Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 33 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar ransa, dole zuciya ta buga idan kuwa haka ne.

"Yah Ramish why are you talking like that? Talking out of control, and you're
shouting like mad............".

Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata cak sakamakon wani irin tsawa da
Ramish ya daka mashi a kan ya yi mashi shiru.

Taku biyu ya yi ya matsa gabansa, dama tin da ya fara bincike a kan masu nikaf
Bilal ya zare hannunsa yaki taimaka masa, tare suke yin komai, amma a wannan karon
Bilal yaki tayasa, hakan yasa zarginsa a kansa ya karu, sannan ga fita da Bilal ɗin
yake yi shi kaɗai a yanzu, idan baku manta ba a ranar da Ummie ta je ɗakin Ramish
nace maku Bilal baya nan, ya fita ko?. To kun ga kuma a tare suke fita, yanzu Bilal
baya taɓa fita tare da Ramish, sai dai ya fita shi kaɗai, ga yawon dare da yake yi
wanda a baya sam baya yi, baya zaman gida ko wajen aiki sosai yanzu, hakan ya kara
ɗarsa zarginsa a zuciyar Ramish, sannan sai ya rinƙa kawowa Ramish wasu silly silly
abubuwa da basu da amfani ya haɗa shi da aiki yasa Ramish baya aiki bincikensa
yadda ya dace, hakan yasa ya ja lokacin bai iya gano gaskiya a kan abin da yake
bincika ba, ga shi gobe taron da zasu yi ne. A takaice abubuwa dayawa ya ja Ramish
ya fara zargin Bilal tun watannin huɗu da suka wuce.

Da karfi Ramish ya damki wuyar rigar Bilal, idanunsa sun ƙaɗa sun yi jajir, da
alama yana out of control ɗin da gaske, jikinsa har wani kerma ta soma yi, yana
gudun tsono abin da zai iya zame mashi narazana ga rayuwarsa, sannan kuma yana san
tono gaskiya ko dan ya san ina ya dosa da suwaye yake tare.

"Ka faɗa mun me kake ɓoye mun". Cikin zafa Ramish ya yi tambayar haɗe da ɗan
ɗaga murya.

Pretending................. Ƙoƙarin nuna gaskiyarsa Bilal ya yi, yana san nuna shi
ba mai laifi bane kuma babu abin da yake ɓoyewa, hakan yasa ya dunkule hannunsa da
karfi ya kaiwa Ramish duka a kirji. Cikin ɗaga murya ya ce.
"Wani irin abu ne wannan? Meyasa na zama abin zargi a gareka? Meyasa zaka
ce ina ɓoye maka wani abin? Mekake nufi da kalamanka a kai'na? Ko kana tinanin ni
zan iya cutar da kai ne?".

(My people's yanzu na ce waye ya kawo maganar cutarwa a nan? Babu rami meya kawo
maganar rami? Shin Ramish ya ce Bilal zai cutar da shi ne da Bilal ya kawo batun
cutarwa? Ku tayani yin alkalanci a nan wajen.)

Da gudu Dr Raj and Yah Rizwan suka fito daga nasu bedroom ɗinsu jin muryar Bilal
cikin faɗa yana magana. Innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne abin da suka furta
a tare.

Zame hannunsa Ramish ya yi daga wuyar rigar Bilal, da hannu ɗaya yasa ya daki
kirjin Bilal da karfi har sai da Bilal ya yi baya baya ya bugu da jikin bango.
Duuuuuuuuuummmmmmmmmm

"You are lying Bilal! There must be something you are hiding for us, and you have
to tell us what you are hiding today!!". Cewar Ramish kenan.

Bilal domin ya kare kansa ya kuma tabbatar da gaskiyarsa sai ya yi ƙoƙarin kawo
abin da zai kawar da batun ya faɗa masu me yake ɓoye masu, sai ya yi ƙoƙarin yin
faɗa da Ramish ta yadda hakan zai ja wancan zancen ta kau.

