Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 26 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



E..............16




Tari sosai Auta ta fara yi, kuka ya ci karfinta, ta rasa me zata yi, idan ta ce ta
yarda da shi ba shi ya kasheta ba, to kenan wanene? Akwai mai kama da shi ne a
kingdom ɗin? Kai ina hakan ma ba zata taɓa yiwu ba, dole shi ne dan kamanninsa ba
zai taɓa ɓace mata ba.

Idan kuma taki yarda da maganarsa wani ɓangare na zuciyar tata yana faɗa mata zata
cutar da zuciyar bawan Allah, zata cuceshi ta sanya shi a damuwa bayan ita kanta
tasan baya karya, iya gaskiya yake faɗe, to ita yanzu ya zata yi da ranta?.

Ta jefawa kanta wannan tambaya da bata da amsa. Shi kuwa sai magiya yake yi mata
yana rantse mata da Allah akan bashi bane, sambatu kala kala yake yi mata. Ko
Pretty da gigin giyar yarinta yake ɗebanta ta fahimci zallar gaskiya a tattare da
shi bare ita Auta da tasan shi fiye da kowa, amma ya zata yi? Ta shiga ruɗanin da
ba zata iya tsayar da zuciyarta a waje guda ta yanke abin da ya dace da ita ba.

Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, akwai tsananin ciwo zuciya ta zargi
masoyin da ta fi kauna sama da komai ya cutar da ita ko ya ci amanarta, wannan
zuciya ta kan iya kamuwa da ciwo, kuma da matikar wahala ta iya sake yarda da wani.

Kuka ita ma Pretty ta fara yi tana cigaba da ambatar Auta ta tashi, ta daina
yin kuka................ Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin yadda ta
rikiɗe da yin tari mai sauti mai kuma karfi har tana kwarewa, cigaba da bata hakuri
ya yi yana kara rantse mata da Allah bashi bane.

Bata kulasu ba, ta yi wannan kukan har sai da ya isheta, sannan ta tsagaita dan
kanta. Yana ƙanƙame da ita, tin yana sambatu shi ma har ya ƙasa iya cigaba da yin
magana ya yi shiru.

Pretty tin tana kuka har ta yi shiru dan dole. Dan sun lura Auta ba zata ji
rarrashin nan da suke burin yi mata ba.

Sai da suka ji ta dakata da kanta ne Hoorain ya yi saurin ɗago da kallonsa a kanta,
da kyar murya na rawa ya iya ce mata. "Dan Allah ranki ya daɗe ki yi hakuri, wlh
bani bane, kuma ba zan taɓa iya cutar dake ba, please trust me!".

Shiru ta yi kamar ba zata tanka mashi ba, idanunta a datse gam, jikinsa dik sai
kerma yake yi, da kyar ta ɗaga hannunta izuwa saman hular yakin dake face ɗinsa
dai'dai saitin kumatunsa. A hankali ta waro idanunta a kansa, sun yi jajir kamar
wuta saboda ta sha kuka har ta goge Allah.

"Hoorain na san ba zaka yi mun karya ba, saboda baka yi baka saba ba, ina da
tabbacin a kai'na kuma ba zaka fara ba, dik abin da yake fitowa daga bakinka
zuciyata ta shaida zallar gaskiya ce kawai, na yarda da kai, amma zuciyata tana
cikin tashin hankali da ruɗanin wanenen mai kama da kai da ya yi yunƙurin kasheni?
Meyasa sai a siffarka za'a zo cutar dani? Dan kawai zuciyata ta shaku da kai? Shin
akwai wanda shakuwarmu ta tare mashi wani abin ne ko ta takura mashi?".

Lalllai sai ka saurara da kyau zaka iya gane me Auta take faɗe, saboda yadda voice
ɗinta ya dashe na kukan da ta sha. Tabbas ya ji maganganunta dikka shi kam, dan a
matse yake da buƙatar san jin ta furta mashi ko da kalma ɗaya ne, dako yake yi dama
shiyasa ya kasa kunne ya saurara da kyau.

