Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 91 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

(SAW) ya ce. Lallai Allah yana jin tausayin bayinsa
fiye da yadda uwa take jin tausayin ɗanta. Girman soyayyar dake tsakanin uwa da
ɗanta babban abu ne da har Allah yake kwatance da shi Manzon Allah ma yake kwatance
da shi. Wannan hadisi yana nuna irin ƙauna da kulawa da uwa take ma ɗanta, wanda
idan aka raba su, yana da matuƙar wahala ga ita da yaron ma gabaɗaya".

"Kazalika cikin tirmidhi Manzon Allah (SAW) ya haramta raba uwa da ɗanta, ku ji fa
haramtawa ya yi, har ya ce. Dik wanda ya raba uwa da ɗanta, Allah zai raba shi da
ƙaunarsa a ranar Alƙiyama, innalilahi wa inna ilahir, kaga kenan abin babba ne
sosai!!".

"Raba uwa da ɗanta abu ne mai matuƙar raɗaɗi, kuma addinin Musulunci ya hana hakan.
Iyayen suna da haƙƙi a kan ƴaƴansu, kuma raba su ba tare da wani dalili na shari'a
ba babban zalunci ne, gaskiya yakamata mu yi dik mai yiwuwa wajen dakatar da Big
Bro daga raba ƴaƴa da iyayensu, idan ba haka wlh wata balai tana gab da afka mashi,
saboda dik abin da ka ji Manzon Allah (SAW) ya haramta to ba kara mun abu bane". Ta
kai karshen maganar tare da ɗago kallonta a kansa. Gabaɗaya mood ɗinsa ya canza, ya
shiga damuwa jikinsa dik ya yi sanyi.

Cigaba ta yi da cewa. "Batu a kan tsafi kuma wani abu ne da Allah ya la'anci masu
yi, ba abu bane mai kyau, bari in ɗauko maka shi daga farko, a cikin suratul
Baqarah sura ta 2 ayata 102 Allah ya ambaci Harut da Marut, wasu mala'iku ne guda
biyu da Allah ya saukar zuwa ƙasa a zamanin Annabi Sulaiman (A.S) domin su jarabta
mutane da ilimin sihiri (tsafi). A lokacin mutane da yawa sun fara amfani da tsafi
don cutar da wasu, musamman ma dan raba miji da mata, ko dan cimma wata mummunar
manufa nasu. Allah ya aiko da Harut da Marut zuwa garin Babila wato Babylon a
Iraki, domin su gwada mutane da basu ilimin sihiri, amma kafin su koyar da wani,
sai su ce masa. Mu fitina ne, kada ka yi kafirci. Wato suna faɗawa mutum cewa.
Wannan ilimi ba domin amfani da shi bane. Mu kawai jarabawa muke yi kar ka yi
amfani da shi zaka fita daga addini!!"

"Yayin da mutane suka cigaba da karɓar wannan ilimi, da yawa daga cikinsu sun yi
amfani da shi wajen cutar da juna. Allah ya nuna cewa wannan ba nufinsa bane, kuma
wannan ilimin bai fito daga Annabi Sulaiman ba. Annabi Sulaiman bai taɓa yin sihiri
ba! Kuma bai koyar da shi ba, shayatu ne suka buɗe ƙofofin tsafi ga mutane, sannan
Harut da Marut suka kasance jarabawa ga masu raunin imani".

"Amma a yau an canza maganar, mutane suna amfani da ruwayoyin israiliyat da suke
cewa akwai Mala'iku guda biyu da suka bijirewa Allah har ya kawosu duniya, wanda
nasan kai ma ka karanta wannan ruwaya". Ta yi maganar tare da dakatawa tana
kallonsa. Shiru ya ɗan yi kamar yana tinanin shin ya karanta ne ko bai karanta ba?.