Da karfi ya nufi Ramish da nufin zai rama dukan kirjinsa da ya yi. Dr Raj da Yah
Rizwan ne suka shiga tsakaninsu da gudu, sanya karfi Bilal ya yi ya bangaje Dr Raj
da karfi har sai da ya faɗi a saman sofa. Yah Rizwan kuma ya taresa yana mai daka
mashi tsawa a kan ya nitsu su bar shir men nan.

Yah Ramish dai yana tsaye yana binsa da kallo, mamaki ne ma ya kama shi, wai yau
shi da Bilal ne a irin wannan yanayi? Wannan wace iriyar musifa ce? Su da suke san
junansu tamkar su yi wa juna numfashi! To wai me matsalar ne?.

Ya jefawa kansa tambaya, jikinsa dik a mace sosai, sam baya san dukan Bilal, dan
wlh idan ransa ya ɓaci za'a iya kwasan Bilal ranga ranga, shiyasa yake ya ƙoƙarin
koran shaiɗan kada ya kaisa ya barosu, dan har yanzu yaki yardanwa da zuciyarsa
Bilal mai laifi ne. Allah sarki zuciya, kun san dama da wuya ya iya karɓar wannan
kaddara idan har ba yaga da gaske ido da ido Bilal ya cutar da shi ba.

Da sauri Ramish ya juya ya koma cikin bedroom ɗinsa, basu ankara ba sai ji suka
yi ya banko kofa da karfi ya murza key, a cewarsa koma menene kamata ya yi ya
binciko da kansa, a matsayinsa na babba bai kamata ya tsaya tambayar Bilal ɗin ba
ma ai, kamata ya yi ya tsaya da kansa ya binciko gaskiya, zubar da girma ne ma ya
tsaya sa in sa da wani, shi da yake da hanyar gane gaskiya, shi da Allah ya bashi
ilimi da kaifin ƙwaƙwalwa! Ai bai kamata ya wani damu ba!.

Yah Rizwan ne ya ja Bilal suka wuce bedroom ɗinsa, Dr Raj kuma ya bi bayan yayansa
Ramish. Sai dai ko da ya je sai ya tadda Ramish ya rufe kofa, har kamar zai yi
knocking sai kuma ya tina halin yayan nasa, yanzu a banza zai ɓata lokacinsa dan
Ramish ba zai sauraresa ba, hakan saya ya juya ya bi bayan Bilal dan ya je ya ji me
ya haɗasu faɗane wai, su da suke kamar twin's................To harshe da haƙora ma
watarana ai suna saɓawa bare ƴan adam malam Dr Raj.

A ɓangaren su Sharifat kuwa, Leesharh ta dawo daga unguwar da ta je cikin ƙoshin
lafiya, ta yi wanka da sallah tana kudundune a cikin bargo saman bed, Sharifat bata
a ɗakin, tana wajen Ummie ɗinta, dan Ummie ta ce ta zo su kwana yau a tare dan tana
da magana da ita.

Shiru ta kwanta tana tunanin duniya, karfe 11 na dare ta buga, time ɗin na
bugawa wayarta ya hau ƙara alamar shigowar kira. With her full confidence ta janyo
wayar.

Ganin private number ya sa ta yi saurin sakin siririn murmushi wanda ya fi kama da
murmushin ramakon gayya. Wayar tana gab da katsewa ta yi picking tare da karawa a
kunnenta.

Shiru aka yi ba'ayi magana ba, a gadarance ta ce. "Hello wanene?".

Daga ta cikin wayar ta tsinkayo muryoyi guda biyu suna magana kus, kus, kus alamar
suna shirya abin faɗe kenan. Da yake bata jin me suke faɗe sai ta ce. "Idan baku
gama tsara abin da zaku faɗa mun tun kafin ku kirani ba me na kirana? Ai da sai ku
bari sai kun gama tsarawa ko?".

