Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 45 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake yi wa
kayan, ita jacket ɗin jikinsa ma take balai'n kauna, rigar ta yi mata kyau, ga shi
har gwiwonsa ya kai, kamar long coat haka jacket ɗin yake.

Kafafunsa dake sanye cikin wasu irin armor sandal ta bi da kallo, takalma bakake ne
hakan yasa hasken fatarsa ta kara fitowa sosai, kafafunsa kyawawan gaske, faratunan
yatsunsa kamar madara, zaka ce bai taɓa taka ƙasa ba.

Ganin ta sauko kasa yasa ya juya zai nufi hanyar zuwa wannan ɗakin dan su je ya yi
aikin, ba ruwansa da zata mutu, shi dai buƙatarsa kawai ta biya.

"One mint big bro". Ta faɗa tana ɗaura hannayenta dikka biyu a saman kugunta. A
tare suka dakata shi da Ronnie, dama Ronnie bai kai ga fita waje ba. So jin
maganarta yasa suka dakata

Dakarawa ya yi da tafiya amma bai juyo ba, ya nuna alamar dai yana
sauraronta....... Ko kaɗan babu tsoron abin da zai iya aikata mata kawai ta nufesa,
a hankali take takawa har ta isa garesa, ta zago ta gabansa suna fuskantar juna, da
kyau ta kara rike kugunta.

Slowly ya ɗaura idanunsa a kan face ɗinta, sai da ya ji gabansa ta ɗan faɗi,
ita kanta sai da ta ji wani irin shock kamar an jona mata wutar lantarki, amma haka
ta daure, cike da kwarin gwiwa zuciyarta na dukan uku uku ta ce.
"Why do you want to remove my brain?" She threw the question at him, her face
hardening as if to make it clear that she was not joking.

Ɗan zaro idanunsa a kanta ya yi, a wannan gaɓar sai da ta ɗan kawar da kallonta
daga cikin idanunsa, saboda da ya zaro idanu sun kara kaifafa sosai da ba zata iya
ganinsa ba.

Ko waye ya faɗa mata zai cire mata ƙwaƙwalwa kuma? Kai Sweetie duniya.

When he didn’t respond, she spoke again. "So, you mean to tell me that you can’t
retrieve anything from me unless you take my brain? Don’t you think that’s a sign
of your failure?"

He stood motionless like a statue, showing no intention of answering her.

She fell silent, her eyes trailing down to his feet, watching how he slightly
shifted them a subtle sign that her words were getting to him. Slowly, she lifted
her gaze back to his face, slightly tilting her hips before freeing one hand from
the grip she had on her waist. Then, with her heart pounding hard in her chest from
fear of him, she forced herself to lift her hand, positioning her fingers right in
front of his face. Her chest felt like it was about to burst from fear, but she
suppressed it.

Shiru ta ɗan yi tana kallan yatsun kafafunsa yadda yake ɗan motsasu kaɗan kaɗan
alamar maganganunta suna taɓa mashi zuciya. Slowly ta ɗago kallanta a face ɗinsa,
ɗan jijjiga ƙugunta kaɗan ta yi kafin ta zame hannunta ɗaya daga rikon da ta yi wa
kugun nata, sannan ta ɗaga hannun nata dai'dai saitin face ɗinsa, kirjinta tamkar
zai fashe saboda tsoronsa, amma haka ta danne.

Kiyasta mashi yatsunta a saitin face ɗinsa ta yi. Her voice was sharp as she spoke,
"I challenge you. Find Spender using only the brilliance of your own mind, without
my help, without hurting me to get to him. Find it on your own. If you can, then I
will acknowledge that you are truly a man. And I want you to understand something,
when it comes to the story of your fate, I am the first page and the last. I am
your destiny, and there’s nothing you can do about it!!. If you truly are a man,
find Spender yourself." Babbar magana, lallai Sweetie jinjina gareki gaskiya, eyye
yarinya ta ƙalubalance Black Tiger, tashin hankali, ya kuke tinanin wannan wasa zai
kaya? Mu je zuwa.

She ended her words with her fingers still pointed at him, her gaze unwavering.