Hannunsa dake cikin hand gloves ɗinsu na mayaƙa ya ɗaura mata a saman face
ɗinta, zafafan hawayenta yake san goge mata amma kuma yana jin shakka shakkar yin
hakan ba tare da ta bashi izini ba, dan haka sai ya ce. "Ina neman alfarma da ki
bani izinin in share maki hawaye kafin na baki amsar tambayarki!!".

"Meyasa kake san goge mun hawayena?". Ta gefa mashi tambaya.

"Saboda bana san ganinsu a face ɗinki, da murmushi mai kwantar da hankula face
ɗinki ya dace, kuma da shi muka sanki, bamu san wani abin bayan cool murmushi a kan
face ɗinki". Idanunsa a kan face ɗinta yau kam ya yi magana.

"Da gaske Hoorain zuciyarka bata san ganin hawayena?". Cike da mamaki haɗe
matsuwa da san jin amsar da zai bata ta yi tambayar.

Jinjina kansa ya yi. "Tabbas zubar hawayenki babban tashin hankali ne wanda zai iya
zama barazana ga zuciyata, bana san shi, hankalina yana tashi sosai kuma rai'na
yana sosuwa matuƙa idan naga kin haɗe rai ma ba sai an kai ga kuka ba".

"Meyasa kake jin hakan a kai'na?". Ta jefa mashi tambayar ne cike da yakinin
abin da take san ji daga garesa zai furta mata ko ranta zai yi sanyi, tabbas ta
yarda da shi, tasan baya yi mata karya, sai dai har yanzu zuciyarta yana cikin
ruɗanin da Allah ne kawai zai iya warware mata, daɗin daɗawa da ace shi ya yi
yunƙurin kasheta tin farko da tabbas ba zai taimaketa a cikin wannan dajin ba,
tabbas daga haɗuwarsu izuwa yanzu da ya jima da gama ƙarisa hallakata ya jefar da
ita, amma ransa ma ya sadaukar ya cecesu, ya kuma yi jinyarta, sannan ya zube
gwiwowinsa a kasa yana neman ta tsaya ya mayar da ita gida, kai gaskiya ko iya
waɗan nan hujojin sun isa a gaskata cewa bashi bane ya yi niyar kasheta, to yanzu
tambayar a nan ita ce wanenen ya yi niyar kasheta? Sannan kada ku manta yana
Kingdom of justice, wato wajen Queen Zarina kenan, to ya aka yi hakan? Lokaci ne
zai warware mana komai In Sha Allah, muje dai zuwa!!.

"Ban san dalili ba, abin da nasani kawai shi ne bana san tashin hankalinki"..

Allah sarki, jin ba abin da ta yi tsammanin ji daga garesa bane yasa ta sauke
wahalallen ajiyar zuciya tare da jawo yawu mai wuyar haɗiya ta haɗiyesa da kyar, ta
yi tinanin zai ce saboda yana santa yasa baya san tashin hankalinta, sai ta ji
akasin haka. Jikinta ne ya kara mutuwa sosai, yanzu ta gama yardanwa kanta da gaske
baya santa, dama ranar ta ji yana faɗawa su Ansar baya santa, ashe ita kaɗai take
dakon kaunarsa. Fahimtar hakan yasa wasu zafafan hawaye masu ɗumin gaske suka fara
wanke mata fuska da gudun gaske.

Bawan Allah, ya so faɗa mata amsar da take san ji, ya so ce mata saboda santa
yasa baya san ɓacin ranta, sai dai tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi, yana jin kamar
ba zai iya furta mata ba, dan yana ganin kamar ba zai sameta ba, kamar ko ya faɗa
mata a banza ne, ba za'a bashi ba kuma ita ma ba lallai ta yarda ta aminta da shi
ba dik da yana ganin kamar tana san shi kuma abokansa suna yi mashi wannan hasashe
na tana san shi ɗin.

Dagewa ta yi da karfinta ta yunkuro zata bar jikinsa. Cikin sauri ya rikota, ƙasa
ƙasa a nitse ya ce. "Zaki fama ciwonki idan kika tashi fa".

