Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soyayya, na kuma kara bincikawa na tabbatar da hakan ne, a binciken
nawa ne ma na gane rashin lafiyan ɗan uwana nine sila, nine na yi mashi shamaki da
abar kaunarsa yasa ya faɗi ciwo........."

Yaushe Auta ta gayawa Rizwan soyayyar dake tsakanin Jawad and Chuchu baiwar Allah?
Allah sarki kila tin kafin ta mutu ta gina masu soyayyarsu dan su cigaba da
kasakcewa da juna, ita kuma nata soyayyan shi ne ya zama ajalinta!!.

Cikin in ina ya idasa maganar sakamakon sarkewa da muryarsa take yi, ga wasu
zafafan hawayen da suka cika mashi idanu, Allah sarki har wani zazzaɓi mai karfi
yake ji tana ƙoƙarin kayar da shi. Dik taurin zuciya namiji soyayya tana sanya shi
ladab, to ga dai Rizwan da ruwan hawaye saboda rasa Jannat da ya yi!.

Tun da ya fara magana tsananin tausayinsa ya kara dabaibaye zuciyar uncle Abbas,
yau da yana da yadda zai yi ya raba Jannat gida biyu ya bawa ƴaƴan nasa da ya yi.

Matsowa ya yi ya rungumi Rizwan, zuciyarsa tana yi mashi zafi ya hau rarrashinsa a
kan ya jure In Sha Allah zai samu wadda ta fi Jannat.

Murya a sarkafe ya amsa da. "Ba dai wadda ta di Jannat ba daddy, nasan ba zan samu
madadinta bama bare wadda ta fita, Jannat ta dabance a zuciyata daddy, ka tayani da
addu'ar Allah ya sassauta mun sonta a rai'na".

Tamkar ƙaramin yaro yake kuka yana magana. Hakika uncle Abbas ya fahimci irin
tsananin sonta da Rizwan yake yi, abin ya wuci tunaninku, yanzu tsoronsa ɗaya shi
ne kada wani abin ya samu first love ɗin nasa, dan a gaskiya soyayyar da Rizwan
yake yi mata hakura da ita zai iya cutar da shi matuƙa.

"Babu abin da ya fi karfin Allah Rizwan, In Sha Allah zaka samu fiye da Jannat,
ina tayaka addu'a a kan hakan, Allah Ubangiji ya yi maka albarka da sauyi na
alkhari".

Sam soyayya ta rufe mashi ido, yaki yarda zai iya samun wadda ta fi Chuchu, gani
yake yi ita ce karshe, daga karshe dai uncle Abbas shiru ya yi ya rabu da shi a
mazaunin ba zai taɓa samun madadinta ba!.

Sosai Rizwan ya sha kukan da bai taɓa yin irinsa ba tun bayan rasuwar
mahaifiyarsu, yau ya kara ɗanɗanar ɗaci a karo na biyu a rayuwansa, da kyar ya iya
sarrafa hawayensa suka dakata da zuba, sosai zuciyar uncle Abbas ta karaya, yana
ganin kamar tabbas wani abin zai faru da Rizwan, dan irin wanna kuka kai akwai
tsorata mutum.

Sun ɗauki lokaci a wannan ɗaki, daga karshe uncle Abbas ya buƙaci da ya tsaya ayi
ɗaurin aure da shi kafin ya tafi. Da farko yaki yarda, ya ce.

"Daddy zuciyata ba zata iya ɗaukar ganin auren Jannat da ɗan uwana ba, Please ka
barni in tafi kawai ko zan samu sauki cikin rai'na, burina kawai in bar kasar nan".

"A'a Rizwan, babu wani abin da zai sami zuciyarka, Allah yana tare da kai, please
ka tsaya ayi wannan ɗaurin aure da kai".
Baya iya yi wa daddyn nasa musu, dan haka ya hakura ya tsaya ɗaurin auren, shiyasa
a wajen ɗaurin auren kowa ya gansa a wani sake sukuku haka kamar dai wanda baya
cikin hayyacinsa, dayawan mutane suna tunanin saboda rashin lafiyan ɗan uwansa ne.

