Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kirki ne ya faru.

Tun daga bakin kofa bappa ya fara tsinkayo shesshekar kukanta, hakan ya bashi damar
kara ɗaga kafa domin ya isa gareta. Tana a kwance saman mattress ɗinsu, ta haɗa kai
da jikin pillow sai kuka take yi kamar ance mata Jaish ɗin mutuwa ya yi ko kuma ba
zai dawo ba har abada, ko da yake hakance fa tun da su Ramish sun tafi da shi
Abuja, ya bar Adamawa kenan.

Sam bata ji shigowar bappa ba, sai dai ta ji an zauna kusa da ita, kamar mai
raɗa ya ambaci sunanta, daga jin muryarsa cike yake da karaya haɗe da sagewar dik
wani kwarin gwiwa da yake da shi, ba komai yasa ya ji wannan rashin kwari da cire
tsammani ba face yadda suka ɗauki Jaish ba tare da sun buƙaci ganinsa ba.

Bugu da ƙari Mahreen ta gaya mashi basu yi wa kowa magana ba, sannan shi ma Jaish
bai buƙaci da su nemi kowa ba, tun daga nan bappa ya yanke tsammanin Jaish zai
waiwayesu, kuma hakance, dan dakamar wuya, su Ramish basu kyauta ba da basu nemi
bappa da ya riƙe masu ɗan uwa tsawon watanni kusan shekara ba, hakan ya nuna sun
nuna basu son wata alaƙar dake tsakani and basu da buƙatar sake waiwayar garin,
gaskiya basu yi halarci ba sam.

Amma da yake su maza ne basu ji komai game da hakan ba, da mata ne suka zo
ɗaukarsa kun san dai dole zasu nemi wanda ya riƙesa, dayawan lokuta a irin wannan
part ɗin maza basu san me ya dace su yi ba, kullum suna tunani ne irin na maza basa
waiwayawa su duba raunin tunani, idan kuma ya haɗe masu babu mace a gefensu sai
taɓarar tasu ta kara yawa, su kasa yin abin da ya dace, da akwai mata a gefensu
cikin wannan tafiya wlh ba zasu bar kauyen nan ba sai sun nemi bappa sun yi mashi
godiya har ma su yi mashi kyauta!!.

Ta ji voice ɗin bappanta, amma kuma bata iya amsa mashi ba, saboda kukan da ya
fi karfinta, da sauri Mahreen ta ƙariso wajen, saman mattress ɗin ta haye tana
amabatar Mahnoor, Mahnoor.

Bappa ya rasa me zai ce mata, ya rasa da wasu kalamai zai yi amfani wajen shawo
kanta, ya rasa me zai yi, ya zauna shiru ba zai iya jure kukanta ba, ya yi rarrashi
kuma bashi da kalaman faɗe.

Sallamar da suka ji a tsakar gidan ne ya ja suka kai kallonsa bakin kofa shi
da Mahreen.

"Kawu Ibrahim ka shi go mana". Cewar Mahreen.

Allah sarki, shi bappa da farko ma bai ɗago muryan mai sallamar ba, tsabar yana
cikin damuwa, sai da ya ji Mahreen ta ce kawu Ibrahim ne ya gane.

Hannun Mahnoor ya riƙo tare da ce mata. "Zo muje".

Ba musu ta tashi ta bisa. Waje suka fito, Ibrahim kanin mamanta yana tsaye rike da
wata sanda a hannunsa, ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Idanunsa jajir
kamar wuta.

"Jaɓɓama lale Ibrahim". Cewar bappa.

Da yauwa ya amsa idanunsa na a kan Mahnoor da dik fuskarta ya yi jajir kamar jan
kosai saboda kuka, kun san farar fata idan tana kuka, har wani ja na musamman face
ɗin yake yi, bare ma wajen dogon hancin nan nata ya yi jajir sosai.

Matsowa ya yi ya karɓeta daga hannun bappa yana faɗin ta yi hakuri. Ɗan
kwanciya ta yi a jikinsa tana ɓoye fuska, soyayyar Jaish ya ja ta manta da batun
kunya har ta bari kukanta na rashinsa ya fito fili kowa ya gani, sai a yanzu dik ta
ji kunya ya mamayeta. Sai ta wani ɓoye fuska a jikin kawu Ibrahim.