Tabbas ya fahimci amsar da ya bata ne ta sosa ranta har take san barin jikinsa,
amma sai ya yi kamar bai fahimta ba, dik dan ya yi ƙoƙarin tsare kansa daga shiga
bala'i.

"Kada ka damu Hoorain, a yanzu na samu kwarin gwiwar son mutuwa fiye da
rayuwata, babu wata amfanin zamana a duniya tin da burina ba zai cika ba, ka barni
ciwon ya fama kawai na mutu............"
Bata iya ƙarisa maganar ba kuka ya cikarfinta sosai wanda ya tilasta
mata yin shirun dole.

Wani irin bargon sanyin jikine ya lulluɓesa, sai ya ji ya yi nadamar faɗa mata
hakan da ya yi, yanzu bata da lafiya, kamata ya yi ya faɗa mata kalamai masu sanyi
da zasu kwantar mata da hankali, ba ya tsaya biyewa zuciyarsa ba.

"Ranki ya daɗe ki yi hakuri, ki sani rayuwanki shi ne namu, kada ki yi mana wasa
da shi kin ji?".

Pretty dai kallansu kawai take yi, sun yi nisan zango cikin larabcin da suke yi,
dama ita ba sosai ta iya ba, sama sama ne haka, ta fi iya turanci a kan Larabci,
Sweetie ta fita iya larabci, dan haka sai ta dai'na fahimtar abin da suke faɗe dan
sun yi mata nisa, kawai ta hau aikin binsu da kallo.

"Hoorain ina san ka dai'na yaudarar zuciyata haka nan, ka barni dan Allah, wai
me na tsare maka ne ma da kake wahalar da ni?". Cikin kuka ta yi maganar.

Sam bai gane maganar da take yi ba, shi ya rasa ya zai yi, dan gaskiya ya san ko
mutuwa yake yi ba zai sameta ba, yanzu haka mutuwa yake kwana yana wunin yi a cikin
zuciyarsa dik a kanta, to ina ga ya furta mata soyayya sun kuma kara shakuwa da
juna? Me kuke tinanin zai faru a lokacin da za'a rabasu?.

"Dik wani abin da bakya so daga yau na dai'na yi, ba zan sake ba kin
ji?". A sanyayye ya yi maganar.............. "Ka tabbata dik abin da nikeso zaka
yi?". Kai ya gyaɗa mata alamar ya tabbata. Ajiyar zuciya ta sauke tare da zame
hannunta daga face ɗinsa, a hankali ta yunkura zata bar jikinsa.

"Akwai in da kike san zuwa ne in kai ki?". Ya jefa mata tambaya. "A'a zan sauka
daga jikinka ne kawai ina ga sai ya fi mun daɗin faɗin abin da nike san ka yi mun".

Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, sannan ya sauketa ƙasa a
hankali cike da kula yana ce mata sannu. Zama ta yi a ƙasa suna fuskantar juna,
tana matuƙar jin azabar ciwon da yake jikinta, amma haka ta daure.
"Yaushe zaka mayar da ni gida?."
Tambaya ta farko da ta fara jefa mashi kenan.

"Yanzu haka a kan hanyar gida muke, ƙoƙarin mayar dake nike yi, sai dai muna da
nisa sosai, zamu iya yin kwana biyu a dajin nan kafin mu iya fita". Cikin girmamawa
ya bata amsar.

"Ka zauna da kyau to sai mu yi magana". Ta faɗa a sanyaye.

Matsawa kusa da ita Pretty ta yi suka manne da juna. Kallo ɗaya Hoorain ya yi wa
Pretty ya kawar da kansa, ya maida kallansa a kan ruwan dake gudu a gefensu, yana
satar kallan Zunaira ta witsiyar ido.

"Ranki ya daɗe nafi san in tsaya a kanki dan tabbatar da babu wani abin cutarwa
da zai tinkaro in da kike". .
Kai ta girgiza mashi kafin ta ce. "Kada ka damu, babu wani abin cutarwa da zai
cutar da mu In Sha Allah, yanzu dai zauna".