A lokacin da uncle Abbas ya kammala gaya masu yadda aka yi suka mallaki juna,
gabaɗayansu hawaye ya gama wanke fuskokinsu, jikinsu ya yi matuƙar sanyi, sun ji
sun karaya sosai, tsananin tausayin Rizwan ya mamaye duƙatansu!.

Da kyar Jawad ya iya cewa. "Daddy ina Yah Rizwan ɗin yake yanzu?".

Miƙewa tsaye uncle Abbas ya yi yana faɗin. "Rizwan ya wuce Dubai tun bayan barinsa
wajen ɗaurin aure, ina zargin da zazzaɓi a jikinsa ma ya tafi".

A ɗan razane Chuchu ta ce. "Zazzaɓi kuma daddy?".

Kai ya gyaɗa masu tare da nufar hanyar fita dan ya basu waje su ga juna a matsayin
ma'aurata yanzu.

Da ido suka bishi har ya fice, kamar abin haɗin baki suka dawo da kallonsu a kan
juna a tare, dikkansu fuska jaga jaga da hawaye.

Hawayen farinciki, na tausayin Rizwan da kuma na ƙoƙarin rabasu da akayi.

"Jannat kin ji sadaukarwar da Yah Rizwan ya yi mana ko? Kin ji ƙoƙarin da
Auta ta yi a kanmu dan kada a rabamu ko? Ashe ita ta je ta gayawa Yah Rizwan muna
san juma?"?

Jinjina mashi kai ta yi tana cigaba da hawaye.

"Miƙo mun wayata bari in kira Yah Rizwan ɗin, in mun gama waya sai ki kira mun
Autaa cikin gida".

Allah sarki anata shagalin biki babu wanda ya lura da auta bata a gidan, baki sun
yi yawa kowa zai zaci tana ɓangaren ɗan uwansa ne, sai dai kuma, kowa yasan bata
rabuwa da Chuchu, so idan aka yi wa Chuchu kallon farko basa tare, aka sake ganinta
na biyu basa a tare, a karo na uku dole a tambaya ina take?.

Miƙewa ta yi a hanzarce ta zagaya ta ɗayan gefen bed ɗin ta ɗauko mashi wayar tasa.

Zuwa ta yi gabansa ta miƙa mashi tana faɗin. "Ga shi nan".

A maimakon ya karɓi wayar sai ya janyo hannunta ta faɗa jikinsa. A tare suka sauke
sanyayyar ajiyar zuciya. Hannunta dake rike da wayar ya riko, kamar mai raɗa ya ce.

"Wannan flowers ɗin sun yi kyau sosai, wadda ta zana maki ta iya sosai".

A ɗan shagwaɓe ta amsa da. "Ai saboda kai aka yi".

Ɗan karkata kansa kaɗan ya yi tare da ɗan leƙo face ɗinta. "Anya kuwa? Dan Yah
Rizwan dai aka yi, kuma nasan sai da aka kai ruwa rana dake kafin ki aminta ayi shi
ko?".

Kai ta gyaɗa mashi alamar e.

"Da baki bari anyi maki ba da kin yi mun asarar kyau kenan, kin ga yadda kika yi
kyau kuwa?".

Ɗaga kai ta yi suna kallon juna, hawayen fuskarta har ya fara bushewa, a ɗan
shagwaɓe ta ce. "Da gaske na yi kyau?".
Kai ya gyaɗa mata alamar e, yana yi mata wani irin mayen kallo mai wuyar fassaruwa.

"To shikenan yanzu kam tin da kai ne mijina bari in je mama Haulat ta kara
gyara mun jikina".

Bai san sadda ya ɗan saki murmushi ba a lokacin da ta yi wannan magana. Ya ji sanyi
a ransa har da ajiyar zuciya.

Kamar mai raɗa ya ce. "Da gaske nine mijinki yanzu? Ke mallakina ce kenan?".

Kai ta gyaɗa idanunta sarƙafe cikin nasa babu ko kyaftawa, ko kunyarsa bata ji ba.

Shi ma babu ko kunya ya matso dab da ita kamar zai sumbaci lips ɗinta, har ta
zaro mashi idanu tana kallonsa, sai kuma ya karɓi wayarsa dake hannunta ya ɗan ja
baya yana kallonta.

Number Rizwan ya shigar dan ya kira, ta kafe da kallonsa kamar nace zan kwace
mata shi.