Shiru basu amsa mata ba, cigaba da magana ƙasa ƙasa suka yi. "Okey ni ina da abin
yi, idan kun gama shawartawa zaku iya sake kirana, dan nima yanzu jiran call ɗinku
nike yi". Ta kai karshen maganar tana ƙoƙarin cire wayar a kunnenta da ta katse
kiran.

"Kada ki kuskura ki katse mana call". Daga ɗayan ɓangaren aka faɗi hakan. Gabanta
ne ya yi wani irin mummunar faɗuwar jin voice ɗin kamar na Bilal. Amma sai ta
daure, kun santa da jajircewa, ta nuna kamar bata san masu kiran nata ba, cikin
nuna isa ta ce. "Da yake wayarku ce ba sai ku hanani katseta in gani ba".

"Ke kin san da suwa kike magana kuwa?".

Siririn tsaki ta ja, har da wani wuwwurga idanunta sama da ƙasa ta yi masu kallon
up and down kamar tana gabansu, a walaƙance ta ce. "A fagen iskanci ko da shaiɗan
nike magana karshe kenan a dik wani zalinci ko? To ko da shi nike magana bai isa ya
ɗaga mun murya ya faɗa mun ga abin da zan yi da wayata ba".

Da suka fahimci faɗa ta zo da shi, su kuma lallaɓata suke da bukatar yi, dan su
suke nema a wajenta, sai suka sassauta murya, cikin nitsuwa aka canza murya, da
alama wani ya karɓi wayar.

"Dik ba wannan ba, magana muke san yi dake, ajiye dik wani zafin kanki da
tashen balajarki a gefe ki sauraremu".

Jin haka yasa ta amsa da. "Ina jinku".

"Kin san da cewa aikinki bai kare ba ko baki sani ba?". Ya jefa mata tambayar haɗe
da yin shiru yana jiran amsarta........... "Zaka iya cigaba da magana, saboda ba
zan iya kowace magana in amsa ba, idan ka gama faɗar dik abin da zaka faɗa sai in
tattare in baku amsa guda". Ta yi maganar tana miƙewa zaune.

"Okey zaki iya yin dik abin da kike so, amma ina san ki sani mahaifinki na
hannunmu, ko ki yi mana abin da muke so, ko kuma yau lahira ta yi bako, wlh a daren
nan idan baki nemo mana masaniyar a in da su Ramish zasu yi wannan taro ba, tabbas
zaki rasa mahaifinki".

Tin da take a rayuwarta bata taɓa yin dariya irin wanda ta ƙaƙalo dan dole a yanzu
ba. Bushewa da dariya mai ɗan sauti ta yi. Shiru suka saurara suna jinta, har da
rungumo pillow ta yi a kirjinta tsabar dariya.

Sai da ta yi mai isarta sannan ta dakata haɗe da ɗaure fuska lokaci guda, sannan ta
sauko ƙasa daga saman bed ɗin, gaban mirror ta nufa wayar na manne a kumnenta, har
ta kusa isa wajen kuma sai ta koma ta kunna wutar ɗakin yadda zata ji daɗin ganin
kanta da kyau, sanye take da wando da riga na barci masu kyau launin ash colar.

Tsayuwa ta yi a gaban mirror, cike da kwarin gwiwa take bin kanta da kallo, dik sun
yi shiru suna jinta, amsarta kawai suke san ji.

Raunartar da muryarta ta yi, kamar wata marainiya haɗe da fuskar tausayi, cikin
nuna damuwa ta fara magana kamar haka.