Tin da ta fara magana bai motsa ba yana sauraronta har sai da ta kai aya, sannan ne
ya ɗan nisa kaɗan, cikin zafa ya kai hannunsa zai capki wuyarta, dan ya lura bata
azabtu bane shiyasa har yanzu take da kwarin gwiwar yi mashi magana, bai san karin
gwiwar ya samo asali ne daga dogara da Allah da ta yi ba, ba wai dan bata azabtu
bane, ta dai rike Allah ne kawai.

Wani irin zulle mashi ta yi, ƙasa ta sunkuya sai ta tafi da karfi ta faɗa saman
lion chest ɗinsa, dama ta yi wa kanta alkawarin ba zata taɓa bari ya sake taɓa mata
lafiyar jikinta ba, sai dai ayi wacce za'ayi.

Ai tana faɗawa jikinsa sai da ya ji komai nasa ya tsaya cak na wucin gadin. Lokacin
guda ya ji har ɗan juyi ɗakin ya yi mashi, ita kanta sai da ta rasa nitsuwarta,
wani irin azabbabben shock da ta ji wanda bata taɓa jin irinsa ba, sai da ta ji
gabaɗaya gaɓɓan jikinta sun mutu.

Ronnie dai mutuwa tsaye ya yi tamkar wanda aka dasa, dan kalaman Sweetie sun fi
karfinsa, ƴar yarinya da ita wai ta ƙalubalance Black Tiger, wannan bala'i dame ta
yi kama?.

Cikin zafa yasa hannu zai ɓanɓareta daga jikinsa ya yi wurgi da ita, ina ai bata
bashi wannan dama ba, hannu tasa ta riko waist ɗinsa da karfi, dan dolensa ya lafa
da yunkurinsa, barema yadda take kara shigewa jikinsa da karfi.

Shiru ya ɗan dakata yana tinanin irin hukuncin da zai yi wa wannan yarinyar. Jin ya
yi shiru yasa ta sakesa tare da ɗago kanta daga saman lion chest ɗin nasa.

Da yake ya fita tsawo sosai sai ta ɗan ɗaga kafafunta sama, a hankali ta kai
hannunta ta shafa gefen lallausan kumatunsa, ƙasa sosai ta yi da murya wajen furta.
"I am your destiny, hakuri zaka yi da ni fa big bro, I challenged you, kada ka
ɗauki zafi sosai mana, ko ka manta a sharaɗinmu babu batun cutarwa ne? Ba zaka
cutar da ni ba kuma zaka yi nasarar samo Spender, ka yi hakan zan sara maka kuma na
yarda kai namiji ne". Ta kai karshen maganar tare da ƙara ɗaga kafanta sosai,
sumbata ta manna mashi a lallausan kumatun nasa sannan ta juya cikin wani irin
tafiya mai nuna cike take da confidence ta nufi hanyar fita waje kirjinta tamkar
zai fashe saboda tsoro.

Ya subhanallah, yadda kuka san an dasa Black Tiger a wajen, ta gogewa Ronnie haddar
dake kansa gabaɗaya, nasan ba Ronnie kawai ba, har da ku masu karatu ta goge maku
hadda ko? Wannan yarinya Sweetie nan gaba ban san ya zamu yi da ita ba, da alama
idan Black Tiger bai yi da gaske ba fa zai rasa bakin magana a gabanta.

Tana zuwa kusa da Ronnie ta kyasta mashi yatsu a saitin face ɗinsa kafin ta
wucesa, tana taku kamar wata hawainiya, tafiya mai matuƙar ɗaukar hankali, dik wasu
albarkatu na jikinta suna motsawa a dik san da ta taka kafafunta ta yi taku ɗaya.

Har ta isa kofar room ɗin Ronnie da Black Tiger babu wanda ya iya motsawa daga in
da yake tsaye, ita kuma bata juyo ba ta sanya password na kofar kamar yadda Ronnie
ya koya mata.