Ba musu ya zauna, amma bai so hakan ba, sai ya lankwashe kafafunsa ya ƙarisa zama
daga durkushen da yake.

"Ina wayata take?". Ta gefa mashi tambaya.
Shiru ya ɗan yi, yana tinanin a ina wayar take, shiga tashin hankalin da ya yi a
sanadiyar ɓatarta ya ja ya mance ina ma wayar tata yake.

Ganin yana tinani yasa ta fahimci ya ajiye wayar a in da ya manta ne, dan haka sai
ta kawar da zancen da cewa. "Hoorain ina san ka mun wata alfarma guda ɗaya kafin
mu koma gida".

A kanta ya tsayar da idanunsa, sannan ya ɗan jinjina mata kai kafin ya amsa da.
"Wace alfarma kenan gimbiya?".

"Ina san idan ba damuwa dan Allah ka bari in kalli face ɗinka ko da sau ɗaya ne a
rayuwata kafin mu koma gida, ina san kallanka sosai"............ Shiru ya ɗan yi
lallai Zunaira ta zo da babbar magana, ga shi a wannan gaɓa ba zai iya yi mata
gardama ba, saboda ta kuresa a yanzu, alfarma ta nema wanda ta wuci hakan a
wajensa, innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ya zai yi yanzu? Tun yana ɗan
shekara bakwai ya fara sanya hulunan yaki yana rufe face ɗinsa, kunga kuwa tin ba'a
san za'a haifeta ba kenan, babu wanda ya taɓa matsuwa da ya ga face ɗinsa sai ita,
dan haka bashi da kwarin gwiwar kallanta ya ce ba zai iya yi mata wannan alfarma
ba, ransa dai bai so ba, amma ya zai yi tin da farincikinta yake so!.

"In Sha Allah ba zamu bar cikin wannan daji ba har sai kin kalli face ɗina
ranki ya daɗe, na yi maki alkawari, amma ba yanzu ba dan Allah, kin ji ko?".

Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sannan ta ce. "Ina Abbo?".

"Yana gida na barosa"....... Shiru suka ɗan yi kamar babu mutane a wajen.

"Hoorain". Ta ambaci sunansa a hankali. Ba tare da ya dawo da kallonsa a kanta ba
ya amsa mata da na'am.

"Meyasa baka san kallona kai tsaye sai dai ka rinƙa satar kallona kamar wanda
bashi da gaskiya?".
Ba tare da ya juyo da kallan nasa a kanta ba ya ce.
"Saboda in kina tare da ni bana iya ɗaukar minti ɗaya ba tare da na ganki
ba, ba zan iya zuba maki ido in yi ta kallanki kai tsaye ba kamar yadda ba zan iya
daure ban kalleki ba, shiyasa nike kallanki a sace".

Haka kawai baiwar Allah ta ji murmushi ya kubce mata, wato shi baya shakkar faɗar
gaskiya fa, bawan Allah. Sosai ya ji daɗi harda sauke nannauyar ajiyar zuciya
lokacin da ya kalli ta yi murmushi, har ya ji ransa ta sanyaya sosai.

"Meyafaru kake sauke ajiyar zuciya?". Ta jefa mashi tambaya.
"Saboda kin yi murmushi shiyasa na ji sanyi a rai'na, ban ma san na sauke ajiyar
zuciya ba sai da kika yi magana".

Allah sarki zuciyar masoya, sai ta ji wani irin daɗi ya kara ratsata, har tana ji
kamar ta kasance da shi a cikin wannan yanayi a wannan waje na har abada, ita jin
daɗi da daular da suke da shi ba shi ne a gabanta ba, Hoorain shi ne kawai
damuwarta, in dai zasu zauna cikin wannan yanayi mai daɗi yana ganinta tana ganin
shi to ta gwammaci zama a wannan daji fiye da ta koma wajen ƴan uwanta.