(My people's kun san me? Wlh rubuta sunan israiliyat yana ban wahala sosai😅 wani
lokaci sai na zo rubutawa sai in saka ilsiyat😅 kai ko karanta sunan akwai wahala,
israiliyat😅)

"Ka manta ko?". Ta jefa mashi tambaya, kai ya gyaɗa mata alamar e. "Ni ban manta
yadda yake a rubuce a littafan yahudawa da kiristoci ba, bari in faɗa maka ko zaka
tina. Cewa suke yi Harut da Marut sun faɗi wata jarabawa daga Allah, inda suka
sauko duniya cikin surar mutume ba tare da izinin Allah ba. A ƙarshe, sun ci
jarabawar, sun yi kuskure, sai Allah ya azabtar da su. Akwai labarai da ke cewa
Allah ya zaɓi su su zaɓi azaba a duniya ko azaba a lahira, sai suka zaɓi su sha
azaba a duniya. Wasu riwayoyin har suna cewa suna rataye a cikin rami a Babylon
suna shan azaba har yanzu. Dan haka babu wani Mala'ika da ya saɓa maganar Allah,
sai shaiɗan wanda girman kansa ya ja mashi, in short tsafi abu ne wanda Allah ya
harabta shi gabaɗaya, ina fatan Big Bro ya dai'na". Ta kai karshen maganar tare da
jan kumatunsa, ya yi shiru ya tsareta da kallo.

"Sweetie waye ya baki magic to ke?". Yadda ya yi tambayar ka rantse da ALLAH ba shi
ya yita ba.
Ɗan zaro mashi idanu ta yi har sai da yaga kyallin idanun nata a idonsa. "Ni ma
wlh ban sani ba, rana tsaka kawai na gansa, amma ina ga wanna ina zargin wani
abin". "Kamar me kenan?!". Shiri ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Zan faɗa maka gaba,
yanzu dai zo mu yi karatu, ina san ka koya mun wani karatu".

Gabaɗaya mood ɗinsa ya canza, saboda ya ji bala'i zai iya saukowa yayansa, ba zai
iya jurar hakan na, so hankalinsa a tashe. "Jeki ki kawo books ɗinki mu yi
karatun". Ya faɗa yana ɗauko wayarsa zai duba time, so yake ya ga ko lokacin yin
dinner ɗinsu ya yi ne. Saura 30 mins su ci abincin, dan haka yana da lokaci koya
mata karatu, idan suka ci abinci kuma bedroom na Black Tiger zasu wuce su je su
takurawa rayuwarsa da hira!!.
======🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



59


Tattaro takardunta ta yi ta dawo kusa da shi ta zauna, ajiye wayarsa ya yi, dik
mood ɗinsa babu daɗi, ya ji matuƙar damuwa a kan yayansa, hankalinsa ya tashi, haka
ya hau koya mata karatu cikin natsuwa da fahimta yadda zai shiga kwakwalwarta
sosai. Tana bala'in son karatu sosai yarinyar nan, ga ƙwaƙwalwar tata kuma akwai ja
ba karya.

Sun yi nisa cikin karatun da suke sai jin voice ɗinsa ta yi ya ce. "Sis ranar kin
ambaci yayana da sunan Fir'auna, kin ce zalincinsa kamar na Fir'auna wanenen shi
Fir'auna ɗin?". Shi dai a dame yake, yana san a ce ga abu guda ɗaya da yayansa yake
yi na kirki, amma babu, kome zalinci yayansa yake yi. Shiru ta ɗan yi tana tinanin
a yaushe ta ce wa Black Tiger azzalumi Fir'auna kuma? Lallai ba shakka Ronnie yana
kaunar yayansa sosai, wato dik abin da aka danganta yayansa da shi baya manta
wannan abin.

Can ta tuna a ranar da yake kona mutanen birnin da wuta, tabbas a wannan rana ta
kirasa da azzalumi Fir'auna kawai, still a ranar da ya ce zai konata ita ma har ya
kaita daji ya ɗaure, ba shakka a wannan rana ma ta kirasa bakin azzalumi kuma
Fir'auna, lallai Ronnie, wato bai manta ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.
"Ɓacin rai yasa na kirasa da wannan suna, amma ba haka bane, zalincin da yake yi ne
ya bakanta mun rai"........ Yana rubuta mata wani note ya ce. "Okey Fir'auna
azzalumi ne kenan? Shiyasa kika danganta shi da yayana?". Ya kai karshen maganar
yana ajiye pen dake hannunsa, kai my people's Ronnie yana da very very good hand
writing, wlh rubutunsa ba dai kyau ba!!.

