dan haka a kan wannan hanya zai
mutu, Zunaira ba zata taɓa zama mallakinsa ba, Omerish ka fita mun daga ɗaki!!".
Cikin tsananin ɓacin rai King ya yi maganar!. Smart ya ɓata mashi rai sosai, bai so
ace Smart yana magana no respect haka a garesa ba, abin ya koma mashi rai matuƙa.
"Dad Zunaira ba zata auri zaɓinka ba, zaɓinta zata aura, kuma Hoorain shi ne
zaɓinta, shin akwai wanda ya taɓa tauye maka hakkinka ne dad da zaka nemi ka
tauyewa rayinya nata?!". Shi ma Smart cikin fushi ya yi maganar.

Abin da momma take gudu shi ne ya faru, tin ɗazun sai ƙoƙarin dakatar da su take
yi, amma abin ya ci tura, ga shi har sun jawo ɓacin rai ya shigo cikin al'amari,
shaiɗan yana neman yin galaba a tsakaninsu...... "Zamu gani idan kai ka haifa mun
Zunaira ɗin sai kasa ta auri wanda ba zaɓina ba!!". King ya faɗa da kausasshiyar
murya. "Zaka gani dad, tin wuri kafin ka ji kunya ka canza wannan abin, idan ba
haka ba kana ji kana gani zan hana wannan aure".
Tin da ya shigo ɗakin yana tsaye yadda yake bai motsa ba, sai iya magana cike da
iko da isa!.

Cikin zafa gadan gadan King ya nufesa yana faɗin. "Ni kake faɗawa zan gani kuma zan
ji kunya?. To idan har ka haifu kasa in ji kunyar!!". Ko kaɗan bai ji tsoron daddyn
nasa ba dik da yana nufosa ya amsa mashi da. "Zakuwa ka gani, in dai baka canza ka
bawa Zunaira zaɓinta ba to tabbas zaka sha kunya, kuma Allah ma ba zai kyaleka ba,
zalincin ya yi yawa...".
Kara hasala zuciyar King ya yi, da zafa ya ƙarisa wajen da nufi ya ɗauke
Smart da zazzafar mari, sai dai kuma Momma ta yi gudun shiga tsakaninsu, yau taga
tashin hankalin da bata taɓa zata ba, hankalinta a tsananin tashe ta rike hannun
King da yake ƙoƙarin kaiwa Smart mari, jikinta har kerma yake yi ta fara bawa King
hakuri. Shi kuwa Smart ko jezau bai yi ba, kamar ba shi aka nufa da mari ba.

"Rahilarh ki matsa mun daga gabana, dik abin da ya faru ba ke kika ja mun ba?
Dik cikin ƴaƴana akwai wanda ya isa ina faɗa yana faɗa ne? Dik suna da tarbiya kuma
suna respecting ɗina, kin cutar da ni Rahilarh, kin zalunci zuciyata, kinsa yau ɗan
cikina, ɗan da na fi kauna sama da kai'na ne ya tsaya a gabana ina faɗa yana faɗa
har yake ce mun zan yi danasani a rayuwata saboda rashin tarbiya!"....... Nisawa
Smart ya yi, ya ji King yana ƙoƙarin zagan mashi daddynsa na France, wato shi ne
bai bashi tarbiya ba, maganar ta kora ransa sosai, cike da takaici ya ce. "Suma
ƴaƴan dake da tarbiyar nan gaba kaɗan zasu dai'na yi maka biyayya idan har zaka
cigaba da tauye masu hakkokinsu kana zaluntarsu dan wani san zuciya taka, suma zasu
dai'na bin umarninka a lokacin da zasu fahimci suna da ƴancin kansu". Cikin kunar
rai ya kai karshen maganar.
Ran King idan ya kai miliyan to fa a wannan gaɓar ta ɓaci,
zuciyarsa a tafashe ya kwace rikon da momma ta yi mashi, yana huci kamar wani zaki
ya damki wuyar rigar Smart. Momma bata ɓata lokaci ba wajen sake shiga tsakaninsu,
cike da tashin hankali ta fara faɗin King ya yi hakuri ya sake shi a bi komai a
hankali, tasan koma me ya faru ita ce sila, kowa laifinta zai gani, kuma hakan take
laifinta ne, ita ta kai Smart in da tarbiyarsu ya saɓa da na gidan sarauta, krista
ce fa ta tarbiyartar da shi, kunga kuwa dik abin da suka gani sai dai su ja baki su
yi shiru kawai.