Na'urar ce ta sanar masu da cewa number wayar Rizwan a kashe, sosai ya ji babu
daɗi, sai ya ji ya kara karaya, nan take ya kara jin ya shiga damuwa matuƙa.

Ganin ya shiga damuwa yasa ta kai hannu ta ɗan shafa kumatunsa. "Yah Jawad ka yi
hakuri nasan yana hanya ne, idan ya sauka zai kunna wayarsa".

Dawo da kallonsa sosai a kanta ya yi, tin da ta fara magana yake kallon lips ɗinta
har ta kai aya.

Ɗan rankwafo kanta kaɗan ya yi. "Jannat ina kaunar Yah Rizwan, ba zan iya jure
ganinsa a cikin damuwa ba, ban san ya zan yi da rai'na ba".
Cikin tsananin damuwa ya yi maganar.

Hannunsa ta ɗan riko a cikin nata, can kasa cikin kasalalliyar murya ya
ce...........

Idan kunga tsayin page ɗinku yana raguwa to rashin comment ɗinku ne sila.🥱




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Hannunsa ya ɗan riko a cikin nasa, can kasa cikin kasalalliyar murya ya ce. "A'a
Jannat, na tabbata damuwa ba zata bari ya kunna wayarsa ba, lallai ina san tafiya
Dubai a yau".

Zaro idanunta waje sosai ta yi, kamar zata yi kuka ta ce.
"Dan Allah Yah Jawad ka yi hakuri, babu abin da zai same shi, kuma In Sha Allah
anjima yana sauka daga jirgi zamu samu wayarsa a buɗe".

Tana magana tana share mashi hawayen dake bin ƙuncinsa, ya shiga damuwa sosai na
jin halin da ɗan uwansa yake a ciki.

Shiru bai sake yin magana ba, dan shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin dake a cikin
ransa.

==========================💘

Sosai King ya yi mamakin jin busoshin yaki da ake ta famar busawa a cikin kingdom
ɗin, sai dai bai tashi hankalinsa ba, saboda shi ɗin dakakken namiji ne wanda babu
tsoro ko miskala zarratin a cikin jininsa.

Kai tsaye fada ya nufa domin yasan me yake gudana ake ta buga mashi bososhin yaki
har haka.

A nan ya isko commander Zafar da sauran wakilan fada gabaɗaya, cikin takun jarumta
ya ƙarisa saman kujerar mulkinsa, tin da ya shigo kuma warriors guda biyu suka take
mashi baya har izuwa wajen kujerar tasa.

Miƙewa tsaye daga saman kujerunsu su commander Zafar suka yi domin bashi girma, har
sai da ya zauna saman tasa kujerar sannan suma suka zauna.

Dik sun kasa kunne suna jiran umarninsa da abin da zai faɗa. Shi ma idanu ya bisu
da shi har na tsawon good 5 mins, kun san halinsa akwai jin kai da izzar sarauta,
su kuma suna tsoron fara yin magana hukunci ya hau kansu a kan bai basu iznin ba.

Sai da ya cika ya hantse sannan ya ɗan yi gyaran murya cikin nutsuwa, cike da izza
ya fara ƙoƙarin buɗe bakinsa domin ya yi magana.

Wani bujumin warriors ne ya shigo cikin fadan bisa umarnin salama, sanye yake
cikin kayansa na mayaka, dik da cikin hular kayan yaki yake zaka iya fahimtar face
ɗinsa babu alama sassauci ko annuri.

Shigowarsa ya dakatar da King daga maganar da yake da niyar yi, suka zubawa
wanna warriors ɗin idanu.
Takowa ya yi cike da jarumta har izuwa tsakiyar fada, sannan ya ɗan risinar da kai
wanda kun san wanna dole ce a gidan sarauta, girmamawa ce ga sarki wanda ya rataya
a wuyoyinsu dole!.

Cike da girmamawa ya ce. "Ranka ya daɗe ina neman izinin yin magana".
Muryarsa akwai kaifi a cikinta, maganarsa akwai zarra a cikinta, yanayinsa akwai
tsantsar jarumtaka matuƙa, tsayayyen namiji sosai, ga tsawo da cikar halitta
matuƙa. Cikin kwararriyar larabcinsa ya yi maganar.