"E gaskiya Fir'auna azzalumi ne sosai, yayanka yana kwace yayan mutane ya
mayar da su sojojin yakinsa dan ya tara runduna mai razanar da zuƙatan manyan
masarautu, ya kuma yaki dik masarautar da yake so saboda karfin sojojin yaki, shi
kuma Fir'auna yana kashe dik wani yaro namiji da za'a haifa a Masar, dan baya son a
samu wani namiji da zai girma har ya kwaci mulkinsa, bokayen fadarsa ne suka shaida
mashi da za'a haifo wani yaro daga cikin banu Isra'ila wanda zai tsigesa daga kan
mulki ya mulki kasar, wannan dalilin yasa fir'auna yake kwace yaya maza yake
kashesu, amma da Allah ya tashi nuna mashi shi Allah ya sha gaban tinanin ɗan adam,
sai yasa fir'aunan da kansa ya reni Annabi Musa ɗin har zuwa girma, kuma ya yi
sanadiyar hallakarsa, so yayanka bai da zalunci kamar na Fir'auna, ka kwantar da
hankalinka, shi kuskuren da yake in da yake kwace ƴaƴa maza ya rabasu da iyayensu
ya mayar da su warriors dan kawai ya zama mai karfin iko a duniya!!".

Shiru ya yi yana kallon ɗan bakinta. "Har yanzu baki faɗa mun wanenen Fir'auna ɗin
ba ai! Ni yanzu ban san waye shi ba da har yake kashe ƴaƴa maza!". ..........
Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce.

"Fir'auna yana ɗaya daga cikin manyan sarakunan Masarawa, kuma Alqur'ani ya
ambaci shi sau dayawa a matsayin mai girman kai da zalunci. Ya kasance mai mulkin
kama karya wanda ya zalunci banu Isra'ila, yana da'awar cewa shi ne UBANGIJI. Amma
a ƙarshe, ALLAH ya kunyata shi kuma ya hallaka shi a cikin ruwa. Ba'a taɓa tantirin
ɗan iska biyun Fir'auna ba, kuma daga kansa ba za'a sake ba!! Fir'auna yasan
gaskiya amma yake take sani, bakin munafuki ne azzalumi!, karfin mulkinsa ya wuci
yadda kake tunani!!!".

"Fir'auna yana da ƙarfi sosai a lokacin da yake mulki. Alqur'ani ya bayyana wasu
abubuwa da ke nuna ƙarfinsa. A cikin suratu Zukhruf, sura ta 43 aya ta 51 ALLAH ya
ce. Fir'auna ya ce. Ya ku mutanena! Ashe ba ni ne mai mulkin Misra ba, kuma ga
waɗannan rafukan ruwa suna gudana daga ƙarƙashina? To shin ba kwa gani ne?"

"Cikin suratul Qasas sura ta 28 aya ta 38, Fir'auna ya ce. Ya ku shugabanni! Ban
san wani abin bauta wa gare ku ba sai ni. To ya Haman! Ka hura mini wuta a kan
tubali, sa'an nan ka gina mini hasumiya, dan in iya hawa zuwa ga UBANGIJIN Musa.
Kuma lalle ne, ina ganin shi mai ƙarya ne, innalilahi wa inna ilahir rajiun!!.
Wannan yana nuna girman kai da alfaharin Fir'auna da mulkinsa, har yana isgili da
cewa zai hau zuwa ga UBANGIJI dik dan ya nunawa mutanensa karfin ikonsa da isa
wanda zai yi amfani da hakan wajen tilasta masu su bauta mashi!!"

Cikin suratul Qasas sura ta 28 aya ta 4. ALLAH ya ce Lalle ne, Fir'auna ya yi
girman kai a cikin ƙasa, kuma ya raba jama'arsa kungiyoyi. Yana raunana wata
ƙungiya daga cikinsu, yana kisan ƴaƴansu maza, yana barin mata su rayu. Lalle ne
shi mai ɓarna ne. Fir'auna ya bautar da Banu Isra’ila, yana tilasta musu aiki
tukuru a matsayin bayi, zaluncinsa ma ba zai faɗu ba!"

"Amma da yake ALLAH gafurur rahim ne, sai ya aiko Annabi Musa (AS) da wahayi dan ya
kira Fir'auna zuwa ga gaskiya, amma Fir'auna ya ƙi. Cikin suratul Taha sura ta 20
aya ta 24 ALLAH ya ce. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle shi ya ƙetare iyaka, kada ka
manta Fir'auna shi ya reni Annabi Musa ɗin har ya girma, shi ne ma yasa ya rai'na
Annabi Musa sosai, sannan Annabi Musa baya iya yin magana saboda harshensa a naɗe
take bata fitar da magana, cikin suratul Zukhruf sura ta 43 ayata 52 Fir'auna ya
ce. Ko kuwa ni ne mafi alkhairi daga wannan wanda ba shi da kimar magana, kuma
kusan ba zai iya bayyana magana ba?. Fir'auna ya raina Musa saboda ba shi da
harshen da ke fita da kyau, har isgili yake yi mashi a kan maganarsa!!"