"Ibrahima lafiya kuwa?". Cewar bappa, ya yi tambayar ne bisa ganin kamar ran
Ibrahim ɗin a bace, ga idanunsa sun yi jajir sosai.

"Babu komai babbo, dama na zo kara tabbatar da abin da na ji kuma nasan dama
zai iya faruwa ne, amma kukan Mahnoor ya riga da ya bani amsa".

Shiru bappa ya ɗan yi dan bashi da abin sake cewa, Jaish ya jefa shi cikin matsala,
ga yanayin al'adarsu yanzu zasu ɗauki laifin dik su ɗaura a kansa, bare dama ya
hana Faisal ita, ai shikenan kuma ya kara shiga uku da dangi, sai kuma abin da
Allah ya yi.

"Bobbo zan tafi da Mahnoor zuwa gida". Ya yi maganar ne rai a dakile, dan idan
ransa ya kai miliyan wlh a yau ya ɓaci sosai, tin ainahi yana balain tausayawa
Mahnoor baiwar Allah.
Bappa bai iya ce mashi ko uppan ba, dan bai san me zai ce mashi ba, kuma at this
point bai isa ya ce zai hana shi tafiya da ita ba, shi kansa zai so a tafi da ita,
su je Inna ta rarrasheta ko za'a samu ta yi shiru.

Ibrahim ya lura da cewa ɓacin ran da yake ciki sam ko rabin na bappa bai kai ba,
dan ya lura bacin rai ya hana bappan yin magana. Dan haka sai ya ɗan sassauta ya
danne nasa ɓacin ran ya ce. "Bobbo bari muje ko?".

Kai kawai bappa ya iya gyaɗa mashi ba tare da yin wani yunkuri ba. Jiki ba kwari
Ibrahim ya ja hannunta suka nufi waje, sai binsu da kallo bappa yake yi. Da sauri
Mahreen ta bi bayansu, dan kun san tana kaunar ƴar uwarta.

Suna tafiya bappa ya shige cikin ɗakinsa, saman ƴar gadonsa ya hau ya kwanta, ya yi
iya yinsa ya rufe idanunsa ko zai ji saukin abin da yake ji har barci ta yi awon
gaba da shi, amma ina ya kasa, idanun ma sun ki rufuwa.

Kamar a mafarki ya hango suit ɗin Jaish da suka tsinto shi da shi makalle a jikin
kusa ta bayan kofar shigowa, tun ranar da bappa ya cire mashi suit ɗin ya makala a
wajen babu wanda ya taɓa taɓa shi.

A hanzarce ya miƙe zaune a saman gadon, tunani ya fara yi a kan watakila zai iya
samun wani abin mai muhimmanci a cikin aljihun kayan, hakan yasa ya yi saurin
miƙewa tsaye, da sauri ya diro kasa.

Kai tsaye kayan ya je ya ciro, a bakin gadon ya koma ya zauna, dik jikinsa a mace
bawan Allah. Aljun kayan ya fara laluɓewa. Cikin sa'a ya fito da wallet a aljihun
wandon.

Ɗan kurawa wallet ɗin ido ya yi kafin ya ajiye a gefe ya sake mayar da kallonsa a
kan kayan.

A aljihun rigar ya ciro dalleliyar wayar Jaish, ya sha mamakin ganin wayar sosai,
gata kamar sabuwa, bata ci screen ko ta lalace ba, sai dai bata kawo wuta, a kashe
take.

A gefensu ya ajiye kusa da wallet ɗin ya cigaba da binciken aljihun, a nan ya samu
passport, dama kun san da niyar yin tafiya Jaish ya bar gida, so ga passport ɗinsa
da komai, amma ruwa ya jiƙasu har sun ɗan yayyege, sun kuma manne da juna babu
halin bappa ya buɗe ya karanta.

Hakan yasa ya ajiye a gefe, cigaba da laluɓar aljihun ya yi har sai da ya tabbatar
da babu wani abin da ya bari a ciki. Sannan ya ajiye kayan a gefe ya kai hannunsa
ya ɗauko wallet da ya fitar da farko.

