Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 36 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alamar yeah uncle Jahiz kyakkyawa ne. Wani irin kallan
up and down Aneesa ta watsa mata kafin ta ce. "Haka ne kam, gaskiya kyakkyawa ne,
amma kuma kada ki bari zuciyarki ta yaudareki a kan hakan, dan shi ɗin ba zai iya
dai'daita kansa da kowa ba, amma menene a tsakaninku da shi da ya ce kina da
mahimmanci a rayuwarsa? Dan dai nasan a familynmu gabaɗaya babu irinku koda na nesa
ne!". Cike da shegantaka da rai'nin wayo ta yi maganar, tana wani binta da
matsiyacin kallo.

Zee ta fuskanci kalaman cin mutuncin a juye Aneesa take aiko mata da shi, dan haka
sai ta yi shiru bata sake amsa mata ba, amma tabbas ta ji babu daɗin hakan, a
tinaninta Aneesa zata karɓeta hannun biyu tun da basu wuce mate a shekaru ba, sai
taga akasin hakan.

Jin bata amsa mata bane yasa ta wuce gaba tana faɗin. "Ki karisa ciki akwai toilet,
ki yi wanka, sai ki duba dressing room ɗina akwai wani part da na ware zaki ga a
jikin glass ɗin na rubuta n-n, ki buɗe glass ɗin ki ɗauki kayan da suka maki a
ciki, ni ina da abin yi". Ta kai karshen maganar tare da ficewa.

Bayanta Zee ta bi da kallo har ta fita daga cikin ɗakin, sannan ta dawo da kallonta
a kan alatun dake makare a cikin ɗakin, one after the other ta fara bin komai na
cikin ɗakin da kallo, ita kanta a yanzu ta yarda lallai su Aneesa ba sa'anta bane,
sun wuce da class ɗinta, irin wannan Daula haka? Ga yaran gidan dikka kyawawa
gaske, ƴan gayu, kamar su suka yi kansu, ga iya wanka da tsabta, sai balai'n shan
kamshi da jiji da kai suka iya.

Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata kimai ba sai ta wuce ta nufi in da take
zatan shi ne toilet na room ɗin, tana tafiya tana zuba ƙauyanci.

Ita kuwa Aneesa tana fita kai tsaye ɗakin kuyangun da suke yi mata hidima ta nufa,
ko sallama babu ta shige ciki. Ƴan mata guda biyu ne suke zaune saman katan bed
ɗinsu suna hira.

A takaice ta ce. "Ina da bakuwa a ɗaki, idan ta gama wanka ku wanke mun toilet da
P.Z, sannan ku bisa da toilet perfumes kamar kala goma haka, dan bana san in ji
wani iska ya canza daga na kamshi da na saba shaƙa, ku kara gyra mun ɗaki, kada ku
bari na dawo na ji wani abin in ba kamshi ba". Tana kai karshen maganar bata jira
amsarsu ba ta yi wajen.

Sun risinar da kai suna ƙoƙarin ɗaga mata gaisuwa, amma ina har ta wuce ta fita
abinta. Da kallo suka bita suna kara jinjina halin ƴaƴan King, yaran nan babu mai
iya masu sai iyayensu.

Tana fita bata zame ko'ina ba sai room ɗin Fanan. Tana shiga ta isko Fanan na zuba
barci, ta wani baje a gadanta tana barci cikin nitsuwa, kai ba ɗan'kwali arab hairn
nan nata a watse har face ɗinta. Hayewa saman bed ɗin ta yi tana ɗan turo baki.

Ƙaramin pillow ta ɗauko, duka ta kaiwa Fanan a tsakiyar baya tana faɗin. "Aunty
Fanan tashi ki ji wani labari".

Miƙa ta ɗan yi, kamar zata yi kuka, murya cike da barci ta amsa da. "Kai Neesha me
kuma na yi maki fisabilillah? Ki barni in cigaba da barci na mana, jiya momma ta
kawo mun wasu darty girls sun hanani barci, sai hauka suke mun"...................
Gyarawa Aneesa ta yi, ta manna bayanta da jikin headboard na bed ɗin, sannan ta ce.

"To cigaba da barcin za ayi maki kafa kuwa".