"Sannan Fir'auna ya kirawo bokayensa dan su fafata da Musa, amma Allah ya kunyata
su. A zamanin Fir'auna sihiri ya kasance sanannen abu, kuma bokaye sun yi amfani da
shi dan cin galaba kan Musa (AS). Fir'auna ya nemi su yi sihiri dan su nuna cewa
shi ne mai iko, amma Allah ya nuna cewa sihirinsu ba komai ba ne.
"Cikin suratul A'raf, sura ta 7 aya ta 116 da117 annabi Musa ya ce. Ku jefa
abin da kuke jefawa. Sai da suka jefa sai suka sihirce idon mutane kuma suka razana
su, suka zo da babban sihiri. Sai muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa. Ka jefa
sandarka. Sai ga shi tana haɗiye abin da suka yi ƙarya da shi".

"Cikin Suratul TaHa sura ta 20 aya ta 66 zuwa 69 ALLAH ya ce. A'a ku jefa. Sai ga
igiyoyinsu da sandunansu suna ɗanɗanawa kamar su masu tafiya saboda sihiri. Sai
Musa ya ji tsoro a zuciyarsa. Muka ce mashi. Kada ka ji tsoro! Lallai kai ne mafi
rinjaye, ka jefa abin da ke hannunka, zai hadiye abin da suka aikata. Lallai abin
da suka aikata sihiri ne, kuma ba zai yi nasara ba!!".

"Waɗannan ayoyi sun bayyana cewa Fir'auna ya dogara da sihiri ne, amma Allah ya
kunyata bokayensa ta hanyar annabi Musa (AS). Kuma kaga dik iskanci da girman kan
nan na fir'auna?". Ta jefa mashi tambayar tana kallonsa, kai ya gyaɗa mata alamr e,
nisawa ta ɗan yi kafin ta cigaba da cewa. "Dik iskancinsan nan yana bala'in tsoron
mutuwa kamar ransa, ka lura, dik mai aikata laifuka wlh bala'in tsoron mutuwa ne da
shi, bawan ALLAH baya tsoron mutuwa! Amma fa a lokacin da mutuwar ta riskesa sai ya
yi ƙoƙarin tuba ya koma ga Allah, kaga kenan dama yasan ALLAH kenan".

"Cikin suratul Yunus, sura ta 10 aya ta 90 zuwa 92. ALLAH ya ce. Mun tsallakar da
Banu Isra'ila daga cikin teku, sai Fir'auna da sojojinsa suka biyo su da zalunci da
girman kai, har da ruwan ya rufe shi, sai ya ce. Na yi imani, lallai babu abin
bautawa sai wanda Banu Isra'ila suka yi imani da shi, kuma ni ma ina daga cikin
musulmai. Allah ya ce. Yanzu? Bayan kuwa a da ka kasance mai ƙi, kuma daga cikin
masu ɓarna? To yau za mu cece ka da jikinka, domin ka zama alama ga waɗanda ke zuwa
bayanka, kuma lallai mutane da yawa sun kasance gafalallu daga ayoyinmu. Wannan
ayar ta nuna cewa Fir'auna ya tuba ne a lokacin da ya ga hallaka, amma Allah bai
karɓi tubarsa ba".

Uhm dik iskancin mai iskanci ba zai taɓa kai Fir'auna ba, amma shi kansa da ya kira
kansa da ALLAH da ya ji azabar fitar rai ya shaida babu abin bauta da gaskiya sai
ALLAH har ya yi ƙoƙarin tuba, wannan kawai bai ishi mutane ishara da su kama ALLAH
gam du rike ba? Me kake nema a duniya da har zaka yi bautar mutum irinka ko wata
dabba? Wai ni har Fir'auna ma ya shaida ALLAH ALLAH ne to kai kuma a suwa da ba
zaka damki hanyar gaskiya ba! Ku duba iskancin Fir'auna a bayan kasa fa? Amma da
yaga mutuwa har da su zuba! A wasu ruwayanma cewa suka yi Mala'ika ya toshe bakinsa
ya hanasa tuba, amma ni wannan ruwaya ban tabbatar da ingancinta ba, abin da na
sani daga Alqur'ani da ayoyinta shi ne ya ce ya tuba ya shaida ALLAH ALLAH ne kuma
ya zama musulmi daga ranar, ALLAH yaki karɓar tubansa!!.

