Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A kasale sosai voice ɗinsa take fita.

Ko a jikinta kamar an yakushi kakkausa, cikin sanyin murya ta ce.
"Ni da nike da Allah da manzonsa meyasa zan ji wani damuwa dan wani bawan
Allah ya cusguna mun? Dik abin da kaga ya faru dani mukaddari ne daga Allah, kuma
mu mun yi imani da Allah dole mu karɓi kaddararmu hannu bibbiyu a dik yadda ta zo
mana in ma mai kyau ko akasinta!".
Baiwar Allah tana magana tana murmushi.

Ɗan zaro idanu Floris ta yi tana kallon Ronnie, ta ji sabon karatu yau. Shi ma
Ronnie zancen Sweetie ya taɓa zuciyarsa, dan haka ta wutsiyar idanu ya kalli Floris
while ainahin kallonsa yana a kan Sweetie, tabbas har cikin ransa ya ji yana son
sanin wannan Allah da manzonsa da idan ka riƙesu ka bi umarninsu ba zaka taba shi
damuwa ba, dik wahalar da Sweetie ta shiga, ga makanta dik, uwa uba aka rabata da
ƴar uwarta, ga rashin iyaye, dik bata taɓa shiga damuwa ba dan ta rike Allah da
Manzonsa, dik azabar Black Tiger bai ɗaga hankalinta ba saboda ta rike Allah,
hakika zai so shi ma ya san ta yadda zaka bi ka rike Allah har ka more haka, sai
dai kuma da kamar wuya in dai yana Black world.

"Ya kayi shiru Ronnie?". Cewar Sweetie.

Girgiza kai ya yi ba tare da ya furta uppan ba, amma abin ya bashi matukar mamaki
kuma ya ratsa zuciya da gangar jikinsa, sai nanata kalmar idan ka rike Allah da
manzonsa, ka yi imani da su ba zaka shiga damuwar komai ba, Allah ba zai bari ka ji
kunci ba, sai nanatawa yake yi a cikin ransa yake yi, like wow abin ya ƙayatar da
shi ba kaɗan ba.

"Ronnie zaka je wasa ne?". Floris ta jefa mashi wannan tambaya.
Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya yi magana ba, da alama jikinsa ya yi weak sosai,
bawan Allah ya ji ɗaya daga cikin karfin ubangijin gaskiya!!.

Idanunsa a kan Sweetie, ita ma tana rike da wayarsa da ta karɓa daga hannun Floris
dan ta gani, amma kallonta da nutsuwarta na'a kansa, Allah Ronnie ko baka son ganin
kowa in yana waje sai ka ji sha'awar ɗaura idanunka a kansa, saboda kyau, sai ma
idan yana murmushi tare da ƴanmatansa.

Ga shi ya karyawa Delisha kafa tana can tana jinya, wato Ronnie ma fa mugune wata
sa'an, yanzu haka ta fara samun sauki tana koyan takawa da sanda, amma ta ji a
jikinta kam, ta gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah ne ƴar banza.

"Ronnie zan bika wajen wasan ka ji?". Cewar Sweetie.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Zo mu je, time ya cika, tun da kuka zo gidan
nan ke da Floris kullum nine bayan shiga wajen wasa".
Murya a kasale ya yi maganar.

"Meyasa to?". Sweetie ce ta jefa mashi tambayar.

"Saboda biye maku da nike yi mana, kullum nine karshe".

Floris ce ta karɓi zancen da cewa. "And you're a winner everyday ba".

Kashe mata ido ɗaya ya yi alamar haka ne zancenta. "To kuzo mu je".
Ya faɗa yana miƙa masu hannu.

Kusan a tare suka kariso gabansa, wayarsa dake hannun Sweetie ya fara karɓa ya zura
a aljihu kafin ya kama hannayensu, suka nufi waje.

Sai daɗi Sweetie take ji yau, hakika tana da karfin tawakkali da imani da Allah
Sweetie, ta yadda da kaddara mai kyau ko maras kyau, bata sanyawa kanta damuwa ko
kaɗan, idan ta tuna kuncin dake cikin rayuwarta, cikin sauri take tunano girma da
niimomin da Allah ya yayi mata, hakan yakesa ta mance ƙuncinta, mu koya daga gareta
domin mu ji daɗin gudanar da al'amuranmu cikin nutsuwa, mu kuma kara karfafa
imaninmu!!.

