Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 59 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gadan tana ja da baya har suka kurewa jikin bango. Rumfa ya yi mata da
kirjinsa, yana huci ya sake tambayarta ina wayarta? Dan a tinaninsa yanzu kenan
tana hira da maza ta wayar, dan haka a yanzu zai yi rugu rugu da wayar ba kuma zai
sake saya mata wani ba, sai yanzu ya gane ashe kuskure babba ya tapka da bai sanar
da ita cewa ita matar aure ce dan haka ta nisanci mazan waje ba, yazama dole yau ta
san matsayinta.

Shiru ta ki yi mashi magana, hakan ya kara zafafa kunan da ransa yake yi, cikin
fushi ya cire hannu zai ɗauketa da gigitaccen mari. A hanzarce tasa hannu ta kare
fuskarta haɗe da fashe mashi da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Dakatawa da
yunkurinsa ya yi yana huci sosai, ya ɗauki zafin da har zata kaisa ga aikata aikin
danasani, shi da bai taɓa dukan mace ba yau ya kwantanta, kuma a kan wadda yake
kauna fiye da komai, sai ya ji rashin daɗin hakan a ransa.

Cikin zafa ya juya zai je wajen Ammo ya ji dalilinta na barin baby ta kula wani
namijin bayan ita tasan komai. Yana juyawa baby ta yi saurin riƙo hannunsa tana
kuka. Ƙasa ta zube gwiwowinta a gabansa ba tare da ta saki hannun nasa ba, cikin
kuka ta ce. "Tin da nike da kai ban taɓa ɓata maka rai ba a rayuwata sai yau,
tabbas ba zan manta da wannan rana ba a rayuwata, ka yi hakuri baby ba zan kara ba,
na tuba ka ji? Bana fatan wara rana ta zo wadda zan ɓata ran wanda na fi so sama da
komai a duniya, wanda ya so ni ya kuma sanyani da farincikin da ban taɓa zata zan
shiga ba a rayuwata, tabbas na yi kuskure".

So mugun abu ne wani lokaci, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta sanyaya, jin kukanta
yasa ya ji zuciyarsa ta karaya, yana santa baya san kukanta. Dan haka a hankali ya
juyo gareta yana sauke ajiyar zuciya. Ɗan duƙawa ya yi yasa hannunsa ya ɗagota, sai
hawaye take ta shararawa. Rungumeta a jikinsa ya yi yana jin zuciyarsa ta sanyaya.
Sai shessheka take yi, kukan gaske ta yi, dan bata taɓa tinanin ransa zai ɓaci har
haka ba, sai dik ta yi nadamar abin da ta aikata.

"Baby ka yi hakuri ka yafe mun ka ji?". Ta faɗa tana kara shigewa jikinsa. Kasa
ƙasa da kyar ya iya cewa. "Babu komai bab ɗin babynta, komai ya wuce, yanzu ki faɗa
mun ina mutumin yake sannan meyasa zaki fara soyayya da wani ba tare da kin sanar
da ni ba?". Wato dai har yanzu bai huce ba, buƙatarsa a faɗa mashi ina mutum yake
kawai.
"Am so sorry my baby, wasa nike yi maka, ni babu wani da nike so a duniya sai
kai". Wani irin ajiyar zuciya mai sanyin gaske ya sauke, cikin sauri ya ce. "Are u
sure?". Kai ta gyaɗa mashi alamar yeah.

Ai bai san lokacin da ya rungumeta kam a jikinsa ba, bai ma san time da ya hau zuba
mata ruwan albarka ba, cikin sambatun nasa ne yake haɗawa da. "Kada ki yarda ki
kula kowa, ke ɗin mallakina ni kaɗai". ....... "Baby mallakinka kuma?". Ta faɗa
irin like bata san komai ba.
Kai ya jinjina mata tare da amsa mata da e. "Baby to kenan ba zan yi aure ba
tun da ni mallakin ka ce". Cikin shagwaɓa ta yi maganar dan ma ya ɗauka har yanzu
yarinta na damunta bata san komai ba........ Wato ita ma baby yar duniya ce fa,
tasan kan tsiya kala kala, wai ya ɗauka har yanzu yarinta na ɗawainiya da ita bata
san komai ba.