Waro idanunta waje ta yi, cikin magagi ta ce. "Ban gane za'ayi mun kafa ba, me kike
nufi?".

Cikin halin ko in kula ta amsa mata da. "Ina da tabbacin waɗan nan dirty girls da
aka kawo maki daren jiya ɗaya daga cikinsu ce kishiyarki, renon kishiya kika yi
jiya".

A zabure Fanan ta miƙe zaune, har ji ta yi barcin nata ya watse, tana zaro idanunta
ta ce. "Wai me kike nufi? Ban gane kishiya ta ba?"........... Kunna wutar screen
ɗin wayarta Aneesa ta yi, cikin halin ko in kula ta cigaba da cewa. "Na zo yi maki
mummunar albishir ne, Yah Jaish dai ya yi aure, kuma waɗan nan ƴan kauye da momma
ta kawo ɗaya daga cikinsu ce matar tasa..........."

Ai katse maganar ta yi ta ƙasa karisawa saboda wani irin capka da Fanan ta kai mata
a wuyar rigarta, a haukace ta kai mata capkar, bata ma san ta yi hakan ba, kun san
larabawa da balai'n kishi kamar me, tuni hankalin Fanan ya bar jikinta, har wani
juyi taga ɗakin nata ya yi mata kamar fanka saboda tashin hankali, sai ta ji kamar
kunnuwanta ne suka sharara mata karya.

"Ke Aunty Fanan, bafa ce maki na yi nice kishiyar taki ba, mai da wukar, ni mai
kawo labari ne kawai". Ta kai karshen maganar tana zare hannun Fanan daga wuyar
rigarta. Ta gama aikinta sai ta sauko kasa gadan ta nufi waje abinta. Wato wlh
Aneesa yar ikka ce, kawai ta kawo labari ta tafi ta bar Fanan da tafasar zuciya.

Lallai ba shakka safiyar yau bata yi wa Fanan daɗi ba, kuma na tabbata ba zata taɓa
manta wannan safiya ba, Allah sarki soyayya, ba laifinta bane.
Da gudun gaske ta yaye bargon da ta lulluɓa, ƙasa ta diro, wani irin kuka mai karfi
ne ya zo mata, da sauti ta saki kukan tare da watsawa a guje sai waje. Bata zame
ko'ina ba sai part na uncle Abbas wajen Mammie ɗinsu. Tana shiga kai tsaye bedroom
ɗin Mammienta ta nufa.

Nan ta isko Sarina da Mammiensu zaune a saman bed, Sarina ta tada kai da cinyar
Mammie suna shirya muguntarsu.

Ai a haukace ta shigo tana ihu, har ta razana Sarina ta yunkura zata gudu. Saman
bed ɗin ta haye ita ma, Mammiensu ta rungumo tana faɗin. "Na shiga uku Mammie, shi
kenan rayuwata ta zo karshe, ki taimakeni kada na mutu Mammie".

Sarina dai baki ta saki galala tana kallon ikon god.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Rungumeta Mammie ta yi tana faɗin. "Ya isa haka, yi shiru ki faɗa mana menene yake
faruwa?".
Ƙasa yin shiru ta yi, sai ma wani irin shessheka take yi tamkar zata haɗiyi
zuciya ta mutu.
A kule Sarina ta ce. "Ke bama san hauka, dalla rufe mana baki ki faɗa mun me yake
faruwa?". ........... Sanin bakin halin Sarina yasa ta haɗe malaman jikin waje guda
ta nitsu, cikin muryan kuka ta fara kora masu bayanin yadda Aneesa ta kora mata.

Wata iriyar zabura Mammie ta yi, dan kuwa tasan da cewa Queen Zarina tana san
Jaish, kuma tana san shi ne a matsayin saurayi ba wanda ya taɓa aure ba, in kuwa ya
yi aure akwai matsala, dan haka dole su yi saurin kawar da Mahnoor tin kafin ya
rasa samartakansa, samartakan nasa Zarina take so, shiyasa kuka ga a yanzu Mammie
ta daina goyan bayan Fanan a kan soyayyar Jaish.

HMMM BABBAR MAGANA.