Wato soyayya fa hegiyar aba ce, ko da yake ayoyi sukutum ne da ita a cikin
Alqur'ani mai girma, dan haka zata yi fin hakan ma in dai so ce, Allah dai ya
taimakemu kada ya bamu damar san waɗan da basa sanmu, Allah ya haɗamu da masu sanmu
na gaskiya!!.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Sun jima a wannan waje suna hira, tun yana amsa mata kai tsaye har ya dawo binta da
okey da kuma e or a'a, dan shi bashi da yawan magana, sai jansa da hira suke yi,
dan yanzu Pretty ma ya ware ta fara tayata.

Sai da rana ya tsaga ne ya ce masu su zo su koma wajen da ya tanada masu bari ya
nemo masu abin da zasu ci. Basu yi mashi musu ba, suka miƙe da kyar Auta tana jan
kafafunta a ƙasa.

"Ranki ya daɗe ina neman wata alfarma". Ya faɗa yana kallan ƴan fararen kafafunta.

Jinjina kai ta yi. "Ina jinka". "Dan Allah ki bani damar in ɗaukeki zuwa wajen".
"Meyasa?". Ta sake jefa mashi tambaya. "Saboda bana san ganin kina shan wahala".

Wani irin daɗi ta ji ya ziyarceta a ranta, tabbas bata cire ran Hoorain zai sota ya
kuma bayyana mata soyayyarsa ba a yanzu.

Jinjina mashi kai ta yi alamar ta bashi dama, ai tin kafin ta gama zayyana ta
bashi damar ya ɗauketa cak sai saman kirjinsa na zakunan mazajen nan, ya riko
hannun Pretty suka kutsa cikin dajin, suka koma in da suka fito, wato wajen da ya
gyara ya tanada dominta, waje mai cike da yanayin soyayya da nishaɗi.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangare guda kuwa, Sadauki kusan hauka ya yi a lokacin da ya kawo masu ziyara bai
samesu a wajen ba, yau a karon farko sai da ya durkushe gwiwowinsa a ƙasa, dik da
ba'a iya ganin face ɗinsa sai idanu, yau sai da tashin hankali ta bayyana acikin
idanun nasa mai firgitarwa.

Cike da tashin hankali da damuwa ya fara kewaye arear wajen yana nenan ta ina zai
gansu? Damuwarsa ma yadda Auta take da ciwo a ciki bata warke ba, hakan ta kara
ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa har kerma yake yi yana tsuma. Ya ɗauki a kallah
mintuna 30 yana kewaye a yankin yana nemansu, dan gani yake suna nan a wajen basu
yi nisa ba.

Wani irin damuwa ya ƙara shiga a lokacin da ya yardanwa kansa basu nan, basu wannan
yankin kwata kwanta sun yi nisan zango, ga shi babu wata makama da ya gani wanda
zai iya hasashen meyafaru da su? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne kawai
kalaman da yake ta maimaitawa, ya shiga damuwa na wuce misali.

Da kyar ya iya jan kafafunsa ya kutsa cikin dajin da ya je ya cigaba da nemansu a
can ko Allah zai sa ya gansu.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

After some minutes, rana ta take sosai, zaune Pretty da Auta suke a saman dutse
kusa da wata bishiyar gwaiva, hannunsu rike da ganyen ayaba mai ɗan faɗi, gasassun
kifi ne a saman ganyen ayabar wanda Hoorain ya kawo masu, ga kayan fruits a
gefensu, basu san daga ina ya samo kifin ba, su dai ya ce masu su yi zaman jiransa
yana zuwa, shi ne ya dawo masu da kifi gasassu kuma ya sake tafiya ya barsu ya ce
yana zuwa.

Sai rarraba idanu Auta take yi tana jiran taga ta ina zai ɓullo, ta gaji da
jiransa, dik bayan second ɗaya kara ɗaukin san ganinsa take yi, bata gajiya da shi,
a kullum tana san taga tana a tare da shi.

Ita kuwa Pretty tinanin kifin kawai take yi, kunsanta ita da ci akwai amana, sai
tinanin kifin take yi, ya bata sha'awa, ta yi mamakin ganin irin gashin da ya yi
masu, tana da yakinin a wajen wancan wuta da ya kunna mata dan jin ɗumi ɗazun nan
ya gasa masu, ya kamo kifin a kogi kenan ya gasa a can.