King ya ɗauki almost 3 mins kafin ya ɗan motsa lips ɗinsa, cike da izza ya
bashi izinin yin magana.

Ba tare da ɓata lokaci ba wannan warriors ɗin ya kyankyasa mashi cewa akwai baki
a wajen babban gate na Kingdom ɗin wanda suke da buƙatar a basu izinin shigowa dan
su yi magana da shi.

Nan ma sai da King ya ɗauki ƴan mintoci kafin ya buƙaci sanin wasu irin baki
ne?.

Kamar ba mutun ne yane magana ba wanna warriors ɗin ya amsa da. "Ga dikkan alamu
wani sarki ne da tawagarsa, bamu da masaniyar daga ina suke, amma ga dikkan alamu a
kan hanya suke".

"Sune silar buga waɗan nan busoshin yakin?". King ya jefa mashi tambaya cikin
nutsuwarsa.

Cikin dakiya ya amsa da. "Sune ranka ya daɗe".

Kallan commander Zafar King ya yi kafin ya dawo da kallonsa a kan sarkin fada da
kuma sarkin gida da suke binsa da kallo.

"Commander ina san sanin su wanene waɗan nan cikin ƙankanin lokaci". Ya kai
karshen maganar tare da ɗagawa wanna warriors ɗin hannu alamar shi kuma zai iya
tafiya ba tare da King ɗin ya sake waiwayarsa ba.

Cikin zafa ya juya yana taku manyan maza ya nufi waje.
Miƙewa tsaye commander Zafar ya yi tare da ɗan risinar da kai alamar
ya karɓi umarni, sannan ya nufi waje, sarkin gida ne ya take mashi baya da kara
karfafa ida nufin King.

=========HOORAIN=========💘

Zaune suke cikin wannan small garden in da Auta ta kamasu suna hiranta ranar da
daddare, shi da Ansar da Anwar, hannunsa na riƙe da wayar Auta while tasa wayar
tana a cikin aljihunsa, ya kurawa wayar kallo babu ko kyaftawa, Ansar da Anwar suna
ta hira a kan bikin da ake gudanarwa, ba'a taɓa biki a cikin gidan ba bayan na
uncle Abbas da ya zamana shi ne na karshe tsawon shekaru, daga King har uncle Abbas
babu wanda ya taɓa aurar da ɗa or ƴa sai yau, shiyasa murnar ta zarce tinanin mai
tinani.

Hotonta ya zubawa idanu yana ta kallo, tana tsaye kusa da wasu flowers dake
cikin lambun daddynsu, hannunta ɗauke da Felix ɗinta tana shafe lallausan gashin
jikinsa, murmushin dake kan fuskarta ya yi matuƙar kara tsatso tsantsar kyan da
Allah ya zuba mata, dimples ɗinta dikka sun lotsa, yarinya mai kyau da haiba game
da kamala, ga farinjini da sace zuƙatan mutane da murmushi ɗaya kawai!. Tana sanye
da alkyabbarta har kasa launin golden and white.

Ya luluƙa duniyar tinanin da shi kaɗai ya barwa kansa sanin me yake tinawa, dik da
ba'a iya ganin face ɗinsa alamu sun nuna yana cikin kunci da bakinciki game da
damuwa, kwata kwata baya tare da su Anwar.

Nisawa ya yi a lokacin da ya ji saukar hannun Ansar a saman shoulder ɗinsa.

"Mekake tunani ne angon gimbiya?". Cewar Ansar.

Ɗan girgiza kansa kawai ya yi alamar babu komai ba tare da ya yi yunƙurin yin
magana ba.

Anwar ne ya ce. "Our Hero ka kwantar da hankalinka, In Sha Allah ba za'a hanaka
gimbiya ba, da izinin Allah ita ɗin rabonka ce".

Ansar ne ya amsa da. "Gaskiya ya cika sanyawa kansa pressure dayawa, gimbiya fa
ita ta nuna tana sanka, kaga kuwa ina da tabbacin In Sha Allah babu wanda zai yi
maka shamaki a tsakaninku, ko King sai ya sarara a wannan al'amari".

Shi dai ko uppan bai da niyar cewa, hasali ma kansa a ƙasa bai da niyar ɗagowa
bare asa ran zai yi magana.