A baya ta so Fanan ta mallaki Jaish, amma da Zarina ta nuna kwaɗayinta a kansa sai
Mammie ta janye, shiyasa kuka ga ta dai'na bawa Fanan dik wata gudunmawa, ita kuma
Fanan lokacin da Mammie take matsa mata ta rinƙa zuwa wajen Jaish dan ta samu
soyayyarsa, a lokacin bata wani feeling a kansa sosai, daga baya sonsa na gasken
gaske ya shigeta, a lokacin ne kuma Mammie ɗinsu ta zare hannunta a
lamarin,........................... Tashin hankali, lallai akwai cakwakiya.

Mahnoor ta ko'ina sai tarin makiya kike da su, Allah dai ya fiddaki, amma akwai
matsala, Mahnoor zata yi kishi da Queen Zarina and Fanan, kai my people's shin kuna
ganin wannan abu ne mai ɓullewa ga Mahnoor kuwa? Babban abin takaicin ma shi ne
mijin da ake ta wannan bura uba a kansa ɗin ma bai san suna yi ba, hasalima
dikkansu ba wanda ya ke kalla da mutunci, dik ya tsanesu, akwai bala'i a kingdom of
power wlh, ga dai can Zarina ta tura a ɗauko mata shi, wayyo Allah Jaish yaron
Mommarsa zaka yi bayani dan gidanku in ka jika a komar Zarina, ina dai Mahnoor ce
baka so? Mu je zuwa zaka so Zarina dan dole ai.

Wani irin matsiyacin tsaki Sarina ta ja. A walaƙance ta dallawa Fanan wani
tsinannen harara wadda sai da tasa Fanan haɗiyar yawu mai wuyar wucewa.

"Shashasha kawai, ke yanzu a kan namiji kike wannan kuka Fanan? Me aka yi aka
yi Yah Jaish? To ko mata dubu zai aura cikin minti nawa zaki ci uban shegu ki
kaɗasu hanyar yamma? Ke sai kace ba jininmu bane a jikinki! Ni kam anya Mammie
Fanan ƴar ki ce kuwa?"........... Cewar hajiya Sarina almasifatu rasa kunya.

Bata jira amsar Fanan ba ta ɗaura da cewa. "Ko ƴar autar sarkin aljanu ya aura
karshe kenan ko? To ubanta zaki ci kawai, zan yi supporting naki ba dan komai ba
sai dan kina sansa, dole in tayaki mu kwato maki shi". Tana magana tana dallah mata
wannan makirin hararar.

Mammie cikin karayar zuciya ta ce. "Fanan da gaske son Jaish kike yi?". Yadda ta yi
maganar zaku fahimci wlh zuciyarta ya karaya matuƙa, tana san ƴaƴan nata sosai,
bata jin zata iya marawa Zarina baya ta mallaki Jaish in dai har da gaske Fanan
tana san shi, kuma ba zata iya rabuwa da shi ba, ba zata cutar da ƴaƴanta ba
gaskiya, dan tasan ya zafin so yake.

"Zaki iya hakura da shi?". Cike da tsoron amsar da zai fito daga bakin ƴar tata
ta sake jefa mata wannan tambaya.

Wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskar Fanan, cikin murya mai ban tausayi ta amsa
da. "Mammie wlh mutuwa zan yi idan har na ce zan hakura da Yah Jaish, wlh ina sansa
so mai tsanani, ban taɓa san wani abin kwatankwacin jin sautin muryarsa kawai
bama.........."

Katseta Sarina ta yi cikin tsiwa. "Ke dallah ki dai'na jero mana wasu sambatu, ni
natsani jin kalaman soyayya a bakin mace, idan kin ga dama ki dafa shi ki cinye,
amma kada ki faɗa mun, kina son shi e kina son shi ya wadatar, ba sai kin kara mana
da yadda kike ji a ranki ba"........... Wai Sarina sai shirin Allah, wannan yarinya
da ba dan ma jinin Akka na gudu a jikinta ba wlh ina ga shaiɗancinta sai ya wuci
yadda ake tinani.

Shiru Fanan ta haɗiye sauran maganganunta tana shessheka haɗe da kawar da
kallanta daga kan Sarina.