Da kyar ya iya ɓalle wallet ɗin ya buɗeta, sannan ya fara fito da abubuwan dake
ciki, akwai takardarsa na ɗan kasa, ID cards da sauran muhimman cards.

Dik babu wanda bappa ya iya karantawa ya gane, saboda rubutun turanci ne a jikinsu,
dibasu ya fara yi one by one yana binsu da kallo ba tare da yasan amfaninsu ko me
zai yi da su ba.

Da yake yasan waya sai ya ɗauko na Jaish ɗin yana ta kallo, ya rasa ta ya zai yi ya
kunnata, dan ya danna wajen kunnawa da ya sani na wayoyi amma taki kunnuwa, hakan
yasa ya ji jikinsa ta kara sanyaya matuƙa, ya ga rashin amfanin bincikar aljihun
tun da bai samu wani abin da zata taimaka mashi ba.

Daga karshe ya kwashi komai ya mayar in da ya fitar, ya ɗauki kayan ya mayar ya
makalesu, ya dawo ya kwanta yana tunanin yadda zai yi da wannan al'amari, ya saba
da Jaish sosai wanda rabuwarsu lokaci guda haka babu ko sallama zai iya haifar
mashi da babbar matsala, and ya zai yi da Mahnoor?. Ya jefawa kansa tambaya.

A ɓangaren Nenne kuwa, murna kamar zai kasheta, tuni ta je ta kyankyasawa
gwaggo ga abin da yake faruwa, sun yi matuƙar jin daɗin hakan, gwaggo har da wani
bata shawara da ta ɗaura ɗamarar zaman gidan bappa a yanzu dan ta dawo da ƴancinta
da ta rasa a baya, sannan ta tabbatar ta gallazawa Mahnoor har sai Inna ta ji ɗaci
a ranta tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu.

Ba ƙaramin daɗi Nenne ta ji ba jin abubuwan da gwaggonta ta ce, dan haka ranta fes
ta janyo doggin kafafunta ta nufo gidan bappa da su.

A hanya ta haɗu da Ibrahim da su Mahreen. Ko tsoron Allah babu bare kunya ta wani
dakatar da zu har da cewa.

"Kai Ibrahim ina kuma zaka kai su?".

Bai tankata ba, ga dikkan alamu basa zaman lafiya da ita, ko kallon in da take ma
bai yi ba ya sanya kai zai wuce ya cigaba da tafiya.

"Ba da kai nike magana bane Ibrahim? Nace ina zaka je da su?"
A harzuƙe ta yi maganar, irin ranta ya ɓaci ɗin nan, ya za'ayi ace tana mashi
magana zai bawa banza ajiyarta yasa kai zai wuce?.

Still dai bai tanka ba, bai yi kamar yasan da halittar bil'adama a wajen bama, ya
cigaba da tafiya hannunsa sarkafe dana Mahnoor.

"Ke Mahreen zo nan ki wuce mu tafi tun da ke kam nike da iko da ke!!".

Cike da isa da gadara ta yi maganar, irin Mahreen ƴarta ai dole ta bi
umarninta. To kun san halin Mahreen ba sai na sake faɗa ba, yarinya ce da bata bin
bayan rashin gaskiya komai ƙanƙantarta, dan haka sai ta ce.

"Nenne ni kam kawu Ibrahim zan bi, ina gidan Arɗo yau".

"Ban yarda da haka ba! Zo maza ki wuce mu koma gida". Cikin gadara ta yi
maganar.

"Nenne wai idan mun je gidan me zan yi maki? Kawai in je in zauna?".

Kai ta gyaɗa mata alamar e, sannan ta ɗaura da cewa.
"Kwarai kuwa, ko ban isa in ce ki yi abu bane?".

Shiru ta ɗan yi tare da juyawa ta kalli Ibrahim da Mahnoor da suka ɗan yi nisa a
tafiyar da suke yi, sun barta tsaye tana biyewa Nenne.

"Ni gaskiya Nenne ba zan koma gida ba, wajen ƴar uwata zan je, ke bakiga kuka
take yi bane? Zan je ne mu rarrasheta, yau a gidan Arɗo zamu wuni!".
Tana magana tana turo baki na rashin kunya da kuma shagwaɓa

"Eyee ke da in nace ki je wajen gwaggo sai ki ce mun baki son zuwa ke ba zaki je
gidan Arɗo ba, amma yanzu saboda munafurci ne har da cewa a can zaki wuni ko?".

