Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin maraici ai zasu so ace ga mai kama da
su ko dan su ji sanyi a ransu, ko da ba ɗan uwansu bane zasu ji matuƙar daɗin hakan
suma yau sun ga mai kama da su, amma ta nuna halin ko in kula, dik yadda aka yi ba
iya baiwa kawai gareta ba, ta san tarihin iyayenta, tasan in da za'a iya samunsu,
dole akwai abin da take ɓoyewa, yarinya ƴar karama da ko 13 years bata cika ba sai
shegen wayo........

Wannan cikin nata ba shakka ya fi tara sirri a cikinsa fiye da yadda yake
ɗaukar abinci, dole a jinjinawa Sweetie yarinya mai wayo kuma ƴar baiwa.

"Sweetie wai ke baki mamakin abubuwa ne?".
Floris da abin yake damunta a rai ta gaza haɗiyewa ce ta jefa mata wanna
tambayar, dan ita dai gaskiya tana mamakin rashin bayyana farinciki ko bakincinkin
da Sweetie bata yi, baka taɓa gane a wani irin yanayi take!.

Ɗan motsa gefen bakinta sweetie ta yi kamar zata ɗan yi tsaki haka, alama ce ta
amsa magana ba tare da ta buɗi baki ba, alama ta yi mata da ita bata wani jin
mamakin komai a rayuwarta, dan ta ga abubuwa daban daban da suka girmi shekarunta
kuma kwakwalwarta ya ɗauka, taga kaddarori da jarabawa daban daban, so yanzu ta
daina nuna damuwa.

"Kina burgeni sosai Sweetie, and kyanki yana tafiya da ni, Please can we be a
friends?". Cewar Floris.
Ta yi maganar tana miƙa mata hannu kamar mai shirin yin musabaha.

Babu wani ɗaukin hakan a tattare da Sweetie, babu wani shauki, ta jinjina mata kai
tare da miƙo mata nata hannun tana faɗin. "Yeah we can".

Sam Floris bata ji daɗin ganin yadda Sweetie bata nuna shaukin hakan ba, amma
bata nuna rashin jin daɗin nata a fili ba, ta danne ta kama hannunta suka gaisa,
daga yau sun zama abokai kuma ƴan uwa.

"Amatsayina na abokiyarki kuma ƴar uwarki na ɗauki alawarin koya maki dik
abubuwan da na sani a duniyar nan". Cewar Floris.

Kanta a kasa tana kallon ƴan yatsun kafafunta da suke ɗan yi mata zafi saboda karon
da suka yi da Ronnie a lokacin da take ƙoƙarin shiga room na Black Tiger, so a
lokacin ya taka mata ƴan yatsun kafafunta, ƴar ƙaniya tun ɗazun da take tare da shi
bata ji zafin ƴatsun nata ba sai yanzu da ya shiga toilet ne ta gane ashe suna yi
mata zogi, ɗazun ganinsa ya kwashe zogin.

So kanta a ƙasa ta amsawa Floris da. "For sure nima zan koya maki dik abin
da na sani a rayuwata, ciki kuma harda addinina".

A hanzarce Floris ta amsa da. "Nima zan koya maki nawa addinin".

Jinjina kai Sweetie ta yi. "Na yarda ki koya mun dik abin da kika sani dangane da
addininki, na kuma yi maki alkawari a dik lokacin da muka yi zurfi cikin koyan
addinan guda biyu, idan har baki ji addinina ya burgeki ko kuma ya kwanta maki a
rai ba, ko kin gane addinin gaskiya daga ciki ba to ni zan koma naki addinin!".
Babbar magana!!

A ɗan ruɗe Floris ta zaro idanu waje, mamaki fal a ranta ta ce. "Zaki dawo
addinina? Da gaske kike yi please?".

Girgiza kai Sweetie ta yi tare da dawo da kallonta a kan Floris, ya tabbata Floris
yarinya ce, ai shi addinin gaskiya baya ɓuya yarinya, wuyarta ki fara koyan ilimi
daga cikinta, kina farawa ko ance ki bari ba bari zaki yi ba, yo Allah wasa ne?!.

