Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 41 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki yi
gaggawar bayyana matsalolinku na gida ga kowa. Kula da sirrinku zai taimaka wajen
magance matsalolin cikin sauƙi. Kauna da kulawa. Dik da nasan yana da wuyar sha'ani
kuma zai yi wuyar juyowa gareki, dik da haka ki nuna mashi soyayya da ƙauna, sannan
ki kula da dangi da abokan arzikinsa. Wannan zai sa ki samu ƙima a gidansu. Hakuri,
hakuri, hakuri, ki kasance mai haƙuri. Komai yawan ƙalubale, haƙuri yana da
muhimmanci don magance su. Ki rike ibada sosai. Wannan yana kawo albarka a cikin
aure. Kar ki yi gaggawa wajen yanke hukunci idan ya yi maki wani abin. Idan akwai
matsala, ki nemi hanya mai kyau don magance ta kamar yin nafilfilin dare dan neman
maslaha daga wajen Allah. Ki kasance mai ilmantarwa. Karatu da ilimi suna taimaka
miki wajen zama mai cikakken basira a rayuwa. Na faɗa na kara faɗa maki, mijinki
yana san kwalliya sosai, sannan na manta ban faɗa maki cewa shi mutum ne mai san
zanen lalle a hannun mace ba, ko ni da nike mahaifiyarsa idan na yi lalle ya rinƙa
magana kenan, ya kalla ya sake kallah, har hoto yake ɗaukar hannuna, Jaish mutum ne
mai san lallaɓawa, tin yana karami haka yake, baya san a ɗaga mashi murya, sannan
baya san yana magana ki yi magana, ki kula da wannan, baya san cin abincin a kan
lokaci, hakan kada ya ɓata maki rai ki ɓata mashi shi ma, cikin ruwan sanyi da
sigar soyayya da lalama zaki koya mashi cin abinci a lokacin da kika yi ra'ayi,
yana da zuciya sosai, wannan gado ce, dik suna da zafin zuciya da saurin fushi,
idan ransa a ɓace kada ki yi saurin kula shi, ki kyalesa na ɗan lokaci ya sauko, in
ba haka ba ba zaku kare da kyau ba".......... Ɗan dakatawa ta yi tana mayar da
numfashi.

Mahnoor kuwa ta kasa kunne tana saurari yadda yakamata. Shiru ta ɗan tsaya na ƴan
mintuna tana kallan fuskar Mahnoor kafin ta nisa ta ɗaura da cewa.

"Kin ji kaɗan daga cikin abin da yake so ta waje, sai ta ciki, ba zan ɓoye
maki komai dangane da mijinki ba, saboda yanzu a ƴa na ɗaukeki ba sirika ba,
burinmu mu shawo kan mijin naki ne, dole na fayyace maki komai dan mu yi nasara".

Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tana kara kasa kunne ta saurara da kyau, saboda tana
bala'in san Jaish, dik abin da zai juyo mata da hankalinsa a kanta to tabbas zata
yi shi.

"Mijinki yana da sha'awa mai karfi wanda zance maki dikkansu haka suke, sai ki
shirya, amma yana da dauriya sosai, sannan baya san mace mai shigar manyan kaya, i
mean matar aurensa, saboda na karancesa sosai a kan hakan, dayawan lokuta yana san
sayawa kanwarsa kananan kaya dan yana yi mata kallan yarinya, so yana san shigar
manyan kaya, wannan zan sa a yi maki akwati set guda a wajen haɗa lefenki, so
Haulat zata koya maki yadda zaki yi amfani da su".

Mahnoor da bata san me ma mommar take nufi ba a maganarta ta karshen nan, ai sai
amsa mata take yi to kawai kanta a ƙasa.