Sosai filin wasan skaternsu yau ya cika, matasa sai gwada baiwarsu suke yi, ga
ƴan gasa sun shirya tsaf, tsabar kaunar wasan da Ronnie yake yi, yanzu haka yana
kammala karatunsa zai shiga wasannin duniya gabakiɗaya bisa yardar Black Tiger, ya
yi mashi hakan ne dan ya faranta mashi ransa sosai.

Kowani matashi yana gwada baiwarsa, babu nuna ragonta, dik sun tsaya tsayin
daka dan nuna jarumtarsu.

Saman ƙayatattun kujeru na musamman ya zaunar da Floris and Sweetie wanda tun
shigowarsu wajen idanun kowa yake a kansu.
Saboda kaunar wasannin Ronnie yasa Black Tiger ya gina masu wannan stadium ɗin, dik
dan farincikin kanin nasa.

Tin da ya sako kafafunsa cikin wajen jama'a suke ihun sunansa da ɗaukar tafi da
hannayensu, ji kake fito ya karaɗe ko'ina, da alama suna murnar zuwansa sosai. Ya
saye zuƙatan kowa!.

Sai da ya sumbaci kumatun Sweetie and Floris sannan ya juya ya shiga fili, nan fa
tafi da fito ya kara yawaita sosai.

Master Devil ne ya bashi skatersa ya sanya a ƙafafunsa, dik wajen nasa takalmar
ce kawai ta fita daban, dan haɗuwa da tsadarta ya wuci tunaninku, dik takalmar
wasanninsa da ɗanyar gold Black Tiger yasa aka kyara mashi su, kunga kuwa ai bazama
ayi zancen tsada ba, dan akwai kuɗi kam.

Zuba mashi idanu su Sweetie suka yi suna ta kallonsa, shi ma idanunsa yana a
kansu. Ƴan wasa gabaɗaya sun tsaya layi kowa jira yake yi su fara, sai fito ake yi.

Wani katon warriors wanda ya ji horo ya ƙoshi ne ya hura masu usir dan a fara
wasa. Tafi da karfin sautin fito ne ya kara karaɗa wajen.

Floris ma tafi ta fara yi tana faɗin Ronnienta ne winner. Ganin tana tafi yasa
Sweetie ma ta fara yi, yanzu dik abin da Floris ta yi ita ma sai ta yi.

Kun san wasan skater kusan yana tafiya ne da zuciyar mutum, kamar gudun doki ne,
idan kana a kan doki, to gudunsa ya ta allakane da yanayin bugawa da gwazon
zuciyarka, shi ma haka yake.

====================💘🔥

Ko gargada Ronnie bai taɓa yi a wasan skater ba, sai ga shi yau saura kaɗan ya
yi wani mummunar faɗuwa Black Tiger ya tare mashi da magic ɗinsa, ba komai ya
haifar da hakan ba kuma face Sweetie.

Suna tsaka da tafi ita da Floris suna kallonsu suna nishaɗi, kwatsam sai ta nuna
takalmar ƙafarsa da yatsanta tana tambayar Floris amma takalmar Ronnie na gold ne
ko?. Dan ta gansa yana kyalli sosai.

Wannan nuna shi da yatsa da ta yi unexpect magic ɗinta ya fita, baiwar Allah sam
bata ma san yadda zata sarrafa magic ɗinta ba, dan bata san da shi a tattare da ita
ba, in dai zata nuna abu da hannu to da wuya idan magic ɗin bai fita ba, kuma a iya
hannun hagunta ne abin.