Darussa daga rayuwar Fir'auna

"Dik wani mulki ko iko ba shi da wani amfani idan ba ayi amfani da shi ta hanyar da
ALLAH ya umarta da adalci ba. Girman kai da zalunci suna haifar da hallaka!!. ALLAH
yana iya jarrabtar mutane da iko dan ganin yadda za su yi amfani da shi. Tuba tana
da muhimmanci, amma idan mutuwa ta zo, ba za a karɓa ba!. Wannan shi ne tarihin
Fir'auna a taƙaice daga Alqur'ani da binciken tarihi". Ta kai karshen maganar tana
kallonsa!.... MASU KARATU DIK WANDA YA KARANTA NAN YA DAURE YA FURTA ASTAGFIRULLAH
KO DA SAU UKU NE, TUBA TANA DA KYAU SOSAI, DAGA NAN A DAURE A JEFA TEEMA TAKU TA
AMANA A ADDU'A KUN JI MY PEOPLE'S!.
"Mu je mu yi dinner". Ta faɗa tana miƙewa................ Hakika ya ji a gaskiya
lokaci ya yi da yayansa zai daina mulkin zalinci kada ALLAH ya hallakasa, yanzu ya
fahimci zalunci bata da wata amfani face halaka mai muni!.

Ganin bai amsa mata bane yasa ta ja dogon kyakkyawan shap nose ɗinsa. Ajiyar zuciya
ya sauke kafin ya miƙe ya sauko ƙasa. Ta fahimci halin da yake a ciki, dan haka sai
ta ce mashi. "Kada ka damu, Big Bro ya kusa zama adalin sarki mai jin ƙan
mutanensa, da zarar ya musulunta shikenan komai zai canza, kuma zamu yi nasara, ina
jin hakan a jikina, ban taɓa jin cewa lokacin samun saukinmu ya gabato ba sai a ƴan
kwanakin nan, tabbas da izinin mai dikka zamu yi nasara Bro".

Sosai ya ji daɗin kalamanta har ya samu zuciyarsa ta yi sanyi ya iya cin abinci mai
ɗan yawa, ba dan kalamanta ba da wuya yau ya iya cin abinci sosai, ko da suka je
wajen cin abincin ma, suna ci tana jansa da tsokana tana kara kwantar mashi da
hankali har suka kammala, sannan suka miƙe suka nufi bedroom na Black Tiger.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥


Zaune suke a cikin room ɗinsu ita da Leesharh, yanzu Leesharh ta samu abokan zama,
wato Guyson and Auta, kullum suna tare, yanzu Ramish yana iya fita bata da matsala,
dan akwai mahaukatan tsaron da Smart ya zuba masu tamkar ba zasu bar mutuwa ya
shiga ya ɗauki ransu ba, ga jami'ai guda biyu dake gadi a cikin gida waɗan da suke
parlour, ɗayan jami'in shi yake yi masu girki, so yana kasancewa ne a cikin
kitchen, ɗayan kuma yana zama ne a parlourn kuma shi yake kai masu abinci har cikin
bedroom ɗinsu idan sun buƙata, tsuhuwa ta dai'na yi masu girki sai dai ta yi wa
kanta, a tinanin Ramish suna jin daɗin zama da tsohuwar ce ma shiyasa bai mayar da
ita gidan Abbie ba!

Yanzu tsohuwar burinta kawai taga ta bar wannan gida, dan a tsorace take kada
asirinta ya tonu a kamata, tun ranar da ta ɗaura idanunta a kan Smart ta shiga
tashin hankali da fargaba, abin dariyar kuma wai zuciyarta ta kamu da son Ramish
matuƙa!!.
---------------------------------------🔥🔥🔥

Sai hira suke yi Leesharh da guyson, amma ita Auta tana zaune ta jingina kanta da
jikin bango, hannunta riƙe da wayar da Smart ya saya mata sabo, ta fara warwarewa
baiwar Allah, amma ba karya ta ji jiki matuƙa. Sai ƙoƙarin janta da hira suke yi
amma taki kulasu.