Take kofar ta buɗe ta nufi waje abinta. Tana fita ta zube gwiwowinta a kasa a wajen
tare da dafe saitin zuciyarta tana sauke numfashi da sauri sauri. Ƙasa ƙasa ta
furta. "Allah na gode maka da ka bani ikon da kwarin gwiwa na iya aikata hakan a
garesa, Allah Alhdulillah da baka bari bugawar da zuciyata take yi a lokacin da
nike gabansa ya kasheni ba, Allah ka cigaba da dafa mun kana kareni, Allah kaga
zuciyata jahadi nike san yi, Allah ka cigaba da ɗaurani a kansu, astagfilullah,
astagfilullah, astagfilullah, Allah na tuba, Allah ka jiƙaina ka cigaba da karamun
kwarin gwiwa kana bani ikon daurewa na yi magana yadda yakamata a gabansa".

Tana kai karshen maganar ta fashe da kuka saboda yadda kirjinta yake duka tara tara
ya wuce tinaninku, a tsananin tsorace sosai take fa, kawai shegen karfin ne. Ta ɗan
jima a wajen tana hawaye kafin ta miƙe da gudu ta nufi ɗakin Ronnie, tana zuwa ta
faɗa saman bed tana ƙara rushewa da kuka mai tsuma zuciya.

Kamar kuma wadda aka dakatar ta yi saurin miƙewa tana gogewa hawayenta, dan ta tuna
Black Tiger zai iya ganin tana kuka, ita kuma bata san bashi wata kofar da zai
fahimci tana jin tsoronsa. Babbar magana, yanzu za'a fara buga wasa a Black world,
my people's Black Tiger fa ya ji sumbata ya yi sumar tsaye ɗan ƙaniya, ina da ya ce
baya ji, yanzu Sweetie zata yi mana maganinsa ai. Ku dai muje zuwa.

🔥🔥🔥 KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER.🔥🔥🔥
Gabaɗaya barci ya kauracewa idanunsa, banda kyakkyawan surar jikinta da ya gani
lokacin da ta fito wanka ranar da zasu je wajen Khadijah babu wani abin da yake
tunawa, haƙiƙa idan ya ce zuciyarsa ta kamu da san Zee to bai yi karya ba, sai dai
kuma yana jin zuciyarsa bata kyauta mashi ba, dan shi yana da ra'ayin auren mace
mai 25 years ne ba yarinya kamar Zee ba, dik tinaninsa ya kulle a kanta, sai dai
kuma ta wani ɓangare ya fi yarda da cewa ya kwaɗaitu ne da surar jikinta kawai, dan
shi ne abin da ya tsaya mashi a ransa.

Sai safa da marwa yake yi a cikin tsakiyar parlournsa, kwanciya wannan ya gagara
yi, kirjinta daya kurawa idanu wancan ranar kawai ƙwaƙwalwarsa take hasko mashi a
idanunsa, gabaɗaya ya gaza iya rike kansa.

Time ya duba a wayarsa dake hannunsa. 11:00pm dai'dai, gabaɗaya sai ya ji zuciyarsa
tana fusgarsa a kan ya je ya ganta a daren nan, ya yi ƙoƙari wajen ganin ya tursasa
zuciyarsa ya hakura da zuwa ganinta, amma ina abin ya fi karfinsa, dan haka dole a
cikin wannan dare ya fito sanye da sleeping dress a jikinsa.

Kai tsaye part ɗin mama ya nufa, yana tafiya tamkar wanda yake tsoron taka ƙasa,
can ƙasan maƙoshinsa ya yi sallama kafin ya tura kofar ɗakin a hankali ya shigo,
light na ɗakin a kunne yake, suna kwance saman bed suna zuba barcinsu, Aneesa na
gefe ita ma Zee tana gefe, gadan nasu yana da matuƙar girma sosai.

Ji ya yi tamkar ya juya gudun kada Aneesa ta farka ta gansa a kansu, amma kuma
zuciyarsa ba zata iya hakura ba muddin bata ga fuskar Zee ba.

Daurewa ya yi ya ƙarisa ciki yana ji tamkar ba shi ba, wai yau shi ne ya folawa
mace under 18 years, gaskiya zuciyarsa dai bata yi mashi adalci ba, shi ne abin da
yake ta faɗa yana maimaitawa.

