Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 16 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Momma tana yi mashi fiye da haka idan ya yi tafiya ya dawo, to amma bata ruwan
hawaye a kan tafiyarsa da dawowansa, yau sai ga shi tana hawaye, sai ƙwaƙwalwarsa
ta fara bashi lallai akwai wani dalili mai karfi da yasa iyayen nasa suka yi
mamakin dawowarsa, ƙwaƙwalwarsa ce ta tariyo mashi yadda King ya tarbesa, abin sai
ya yi mashi some how haka.

Raba jikinta da nasa momma ta yi ta fara binsa da kallo, tana duba shi daga sama
har ƙasa, kamar tana tabbatarwa idanunta shi ne ko ba shi ba.
"Kai ne Jaish, da gaske kai ne ka dawo gare ni, Allah mai iko, Allah mai
kyauta mai kari!". Ta furta cikin muryar da ta ƙunshi da dukan ƙauna ta duniya.

"Momma nine mana, akwai wani abin ne?".

Zata yi magana idanunta suka sauka a kan uncle Jahiz dake bayansu, kai ya girgiza
mata a kan kada ta faɗa mashi komai.

Dan haka sai ta rabu da shi a in da ta ce mashi babu komai. Ya yarda da babu komai
ɗin, sai ya ce mata.
"Momma zan je in yi wanka, and then am feeling hungry".

Cike da kauna ta ce yanzu za'a kawo mashi abinci a bedroom ɗinsa, ya je ya yi
wankan. Har ta ɗan samu sassauci a ranta.

Yana san tambayar ina Auta, sai dai tamkar an ɗaura tongue ɗinsa, ya ji ta yi mashi
nauyi ya kasa tambaya, haka ya wuce bedroom ɗinsa ba tare da ya tambaya ba, sai dai
cikin ransa tunanin Autar ce kawai.

Momma kuma ta koma saman bed ta kwanta.

••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangaren mutanen fada kuwa, neman Hoorain aka shiga yi babu kakkautawa, a nan
warriors dake bakin gate suka isar da sakon ai ya fita baya a cikin kingdom ɗin.

King ne ya umarci warriors guda huɗu da su bi bayansa cikin gaggauwa su sanar da
shi King yana buƙatar ganinsa.

Sosai commander Zafar ya shiga tsananin tashin hankali na abin da yake faruwa, har
wani irin kaiwa da komowa yake yi a cikin Kingdom ɗin, ya gaza zaune ya gaza tsaye,
ya rasa sukuninsa, damuwarsa ɗaya a nan ita ce meyasa Hoorain zai fita daga kingdom
of power? Ina kuma ya tafi?.

MY PEOPLE'S AKWAI GAGARUMIN MATSALA! ME KUKE TUNANIN YASA HOORAIN YA GUDU? KENAN YA
ZAƁI DA YA BAR MAHAIFINSA CIKIN WAHALA A KAN SHI YA KARƁI HUKUNCI?.

==========================🔥

•••••••••••••JIMETA YOLA•••••••••••🔥

A yau ne bappa ya miƙa sadakin Mairo dan cikar burinsa. Katuwar bujumar saniya ya
bayar a matsayin sadakin.

Tun safe Nanne take faman zazzaga masifa tana aikin aika mashi da tsinuwa da
bakaken maganganun. Amma yadda kuka san an shuka dusa a gona, ko kaɗan bai nuna
alamar kamar yasan da wata halitta ita wai Nenne a duniya ba, sai hidimar gabansa
yake yi, nan da kwana uku za'a ɗaura aure dan Mairo ba budurwa bace, ta taɓa yin
aure sai dai bata taɓa haihuwa ba, mijin nata ne ya rasu aurensu da wata biyu.

So ba wani bikin da za'a gudanar mai tarin yawa dan dikkansu ba yara bane kuma ba
saurayi da budurwa bane.

Wunin yau a gona bappa ya wuni shi da Mahreen da Mahnoor, sun bar Nenne da
shakan kayan takaici.

Tun da suka je gona da safe har yamma suka dawo, tun kuma da suka je Mahnoor bata
furta ko uppan ba, tana dai zaune shiru.

Da kaga idnaunta zaka san tana bala'in jin barci, dan har sun ɗan kumbura sun yi
jajir, jiya yadda taga rana haka taga dare, ta kasa yin barci, Jaish ne kawai a
cikin ranta, tana manne da kayansa a kirjinta har wayenwan gari.

Da kyar ta iya gabatar da sallar asuba, tun da ta yi sallah kuma ta fito ta kama
yin aikace-aikacenta tamkar yadda ta saba yi, bata ma jira sai Nenne ta zo ta yi
mata tashin cin mutumci ba, sai ta koma ruwa kawai gwanin ban tausayi.

Yanzu haka tana zaune a cikin gonar nan gyangyaɗin barci take yi, sai barcin ya yi
kamar zai ɗauketa sai kuma ta zabura ta farka kamar wadda aka razana.