Wani ɗan siririn haske ne ya fita daga hannun nata kai tsaye sai kan takalmar
Ronnie da ta nuna hasken ya nufa, hakan ya haifar mashi da tuntuɓe, da yake Black
Tiger yana ganinsu ya ga magic ɗin nata, ya kuma yi sauri ya tare shi, amma dik da
haka da yake nata yana da karfi sosai sai da ya sa Ronnien tuntuɓe kamar zai kifa
ƙasa, da ya faɗi kuma za'ayi mummunar faɗuwa, saboda ƴan wasa dayawa suna biye da
shi a baya, da dik zasu faɗi, wasu su faɗi a kan junansu.

Dayawan mutanen dake wajen sun sha madarar mamakin ganin Ronnie ya yi tuntuɓe, sai
dai ba wanda ya ga dalilin hakan, shi kansa ya ɗan yi mamaki, dan dai wajen flat
yake babu wani gargada, to me ya sanya shi wannan tuntuɓe? Ya jefawa kansa tambaya.

Yana can yana wannan tunani har wasu ƴan wasa biyu suka tsere mashi ba tare da ya
farga ba, sai da ya ji ihun Floris tana ambatar sunansa ne ya dawo daga duniyar
tunanin da ya afka.
Cikin tafasar jini ya fara gwabza wasan, kafin wani ɗan lokaci ya wuce waƴan can.

A lokacin da ƴan wasan can suka wucesa har sai da damuwa da rashin jin daɗin hakan
ya bayyana a saman face ɗin sweetie, Allah sarki bata san ita ce sanadi ba.

Shiru Black Tiger ya yi yana tunanin meyakamata ya yi domin cire magic dake
jikin Sweetie? Dan in ba haka ba watarana zata iya zama ajalin Ronnie ba tare da
sun sani ba, ko da bai rabata da magic ɗin ba ya zamana shi yake sarrafa magic ɗin
nata, dan tsaro, ita bata san da shi a tattare da ita ba, zata yi ɓarna sosai a
dalilin hakan.

Can wani zuciya ya ce mashi. "To ai kila saboda magic ɗin nata ne yasa aka ce ita
ce zata kawo karshenka!".

Tuna hakan yasa ya kara ɗaur wanna fuska mai kama da hadarin, dan in kuwa hakan ce
da wuya ya iya sarrafa magic ɗinta, tunani ya fara yi a kan wacece ita ma tukun nan
? Ina asalinta yake? Wani shafaffe da mai ya bata magic?. Waɗan nan sune tunanin
dake ransa!.

Ni dai bana tunanin mahaifiyarsu Sweetie ce ta bata magic, domin kuwa mom ɗinsu
baiwar Allah ce mai riƙo da addini, ga shi har ta koyar da su karatun addini da har
suka koyawa Kamran ga shi yanzu tana karantar da Ronnie girman Allah, kun ga kuwa
mom ɗinsu mutuniyar kirkice, da wuya ta koya masu tsafi.

Dik yadda aka yi ko dai mahaifinsu ne ko kuma wannan sadauki mai taimaka masu ɗin,
akwai dai cakwakiya da sarkakiya mai ɗaure kai, to Pretty ma tana da shi ne ko dai
iya Sweetie ce kawai?.

Da alama kuma ita ma Sweetie sai da ta haɗu da Black Tiger ne magic ɗinta ya
bayyana, dik yadda aka yi magics ɗinsu yana da alaƙa ko dai wani abin makamancin
hakan!!.

Lokacin da Ronnie ya matso kusa da su sai da ya kashe masu ido ɗaya. Fito mai
sauti Floris ta saki, ita kuma Sweetie da bata iya fito ba sai kawai ta sakar mashi
murmushi tana cigaba da yi mashi tafi.

A karo na biyu ta sake cewa Floris. "Amma skater kafar Ronnie da gold aka yi ta
ko?".

Kai Floris ta gyaɗa tare da cewa. "Yeah, da gold yaya yasa aka yi mashi".

Ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin yadda suke facaka da gold, bayan kuma Ronnie ya
gaya mata irin tsada da darajar da gold yake da shi, amma a haka suke abin da suka
ga dama da shi, bata san arzikinsa Allah ya yi masu ba, a tunaninta saya suke yi,
hakan yasa take kara jinjinawa karfin arzikinsu.

Da gudu Floris ta miƙe ta nufi cikin wajen wasa, da idanu Sweetie ta bita
tana mamakin ina zata je to?.