Ta side ɗinta ya zo, duƙawa ya yi a saman gwiwowinsa a gaban bed ɗin. Tana
kudundune a cikin bargo, tun daga kan yadda Zee take barci mutum zai iya fahimtar
ita ɗin macece mai kama kanta, wacce ta san mutumcin kanta, nitsastsiya mai sanin
yakamata, dan ko a cikin barcinta ta haɗe jikinta waje guda ta yadda bata ba da
kofar da komai ƙanƙantar tsiraicinta zai iya bayya idan barci ya yi nisa ba, ta
haɗe kafafunta waje guda ta kuma dungule hannayenta ta turasu a tsakanin cinyoyinta
ta kusa da gwiwa, idan ka ganta zaka yi zaton ta takure kanta dayawa, amma ba haka
bane, saboda ne da irin kwanciyar ya ja hakan, ga kuma irin tarbiyar da ta samu tun
kan kanwar shaiɗan Hauwa ta shiga rayuwarsu ta ruguje komai.

Zubawa face ɗinta idanu ya yi sosai yana kare mata kallo, hankalinsa dikka a kan
lips ɗinta, Allah ya gani zuciyansa ya biya da wannan black beautyn, Zee dai a
Nigeria fara ce tas, amma a gabansu baƙa ce gaskiya, shiyasa ya kirata da sunan
black beauty.

Hannunsa na kerya ya kai ya ɗan janye bargon da ta lulluɓa ƙasa. Kayan barcin
Aneesa riga da wando ne a jikinta, kasancewar bata sanya bra ba sai tula tulanta
suna tsole idanun mai kallo. Shi dai da alama kirjinta yana ɗaya daga cikin abin da
ya ja ra'ayinsa a kanta. Dawo hannunsa kusa da face ɗinta ya yi dan ya taɓa
lallausan kumatunta, sai dai bai kai ga yin hakan ba ta fara motsi tana san
farkawa, saboda ta ji alamar kamar ambuɗe mata jiki. Ya janye mata bargo.

Aneesa kuwa ta baje abinta sai zuba barci take yi, ta rungumi teddy a kirjinta a
cewarta Yah Rizwan ta runguma,........... Kai Hasbunallahu wani'imal wakil, wlh
jikokin Akka sai shirin Allah, ba matan ba ba mazan ba, da alama dik sun yi gadon
jaraba, kai kun ji Aneesa da wani tsiya, wai Yah Rizwan ta runguma, kai jama'a ana
abu a kingdom of power.

A hanzarce ya miƙe tsaye, ganin sosai ta fara motsawa zata farka yasa ya yi
saurin juyawa zai fice daga ɗakin. Sai dai bai kai ga fita ba ta waro idanunta waje
kai tsaye sai a kan bayansa yana tafiya. A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar bed ɗin
tana kallansa. Bata gane wanene bane, saboda ya bata baya, sai dai zuciyarta ya
zargan mata cewa shi ne, saboda shi ne kaɗai a gidan wanda gashin kansa bai yi dark
black ba, ya ɗan yi brown brown haka.

A hanzarce ta dawo da kallonta a kan jikinta dan ta tabbatar da ba wani abin aka yi
mata ba!. Ganin babu komai yasa ta yi saurin saukowa kasan bed ɗin, ashe gara da ta
ce da Aneesa su rinƙa barin wutar ɗakin a kunne dan suga mai shigowa, to ga shi ya
yi amfani.

Bayansa ta bi da sauri dan ta ga wanenen? Tana da karfin hali ita ma, a ranta take
rayawa lallai lokacin barinsu gidan nan ya yi tun da dai maza ne suke shigo masu
ɗaki da daddare.

Da sauri ta fito daga bedroom ɗin nasu ta nufi bin bayansa. Sai dai ko da ta fito
bata gansa ba, babu shi babu alamarsa, ɗan waige waige ta tsaya yi a wajen, kamar
dai a mafarki ta hango inuwar mutum ta wajen wannan kofa da Guyson ya bi ranar ya
je wajen dinner Jawad, kun tuna ranar da ya haɗu da aljanar nan? Kun san ai dama ta
part ɗin mama ne kofar yake ko idan baku manta ba? To ita kuma Zee kunga a part ɗin
take tare da Aneesa, so tana fitowa sai taga inuwar mutum kamar dai yadda aka yi wa
guyson.