"Kai ma dai Ansar ka faɗa, dik ya bi ya takura kansa kamar...........".
Ɗaga mashi hannu Ansar ya yi alamar ya yi shiru, dan ya lura da gaske Hoorain
yake a cikin damuwa ba kamar yadda suka saba ganinsa a ɗan siririn damuwa a kan
Zunaira ba, yau abin na daban ne, gabaɗaya yanayinsa ya canza, sam baya cikin
sukuninsa, yana nan a wani birkice haka.

Ni kuwa nace rai wasa ne? Ka ɗauki ran makiyinka ma ya ka kare da faɗuwar gaba da
fargaba bare kuma ka ɗauki ran wadda ta fi kaunarka sama da kowa a duniya?! Ai dole
nema ka birkice, bama kaga komai ba tukun nan, sai gaba idan abin ya yi tsamari,
soyayya ai ba karya bace, aya sukutum Allah ya saukar saboda soyayya,

A cikin Al-Qur’ani mai girma, Allah ya yi magana a kan soyayya a wurare da
dama. Daya daga cikin shahararrun wurare da Allah ya yi magana a kan soyayya shi ne
a cikin Suratul Rum, aya ta 21

Wannan aya tana nuna cewa soyayya da tausayi suna daga cikin ni’imomin Allah,
kuma an sanya su domin mutane su more zaman lafiya da juna a rayuwar aure, so kunga
kuwa soyayya ba karya bace ba kuma abin wasa bace, mukaddari ne daga Allah.

"Hoorain lafiya kake kuwa? Meyake damunka?". Ansar ne ya jefa mashi wanna tambaya.

Sun shiga damuwa matuƙa cikin kankanin lokaci na ganinsa a cikin mawuyacin hali.

Bai amsasu ba, sai ma kara risinar da kansa kasa da ya yi haɗe da kashe hasken
screen ɗin wayar tata yana jan dogon numfashi.

Anwar ne da ƙaguwa da san jin me yake damun abokin nasu ya cika mashi ciki ya
sake jefa mashi tambayar menene yake damunsa a karo na biyu.

Ɗan siririn tsaki ya ja tare da miƙewa cikin zafa ya nufi barin wajen, dan kwata
kwata baya san jin magana a kusa da shi, dik wanda zai yi mashi magana muryar
Zunaira yake ji a tattare da shi, koma wannene, hakan ba karamun ɗaga mashi hankali
yake kara yi ba.

Da ido suka bishi har ya kurewa ganinsu, a tare suka dawo da kallonsu a kan juna
suna mamakin birkicewar da ya yi har haka, basu taɓa ganinsa cikin irin wannan
yanayi ba!.

=========================💘
Cikin ƙanƙanin lokaci commander Zafar ya dawowa King da labarin sarkin Daular
Qahtan wato Qahtaniyawa ne ya zo, kunsan manya manyan labarawa sun kasu kabila
kashi uku ne, nasan dayawa baku taɓa sanin larabawa mabanbanta bane ko? To gaskiya
mabanbanta ne, amma manyan kabilunsu sun kasu kashi uku ne, babbar kabila mafi
ɗaukaka a duniya cikin larabawa sune ƙuraishawan Modarawa, kabilun modarawa daga
cikin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) ya fito, shiyasa ta kasance ma
ɗaukakiyar kabila, daga ƙuraishawan Modarawa sai kuma Qahtan wato Qahtaniyawa, su
ne na biyu, sai kuma larabawan kangi, su ne kabilun da suka fi kowanne shahara da
ɗaukaka a cikin larabawa.

Sosai King Zuhair ya fusata jin cewa sarkin Daular Qahtaniyawa ne ya ziyarcesu,
cikin ɓacin rai haɗe da kakkausan murya ya umarci commander Zafar da a je ya yakesu
yanzun nan ba tare da ɗaga kafa ba!.

To me dalili?.

Wanna furuci tasa ta yi dai'dai da shigowar aunty miemie cikin fada, ta dan tsorata
jin mahaifin nata yana magana da kakkausar murya haka, dan haka sai ta zama mai
risinar da kai game da sanyaya kalamanta da kuma tausasasu a wajen yi mashi magana.

Cikin girmamawa ta tambayesa me yake faruwa a dai'dai lokacin da take zaka saman
kujerar kusa da shi!.

Bai so sanar da ita abin da yake faruwa ba saboda sanin halinta da ya yi, amma
bashi da biyunta a kaf kingdom of power, da ita suke yin shawara, yana kaunarta ya
kuma san ba ta kawo shawarar banza, dan haka sai ya sanar da ita ga abin da yake
faruwa.

Shiru ta ɗan yi na ƴan mintuna tana nazari, akwaita da hangen nesa, shiyasa irin
su King Zuhair masu saurin fusata suna buƙatar irinta a gefensu dan in sun fusata
ta dakatar da su daga ɗaukar hukunci cikin fushi, babu wanda ya fi karfin kuskure
da kuma ayi mashi gyara!!.

"Daddyna Allah ya kara maka tsawon rai da tsawon kwana, nasan yardar da ka bani
yasa ka sanyani a sahun gaba wajen yin shawara domin mu tantance abin da yake
dai'dai da kuma ba dai'dai ba, yardar da ka mun yasa nake jin kaina a matsayin mace
zaƙwaƙura mai yin abin da ya dace, dan yardarka ga mutum ba ƙaramin abu bane, sai
mutun ya cika mai sifofin kamala zai samu wannan matsayi, ina alfahari da kai kuma
ina farincikin kasancewa yar cikinka, bana fatan rana ɗaya da zata zo na saɓa
maganarka komai kankantarta, hakika da dikkanin ƴaƴan duniya zasu samu uba irinka
to tabbas da kowa ba zai so matsawa kusa da mahaifinsa ko nan da can ba, kai ne
bangona kuma farincikina, abin alfaharina sanyin idaniyata ni da ƴan uwana,
duniyarmu gabaɗaya, ɓacin ranka dai'dai yake da rugujewar Daular Qahtaniyawa
daddyna, meyasa zaka ɓata ranka a kan waɗan da kasan already bayinmu
ne?"................. Ta kare maganar haɗe da jefa mashi tambayar tana kallonsa.

Tun da ta fara magana ransa ya fara sanyaya, yana shiga tsananin farinciki a dik
lokacin da ƴaƴansa suka furta suna alfahari da shi, farincikinsa ba mai misiltuwa
bane, hakan yasa ransa ta wani irin sanyaya sosai.

Fahimtar ya yi farinciki da jin kalamanta yasa ta ɗaura da cewa. "Daddyn yin yaki a
halin yanzu da muke cikin nan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, saboda kaga muna da
baki daga ƙasashe daban daban, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa
rayukansu, ina neman alfarmar da a janye batun yakin nan ayi masu lamauni, nasan
kai mai afuwa ne mai kuma tausayin jama'arsa ne".

Sosai su commander Zafar suka ji daɗin furucinta, sun kara ganin girmanta, dama
can suna tsananin kaunarta saboda sanin yakamatanta suna kuma girmamata, bata da
san kai, hukunci cikin adalci take yankewa.

Cike da tsantsar so da kaunarta ya ce. "To Raeesa me kike san na yi masu a yanzu
kenan? Kin dai san babu wanda na tsana a duniya biyun King Abdul Mutallab da kuma
King Al Mustapha".

Nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Na sani daddyna, kuma kana kan dai'dai, amma idan
ba damuwa ni ka bani izinin in je in yi magana da shi".

"Kina ganin hakan zai sakaki farinciki ya kuma biya buƙatarki?".

Jinjina mashi kai ta yi tare da amsawa da e. Dawo da kallonsa a kan commander Zafar
ya yi tare da bashi umarnin da ya yi mata rakiya haɗe da wasu zaƙwaƙuran warriors
ɗin su take mashi baya, kada su bari komai ƙanƙantar wani abin ya taɓata.

Cikin girmamawa suka risinar da kai haɗe da karɓar umarni. Miƙewa tsaye ta yi tare
da karisowa gaban King, ta duka a saman gwiwowinta cikin ladabi da biyayya ta
bayyana godiyarta a garesa haɗe da nuna mashi ta yi farinciki na sauraron korafinta
da ya yi ya kuma yi amfani da shawarinta.

Hannunsa ya ɗaura saman kanta ya fara kwararo mata madarar albarka. Su commander
sai tayata amsawa suke yi da amin ya Allah.