"Tabbas in dai kika nutsu kika sami ishasshen ilimi a kan addinina, kika
zurfafa tunani, kika yi dik abin da na gaya maki to ba shakka in baki gamsu da
addinina ita ce ta gaskiya ba zan bi taki". Cewar Sweetie.

Sosai Floris ta ji daɗin wannan furuci na Sweetie, kuruci dangin hauka, ita yanzu
a ganinta zata yi wa Sweetie wayo ne ta shigo addininsu, bata san Sweetie kam da
wayonta aka haifo ta ba, ko mai shekara 20 ba ya gwada mata dabara ba, yarinya
kamar renon tsafaffi, Floris sai dai mu ce welcome to Islam, dan na tabbata dabarar
Sweetie ba zai barki ki iya tsallake wanna challenge ɗin ba, bari ma mu zo mu fara
shirin tarbar sabuwar baƙuwa a cikin addininmu..............

Fitowa Ronnie ya yi ɗaure da bathrobe a jikinsa, launin milk color, white
hairnsa yana ɗigar da ruwa.

Kallonsu dikkansu suka kai a kansa, yana da sexy gorgeous body shi ma, kamar
yayansa, ga yanayin koreans skin ɗinsa sai dai muce masha Allah.

"Beb kai fa nike jira tun ɗazun, ka zo mu tafi". Cewar Floris.

Idanunsa a kan Sweetie ya amsa da. "Ten minutes".
Daga haka ya wuce dressing room ɗinsa.

A gaggauce ya shirya cikin ƙananan kaya crazy, ya fito fes abinsa, ya tsaya gaban
mirror ya canza ɗankunnen dake kunnensa, dama suna dayawa har da wani ta saman
kunne, dik ya canzasu, ya ɗauki wani haɗaɗen gold pil ya sanya a kusa da lips ɗinsa
ta ƙasa, sai ya so ya yi kama da mace, sai ma da ya busar da gashin kansa ya tara
ya ɗaure, idan baka ga kirar sexy badynsa ba kaga iya face ɗinsa zaka yi zaton mace
ce ba namiji ba, kyau iya kyau.

Time da ya fito kasa hakuri Sweetie ta yi har sai da ta ce. "Ni Ronnie na
rasa gane da kai da yayanka waye ya fi wani kyau? Kuma sam baku kama da shi fa, shi
kamanninsa ma daban yake".

Tabbas basa kama, dan Black Tiger dai ba koreans bane, Black Tiger ya fi kama da
turawa gaskiya.

Ɗan lumshe idanu ya yi yana sakar mata murmushi.
"Na fi yaya kyau mana". Cikin zolaya ya yi maganar.

A hanzarce ta ce. "Tun da ka amsa ka fi shi to tabbas baka fishi ba, shi ya fika,
dan dik wanda yake da abu baya fitowa ya ce yana da shi, sai dai a gaya mashi yana
da shi, dan haka baka da kyau".


Floris da mamaki ya gama kasheta ne ta tsoma baki kamar wata mara lafiya a in da
ta ce.
"A ina kika taɓa ganin yayansa har kika san yana da kyau haka?".

Ta ji abin da bata taɓa ji bane, dan tasan ko Ronnie bai san kamaninsa ba, mamaki
kamar ta sume a zaune.

Ɗago kai Sweetie ta yi da nufin ta bata amsa unexpect idanunta suka sauka
cikin nashi. Girgiza mata kai ya yi a kan kada ta faɗawa Floris yadda aka yi da
kuma yadda yayansa yake, ya ɗaura yatsarsa ɗaya a saman lips ɗinsa alamar ta yi
shiru, hakan yasa ta mayar da kanta ƙasa ta rasa abin cewa, ita ga shi ba karya ta
iya yi ba.

"Sweetie ki amsa mun mana". Cike da ƙaguwar son jin amsa Floris ta sake
tamnayarta.

Hakan yasa Ronnie ya katsesu da cewa. "Let's go beb".
Ya yi maganar tare da miƙawa Floris hannu a kan ta tashi su tafi.