Kai ta gyaɗa haɗe da cewa. "Yanzu ma saboda Adda Mahnoor zan je, ba dan ita ba ni
Allah ya sawwaƙa in je gidan Arɗo".

Salati Nenne ta saka ta sanar da Ubangiji, sannan ta ce. "Kema yanzu kin koyi
munafurci koh Mahreen? Wato Mahnoor ta koya maki munafurci da rashin kunya ko?".

Ɗan zaro idanu waje ta yi, cike da mamaki ta ce. "Adda Mahnoor da munafurci kuma?".
Kai Nenne ta gyaɗa alamar e haɗe da cewa. "Ko karya nayi ne?".

Kai tsaye Mahreen ta amsa da. "Wlh karya ne! Adda Mahnoor bata munafurcin kowa,
nice ma nan kullum nike kawo mata gulmar Inna Rabi, kuma har faɗa take mun a kan in
dai'na gulmar mutane idan basa nan, in ya zama dole na yi maganarsu to ya zamana
maganar da zan iya maimaitawa a gaban idanunsu su ji ransu bai ɓaci ba zan faɗa,
kullum sai ta yi mun nasiha, ai Nenne ke da wancan gwaggo mai ido kamar na aljanun
ne ma kuke yin gulmar mutane, ba har zagin Inna kuke yi ba? Ai ina jinku dik abin
da kuke............."

Bata kai karshen maganar ba ta yanka a miliyan ta bi bayansu Mahnoor sakamakon
cabka da Nenne ta kai hannu zata yi mata.

"Mahreen ki dawo nan kada ki yarda ki bisu".
Nennen da ranta ya gama ɓaci, ta kawo har wuya ne ta faɗi haka, tana da bala'in son
girma, amma sai dai bata san ta yadda zata bi da mutane su girmamata ba, yau ga shi
ƴar cikinta ke gaya mata ita ce munafuka kuma ma gulmaciya, me ya kai wannan ciwo
fisabilillahi? Alhaki ai kuykuyone, ga shi ta fara gani.

Ina kafa me na ci ban baka ba? Kafin Nenne ta dasa aya a maganarta ma Mahreen
ta kurewa ganinta, kamar wata haske ta wuce fiwwww, yarinya mai saa mai kuma baiwar
iya gudu.

Galala Nenne ta saki baki tana jin ɗacin maganganun Mahreen a ranta, karin ɓacin
rai ma shi ne yadda Mahreen ta haɗe har da gwaggo ta zage, abin ya bakanta mata
matuƙa.

Ta ɗan jima tsaye a wajen tana tunani, wucewar da Mairo ta zo zata yi a kusa da ita
ta ɗaga mata gaisuwa ne ya fargar da ita ashe a kan hanya take tsaye.

Wani irin ƙasƙantacen kuma walaƙantatcen kallo ta bi Mairo da shi, bata amsa
gaisuwar Mairo ba, sai wani kallon up and down da take binta da shi, ashe a wajenta
Mahreen ta gaji irin wanna walaƙantatcen kallo da take yi wa mutane, wlh dik yadda
kake ji da kanka idan aka yi maka irin wannan kallo sai ka ji kamar kai ba kowa
bane, ka ji ka kaskanta ka walaƙanta, sam kallon bashi da daɗi.

Ganin haka yasa Mairo ta nufi kama kanta ta wuce, salum alum ta kama hanya,
dama tasan Nenne bala'i ce, ta gaisheta ne kawai dan kada ace ta ganta bata
girmamata ba.

"Ke zo nan?". Cewar Nenne.

Ba musu Mairo ta juyo ta dawo wajen ta tsaya, cikin sanyin murya ta ce. "Adda gani
nan......."

Bata idasa maganar ba ta shanyeta dif sakamakon wani bahagon marin da Nenne ta
sakar mata tasssss. Nenne bahaguwa ce, haka yaran Arɗo dikka suke lefty, harta
Ibrahim bahagone, hakan yasa Mahnoor take bahaguwa ita ma, ta gada wajen mamarta,
Arɗo shi ne ainahin bahago, so a wajensa suka gada.

