Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 52 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyo kai kafin Smart namu na kasar
France ya rufa mashi baya. Ihun sunansa da karfi Auta ta yi Yah Omerish sannan ta
tafi da gudun gaske ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai sauti.

Gabaɗaya parlourn zaro idanu suka yi suna kallonsa. A miliyan momma ta miƙe tsaye
tana dafe saitin zuciyarta dake mata barazanar tarwatsewa........... King kuwa, ya
zaro idanu ya kalli Auta ya sake kallan Smart, saboda kaman dake a tsakaninsu, shi
dai Auta kawai ya sani, to wanenne wannan mai kama da ita ɗin? Ya jefawa kansa
tambayar cike da mamaki game da ƙaguwa da san jin wanene?.

Cikin wani irin murya a mai kama da marairacen murya momma ta furta. "Omerish meya
kawoka nan? Meyasa ka zo? Meyasa baka sanar da ni zaka zo ba?".

A miliyan King ya dawo da kallonsa a kan Momma, ita ma Akka ta dawo da kallanta a
kan momma, nan ta dikka family suka dawo da kallonsu a kan momma.

"Dama ni nasan tabbas a shekarun baya karya Rahilarh ta yi mana, a lokacin da
wancan matsala ta faru tabbas nasan Rahilarh munafurtarmu ta yi". Cewar Mammie da
ta gaza iya haɗiye abin da yake ranta.

Sarina kuwa, miƙewa tsaye ta yi kallanta a kan Smart da ya rungume Auta yana cigaba
da goge mata hawaye yana kallan momma, shi bai bi ta kan King bama, dan bai ma san
wanene King ba, iya momma da yaranta kawai ya sani, bayansu shi bai san kowa a
cikin kingdom of power ba.

My people's me kuke tinanin ya kawo Smart kingdom of power? Me alaƙarsa da momma?
Ya aka yi yasan su Jaish bai san su Ramish ba? Me ya faru a shekarun baya da suke
ikirarin momma ta munafurcesu?. To dama na faɗa maku a week ɗin nan zaku sha
surprises, taku dai har kullum Princess Teema queen of surprise!!.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬

34


"Omerish". King ya maimaita sunan kallansa a kan momma da ta miƙe tsaye tana zaro
idanu. Lokacin guda ta fara kame kame alamar rashin gaskiya.

"Wani isasshe ya sanya Zunaira kuka a cikin gidan nan? Dama abin da kike ɓoye mun
kenan momma? Yau tsawon 2 month kenan tin kafin na yi tafiya (duniyar wata) har na
yi na dawo kullum idan na kiraki na ce ina Zunaira sai ki yi ta kauce mun, ashe
zalintarta ake yi kika ɓoye mun? Shiyasa hankalina ya gasa kwanciya mana! Me ta yi
maku kuma waye ya mareta a face ɗinta?!!" Cewar Smart, ya kai karshen maganar cikin
kakkausar murya.

Gabaɗaya parlourn tsit suka yi an rasa mai bashi amsa, dan dik sai da suka sha
jinin jikinsu ganin kwarjin dake face ɗinsa, an rasa mai tanka mashi, shi kansa
Jaish shakkarsa yake yi dik da sun yi sabo matuƙa, amma yana shakkar wani ɗan abin
da ya saɓa ya haɗasu.

Akwai wanda ya taɓa tina lokacin da Jaish yake yi wa su Omaid nasiha time da zasu
koma school? Kun tina a cikin nasihar da yake yi masu ya ce in basu natsu sun mai
da hankali a kan karatu ba zai mayar da su ƙasar Faransa! Kun tina wannan lokaci?
To wajen Smart yake nufi kenan, baku ji su Omaid ɗin sun ce ya yi hakuri gara masu
Yah Ramish a kan Faransa ba? Basa san zuwa wajen Smart dan ubansu zasu ci, sau biyu
suka taɓa kai mashi ziraya kafin su dawo sai da suka haddace rabin Alqur'ani mai
girma, suka natsu kaman wasu malaman da'awa, da suka koma Dubai sai suka
watse...........😅

King dai kusan suman tsaye ya yi, saboda ganin abin yake yi tamkar a mafarki, ya
aka yi Smart yake kama da Zunaira over haka?.