Ɗan tsorata ta yi, sai kuma ta tina abin da mamarsu take yawan faɗa masu a kan
kada su ji tsoron kowa face Allah da ya haliccesu. Tuna hakan yasa ta ce bari ta je
ta leƙa kila inuwar wanda ya shigo masu ɗaki ne, yau so take taga wanenen?. Ba tare
da tina abin da zata iya gani ba ta nufi kofar, tana taɓa kofar kuma sai ta jita a
buɗe.

Wai nace ba, meyasa wannan kofar a dik lokacin da wannan inuwa ta gifta kofar yake
buɗe kansa da kansa ne? Kun san fa ba'a buɗe wannan kofa kwata kwata, ko da rana a
rufe yake, so meyasa in dai inuwa ta gifta kofar zai buɗe? Muje dai zuwa.

Jan kofar a hankali Zee ta yi da nufin ta fita waje, daga bayanta ta ji muryarsa
ya ce. "Ina zaki je a daren nan, sannan kofar nan ai ba'a buɗeta". A hanzarce ta
juyo da kallonta a kansa, uncle Jahiz ɗin ne dai, yana tsaye yana kallanta.

Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin juyo da jikinta a garesa dan ta bashi amsa ta
wuce ciki, unexpext idanunta suka kallo mata fuskar mace mai kama da aljana ga wasu
kahohhuna dogaye a hancinta har zuwa bakinta, jini na bin jikin kahon, sannan
idanunta manya manyan jajir kamar wuta, gwanin ban tsoro.

Ai Zee bata san time ɗin da ta zunduma wani irin ihu mai doɗe kunne ba, kwata kwata
bama ta san ya akayi ba sai ganin kanta ta yi a kirjin uncle Jahiz, shi kuma fa
babu abin da ya gani, ita kaɗai aka tsorata, kada ku manta uncle Jahiz fa na Aliyah
ce, Aliyah kanwar Mammie shugaban mashirikai ita mammie ta ce zata auresa in baku
manta ba, to ni dai ina ga kila saboda uncle Jahiz ya nuna ra'ayinsa a kan Zee yasa
Mammie ta fara ɗaukar mataki, amma ku ya kuke gani?.

Kankame shi ta yi tana ihu. Gudun kada ta tashi family yasa uncle Jahiz ya yi
saurin toshe mata baki da hannunsa yana kai kallansa a wajen da ta baro take ihun.
Shi dai bai ga komai ba face kofa kawai, to meyasakata ihu har haka? Ya jefawa
kansa tambaya.

Motsi ya ji a bayansu ta wajen part ɗin momma, hakan yasa ya yi saurin janta
baya dan ma kada wani ya gansu, ganin kamar razana sosai ta yi yasa ya fara tofa
mata addu'oi har lokacin bai zame hannunsa daga bakinta ba. Ita kuma tana ƙanƙame
da shi.
Addu'oin da yake tofa mata ne yasa ta fara samun nitsuwa hankalinta yana dawowa
jikinta, tsoratar da ta yi yasa har ta fita a hayyacinta.

Ganin ta ɗan fara nitsuwa yasa ya jata suka karisa shiga bedroom ɗin
Aneesa, a saman sofa ya zaunar da ita tare da zame hannunsa daga bakinta, ya kurawa
face ɗinta idanu yana kallanta. Ta ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ta iya dawowa
dai'dai, hankali a tashe take kallansa, sai kuma ta kasa yin magana.

Cikin nitsuwa ya tambayeta dalilin ihun da ta yi, ta kasa bashi amsa, tamkar an
ɗaure mata tongue ɗinta, ganin hakan yasa ya ce ta je ta kwanta da safe zasu yi
magana kuma kada ta sake fitowa. Ba musu ta miƙe ta isa bakin bed ɗinsu, hayewa ta
yi ta kwanta har wa lokacin tongue ɗinta a ɗaure ta kasa iya yin magana.