A miliyan Mairo ta dafe ƙuncinta, take wasu zafafan hawayen suka faso idanunta a
guje suka fara tsere a saman kumatunta, jikinta har ɗan kerma yake yi, hannun da ta
dafe ƙuncinta sai rawa yake yi.

Tsabar masifa da rashin kunya irin na Nenne wai ƙoƙarin kara mata marin take
yi, daga bayansu suka ji muryan bappa yana faɗin.

"Kada ki kuskura ki sake marinta". Cikin zafi ya yi maganar, ya jima bai zafafa
a magana irin haka ba, tun maman Mahnoor tana nan, yau ransa a ɓace ne yasa ya
zafafa.

Sanin halinsa da kuma jin ya zafafa yasa Nenne bata kara kai mata marin ba, dan
tasan fa bappa ruwa ne ya daki babban zakara yasa ya yi sanyi.

"Jeki abinki Maryam". Ya yi maganar ne yana kallon Mairo da idanunta suke jajir,
dan fa ba karya ta maru sosai.

Wucewa ta yi ba musu, dan tana da ladabi da biyayya. Shi ma bappa zuwa ya yi ya
wuce Nenne tsaye a wajen kamar gunki bai ce mata uppan ba ya nufi hanyar gidansu
Faisal, dan bappan Faisal ya aiko ya zo yana son ganinsa.

Bakinci ta kara taruwa ta yi wa Nenne kaho a wuya, ta rasa da wanne ɗaya zata ji!
Wata zuciya ta ce mata ta bi bayan bappan ta je cikin mutane ta ci mashi mutunci ko
zata huce haka nan. Wani zuciyar kuma ya ce ta bi bayan Mairo ta laƙƙaɗa mata ɗan
banzan duka, hakan zai sa ran bappa ya ɗacaca sosai. Wani zuciya ya ce ta koma gida
dik zasu zo ne su sameta tun da gwaggonta ta yi mata alkawarin zata murza kambunta,
zata baza mulki a cikin gidan.

Tunani dai kala kala cike fal a ranta ta rasa madogara, sai zallar mugunta a bakar
zuciyarta.

Daga ƙarshe dai da ta ga babu sarki sai Allah, sai ta shafawa kanta ruwan sanyi ta
nufi gida tana ta wani kunkuni tana tsinewa bappan da bai san tana yi ba a cikin
zuciya.


😥
========================

BLACK WORLD🔥

Shiru Sweetie ta kwanta saman bed ɗin Ronnie tana tunanin duniya, su kuwa suna
church. Can tunanin kyan Black Tiger ya ratso mata ta cikin kwakwalwarta. Ai a
miliyan ta tashi zaune tana ɗan sake fuska.

Can sai ta fara ganin shi a idanunta yana yi mata gizo, ta mutu a kan romance
pink lips ɗinsa.

Zuro ƴan kafafunta kasan bed ɗin ta yi, sanna ta diro ƙasa, dan gadon yana da tudu
sosai. Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi wajen glasses da ta gani kusa da tampatsetsan
mirror.

Takardu ne cike tab a cikin glasses ɗin, su handout, Bible, drama books, text books
da dai sauransu, Ronnie akwai san karatu sosai, shiyasa yake da tarin takardu
sosai.

Ƙoƙarin buɗe glass ɗin ta yi a tunaninta dan ta duba ko akwai hotunan Ronnie da
yayan nasa, sai dai abin da bata sani ba shi kansa Ronnie ranarsa ta farko ce na
ganin yayan nasa a lokacin da ta gansa.

Kasa buɗe door ɗin ta yi, dan komai nasa mai mahimmanci killace yake da securitys.

Sam bata ji daɗin hakan ba, dan ta so ta gansa. Gaban mirrorsa ta nufa dan ta ga
kanta ko zata rage kewar Pretty da take ji.

Hannayenta dikka biyu ta sanya ta dafe saman glass na saman table ɗin mirror,
ta zubawa kanta idanu ta cikin mirror tana kallon kyan da ubangijin talikai ya yi
mata.
Tunanin yadda kamannin Kamran ɗinta zai iya kasancewa ne kawai ya faɗo mata a
ranta, da shi take kwana take kuma tashi.