"Okey ba zaku iya faɗa mun wanda ya mari Zunaira ba sai ran kowa ya ɓaci ne?".
Smart ya yi maganar cikin kakkausar murya again.

Tsit suka yi har lokacin an rasa mai iya tanka mashi, Sarina tini ta sha jinin
jikinta, a tinaninta yadda Smart yake a hotonsa da ta sato daga ɗakin momma haka
yake a zahiri, sai taga ina, wannan da zafi sosai yake.

•••••••••••••••••••🔥

Uncle Abbas ne ya yi ta mazan miƙewa tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Mahaifinta
ya hukuntata". Wani irin kallo ya jefi uncle Abbas da shi wanda yasa su Dr Raj zaro
idanu waje, dan kallo ne mai kama da mugun kallo.

"Saboda shi mahaifinta ne sai aka ce ya zalinceta? Meta yi mashi? Shi yaga face
ɗin Zunaira ya yi kalar wanda za'a ɗaura hannu da sunan duka a kai ne?". Yana
magana yana bin uncle Abbas da mugun kallo.

Tashin hankali, zaro idanu gabaɗaya parlourn suka yi, barema ita momma da ta fi
kowa shiga damuwa, dan kana ganinta zaka san tana cikin tashin hankali.

A karo na biyu uncle Abbas ya sake yin karfin halin cewa. "Mahaifinta fa nace maka
ba wani ba, and wanenen ma kai da ka shigo mana cikin family without our
permission?".

Shiru Smart ya yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Then so what idan mahaifinta ne
shi? Akwai in da aka bashi damar ya zalinceta ne?". Shiru gabaɗaya parlourn suka yi
suna kallansa da mamaki, hankalin kowa a tashs, wai King yau ake cewa meyasa zai
hukunta Zunaira? Tashin hankali lallai Smart ya zo da sabon alamari.

Uncle Abbas ne ya sake yunkurawa zai yi magana Smart ya ɗaga mashi hannu cikin
zafa alamar ya ja bakinsa ya yi mashi shiru a wajen. Cike da isa ya ce. "Bana san
na sake jin ka bani amsa, babu wasu mutane a cikin parlourn ne sai kai?". Ya yi
maganar yana mai da kallansa a kan King da ya rasa bakin magana kawai yana kallan
momma.

Jaish ne ya ce. "Yah Omerish uncle Abbas ne fa, he's our second dad, why kake
yi mashi magana haka?". .............. "So what idan kanin dad ne? Da shi na yi
magana ne da zai rinƙa amsa mun?".

Zaro idanu Akka ta yi tana kallan Smart. (Akka taga wanda ya fita iya hau😅)

Shiru Jaish ya yi bai sake yin magana ba, dan shi yasan waye Smart. Akka ce ta
katsesu da cewa. "Wanenen kai wai da ka shigo cikin family na kake neman tayar mana
da hankali ka canza mana alkibla?". Ta faɗa tana ɗaure fuska sosai. Dan ita ma Akka
ta sha jinin jikinta ne yadda taga yake mugun kama da Auta, sai ta sha jinin
jikinta.

Wani irin kallo ya bi Akka ɗin da shi, shiru bai amsa mata ba, bashi ma da niyar
amsa mata.

Mummyn Chuchu ce ta miƙe tsaye, cikin sanyin murya da magana cike da dattaku da
sanyin word irin na uwa ta ce. "Ai kamannin dake face ɗinsa kawai ya isa ya baku
amsar wanenen shi ba sai kun nemi ji daga bakinsa ba, babban yayanku ne mana, ku
baku ga kamanninsa da Zunaira ba ne? Baku ga kamanin Rahilarh a face ɗinsu bane?".