Dik abin da take ciki bappa yana sane, ya dai yi shiru ne kamar bai ganta ba, bawan
Allah bashi da abin faɗe.
Yanzu so yake yi ya samu Arɗo su yi magana a kan wannan aure nata, tabbas Arɗo zai
iya warware wannan aure, dan matsayin alkalin kauyen yake, da ace mijin Mahnoor ɗin
sun san shi, sun san tushensa, sun san asalinsa ne ya tafi bai dawo ba, to wannan
addini ya bada damar a jira na tsawon shekaru biyar, wata mas'haban ta ce shekaru
uku in bai waiwayeta ba sai a raba auren, amma basu san shi ba, basu san daga ina
ya fito ba, mutum ne ko aljani dik basu sani ba, kaddara tasa aka aura mashi ita,
daga baya ya ɓace daga ganinsu to wannan a musulunci wakkwaran bincike za'ayi domin
a tabbatar da mutum ne shi ko aljani, idan kuma babu ta yadda za'ayi a bincika
kamar dai shi Jaish ɗin to wannan alkali yana iya raba auren!.

To yau da daddare ya shirya zai je ya samu Arɗo su tattauna.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Zaune take karkashin bishiyar mango, ta buga uban tagumi, a zahiri zaku ga kamar
tana kallon bappa da Mahreen dake aikin cire kananan ciyayin da suke fitowa bappa
wajen masararsa.

Amma a baɗini tunanin kyakkyawan mijinta take yi, ganinsa kawai take yi a idanunta
yana yi mata gizo.

Kamar daga sama ta ji an ce............


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Kamar daga sama ta ji an ce. "Mahnoor".
Kin ɗago kai ta yi, dan tasan tabbas Hamma Faisal ne, voice ɗinsa ba zai taɓa ɓace
mata ba.


Bai damu ba dan bata amsa mashi ko ya ɗago ta kallesa ba, sai ya nemi waje kusa da
ita ya zauna yana ƙoƙarin sake yi mata magana haɗe da kai hannunsa kusa da face
ɗinta da nufin zai goge mata guntun hawayen dake face ɗin nata.

Ai a miliyan ta miƙe tsaye daga kusa da shi yadda kuka san wadda aka kawowa wuta
kusa da ita.
Mamaki ne sosai ya kama shi, bai taɓa tunanin zai zauna a kusa da ita ta guje
shi ba, ita kuma auren da yake kanta take karewa mutuncinsa, tana daraja kanta,
aurenta da kuma mijinta, so bata ga dalilin zama kusa da wani ba ko da ɗan uwan
nata ne, bare kuma shi da ya taɓa santa a baya, babu wannan magana.

Miƙewa tsaye ya yi shi ma dan ya yi magana da ita. Sai dai bai kai ga buɗe baki ba
da gudu tasa kai ta bar mashi wajen, dama lokacin komarsu gida ya kusa, sai kawai
ta nufi gida wani irin zafafan hawaye suka fara zubo mata, ɗacin zuciyarta ya yi
mata, yau da Jaish yana nan ai Hamma Faisal ba zai zo kusa da ita har haka har ya
nemi yi mata magana ya nemi taɓata ba, gaskiya ta yi babban rashi matuƙa.

Da gudu Faisal ya bi bayanta, dik abin da ya faru a kan idanun bappa ya faru, ita
kam Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi, dik abin da ake yi bata da labari, ta
shiga duniyar tunanin ina Jaish yake?.

Hmmmm Mahreen ma ta damu da Jaish haka bare Mahnoor da suka saba kwana ɗaki ɗaya,
ya yi ta gwada mata soyayya, ai dole ta yi kukan rashinsa wlh.

Bappa ya kawosu gonar nan ne domin su rage damuwa, amma ina sai suka zo suka
buga mashi uban tagumi suna kuncin abin da yake faruwa.

Tana shigowa cikin gida ta wuce ɗakinsu da gudu, a lokacin Nenne tana cikin
ɗakinta, so bata ga shigowarta ba.

Kusan a tare suka shigo da Faisal ɗin, da yake hankali bata gama isarsa ba, sai ya
bita har cikin ɗakin mijin nata, shi a dole zai rarrasheta.

Saman mattress ta faɗa tana cigaba da kukanta kamar wadda aka yi wa wahayin hakan.

A kan kayan Jaish da bappa ya bata ta kwanta tana jin kamshin jikinsa a jikin
kaya, gani take kamar shi ne a wajen.

Kamar daga sama ta ji mutum a kusa da ita yana magana ƙasa ƙasa. Ai a zabure ta
miƙe zaune, ido cikin ido ta kalli Faisal da yake dab gadan yana kallonta.

A miliyan ta miƙe tsaye, bata yi zaton ya biyota ba, tana san cewa ya fita mata a
cikin ɗaki, amma kuma ta kasa yin magana, dan haka sai ta wuce ta raɓa gefensa zata
fita waje.