Miƙa mashi hannu ta yi ya kamata ta miƙe tsaye, tana matuƙar son ta ji amsa amma ya
hanata ta hanyar janta suka nufi waje yana yi wa Sweetie bye bye haɗe da ce mata
kada ta kuskura ta fita waje, ta zauna a ɗaki by 7 zasu dawo.

Da okey kawai ta bisu har suka fice, gyarawa ta yi ta kwanta tana tunanin rayuwa
haɗe da masoyinta Kamran, true love never end, har yau har gobe soyayyar Kamran
yana ranta, soyayyar gaskiya take yi mashi, ga shi bata san kamanninsa ba, a haka
dai take balai'n kaunarsa, shi kuma kada ku manta soyayyar a mutu yake yi wa
Pretty, dan tun faɗowarta duniya sonta ya dasu a ransa, ko yaya wannan abin zai
kasance? Mu je dai zuwa.

===========🔥💘============

IDAN MUKA WAIWAIYA FRANCE KUWA.

SMART

Tsulundun yake tsundume a cikin jacuzzi cikin toilet ɗinsa, har saman lion chest
ɗinsa ruwan take, haɗaɗɗen kunfa fari tas ne cike a cikin jacuzzin, hakan ya hana
damar ganin tsiraicinsa, ya jiƙa haɗaɗɗen dark black hairnsa da ruwa, hakan yasa
gashin ya kwanto mashi rabi a gefe gefen face ɗinsa, rabi kuma a bayan wuyarsa,
face ɗinsa gabaɗaya a jike yake da ruwa, zara zara eyelashes ɗinsa suna jike, hakan
ya bada damar kyansa ya kara bayyana sosai.

Tinanika kala kala ne cike a cikin ransa, wani irin binciken kwakkwafi a kan wani
technology da zata ciyar da duniya gaba yake yi, a part from duniyar wata da yake
shirin zuwa yana nan yana wata aiki ma dan kara bunƙasa kimiya.

So yake ya leƙa duniyar karkashin ruwa bayan idan ya dawo daga duniyar wata, ya sa
ana shirya kashi nautilus, wato wani katafaren jirgin ruwa ne wanda zai kai ka
karkashin teku cikin kwanciyar hankali, yana dawowa daga duniyar wata yake son
afkawa can, burinsa a kullum ya kawo wata kimiya da zata tashi kan duniya, ga shi
da bala'in iya zurfafa tunaninsa a kan dik wata aiki da yasa a gaba, ga dogaro ga
Allah hakan yasa yake yin nasara a dikkan lamuransa, dayawan masu fikira daga
wajensa suke samun fasaha, nutsuwarsa da bin komai daki daki shi ke kara bawa
mutane mamaki, jan ajinsa da halin ko in kulansa, bai ɗauki komai matsayin wani
abin a zo a gani ba, wasa da makaman kare dangi kamar mai wasa da dunkulen wasa
yakan ɗaga hankulan jama'a matuƙa, musamman wasa da rocket da yake yi, yana ɗaga
hankulan makusantansa, saboda suna tsoron rasashi, shi kuwa lafiya lou yake komai
ɗinsa.

Ya ɗaga kai sama idanunsa a lumshe, da alama ba ƙaramin daɗin ruwan yake ji ba,
kuma ga dikkan alamu tunaninsa da yake faɗaɗawa tana tafiya mashi yadda ya dace
duba da yadda ta nutsu ya nutsa cikin tunanin nasa.

While ita kuma mom suna can gym ita da dad suna motsa jiki, mom tana bawa furenta
ruwa, kun san ta kware a wannan harkar, wajen gym ɗin gabaɗaya kewaye yake da tsaro
na ban mamaki, amma hakan bai hana mom soyewanta da ɗan dattijon mijinta ba. Su fa
sam basa tsufanwa soyayya.

A hankali ya waro idanunsa jin alamar shigowar mutum cikin room ɗinsa. Kamar
wanda baya son motsawa ya juya idanunsa izuwa saman katafaren Tv dake manne da
jikin bango a cikin toilet ɗin.