Mammie kam shiru ta yi kamar wadda ruwa ya cinyeta, ta rasa abin faɗe, iya abin
da ta sani shi ne lallai a wannan gaɓa ba zata taɓa taimakawa Queen Zarina ba, tun
da Fanan ta kamu da san Jaish dole yarta ce zata mallake shi............ Bala'i
can, kai my people's me kuke tinanin zai faru? Jaish shi kaɗai mata uku, dik bama
wannan ba, ya mammie zata kaya da Queen Zarina?.

Riko hannun Fanan Sarina ta yi. "Zo mu je ɗaki in baki lecture yadda zaki yi
maganain Yah Jaish ya dawo tafin hannunki, a wannan karon bama buƙatar Mammie, dan
ita bata san salan zamani ba, na da can ta sani, Mammie ke kuma mun baki aiki kawar
mana da matar da aka aura mashi ɗin koma wacece".

Tana magana tana janyo hannun Fanan har ta sauko kasan gadon. Cikin shessheka murya
a hanzarce Fanan ta ce. "Aunty Sarina bafa wata matar azo a gani bace, wlh
tantagaryar ƴar kauyece wadda bata da banbanci da dabbobi, kuma kin ganta yar
datti, amma kuma wlh tana da kyau sosai, dan ya fini kyau".

Ɗan taɓe baki Sarina ta yi tana ɗaure fuska. "Kin san matar tasa ce? Kin taɓa
ganinta ne?".

Da sauri ta amsa da. "E jiya fa a ɗakina momma ta kawosu suka kwana, sai kin gansu
wasu kucaku da su ƴan datti, ɗakina ya yi ta wari sai da nasa aka kwashe bedsheet
da suka taɓa da dik wani abin da suka yi amfani da shi aka zubar da su, na sa aka
zuba tirarika sannan na iya kwana".

"What?!!" Sarina ta faɗa cikin ɗaga murya. Jinjina kai Fanan ta yi
alamar tabbatarwa.
"Muje in gansu". A gadarance ta yi maganar.

Banda idanu babu abin da Mammie take binsu da shi, ta rasa abin faɗe, tinanin
balai'n dake tinkarota kawai take yi a kan wannan case ɗin.

"Aunty Sarina yanzu kam sai dai mu je mu tambayi Neesha ta bamu labarin in da matar
tasa take, dan Haulat ta zo da safe ta ɗaukesu". Cewar Fanan.
A ƙagare da san ganin Mahnoor Sarina ta amsa da su je wajen Aneesa ta basu
labarin ina Mahnoor take. Da wannan shawara suka nufi waje hannunsu cikin najuna,
har wa yau dai Sarina tana cikin wannan ɗan iskan shigar tata mai tada hankalin
maza.

Mammie da ta afaka duniyar tinani sam bata san lokacin da suka fice daga ɗakin
ba, mafita kawai take tinawa kanta.

Basu zame ko'ina ba sai part ɗin King, ɗakin Aneesa kai tsaye suka nufa. A lokacin
ta fito daga wanka ɗaure da towel a kirji, tana tsaye a gaban mirro, sai tashin
kamshi ɗakinta yake yi.
Zee tana zaune a saman sofa ta buga uban tagumi tana bin Aneesa da kallo, tana
cikin shigar abaya mai bala'in tsada na Aneesa launin ash colar, ta yi matuƙar kyau
sosai, ta yi rolling veil a kanta.

Tun sako kafarsu a cikin ɗakin Sarina take bin Zee da wani matsiyacin kallo da in
aka yi wa mutum sai ya ji kamar shi ƙasƙantace ne. Ganin haka yasa Zee ta kawar da
kanta daga kallonsu, ga shi kuma tana bala'in san kallan nasu, saboda larabawan
ainahi suna da tsananin kyau sosai, amma ta lura kamar gabaɗaya familyn King daga
mazan har matar dikka tacaccun ƴan duniya ne masu jiji da kansu, babu mai saukin
kai da za'a ɗaga idanu a gani ya ɗan tarbi mutum da fuska mai sauki sauki koda ba
fara'a ma, gabaɗayansu daga matan har mazan fuska kamar an aiko masu da saƙon
mutuwa. Allah sarki bata samu Zunaira da Chuchu bane shiyasa take wannan tinani.