Ai a miliyan su Dr Raj suka zaro idanu, a zabure mama ta miƙe tsaye, hankalinta a
tashe sosai ta ce. "No........ Impossible!!, ta ya aka yi ya zama yayansu? Kin dai
san bayan Ramish babu wani babba a gidan nan ai!".

Uncle Jahiz ne ya miƙe tsaye shi ma, a kan momma ya tsayar da kallonsa, a nitse
ya ce. "Momma ki warware mana wanene shi, dan nasan ke kaɗai zaki bada wannan amsa
mu fita cikin duhun ruɗani".

Yana rufe maki Smart ya dubi King ido cikin ido, talk without respect ya ce. "Me
Zunaira ta yi maka ka daketa?".............. Subhanallah, idanun da jama'ar cikin
parlourn nan suka zaro sai ya bawa mutum tsoro, hankalinsu ne ya kara tashi, ba'a
taɓa yi wa King magana yadda Smart ya yi a yanzu ba, King fa, tab lallai akwai
matsala.

Momma ne ta katse shi cikin ɗan ɗaga murya.
"Omerish daddynku ne fa! Meyasa zaka yi magana haka without respect?"........
Ɗan waro idanunsa a kan King ya yi kafin ya ce. "Ko baki faɗa mun ba i already knew
that she's my dad, bcoz of his face, yana kama da su Ramish, so ai already knew
that, kawai ya faɗa mun dalilin da yasa ya daki Zunaira?".

Tashin hankali, King kuma daddyn Smart? To fa!! Ya aka yi hakan ta kasance?
Daddynsa na Paris fa? Waye shi da har suke kama sosai?...... Tsit suka yi,
gabaɗaya Mammie ta ji cikinta sai murɗawa yake yi, mama hankalinta ya kara tashi
sosai, a tinaninta Ramish shi ne magajin mahaifinsa, tana jin daɗi itace mai power,
har tana hasashen gaba kaɗan ita ce zata zama mai murza kambun power crown da ya fi
kowani crown karfin iko, ta yi mulki san ranta, ta gama tsara plan ɗinta rana tsaka
kawai a wargaza mata komai a wani ce Smart ɗan King ne? Tab aikuwa ba zai yiwu ba.

Auta dai ta kwanta shiru a jikinsa tana shessheƙar kuka, Omaid and Obaid da
yake sun san ko waye Smart sai suka kara natsuwa suna kallan wannan tashin hankali
da aka shiga. Ita kuwa Mammie burinta kawai a warware masu wannan cakwakiya dan
tasan wani mataki yakamata ta ɗauka.

"Tambayarki fa nike yi Rahilarh, wanenen wannan?". Cewar King, dan hakurinsa ta
fara kurewa, saboda ya zo har wuya yanzu, abin ku da jinin sarauta, basa ɗaukar
raini, maganar da Smart ya yi mashi without respect shi ne ya bakanta ransa yake
san hukunta Smart, amma sai yasan wanene shi tukun nan, dan tin da ya ɗaura
idanunsa a kan Smart ɗin ya ji wani irin kaunarsa ya ratsa mashi zuciya........
Babbar magana!!.

"Ɗan kane". Tashin hankali, momma ta bawa King amsa tana kallan cikin idanunsa.
Zaro idanu King ya yi tare da sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, ɗana kuma?.
Ya maimaita kalmar a cikin ransa. Lokacin guda ya ji wani irin sanyi ta ratsa
zuciyarsa, dik da bai san ta ya aka yi Smart ya zama ɗansa ba, ba shakka ya ji
sanyi a ransa, sai dai kuma ta wani ɓangare ya ji ransa ya sosu matuƙa, dan dik
cikin ƴaƴansa babu wanda ya taɓa yin gigin yi mashi magana yadda Smart ya yi mashi,
kowa respecting ɗinsa yake yi sosai.

Uncle Jahiz da ya ji zancen kamar a mafarki ne ya yi saurin cewa. "Momma how comes
hakan zai kasance bamu sani na?". A ruɗe ya yi maganar.

Wani irin tsawa mama ta daka wajen cewa. "Ina hakan ba zai yiwu ba! Ta ya akayi ya
zama ɗansa? Hauka ne abin?!!".
Kowa ya ji maganganun mama yasan meyasa take faɗin hakan. Ita dai mummyn Chuchu
shiru abinta, amma dai ita ma ta ji babu daɗi a ranta dik da tasan cewa dama ba ita
bace da mulki tin da Ramish ya girmewa Bilal, amma dai ranta ya ɗan sosu kaɗan
bayyanar Smart.

Mammie kuwa mutuwar tsaye ta yi, tabbas tasan momma ta ɓoye Smart a rikicin da aka
yi a baya, amma bata taɓa zatan irin wannan bayyana Smart zai yi ba, yaro ya fi
ubansa zafa, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, ya dame King a zafin
zuciya da jiji da kai, ga shi da magana kai tsaye babu wata ɗar ɗar, kuma magana a
kaifafe, ga uban kwargini. Sosai hankalin Mammie ya kara yashi over, tinaninta ɗaya
ya za'ayi su ga bayan King ga wani zakin ɗan nasa ya kara bayyana, idan ma ta ce
zata auri King ɗin wlh waɗan nan zakunan ƴaƴan nasa zasu iya cinyeta da ranta, kai
ta ko'ina abin babu sauki a gareta.

"Ki yi mana bayani ta ya aka yi wannan ya zama ɗana?". Cewar King kenan. Jinjina
kai momma ta yi kafin ta ce. "Kowa ya samu waje ya zauna".
Babu musu suka koma saman sofas da suka tattashi suka zauna suna jiran
momma ta kora masu bayani.

"Omerish ka samu waje ka zauna bari mu yi magana ko?". Cewar Momma. Bai musa ba ya
wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna tare da zaunar da Auta a saman laps
ɗinsa, sannan ya ce Guyson ya taso ya zo ya zauna a kusa da shi.

Da sauri guyson ya taso, dama tin ɗazun yake san yin magana amma ya kasa, dan shi
ya fi kowa sabo da Smart, dik in aka yi karamar hutu a school sai ya je France,
Auta kuma sai ta je Dubai Smart yake tura jirgi ya ɗaukota karkashin kulawar Jaish
ba tare da sanin kowa ba, wani lokaci kuma Jaish ɗin ne yake ɗaukarta daga kingdom
of power ya ce sun tafi yawo sai su wuce wajen yayan nasu a Faransa ɗin, in short
dai guyson ya fisu sabo da shi sosai.

Shi kuma Smart ya fi shakuwa da Auta, dan kamar yadda take kama da shi a fuska haka
jininsu ya yi matuƙar haɗuwa, tamkar ransa yake santa, yanzu haka dalilinta ya zo
kingdom of power, dan tin kafin ya tafi duniyar wata yake san momma ta haɗa shi da
ita, amma momma tana yi mashi kona kona, ba komai yasa ba kuma face Auta ɗin ta
ɓata a lokacin, momma tana gudun faɗa mashi ta ɓata dan kada ya ce zai zo ko ya
ɗauki wani mummunar mataki, shiyasa taki faɗa mashi, idan ya kira guyson ma ya haɗa
shi da Auta shi ma ya yi ta yi mashi kwana kwana dan momma ta hanasa faɗa, haka
Jaish ma, daga karshe da ya gaji ne yana dirowa daga tafiyar da ya yi ya ɗaga jirgi
sai kingdom of power, kun ji dalilin zuwansa.

Gabaɗaya parlourn tsit suka yi bisa umarnin King, sun zuba idanu suna jiran su ji
me momma zata ce, kowa idanunsa a kanta. Akka ta lura Smart ya fita zafa sai ta
natsu, dan ta lura shi ya gado ainahin zuciyar king Abdul Malik, su King Zuhair dik
basu gada yadda yakamata ba, ga wanda ya fisu zafa, tsit kuke jinta a parlour kamar
babu ita!!.

Gyara murya momma ta yi kafin ta fara jawabi dallah dallah kamar haka.
"Kamar yadda na faɗa Omerish ɗanka ne to hakan ne babu shakka a wannan
al'amari".