Miƙewa ya yi ya koma kusa da ita, addu'oi sosai ya tofa mata, tin tana satar kallan
face ɗinsa har ta lumshe idanu tana sauke ajiyar zuciya alamar hankalinta ya
kwanta. Jin saukar ajiyar zuciyarta yasa ya fahimci ta samu natsuwa, bargo ya ja ya
lulluɓeta tare da karisawa gaban switch ya kashe masu wutar, sannan ya fita ya
janyo kofar ya rufe masu.

Dik wannan bidiri da ake yi Aneesa tana can duniyar mafarkin ita da Yah Rizwan,
bata farka ba, amma abin mamaki kuma zata iya wayan gari ta bada labarin abin da ya
faru daren jiya ɗin, anya Aneesa mutum ce kuwa? Ta fara bani tsoro sosai gaskiya,
amma mu je zuwa, ita ma labari zai biyo ta kanta ne, lokacin na nan tafe.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A tare Jawad and Jaish suka jera har izuwa takiyar main parlour, a nan ne suka
rungumi juna tare da yi wa juna good night, a daidai lokacin Chuchu da Mahnoor suka
iso wajen.

Wucewa gaba Jaish ya yi ya nufi part ɗinsa ba tare da ya kalli in da Mahnoor take
ba, shi kuma Jawad ya rike hannun Chuchu yana janyota jikinsa suka wuce nasu part
ɗin suna yi wa Mahnoor good night.

Shiru ta ɗan tsaya a wajen tana tinanin yadda zata kwana da shi ɗaki ɗaya yau.
Ganin tsayuwa ba zai haifar mata da mafita bane yasa a nitse ta taka ta bi bayansa.

Tana sako kafafunta a cikin parlonsa ta ji kamshi na daban ba kamar wanda ta ji da
rana ba, kenan ancanza mashi perfume, shakar kamshin ta yi ta lumshe idanunta,
cikin natsuwa ta ƙarisa shiga cikin parlourn.

Mama Haulat ta isko zaune saman sofa tana dudduba wasu sexy sleeping dress dake
cikin kwalayensu. Cikin girmamawa ta ce. "Barka da dare mama Haulat".

Fuska ɗauke da fara'a mama Haulat ta amsa da. "Yauwa barka dai amarya kuma
sarauniyarmu, zo nan ki ɗauki kayanki ki wuce ɗakin mijinki". Ɗan siririn murmushi
ta saki kafin ta karisa kusa da mama Haulat, sannan ta ce. "Mama kaya kuma?".

Jinjina kai ta yi tare da amsa mata. "E kaya, momma ce ta ce abaki wannan kayan su
zaki saka, kuma ta ce karfe tara kije ki ɗaukawa mijin naki cappuccino". Kasa da
kai Mahnoor ta yi alamar ta ji kunya ance mijinta. Miƙo mata kayan mama Haulat ta
yi ta karɓa tana wani sunkuyar da kanta ƙasa.

"Kada ki nuna jin kunya a wannan ɓangaren, domin kunya bata da wani amfani, ki
tsaya tsayin daka ki faranta ran mijinki shi ne dai'dai, ki sani yanzu kin shiga
layin da Mala'iku zasu yi rubutu a kanki a kan aure, so yana da kyau ki kula sosai,
ki sanya shi farinciki domin ki samu rahamar Allah, na ɗaukeki ne tamkar yata, dan
haka a matsayina na uwa shawarata a gareki shi ne ki ajiye wannan kunya a gefe"
Ƙasa ta yi da kanta wajen amsa cewa ta gode sosai kuma In Sha Allah zata yi amfani
da shawarinsu ita da momma, fatan alkhairi da fatan nasara mama Haulat ta yi mata
sannan ta ɗaura da cewa sai da safe.

Bedroom ɗin ta nufa cikin natsuwa. Baki ɗauke da sallama ta shiga ciki, babu kowa a
ɗakin sai tashin daddaɗar kamshi da yake. Shiru ta tsaya tana bin ko'ina da kallo,
tinani ta shiga yi a kan ina yake ne? Ko dai bai shigo ɗakin ba ne?. Ta kai almost
5 mins a ɗaya a wajen kafin ta iya fahimtar yana toilet yana wanka ne.