Gajiya da gafara sa bataga kaho ba Auta ta yi, dan haka sai ta miƙe tsaye, a
hankali ta ce. "Pretty zauna ki jirani ina zuwa".

"Ina zaki je ki barni?". Ta jefa mata tambaya.............. "Ke dai ba zan yi nisa
ba kuma ba zan wani jimaba, ina zuwa yanzu".

Jinjina kai Pretty ta yi tana cigaba da gutsirar kifinta tana kaiwa baki abinta
sarkin ci kawai, har yanzu dai bata canza hali ba a fagen ci.

Saukowa kasan dutsen Auta ta yi, sannan ta miƙi hanyar da take tinanin yana ta
wajen. Tana tafiya tamkar mai tsoron taka ƙasa, saboda ciwonta idan ta yi sauri zai
fama. Tafiya a hankalin yasa bai ji zuwanta ba, yana tsaye saman dutsen dake gaban
wannan koramar, yana ƙarisa wanke takobinsa da bai samu ya yi ɗazun ba.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Tin da ta doso wajen ta hangosa daga nesa tsaye saman dutse, gabanta ne ya yi wani
irin faɗuwa sosai, kirjinta ya bada dukan uku uku, bata san time da ta ɗaga kafarta
da sauri wajen ƙarisawa garesa ba. Sam bai ji alamarta ba, ya bawa hanyar da take
zuwa kuma baya yana karisa wanke wanke takobinsa da bai ƙarisa ɗazun ba. Ya kuma
ɗauro alwala dan ya yi sallah.

A wani irin slow ta ambaci sunan cike da salon da bata san ta iya shi ba.
"Hooooooooooraiiiiiiiiiiiiin" haka ta faɗi sunan.

Da karfi ya juyo domin ya ji abin ne kamar almara, kamar voice ɗinta kamar kuma ba
nata ba, sai ya ji kamar mafarki kamar kuma gizo, hakan yasa ya yi saurin juyowa da
karfi.

Juyowa da ya yi da karfi yasa kyakkyawar dark black curly hairnsa ya watse kamar
wata mace kamar kuma wanda aka hurawa gashin iska ya watse haka.

Ya ilahi ya lilliahi! Mutuwar tsaye ta yi tana kallansa, kamar wadda aka zarewa
rai, ta kame kam. Shi kuwa cikin zafa ya diro ƙasa daga saman dutsen, da wani irin
gudun gaske ya nufota. Zaro idanunta ta yi tana mamakin me zai yi mata da ya nufota
da irin wannan uban gudun kuma? Ga lafiyayyar takobinsa a hannunsa.

Ku me kuke tinanin zai faru? Yau dai ta ganshi babu hular yaki, ko ya kamanninsa
take? Meyasa ya nufeta da gudu dan ta gansa bai rufe fuska ba, meyasa ta yi sumar
tsaye dan ta gansa? To ni dai bari in leƙa Black world muga me suke ciki kafin in
dawo muga me zai yi mata kuma mu ga ya kamanninsa yake da yake ɓoyewa tsawon
shekaru, yau dai komai ta bayyana..........🥱

••••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••••🔥

A wani irin razane Ronnie ya juyo da kallonsa a kan yayan nasa. Wani irin razana ya
yi ganin yadda Black Tiger ya ɗaure fuska tamau alamar babu tausayi babu imani.

Nan take wasu irin zufa suka fara keto wa Ronnie babu kakkautawa, shikenan yau
Sweetie ta ja mashi yanka kazar wahala, watar azabarsu ce ta tsaya.

With her full confidence sweetie ta ce. "Ronnie kada ka damu, kwantar da hankalinka
ka dai'na yin zufa, Big bro kana ɗagawa Ronniena hankalifa, kuma ni bana san hakan,
ka dai'na kada rai'na ya ɓaci". Yadda ta yi maganar yadda kuka san uwar Ronnien ce
take magana.

Ronnien da ya kusa sakin fitsari a wando saboda tsorata ne ya kara zaro idanu waje
tare da juyowa gareta da kyau ya kuma saki hannunta da ya rike.