Kirjin mama and Mammie ne suka bada dum dum da karfi!!. Hankalinsu ne ya kara
tashi, lokaci guda suka fara haɗa gumi, momma ta jiƙa masu aiki, mama kam kasa
hakura ta yi har sai da ta ce. "Ta ya aka yi ya zama ɗansa shi ne zaki yi mana
bayani!".

Momma bata bi ta kanta ba ta cigaba da cewa. "Dama ba mutuwa ya yi ba, a lokacin da
ka kafe lallai sai na dawo maka da shi, na yi magiya kaki saurarona, dik kunki
fahimtata, kun ki fahimtar abin da nike faɗe, har daddy a wannan karan bai
fahimceni ba, su Yah Rahab kowa yaki fahimtata, Yah Muhammad ne kawai ya iya
fahimtata, a wannan lokacin ne dan Omerish ya tsira da ransa ya kuma rayu sai muka
haɗa baki da Yah Muhammad a kan mu shirya maka ya mutu sai ya tafi da shi kasar
France in da babu wanda zai sake ganinsa domin ya rayu............"

Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon wani tsawa da Akka ta daka mata. "Rahilarh
dama ba gaskiya bane mutuwarsa? Amma kika jefamu cikin tashin hankali? Kina ji kina
ganin mahaifinsa ya rinƙa ciwo kaman zai mutu dalilin mutuwarsa, amma kika share
kamar babu zuciyar tausayi a kirjinki, e lallai".

Kasa da kai momma ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Goggo ki yi hakuri, wlh a
kullum ina kukan ciwon da Yah Zuhair yake yi a kan mutuwar Omerish, na shiga
damuwar da ban taɓa shiga ba, har na karaya na yanke shawarar zan dawo da Omerish
in yaso a kashesa da gaske kowa ya wuta, amma Yah Muhammad ya ce a'a in daure komai
zai wuce, wlh goggo ina tsananin san Omerish shiyasa na yi hakan, amma dan Allah ki
yafe mun, kai ma Yah Zuhair ka yafe mun, nasan na yi kuskure............"

Wai me ya faru a baya ne da yasa har aka so kashe Omerish ɗin?. To mu je dai zuwa,
wanda zata bada labarin abin ya faru a baya bata bayyana ba tukun nan, idan ta
bayyana zaku ji komai.

Katse mata magana King ya yi da cewa. "Kin cuceni Rahilarh, kin cuceni wlh". Yana
kai karshen maganar ya miƙe da sauri saboda wani irin zafi da zuciyarsa take yi
mashi, yasan zai iya faɗuwa a wajen idan ya cigaba da tsayawa saboda zafin zuciya.

Bedroom ɗinsa ya shiga da sauri yana huci, da sauri momma ta miƙe ta bi bayansa,
Aunty MieMie ce ta yi saurin sake miƙewa ta rufa mata baya. Nan fa parlon ya koma
kallon kallo, su Mammie da suka san abubuwan da suka faru a baya sun gane kan
maganar da momma take yi, su kuma su Sarina da basu san tarihin baya ba sai basu
gane kan maganar momma ba bayan cewa Smart ɗan King ne.

Bari in kara maku wani haske kaɗan kafin mu wuce gaba. Tabbas Smart ɗan King ne,
kuma shi ne babban yayansu, ya fi su Ramish dikka.
Ya aka yi ya fi su Ramish?. Mu je dai zuwa, kada ku manta ita ma mummyn Chuchu
tana da babban yaro da ya fi Ramish amma ya rasu, kada ku manta na faɗa maku hakan
a baya.
Akwai wani abin da ya taɓa faruwa a kingdom ɗin a lokacin da momma ta haifesa bai
wuci kwana uku a duniya ba, so a lokacin momma ta gudu Dubai ba tare da sahalewar
King ba, saboda ta ce zata tafi ya hanata, ita kuma tana ganin ɗanta zai mutu ne
idan tana Kingdom of power, shi ne ta gudu bai sani na.
Time da ta koma Dubai, ta yi ta yi ta zauna iyayenta suka ki yarda saboda King ya
ce bai aminta ba, ya ce ta dawo, ta yi ƙoƙarin yi masu bayani a kan in ta koma
tabbas ɗanta zai mutu, amma suka ki fahimtarta, hakan yasa ta yanke shawarar shirya
masu cewa Smart ya rasu. Ta kuma yi nasarar yin hakan tare da taimakon yayanta wato
daddyn Smart na Faransa kenan, sai da kowa ya aminta da Smart ya mutu, sannan
daddynsa ya tafi da shi France.

Momma bata taɓa yin kwana biyu bata yi video call da yayan nata ta ga ɗanta ba,
hakan yasa Smart ya tashi da sanin ita ce mahaifiyarsa, yana yawan tambayarta ina
daddynsa, kullun sai ta ce mashi sai ta zo ɗaukarsa zata zo tare da daddynsa. Time
da ya kai 20 years sai ya matsa mata a kan lallai yana san ganin daddynsa, a
lokacin ne ta kira shi video call ta juya camera ta shiga ɗakin King, so a lokacin
ya fara sanin daddynsa shi kuma King bai lura da video call take yi ba, so bai ga
ɗan nasa ba, da yake yayan momma ɗin yana yi mashi komai yasa bai damu da yazo ga
iyayensa ba, dan suma sun ɗaukesa kamar ɗa dama Allah bai taɓa basu haihuwa ba.

Kun ji a in da Smart ya samo kamanninsa da daddynsa na France ko? Daddyn nasa yayan
momma ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya wato King Badeen kenan, kunga dole a samu kamanni
ai.

Shi kuwa daddyn nasa tun yana yaro ya tafi kasar France, a can ya yi karatu ya
kammala, har ya samu aiki sannan suka fara soyayya da mom ɗin Smart ɗin, suka yi
aure, a dalilin haka ya samu takardar ƙasa ya zama ɗan ƙasa har ya iya shiga
siyasarsu.

Momma kuwa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen nunawa Smart ƴan uwansa gabaɗaya, dan bata
san kan ƴaƴanta su tashi a wargaje, tana san su tashi kansu a haɗe, su kaunaci
juna, ta kuma yin nasarar samun hakan, tabbas sun tashi cike da kaunar juna
dikkansu, sun san juna.

Sai dai shi kuma Smart ba iya kannensa kawai ya sani ba, a lokacin da ya girma
ya gama karantu sai ya fara bincike a kan ƴan uwansa, a nan ne ya san su Ramish
dikka, dik kuma yana kau taimakawa su Ramish a bakin aikinsu sosai, domin dayawan
lokuta da taimakonsa Ramish yake samun karin girma har ya zo matsayin da yake, amma
su basu san shi ba, kuma basu san yana taimaka masu ba.

In short shi ne ma ya binciko in da Jaish yake time da ya ɓata, sannan ya turawa
Ramish address ɗin, so dik abin da suke yi yana gani kuma yana sane da su, momma
take hana shi zuwa ga kingdom of power, ta ce ba yanzu ba sai ya kara girma, dan
tsaro.

Harta gidan Smart dake France in da yake yawan zama in ya bar gidan daddynsa,
wannan gida da sunan Zunaira ya ginata, gidanta ne da ya mallaka mata, yana da nasa
na daban, ya zaɓi ya rinƙa zama a nata ne kawai, yanzu haka yana nan yana kan
bincike a kan masu nikaf dan ya taimakawa Ramish ba tare da sanin kowa ba, shi ɗin
garkuwan gabaɗaya familyn marigayi King Abdul Malik ne, dan yasan kowa su ne basu
san shi ba, kuma yana taimaka masu ta hanyoyi daban daban wanda mutum ba zai taɓa
zata ba idan dai ba faɗa mashi aka yi ba.
Jama'a nace ku zo mu haɗu mu tsinewa tsafi, tsafi karyar banza ne da na wofi, idan
ba karya ba ne meyasa dik tsafin Mammie bai iya gane mata Smart ba? Meyasa ta kasa
iya gane cewa yana raye har ma ya girma? Kullum sai dai ta kare a hasashe shegiya,
karyar banza da wofi, wlh idan mutum zai koma ga Allah ma da ya fi mashi, tsafi dik
surkullen banza ne shegu.