A hankali ta taka ta ƙarisa cikin ɗakin, zata zauna a ƙasa sai ta tuna kaman momma
da mama Haulat, momma ta ce ta mayar da gadansa wajen zamanta kamar yadda zata
mayar da jikinsa gadanta. Tina hakan yasa ta ƙarisa bakin bed ɗin nasa a hankali ta
zauna tana sauke ajiyar zuciya.

Shiru ta yi tana bin ɗakin da kallo tana ɗan shafa kwalin kayan dake ƙasar
hannunta, bata ga lokacin da ya fito daga wanka ya shiga dressing room ba, amma shi
ya ganta a cikin dakin, sai ya kawar da kansa kamar bai ganta ba.

After some minutes ya fito sanye da kayan barcisa masu kyau da tsada, kao tsaye
bed ɗinsa ya nufo, sai da ya matso kusa da ita ne ta iya gane ya fito, a cikin
hanzarce ta ɗago da kallanta a kansa. Unexpectly suka yio four eyes, domin kuwa shi
ma ita yake kallah yana jin kamar ya je ya ɗauki lallen hannunta hoto.

Kwayar idanunsa ne suka rikitar da ita, a ruɗe ta miƙe daga saman bed ɗin, tsabar
ta tsorata har ta ce mashi ina kwana ba tare da ta sam t faɗa ba. Kawar da kallansa
daga kanta ya yi ya haye saman bed ɗinsa ba tare da ya amsa mata ba. Lokacin guda
ta ji jikinta ya mutu na banza da ita da ya yi, sai ya tsaya kamar wata doluwa.

Gabaɗaya ta ji ta karaya da wannan al'amari, sai dai lokaci guda zancen momma ya
dawo ranta a in da take ce mata kada ta karaya, ta jajirce kome zai yi mata, tina
hanan yasa ta ji kwarin gwiwa ya dawo mata, a hankali ta fara takawa ta nufi toilet
ɗinsa dan ta yi wanka.

Ta wutsiyar idanunsa ya bita da kallo, yarasa me yake damunsa, in dai ya ganta sai
ya ji yana sha'awar ya cigaba da kallonta, ni kam nace saboda ita ɗin mallakinka ce
ba tun yau ba, shiyasa kake kasa control na kanka a dik time da ka ganta. Sam bai
yi ƙoƙarin hanata shiga toilet ɗinsa ba, saboda marainiya ce, kuma momma ta ce kada
ya cutar da ita, dan tana kaunarta, ko dan momma ba zai tsawata mata ba..........
Ni kuwa nace anya Jaish yana da gaskiya kuwa? Wai ko dan momma, munafiki ko dai dan
ya ga madarar kyau ba, bani dan momma kawai dai tin ganin da ya yi mata ɗazun ne
zuciyarsa ta buga da sunanta, shi ne zai fake da momma, wlh maza aji tsoron Allah,
amma dai ba koma zaka zo hannun ne, a lokacin ba wanda zai matse bakinka, da kanka
zaka faɗi dan me kake tausaya mata, dan gulma da iskanci irin na jikokin Akka har
da wani saboda ita marainiya ce, oh ni Princess Teema, mun dai san kun yi gadan
abin, dan haka ba wata marainiya, ka dai ga kaya hankali ya tashi.......😅

(Ba ruwana bani na faɗa ba🥱 jarababbu kawai 🏃)

Wayarsa ya laluɓo ya hau latsawa dan ya rage lokacin kafin time na shan cappuccinon
ɗinsa ya yi. Ita kuwa wanka a tsara, sannan ta ɗauki towel ɗinsa ta goge jikinta,
kayan da ta ajiye a wajen wash hand base ta ɗauko, fito da su daga cikin kwalin ta
yi. Cikin natsuwa ta ware kayan. Nan fa ta zaro idanu tana kallansu, wasu irin
shegun sexy sleeping dress ne wanda gabaɗaya net ne jikinsu, riga mai siririyar
hannu ce zuwa gwiwa da ƴar pant ɗinta wanda ita ma net ce.

Shiru ta yi tana tinanin yadda zata yi da wannan kaya. Wani

Please Login or Register in order to submit comment