Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 72 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daraja. Dik wanda ba shi da
arziki ko gata, rayuwarsa bata da kima. Ana amfani da bayi da kuyangu. Akwai
kasuwannin bayi da ake siyar da su kaman dabbobi, kuma manyan gidaje sun cika da
kuyangu da ke aiki ba dare ba rana kamar injuna.

Mu leƙa cikin fadar Sarauniya ZARINA mai cigiɓi cigiɓin nau'ikan azaba. Babban gini
ne mai girma da ɗan duhu. An gina shi da baƙin dutse na zinariya, yana da hasken
fitila ja da launin shunayya. Akwai manyan azurfa da zinariya da aka ƙawata ginin
da su. Sarautar ta tara dukiya daga harajin da ake karɓa daga talakawa da ƙasashen
da suka mamaye, bayin Allah su sha wahala su yi noma sai su karɓe kaso biyu cikin
uku na amfanin gonar su barsu da kaso ɗaya wai haraji, hakan yasa rumbun hatsin
QUEEN ZARINA ya cika har yana amai da kayan abinci, girman wannan rumbu kuwa ya kai
girman gari guda daga cikin garuruwan kasar. Amma hegiyar matar nan bata sadaka
bare kyauta, gara ta bar abincin ya yi ta cike koma lalacewa ne ya yi a kan ta bawa
talakawa!!.

Fadar ta cike take da bayin dake hidima. Kowanne yanki na fadar akwai kuyangu da
bayi masu bauta mata. Babban zaure mai girma. A nan ne take karɓar baki da shari'a,
akwai dogarai masu sanye da rigunan karfe da takubba kamar warriors. Sai ɗakin
sirri a cikin fadar, wani ɗaki ne da ba kowa ke da damar shiga ba, anan ne take
shiryawa ko boye wasu sirrikan mulkinta.

Bari mu taɓo tahiri a kan Queen Zarina wadda kuka jima kuna jin labarinta ba tare
da kun san menene ainahin tsamar dake tsakaninta da Kingdom of power ba, bama ku
san wacece ita ba, shin yarinya ce, babba ce, matar aure ce, ko dai bazawara or
budurwa, dik baku sani va, to yanzu labari ya juyo ta kanta, bari mu faɗa maku ya
take domin yanzu story zai juyota.

Kingdom ɗin nan ba kawai mai arziki bane, yana da cikakken iko a duniya. Nasan ko a
iya haka kun fahimci dalilin da yasa a koda yaushe suke cikin takun saƙa da King
Zuhair, dan shi baya barin mulkin zalinci ta cigaba da tafiya.

Tabbas kujerar mulkin da Queen Zarina take zama banbancinsa da na King Zuhair
kalilan ne, ita ma nata diamond seat ne, sai dai na shi ya fi nata girma sa
ƙawatuwa. Ta dake saman kujerar nan tana haɗe cikin alkyabbarta launin gold mai
daraja, ba karya kyakkyawar gaske ce, zubin Iceland lady, jajir da ita kamar ka
latsa jini ya fita, ga gashin kanta light brow, ka zalika kwayar idanunta light
brown, babbar macece ba yarinya ba, ko dai in ce uwa, sai dai yanayin zubin
halittarta zaka yi zatan irin ƴan 25 to 30 years ɗin nan ne. Da ka kalli face ɗinta
kaga zallar madarar rashin imani, babu annuri kuma babu dariya ko kaɗan, doguwa ce
sosai dik da take a zaune, kun san matan Iceland da shegen tsawo sosai Masha Allah.

Gabaɗaya amintattunta da manya manyan bokayen cikin fadarta suna ciki, daga gefen
damarta wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce zaune a saman kujera ta mulki irin
wanda Queen take kai, sai dai nata kujerar bai kai na Queen girma, kima da kuma
daraja ba. A shekaru yarinyar nan ba zata wuci 17 years ba, ta tsantsara kyau cikin
shiga na ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji da su, ba karya kyakkyawar yarinyar
ce irin uwarta sak.