Wannan dalilin yasa kuka ga Smart and his dad musulmai ne, saboda dad ɗinsa
yayan momma ne, balarabe ne, mom ce baturiya kuma krista, kuma tana da kyan hali,
dan ita ta makale lallai tana san daddy.

To in short dai kun ji yadda labarin Smart ya kasance ko? Nasan a iya wannan
bayanin kun fahimci in da na dosa, ba zan tsaya dogon bayani sosai ba, dan akwai
labari a gaba sosai, gaba zaku ji karin bayani dai. Mu cigaba da labarinmu.

••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Tsaye momma ta isko King a tsakar ɗakinsa, sai huci yake yi, ransa ya kai ƙololuwar
ɓaci, zuciyarsa sai tafasa take yi, momma bata kyauta mashi ba, tasa Smart ya taso
baya ganin girmansa, bai ma san shi ba, wannan ai zalinci ne.

Da alama King ya samu ɗan da zai iya sanya shi ya gane yadda zafin kaunar ɗa yake
da yasa commander Zafar ya hukunta ɗansa ɗaya tilo a duniya, dan ga dikkan alamu
King yana tsananin kaunar Smart over, dan shi ne first born ɗinsa, har ciwo ya
kwanta lokacin mutuwar Smart na karya da momma ta shirya. Wato fa idan Allah ya
tashi kama mutum wlh baka isa ka iya canka ta wace hanya zai kamaka ba, ga shi dai
cikin ruwan sanyi ya kama King bama aje da nisa ba, zakuwa muga yadda wannan
cakwakiya zata kaya.

A gabansa momma ta zube gwiwowinta a ƙasa, cikin sigar ban hakuri ta ce. "Dan Allah
ka yi hakuri Yah Zuhair, wlh ban yi abin da na yi dan na cutar da kai ko wani abin
makamancin hakan ba, na yi ne kawai saboda san da nike yi wa Omerish, ba zan iya
jurar rashinsa ba, kuma kai da kanka ka shaida da tabbas zai iya mutuwa a wannan
lokaci, ba kai da kanka daga baya ka ce in dai'na haihuwa a nan in rinƙa komawa
Dubai in haihu a can ba? Kaga da ban yi mashi hakan ba da mutuwa zai yi, kana ganin
yadda Jaish ya tsira da kyar fa, kasan komai, dan Allah ka mun afuwa ka ji?".

"Kin cutar dani Rahilarh, cuta mafi munin da ba zan taɓa mantawa da shi ba!! Ki
duba yadda ɗana ya taso, ya taso cikin kafurai, bai san darajar manya ba, ki kalli
yadda yake magana da ni tamkar ɗansa ne ni, gaskiya kin cuceni". Cikin zafi ya yi
maganar, bai taɓa shiga ɓacin rai irin na wannan rana ba, abin da ciwo matuƙa wlh,
dan ma tana matsayin ƴar kawunsa ne, kuma Akka na bala'in kaunarta, da wlh sai ya
hukunta hukunci mai zafin gaske.

Aunty MieMie da take binsu da kallo ne ta samu waje saman sofa ta zauna, bata taɓa
kallan daddynsu a cikin irin wannan yanayi ba, gaskiya ko mafarki ta yi akwai ranar
da zata zo King da momma su samu gagarumin matsala irin wannan idan ta tashi daga
wannan mafarki sai ta yi sadaka kuma ba zata taɓa yarda da hakan ba, sai ga shi a
zahiri ya faru, ita dai tasan sosai King yake bala'in san momma.

Mummyn Chuchu da ta shigo tun ɗazun ne ta matso tare da rike Momma dake durkushen
tana ƙoƙarin faɗuwa, ƙoƙari buɗe baki

Please Login or Register in order to submit comment