"Momma ki kyalesa ya yi dik abin da yake ganin zai iya yi, amma dai Zunaira ba
zata taɓa auren zaɓinsa ba!". Smart ya faɗa ko a jikinsa, dan shi zafin da King ya
ɗauka ma ko ɗaya bata dame shi ba, saboda yasan ba komai bane idan aka danganta da
zafinsa idan ya ɗauka. Rai a matuƙar ɓace Momma ta ce. "Omerish idan ka sake saka
baki kan batun auren Zunaira ban yafe maka ba, haba mana, kasheni kake san yi ne?
Meyasa baka tinanin kuncin da zaka sakani a ciki? Meyasa ka canza kake san ɓacin
raina abin da a baya shi kafi tsana fiye da komai? Meyasa menayi maka da zafi
haka?". Ranta ya kai kololuwar ɓaci ne, tana san sasanta abu shi kuma Smart yana
neman kara lalata komai, shiyasa ta yi wannan furucin!.

Jin saukar kalamanta ya yi tamkar saukar aradu, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, a
fusace ya sa hannu ɗaya ya ɓanɓare hannun King daga wuyarsa, cikin zafa ya juya ya
bar ɗakin yana wani huci kamar mayinwacin zaki. Yana fita King ya dubi momma, a
dakile ya ce. "Kin gani ba? Kinga irin abin da kika ja mun ba? To daga yau na
haramtawa Omerish komawa kasar France, ya dawo kenan, ba zai sake komawa ba, dole
ya zauna da mu a nan ya koyi tarbiya da girmamawa na gidan sarauta, ki kira
iyayensa na can ki sanar masu na ɗauki ɗana kenan!!".

Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya koma cikin ɗakin, ransa sai tafarfasa take
yi. Shiru momma ta tsaya, ta rasa waye zata bi, ga Smart ya ɗauki zafi ya fita, ga
kuma King shi ma ya ɗauki zafi, to waye zata bi dan ta rarrashesa kenan? Ta jefawa
kanta tambayar, yau fa ake yinta.

A gefe guda kuwa. Auta ta tsala wankarta tsab, sai murna take yi zata ga jaruminta,
dan kada a gano akwai wanda zata je gani yasa bata saka wani kayan azo a gani ba,
sai ta sanya sleeping dress masu mutunci, riga mai dogon hannu da wando shi ma
dogo. Ta sanya headband a kanta, ta ɗauki wayarta ta nufo waje, wai dan ma idan ta
haɗu da wasu kada su zargi wani wajen zata je. Har ta kai bakin kofa ta juyo ta ce.
"Pretty ina zuwa, dik wanda ya zo nemana ki ce ina wajen Yah Omerish kin ji?".
Pretty dake kwance saman gado bata amsa mata ba, yau miskilancin ta motsa kenan.
Sanin cewa ta jita yasa Autar bata damu da sai ya amsata ba, ta yi gaggawar wucewa
kawai ta fita. Jikinta sai tsuma take yi tana san kallan jaruminta.

Tana fita dai'dai lokacin kuma Abdussalam ya shigo part na family daga ɓangaren
uncle Abbas, ya zo ganinta ne, dama ya yi kewarta sosai, so ya samu labarin ta dawo
shi ne da marmarinsa ya zo ganinta. Ita kuwa a lokacin ta fita ta kofar baya, sai
nemanta guyson ma yake yi, Chuchu and Aneesa dik suna ta nemanta, cikin sanɗa da
dabara ta nufi ɓangaren mayaƙa, tana tafiya tana ɓuya. Har ta isa ɓangaren warriors
ɗin. Kai tsaye ta nufi bedroom ɗinsa, sai murna take yi, a lokacin yana kwance
saman bed ɗinsa, ya idar da sallar isha'i ba jimawa, ya yi wanka yana sanye da
white arabs jallabiya mai shegen kyau, ya ɗauko wayarsa da nufin zai kirata kenan
ya ji knocking, a tinaninsa Abbonsa ne ko su Ansar, sai bai yi magana ba ya ajiye
wayar tare da saukowa kasan bed ɗin ya nufi door.

Ba tare da tambayar wanene bane yasa hannu ya ɓalle key na door ɗin ya ja ya buɗe.
Ai bai san lokacin da ya zaro ido tare da blinking sau biyu a lokacin guda ba
ganinta da ya yi. Cikin gaggawa ta raɓa gefensa ta shige cikin bedroom ɗin tana
dariya, ƙasa juyawa ya yi ya koma, sai yake ganin abin kamar a mafarki, ko kaɗan
bai yi zato ba, kuma ko kusa bai ji labarin ba, shi dai ya ga baki suna ta zuwa,
idan baku manta ba Abbonsa ya ɓoye mashi lamarin, so bai da labari. Saman drawer
dake kusa da bed ta zauna tare da ware tafukan hannunta ta rufe face ɗinta tana
sakin cool smile. Ya jima tsaye a wajen yana al'ajabi kafin ya juyo ya dawo ciki,
rufe kofar da key ya yi, gabaɗaya sai ya ji ya ƙasa iya ɗaga idanu ya kalleta, wani
irin zazzafar sonta ne yake kara fisgarsa. Da kyar ya karisa in da take, a bakin
bed ya zauna suna fuskantar juna, sai ya yi ƙasa da kai ya kasa magana ita ma ta
rufe fuska tana murmushi ta ƙasa magana.