Heleena ce tsaye a tsakiyar room ɗin nasa tana bin ko'ina da kallo, ta kwana biyu
rabonta da ta shigo cikin ɗakin, yanzu ma sai da ta je ta taso dad a gaba tasa ya
yi amfani da laptop ɗinsa ya cire mata door securityn sannan ta shigo.
Tana nan dai cikin wannan ɗan iskan shigar tata, sai dai yau abin ta taazzara, dan
fa cibiya a waje ne yau, ga wasu ƴan iskan breast ɗinta kamar............ Bari na
raga mata kada nan gaba kaɗan ta zama matar Smart in shiga uku.

Yau wandon ma tsabar iskanci bai kai kaurin kafafunta kamar na Nennen Mahreen
ɗin nan ba, hannunta na ɗauke da tray mai shake da small chop, ita dai ta dage sai
ta kawowa Smart small chop ɗin nan, anya ma ba wani abin ta banka a ciki ba kuwa?

Baiwar Allah bata san ma kyamarta yake ji kamar ya yi amai idan ya ganta ba, ta bi
ta matsawa kanta a kan son shi da son kyatata mashi, ina ga sai mun taimaka mata da
tsayuwar dare kila ta dace, matsalar dai taki musulunta ne ita da mom.

Ji ya yi tamkar zai yi amai na ganinta da ya yi, ko bai tambaya ba yasan dad
ne ya buɗe mata door ɗin nan, to ya zai yi da dattijon nasa? Ai sai hakuri kawai.

A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta tare da mayar da idanunsa ya lumshe su,
cikin ransa ya fara tunani wanda shi kaɗai ya barwa kansa damar sanin me yake
tunawa.

Kamar wanda yake mafarki ya furta. "Am coming for it soon". Ya yi maganar tare da
sauke ajiyar zuciya.

A hankali ya miƙe tsaye tare da zuro kyawawan kafafunsa kasa, ya fito daga
cikin ruwa ya nufi ɓangaren towels dake shirye cikin show glass tamkar shop na
sayar da su ne.

Wata fara kal ya ɗauko mai ɗan girma wadda ta tsaya mashi dai'dai kaurinsa, sannan
ya ɗauki wata mai ɗan girma ya nannaɗo hair ɗinsa a ciki domin tsane ruwan. Gaban
wash hand base ya nufa. Tsayuwa ya yi a wajen tare da kurawa kansa kallo a jikin
mirror dake wajen.

Kamar wanda bai san ya face ɗinsa take ba haka ya kafe kansa da waɗan nan idanun
nasa.

Ya ɗan ɗauki lokaci a wajen kafin ya nufi fita waje, shi da kansa yasan shi ɗin
smart ne na gasken gaske, gifted ba.

Jin motsin fitowarsa daga cikin toilet ɗin yasa Heleena yin saurin ajiye mashi tray
dake hannunta ta juya da sauri, har da haɗawa da ɗan gudu ko ɗar bata ji ba na
wannan uban high heel dake kafanta, tana son sanya shi a idanunta amma tafi jin
tsoron haɗuwa da shi sama son kallonsa da take, dan a kullum hata kyau, ita ake
bari da dakon danasani in suka haɗu.

Sarai ya ga fitarta, amma ko a karkashin sillpers ɗinsa ya wuce izuwa dressing
room. Jim kaɗan ya fito shirye cikin tsadaddiyar jogger a jikinsa ta kasa, ta sama
kuma round neck polo shirt ce, dikka white colors ne.

Hanunsa na ɗaure da wata dankareriyar Rolex-pnd wanda a kalla kuɗinsa ya kai 18
million dollars. Sai tashin kamshin perfume ɗin Mf yake yi, wanda kuɗin wanna
perfume ɗin ya wuci tunaninku.

Wayarsa ya ɗauka ya nufi waje a gaggauce, ko kallan abin da Heleena ta kawo bai yi
ba, ya fice.

Kamar dai yadda dad ya saba saka mashi takunkumi na idan zai fita sai da tsaro gaba
tsaro baya, hakance ta kasance, da ya ce wa dad shi fa yanzu ba yaro bane dan Allah
su kyalesa ya shakata, shi jarumi ne ba rago ba.
Da sauri mom ta karɓi zancen da cewa shi yaro ne kuma dole ta saka idanu a kansa.