Tana zuwa ta daka tsalle ta faɗa jikin Ronnie dake tsaye, abin ku da babu Muslunci
a waje, iyayen Floris suna wajen suna ganin wasan, amma ko kaɗan basu damu ba dan
Floris tana yawan rungumar Ronnie, shi ma kuma yana ɗaukarta, wani lokaci har
goyata yake yi, babu ruwansu......... Kai wato musulunci fa ya yi a rayuwar nan,
Allah dai ya bar mu a cikin addininmu har karshen rayuwarmu, samun kanka a cikin
addinin musulunci ba karamar ni'ima bace da Allah ya yi maka, yakamata a kullum
bawa ya rinƙa yawaita godiya ga Ubangijin taliƙai!!.

Da hannu ɗaya Ronnie ya ɗaga Floris, a saman shoulder ɗinsa gabaɗaya ya zaunar
da ita, ta ɗaga hannayenta jikka biyu sama ya fara playing skater da ita, dama idan
da sabo sun saba yin haka, dik cikin ƴan wasan babu wanda yake da karfin iya ɗaukar
wata ya kuma yi playing wasa da ita sai Ronnie, shi kaɗai ne yake iya goya Floris
ko ya zaunar da ita a saman shoulder ɗinsa, ta zauna tamkar tana zaune a saman
kujera, ya yi ta wasa da ita, shi ya fita daban da sauran ƴan wasa.

Da hannu ya yi wa Sweetie alama a kan ta zo. Ba musu ta taso cikin nutsuwa ta
ƙariso in da yake. Nan fa kallo ya koma kanta, sun ga madarar kyau.

Haka kawai yau Ronnie ya tsinci kansa da jin haushin mutanen wajen dan suna ta
ganin Sweetie, bai taɓa damuwa dan sun kalli wani ko wata ba, idan baku manta ba ya
taɓa faɗawa Sweetie cewa sai mace tana da kyau ake kallonta, idan ma jama'a basu
kallonta ai bata cika mace ba, to sai ga shi yau Sweetie ta cika mace ana kallonta
kuma yana jin haushi.

Gabaɗaya idanun jama'a ya dawo kanta. Tana zuwa ta tsaya a kusa da shi, dik sai
ya ji wasan ta fita a ransa, ji ya yi su koma cikin gida kawai.

Amma haka ya daure ya sanya ɗayan hannunsa ya ɗagata sama sai saman shoulder ɗinsa
ta ɗayar gefen, ita da Floris suka haɗe hannaye suka ɗaga sama suna sakin murmushi.

Nan take wajen ya ɗauki ihu da fito, haƙiƙa Ronnie ya samu horo mai kyau, ko
nauyinsu bin ji ba ya fara rolling da su a saman shoulders ɗinsa, abin ya yi
matuƙar ƙayatarwa ya kuma ɗauki hankular jama'a, basu taɓa ganin irin hakan na. Su
Sweetie kamar wasu ƴan baby.

Allah sarki Delisha kuwa tana can tana fama da dogara sanda. Dik abin da suke yi
master Devil yana ganinsu, dan yana wajen.

Tabbas wasan yau ya kayatar matuƙa, wasa ne da ba'a taɓa yin irinsa ba, Ronnie ya
kawo sabon salo ya kuma kara tafiya da zumatan mutane dayawa.


__________AFTER SOME MINUTES🔥

Yamma ta yi, rana ta yi sanyi irin bayan la'asar ɗin nan. Barci mai nauyin gaske ne
ya ɗauki Sweetie, tana kwance saman bed ɗin Ronnie, dan yaki yarda ta bar room
ɗinsa, saboda yana ganin kamar idan ta bar room ɗinsa Black Tiger zai iya cutar da
ita, yana ganin kamar zamanta a nan ne zai hana Black Tiger taɓa lafiyarta.

Floris tana tare da Angela suna buga triangle game kamar yadda suka saba,
Angela ɗaya daga cikin yara marayun Black Tiger ne, kyakkyawar yarinya mai farar
zuciya, zubinta sak na ƴan Black world ɗin.