Abin like wow gwanin birgewa, yadda suka zauna abin ya ƙayatar, kamar wasu mata da
miji da suka mallaki juna!. Almost five minutes suna a haka kafin ya ɗan nisa,
kansa a ƙasa yaki ɗagowa ya ce. "What a wonderful surprised! Gaskiya ba zan taɓa
manta wannan rana ba my Hoonaira". Taki cire tafukanta daga face ɗinta ta ce. "My
Hero ka ƙara kyau sosai, ka ɗan yi kiba abinka"........ "Na sha drips ba adadi ai
dole na yi kiba, kema ai kin kara kyau sosai, kinsa na ji tamkar yau na fara
ganinki". Cike da mamaki ta ce. "Dama ka ganni ne?". Ta yi maganar ne saboda taga
ko sau ɗaya bai ɗago ido ya ganta ba, kansa a ƙasa, kuma ya ce ta kara kyau, ko a
ina ya ganta?..... Bata san ɗan ikka ne yana satar kallanta ba, mai kunya irin na
Jaish😅

Kai ya jinjina mata alamar ya ganta mana. "My Hero kai ne fa kullum kake
damuna a kan yaushe zan dawo, na dawo cike da muradin zuwa in ganka, na zo kuma ka
yi ƙasa da kai, kaki ɗagowa mu kalli juna, to me yasa?". Cikin shagwaɓa sosai ta
kai karshen maganar. Ɗan ɗago idanunsa ya yi ya saukesu a kan kyawawan kafafunta
dake cikin wasu kyawawan flip flops masu laushin takawa. "Ni ai na ganki". Ya faɗa
idanunsa na ɗan rawa, kamar yana tsoron ɗagowa ya kalli kayan jikinta ne!..... "No
my hero, ni gaskiya ban yarda da irin wannan kallon ba, ni fa yanzu nasan gaskiyar
abin da yake cikin zuciyarka kamar yadda kasan nawa, meyasa zaka cigaba da azabtar
mun da kanka wajen hana idanunka kallan abin da kasan zai zama mallakinka koma in
ce ni taka ce?". Kamar zata saka mashi kuka ta yi maganar.
Nisawa ya ɗan kara yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗimi, lallai ba shakka yau ta
yi mashi abin da tasa saura kaɗan farinciki ya kashesa, dan a lokacin da ya buɗe
kofar nan ya sauke kallansa a kanta saura kaɗan numfashinsa ta dakata da
breathing!. Slowly ya ɗago da kallonsa izuwa saman face ɗinta, cikin natsuwa ya ce.
"Ba wai ina hana kaina kallanki bane, bana san kallan ya wuce na Musulunci ne,
nasan in dai na ɗaga idanu direct na kalli face naki to fa zan zarce kallan
musulunci, dan ba zan iya hakurin zare kallona daga kanki ba". Ya kai karshen
maganar yana tsayar da idanunsa a cikin nata, kallansa take yi kawai tamkar ta
mayar da shi cikin kirjinta haka take ji. Take idanunsu ya sarkafe cikin na juna,
suka mace da zubawa juna kallon kauna, wani irin salon kallo da suke aikawa junansu
mai cike da saƙonni da suke nuna tsantsar kewa da kauna juna tin da nike a wajensu
kawai na taɓa kallan irin wanna salon kallon. Ko waye ya koya mashi? Gara ita Auta
mun san daga ina ta koyo, shi fa? Mu dai mun san banda yaki babu abin da ya iya!.

"My Hero na yi kewarka fiye da yadda zato zai iya zata". Ta yi maganar ba tare da
cire kallonta daga kansa ba. Ajiyar zuciya ya sauke. "Gaskiya na fiki shiga cikin
kewa, kullum tinaninki ya zame mun tamkar iskar da nike shaƙa, kome nike yi ke nike
tinawa, kina rai'na fiye da yadda tinani zai iya tinani". Cigaba da sakar mashi
narkakken smile mai narka dakakkiyar zuciyarsa na warriors ta yi. "Please ina neman
alfarman da a cire mun hannun nan in ga fuskar Hoonairata yadda yakamata". Ya yi
maganar yana ɗan satar kallan dogon kyakkyawan wuyarta zuwa ƙasa kaɗan, ya ɗan yi
mamakin ganin sauyawarta, kwata kwata fa bata cika wata biyu da barinta kingdom ɗin
ba, amma ta sauya sosai, ya yi mamakin ganin yadda kirjinta ya ciko sosai, sai da
ya ji tsikar jikinsa ta tashi, sai da ya ji kamar an jona mashi lantarki, ya yi
danasanin kai kallansa wajen!.