"Babu wanda zaki aura sai babynki, ke ɗin matata ce ni kaɗai, dan haka kada ki
kula kowa kin ji?". Da alama yana out of control yake wannan sambatu, dik dan
murnar bata kula kowa bane fa, kamar ba yanzu ya gama bambami kamar zai tashi gidan
ba.

"Baby kai zaka aureni kuma?". Ta tambaya like bata gane me yake nufi ba........
"Yeah ko baki san hakan ne?". Ya jefa mata tambayar tare da ɗan raba jikinsa da
nata yana kallan face ɗinta dan yaga reaction ɗinta. Tafukan hannayenta ta kai ta
rufe face ɗinta tana murmushi.

Shammatarta ya yi ya ɗauketa cak sai saman bed yana faɗin. "Kin ɗaga mun
hankali over, kin sa na ji wani irin, dan haka yanzu zo mu yi hira babu in da zan
je, kwantar mun da hankali kamar yadda kika ɗaga mun, yau i think ma a nan zan
kwana". Ya kai karshen maganar yana kwanciya da ita a saman bed ɗin.

A cikin kirjinsa ta tura kanta tana faɗin. "Zan ji daɗi idan ka kwana a nan,
dama haka nike so, kwantar da hankali kuma yanzu kuwa zan kwantar maka".
Rungumeta sosai ya yi tare da ja masu bargo ya rufesu har kai. .............To
baby sai dai mu ce asuba ta gari Allah yasa iya barci kawai baby zai yi....👀🥱
Bari mu leƙa wani part mu dawo muga ya za'a kwantarwa da baby hankali, sai mun bi
kwakkwaf😅

🔥🔥🔥BLACK WORLD.🔥🔥🔥

Yau ta kama Sartuday, bayan kwanaki biyar kenan da fara zuwan Sweetie school, daren
yau za'ayi babban partyn su Ronnie. Tin safe ake ta shirye shirye, kayan da Black
Tiger ya sayawa Ronnie da zai saka a wajen wannan party lallai ba'a taɓa wani ɗa da
ya taɓa sanya kwantankwacin irinsu a faɗin birnin ba, dan kuɗin kayan kawai ya kusa
kuɗin jirgi guda ɗaya cikin jiragen Black Tiger.

Tun kwana uku da suka wuce Ronnie da Sweetie suka haɗu suka zaɓi kayan da suke ga
ya yi masu da irin design da suke so, kayan ya haɗu matuƙar haɗuwa, three-piece
suit ce ajin karshe a tsada na Ronnien, cover shoes da zai haɗa da kayan ma almost
hundred million take. Ita kuwa Sweetie dama wani irin daddatsetsen gown ya zaɓa
mata wanda ya sha kwalliyar duwatsu na alfarma, kayan sun kai makurar haɗuwa, sai
dai fa ita da Floris aka saya masu iri guda, kuma Ronnie ne ya ce hakan, dan shi
har yau har gobe yana san Floris sosai, matsayinta bai canza a zuciyarsa ba, ita ce
dai ta ja baya da shi.

Kayan nasu ita da Ronnie kalarsa ɗaya, yadda kuka san amarya da ango, dikka milk
color ne, sai murna Ronnie yake yi ana ta hidima, jama'a na ta kai koma, dama jiya
za'ayi partyn fa, sai Sweetie ta ce da Ronnie a ɗaga zuwa yau saboda girma da
falalar ranar jumma'a bai kamata su yi party a ranar ba. Aminta ya yi da hakan
shiyasa ya riko yayansa da a ɗaga wannan taro zuwa yau, da yake Black Tiger bai san
dalilin ɗagawar ba sai ya yarda, da yasan saboda addinin Sweetie ne ba zai yarda a
ɗaga ba, saboda bayan san musulunci, a jininsa tsanar addinin take. Kada ku manta
autan ruhohi ne shi ɗin, kunga tsanar addinin a jininsa take.

Abin da baku sani bama, da Ronnie ya same shi da batun dakatar da halaccin luwaɗi a
birnin sai ya ce kowa yana da ƴancin yin abin da yake so, dan haka shi ya halatta
yin hakan, kada Ronnie ya kara zuwa mashi da wannan zance kuma kada ya kuskura ya
hana kowa aikata luwaɗi ko zina, shi ya yarje masu su yi, su more rayuwarsu.
Da farko Ronnie ya damu sosai, har yake jin kamar ya gudu ya bar birnin
saboda kyamar abin dake ransa, amma Sweetie ta tsaya tsayin daka wajen nusar da shi
cewa ya yi hakuri watarana komai zai wuce, ba'a da'awa cikin sauki dama, kuma dama
yadda suke ƙoƙarin nan dole shaiɗan ba zai so hakan ba, idan shaiɗan ɗin ya gwada
ringayarsu ta ɓangarensu suka ki yarda Allah ya tsaresu daga sharrinsa, to sai ya
koma masu ta wani ɓangaren, tana da tabbacin shaiɗan ne ya koma jikin Black Tiger
yasa yaki yarda da wannan doka, dan haka ya kwantar da hankalinsa zasu yi nasara a
kan big bro, da sun yi nasara kuma shikenan komai zai tafi yadda suke so, da kansa
zai yarda da dokar, su zasu zama masu kafa doka kai tsaye ma ba sai sun ji ta
bakinsa ba.

Da kyar dai Sweetie ta iya shawo kansa ya yarda, dik wani abin da Sweetie zata ce
addininta ya yi hani da shi to shi kuma Black Tiger sai ya halasta wannan abin wa
ƴan birnin, dik dan kiyayyarsa ga Musulunci, amma dik da haka Sweetie bata taɓa
nuna ta damu ba, saboda tana koyi da annabawan Allah waɗan da suke da hakuri da
juriya mai tarin yawa dan cinwa nasara...... ALLAH KA BAMU IKON YIN KOYI DA SU.

••••••••••••••••••••••••••••♥️

An ƙawata hall ɗin da za'a gudanar da wannan party matuƙa, yanayin tsarin hall ɗin
hakika ya ƙayatar kuma kowa ya gani yasan anzubar da makuɗan kuɗaɗe ba kaɗan ba.
Kayan Ado wato decorations masu zafi da tsantsar kyau. Yanayin theme na wajen
launin white and gold ne, an zubawa gold ɗin kwayaye masu bata haske a in da suka
kara haskaka wajen matuƙa, gold ɗin ya kara haske da ƙawata wajen.

A gabaɗaya wajen an ƙawata shi ne da wasu irin kyawawa kuma tsadaddun balloons,
furanni masu kyau, da kujeru masu rufi (chair covers) da ribbons masu launin gold
and white. A saman haɗaɗɗun tables dake wajen gabaɗaya akwai wasu centerpieces masu
kyau irin su furanni, kyandiru da fitilu masu kyalli da suka kara ƙawata wajen.

Tables na wajen sun kasance a tsari mai kyau. Table da tsadadden kujerar da
shugaban party zai zauna wato VIP table a gaban hall ɗin yake, yana fuskantar kowa
kenan. Wajen da aka shirya abincin da aka shigo da su dan rabawa a wajen part ɗin
yana ɗan nesa da wanen tables ɗin.

And manya manyan fitilu dake wajen masu duhu ne amma na alfarma, ga wani katan
chandeliers mai wuta launika daban daban da ya kara ƙawata wajen a sama tsakiyar
hall ɗin. Wajen kujerar zaman Ronnie namu and Black Tiger namu ya kasance da ƙarin
haske na musamman don jama'a su samu damar ganinsa da kyau. My people's wajen nan
ya haɗu, kuɗi sun yi kuka, tun daga kan tsarin wajen zaku gane ɗan gata kuma
shalele ne zai yi party, abin ya haɗu fiye da tinaninku.

Shi kansa Black Tiger sai shirye shiryen zuwa wajen yake yi, dan tun karfe 4 na
yamma za'a fara, kwana za'ayi ana yi. Ronnie kuwa tini ya gama shirinsa, dan yau
rana ce ta musamman a garesa, yau zai shiga office ɗinsa a matsayinsa na babban Dr,
apart from this hospital ɗin gabaɗaya mallakinsa ne. Ku kunsan abin ba'a magana sai
shiru!!.

Tin karfe uku Ronnie ya tafi wajen part da nufin Sweetie zata biyosa daga baya, dan
ita ta ce sai 4:30 zata zo, zata ɗan yi barcin rana ne, ya so su jera a tare, amma
taki yarda. Sam bai nemi Floris ba, saboda yana tinanin zata zo a tare da Sweetie.
So sai ya yi gaba, ya sha kwalliyarsa, sai dai har yau yana saka waɗan nan chairs
and ring ɗin, ga earing, a yau ma dik ya zubasu a jikinsa, ya yi kyau kam matuƙa
sai dai haramun ne, amma ya yi wa Sweetie alkawarin a hankali hankali zai dai'na
sakawa In Sha Allah, ta taya shi da addu'a. Kun san sabo da yin abu barinsa lokaci
guda abu ne mai wahala

Sai dai kuma tana can part na master Devil ba tare da sanin kowa ba, akasi aka samu
tsakaninta da master ya yi mata fyaɗe, ya yi mata fyaɗen kuma ta ji ciwon sosai da
yasa ta rasa jini sosai, kun san ba za'a haɗata da master ba dama, shararren mai
bawa ƴan Wrestling horo, zakwakuri kuma zakaran da ya buge kowa except Black Tiger
and Ronnie a faɗin birnin, namiji mai ji da karfi da lafiya ita kuma ƴar yarinyar
da bata wuce Sweetie ba, da kaɗan ta fi Sweetie fa, kun ga kuwa dole karonsu ba zai
yi kyau ba, ya kuwa yi mata fata fata saboda bashi da imani da tausayi, ko da yake
shigarsu na banza ya ja masu ai, yana kan network ta samesa, shi kuwa ya cika aiki
ya rage zafi da ita, ɗan ikka, ko da yake ba laifinsa bane, dik maza masu yin gym
shegen jarabar tsiya suke da shi, saboda gym da suke yin nan yana kara buɗa
jijiyoyin jikinsu ya faɗaɗa halittarsu hakan yasa sha'awarsu yake yawaita matuƙa ta
yadda ba zasu iya zama babu mace a kusa ba.

So master yana tsoron fitar da ita zuwa hospital dan a iya saninsa yasan cewa
budurwar Ronnie ce ita, so fitar da ita zai iya haifar mashi da babban matsala mai
girman gaske, hakan hasa ya turata cikin toilet ɗinsa, a cikin jacuzzi ya sanyata
ya rufe kofa da key, jininta na ta zuba har ta rasa ranta ba tare da ya sani ba,
shi a cewarsa sai dare zai ɗauketa zuwa hospital a lokacin babu wanda zai sani, bai
san cewa rai ya yi halinsa ba.

Sai dai fa dik abin da ya faru Black Tiger ya sani, amma ko a jikinsa saboda bashi
da wata alaƙa da hakan, dama Floris Ronnie ya kawota empeir ɗin, dan haka shi ko
cin namarta ɗanye ake yi ba abin da ya sha mashi kai, shi idan kunga yana magana a
kan abu to fa ta shafe shi ne, idan bata shafesa ba ko kallo baya ɗaga idanu ya yi.
So dik abin da suke aikatawa yana sane da kowa.

Fyaɗen da master ya yi wa Floris ne yasa bata zo janyo mashi Sweetie ba, kunga babu
ta hanyar da zai samu Sweetie, da ya tabbatar wannan dama ta kubce mashi, cike da
ciza yatsa na zafin rasa wannan dama ya fara ƙoƙarin shirya ta yadda zai yaudari
Ronnie ya fitar da shi daga birnin, su je wajen birnin ya biya buƙatansa da shi
kafin ya halaka shi, amma fa dik a tafin hannun Black Tiger yake dik wani
shirinsa........... Hmm da shi ya raina capacityn Black Tiger ne, a tinaninsa ai
baya kallan cikin ɗakinsa shiyasa idan ya shiga cikin yake sheke ayarsa son ransa.
Bai san gar Black Tiger ya san komai ba, dik sheke ayar da suke yi shi da su Oxil
yana sane da su, harta aman da Ronnie ya rinƙa yi ranar dik yasan da hakan.

(Wato guy ɗin nan Black Tiger ɗan duniya ne, wato dik wani iskancin da suke yi yana
gani?🤔 Anya Black Tiger yana da feeling kuwa?🤔 Ina ƴan team ɗinsa? Maza ku fito ku
faɗa mana ya aka yi yake iya kallan dik wani iskanci kuma baya jin komai?🤔)

••••••••••••••••••••••••••••••••••••♥️

Da misalin karfe huɗu dai'dai bayan Sweetie ta yi sallar la'asar, wanka ta
tsantsara, ta shirya cikin wannan gown ɗin, da kanta ta gyara gashin kanta, Ronnie
ya ce zai kawo mata mai gyata ta ce bata so, zata yi da kanta, dan haka da kanta ta
gyara kayanta.

My people's Sweetie ta yi masifar kyau a cikin waɗan nan kaya, omg, her wellcome
and goodbye so masha Allah, ta ko'ina tana cike ɓulɓul, yar 13 years kamar wata ƴar
15, sai kara cika take yi dan hankalinta a kwance yake tana samun farinciki sosai
daga bro ɗinta Ronnie, wani ɗan siririn chain na zinari da Ronnie ya bata ta sanya
a wuyanta, ɗaya daga cikin chains da yake sakawa ne, ta ce ya yi mata kyau sai ya
bata, tsadar bala'i ne da ya shi.

Kara haskakawa gurun wuyarta ya yi, ga fararen hakwaranta na kara haskawa, wlh kyan
da ta yi a yau baki ba zai iya faɗarsa ba, ku hasko yadda wannan golden hair ɗin
nata yake kyalli, ba'a gyara shi bama tin ainahinsa mai kyalli ne bare kuma ya sha
gyara? Ku kanku kun san dole ta tafi da imanin dik wanda zai kalleta.

Wasu shegun high heel ta sanya a kafafunta, irin covers ɗin nan ne, rigar tata na
ja mata har ƙasa, a gaban mirror ta tsaya, ta juya ta sake juyawa, ita da kanta
tasan ta yi kyau. Black Tiger yana ƙoƙarin nasa shirin shi ma, so hankalinsa sam
sam baya a kanta.

Haba cikin wani irin taku mai kama da tafiyar hawainiya ta nufi waje, sai tashin
kamshi take yi, kai tsaye bedroom na big bro ta nufa, tana tafiya tana wani yauki,
dik Ronnie ya koyawa yarinyar nan sanka sanka na iyashege wlh, kowani rana sabon
babi take buɗewa.

Dai'dai lokacin da ta buɗe kofar ta danno kanta ciki, shi kuma yana tsaye a kusa da
bed ɗinsa yana ƙoƙarin ɗaura necktie na wuyarsa. Ya subhanallah, my people's Black
Tiger ya haɗu, idanunsa kalar nata sak dama idan baku manta ba na faɗi wannan,
yadda kuka san ya karawa idanun kala, sai suka yi olive sosai, da alama hankalinsa
a kwance yake.

Sanye yake da three-piece suit shi ma irin na jikin Ronnie, da kalar da komai
iri ɗaya ne, ya yi masifar kyau sosai, mutum zai iya ɓata tsawon wuni guda yana
kallan guy ɗin nan bai gaji ba!

Dark black curly hair nan nasa ya yi mata wani irin gyara na musamman da ya sha
bambam da gyaran da yake yi kullun, kai daga ganinsa kasan yau rana ne na musamman
a garesa.

Tana shigowa ƙamshin perfume ɗinta ya haɗe da nasa sai ya bada wani sihirtatcen
kamshi na musamman. Tin da ta shigo idanunta suke a kansa, baki ta saki tana kallah
halittar Allah, lallai ba shakka Allah ya yi halitta a wannan waje, Black Tiger ya
haɗu.
Like wow abin yaƙayatar over, ita da shi sai suka fito tamkar amarya da ango,
saboda yanayin shigarsu. Sarai ya ji shigowarta, amma yaki ɗagowa ya kallesa, dan
kada ku manta kashin wuyarsa ta zame mashi. Tin daga kan haɗadɗun cover da suke
kafafunsa har zuwa dark black curly hairnsa ta bi da kallo a cikin zuciyarta tana
furta wow. Kuma abin da zai baku mamaki da ita dik wannan yabon kyansa da take yi
tana mutuwa da san kallansa fa bata taɓa jin sansa a ranta ba, ita dai Kamran take
so, shi kuma yanayi mata kyau tana jin daɗin kallonsa, hasali ma ta fi jin Ronnie a
ranta sosai fiye da shi, ko kila saboda krista ne yasa hakan?.

Misali yanzu da ace babu Kamran to tabbas zata iya yin soyayya da Ronnie, amma ban
da Black Tiger, amma fa Kamran na raye, dan haka babu kowa a ranta sai shi.

Cike da yanka irin ita mai class ɗin nan ta tako izuwa gabansa, zuciyarta na
harbawa da karfi tasa hannu ta riko necktie ɗin nasa da yake ƙoƙarin ɗaurewa tana
faɗin. "Big bro bari in hutar da kai".

Sam baya san ɗaga ido ya kalleta, dan haka sai ya yi ƙasa da idanunsa wai dan ma
kada su haɗa ido. Sai da unexpect ya sauke kallan nasa a kan yatsun kafafunta. Waro
idanu ya yi da kyau a kansu, da yake ta cire takalman nata a kasan carpet dake
gaban bed ɗin kafin ta ƙariso in da yake, hakan ya bashi damar ganin yatsunta,
sosai ya zaro idanunsa waje a kansu. Kafarta na dana yatsunta guda shidda ne ba
biyar kamar na sauran mutane ba. Ganin hakan ya yi mugun ɗaga mashi hankali, lokaci
guda ya ji jiri ya ɗebesa, kafin ya ankara ya tafi zai kifa, gabaɗaya ya rinjayeta
suka faɗa saman mattress ɗin, tsikar jikinsa ne ya fara tashi sosai na ganin yatsun
nata da ya yi.

To me dalili kenan?.

Jikinsa har kerma yake yi, lokaci guda ya ɗago da kansa da kallonsa a saman face
ɗinta, ya danneta ta yadda ko numfashi bata iya yi da kyau. A take idanunsa suka
rikiɗe suka yi jajir kamar wuta, kwayar idanunsa suka tura olive sosai, harta
kumatunsa sai da ya fara kerma kamar mai rawan sanyi, wani irin yanayi da ya shiga
ya in ka gansa sai ka razana.

Lokacin guda ya fara yin wani irin jijjiga mai karfi gaske a kanta. Wani irin
mahaukacin razana ta yi, bata san lokacin da ta fara ambatar sunansa da kyar da
kyar tana ƙoƙarin yadda zata yi ta turesa daga kanta, da yake yana kanta sai tana
iya jiyo yadda zuciyarsa take harbawa da karfi karfi gudu gudu sosai na wuce
misali.

Hankalinta ne ya ƙara tsananta tashi sosai, cikin ruɗani ta rinƙa ƙoƙarin turesa
daga kanta, amma ta ƙasa koda motsa shi. Shi kuwa ya ɗauki a kallah minti biyu yana
wannan jijjiga kafin gabaɗaya ilahirin jikinsa ya sake alamar ya mutu ko ya suma a
kanta. Tashin hankali, to ita yanzu tayaya zata iya cetan ranta? Kun dai san ba iya
ɗaukar nauyinsa zata yi ba ko? Ga shi ko numfashi bata iya yi, wai menene ma ya
rikiɗashi lokaci guda haka? Meyasa ya shiga wannan hali daga ganin yatsunta shidda
ne ba biyar ba?. Uhm akwai matsala fa.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Azabar da ta ji tamkar zata mutu ne yasa ta ware tafukan hannunta tana san yin
amfani da magic ɗinta ta ɗaga shi daga kanta. Ta kuwa yi sa'a ta samu damar yin
hakan. A gefenta ta kwantar da shi, sannan ta shiga mayar da numfashi da karfi
karfi, kun san idan mutum ya rike numfashinsa na ƴan sakannin yana saki da karfi
karfi zai fita. To haka ita ma ta yi, ta kwanta shiru tana mamaki wani irin masifa
ce yau take shirin faruwa da su kuma? Black Tiger da suma? Kai abin babba ne dik da
a wajen Allah wannan ba komai ba ne, amma da mamaki daga kallan yatsun kafafunta
sai ya suma, dik taurin zuciyar da balai'nsa, ga magic, amma farar ɗaya ya sume
haka? Kai akwai matsala gaskiya.

Ta ɗauki a kallah 3 mins kwance shiru haka kafin ta samu numfashinta ya daidaita,
miƙewa tsaye ta yi da kyar, har lokacin tana yin ɗan nishi kaɗan kaɗan alamar da
gaske ya yi mata nauyi over. Juyo da kallonta a kansa ta yi, yana kwance flat
tamkar babu rai a jikinsa. Shiru ta ɗan yi tana tinanin abin da ya faru da ita
daren jiya ga mafarke mafarken da ta rinƙa yi.
Me ya faru daren jiya kenan?.

Saman bed ɗin ta haye, a daidai wajen kansa ta zauna tare da haɗe hannayenta dikka
biyu ta tallabo kumatunta idanunta a kan face ɗinsa. Cikin natsuwa ta fara ambatan
sunansa da big bro. Sai dai ina ko motsawa bai yi ba, cire hannunta ɗaya ta yi daga
kumatunta ta mayar saman nasa kumatun.

A zabure ta zare hannunta daga jikinsa saboda wani irin azabbabben zafi da jikinsa
ya yi kamar wuta, lokaci guda jikinsa ya yi wani irin zafin zaw. Miƙewa daga zaune
ta yi ta durkusa a kan gwiwowinta, sannan ta kai hannunta saman necktie da yake
ƙoƙarin ɗaurawa kafin ya sume. Kwance tie ɗin ta yi ta ajiye a gefe, sannan ta hau
ɓalle botiran rigar jikinsa, ta buɗe rigar sama ya rage saura na biyun da na ciki.
Addu'oi ta fara tofa mashi tana fatan Allah ya tashi kafaɗunsa, tana san zuwa ta
kira Ronnie amma bata san tafiya ta barshi dan bata san me zai iya faru a bayanta
ba, baya bata kaɗan.

Ta jima sosai tana yi mashi tofin addu'oi ba tare da wata barazana ba, sannan ta
sauko ƙasa ta nufi toilet, bowl ta ɗauko mai ɗauke da ruwa mai sanyi a ciki, sai
towel fari tas ɗan madaidaici da ta ɗauko. Har zata nufosa sai ta ce bari ta ɗauko
almakashi dan ta tsaga singlet ɗin jikinsa tun da shi bashi da botir bare ta buɗesa
kamar yadda zata buɗe sauran kayan jikinsa, ba iya ɗagasa zata yi ta cire shi ba
kuma, so dole ta tsaga shi da almakashi kawai.

Dan haka sai ta duba a cikin drawers ɗinsa, a wajen mirror ta samu almakashi. Har
zata juya ta bar gaban mirror idanunta suka sauka a kan wajen partyn Ronnie da abin
da yake faruwa a wajen. Shiru ta ɗan tsaya tana kallan gabaɗaya al'ummar dake
wajen, lokaci guda ta ji wani irin mummunar faɗuwar gaba a lokacin da taga fuskar
Ronnie, shi kuwa sai murna yake yi yana farinciki.

A cikin zuciyarta ta ce. "Dik in da faɗuwar gaba yake ba alkhairi bane yake biyowa
baya, ya Allah ka dubemu da idanun rahma, ina jin kamar wani abin ne zai faru, ga
big bro ya suma, idan na tina Ronnie ko in na gansa sai gabana ya faɗi, ya Allah ka
juya mummunar kaddararmu izuwa kyakkyawa ko kuma ka sassauta mana ita daga cikin
niimominka ya rahmanin rahim". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta nufi Black
Tiger, tana tafiya tana waigo mirror nasa.

Har ta haye saman bed ɗin hankalinta

Please Login or Register in order to submit comment