Sarina na ƙoƙarin ambatar sunan Aneesa dan ta tambayeta sai Aneesa ta yi saurin
katsesu da cewa. "Aunty Sarina nasan bai wuce amaryar Yah Jaish kuka zo tambayata
ina take ba, ai dama nasan sai kin so ganinta, to ba fa wata shegiya bace, ku
kwantar da hankulanku, yar kauye ce mara gata wanda ko a ƴar aiki ba zan ɗauketa
ba, banza ya fi mun ita muhimmanci, dan haka ni ban ga abin da zaku nemi gani a
wajen bama, sai dai fa tashin hankalinku ɗaya ne"....... Dakatawa ta yi da magana
tana wurga masu kallo ta cikin mirror.

Aneesa wlh karshe ce yarinyar nan, wannan idan Allah ya taimaketa Yah Rizwan ya
shiga hannunta shikenan kuma sai abin da ta so, yarinya ta iskance tun bata kai
ko'ina ba, Allah ya ceci Yah Rizwan.

Cike da fadanci Sarina ta amsa da. "Mecece matsala gudan?"..... Shiru Aneesa ta
ɗan yi na kamar one min, sannan ta amsa da. "Momma, momma tana bala'in kaunar
yarinyar dik da take kazama maras gata".

Siririn tsaki Sarina ta je. "Wannan ba matsala bane, ke dai yanzu faɗa mana in da
take?".

Cikin halin nuna ko in damu Aneesa ta faɗa masu Mahnoor suna ɗakin gyara. Sai dai
tasan su Sarina basu isa faɗa da momma ba, dole su gama dik iskancinsu su dawo
lallaɓa momma kam, dan ta gagari kowa a gidan, kafun Allah ce ita.

Sai binsu da kallo a sace Zee take yi, dan kyansu take san kallansu ba dan komai
ba.

Juyawa Sarina ta yi, har lokacin hannunta rike da Fanan dake ta sauke ajiyar
zuciya saboda kukan da ta sha. Har sun kai tsakiyar ɗakin zasu nufi waje Sarina ta
dakata, juyo da kallanta a kan Zee ta yi. Wani irin kallan walaƙanci ta watsa mata
up and down kafin ta ce.
"Neesha wacece kuma wannan?".

Aneesa na cigaba da gyaran gashin kanta ta amsa masu da. "Bakuwar second dad ne".

"Wannan kucakar? Daga ina ya samota?".Sarina ta sake tambaya........... Tara gashin
kanta Aneesa ta yi ta ɗaure, sannan ta juyo garesu da kyau, ta ɗan jingina bayanta
da jikin mirror kaɗan, sillent talk ta yi wajen cewa.

"Wannan ne kuma zaki iya tambayarsa, bani da alaƙa da hakan kuma bana san
yin alaƙa da hakan shiyasa ban nemi sanin labari a kan meyake tsakaninsu ba". Tana
kai karshen maganar ta wuce dressing room ɗinta.

Harara Sarina ta bi Zee da shi kafin tasa kai ta nufi waje, kai tsaye ɗakin gyaran
suka nufa. Sai dai ko da suka je mama Haulat ta hanasu shiga, saboda doka ce momma
ta saka bata yarda ta bawa kowa daman ya shiga wannan ɗaki ba har sai su Mahnoor
sun fito.

Tatas Sarina ta yi wa mama Haulat, rashin kunya tas ta yi mata wanda ko kare ba zai
sinsina ba, sannan ta ja hannun Fanan suka ta fi tana faɗi ko mama Haulat zata mutu
yau ba sai gobe ba sai sun shiga ɗakin nan sun ga Mahnoor, ta jira dawowansu a karo
na biyu.

Ko sannu mama Haulat bata ce masu ba har suka fice, wucewa ta yi ta rufo kofar da
Mahnoor suke ciki ɗin, ta zo ta ɗauko kayan marmari dan ta kai wa Jaish yana lambu.
Allah sarki mama Haulat baiwar Allah ƴar amana, matar nan tana da ƙoƙari sosai, ba
ƙaramin fama ta sha da Mahreen ba kafin Mahreen ta yarda a shafa mata haɗin gyaran
jiki a jikinta, har zagin mama Haulat ta yi, amma dik da haka bata tuna ta wani
damu ba, sai ma hakuri da ta rinƙa bawa Mahreen ɗin.