Ni dai nace mom bata san dik saka idanunta a kansa na banza bane, domin kuwa shi da
dad dai sun mata wayo, sun gwada mata kwarewa suna can bayan fage suna
sharholiyarsu da rocket.

Kamar zai yi masu gardama, amma farincikinsu shi ne nasa, dan haka ya raba
masu sumbatar kauna a kumatu tare da wucewa ya nufi jerin gwanon motocin da aka
jera domin shi.

Sai dai kamar kullum gidansa ya je ya baro securitys ɗin ya ɗauki tsadaddiyar
motarsa ya wuce World ɗinsa, wato duniyarsa, dan yana bala'in kaunar wannan rocket
factoryn nan nasa fiye da komai, nan ne duniyarsa, yana alfahari da baiwa da ilimin
da god ya bashi.

Yau ta kama saturday ne, garin ya yi shiru sosai, kowa yana makale a gida, ga
wani uban sanyi dake zuba kamar ana watso dissa, a haka kuma bai sanya jacket a
gida ba sai da ya je gidansa ya ɗauki wani katan puffer jacket ya sanya.

Weekend ba aiki ba zuwa office, kowa yana cikin gida, su kuma a yau ne suke
gwada lunching manya manyan makamansu da suka ɗauki tsawon watanni suna haɗasu, sun
yi aiki tukuru domin tabbatar da ingancin dik abin da zasu haɗa, sun sadaukar da
lokutansu ba dare ba rana suna aiki, fatan komai ya dai'daita yadda suka tsara
kawai suke yi.

A lokacin da ya isa world ɗin nasa har an gama shirya komai na tashin makamin, shi
kaɗai ake jira da ya zo ya saita in da zata nufa ya saketa, shararren makami ne
wanda ya ɗara bmt-59 a girma, a kullum burin Smart ya kirkiran wasu makaman da babu
masu kwatankwacin haɗarinsu a duniya, ya zamana su ne na farko da zasu mallakesa,
to yanzu ya yi nasarar kirkiran kala ɗaya wanda ya sha wahala wajen kirkirota, ya
kuma ɗauki tsawon watanni, yana fatan yanzu idan ya gwadata ta tafi yadda yake so.

Babban yaronsa a wajen mai suna Robbert ne ya fara isowa garesa ya tarbesa
domin sanyaya mashi ransa. A tare suka ranƙaya izuwa room na GUIDANCE SYSTEMS
COMPUTER'S.

Wato ɗaki ne mai cike da na'urorin controlling na nuclears ɗin da suke kyarawa,
wasu irin mahaukatan systems ne masu ban mamaki, masu aiki babu kama hannun yaro,
babu batun sanyin battery ko tsufa, dik bayan kwana uku ake zubo sabbi saboda
tsaro, dan kuskure kaɗan idanun suka yi an shiga ɗari ba uku ba, so suna da karfin
aiki fiye da tunaninku, dan ba kamar sauran systems da kuka sani bane.

Gaban wani dankararen guidance system computer ya tsaya.

"Everything is ready sir". Cewar Robbert dake tsaye kyam kamar mutum mutumi
ta gefensa.

Jinjina kai kawai ya yi tare da sanya hannunsa a saman glass na na'urar, touch
screen computer ce.

Wasu bakon lambobi ya shigar kafin nan ainahin cikin na'urar ta buɗe, go come ya
shigarwa ƙwaƙwalwar rocket da zasu harba ɗin, sanna ya yi setting ɗin iya gudunta
da suke buƙata, ya kuma yi setting na iya tafiyar da zata yi da nisan da zata yi ta
juyo.

Sannan ya duba payload ɗinta da kyau. Already nuclear ɗin tana a saman launch
pad ɗinta, su Robbert sun shiryata da kyau, amma dik da haka sai da Smart ya kara
duba launch pad ɗin da kyau, ba wai dan bai yarda da ingancin kwarewar su Robbert
ba ne, tsaro ce kawai, dan yasan ita samun kuskure a kanta dai'dai yake da ɗaukar
rayukan mutane da dabbobi bila adadi.