"Dan Allah kada ku cutar mun da babana, zan yi dik abin da kuke so, ku yi
hakuri kun ji?..................." Tana gama faɗar haka ta wani irin ɗaure fuskarta
sosai, cikin kakkausar murya ta cigaba da cewa. "Haka kuke son jin na faɗa ko? To
baku isa ba, wlh ba zan sake yin abin da kuka ce ba, mahaifina kuma Allah ne ya
haliccesa ba ni ba, dan haka shi zai karesa ta in da baku taɓa zata ba, ba zan sake
cutar da wani a dalilinku ba, na saka mashi guba na cutar da shi a farko, na sake
zama sanadiyar da aka harbesa da bullet, na sake zama sanadiyar da aka shirya bomb
da zai kashe mutane dayawa, na cutar da Ramish sosai wanda dole a yanzu na gyara
kuskure kada Allah ya kamani, shi kuma babana ku je ku da Allahn da ya haliccesa,
sannan kada ku manta idan kun kashe babana ku kuma ku tabbata a duniya kada ku
mutu, daga karshe ina yi maku mummunar albishir da cewa wlh tallahi dik da ban taɓa
ganin fuskokinku a zahiri ba, to ku sani zan iya gane ne ku, sannan ku sani nasan
gidan wannan mata mai kibar, bugu da kari kuma ku sani dik maganganun da muke yi da
ku tun daga ranar farko har zuwa yanzu ina da recording ɗinsa in audio a cikin
memoryna da na yi mashi ajiya mai kyau, dik time da muka yi waya ina recoding in
saka memoryna in yi copy in cire in ajiye dan samun shaida, ku jirani yanzu
lokacina ne, dik sai na ɗauki fansan abin da kuka yi mun, kuma Ramish da izinin
Allah ya fi karfinku, daga yau ni zan zame mashi garkuwa mai taimaka mashi ta
hanyar da bai zata ba, sai asirinku ya tonu azzalumai, kuma ku kwana da sanin cewa
nasan wanenen Bilal a cikinku, kuma tabbas dan na taya Ramish aiki zan shiga jikin
Bilal, zaku sha mamaki". Babu tsoro ko miskala zarratin a ranta ta zayyano
maganganun nan. Tana gama faɗar hakan ta katse wayar tare da kashe shi mai
gabaɗaya.

Idan hankalinsu ya kai muliyan to fa a yau ya tashi. Ita kuwa kallan kanta a cikin
mirror ta yi, a fili ta furta. "Lokacin ku ya fara daga yanzu, wlh ba zan dai'na
zargin Bilal ba, kuma zai gane bashi da wayo a lokacin da zan kama shi cike da
hujojin da ba zai iya kubcewa ba, zai sha mamakina, sun ɗauka bani da ilimi bani da
wayo ko? To su shirya, Bilal kai ma lokacinka ya fara, zaka sha game na karya, zaka
gane baka iya cin amana ba, am sorry Yah Ramish, kila idan na tayaka wannan yakin
ka iya yafe mun laifukan da na yi maka, is time now!". Ta kai karshen surutan nata
tare da juyawa ta isa ga switch, kashe wutar ɗakin ta yi ta wuce izuwa saman bed
abinta.

Jama'a na ce ku tafawa Leesharh, ana ganinta kamar wawiya ashe tana da wayo, kenan
harda recoding na maganganunsu ta rinƙa yi? Lallai ta cika jajirtatciya, kenan
saboda ta gane wanenen Bilal ta aminta da soyayyarsa ko dai ya abin yake? Akwai
cakwakiya kuwa! Muje dai zuwa dan muga ya wannan wasa zata kaya. Amma kuna tunanin
masu nikaf zasu barta da ranta? Kada ku manta ta yi masu barazana da hujoji masu
karfi kamar recoding nasu, sanin gidan Hajiya two seater, sanin Bilal da dai
sauransu, kuna tunanin zasu barta ta tona masu asiri?. To sai dai muce Allah yasa
ta kai wayewar garin gobe, dan gaskiya akwai matsala, suna fa da mutane a cikin
gidan, ga shi Sharifat bata ɗakin yau, fatana kada su saka mutanensu su biyo dare
su kasheta fa.........😥

••••••••••••••• FOREST•••••••••••••••🔥🔥🔥

Kwance suka isko Pretty a cikin runfar da ya yi wa Auta a lokacin da suka ƙarisa
wajen. Ta yi barci baiwar Allah, ta cinye kifinta tas har da haɗawa da na Auta
abinta, dik ta yi masu tas.