My people's ku tafawa uwa ta gari, wato dik abin da ƴaƴanta suke yi tana sane tana
yin recoding a ƙwaƙwalwarta, ashe ta san Jaish yana san lalle, kun tuna idan ya zo
ya samu mama Haulat ta yi mata lalle sai ya yi ta yabawa? Ashe dik tana ganinsa,
ashe ta iya karantar abin da yake so da wannan da baya so, gaskiya wannan ita ce
uwa ta gari, ba tare da ƴaƴanta sun faɗa mata ga abin da suke so ba ta rigasu sanin
abubuwan da suke so, wani lokaci suna son abu basu ma san son shi suke yi ba, amma
tsabar kula irin nata ita ta gane hakan, wata uwar ko kasheta zaki yi yanzu ki ce
ta kirga maki abubuwa goma da yaronta yafi so ba zata kawo maki su ba, kuma tana
sansa ba wai bata sansa ba, wasu ne akwai rashin kula sosai wlh, irinsu ne ƴaƴa su
yi ya aikata abubuwa tsabar rashin kula zasu ce basu sani ba, yanzu ku momma bata
burgeku ba yadda take zayyano abin da ɗanta tafi so ba tare da shi kansa yasan da
yana sansu ba? Abin bai ƙayatar daku ya yi maku daɗi ba? Ki karanci yaronki ki san
me yake so ma ke zaki fi kowa jin daɗi da moresa, dan in kika san me yafiso fa wlh
dik in da zai je sai ya dawo wajenki, dan zai ga kamar dik duniya ke kaɗai ce kika
iya fahimtar kika sansa sosai. So yana da kyau dikkan mata su yi koyi da halin
momma, ita ake cewa uwa ta gari wlh. Daga karshe Allah ka haɗamu da iyayen miji na
gari irin momma.

(Amma fa momma ta gama kwancewa Jaish namu na amana zani a kasuwa😅 zata sa
Mahnoor ta raina shi😅)

Daga haka Momma ta sanar da Mahnoor abin sa yasa Jaish ya ce bai sansu ba a yanzu,
dan haka kada su ji haushinsa ko su ga laifinsa, ya so ta ne a lokacin da baya
cikin hayyacinsa, daga karshe ta ɗaura da cewa. "A yanzu ma In Sha Allah zai so ki,
zan tayaki yakin neman shawo kansa, kada ki sare ko ki cire rai, mu nan gidan
jajirtattune, kema jajircewa zaki yi ki jure har mu yi nasara, sai abu nagaba da
zan faɗa maki, in dai ba kin lura ransa a ɓace ba to in ya ce ki bar gabansa ko ki
tashi a kusa da shi kada ki tafi, amma idan ransa a ɓace wannan kam ki tafi in ba
haka ba ayi ɓatacciya, ki yawaita kasancewa a tare da shi, a kullum karfe 9 na dare
yana shan cappuccinon, ni kuma nike haɗa mashi da kai'na, ki zo ki rinƙa ɗauka
mashi kina kai mashi, kada ki yarda yana zaune a waje shi kaɗai, kada ki ji
tsoronsa dan a labarinku na baya na ji kina tsoronsa, to a yanzu ki ajiye tsoron
nan ki rinƙa kusantarsa sosai".

"Muhimmin abu nagaba shi ne, yanzu ki sani dik wata ɗawainiya nasa zai dawo kanki,
kama daga kai mashi abinci, sanya shi ya ci, shinfiɗa gadonsa, mace mai dabara bata
bari kowa ya ga makwancin mijinta, dan haka kada ki bada kofar da zai ce a dawo
mashi da kuyangu masu yi mashi hidima a zuwan ke baki iya gyara mashi shinfiɗa ba,
ki koyi yi mashi shinfiɗa da kyau, ki ɗara dik kuyangun da suke yi mashi hidima a
baya yin komai yadda yakamata kuma yadda zai ƙayatar da shi, dik Haulat zata koyar
dake kin ji ko?".

Kai ta gyaɗa tana amsawa da e ta ji.

Sosai ta fayyace mata dik wasu abubuwan da Jaish yake so da wanda baya so. Dik abin
da take faɗe yana shiga kunnuwan Mahnoor yadda yakamata. Suna tsaka da hiran ne
Omaid and Obaid suka shigo cikin ɗakin baki ɗauke da sallama.

Momma ce ta amsa masu sallamar tana jinsu da kallo.

Saman gadon Omaid ya haye yana turɓe fuska ya kwanta a can gefe. Shi kuwa Obaid
sarki a rashin hakuri, wani kallo mai kama da harara ya wurgawa Mahnoor. "Momma who
is she? She looks like Aunty Chuchu". Ya yi maganar yana kare mata kallo.