Sanye yake da swimming short, babu riga a jikinsa, yau ainahin wrestling
surarsa ta bayyana, idan ka gansa a cikin kaya sai ka gansa ɗan siriri zubin
Koreans ɗin, ashe ba haka bane, murɗaɗɗen mutum ne sosai, daga wanka ma ya fito.

White hairnsa a ɗaure ya busar da ita. Part na Black Tiger ya shiga, a maimakon ya
shiga master room na yayan nasa sai ya wuce izuwa gym, ta wani glass way mai
matuƙar burgewa da ɗaukar hankali ya bi.

Yanayin hanyar idan ka hau kana iya ganin kasa, sai kaga kamar zaka faɗa idan baka
saba bi ba, dan zallar glass ne.

Like wow, sai dai mu ce masha Allah, amma wanna waje ya amsa sunansa gym ɗin da
gaske, ya kawatu da abubuwan motsa jiki kala daban daban masu bala'in kyau.

Cikin shigar da ya saba ganin Black Tiger da shi yau ma ya gansa.
Kusa da shi ya tsaya, a ɗan shagwaɓe ya ce. "Brother open your face, because you
look so beautiful, I want to see you again, Please stop covering your face".
Kamar zai yi kuka ya kai karshen maganar, kamar wani ɗan yaro, ashe haka
yake magana da Black Tiger, sai dai kada ku manta cikin harshen koreans suke
magana!.

Wasu irin mahaukatan barbell mai ɗauke da weight plates masu bala'in nauyin da
zasu iya kai goma goma ta kowani ɓangare ne a hannun Black Tiger yana ta ɗagasu
yana saukewa.
Da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci ya jima a gym ɗin yana motsa jiki, ga
wani care luxury glass a idanunsa, hakan yasa ba'a iya ganin kwayar, gaskiya Black
Tiger hege ne, ganinsa kawai yana firgita hantar manya da ƙananan halittu.

Bai tankawa Ronnie ba yana cigaba da ɗaga wannan barbell ɗin kamar bai san da
halitta a wajen ba.

Ɗan zunɓura baki Ronnie ya yi tare da ƙarisawa wajen, DUMBBELL ya ɗauko ya fara
ɗagawa yana kallon kwanjin hannunsa, ga wasu layukan guraye a cikinsa kamar wanda
ya zana da gangan, kuma dik horo ne ta yi mashi yawa, cikin nan nasa a shafe manne
da baya.

Cigaba da ɗaga dumbbell ɗin ya yi yana kara zunɓura baki shi a dole Black Tiger
bai kula shi ba ya ɓata rai.

Ya kai a kallah 10 mins yana ɗaga dumbbell kafin ya ajiyesu ya nufi gaban
yayan nasa wanda tin da ya zo wajen bai kalli in da yake ba, aikinsa kawai yake yi
yana ta haɗa uban zufa saboda wahala, wajen kuma gabaɗaya kewaye suke da A.c dake
busa sanyi, amma bai hana shi zufa ba.

Wlh ba dik kai ba iya ɗaga barbell mai weight plates guda biyar ma, sai a tara
maza dubu ba a samu biyu masu iya ɗaga mai biyar ba, shi kuma Black Tiger mai goma
kuma manya manya yake ɗagawa, har yau Ronnie a iya mai huɗu kawai yake iya ɗagawa,
shi ma sai da Black Tiger ya tsaya tsayin daka sannan ya iya jajircewa.

Isar Ronnie gabansa ke da wuya ya sauke barbell ya mayar da shi mazauninsa,
sannan ya duka ya yi shirin fara press up.

Hayewa saman tsakiyar bayansa Ronnie ya yi yana cigaba da zunɓura baki. Bai kula
shi ba ya fara press up da shi babu kama hannun yaro, da yake gwarzon namiji ne ya
saba, sai da ya yi press up 200 babu hutawa, shi ma Ronnie yana tsaye a kan
kafafunsa a tsakiyar bayan nasa kamar wadda aka sassaƙa, ko gezau bai yi ba.