Kallon Hoorain Auta ta yi, a ɗan shagwaɓe ta ce. "My Hero yunwa fa nike ji". Cike
da mamaki ya amsa da. "Ba na kawo maku abinci ba".

Taku step biyu ta yi ta matsa kusa da shi. "Ai ɗaukin ganinka yasa na tafi na bar
abincin, kaga kuma Pretty ta cinye".

Jinjina kai ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Bari in je in kama maki wata in gasa
sai in kawo maki, je ki zauna kusa da Pretty".

Make mashi kafada ta yi ba tare da ta yi magana ba. Kawar da kallansa a kanta ya yi
yana tambayar menene kuma. "Ni dai sai dai mu tafi tare". Kamar zata yi kuka ta
yi maganar.

"A'a bana san ki wahala, wajen da ɗan nisa, zauna bari in dawo". Kara make mashi
kafaɗa ta yi. "A'a ni ban yarda ba sai dai mu tafi tare".


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




"A'a bana san ki wahala, wajen da ɗan nisa, zauna bari in dawo". Kara make mashi
kafaɗa ta yi. "A'a ni ban yarda ba sai dai mu tafi tare".

"Haka kike so?".
Kai ta gyaɗa mashi da sauri alamar e. Da hannunsa ya nuna mata hanya a kan ta
wuce su tafi.

Sake make mashi kafaɗa ta yi. "Ni dai ko ka wuce gaba ko kuma mu jera a tare". Ta
faɗa tana ɗan karkata kanta.

"Meyasa to?". Cike da mamaki ya yi tambayar............... Ɗan ɗaure fuska kaɗan
ta yi, cike da zolaya ta ce. "Saboda bana san in wuce gaba ka yi ta kallona, ina
tafiya kana kirga mun taku na one by one kana kalle mun shape na bayana kaga ba
alkyabba na..........."

Ƙasa ƙarisa maganar ta yi sakamakon ɗagowa da ya yi a miliyan ya sauke kallansa a
kanta, kwata kwata abin da bai taɓa kawowa a ransa ba kenan, mamakinta ne ya kama
shi, ko a ina ta koyi magana har haka........ Ni kuwa na ce tana matsayin masoyiya
kuma aminiyar Chuchu ƴar wanka ai fin haka ma zaka ji, su da suka kware wajen bawa
flowers ruwa, ai a banza uncle Jahiz yake cewa basu girma ba, ya zo ya gansu tare
da flowers ɗinsu a nan ne zai tantace sun girma ko basu girma ba, yaran yanzu ai da
wayonsu ake haifarsu.

Ganin ya yi shiru kamar wanda ya yi suman tsaye ne yasa ta ɗaga mashi gera guda
alamar yane?. Shi kuwa shirun da ya yi tinanin time da take ƴar yarinya da bata
wuce 5 years ba yake ɗaukarta idan sun fito ita da su Chuchu yake yi, dan a lokacin
an bashi ragamar kula da ita.

Ganin ta ɗaga mashi gera guda yasa ya nisa tare da kawar da kallonsa daga kanta,
kamar ba zai yi magana ba, sai kuma dan ya cire mata tinanin nan na banza na cewa
yana kallan shape ɗin jikinta yasa ya ce. "Ai na rigada na gama kalle shape ɗin tin
bai fito ya zama cikakken shape ba, dan a shekarunki biyar kam ai bai fito ba, kuma
a hannunna shape ɗin ya bayyana, dan haka na san..........."

Bai ƙarisa maganar ba ta rufe mashi baki ta hanyar harara da ta dallah mashi. Kawar
da kansa ya yi tare da juyawa yana jin kamar ya saki murmushi, sai dai bai iya
murmushin ba, zuciyarsa ta ji daɗi ganin yadda ta ɗaure fuska tana harararsa.