Baki ɗauke da sallama guyson ya shigo, dikkansu suna cikin white arabs
jallabiyas masu bala'in kyau, yau sun fito a larabawansu sak.
Saman gado kusa da Omaid guyson ya haye yana turo baki, cikinsa ce take ɗan yi
mashi ciwo kaɗan kaɗan, da alama ciwonsa ce take san tashi. Yana kwanciya kallonsa
ya sauka a kan Mahnoor da ta yi ƙasa da kanta tana ta satar kallansu Omaid, a
ganinta sak suke kama da Jaish, kun san jini ba wasa ba, sun yi mata bala'in kyau,
sai dai ta shiga ruɗani wajen ƙasa tantance Omaid and Obaid mutun ɗaya ne ko biyu
saboda kamanninsu.

Zaro idanu guyson ya yi, da ɗan karfi ya furta. "Momma wannan ba matar Yah Jaish
ɗin nan ba ce?". Ya yi maganar yana miƙewa zaune an fasa kwanciya, yaga ta goge ta
yi kyau kamar ba ita ba........ Lallai guyson yana da basira sosai, bai fa wani
jima da sanin Mahnoor ba, amma dik wannan gyara da ta sha ya iya ganeta.

Wani irin ɗan iskan dariyar ƙeta Obaid ya yi kafin ya ce. "Yah Jaish ɗin ne da
mata? Tab hau kenan". Ya kai karshen maganar yana sake watsewa da dariya.

Shi kansa Omaid jin zancen sai da yasa ya miƙe zaune. "Da gaske Yah Jaish ya yi
aure?". Ya yi tambayar yana zare idanu.

Guyson ne ya wurgawa Obaid harara kafin ya ce. "To dariyar me kake yi sarki?".
Zama Obaid ya yi a saman sofa, cike da iyashege ya fara faɗin. "Yah Omar ba dole in
yi dariya ba, wai Yah Jaish da mata? Amma wannan ta shiryawa azabansa ko? Dan dik
gidan nan bayan Yah Ramish babu bakin mugu biyunsa, wlh i pity for his wife".

Omaid ne ya capki zance da cewa. "Waye ya ce maka ma akwai wadda zata iya zaman
aure da shi? Mutumin da bayan bada umarnin babu wani abin da ya iya, su kuma mata
suna san soyayya da kulawa haɗe da lallaɓawa kamar jarurai, shi kuma yana abu kamar
bosawa bashi da wani shaukin love".

Tab wato Omaid ɗan duniya ne, ko daga ina ya san shaukin love kuma? Kana ganinsa
kaman shiru shiru ashe A ne shi ma, dama fa masu shiru shirun nan hmmm idan suka yi
wata tsiyar sai ƙwaƙwalwa ta kasa ɗauka.
Momma dai binsu da kallo kawai take yi abinta.

Harara Guyson ya wurgawa Omaid kafin ya ce. "Kai daga ina ka san shaukin love
ɗin?".

Obaid ne ya amshi zancen da cewa. "Tab ai Omaid ƴan'matansa sun kai uku a school,
har faɗa ake yi a kansa sosai, love yake bugawa over"........... Momma ce ta
katsesu da cewa. "Kai kuma ƴan'matanka nawa?"....... Ɗan ɗaure fuska kaɗan ya yi.
"Momma ni ai bana soyayya, me zan yi da mata? Bani da lokacinsu gaskiya".

Girgiza kai kawai guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce da Mahnoor. "Kada ki
biyewa waɗan nan, kin yi kyau sosai, ina sisterki da ta yi mun kallan matsayin Yah
Jaish ɗin nan take?".

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da Mahreen tana ɗakin da aka yi masu gyaran jiki.......
"Kada ki takura kanki wajen sunkuyar da kanki da sunan kina jin kunyarnmu, mu
kannen Yah Jaish ne, kinga mu kannenki ne, ki ɗaukemu a haka kin ji?". Cewar guyson
again, yaro mai sanyin hali.

"Waye kaninta?". Cewar Obaid, a kule ya yi maganar. Hararar wasa guyson ya wurga
mashi kafin ya ce. "Mu mana, mune kannenta". Kallon uku saura kwata ya bita da shi
kafin ya amsa da. "A'a sai dai ku, amma ni wannan ƴar karamar yarinyar ba zan ce
mata aunty ba, na fita shekaru fa". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa fuuuu ya
nufi waje.