Abin dai gaskiya da mamaki, sun kware kam wajen yin wanna zallar madarar
jaruntar.

Dikkansu sai da suka yi sharkaf da zufa, gabaɗaya fuskar Ronnie kamar wanda aka
watsawa ruwa, shi kuma big man da yake face ɗinsa a rufe sai ya zamana ba'a gane
halin da yake ciki.

Wucewa ya yi ya nufi room ɗinsa bayan sun kammala. Da sauri Ronnie ya bi bayansa
yana saka mashi kukan shagwaɓa a kan lallai ya buɗe fuskarsa ya gani, dan shi
gaskiya Black Tiger ya yi mashi kyau, kuma ba zai iya tafiya ba tare da ya gansa
ba, in baku manta ba kaunar kyau a jinin Ronnie yake, dik wani abu mai kyau to yana
kaunarsa sosai.

Tamkar Black Tiger kunnuwarsa sun doɗe, sai ya nuna kamar bai san da wani Ronnie
ba, ya shige cikin room nasa. Har ciki Ronnie ya bisa.

Toilet Black Tiger ya nufa cikin wani irin tafiya mai matuƙar ban mamaki da
al'ajabi, kamar wanda baya taƙa ƙasa.

Saman wannan DAULAR bed ɗin nasa Ronnie ya haye ya kwanta, shi fa ya rantse ba zai
fita ba sai ya ga face ɗin yayan nasa, ga shi by 5:30 zai tafi church, yanzu kuma
5:06.

_____________ SWEETIE ___________🔥💘

Kamar a mafarki ya tsinkayo sanyayyar voice ɗinta tana faɗin.
"Where are you Ronnie? Why are you leaving me alone in the room? Do you want
the man who made me suffer that day to come back and take me away again?"
Idanunta sun yi jajir sun ɗan kumbura, jikinta dik a mace alamar barci bai
isheta ba, golden white hair nan nata a watse kamar wadda aka kwato daga bakin
kura, sanye take da kayan barcin Floris riga da wando masu dogon hannu launin sky
blue, ba karya ta yi kyau sosai, tin da ta yi sallar la'asar take zuba barci.

Tana magana tana nufo master room ɗin, dan tasan a nan kaɗai zata same shi, saboda
ta je parlourn kasa baya nan, Floris and Angela ta samu, Floris ta ce mata yana
wajen yayansa, ko tsoro bata ji ba shi ne ta biyosa, akwaita da karfin halin bala'i
yarinyar nan.

Haba ai a miliyan kamar wani walkiya haka ya diro kasa daga saman bed ɗin,
kafin ƙiftawa da Bismillah har ya kai bakin door room, jikinsa har yana ɗan kerma
wajen buɗe kofar ya fito da gudu kamar wanda aka koro.

Yana sanyo kai suka yi karo da ita, dan tsabar karfin hali irin nata tana ƙoƙarin
buɗe kofar ne ta shigo ciki.

Ai bai dakata ɓata lokacin duba in da ta buge ba, hannunsa na kerma ya ja nata suka
nufi hanyar barin wajen, ya mance da cewa kuka yake yi wa yayansa a kan ya buɗe
fuska, tuni ya wuce.

Kamar waɗan da aka rako ya banke kofar room ɗinsa ya shiga da sauri yana sauke
ajiyar zuciya.

Ita da sam babu tsoro a tattare da ita kuma bata ga abin da zai bata tsoro bane ta
ce.

"Are you okay?"

Bata jira amsarsa ba ta ɗaura da. "Why're you running like that? And why are you
panting like someone who is not honest? Then you sigh is like someone who has
escaped from a group of enemies".

Fuskarta cike tab da mamaki ta yi maganar, dan ita mamaki ya bata!.

Janyota jikinsa ya yi kawai yana sauke ajiyar zuciya, har ga Allah a tsorace yake,
baya burin ta sake haɗuwa da yayansa, dan shi yasan wanene Black Tiger, mutumin da
bai taɓa yafiya ba a tsawon rayuwarsa, bai ma santa ba, baya ɗaga kafa koda kuwa ga
tsinke ne, kana mashi ɗaya zai yi maka ɗari, dole ya ji tsoro!.