Hege Smart ya san nuclear in and out, tun basu tasheta ba ya haɗa mata heat
shields, saboda kara nuna kwarewa a kan aikinsa, kun san na gaya maku nuclear bata
haduwa da waje mai zafi, so dole sai an haɗata da heat shields mai karfi wato
garguwar zafi wanda suke bata iska mai sanyin gaske, mai kareta daga zafi.

Hankalinsa ya mayar kan fetur ɗinta, nasan zaku yi mamakin jin cewa tana da fetur,
to ba fetur kai tsaye kamar wanda ake amfani da shi a motocin yau da kullum ba ne.
Ana amfani da wasu nau'ikan man gas propellants masu ƙarfi waɗanda suka bambanta da
mai na yau da kullum.
Ana saka mata Liquid Propellants, Liquid Oxygen (LOX) da Liquid Hydrogen LH2 da
dai sauransu.

Karfin fetur na yau da kullum ba shi da isasshen ƙarfin samar da kuzari don ɗaga
nuclear izuwa sararin samaniya, shiyasa ba'a amfani da shi. Ana buƙatar mai da ke
samar da hayaƙi mara yawa don kada ya shafi tsarin nuclear da yanayi. Yanayin Zafi
nuclears suna buƙatar mai da zai iya jurewa matsanancin sanyi ko zafi, wanda fetur
na yau da kullum ba zai iya yi ba. Fatan waɗan da basu da ilimi a kan nuclear sun
samu karin haske?.

Bayan ya duba waɗan nan abubuwa dik sun shiryu yadda ya da ce, sai ya dawo da eagle
eyes ɗinsa a kan engines ɗinta dan tabbatar da lafiyarsu, dik sai anbi waɗan nan
matakan domin gwada nuclear, aiki ne tukuru sosai.

Dogon nazari ya ɗan shiga a kan dukkan matsalolin fasaha da na tsaro da za a iya
fuskanta wajen tashin nuclear.

Sannan ya shiga tsara yadda nuclear za ta tashi, wace hanya za ta bi, da kuma inda
za ta sauka, tsarin tashi, da tsarin dawo.

Ana bibiyar nuclear yayin da take hawa sararin samaniya don tabbatar da ta bi
hanyar da aka tsara mata. Dayawa nasan zasu tambayi ta ya ake yi nuclear ta dawo
bayan tashinta, to idan Smart ya harbata in zata dawo zaku gani, kuna tare da Smart
zaku samu ilimi kan nuclear matuƙa dan yana da ilimin kimiya fiye da tunaninku,
kuna tare da alkamin princess Teema taku ta amana zaku samu ilimi sosai ta bangare
dikka biyu, wato boko da Arabic kai harma da kimiya mai tafiya da zamani In Sha
Allah.

Sai da ya tabbatar komai yana intact, sannan ya danna tashinta.


Gabaɗaya jami'an dake kusa da launch pad ɗin sai da suka sanya hannayensu a
kunnuwansu suka toshe da karfi, sannan suka sunkuya kasa. Wani irin mahaukacin fita
nuclear tayi wanda hakan ya haifar da karamar girgizar kasa a wajen, kun san tana
da balai'n karfi, dik in ta fita sai ta girgiza ƙasa.

Tsabar karfinta sai da ƙasan wajen da ta tashi ya rufta ya yi wawakeken rami, a
miliyan ɗari ta fita.

Ajiyar zuciya Smart ya sauke ganin aikinsa ta yi kyau, makamin da ya shafe watanni
yana haɗata yau komai ya tafi dai'dai har sun lunchata, abin ya yi mashi daɗi
matuƙa.

Rest room ɗinsa ya nufa dan ya ɗan kwanta ya huta. Da sauri Robbert ya bi bayansa
ko zai buƙaci wani abin ya biya mashi buƙatarsa.

Suna shiga cikin room ɗin ya nufi wajen drawers ɗinsa. A hankali ya buɗe drawer,
kamar wanda baya son taɓa komai.
DIAZEPAM INJECTION ya ɗauko haɗe da sirinji.