Kamar walkiya haka ta ga mirror yana ƙoƙarin darewa gida biyu, da farko ta ɗan
tsorata, sai kuma ta dake tana cigaba da kallon mirror babu ko kyaftawa.

Kamannin face ɗinta a jikin mirror ne ya fara sauyawa izuwa wani kamanni na daban,
still bata tsorata ba, sai kara zaro idanu da ta yi tana cigaba da kallon kanta.

A hankali ta cigaba da rikiɗa tana canzawa izuwa kamannin da bata taɓa ganin irinsa
ba.

Wani irin haske ne ya bayyana ta cikin mirror wanda yasa ba shiri ta ɗaga
hannayenta izuwa saman face ɗinta dan ta kare idanunta daga samun matsala ta
dalilin wannan haske.

Buɗe tafukan hannunta da ta yi wajen ƙoƙarin rufe face ɗinta ne ya yi sanadiyar
bayyanar nata magic ɗin ba tare da ta sani ba.

Bata ankara ba sai ji ta yi wani irin tsawan tarwatsewar mirror ya daki dodan
kunnenta.

Watsa watsa mirror ya yi a ƙasa, karfi ne ya haɗu da karfi, fitar magic ɗinta yasa
ya haifarta wannan, dan hasken nata ya haɗe da wannan haske da ya fito ta cikin
mirror, kuma nata yana da matuƙar karfi na ban mamaki, shi ne sila.

A miliyan ɗari ta yi kasa da hannunta a in da ta waro idanu tana kallon yadda
mirror ya yi watsa watsa, haƙiƙa a wannan karon ta jijjiga sosai, ba ita kaɗai kuma
ta jijjiga ba, har da shi Black Tiger sai da ya jijjiga, dan kuwa fashewar mirror
nan ba ƙaramar abu bace a wajensa, ba mirror ce kamar kowanne ba, bai taɓa zaton
zata buɗe tafukan hannunta magic ɗinta ya fita ba, da bai yi ƙoƙarin razanar da ita
ba.

And bugu da kari unexpect magic ɗinta ya daki saitin zuciyarsa, kafin ya farga ya
kare kansa haskenta ya tarwatsa tasa da har ya ɗan yi baya kaɗan, ya ji hakan a
jikinsa sosai, sai dai kuma, a take ya juya magic eyes ɗinsa ya kusar da raɗaɗɗin
da ya ji.

Zuciyarsa ta bakanta sosai a kan hakan, ba'a taɓa wanda ya taɓa gigin yi mashi abu
makamancin hakan ba, dan haka sai ya kudurta a ransa dole ya hukuntata ya kuma
durkusar da magic dake jikinta.

Ita kuwa sai ƙoƙari take yi ta fahimci abin da ya faru da har ya kawo
tarwatsewar wanna mirror haka?.

Ji ta yi ɗakin ya fara juya mata, sai ta fara ganin kamar fanka yake yi mata. Da
gudu ta bar gaban mirror ta haye saman bed.

Nan take wani iska mai karfi ya banko kofar ɗakin ya shigo, tana ƙoƙarin juyar da
kallonta izuwa wajen kofar ba zato ba tsammani ta ji saukar wani mahaukacin mari a
kuncinta wanda bata ga hannun mutum ba, bata san daga ina marin ya fito ba.

Tun da take a rayuwarta bata taɓa jin wani abu mai bala'in zafin wannan mari ba,
dik da magic dake jikinta hakan bai hana ta ga wani irin duhu ya gilma mata ba, har
wani irin jiri mai karfi ne ya ɗebeta daga zaune, na ƴan sakanni ta gaza gane a
wani duniya take, kunnuwanta gabaɗaya sun toshe bata iya jiyo sautin komai.

Gabaɗaya kwayayen fitillu masu hasken da suka kawata ɗakin ne suka fara ɗaukewa
suna sake kawowa a lokaci guda, dai'dai lokacin da ta dawo cikin hankalinta take
ƙoƙarin fahimtar me yake faruwa. Dai'dai lokacin chandelier ɗakin ta jijjigo daga
sama ta yo kanta a guje.