A kule ta ce. "Wannan shi ne babban kuskuren da mace zata yi ta so wanda ya san
yarintarta, kullum sai ya yi mata gori, koma dai me zaka ce ka ce, ai a da lokacin
da shape ɗin ya bayyana a hannunka kana kallona a matsayin kanwarka ce, yanzu kuma
kallon masoyiya kake mun, dan haka manufarka a kallona yanzu ya sauya!".

Ya fahimci maganganunsa sun ɗan sosa ranta, dan haka sai ya juyo da nufin ya bata
hakuri. Ganin ya juyo kuma taga alamar hakuri zai bata yasa ta juya mashi baya irin
ta yi fushin nan.

Yana ƙoƙarin fara yin magana ta yi saurin barin wajen ta nufi wata hanya daban tana
ɓata rai. Ɗan girgiza kai kawai ya yi, dama yasan fin haka ma zata yi, dama renonsa
ce ita, mata, mata, mata sai dai shirin Allah wlh, dik yadda mace take sonka hakan
ba zai hanata yin abin da ta yi niyya a kanka ba, kai idan mace bata wahalar da kai
ma wlh ba son gaskiya take yi maka ba, wata haka kawai zata kirkiro faɗa, ku yi ta
yi har sai ta kureka, sai kuma ta ce wai tana gwadawa ta ga irin karfin son da kake
yi mata ne, ta azabtar da kai, idan ka yi complain ta ce baka sonta, mu dai sai
shirin Allah wlh.

Ganin ta ɗan yi mashi nisa yasa ya yi saurin rufa mata baya. Fahimtar yana
biyota yasa ta watsa a guje ta shige cikin wasu dogayen ciyayi dake kusa da korama.

Ba shiri ya bita da gudu dan kada ta ci karo da wani abin ya cutar da ita.

Yana sanya kansa a wajen ciyayin zai bi bayanta ita kuma tana fitowa da gudun
gaske. Karo suka unexpext. Baya baya ta yi zata faɗi ya yi saurin riƙo hannunta.

A miliyan ta faɗa jikinsa haɗe da datse idanunta gam, a tsananin tsorace murya na
kerma ta ce. "Tamisa, wlh akwai tiger a wajen ruwan nan". A rikice take maganar
tana haɗe word, jikinta har kerma yake yi.

Shiru ya ɗan yi yana jin yadda kirjinta yake bugawa da karfi karfi alamar ta
tsorata sosai.

(Anya Hoorain ba shiru ya yi yana jin daɗin tula tulanta da suka taɓa chest ɗinsa
ba kuwa🤔 shi ma yanzu ban yarda da shi ba 🥱 team Hoorain kada ku ce na ce, na ce ɗin
😅
a zo a saka mun gas)

Kamar saukar aradu haka ya tsinkayo gurnanin damisam a kunnensa. Kafin ya tabbatar
da gaskiyar abin da yake ji tuni ihunta ya fasa dodan kunnnesa, da karfi ta zunduma
ihun haɗe da cewa. "Hoorain ba ka jishi ba, wayyo daddyna". Yau ta manta da my
hero, Hoorain kai tsaye aka ce, ƴar ƙaniya ta hango mutuwa!.

A tsananin rikice ta yi maganar tare da sakesa zata gudu ba tare da tasan in da
zata nufa ba. Ya fahimci ta rikice sosai, idan ya barta ta tafi ma zata iya afkawa
wani wajen ta cutu, idan kuma ya tsayar da ita ba zata taɓa barinsa ya kwaci kansu
daga hannun wannan damisa ba, to yanzu me abin yi kenan?.

Ya jefawa kansa tambaya, a hankali ya sanya hannunsa a waist ɗinsa dan ya ji ya
mayar da takobinsa mazauninsa ɗazun ne ko bai mai da ba.

Kankameta ya yi da hannu ɗaya ya hanata tafiya. Ajiyar zuciya ya sauke jin takobin
yana nan. Da karfi ta riƙesa tana ihu taki ta yi shiru. Yana tinanin yadda zai yi
da ita sai ganin damisan ya yi a gabansu ta fito ta wajen koramar da gudun bajinta.