Wayar tata ce ta ɗan yi kara alamar shigowar sako, ɗan nisawa ta yi kafin ta kai
kallonta a kan sakon. "My Queen yanzu kin manta da ni tsawon lokaci, na sha wahala
kafin na samu numberki, meyasa baki nemeni ba? Ko dai yanzu baki san kalamaina
ne?". Shi ne abin da yake rubuce a jikin sakon. Shin kun tuna lokacin da wani guy
yake turo mata saƙonni? A lokacin da take tare da uncle Taheer? Kun tuna lokacin
tin kafin ma ta fara soyayya ta zahiri da Hoorain! To wannan guy ɗin ne, kun san ta
canza wayoyi har sau uku, shiyasa ya rasa numberta, sai yanzu ya samu sabon da
Smart ya bata last week, kuma wannan sabon number mutane biyar ne kawai suke da
shi. Daga Smart, Ramish, leesharh, guyson sai Jaish, ko Momma bata da shi, ko daga
ina ya samo number? Ko da yake mai san abinka ya fika dabara.

Siririn tsaki ta ja wanda yasa Leesharh da guyson dawo da kallonsu a kanta, har
suna haɗa baki wajen tambayarta lafiya kuwa. Kai kawai ta girgiza masu alamar babu
komai. Kallo juna suka yi, guyson ne yasa hannu ya karɓi wayar tata domin ya duba
me ta gani take yi wa tsaki!.

Daidai lokacin ɗaya daga cikin jami'an ya yi masu sallama a kofar room ɗin tare da
shigowa. A tare Leesharh and guyson suka kai kallonsu a kansa haɗe da amsa mashi
sallamar, ita kuwa Auta ta lumshe idanu tana san yin kuka, ta tina kalaman guy ɗin,
idan baku manta ba a da can ta ce tana bala'in son kalamansa.

"Akwai wani abin ne?". Guyson ya tambayi jami'in. With full respect ya ce. "Abinci
ne is ready, in kawo maku ne?". Jinjina mashi kai guyson ya yi alamar e ya kawo.
Juyawa ya yi cike da jarumta ya fice daga ɗakin. Miƙewa Leesharh ta yi tana faɗin.
"Yah Omer bari in yi wanka kafin muci abincin". Da okey ya amsa mata, kofar bedroom
ta nufa dan fita, har ta kai wajen muryarsa ya dakatar da ita. "Aunty Aesh kada ki
manta da yi mun Nigerian tea anjuma fa".

A miliyan ta juyo da kallonta a kansa. "Yah Omar wacece kuma Aunty Aesh?". Signal
da gera guda ya yi mata kafin ya kashe mata ido ɗaya. "Kece Aunty Aesh namu mana,
ko kin ɗauka ban san Yah Ramish ɗinmu na ƙoƙarin tsaraki kekuma kin ki bada haɗin
kai bane? To ni narigada na bashi ke shiyasa ma nike kiranki da Aunty". Hararar
wasa ta wurga mashi. "Ni Yah Ramish yayana ne kawai, bayan haka babu wani abin". Ta
kai karshen maganar tare da juyawa zata cigaba da tafiya.

"Uhm mun san komai fa Aunty Aesh, shiru kawai nike yi, sai wahalar mun da yaya
kike yi, ya yi ta faman lallaɓaki yana san ganin kina farinciki, sai ki ta wani sha
mashi kamshi kina nuna ke bakya sonsa bayan kuma nasan sonsa kike kamar hauka, dik
ina ganinku ai, sai kuma na faɗa mashi kina sonsa kawai ja mashi rai kike yi".

A miliyan ta sake juyowa dai'dai lokacin da ta kai bakin kofa. "Yah Omar
fisabilillah a yaushe ka ji na ce ina sonsa ni?"........ Harara ya wurga mata shi
ma tare da cewa. "Uhm me hotunansa suke yi a sabuwar wayar da ya saya maki? Wayar
nan ko sati bata yi a hannunki na amma har kin cikata da hotunansa da kika rinƙa
ɗaukarsa ba tare da ya sani ba, idan ya zo nan dik in da ya yi kallonki a kansa
kamar yadda shi ma dik abin da yake yi yana satar kallonki, dik fa nasan komai,
kawai idan zaki bada kai ki rungumo mun yayana ki kula mun da shi gara ki bada kai,
idan ba haka ba kuma wlh basu mutuwar sonsa Allah ya yi yawa da su, kina ji kina
gani wata zata kwace maki shi". MY PEOPLE'S KU TAFAWA KAIFIN ƘWAƘWALWA IRIN MA
ƳAƳAN MOMMA, ASHE GUYSON YA HARBO JIRGINSU, YASAN KOMAI!