Da kallo dikkansu suka bisa har Mahnoor ɗin ma, shi a dole ransa ya ɓaci ance shi
kanin Mahnoor ba zai ɗauki hakan ba.

Dab zai fita Jaish yana sako kai zai shigo. Karo suka ɗan yi, da sauri ya ja baya a
ransa yana cewa shikenan yau ranata ba zata yi kyau ba tun da na haɗu da Yah Jaish.
A fili kuma sai cewa ya yi. "Good afternoon Yah Jaish".

Kallon tsab Jaish ya yi mashi kafin ya amsa da. "Afternoon, from where to where?".
Fuska a ɗaure tamau ya yi maganar. Guyson ne ya fara yi mashi dariya, suna bashi
dariya yadda suke nitsuwa a gaban Jaish, zaka rantse da Allah malaman da'awa ne
idan ka gansu a gaban Jaish ko Ramish, a bayansu kuwa ko shaiɗan sai ya sara masu a
rashin mutunci.

Matsawa kusa da Mahnoor guyson ya yi, yana dariya ƙasa ƙasa ya ce. "Kinga dik
iskancin nan nasu mijinki maganinsu yake yi, tsoronsa suke ji kamar su mutu, baki
ga sun nitsu ba?".

Ita kanta sai da abin ya so sakata dariya, yadda Obaid ya rinƙa tada jijiyoyin wuya
yanzu a nan, amma daga ganin Jaish kamar wani kurman da ya wuni bai ci abinci ba ya
zama, ya nitsu tsit.

Cikin in ina Obaid ya amsa da. Daga wajen momma ɗaki kuma zai tafi ya kwanta. "Ka
aikata wani abin ko?". Jaish ya faɗa yana wurgawa momma dake kallonsa ido. Wato
Jaish yasan halinsu sarai, basa zama basu yi wani laifin ba, shiyasa dik in ya haɗu
da su sai ya ce sun aikata wani abin.

Wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji na jin sanyayyar muryar mijin nata, wani irin
azabbabben sonsa ne yake kara taso mata, ji ta yi tana san ɗago kai ta kallesa amma
tana tsoron su haɗa ido, kuma tana kunyar momma ta kamata tana kallansa, sai kawai
ta danne ta ƙara yin ƙasa da kai, amma tabbas tana kewansa, yanzu an kusa sati
biyar rabonta da su kasance a hare kenan.

Sarai momma ta fahimci har yanzu Mahnoor tana tsoron Jaish sosai, kamar ma yanzu
tsoron nasa karuwa ya yi a ranta, lallai sai ta tsaya tsayin daka ta cire mata
wannan tsoro idan suna san yin nasara.

Wani irin kallo Jaish ya wurgawa Obaid har sai da ya haɗiyi wani yawu mai wuyar
wucewa, sannan tin kafin Jaish ɗin ya sake yin magana ya yi saurin faɗa mashi dik
abin da ya aikata, wato guyson ya ce Mahnoor Auntynsu ce shi kuma ya ce ba Auntynsu
bace dan ya fita shekaru, dan haka ba zai ce mata Aunty ba, tsab ya faɗi abin da ya
yi.

Momma da guyson sai murmushi suke binsu da shi. Jin abinda Obaid ya faɗa yasa ya ja
siririn tsaki tare da karisowa ciki, dan a cewarsa shi ma ai bashi da haɗi da
Mahnoor ɗin bare ya ji babu daɗi dan sun ki accepting ɗinta sun yi mata rashin
kunya.

Saman sofa Jaish ya zauna, shi kuma Obaid ya yi saurin ficewa waje. Cikin girmamawa
Omaid ya ɗagawa Jaish gaisuwa, amsa ɗaya ya yi hankalinsa gabaɗaya a kan momma.

Ƙasa Omaid ya yi, da sauri ya bi bayan Obaid, dan basa zama inuwa guda da
Jaish. Guyson kuma cigaba da hira da Mahnoor ya yi ba tare da damuwa ba, dama abin
da yasa a kauye ya ji kyamarsu ma, saboda datti ne, yanzu kuma sun yi tsab dan haka
bashi da wata matsala da su.