Wani irin zaro idanu Robbert ya yi na ganin wanna allura ta DIAZEPAM da ya ɗauko,
allurar barci ce, wato shi fa Smart baya tsoron a mutu, fisabilillahi ka tashi
nuclear ta yi sama sannan tsabar iskanci ka ɗauko alluran barci zaka yi wa kanka?
Idan nuclear ta tashi dawowa waye zai tareta?.........🤔

Ko in aka samu wata matsala ba fata muke yi ba waye zai kula da wanna ɓangaren?.

Robbert ya tsorata amma kuma bashi da bakin iya yin magana, yana ji yana gani
Smart ya dannawa kansa DIAZEPAM ɗin nan a jinin jikinsa.

Saman bed ya haye ya kwanta tare da barin kayan alluran a saman drawer Robbert ya
zo ya tattare kenan.

Nan take idanunsa suka fara dishi dishi yana kallon ɗakin bibbiyu. Robbert
yana tsaye a bakin door room yana ta al'ajabin Smart, da yake shi sabon jami'i ne,
bai saba da halin Smart namu uban jan aji da jiji da kai ba.

Wayar Smart ce ta fara ringing, yana gani dishi dishi ya lalubo wayar daga
aljihunsa. Idanunsa bibbiyu take ganin mashi wayar. Sunan mom ce ya bayyana a saman
screen ɗin, amma ya gaza iya gane abin da yake rubuce, sai yake ganin kamar Heleena
aka saka............😅

Ganin hakan yasa ya ja godon tsaki tare da ya wurgar da wayar a gefensa, kafin wani
ɗan lokaci barci ta yi awon gaba da shi. Bashi da number Heleena fa, kawai sharrin
alluran barci ne yasa ya ga kamar numberta ne.

To Smart team ina fatan kun shirya tarar wanna bujumin nuclear idan ta juyo.🤔

A gaskiya Smart ɗan ikkan zamani ne, wasa yake da nuclear kamar wanda ya samu ƴar
tsana, to thank god dai idan ta juyo ta kansu zata dawo ba kanmu ba, ga shi ka yi
barci ba mai kashe engines ɗinta ya rage mata gudu a yayin dawowa, sai ta afko maku
a miliyan ta yi sama da ku tun da kai iskancinka ya wuce misali, ni dai na yi nan.
Smart team sai a shirya zaman makoki dan da alama za'ayi rashi!.🥱



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

==========🔥🔥🔥===========




ALKALAMIN
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




======JIMETA🔥YOLA========

A tare da Mahreen bappa suka dawo cikin gidan, a lokacin su Jaish sun ɗan jima da
tafiya, iyaka rashin jin daɗi bappa ya ji, har kansa ya ji tana yi mashi ciwo,
gabaɗaya sai ya ji duniyar ta yi mashi wani irin, dan Allah ya gani yana kaunar
Jaish, ya ma mance da auren da ya haɗa a tsakaninsa da Mahnoor, shi yanzu bakincin
ɗaukar mashi yaron da suka yi ne a ransa.

Shiru ya zauna a cikin ɗakinsa yana tunanin mafita, while ita kuma Mahreen tana ta
aikin matsa mashi. Sai faɗi take.

"Bappa dan Allah ka tashi ka je ka karɓo mana hammanmu, su dawo mana da shi".

Kasancewar hankalinsa baya'a jikinsa sai ya zamana sam baya jin diran kamalan
Mahreen a kunnuwansa.

Kamar daga sama ya ji tana faɗin. "Bappa Adda Mahnoor fa tana can tana ta kuka, dan
Allah ka je ka ɗauko mana shi".

Jin batun Mahnoor yasa ya tuna da ita, a hanzarce ya miƙe ya fito. Da gudu Mahreen
ta biyo bayansa, dan a tunaninta bayan Jaish zai bi.

Ɗakinsu ya nufa domin ya duba ƴar marainiyarsa. Ita kuma Nenne tuni ta ruga gidan
Arɗo dan ta gayawa gwaggonta ai an ɗauki Jaish, yau farinciki a wajenta ba'a
misiltawa.

Sai wani daɗi take ji tamkar wani abin

Please Login or Register in order to submit comment