Wani jibgege da shi, ya ci ya ƙoshi, ruwa ya zo sha a wajen koramar ta je ya ganta,
kun san kuwa dole ya biyota dama shi ne kuma ya biyota ɗin.

Ko kaɗan Hoorain bai ji tsoro ba, ita kuwa jin gurnanin dab da su yasa ta kara
ƙanƙamesa tana faɗin shikenan ta mutu yau. Ido cikin ido Hoorain ya kurawa damisan
nan kallo babu ko tsoro.

Wani irin uban tsalle wannan damisan ya daka sai kansu da gudun gaske. A
miliyan Hoorain ya ture Auta gefe da karfi, cikin zafa shi kuma ya durkushe
gwiwowinsa a ƙasa, hakan yasa damisan ya wucesu ya dira a bayansu.

Cikin zafa Hoorain ya juyo ga damusan tare da miƙewa tsaye, ita ma da ya tureta ta
faɗa cikin ciyayi a haukace ta miƙe tsaye, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita.
Hakan yasa suka rabawa damisan hankali gida biyu, ya ganta ya ga Hoorain, ya rasa
wazai fara kaiwa farmaki.
Tsayuwa cikin jarumta Hoorain ya yi tare da ƙara ɗaure fuska sosai, irin babu wasa
a tattare da shi ɗin nan. Yasan halin dabobi sosai, yasan da cewa komai ƙanƙantar
motsin da suka yi yanzu damisan nan zai sake daka tsalle ya yi kansu ne dan zai yi
tunanin hari zasu kawo mashi. Hoorain yana san zaro takobinsa yana tsoron motsawa,
shi ba damuwarsa ya motsa damisan ya yi kansu ba, da kansa shi kaɗai zai yi da da
sauki, idan ya yi kan Auta ai damka ɗaya zai yi mata sai gawa.

Yana ƙoƙarin zare takobinsa cikin dabara Auta da ta miƙe tsaye a yanzu ne ta
kurma ihu tare da nufarsa da gudu. Motsin da ta yi ya yi dai'dai da damisan ya sake
daka tsalle ya yi kansu. Hakan ya bawa Hoorain damar zare takobinsa, da karfi yasa
hannunsa ɗaya ya sake ture Auta baya ta koma in da ta taso, da karfi shi ma ya yi
gefe, a karo na biyu damisan ya sake dira a bayansu, Auta ta sake tafiya ta faɗi
cikin ciyayin dake wajen again.

"Kada ki tashi". Shi ne abin da Hoorain ya faɗa mata da karfi, amma ina bata
jinsa saboda tashin hankalin da take ciki.

A lokacin kuma ran damisan nan ya gama ɓaci, ya fusata sai ya nufi Hoorain da
karfin gaske yana wani irin buɗe baki. Ko kaɗan Hoorain bai tsorata ba, yana tsaye
damisan ya isa garesa, cikin zafa suka fara kokawa yana ƙoƙarin zana mashi fata da
takobinsa, daga karshe ma takobin faɗuwa katsa ta yi damusan ya haike mashi, da
waɗan nan shegun faratunan hannun nasa ya fara kai mashi gafsa ta ko'ina Hoorain
yana ƙoƙarin kaucewa.

Tsorata na ganin damisan ya kayar da Hoorain a ƙasa ya haiƙe mashi yasa numfashinta
ɗaukewa diff ta zube ƙasa. Shikuwa kokawa suka cigaba da gwabzawa da damisan,
ƙoƙarin kama agarar damisan ya fara yi tun da takobinsa ta faɗi ƙasa, in ya kama
agaransa dolen dolensa ya risina mashi.

Gabaɗaya damisan ya yagushe mashi face ɗinsa, gwabzawa suke yi sosai, daga shi har
damisan kowanne daga cikinsu burinsa ya cinma abin da yake muradi, damisan yana
haran wuyar Hoorain, shi ma yana haran agarar damusan.

Ya sha wahala sosai kafin ya samu ya ture damisan daga kansa, sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment