Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 78 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi kuka. "Aww
dama baki san da kwalliyar ba?". Cikin dariya ya yi maganar!. Takaici kamar Omaid
ya kifa mata mari, shi kallan wawuya yake yi mata, ya tsani wawta a rayuwarsa.
Miƙewa tsaye ta yi, jiki ma ɓari ta isa wajen guyson. "Yah Omar wlh ban san anmun
kwalliya ba, faɗa mun ya na yi?!". A rikice take maganar.

Har lokacin dariya taki sake shi. Hannunta ya riƙo tare da janta suka nufi
gaban tampatsetsan mirror Momma. A wajen ya tsayar da ita tare da nunata ta cikin
mirror da hannu yana cigaba da dariya ya ce. "Look at you". A hanzarce ta kai
kallanta kan mirror. Ai a miliyan ta wani irin zaro idanu waje, take kuma ta ji
wani irin kunya ya kamata, gabaɗaya face ɗinta uban kwalliya na mahaukata. Kunya
tamkar ta natse ƙasa, ta gagara juyowa ta kalli su Momma, sai dariya guyson yake
cigaba da yi, ta tsaya a wajen tsit kamar daskararren man shanu.

Kallan Jaish Momma ta yi tare da cewa. "Me ta yi maka da ka yi mata irin wannan
kwalliya haka?". Ƙasa ƙasa ta yi maganar ta yadda babu wanda ya ji sai ita da shi
ɗin. Nan fa shi ma kunyar rashin kunyar tasa ta motsa, ƙasa ya yi da kai, kamar
yana tsoron yin magana ya amsa da. "Babu kawai na tina abin da ta taɓa yi mun ne a
garinsu". Cike da mamaki Momma ta bishi da kallo. "Kenan yanzu ka tina wacece ita a
gareka?". Kai ya ɗan jinjina alamar e ya tina, kuma ba tin yau ma ya tina ba, tin
ran zuwan Smart, akwai wani rana da ta shiga ɗakinsa a lokacin yana rike da
wayarsa, idan baku manta ba har ya miƙe tsaye yana kallan wayar kuma yana kallanta,
tin a wannan rana ya tina rayuwarsu na kauye, ba komai yasa ya tina ba face kallan
video bikingsu da ya yi a media, ranar da aka yi bikin in baku manta ba na ce maku
akwai masu vivo wato ƴan gayun kauyen da suka rinƙa ɗaukarsu a video, to a wannan
rana ya tina wacece ita a garesa ta sanadiyyar wannan video, amma ya yi shiru bai
nuna mata kamar ya tina komai ba, sai dai zuciyarsa ta gagara hakura har sai da ya
nemi Mahreen ya kalleta ba tare da saninta ba, kaunar Mahreen a jininsa take wlh,
dan ita ta fara kula da shi a kauye, kowa ya gujesa ban da ita, shiyasa take ta
daban a ransa!.

Ganin ta gagara motsawa a wajen ne yasa guyson ya riko hannunta tare da cewa. "Let
me escort you ki je ki wanke face ɗin naki a part naku sai mama Haulat tai maki
wani make up ɗin mai kyau". Sam bata yi musu ba ta bisa, dan dama so take yi ta bar
wajen. Kunyar momma yasa ta gagara motsawa. Ta kasan ido Jaish ya bisu da kallo har
suka fita, sannan ya miƙe tsaye. "Momma ina zuwa". Tsabar farincikin da Momma ta
shiga na tina Mahnoor a rayuwarsa da ya yi yasa ta gagara yin magana, sai sakin
cool murmushi kawai take yi, shi ma ya lura da yadda ta shiga farinciki, ya ji
daɗin abin matuƙa.

Bayan su Mahnoor ya bi, dama ba wani fita da zai yi, kawai ya biyota ne ya ga yadda
zata kare da ƴan gida, wato a fakaice dai ya rama abin da ta yi mashi, ta sanya shi
jin kunyar bappa matuƙa, tamkar ya natse cikin ƙarƙashin ƙasa a wancan ranar, to
shi ma yau ya rama kunya tamkar ta natse cikin ƙasa.

Lokacin da ya shiga bedroom ɗin har guyson ya wanke mata fuskar yana tayata
goge shi da towel, ya ce ta zauna a saman mirror chair bari ya yi mata wani
kwalliyar mai kyau, dan shi ma ya iya make up sosai zamansa da Sharifat a Dubai, so
ta zauna zai yi mata wani kwalliyar mai kyau.

"Waye ya ce ka wanke mata fuska Omar?". Daga bakin kofa suka jiyo voice ɗinsa, a
tare dik suka kai kallansu a kansa, yana tsaye ya ɗaure fuska tamau,wai irin sai ya
ja mata rai sosai kafin ya fahimtar da ita yasan wacece ita a garesa, yanzu ba zai
faɗa mata ya tina komai ba.

"Yah Jaish baka ga kwalliyar bashi da kyau bane? Shiyasa fa na wanke mata zan yi
mata wani". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar!...... "A haka nike san ta rinƙa kwalliya
kullum, kada ka sake wanke mata, kuma a haka zata fita, in bata san a ganta sai dai
kada ta fita daga nan ta zauna, amma ni irin kwalliyar nike so". Ya kai karshen
maganar tare da shigowa ciki, bilhakki da gaskiyarsa fa ya zage yake maganar, wai
irin kada ma su zaci wasa yake yi. Kallan juna suka yi ita da guyson, take idanunta
suka cika da kwallah, kenan sai dai ta yi ta zama a cikin ɗaki ba zata fita wajensu
Chuchu ba?. Ga shi ya ce irin kwalliyar kawai yake so, wannan ai ba kwalliya bace,
hauka ce. Shi ma guyson sam bai ji daɗin batun ba, amma da yake yayansa ne ya
zartar da hukunci, sai kawai ya yi na'am da hukuncin, ya kuma yi dabara ya zame
jikinsa ya gudu abinsa, ba ruwansa da shiga tsakanin ma'aurata.

Yana fita suka ci karo da Mahreen zata shigo part ɗin, dan tin jiya bata haɗu da
Mahnoor ɗin ba. Sai da gabansa ya faɗi, take wani irin fargaba ya lulluɓesa. Sai
dai kuma sai satar kallonta ta katsan ido yake yi, Chuchu ƴar wanka ta tsantsara
mata kwalliya mai shegen kyau, ta wani kele cikin riga da wando arabiyans dress, ta
yi rolling na veil a kanta, gata fara launin kayan dark ash, sai kyanta ya kara
bayyana, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm kamar zai ɗiga, sai wani turo shi take
yi, kamar ma bata san rufe shi sosai, sai wai yauki take yi bata san taka kasa.

Kamar wani maras gaskiya ya ce mata. "Sannunki". Yana magana cike da ƴan kame kame,
kamar fa tsoronta yake ji, shi kaɗai ya bi ya dibirbirce. Harara ta dallah mashi
wadda ta sanya shi haɗiyar yawu da kyar, cike da gadara ta ce. "Kada ka sake yi mun
magana, kai ɗan iska ne ni kuma mai mutumci"..... Kai innalilahi, wai kunji ita mai
mutumci, to ai mutum baya cewa ga abin da yake da shi, dik wanda yake da abu ba sai
ya faɗa ba, mutane da kansu zasu faɗa mashi yana da kaza, dik mai cewa yana da shi
to bashi da shi ne, in yana da ba zai faɗa ba, yanzu fisabilillah kunga Mahreen ta
yi kalar mutumci? Innalilahi wannan yarinya zata kashe mutum da dariya, ko da yake
dama ance yabon kai jahilci ne, kuma hakan ce, jahilci na ɗawainiya da ita shiyasa
take yawan yaba mashi kanta, ban da jahilci ba zata yi ba ai, zata bari ne a
yabeta!.

"Ki yi hakuri". Shi ne abin da ya faɗa mata, kai ta sa zata wuce tana wani
dallar mashi harara da waɗan nan shegun idanun nata masu saka shi ya shiga shakku
da zargin kansa ko ya yi mata laifi ne. Har ta ɗan yi nisa da shi sai ya juyo da
kallonsa a kanta. "Ki yi hakuri Mahreen, ba zan iya dai'na yi maki magana ba, dan
kina daga cikin mutanen dake burgeni nake kuma kauna". Ya faɗa idanunsa a kanta.
Cak ta dakata da tafiyar da take yi, wai irin ita ma zata yi na ƴan gayun nan, cike
da yanga ta juyo, from head to toe ta bisa da kallo kafin ta ce. "Ni kuma bana
sanka, bana mu'amala da ƴan iska, bana san ragwayen mutane, kuma daga yau ba sunana
Mahreen ba, Aunty Chuchu ta ce sunana big girl, dan haka sunan da zaka rinƙa kirana
da shi kenan, big girl". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta cigaba da
tafiyanta. Binta da kallo ya yi yana mamakin yadda take da shegen tsiwar tsiya, wai
big girl, siririn murmushi ya saki, lallai Chuchu ma bata san zaman lafiya da take
koyawa Mahreen rashin mutunci kala kala, yo in banda abin Chuchu ma Mahreen har
za'a kara koya mata wani abin bayan sanka sankan rashin mutuncin da ta iya? Tab
gaba akwai show kenan, lallai kuwa. A wani ɓangare na zuciyarsa kuma tinani ya fara
yi a kan me zai yi ya birge wannan haɗaɗɗiyar babyn mai tafiya da hankalin mai
lafiya, shi dai har yau kome ta yi birgesa take yi!.

Ya jima tsaye a wajen yana tinanin abin da zai yi ya birgeta har ta fara respecting
ɗinsa, daga karshe ya wuce zuwa in da zai je.

Shi kuwa Jaish guyson yana fita ya wuce saman bed ɗinsa ya kwanta yana satar
kallanta ta witsiyar ido, sai da ya kwanta sannan ya ce ta mayar da kwalliyar dake
kan face ɗinta tamkar yadda ta tashi ta gani, haka yake san ganinta. Yana gama
faɗar hakan ya mai da idanunsa ya lumshesu. Shiru ta zauna tana jin tamkar ta fasa
ihu, a cikin zuciyarta ta ce bata san sai yaushe zata ji daɗin rayuwarta ba, kullun
tana cikin ƙunci ita. Cike da damuwa ta fara yin abin da ya umarceta.

Allah ya shirya mana Jaish, ku ce Amin! Wai ya tina wacece ita ɗin ma ba zai barta
ta samu farinciki da natsuwa ba, sai ya wahalar da ita kafin ya faɗa mata yana
santa? Wannan ai iskanci ne, raina ya fara ɓaci fa........🥱

To bari mu leƙa wani wajen mu dawo.
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

BAYAN WASU ƳAN KWANAKI.

Tun da ta tashi da safe yau bata ji motsinsa ba, kuma bata nemesa ba, sai dai a
karkashin zuciyarta ta damu matuƙa da san jin ina yake yau bai leƙota ba? In dai
yana nan baya taɓa ɗaukar 2 hours ba tare da ta sanya shi a idanunta ba, to ina ya
je yau?. Zuciyarta ta jefa mata tambayar da bata da amsarsa. Shiru ta luluƙa
duniyar tinanin dik abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninsu, take irin salon da
ya rinƙa nuna mata a fitansu da suka yi ya fara dawo mata a cikin kwakwalwarta.

Lokacin guda ta saki murmushinta mai kayatarwa wanda ya kan jima bai samu gurbi a
face ɗinta ba, sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta, cikin
ƙankanin lokaci ta tsinci kanta cikin wani irin farinciki na musamman, har da wani
nisawa kamar.......... 🤫

Can kuma da tinanin Sharifat ya ratso cikin brain ɗinta, cikin gaggawa face
ɗinta ya yi saurin canzawa, siririn tsaki ta ja tare da haɗe rai. A hankali ta miƙe
ta sauko kasan bed ɗin, waje ta nufo domin tasamawa kanta abin da zata sanya a
bakin salati, dan yunwa ya fara addabawa cikinta. Kitchen ta nufa, gidan babu kowa
sai daddaɗar kamshi dake tashi. Dattijuwar dake kula da ita ta yi barci a nata
bedroom ɗin dake kusa da na Leesharh ɗin.

Hot tea ta haɗawa kanta mai daɗi, sannan ta ɗauko small chop a plate ta nufo waje,
da alama yau bai yi breakfast a gida ba, dan kuwa alama ta nuna ba'a shiga kitchen
ɗin nan ba yau. Bedroom ɗinta ta koma, bata jin daɗi dai, amma haka ta tuttura abin
da zata iya ci, sai da ta ji cikinta ya ɗan cika, sannan ta miƙe ta fito da kayan
waje, komawa ta yi ta hau gado, ta cigaba da tunane tunanenta wanda babu jimawa
barci ya yi awon gaba da ita again.

Wunin ranar dai gabaɗaya a ɗaki ta wuni, sai zuba barci take yi tana kara tashi.
Wasa wasa sai har karfe 10 na dare bata ji motsinsa ba, abin ya gefata a cikin
damuwa matuƙa, har ji ta yi kanta na yi mata ciwo, tinani ya fi ɗari a cikin ranta,
wani ɓangare na zuciyarta ya ce mata baya nan, wani kuma ya ce mata yana nan yana
cikin bedroom ɗinsa kila wani abin ne yasame shi yasa ya kasa iya fita, dan haka ta
je ta duba shi. Tinani dai kala kala, daga karshe sai ta miƙe ta nufi toilet, a
gurguje ta yi wanka haɗe da ɗauro alwalar barci, fitowa ta yi ta shirya cikin ɗaya
daga cikin sleeping dress ɗinta dake gidan, ta shafa mayukan da ya saya mata, ta yi
shirinta tsab, ta kuma yi kyau sosai abinta, ta hau gado ta kwanta a zuwan zata
share tinaninsa a ranta, amma sai kuma ta kasa, domin kuwa tana kwanciya tinanin ya
dawo mata sabo pil.

Dogon tsaki ta ja tare da miƙewa zaune, hararar ɗakin ta fara yi sai ka ce shi ya
yi mata laifi, siririn tsaki ta sake ja kafin ta zuro kafafunta kasan bed ɗin ta
miƙe tsaye, kai tsaye ta nufi waje, tana tafiya tana harare harare. Har ta kai
bakin door sai kuma ta dawo ta ɗauki hijabi ta ɗaura a saman sleeping dress ɗin
nata, ta wuce tana kumbura kumatu. Kai tsaye ta nufi master room ɗinsa, ko tsoron
nufar ɗakin bata yi ba, amma ta ji tsoron abin da zata tarar dangane da shi,
fargabarta ɗaya ace bashi da lafiya ne ya kasa fitowa waje.

Siririn sallama ta yi a bakin kofar shiga bedroom ɗin. Shiru babu alamar motsin mai
rai da ta jiyo, jim ta ɗan yi kirjinta na bugawa da ɗan karfi karfi, tana fargabar
tura kofar ta ga menene a ciki. Almost 3 mins tana tsaye a wajen, tsananin fargaba
yasa ta ji tamkar ta juya ta hakura da zuwa ta duba shi, amma zuciyarta ta kasa
amsar hakan, ba zata iya barci ba ko ta koma, ba zata samu sukuninta da natsuwarta
ba idan har bata tabbatar da yana lafiya ba.

Tamkar mai rawar sanyi tasa hannu ta tura kofar bedroom ɗin nasa, kirjinta na
tsananta bugawa, da kyar ta sake yin wani sallamar kafin ta kutsa kai ciki. Lokaci
guda ta saki nauyayyar ajiyar zuciya ganin babu kowa a ciki, sai sanyi da kamshin
mai ratsa zuciya dake ta shi, tin da babu kowa a ciki hakan yasa ta fahimci lallai
lafiyarsa lou tin da har ya fita baya nan. Ta ji sanyi a ranta, dan haka ta ɗan
tsaya tana bin bedroom ɗin da kallo na ƴan mitocin da basu gaza 3 ba, tana yawan
jinjinawa tsabta da shegen san kamshinsa, baya shiri da datti ko kaɗan.

Haka ta gama kalle kallenta ta juya da nufin ta bar ɗakin. Step biyu ta taka sai
kuma ta tsaya cak kallanta a ƙasa, kamar wadda aka dakatar. Can kasan maƙoshinta
kamar mai raɗa ta ce. "Ka yi hakuri ba da gangan na shigo maka ɗakin ba, akwai
dalili". Ta kai karshen maganar tare da ɗago da kallanta a kansa.

Yana tsaye a bakin door na shigowa, ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa,
sanye yake da sleeping dress, da alama bai jima da dawowa ba, hannunsa rike da cup,
kamar dai daga kitchen ya fito, da alama tin safe bai ci komai ba, ga alamar wahala
a tattare da shi, yunwa da gajiya ya tattara a saman face ɗinsa, idanunsa sun yi
jajir sun ɗan kumbura, kamar wanda barci ke binsa bashi, face ɗinsa ta ɗan yi fayau
haka, kamar wanda ya taso daga zazzaɓi, sai dai ya yi kyau sosai, lips ɗinsa sun
kara tura red sosai alamar ya ɗan rasa natsuwarsa na ɗan lokaci.

Wani irin faɗuwar gaba ta ji ganin irin dressing dake jikinsa, ga rigar ma gabaɗaya
gabanta a buɗe, wide chest ɗinsa a waje. Ɗauke kallanta daga kansa ta yi tana jin
kirjinta na bugawa da karfi karfi. Ya tsareta da ido babu ko kyauftawa, tabbas ta
yi kyau cikin wannan hijabi, sai dai shi, dressing dake ƙarƙashin hijabin yake san
kallah, ta rufe ta kuntata shi, gabaɗaya kallansa a kan surar jikinta, idanunsa
kamar wani ɗan maye yau!.

"Am...... In..... To..... Ummm zan iya wucewa in tafi bedroom ɗina?". Ta yi
maganar voice ɗinta na sarkewa, kamar wata maras gaskiya. Ɗan ɗage shoulders ɗinsa
ya yi tare da sake saukesu alamar whyn't, zata iya wucewa kenan. Sanyayyar ajiyar
zuciya ta sauke, kanta a ƙasa taki sake ɗagowa su haɗa ido, dressing ɗinsa yana
haukatar da tinaninta sosai, dan haka bata san cigaba da kallonsa yana canza
zuciyarta, zai sanyata ta ci amana a banza, ita kuma ba zata ci amanar Sharifat
ba!!!....... LEESHARH tamu ta amana mai amana, wai ba zata ci amana ba, ta dage fa
a kan lamarinta, ta riki gaskiya da amana, mazamaza ku yi koyi da ita!!......😅

A hankali ta tako tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta matsa kusa da door ɗin, a
tinaninta idan ta matsa zai bata hanya, sai ta ga akasin haka, yana tsaye yana
binta da mayen kallo kamar a buge yake. A ɗan gefensa kaɗan ta dakata, kamar zata
ɗago ta kallesa sai kuma ta fasa, cikin natsuwa ta furta. "To ai babu hanyar wucewa
sai ka matsa"........ Bai san lokacin da ya ɗaga gera guda ba, irin haka ne? Sai
kuma ya ɗan matsa mata hanya kaɗan wanda shi kansa yasan ba zai ishata wucewa ba,
wato dai barin bakin kofar ne ba zai yi ba saboda iskancin nasa yau kuma ta motsa.

Sarai ta fahimci magana yake nema da ita, dan haka sai ta yi kamar bata gane ba, ta
matsa tare da ɗan kame jikinta, ta raɓa shi zata wuce. Yana binta da kallo sai da
ta isa dab da saitin kirjinsa yasa ɗayan hannunsa ya janyota jikinsa, take ya sauke
wani sanyayyar ajiyar zuciya, ita kanta ajiyar zuciyar ta sauke, har da wani ɗan
kwantawa a jikin nasa, irin ita ma tana ra'ayi kenan. Can kuma sai ta tuna da ƴar
uwarta Sharifat, da sauri ta yunkura zata bar jikinsa tana wani ƴan kame kame.
Hannunsa ya ɗaura a saman bayanta kafin ya furta. "Menene kuma?"....... Tamkar zata
yi kuka ta ce. "Yah Ramish Sharifat fa? Kasan dai kai take jira ko?.........". Wani
irin kallo mai kama da harara da ya wurga mata ne yasa ta yi saurin haɗiye maganar
nata.

Gently ya ce. "Daga yau kada ki sake mun maganarsu a nan, na tsanesu dikkansu, kuma
su nike zargi a kan abin da ya faru a tsakanina dake, zan kuma tabbatar da hakan
soon". Zaro idanu ta yi jin cewa Sharifat tana daga cikin waɗan da yake zargi, ita
dai zata iya rantsuwa da Allah Sharifat ba zata aikata wannan ɗanyan aiki ba, ɗan
gara ma Ummie zata iya cewa zata iya aikatawa, amma Sharifat da take baiwar Allah,
yarinya mai hankali da natsuwa, kai gaskiya da kamar wuya wlh.

"Amma Yah Ramish Sharifat fa.........". Yatsarsa ɗaya ya ɗaura a saman lips ɗinta
alamar ta yi mashi shiru, wani irin shock ya ji lokacin da ya ji soft lips ɗin
nata, sai da tsikar jikinsa suka mimmiƙe, da sauri ya ɗauke hannunsa tare da cewa.
"Me kika zo yi a ɗakina ma tukun nan?"....... Shiru ta ɗan yi, dan bata san me zata
ce ya kawota ba, bata son yasan ta damu da shi har ya yi zatan ta fara son shi ne,
dan ita babu gudu babu ja da baya a maganarta. Jinin Hausa Fulani, magana ɗaya take
yi babu sauyi....... My people's mu gaya mata gaskiya ko mu barta duniya ta gaya
mata?. Yen yen yen, wai magana ɗaya take yi ƴar ƙaniya, na make bakinta ne maras
kunyar karya. Ki zauna nan ga su Sahibatu can suna rububin Ramish kamar su mutu,
sai sun kwace shi zaki ga riƙon amana a idonki ƴar ƙaniya.

"Babu amsa ne?. Ko dai kin zo duba ni ne? Kin yi kewata ne?". Cikin ɗan zoyala
ya yi maganar. Lallausan kallo ta bishi da shi mai narka zuciya kafin ta ce. "Ko
ɗaya, meyasa zan zo dubaka? Meyasa zan damu da kai? Meyasa zan yi kewarka bayan
bani da wata haɗi da kai?"........... "Da gaske baki da haɗi da ni?". Kai ta gyaɗa
mashi alamar e bata da haɗi da shi.

Rage buɗuwar idanunsa ya yi, ya zamana tamkar mai jin barci, sannan ya juyar da
ita ta zamana bayanta ne ke manne da kirjinsa, hannunsa dake saman bayanta ya dawo
da shi saman shafaffiyar cikinta, sannan ya rage tsawonsa a in da ya ɗaura kansa a
saman shoulder ɗinta, can ƙasa ƙasa a cikin kunnenta ya ce. "I think ba zan rasa
baby a nan ba, because I play my game yadda yakamata, kuma irin wannan dogon jinya
da kika sha nasan ma dole na ci kwallo". Yana magana yana shafa cikinta.... (Kam
bala'i, wato ma kenan Ramish da gangan ya yi wannan aika aikan? Leesharh ta yi
gaskiya kenan? Bala'in can, lallai ya kai ɗan duniya na karshe wlh, iye wai ya ci
kwallo?.🤔 Yau ga ɗan iska da tsakiyar rana!🤔)

Ai bata san lokacin da a miliyan ta ce. "Wlh babu, kuma ba zai taɓa yiwuwa ba ko
a mafarki, ba zan taɓa haifar ɗan shege ba, wlh babu, babu wani cikinka a jikina,
ni babu komai". A tsananin rikice take maganar, tana yi tana zaro idanu, ya ɗaga
mata hankali ainun, ina zata sanya ranta idan aka ce ciki ya shiga tsakaninsu? Ai
kawai tana ga kashe kanta zata yi....... Ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin yadda ta
rikice haka, koba komai ta sakar mashi jikinta a jikinsa yadda yakamata, da ta wani
takure gabaɗaya baya jin daɗi yadda yakamata. "Kina ganin kamar wasa nike yi ko? To
gara ma ki yarda mu yi aure sai mu haifi babynmu a gidanmu na aure na sunnah, idan
ba haka ba zaki haifi babyn da zaki ƙasa bashi amsar wanene ubansa kuma ya aka yi
kika same shi idan ya titsiyeki". Ya kai karshen maganar yana ɗage mata hijabinta
cikin dabara.

"Na shiga uku na, Yah Ramish da gaske kake yi? Dan Allah ina da ciki? Shikenan na
shiga uku na, na karya maganar da babana yake faɗa mun kullum, na karya alkawarin
da na yi mashi cewa zan kare mutumcina, shikenan yanzu kowa zai san abin da ya
faru? Shikenan kowa zai ganni da cikin da bani da amsar ina na same shi idan an
tambayeni? Sharifat zata ganni da cikinka? Na shiga uku rayuwata ta kare a banza a
wahale tare da rashin madogara!" Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa tab da
kwallah, zuciyarta ya karaya matiƙa, ta shiga tashin hankali da fargaba.

Shi kuwa tura hannunsa ya yi cikin rigarta bayan ya ɗage mata hijabin, cigaba ya yi
da shafa cikin nata, kamar mai raɗa ya ce. "Ina fatan babyna ya yi kama da ni, dan
ma kowa ya san nine ubansa!!". Kam bala'i yau ga tabbatar rashin kunya da bushewar
ido wajen Ramish........ Haba ai kara birkice mashi ta yi, jin hannunsa a saman
fatar cikinta ya sa ta yi gagawar kwace kanta ta raba jikinta da nasa, tini hawaye
sun gama wanke mata fuska, idanunta sun yi jajir, yanzu ta fara tinanin sauyawar da
jikinta ya yi a ƴan kwanakin nan, gaskiya da alama gaskiya a zancensa, ciki ne da
ita, tana da tabbacin cikin ne ma yasa take damuwa a kansa, shiyasa kenan take kasa
iya barci in bata kallesa ba, babynsa kenan yake sanyata dik wannan abin?. Wani
irin ihu mai sauti ta zunduma tare da zube gwiwowinta a ƙasa a wajen, sannan ta
dafe kanta dake barazanar tarwatse mata, kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta saki
mai sautin gaske.

Har cikin ransa ya ji kukan nata ya ratsa shi, sai ya ji wani irin tausayinta ya
ninku a ransa, tamkar zai faɗa mata gaskiyar cewa zolayarta yake yi, amma kuma ya
ji dole ya barta a kan hakan dan ta aminta da shi su yi aure su rufawa juna asiri.
Tsugunnawa ya yi a kusa da ita, ajiye cup ɗin hannunsa a gefensu ya yi sannan ya
janyota jikinsa, ya rungumeta sosai tare da fara rarrashinta. Ai ina, taki
sauraronsa, sai ma kara tsananta kukan nata da take yi tana faɗin ta shiga ukunta.
Shiru ya ɗan yi yana tinanin me ya dace ya yi mata wanda zai iya shawo kanta cikin
gaggawa ta yi shiru su samu su yi magana.
Ya yi iya tinanin da zai yi amma dik ya kasa iya tinano hanyar da zai shawo
kanta, saboda shi soyayya ba layinsa bane, bai kware a kanta ba. Zuba mata idanu
kawai ya yi yana kallan yadda take kukan, har cikin ransa hakan yake sosa
zuciyarsa, ganin fa ba zai iya jurar kukan bane yasa ya yanke shawarar yin abin da
yake ganin ita ce mafita a garesa. Wato ya matsa dab da ita, cikin zafa ya haɗe
bakinsu waje guda domin ya bata hot kiss da zai sanyata haɗiye kukan dan dolenta.

Aikuwa ya yi nasara, dan kuwa suman zaune ta yi mashi, ta yi tsit tamkar ruwa ya
cinyeta, yau ne ranarta na farko da wani ya fara kissing ɗinta, shi kuwa daga neman
hanyar da zai samu ta yi shiru, sai ya zarce da bata zazzafa mai kwance notikan
ƙwaƙwalwa. Bai ma san time ɗin da ya miƙe da ita a jikinsa ba, gabaɗaya ya wuce
balconynsa da ita bakinsu manne cikin na juna, ita dai ta ƙasa koda motsawa, saman
rest chiar ya zauna da ita tare da kara manneta da jikinsa. Sai da ya bata masu
zafi san ransa, sannan ya saketa tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.

Almost 10 mins suna a haka kafin ya

Please Login or Register in order to submit comment