Abin dariya kuma shi ne Mahreen bata taɓa yarda ta shiga toilet ita kaɗai har sai
mama Haulat ta rakata, wanka ma ita ta yi mata yau, dan tsoron toilet ɗin take ji,
sai su manne waje guda ita da Mahnoor saboda tsoro. Dik da haka mama Haulat ta jure
bata wani damu ba.

A ɓangaren uncle Jahiz kuwa, yana barin wajen su Zee ya dawo in da momma take ya
karɓi babyn Khadija wanda ya sanya mashi suna da Junior, haka yake kiran yaron,
Allah ya saka mashi kaunar babyn nan sosai. Yana ɗaukansa ya wuce wajen King a fada
da shi, a nan suka je rabon zakka.

Sai dai fa dik hankalinsa yana a kan Zee, tinaninta kawai yake yi, yana jin kamar
ya tashi ya zo ya sake dubata, dan yana ganin kamar bata jin daɗin zama da Aneesa,
saboda yasan halin ƴaƴan nasa, haka dai yake ta sake sake ya kasa tsayar da abu
guda.

Da yamma ta yi cikin nitsuwa ya yi wanka ya canza kaya, ya bawa mama Haulat junior
ta yi mashi wanka ta shirya shi cikin shiri na musamman, sannan ya koma ya karɓesa,
ya nufo wajen Zee a ɗakin Aneesa.

Babu kowa a cikin ɗaki, ita kaɗai, ta takure jikinta waje guda, tana kwance saman
sofa barci ya yi awon gaba da ita. Ciki ya kariso, a gaban sofar ya tsaya yana
kallan face ɗinta, har sai da ya ji faɗuwar gaba lokaci guda, ji ya yi kamar kada
ya tasheta, amma kuma ya tina tana san ganin ƴar uwarta, hakan yasa ya fara ambatar
sunanta a hankali hankali.

Da yake bata da nauyin barci sai ta farka. Ganin shi a kanta yasa ta yi saurin
miƙewa zaune tana janjayo kayan jikinta ta gyara. Ɗan kawar da kallansa a kanta ya
yi yana faɗin. "Sorry na tasheki daga barki ko?".

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da ba komai. Sai wani gyara jikinta take yi tana takure
kanta bayan komai nata a rufe yake.

"Kin shirya mu tafi ne?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai. Sannan ta ce. "Dan Allah ka
ɗan bani yaran in rike".

Ba musu ya miƙo mata shi naɗe cikin kyakkyawan abin rike yaro fari kal mai tsada.
Hannunta har kerma yake yi tasa ta karɓesa, ya yi barci, bawan Allah da mama Haulat
ta bashi badara ya sha, ta yi mashi wanka shikenan sai ya hau barci abinsa, bashi
da kukan banza.

"Muje ko?". Ya faɗa yana nuna mata hanya. Gaba ta wuce ya rufa mata baya yana ta
kallanta. Kasa hakura ya yi har sai da ya ce. "Zee kayan nan sun yi maki kyau
sosai, kin yi kyau".

Hankalinta a kan baby ta amsa da ta gode, daga haka bata sake yin magana ba suka
wuce izuwa parking space na gidan. Gidan baya na ɗaya daga cikin motocinsa suka
shiga, driver ya jasu zuwa hospital na cikin Kingdom ɗin.

•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

Bari mu leƙa wani part.

Katafaren gida ne irin contemporary Glass Architecture ne, gini ne na gilashi mai
kauri da tsari mai ban sha'awa don bayar da haske da kyau.
Hawa biyu me mai amfani da escalator mai amfani da lantarki don tafiyar da mutane
sama ko ƙasa cikin sauƙi. Manyan ɗakunan barci guda uku a sama da karamar parlon,
sai main parlour mai girma a ƙasa wanda aka kawata shi da kayan alatu launin pink
and milk.

Akwai wajen wasanni, shakatawa, da filin motoci, grand Living Room, lambun waje
furanni masu kyau da kamshi, ga shuke shuke masu ƙawa na musamman.