Tin Mahnoor tana noƙewa bata yi mashi magana har ta fara sakin jiki suna hira ƙasa
ƙasa, har murmushi ya sakata yi, ko ɗaya kuma bai ambaci sunanta ba, Aunty yake ce
mata cikin girmamawa, ita ma ta tambayesa sunansa, ya ce mata Omar amma ana kiransa
da Guyson, dan haka sai ta fara ce mashi Yah Omar saboda ya fita shekaru, yanzu
kusan 19 years yake da shi.

Kallan tsab Momma ta yi wa Jaish kafin ta ce. "Lafiya kake kuwa? Ya ka dawo office
da wuri?".
Ɗago kansa ya yi da nufin ya yi magana, sai a lokacin ya lura da Mahnoor dake
saman bed ɗin ita ma, kallo ɗaya ya yi mata ya dawo da kallonsa a kan momma, irin
kallan da ya wurga mata mai kama da yana san tambayar wacece wannan kuma? Sai dai
bai tambaya ɗin ba ya ce da momma..

"Kai'na ne yake ciwo shiyasa na tashi office, and am felling hungry". A ɗan
takaice momma ta ce. "Baka yi breakfast ba ka fita ko?". Kai ya gyaɗa mata alamar
e.
"Meyasa baka san cin abinci a kan lokaci ne? Yanzu karfe 12 ta kusa fa amma baka
yi breakfast ba? Dole ma kanka zai yi ciwo ai". Shiru ya yi yana ɗan satar kallan
lallen dake kyawawan fararen hannun Mahnoor, ga zanen lallen sun fita sosai, sun yi
kyau, mayen san lalle ne shi kuma, sai yana magana yana satar kallonsu, da a hannun
Mommarsa ce ko hannun Zunaira yake da sai ya ɗauki hannun hoto, amma ita wannan bai
santa ba, amma dik da haka ya ji yana kaunar lallenta.

Sarai momma tana kallansa dik abin da yake yi, ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin yadda
yake satar kallan lallen, lallai ne kowani mutum yana da rauninsa, kuma abin da
yake so shi ne rauninsa, tabbas zasu yi nasara In Sha Allah, haka momma take faɗe a
ranta.

"Ayya sorry, jeka huta yanzu za'a kawo maka abincinka, idan ka ci sai ka sha
magani". Cewar momma, ta yi maganar tana kallansa.

Sarai ya ji abin da ta faɗa, amma hankalinsa yana a kan lallen Mahnoor, dan haka
sai ya jinjina kai kawai ba tare da ya yi magana ba, sannan ya miƙe da nufin ya
tafi. Har zai juya sai kuma ya tuna bari ya kalli face ɗin mai wannan lalle. Ya
ilahi ya lilliahi, sai da ya ji gabansa ya faɗi time da ya ɗaura idanunsa a kanta.
Da sauri kamar wani maras gaskiya ya kawar da kansa tare da wucewa waje da sauri.
Murmushi a cikin zuciyarta momma ta saki, har ta harbo jirgi ɗan nata, dan har
cikin ransa ya ji kyan Mahnoor ya taɓa shi.

Yana fita momma ta dawo da kallonta a kan Mahnoor da Guyson da suke ta hira ƙasa
ƙasa ba zaka jiyosu sosai ba, cikin nitsuwa da giramma juna.

"Mahnoor tashi Omar ya rakaki wajen Haulat, ku je Omar ka ce da Haulat ta shirya
mun ita sosai ta bata kayan da suka dace zata je kaiwa mijinta abinci, bari in je
in duba kitchen me suka shirya mashi". Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye.

Miƙewa guyson ma ya yi ya sauko kasa yana faɗin Mahnoor ta tashi su tafi, har
lokacin yana jin cikinsa tana ciwo kaɗan kaɗan, amma ya daure suka nufi waje.

After some minutes, momma ta dauke cikin parlonnta wasu kuyangu guda biyu suna
biye da ita a baya ɗauke da manya manyan trays masu shake da kayan cima wanda ta sa
suka shiryawa Jaish. A saman dining table ɗinta suka ɗaura mata, sannan suka zube
gwiwowinsu a ƙasa suna jiran jin ko akwai wani umarni da zata basu.