Rasa bakin magana ta yi, dan ya faɗi komai, bata da wani sauran kalami. Auta ce ta
katsesu da cewa. "Aunty Aesh ki ja ajikinki hai, rabu da Yah Omar ɗin nan, ki
tabbatar kin wahalar da Yah Ramish kafin ki yarda, amma fa ki rinƙa yi mashi
kwalele sosai saboda ya kara rikice maki yana cigaba da sunkuyar maki da kai yana
neman amincewarki, ki wana shi ki ja mashi rai sosai". Cikin sanyin murya sosai ta
yi maganar. Ba kara mun daɗi suka ji ba yau Auta tasa baki a maganarsu, har suna
rige rigen amsa mata.

Guyson ya ce mata. "Aww haka zaki ce ko Auta? Yah Ramish ɗin namu za'a wana, to sai
na faɗa mashi!". Ita kuma Leesharh cewa ta yi "That's my lovely sis, shiyasa nike
sonki, kin iya bada shawara, kanki na ja"................Ɗan yake Auta ta yi wanda
aka ce ya fi kuka ciwo, cikin sanyin murya ta ce. "Yah Omar hakan shi ne maganinku,
kai ma ai naga kana san wannan yarinyar da kake yawan cewa Yah Jaish ya haɗaku a
waya, ina komawa gida zan hure mata kunne ta tabbatar ta baka wahala kafin ta
amince maka". Kun san ita Auta bata san su Mahnoor ba, lokacin da suka zo kada ku
manta ta tafi Paris, da ta dawo kuma tana cikin zulumi, ita totally bata cikin
natsuwa, kunga ta ɓata zuwa forest, ta dawo ba jimawa ta wuce Paris, yanzu kuma
tana nan Dubai, so bata san su waye su ba tukun nan!!.

A fujaje ya zaro idanunsa waje. "Please my pleasure kada ki zuga Mahreen, wlh yanzu
ma haka azabtar da zuciyata take yi, Chuchu na can ta kara lalata mun ita da banzan
shawara, ki rufa mun asiri, yanzu haka ni a matsayin ɗan iska nike a
idanunta"........... Zaro idanu Auta ta yi, a hanzarce ta ce. "Yah Omar ɗan iska
kuma? Kai ɗin ne ɗan iska?"

"No Auta, kome ya faru ni naja take kirana da hakan, kuma yarinya ce, so ba yadda
kika ɗauka bane, manta ma da maganar waye ya turo maki wannan sako?". Ya yi maganar
tare da nuna mata wayarta........ "Ban san wanenen ba ne". Ɗan jinjina kai ya yi
kafin ya ce zai yi bincike a kan number ya ga wanenen, daga haka ya ciro wayarsa ya
ɗauki number sannan ya miƙa mata nata wayar. Ita kuma Leesharh ta wuce ta nufi
bedroom ɗinta.

Wanka ta tsara a gurguje, ta shirya cikin wani haɗaɗɗen abaya mai shegen kyau, ta
yi rolling veil a kanta, ta fito so Masha Allah, sai tashin kamshi take yi. Waje ta
nufo cikin hanzari. Har zata koma wajen su Auta sai wani zuciya ya ce mata ta je
ɗakin Ramish, haka kawai ta tsinci kanta da san zuwa can, wucewa ta yi ta nufi can
tana jin gabanta na faɗuwa, Hasbunallahu wani'imal wakil ta furta a cikin zuciyarta
kafin ta ƙarisa wajen door ɗinsa.

Knowking ta ɗan yi dan a tinaninta kila yana a ciki. Sai dai kuma shirun da ta ji
ba'a amsa mata bane yasa ta fahimci babu kowa a ciki. Ajiyar zuciya ta sauke kafin
ta juya zata bar wajen, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi, har ta yi step biyu na
taku sai kuma ta dakata tare da juyowa ta kalli kofar, a hanzarce tasa hannu ta
tura kofar tare da afakawa ciki....... Shiru babu kowa sai sanyin Ac da
niimantaccen kamshi dake tashi. Ajiyar zuciya mai ɗan sauti ta sauke tare juyawa
zata fita. Unexpected

Please Login or Register in order to submit comment