Jinta a jikinsa yasa ta farga babu riga a jikin nasa, cikin sauri ta ɗago ta kalli
face ɗinsa, while shi ma ita yake kallo. Watsewar da gashin kanta ya yi har
fuskarta yasa bata samu damar ganin face ɗinsa da kyau ba.

Hannu ya kai ya tattare mata gashin waje guda, dan su samu damar ganin juna da
kyau. Dikkansu sun ji daɗin hakan, barema shi da har wani cool ajiyar zuciya ya
sauke.
"Ronnie why are you looking at me like that?"
Ta yi maganar tana ƙoƙarin barin jikinsa, dan ta ɗan tsorata na ganin kirar
halittarsa.

Girgiza mata kai ya yi ba tare da ya yi magana ba, a hankali hankali yake sauke
numfashi, hannunsa dikka biyu ya ɗaura a saman bayanta ya hanata barin jikin nasa.

Da sauri ta ɗago kallonta a kansa. Kurawa juna idanu suka yi kamar waɗan da
suka afka duniyar tunani.

An rasa mai kawar da kallonsa daga kan ɗan uwa, da alama sun mace a kallon junansu
ne.

--------- KNOCKING DOOR-----------------

Knocking door da aka fara yi daga waje ne yasa suka farga tare da dawowa cikin
hanyacinsu, a nutse ya sauke ajiyar zuciya tare da saketa, ya ɗan raba jikinsa da
jikin door ɗin ya kuma saketa.

Idanunta na'a a kan kofar, ta wani zarosu irin like tana mamakin wanene?.

Fingerprint ɗinsa ya sanya a kofar ba password ba, sannan ya wuce ya nufi wajen bed
ɗinsa. Kamar ba shi ya wani rungumi Sweetie a yanzu ba.

Shigowa ciki Floris ta yi tana ɗan tsuke fuska alamar shagwaɓa. Sanye take da irin
wannan shiga tasu ta riga da kuma sket har ƙasa, kayan yana da bala'in kyau, ta
ɗaure gashin kanta a tsakiya, hannunta riƙe da Bibel, da alama shirin zuwa church
ta yi.


Kallo ɗaya Ronnie ya yi mata bai furta uppan ba ya nufi toilet dan ya yi wanka.
Da ido ta bishi tana mamakin ganinsa babu riga, sai kuma ta kara yin wani mamakin
ganin Sweetie a tsaye a bakin kofa.

Kasa haɗiye mamakin nata ta yi har sai da ta ce. "Sweetie me kike yi a nan?".

"Babu komai". Ta bata amsa kai tsaye tare da wucewa ta nufi wajen bed ɗinsa.

Bayanta Floris ta bi tana faɗin. "Ya ke baki yi shirin zuwa church ba?".

Tana ƙoƙarin zama a bakin bed ɗinsa ta answer da. "Na faɗa maki mu bama zuwa
church, masallaci muke zuwa, idan kuna da musque zan je can on Friday".

Tin da ta fara magana idanun Floris yake a kan ɗan bakinta har ta dire aya.

"Sweetie kin mun kama da wata mata da na taɓa gani cikin birnin nan! Sai dai
ba sosai kuke kama ba, idan an ganki a fisge ne dai sai a ga kamar ita ce". Cewar
Floris.

Ba tare da kawo wani dogon tunani ko wani nazari ba ta amsa da. "Kinsan halittun
Allah dayawa, dama dai yarinya kika ce ina kama da ita to da sai in ce Pretty ce
kila, amma ba yadda Ubangijinmu baya halitta".

Karisowa wajenta Floris ta yi, tana mamakin hali irin nata, yarinya sam bata taɓa
ɗaukar abubuwa da mahimmanci, akwaita da careless, bata sanya damuwa a ranta,
hasalima ba zaka taɓa gane ina alkiblarta a zamantakewa ya dosa ba, ji yadda ta
bada amsar cewa da aka yi anga mai kama da ita, tamkar bata da uwa ko wasu ƴan
uwan, a yanayin yadda suka taso su biyu

Please Login or Register in order to submit comment