Da hannu ta yi masu nuni da su tafi, sannan ta samu waje saman sofa ta zauna tana
tunanin irin nasihar da yakamata ta yi wa Jaish a kan Mahnoor. Tana tsaka da wannan
tinani mama Haulat ta yi sallama rike da hannun Mahreen.

Like wow my people's, wai kunga Mahreen kuwa? Tamkar ba ita ba, har ɗan kumatu ta
yi, fatarta ya yi jajir kamar ka taɓa jini ya fita, ta sha gyara da ingantattun
kayan gyara daga Dubai, kayan gyara na musamman, tana sanye da abaya mai bala'in
kyau wanda momma tasa aka sayo masu.

Ita kanta momma tasan yarinyar nan ta yi kyau, sai da ta yi fatan dama ace ita ma
Mahreen ta zama sirikarta mana.

Mahreen yanzu ta ɗan nitsu fa, kun san da san kwalliya, dik abin da mama Haulat
take son ta yi mata sai ta ce ta yi zata yi mata kwalliya, idan ta ce haka sai kuga
Mahreen ta nitsu ta bi umarni, a haka aka samu aka yi mata wannan gyara.

Tin da ta kalli kanta a cikin mirror taga ta yi kyau shikenan ta kara nitsuwa,
yanzu dik bayan awa sai ta ce zata yi wanka a sake yi mata wani make up ɗin mai
kyau, dan shegen bala'in san kwalliya.

Da hannu momma ta nuna mata kusa da ita a kan ta zo ta zauna, sannan ta dubi
Mama Haulat kafin ta ce. "Haulat kawo mun ɗiyata ya zo ta kaiwa mijinta abinci,
daga nan ki shirya ki je part ɗinsa ki shirya ɗaki ɗaya wanda zaki koma can da
zama".

Shiru mama Haulat ta ɗan yi, mace mai amana, ta kasa tafiya kuma.

"Lafiya Haulat?". Momma ta tambaya ganin bata tafi ba. Kasa ta yi da kai, cikin
girmamawa ta ce. "Ranki ya daɗe wlh bana san matsawa daga kusa da ke ne". Allah
sarki, sun saba sosai.

Momma tana ƙoƙarin janyo Mahreen jikinta ta rungume ta ce. "Ai baki bar kusa da ni
ba, jahadi zaki je ki yi wajen ganin kin saita aure, daga nan ai zaki dawo, yanzu
dai ki kuka da yaran naki da kyau".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa da to, sannan ta juya ta nufi waje. Dawo da
kallonta a kan Mahreen momma ta yi, yarinya ta yi kyau kamar ba gajin bappa ba.
Janta da hira momma ta fara yi tana kara wayar mata da kai.

Suka tsaka da hira mama Haulat ta dawo rike da hannun Mahnoor, ya subhanallah, mama
Haulat ta iya shirya amarya fa, ta tsara mata kwalliya mai bala'in kyau da dik
wanda ya kalla sai ya sake kallah, sannan ya bata wani haɗaɗɗen malesian gown mai
bala'in kyau da tsada kaunin brown color, ga Mahnoor da hasken fata sai kalar ta yi
mata kyau.

Rigar ta bi coca colar shape ɗinta ta zauna ɗas, sannan rigar ta fito da komai
yadda yakamata, sai dai sun ɗaura mata kyakkyawan alkyabba a saman kayan, kanta
babu ɗan'kwali sai hular alkyabbar, gashin kanta ya sha gyara sai tashin kamshi
yake yi yana wani sheki, kai my people's wlh Mahnoor ta haɗu matuƙa.

Mahreen tana ganinta ta miƙe da nufin ta je ta rungumota, rikota momma ta yi
tana faɗin. "Zauna kada ki ɓatawa amarya kyalliyarta". Jin haka yasa ta koma ta
zauna tana faɗin. "Ni momma ba zan yarda ba kwalliyar Adda Mahnoor ya fi nawa
kyau".