Ihu mai sauti ta kurma tare da dirowa kasa daga saman gadon, sai wani irin haki
take yi tamkar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi.

Ga mamakinta sai ta ga tana dirowa kasa chandelier ya fasa faɗowa saman bed
ɗin, ya juya ya nufota da karfin gaske.

A juye ta nufi baya baya dan ta fita waje. Sai dai kofar room ɗin ya rufe kansa tun
bayan shigowar wannan iska da ya jijiigo da chandelier.

Ihu take yi sosai dan bata taɓa ganin iska mai karfin wannan ba, ga shi dik in da
ta yi sai chandelier ya bi bayanta.

Kurewa ɗakin ta yi a in da ta mannu da jikin bango tana cigaba da ihu.

Ronnie dake zaune saman chair a cikin katafaren church ɗinsu sai ji yake yi gabansa
yana faɗuwa, sai ya ji zuciyarsa ta tsinke, kansa yana sara mashi, dik ya sara
nutsuwarsa da sukuninsa, yana jin kamar wani abin ne zai faru da shi.

Idan Sweetie ta kurma ihu sai ya ji hakan a cikin ransa, amma sam bai kawowa ransa
ita ce take cikin damuwa ba. Pastor na jawabi babu abin da kunnuwansa suke iya
ɗauko mashi, idanunsa dai yana a kan pastor, amma baya sauraronsa.

Da wani irin karfi na ban mamaki wannan chandelier ya nufeta tsaye a jikin
bango tana ihun neman taimako. Lokacin guda da chandelier ya kusa isa gareta ya
riƙiɗe ya zama wani irin kaifaffen wuƙa mai dafin bala'in, hasken dake fita daga
jikin wannan wuka sai da ya sanyata kanƙantar da idanunta.

Kan wukar ta zanen bakar damusa ce, hasken light blue ne yake fita daga dik wata
kusurwa na jikin wukar.

Kai tsaye wuyar Sweetie wukar ya nufa, da karfi kuma. Wani irin razanannen ihun
ta saki mai doɗe kunnuwa, bata da madogara, ba hanyar gudu, tana ji tana gani zata
mutu.

Ganin cewa wuyarta wanna wuƙa ya nufa yasa ta kai hannayenta ta tare wuyar tata
tana ihu, sai dai a wannan karon bata datse idanunta ba.

Tana tare wuyarta da hannunta unexpect taga wani haske ya fito daga cikin hannunta
ya nufi wanna wuƙa, nan take wanna haske ya dakatar da wukar a dab kusa da ita.

Ya ilahi ya lilliahi, ai sumar tsaye ta yi tana kallon hannunta, her first time
seeing that she has a unknowing magic, she was so surprised!.

Kamar wata wadda aka zarewa ruhi, ido ta kara zarowa tana ganin yadda hasken hannun
nata yake tamkar light aka kunna, abin ya yi mugun ɗaure mata kai, tana son ta
motsa hannun nata ko wani sassa daga jikinta amma ta kasa, dik sai ta ji jikinta ya
yi mata nauyi sosai.

Kafafunta ne suka fara gaza iya ɗaukar gangar jikinta, hakan yasa ta ɗan yi tangal
tangal kamar zata faɗi. Wannan tangal tangal da ta yi yasa hannunta ya ɗan motsa,
hakan ya haifar da motsawar wannan wuƙa da a yanzu yake ƙarƙashin sarrafawar hasken
hannunta.

Kara zaro idanu sosai ta yi tana kallon wanna abin al'ajabi. Da kyar da suɗin
goshi ta iya kama kanta bata zube ƙasa ba. Har lokacin iska mai karfin nan dai yana
cigaba da kaɗawa a cikin ɗakin, Black Tiger yana cikin wannan iskar, ya zuba mata
idanu ne yana kallon gudun ruwanta, amma kuma ya yi matuƙar mamakin karfin irin na
magic ɗinta da har ya iya tare wannan wuka da ya turo mata bai huda fatar wuyarta
ba.

Idanunta a kan wukar, cikin karyewa da sanyin gaɓɓan jikinta ta yi

Please Login or Register in order to submit comment