Wani kamshakin dakakken namiji mai kirar lafiya da karfi ne ya danno cikin fadar,
cikin tafiyar jarumta da nuna isa, yana cikin shiga irin na manya manyan sarakuna
masu karfin iko, da ka gansa babu tambaya kasan basarake ne, jiga jigan warriors
huɗu suna take mashi baya har ya ƙariso saman stage da Queen take, yana shigowa
gabaɗaya manyan cikin fada suka miƙe tsaye except Queen and her daughter.

A saman kujerar gefen damanta ya zauna, yana zama kowa ya koma ya zauna, yana zama
bai fi da minti biyu ba sai ga wani zaƙwaƙurin cikakken namiji mai zubin jarumta
shi ma ya shigo, da alama family ake san haɗawa kafin ayi abin da za'ayi, dan
wannan matashi ma dai falimy ne, saboda shigar dake jikinsa irin ta Prince.

Gefen wannan matashiyar budurwa saman kujera ya zauna. Gabaɗaya ko'ina tsit kake ji
tamkar babu halittu a cikin fada. Queen hannunta na rike da wani ɗan karamun
akwatin lu'ulu'u mai shegen kyau yana kyalli launin gold.

My people's a tinaninku a kingdom of power ake cin amana da munafurci ko? To kun yi
kuskuren tinani, bana jin akwai kingdom ɗin da ya kai nan cin amana da munafurci
dik wannan uban tsaro da kuka gani da izayar da Queen Zarina take yi wa masu
tinanin cin amana kafin ma su aiwatar, wlh dik da haka ta ko'ina akwai makarkashiya
da suka mamayeta, ku dai mu je zuwa.

ZARTAR, shi ne shugaban bokayen a ɓangaren yanke hukunci a kan abin da ya shafi
bayi da sauransu. Gabaɗaya fada ta zuba mata idanu suna jiran jin mezata ce. Ita
kuwa shiru ta yi na tsawo a kallah good ten minutes kafin ta ɗan kara dakewa a
cikin alkyabbarta zubin Uk, cikin kakkaifar murya ta fara magana kamar haka.
"Zartan har yanzu kana nufin baku iya gano in da wannan makulli yake ba? Dik karfin
ganinka, dik karfi eagle eyes ɗinka, amma baku iya sanin in da yake ba?".

Kasa gabaɗaya bokayen fada suka yi da kansu, Zartan da ya kasance wani tsohon
dattijo mai farar gashi kal, ga shi dogo da shi zubin Uk, idanunsa tamkar na mage
gwanin ban tsoro, yana sanye da fararen kaya da wani dogon mayafi dake ja har ƙasa,
gashin kansa da kayan jikinsa iri guda ne, yana da wani tabo a goshinsa kamar zanen
katan maciji ya fasa kai. Zartan yana ɗaya daga cikin Kim family, Kim family kuma
su ne familyn Queen Zarina kenan, kazalika yana da kafa a fada sosai.

Miƙewa tsaye ya yi cikin girmamawa ya ce mata. "Ina kara miƙa hakurina a gareki,
dik iya hangen da zamu yi mun hakanga bamu ga wannan makulli ba, amma dai tabbas
wannan makulli baya kingdom of power, tabbas yana ta wani wajen ne na
daban".......... Tsufa ta fara yawaita a tattare da shi, domin kuwa maganarsa ma
bata fita sosai. Mai da kallanta a kan wannan sarki da ya shigo ɗazun ta yi, a
natse ta ce. "Baka da abin faɗe ne a kan wanna case ɗin Ude?"...... Shiru ya ɗan yi
kafin ya amsa da. "For now dai babu, amma abin da zan ce shi ne zamu yi nasarar
mamaye ko'ina, mu cure duniya ya zama abu guda kuma mu mulketa, ko Zuhair yana so
ko baya so dole sai ya zube gwiwowinsa a ƙasa ya lashi kasan takalmarmu ya kuma
goge mana saman, daga karshe ya zama bawanmu".