Murmushi kaɗan momma ta yi kafin ta sake cewa. "Anjuma da yamma idan zaku je gaishe
da daddy za'ayi maki kwalliya irin nata kema"

Cike da yarinta ta ce da momma. "Ki ce Allah za'ayi mun?". Ɗan zaro idanu Mahnoor
da mama Haulat suka yi. Har mama Haulat zata yi mata faɗa ta gaya mata ba fa wajen
wasa take bai sai momma ta rigata da cewa.

"Ba sai na ce Allah ba, za'ayi maki ke dai". Make kafaɗa ta yi tana faɗin. "Idan
baki ce Allah ba ni na zan yarda ba........".

Bata kai karshen maganar ba mama Haulat ta ɗan daka mata tsawa. "Ke baki da hankali
ne? Sa'arki ce ita? Wai bana ce maki ki rinƙa girmama manya ba?.........".

Ɗaga mata hannu momma ta yi tare da cewa. "A'a Haulat rabu mun da ƴa, dauki kayan
abincin nan ki raka Mahnoor izuwa wajen Jaish saboda yana jin yunwa, ba ruwanku da
ƴa ta". ........... Cikin girmamawa mama Haulat ta amsa da okey a cikin zuciyarta
tana kara jinjinawa kirkin momma da rashin girman kanta, ba kaman sauran matan King
ba, idan su mama ne Mahreen ta isa ma ta zo in da suke ne?. Ai su basa zama kusa da
talaka, ina momma ta dabance a cikinsu, bata ɗauki duniya a bakin komai ba.

Haka dan tana san farincikin Mahreen sai da ta amsa mata da Allah ɗin sannan
Mahreen ta yarda, suka cigaba da hira Mahreen tana zuba mata shirme da hiran kauye
da dai sauran shiririntarta.

Mahnoor kuwa mama Haulat ta ɗauki tray ɗaya na abinci ita kuma ta ɗauki ɗayan,
tamkar wata tauraruwa haka ta bi bayan mama Haulat suka nufi part ɗinsa.

Sai kalle kalle Mahnoor take yi, dan idan baku manta ba bata yawace cikin gidan ba,
part ɗin momma kawai suka sani sai ɗakin gyara. Bata kara zuba ƙauyancinta bama sai
da suka isa part na mijin nata, wani irin daddaɗar kamshi ne ya daki hancinta har
sai da ta lumshe idanu tana kara shaka.

A saman dining table dake cikin parlonsa suka zube abincin, sannan mama Haulat ta
dubeta, cikin mutuntawa ta nuna mata kofar master room ɗinsa da hannun tana faɗin.
"Ga ɗakinsa can shiga ki sanar da shi kin kawo mashi abinci".

Idanu ta zaro, ɗan bakinta ya sha lips balm sai kyalli yake yi yana ɗaukar hankali,
kamar zata sa ihu ta ce. "Mama Haulat tsoron shiga nike ji". Tabbas mama Haulat ta
fahimci akwai tsoronsa sosai a ranta, matsawa kusa da ita ta yi, da hannu bibbiyu
ta dafa shoulders ɗinta, cike da kaunarta ta ce.

"Kina san Prince ko baki san shi?" Kasa ta yi sa kai ta gagara ba da amsa. Mama
Haulat ta fahimci kunya ne da ita sosai kamar dai Jaish ɗin, dan haka sai ta ce.
"Kada ki ji kunyata, ki ɗaukeni a matsayin mahaifiya, ina san ki faɗa mun kina san
shi ko baki san shi".
Ƙasa sosai ta yi da murya. "Ina san shi". Ta bada amsa kunya kamar ta shige cikin
ƙasa. "To lallai in dai kina san shi dole ki tsaya tsayin daka domin yaki a kan
abin da kike so, ki sani Prince ta ko'ina tarin masoya yake da shi waɗan da suke
haukar san shi, yana da kyau ki sani tin da momma ta tsaya maki In Sha Allah zaki
mallakesa, kada ki ji tsoron komai, ba zai dakeki ba, dan su basa dukan mata, kin
gansu hakan nan suna girmama mace musamman ke da kike marainiya, suna da zuciyar
tausayin maraya, zaki yi nasara sosai".

Cigaba da kara mata kwarin gwiwa mama Haulat ta yi har sai da ta ɗan saki jiki ta
aminta zata je, sannan ne ta saketa tana

Please Login or Register in order to submit comment