Sai dai kafin ya kai ga juyowa gareta da kyau Black Tiger ya juyo magic eyes ɗinsa
a inda tamkar walkiya haka ya fisgota ta ƙariso gabansa. Cikin zafa rai a matuƙar
ɓace ya sanya hannunsa ya yi mata wani irin mahaukacin damka a wuya mai razanarwa
wanda sai da ta ji kamshi kamshin mutuwa.

Ta ɗauka wasa yake yi, bata san baya ɗaukar wargi ba, a tinaninta idan tana
tsokanarsa ta wannan hanya zata iya samun damar shiga jikinsa har su fara aiwatar
da plan ɗinsu a kansa, bata san shi ɗin tamkar dutse yake wanda huda jikinsa a
shiga ba ƙaramin abu kamar yadda ta zata bane, in ta yi kokarin shiga jikinsa ya zo
mata da karar kwana ma ai sai ta mutu ba damuwarsa bane.

Wani abin da baku sani bama, da farko wlh Ronnie ya so ya yi amfani da shiga
addininta dan su samu Spender ne, dan ya lura tana san addininta sosai, shi ne kuma
rauninta, amma da yake Allah ba'ayi mashi wayo kuma ya so shi da rahma, sai ya dasa
mashi kaunar addinin a ransa na gaskiya wanda zai ma iya sadaukar da ransa a kan
addinin ba tare da ya ji komai ba!!.

Da gudu cikin tashin hankali Ronnie ya nufi Black Tiger domin ya bashi hakuri ya
saketa. Sai dai bai kai ga ƙarisawa wajen ba ya tsaya cak ya kasa gaba ya kasa baya
kamar mutum mutumi.

Ita kuma ya ƙara shaketa da kyau da kyau, tin tana iya ganinsa har ta fara gani
dishi dishi. Babu imani babu tausayi ya yi wurgi da ita ta tafi ta bugu da jikin
swan chair dake ɗakin nasa ta faɗi kasa.

A wahalce ta saki wani irin azabbabben kuka mai tsuma zuciyar mai imani ba irin
black heart ɗinsa ba, shi ko kaɗan bata bashi tausayi ba. Bai bata damar ta yi
ƙoƙarin jawon numfashinta ba ya sanke amfani da magic ɗinsa ya janyota gabansa tana
zube a ƙasan, shi kuma yana tsaye kamar wanda aka sassaƙa, ransa a matuƙar ɓace ne.

Ko kaɗan bai ji kamar zai tausaya mata ba, kafarsa guda ɗaya ya ɗaga ya sauke mata
saman wuyarta, ya taketa ba tare da kalli in da take ba. Wani irin bargon azaba ne
ta ji ya lulluɓeta, da gaske niyar kasheta ya yi, hasashen Ronnie ya saɓa hanya da
ya ce mata Black Tiger ba zai iya kasheta ba, ashe dai sai in black heart ɗinsa
bata motsa ba, tsab zai aikata fin kisa.

Sweetie ta shiga gonarsa dayawa, dama kuma already ransa a ɗan ɓace yake sakamakon
addaba mashi da duniyar sheɗanu suka yi, suna kutsawa cikin ruhohin tsafinsa suna
birkita mashi lissafi, abin yana bakanta mashi, yana ta ƙoƙarin ya rufe dik wata
hanya da zasu iya riskar ruhohin tsafinsa ita kuma ta zo zata kawo mashi wargi, shi
ne ya tattare haushin waje guda dikka ya sauke a kan!.

Bai ɗauke ƙafarsa daka samar wuyarta ba har sai da yaga ta daina numfasawa ta ɗauke
diff rai ya yi halinsan! Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Sannan ne ya ɗauke
ƙafarsa tare da yunƙurin zai yi ball da ita ta fice mashi daga ɗaki, sai kuma ya
tina idan ya yi hakan gawar tata zata tarwatse mashi a cikin ɗaki ta ɓata mashi
waje, dan haka sai ya yi amfani da magic ɗinsa wajen ɓatar da ita, kafin kyaftawa
da

Please Login or Register in order to submit comment