Wani irin shu'umin murmushi ta saki saboda Ude ya faranta mata ranta sosai, tana
matuƙar yunwar ganin ta cure duniya ya zama abu guda ɗaya, babu wasu kasashe dik a
zama ɗaya, sannan ta zama ita ke mulkarsu dikka, ta murza kambunta ta juya kowa,
dik wanda yake san sanyaya ranta to ya yi mata kamalai irin wanda Ude ya yi mata a
yanzu, koda hukuncin kisa tasa aka yankewa mutum in dai ya yi mata irin kalaman Ude
tana iya yafe mashi.

"Amma ya batun Nieelarh da MUZAFFAR FAMILY fa?. Cewar Queen kenan..... Nieelarh
ƴar cikin Queen Zarina ce, ita ce kuma wannan kyakkyawar matashiyar yarinya dake
gefenta. MUZAFFAR FAMILY wasu jiga jigai ne daga cikin birnin waɗan da su ke da
arzikin dik wani abincin da ake ci a cikin birnin, sannan sune politics family dake
kasar gabaɗaya, mutane ne masu karfin iko da isa, da ace yau zasu ɗauke wa birnin
Justice dik wata tallafi hakika da birnin ta cika da yunwa matuƙa. So head of the
familyn wato MUZAFFAR ya kasance mutum mai girma a fada, sannan mutum mai girma a
birnin, dik bala'in Zarina tana raga mashi, wasu daga cikin mutanen birnin suna
cewa akwai wata alaƙa a tsakaninsu, wasu kuma suna cewa saboda karfin musuluncinsa
yasa bata iya tsafacesa har ma take shakkarsa.

To dik bama wannan ba, haƙiƙa karfin musuluncinsa yasa bata iya tsafe familyn
Muzaffar har ta samu damar sarrafasu san ranta kamar yadda take yi wa sauran
jama'a, amma ba hakan ce tasa take shakkar Muzaffar family ba, akwai wani sirri
nata da shi dattijo Muzaffar ya sani wanda kuma ga dukkan alamu tana tsoron ya fasa
kwai shiyasa take shakkarsa sosai, to a halin da ake ciki yanzu ɗaya daga cikin
Muzaffar family ya nuna ra'ayin yana san ƴarta Nieelarh wanda kuma dan dole ta amsa
da ta yarda da batun, amma ta ƙarƙashin ƙasa tana neman ta yadda zata yi ta warware
wannan batu, saboda ba zata yarda haɗa jini da musulmai ba a cewarta, ta kuduri
niyar ko ta halin yaya sai ta ruguje wannan batu, sai dai kuma ba zata iya yin fito
na fito da Muzaffar family ba!.

Amma me kuke tinanin zai kasance sirrinta da bata san ya fashe kowa ya sani da har
take daurewa ta yi wa Muzaffar family sauki haka?.

Ɗaure fuska sosai Ude ya yi kafin ya amsa da. "Haƙiƙa Nieelarh ba zata shiga
Muzaffar family ba, dan hakan ƙasƙanci ne da faɗuwa a garemu". With his full
confidence ya yi maganar, haƙiƙa yana da tabbaci a kan maganarsa!. Ɗan Nieelarh fa
ƴarsa ce, ba zai bari hakan ya faru ba!.

Jinjina kai ta yi cike da farincikin amsoshin Ude a ranta, sannan ta miƙe tsaye,
cike da bada umarni ta ce. "Zartan ku cigaba da binciken ina Spender yake ta
maduban dubanku, ku tabbatar kun yi gaggawar binciko shi, Ude ina da magana da kai,
ka sameni a ciki main parlour". Tana kai karshen maganar ta yi gaggawar juyawa
alkyabbarta na jan ƙasa sosai ta nufi wani katafaren diamond door da zai sadata da
cikin katafaren gininsu na alfarma wanda ya kasance shi ne family part ɗinsu.
Gabaɗaya mukarraban fada suka miƙe bisa girmamawa a gareta har sai da ta bar
fadar sannan suka koma suka zauna. Tana fita kofar wasu mahaukatan zaƙwaƙuran
warriors suka take mata baya zuwa kofar shiga cikin part ɗin nasu!.

Cikin kakkausar murya mai amon bada umarni Ude ya kara jaddadawa bokayen royal
palace ɗin abin da Queen ta faɗa, daga haka ya miƙe ya bi bayanta ya bar Nieelarh
da Beer wato kanin Zarina ne shi ɗin.

Kai tsaye katafaren parlournsu na alfarma Quren ta shiga, still dai hannunta rike
da wannan akwatin. Saman wani luntsumemen sofa mai zaman mutum uku ta ajiye
akwaitin, sannan ta fara safa da marwa a tsakiyar parlourn tana ɗan bubbuga
hannayenta cikin juna, alamar tana cikin damuwa..... A haka Ude ya shigo ya sameta,
cike da kula sosai haɗe da nuna damuwar ganin halin da take ciki ya ce. "Lafiya
kuwa ranki ya tsananta fiye da kowacce rana?".

A gaggauce ta juyo da kallonta a kansa, cikin kakkaifar murya ta amsa mashi da. "Ba
zai taɓa kasancewa lafiya ba ka ganni a tsaye, kasan da cewa in dai bamu samu
Spender ba tabbas Muzaffar family sai sun ɗauke Nieelarh daga garemu, sannan zata
iya shiga wannan addini nasu, dik bama wannan ba, damuwata shi ne Zuhair ya
tsugunna ya goge mun takalma, na mayar da shi bawa na dattijo mai goge goge a royal
palace ɗina, na mayar da matansa kuyanguna, na mayar da ƴaƴansa masu yi mun hidima,
mazan kuma masu ɗeben kewa, na sa ya ɗanɗani ɗacin da ya ɗanɗana mana na kashe mun
mahaifi da ya yi ya kuma ruguje Thomas family!!".

"Wannan kuduri naki ba zai taɓa kasancewa ba, na sha faɗa maki ki hakura kawai".
Wata murya ce ta furta hakan a yayin da take ketowa izuwa cikin parlourn.
Kyakkyawar matashiyar yarinya ce da bazata wuce 23 years ba duniya, fara ce tas
kamar madara, kyakkyawar gaske ajin farko, tana shirye cikin alkyabbarta na sarauta
na alfarma wanda ya sha kwalliya da duwatsun lu'ulu'u, da ganinta kasan jinin
sarauta ce. Kwayar kyawawan idanunta sun kasance hazel eyes ne mai ɗan duhu, hakan
yasa ya yi kama da green eyes sosai. Idanun nata basu da girma sosai, amma suna da
kyau matuƙa.

Queen Zarina zata yi magana Ude ya rigata da cewa. "Ke Rishma kina da hankali kuwa?
Ita kike faɗawa magana gatsau haka?". Da wani irin kallo ta bisu, da kaga wannan
kallan kasan na takaici ne, sannan ta ce. "Ude idan baka tuba ba, babu shakka zaka
mutum a kaskance, zaka mutu mutuwa mafi munin da ko kare sai ya fika daraja a wajen
mutuwa........."

Dan dole ta haɗiye sauran maganar nata saboda wani irin uban tsawan da ya daka
mata, ba shiri ta yi tsit tana jin kirjinta na bugawa da karfi karfi.
"Keeeeee Rishma, ki iya harshenki ko kuwa na datse maki shi a yanzun nan!!!!". Shi
ne abin da Ude ya faɗa...... "Ude ba zan iya harshe na ba, ka rigada ka ketare
iyakarka, na dai'na jin tsoron dik wanda baya tsoron Allah, tin kan lokaci ya kure
maka Ude ka tuba...... ". A miliyan ta haɗiye maganar nata sakamakon nufarta da ya
yi gadan gadan tare da cire hannu zai ɗauke mata fuska da mari. Sai dai kuma bai
kai ga sauke mata marin ba aka rike hannunsa cak ta baya. Cikin wani irin fusata ya
yi zafan juyowa dan yaga wani mai karan kwana ne ya rikesa. Sai wani irin huci mai
zafi yake fitarwa, ran maza ya ɓaci. Ita dai Queen tana tsaye tana binsu da kallo.

"Kada ka sake ka ɗaura hannunka a jikinta Ude, idan kuma ka yi gangancin yin hakan
tabbas hannunka ba zai sake kasancewa naka ba, dan sai na datse maka shi!!". Shi ne
abin da wanda ya rike hannun nasa ya faɗa. Wani kyakkyawa mutum ne wanda da ka
gansa kasan ɗan uwan princess Rishma ne, dan suna kama sosai, yana tsaye tsayuwar
jarumta, cikakken namijin gaske ne, fari tas da shi, yana sanye da wani irin kaya
mai kama da na warriors, sai dai ba su bane, wannan kayan jarumai ne.

Mamaki tamkar Ude zai sume a wajen ne ya bayyana a saman face ɗinsa, da kyar ya
iya cewa. "Rishan ni yau kake kira da Ude?"....... Wani irin kallan kuna ya bisa da
shi kafin ya yi wurgi da hannunsa da ya rike, sannan a gadarance ya ce. "Da kana da
wani suna ne bayan Ude?". Babbar magana!.

Kum san menene yake tsakanin Ude da Rishma and Rishan? To Ude babban yayansu ne, ya
juya masu baya saboda Queen Zarina, ba zaku taɓa fahimtar wani kulli bane a wannan
masarauta sai nan gaba kaɗan, ta ya aka yi su Rishan suke matsayin musulmai shi
kuma Ude dake matsayin babban yayansu yake katon krista? Ya aka yi Ude dake
matsayin mijin Queen bai zauna a kujerar mulki ba sai ita? Meyasa yake biye mata
kaman ita take da shi? Meyasa ya juyawa ƴan uwansa dikka baya ya bi addinin matarsa
ya kuma damka mata ragamar garin a hannunta tana yin yadda ta so? Ina dattijo
mahaifinsu Rishan yake? Menene dikka wannan rikicin. Gaba kaɗan zaku sha mamaki a
kan wannan masarauta da kullin dake cikinta, akwai gagarumin case.

Sumar tsaye Ude ya yi, ya ƙasa yin wani ƙataɓus, bai taɓa zatan kannensa zasu
juya mashi baya ba, su kuwa sun gaji da yi mashi nasiha ne, sun gaji da biye mashi
suna sa ran zai juyo ya musulunta su koma yadda suke a da can baya, ya karɓi
karagar mulkinsa ya cigaba da gudanarwa bisa adalci kamar a baya, sun gaji da dik
abin da yake yi, yanzu babu wani sauran ɗaga kafa, dole su yi fito na fito da shi
dan su samu salamar ciwon dake cikin zuciyarsu.

Wucewa Rishan ya yi ya riko hannun Rishma tare da janta suka fice daga cikin
parlourn. Ko sau ɗaya Queen Zarina bata yarda ta ɗaura idanunta a kan Rishan ba,
alamar akwai wata a ƙasa kenan, ta dai bisa da kallo da ya juya yana tafiya tana
mamakin rikiɗewarsa..... A gabaɗaya kingdom of Justice ɗin nan, babu cikakken
jarumi na cikin gida biyun Rishan, shiyasa suke shakkarsa, zance na gaskiya har Ude
shakkarsa yake yi, idan yana magana a waje ba'a tankawa, namijin gaske ne. Har suka
kurewa ganinsu Ude bai iya furta word ba, ya shiga ruɗani. Tsafin Zarina ya kasa
yin aiki a kan mutane biyun nan, wato da Rishan da Rishma, kullum suna tare da
Dattijo Muzaffar shi yake taimaka masu da shawari a kan dik abin da ya taso masu,
su biyu suke rayuwarsu bayan juya masu baya da yayan nasu ya yi!.

Sai dai suka fice daga parlourn ne ya dawo da kallonsa a kan Zarina dake tsaye
kamar bata a wajen, a hankali ya buɗi baki zai yi mata magana kenan ta yi saurin
ɗaga mashi hannu. "Har yanzu yara ne, ka yi masu uzuri". Ta kai karshen maganar
tare da wucewa fuuuuuu kaya na jan ƙasa, kamar wata kunfa ta wuce sama, tana wani
taku mai kama da magic walk, sannan fuskarta ya nuna tabbas akwai wani abin, sai
dai ita baka taɓa iya karantar ina ta dosa, baka sanin me zata aikata sai lokacin
yin abu kawai kaga aiki da cikawa, ba shakka akwai abin da take da niyar yi a kan
Rishan da Rishma, saboda yadda ta kallesu da suna barin parlon ba kallan lafiya ba.
Matsawa kusa da stair case ɗin Ude ya yi yana cigaba da kallonta har ta kurewa
ganinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya koma fada.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Zaune suke cikin wani haɗaɗɗen park mai matikar ɗaukar hankali, ya kaita yawace
yawace sosai daga karshe ya biyo da ita a nan dan su ɗan huta. Sai dai fa dik
wannan yawon da suka yi taki sakan jiki da shi. Dik in da suka je tana takure waje
guda, bata ma san motsawa, dan dai yana matsa mata ne yasa take yarda tana binsa.

Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park ɗin ta gefe tana kallan
yadda big girls suke nishaɗi suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita
a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta ɗaukarwa kanta
alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waɗan
nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar
gidan Abbie, ba zata zauna ba.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




50



Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park ɗin ta gefe, tana kallan
yadda big girls suke nishaɗi suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita
a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta ɗaukarwa kanta
alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waɗan
nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar
gidan Abbie, ba zata zauna ba.

Tana can tana tinani shi kuma ya yi masu oder kayan sha mai tsabta, tsada da
haɗuwa, bata san time da ya yi ba sai gani ta yi an ajeye mata abu a gabanta. A
hankali ta ɗago da kanta ta ɗan saci kallansa ta ƙasan ido, while shi ma ita yake
kallo, ya ga ta saci kallonsa, amma sai ya basar kamar bai gani ba ya ce mata
bismilla ta sha mana. Kai ta ɗan girgiza mashi kafin ta amsa mashi da a'a ba zata
sha ba ta ƙoshi.

Ƙasa sosai ya yi da murya, tamkar mai raɗa ya ce. "Please Aesh, ko kaɗan ne? Ba dan
ni ba, dan Allah"...... Yunƙurawa ta yi zata yi mashi magana ya yi gaggawar sake
cewa. "No Aesh, don't say anything please, kawai ki sha". Haɗiyi abin da ta yi
niyar faɗa ta yi, sannan ta kai hannu ta rike stro dake ciki haɗaɗɗen cup ɗin, ɗan
jujjuyasa ta yi kaɗan kafin ta ɗan duka ta sanya bakinta. A hankali ta ɗan zuƙa.
Slowly ya ɗan lumshe idanunsa, dan har cikin ransa ya ji wannan zuƙa da ta yi,
nisawa ya yi kafin ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta yana mayarwa kan wayarsa
dake vibrate. Call ɗin Bilal ne ya shigo, kamar zai yi picking sai kuma ya fasa
tare da kashe wayar ma mai gabaɗaya, ya tura cikin aljihunsa sannan ya harɗe
hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa, gabaɗaya ya zuba mata waɗan nan dara daran
idanun nasa yana kare mata kallo.
A hankali take cigaba da shan abin tana ɗan tsuke fuska alamar ya yi mata sanyi
sosai. Kamar ance ta ɗago ido tana ɗagowa suka yi four eyes, ɗan zaro idanu ta yi
like wow and like kallan me kake mun?! Shi kuwa gera guda ya ɗan ɗaga mata kafin ya
sauke ajiyar zuciya, abin gwanin birgewa sosai....... Wani irin kallo ta wurga
mashi mai kama da harara, shi kuwa ya yi mata nuni da idanunsa izuwa kan cup ɗin
alamar ta cigaba da shan abin da take sha bai san iskanci.
Make kafaɗa ta yi tare da girgiza kai, sannan ta ɗan ture cup ɗin gaba alamar
ba zata cigaba da sha ba kenan. Ɗan jinjina kansa ya yi like irin yarinya baki
sanni ba ne. A fili kuma sake nuna mata cup ɗin da ido ya yi alamar ta cigaba da
sha...... Wannan kallo dai mai kama da harara shi ta sake binsa da shi kafin ta
nuna mashi cikinta da hannu alamar ta ƙoshi ba tare da ta yi magana ba, alamar dai
yau ƴar kurma kurma suke jin yi. Ɗan kawar da kallonsa daga kanta ya yi kafin ya
ɗan yi gyaran murya kaɗan, sannan ya ce. "Aesh you're giving me to much of
headache".

Tamkar bata ji sa ba ta cigaba da binsa da wani irin kallo, har cikin zuciyarta
take rasa natsuwarta a dik lokacin da take kallonsa, sai dai kuma bata wani ɗaukar
hakan a matsayin wani abin azo a gani, ta fi ɗaukar abin ma a matsayin tsoronsa
saboda abin da ya shiga tsakaninsu.

Suna a haka masu kawo oder suka sake sauƙe masu tsadaddun plate masu shake da kayan
fruits kala kala very fresh a ciki. A gabanta yanzu ma suka sauke, kallansa ta yi
cike da mamaki kafin ta ce. "Wannan fa?".... "Is yours". Ya bata amsa yana kallan
yadda kankanar ta yi balai'n kyau, sun yankata shape of heart kanana da manya, gata
jajir zata yi zaƙi.

"Ni gaskiya na ƙoshi mu tafi gida". Ta faɗa kallanta a kansa..... "Babu in da
zamu je matsawar baki sha fruits ɗin nan ba". With full confidence ya bada amsar,
irin da gaske yake yi ɗin nan. Bata da zaɓin da ya wuce dole dole ta sha, tamkar
zata saka mashi kuka ta kai hannu saman plate ɗin, sai kuma ta ƙasa ɗaukar komai,
saboda yadda aka yayyanka fruits ɗin shape of heart ya yi matuƙar birgeta, tamkar
ance masu masoya ne suka yi oder, basu san waɗan nan abokan faɗa bane.

Ta shagala da kallan fruits ɗin tana tinanin wanda yakamata ta fara ɗauka
unexpected ta ga hannunsa a cikin plate ɗin, a hanzarce ta saci kallansa, sai dai
kash, tana ɗagowa suka haɗa ido, da sauri ta kawar da kallonta a ranta tana faɗin
shegun idanunsa a wajen kamar ball, sai ya yi ta kallan mutum, kuma ga idanun nasa
da shegen saka mutum cikin shakku da tsoro, sai yasa ka ji baka yarda da kanka ba,
shi tsabar kwarewarsa a aiki ma kana haɗa ido da shi zaka ji baka da gaskiya koda
kana da shi, yasa ka ka ɗaurawa kanka laifin da baka aikata ba dan bala'i irin
nasa.... Kai Leesharh da Ramish duniya ne, wai yasa ka kaɗaurawa kanka laifin da
baka aikata ba, wlh Leesharh akwai ƴar air nike faɗa maku, ta za'ayi baka aikata
laifi ba ka ce ka yi? Ko da yake sai dai idan baka tsargu ba, tsab zaka ce ka yi
bayan baka yi ba.

Shikuwa bawan Allah, kankana ya ɗauka tare da sanya mata a hannunta. "Idan na tsaya
jiranki ki zaɓa za mu kwana a nan, oya take this one". Ya kai karshen maganar yana
sanya mata shi a cikin hannunta, sannan ya janye hannunsa baya. Ɗan ɗaure fuska ta
yi tare da wurga mashi hararar kasar ido, a cikin zuciyarta ta ce mugu kawai, ba
zan yafe maka ba koma me zaka yi mun. A fili kuma ta kai kankantar saitin bakinta
ta ɗan gatsa. Wani irin sanyin daɗi ta ji kankanar ta yi mata, ga zaƙi ga shi daga
freezer aka cirosa, ai bata san time da ta sauke ajiyar zuciya ba, babu wanda ya ce
Leesharh kara ta sake mayar da ragowar bakinta a gaggauce zata sake gatsa, sai dai
kuma bata kai ga gatsan ba ya kai hannu ya kwace kankanar, dama ta gatsi rabin
heart a gatsan farko,

Please Login or Register in order to submit comment