"Ni dai a'a, kunyarka nike ji, ba zan iya buɗe fuskata ba". Ta faɗa tana zuba
mashi wani irin salon kallo na musamman, ɗaya ne daga cikin irin salon da ta tanada
zata rinƙa yi mashi a gidan aurensu.
"Yau kuma ni ake kunya?". Cikin sanyin murya sosai ya yi maganar. Kai ta
jinjina mashi alamar e kunyarsa take ji!. Shiru ya ɗan yi, can kuma sai ya ce.
"Kenan yanzu idan muka yi auren ma haka zaki mun? Ki ta rufe mun fuska da sunan
kunyata?"...... Ɗan turo baki ta yi kafin ta ce. "E haka zan yi, idan ka takura sai
ka rabani da kunyar in daina ji, kaga sai ka samu sauki". Wani irin daɗi ya ji ta
lulluɓe zuciyarsa, ƙasa ya yi da murya, cikin tsigar dabara ya ce mata. "To
shikenan, amma yanzu dai please a barni in kalla ko sau ɗaya ne?".

Kai ta ɗan girgiza tare da faɗin. "Ni kunya nike ji! Ba zan iya ba". Cikin
wannan shagwaɓa tata mai tafiya da imanin ta yi maganar, sai ya ji tamkar an tsira
mashi allura a tsakar ka.

"Please my Hoonaira, wannan kunyar zai cutar da ni fa, Please mana, shin baki son
in ji daɗi ne?". Murya a raunace ya yi maganar..... "To rufe idanunka sai in buɗe
maka"..... Ba musu cikin sauri ya datse idanunsa, dan a tsananin ƙage yake da san
ganin face ɗinta. Zame hannayenta daga face ɗin nata ta yi, sannan ta riko hannunsa
da hannunta ɗaya, ɗayan hannunta kuma ta bayyanar da kyakkyawar diamond ring da ta
ɓoye a ciki ta yi, ware kyawawan yatsun hannunsa ta yi a in da ta zura mashi ring
ɗin a yatsarsa dake kusa da babba na tsakiyar nan, sai wani irin balai'n kyalli
zoben yake yi. Tamkar dan hannunsa aka yi ta!.

Shi kuwa har cikin tsakiyar ransa ya ji ya amsa a lokacin da ta riko hannunsa,
gabaɗaya sai ya ji tamkar ba'a duniya yake ba, amma ya daure yana jinta ta sanya
mashi zoben, bai ta shi jin tamkar yana duniyar mercury ba sai da ta kai ɗan
bakinta ta sumbaci ring ɗin, ai bai san lokacin da ya waro idanunsa waje ba, kai
tsaye sai saman face ɗinta ya sauke kallonsa, nan fa ya kara kiɗimewa sosai, dan
wani irin sihirtatcen kyau da ta kara yi, kumatunta ɓulɓul. A take yanayinsa ya
fara canzawa, dannewa ya yi tare da ƙoƙarin kawar da dik wani tinani. Muryarsa na
ɗan sarkewa ya furta. "Ring ɗin nan ya yi tsananin kyan da shi kansa kyau ya
jinjina mashi, zan iya sumbatarsa?". Ya yi tambayar idanunsa a kanta babu ko
kyaftawa. Yatsa ta kai saman ramin da ya lotsa a kumatunsa, wato kyakkyawan dimples
ɗinsa. "Zaka iya sumbata, ai naka ne, my hero dimples ɗinka sun fi nawa kyau
sosai".

Tamkar wadda ta jonawa lantarki haka ya ji da ta taɓasa, wani irin azabbabben shock
ya ji, da kyar ya iya dannewa, ya kai hannunsa saitin ɗan bakinsa ya sumbata, sai
ya ji tamkar lips ɗinta ya sumbata, dama saboda ta sumbaci ring ɗin ne ya ce zai
sumbata shi ma, dan ya ɗaura lips ɗinsa a in da ta ɗaura tata!. Ƙasa jure jin
hannunta a kumatunsa ya yi, tana jefasa cikin wani yanayi, hakan yasa ya kai
hannunsa ya riko hannun nata, a hankali ya zameta daga face ɗinsa, sai dai kuma ya
kasa iya sakinta, dan wani irin tsantsar kaunarta dake fusgarsa, ga skin ɗinta very
soft shiyasa ya kasa iya sake mata hannu.

Ganin abin yana neman zame mashi wata matsala ne yasa ya ce. "My Hoonaira kada fa a
nemeki a cikin gida"....... Ɗan zaro mashi eyesball ɗinta ta yi kafin ta ce. "Uhm
nemakam ai nasan sai anyi, ban ma san ina zan ce na je ba".

"To mu je in mayar da ke kada a samu matsala". Yadda ya

Please Login or Register in order to submit comment