Babban Kitchen na Zamani (Modern Kitchen) mai ɗauke da kayan girki na zamani (smart
appliances) Dining Room wajen cin abinci mai ɗauke da fitilu na alfarma. Guest
Room, ɗakunan baki guda biyu masu zaman kansu. Restroom, tare da kayan zamani.

Hawa Na Biyu (First Floor)

Master Bedroom. Babban ɗaki mai ƙunshe da toilet, wardrobe na zamani, da balcony
haɗe da kayan alatu na more rayuwa. Mini Library. Wurin karatu da nazari. Gaming
Room. Wurin wasanni da na’ura masu ban sha’awa. Cinema Room. Wajen kallon fina-
finai na zamani. Office Space. Wajen aiki ko haɗuwa da abokan ciniki. Guest Lounge.
Wani parlour na musamman ga baki. Indoor Pool. Ruwan wanka na sama mai gabaɗaya mai
ɗumi na musamman. Barbecue Space. Filin girke-girke na musamman, sune a sama.

Waje hararbar gida (Outdoor)

Swimming Pool. Babban ruwan wanka mai kyau. Garden. Lambun shakatawa da kujeru.
Playground. Wurin wasan yara da manya. Parking Lot. Wajen ajiyar manya-manyan
motoci, har guda 8. Shake yake da motoci irinsu, Rolls-Royce Phantom, Bentley
Bentayga, Lamborghini Urus, Mercedes-Maybach S-Class, Ferrari Portofino. Gidan ya
haɗu matuƙa.

Sai dai dik girmansa da ƙawatuwansa mutane biyu ne kawai suke rayuwa a cikinsa,
daga wata dattijuwa sai jikarta. Tsohuwar dattijuwa mai cikar kamala, da ƴar
matashiyar jikarta da ba zata wuci 18 to 19 years ba a duniya.

Kyakkyawar gaske ce yarinyar, gata so sillent haka, tin da ta taso a tare suke da
wannan kakar tata, da farko rayuwa suke yi a cikin wani kango wanda da shi da banu
dik ɗaya ne, dik ya rurrushe babu kofa, gini ne na laka da ya jima ya sha wahala,
ci da kyar sha da kyar, idan sun samu cin safe basa sanya ran zasu samu cin rana,
basu da gata basu da galihu.

Ga jikar tata kuma Allah ya yi mata basira sosai, akwai ilimi da balai'n san
karatu, tana zuwa govment school dake kusa da unguwarsu, dik da makarantar a lalace
sai a hankali, hakan bai hanata zagewa ta mayar da hankali a kan abin da ake koyar
da ita ba, tana da hazaƙa sosai, suna cikin ƙuncin rayuwa matuƙa, amma dik da haka
basu kuskura sun yi wani abin da zai kaucewa faɗin Allah ba, sun kula da kansu da
dokikin Allah, sun cigaba da jure wahala.

Wani lokaci idan yunwa ta yi yunwa har bara suke fita su yi, in kuma suka je yin
bara duniya ta lalace sai lalatattun cikin mutane su nemi lallata mata jika, hakan
yasa ta datse batun neman taimako wajen kowa, suka dukufa suka mai da lamuransu ga
Allah dan ya taimaka masu ba sai an ci zarafinsu ba.

Wataranar Friday wannan matashiyar budurwa zata je karɓan hutun kammala primary
school bayan rubuta common entrance, sun shirya ɗan ƙaramin party na dai'dai ƴaƴan
talakawa, dik da bata kai ko biyar nata wajen haɗa kayan wannan party ba, amma ta
shiryar dan ta je ko gani da ido ne taga masu yi.

A hanyarta na zuwa school mota ya bugeta, bata ji ciwo sosai ba, saboda mai motan
ba gudu yake yi ba, da yake bawan Allah ne mai sanin yakamata ga ilimin addini sai
ya tsaya ya ɗauketa ya kaita asibiti.

A nan aka ɗan dudduba dik in da ta ɗan kukkuje aka yi mata dressing ɗinsa tsaɓ tare
da bata magunguna. Ya biya kuɗin sannan ya ɗaukota a mota tana yi mashi kwatance
har ya maido da ita gida. Bayan ya sauketa a kofar gida tana rike da ledar
magungunanta a hannu, har zai juya kan motarsa kuma sai ya fasa ya dakata.

Dama

Please Login or Register in order to submit comment