Tsawon 5 mins tana tsugunne a gabansa har sai da ya gama zuba mata addu'oin nasa ne
ya bata umarnin ta tashi su je. Sumbata a goshi ta ɗan miƙe ta kai mashi kafin ta
miƙe tsaye gabaɗaya, ta yi gaba su commander Zafar suka rufa mata baya, alkyabbarta
sai jan kasa yake yi.

===========================💘

Tin daga nesa ta hango sarkin Qahtaniyawa dake a saman koshashiyar dokinsa, kai
daga ganinsa kasan ya ji izza da isa malam, dukiya ta yi mubaya'a, kayan adan da
aka kawata dokinsa da yake kai kawai ba karamar dukiya bace, babban sarki ne mai
isa da izza, sai dai a karkashin Daular kingdom of power suke, sun taɓa bijirewa
umarni da dokikin King Zuhair har ya yakesu.

Warriors sun kai 20 zaƙwaƙuran sadaukai ne suka take mata baya, tana a tsakiya,
commander Zafar yana gefen damanta, sarkin Fada yana a gefen hagunta, kai daga
ganin yadda take taku kasan jinin Modarawa ne yake gudana a cikin jikinta, ga jinin
mulki dake ratsa jikinta, ai kunsan abin ba'a magana.

Ganinta yasa King Al-Mustapah ya buƙaci sauka daga saman dokinsa, dan ko baa gaya
mashi ba yasan ita ta wakilci King Zuhair, dama yasan da wuya King Zuhair ya yarda
ya basu fuskar da zasu iya shiga cikin kingdom of power ɗin ko su sami damar yin
magana da shi kawai dai sun gwada ne dama, kun san ance a rashin ta yi ake barin
arha.

King Al-Mustapah yana sauka daga saman dokinsa dikka sauran ƴan rakiyansa ma
suka yi kasa, suka sauka.

Step biyar tsakaninta da shi ta dakata a wajen tana kallonsa from up to down.

Cikin girmamawa ya yi mata barka da zuwa. A maimakon ta amsa sai ta yi shiru na
tsawon good 2 mins tana kare masu kallo.

Har sun fidda ran zata tankasu, har sun fara tunanin ko dai King Zuhair bai bata
damar ta yi magana da su bane, ko kuma wani abin ake shirya masu.

Sun luluƙa duniyar tunani kamar daga sama suka tsinkayo voice ɗinta tana faɗin.
"Menene ya kawoku nan?".

A kanta King Al-Mustapah ya tsayar da kallonsa, tsohon zumar soyayyarta ce ta
taso mashi, ya so Aunty MieMie kamar hauka, amma King ya hanashi ita sakamakon
tsohuwar mummunar gaba dake a tsakaninsu tun iyaye da kakani, kada ku manta jinin
Modarawa basa yafiya kuma basa matuwa, in baku gaji da faɗa ba ko shekara miliyoyin
za'ayi ana yi ba zasu gaji ba.

Dalilin haukar san ta da yake yi ne ma yasa yake bata girma kamar yadda yake bawa
mahaifinta King Zuhair.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

"Dama mun zo ne muna masu miƙa wuya haɗe da mubaya'a kamar yadda muka buƙata a
baya mai girma King ya ki yarda, bamu gaji ba a wannan karon ma mun sake dawowa da
kokan bararmu a garesa, ki taimaka ki sanar da shi mun durkusa a kan gwiwonmu muna
masu mubaya'a da kaskantar da kai, ya yi hakuri mu koma zama kamar da tsawon
shekaru da suka shuɗe, wanna gaba na iyayenmu ne ba namu ba..............."

Ɗaga mashi hannu ɗaya ta yi alamar ya yi mata shiru, hakan ne ya katse maganar da
yake yi.

Tin da ya fara yin magana ta fahimci akwai zallar munafurci da tuggu haɗe da
sharri da zallar karya a cikin kalamansa, a yanayin karantarsa da ta yi ta fahimci
shigo shigo ba zurfi yake san yi masu, so ta gane komai, shekara nawa tana tare da
waɗan da suka fishi sanin duniya, zata iya cewa dik duniya bata

Please Login or Register in order to submit comment