Da sauri ya riƙo hannunta dan ta tsaya ya rarrasheta, Allah sarki, shi har yau har
gobe yana santa bawan Allah.

Wani irin fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi da karfi, a zuciye cikin
ɓacin rai haɗe da ɗaga murya ta furta.

"Ka sakeni Hamma Faisal!!".

Ya yi mamakin jin tsawarta a garesa, amma santa ya rufe mashi idanu da baya ganin
laifinta, a baya ko ɗaga murya a magana Mahnoor bata yi, idan ma baka da nitsuwa ba
zaka iya jin magana ba idan ta faɗa, tsabar yadda take magana a hankali ƙasa ƙasa
cikin nitsuwa, amma yanzu rashin Jaish yasa ta fara faɗa.

"Mahnoor na ji na sakeki, amma dan Allah ki daina yin kuka kin ji? Ki yi shiru
dan Allah sai ki faɗa mun meyasameki, meyasa kike kuka?".

Raɓawa gefensa kawai ta yi zata wuce, domin kuwa bata san ya tsaya mata a cikin
ɗaki.

Bata kai ga fita ba ta tsinkayo muryar Jumma yar Inna Rabi wato amarya tana yin
sallama a tsakar gida. Ai da gudu ta ƙarisa fitowa waje.

Suna haɗa ido da Jumma ta karisa da gudu ta faɗa jikinta tana kara karfin kukan da
take yi, rungumeta Jumma ta yi, dama abin da ya kawota kenan, Inna Rabi ce ta
turota da tazo ta jajantawa Mahnoor ɗin, sannan ta rarrasheta, Allah sarki Inna
Rabi tana kaunar Mahnoor sosai, dik yadda aka yi sun yi zaman amana da mamar
Mahnoor sosai.

Wani irin mummunar faɗuwar gaba Jumma ta ji ganin Faisal ya biyo bayan Mahnoor
ya fito daga cikin ɗakin shi ma, ga Mahnoor ɗin kuma tana kuka, abin ya yi mugu
mugun bata mamaki, to me ya kai shi cikin ɗakin matar aure kuma? Jumma ta jefawa
kanta tambayar.

Sai ta ji kirjinta ya buga, tasan mutanensu fa wasun su ba hankali ne da su
ba, kada ace wani abin ya je ya yi wa Mahnoor da yasa take kuka haka tamkar ranta
zai fita.

Koke kokensu ya ja Nenne ta fito daga cikin ɗakin, basu ga fitowarta ba sai dai
suka ji murya tamkar saukar aradu ta daka masu wani irin uban tsawa.

"Uban me kuke tsaya yi mun a tsakar gida kuna wani yi mun koke koke na munafurci
zaku hanani shaƙatawa".

Jumma uwar rashin kunya idanunta a tsaitsaye kar ta ce. "Kai dama idan za'ayi wa
mutum kishi shakatawa yake yi kenan?".

Zaro idanu Mahnoor ta yi, ai bata san lokacin da ta dakatar da yin kukan nata ba,
lallai Jumma bata san bala'i da ake yi a wannan gida a kan wannan kishi da za'ayi
ba ne! Da ba zata yi magana ba!.

Fusata Nenne ta yi, ranta ya sosu da jin kalamar Jumma, sai dai ba halin ta yi mata
komai, saboda su fa ba ƙaramin aikinsu bane yanzu idan ta daki Jumma mijinta ya zo
ya ci uban Nenne ɗin, su mazansu sun iya tarewa matansu faɗa, kai ko yaransu ka
daka ba zaman lafiya har sai sun rama.

So Jumma matar aurece a yanzu tana tsoron dukarta bata san ya halin mijinta yake
ba, kila mai tsauri ne a kan iyalansa.

Jumma da ta ga Nenne bata kulata ba sai ta ja hannu Mahnoor suka raɓa jefan Faisal
suka koma cikin ɗakin.

A saman mattress suka zauna, hannu Jumma tasa tana goge mata hawaye tana cewa ta yi
shiru yanzu ai ta zo zasu yi shawara a kan mafita, dan haka ta yi shiru suyi
magana.

Ƙoƙarin danne kukan nata ta yi, amma abin ya ci tura, ta kasa dannewa, dan
hawayenta cigaba da fasowa suke yi.
Tun Jumma tana goge mata hawayen har ta rabu da su kawai, dan sun ki tsayawa.

Cike da tausayawa ta ce. "Mahnoor yanzu kukan ne kike yi fisabilillah?".

Kifa kanta a saman gwiwonta ta yi, tana jin tamkar an ɗaura zuciyarta a saman wuta
mai cin bala'i ne, cikin kuka da ɗan ɗaga murya ta ce.
"Jumma bappa ya ce zai raba aurena da Hamma a aura mun hamma
Faisal..........."

Wani irin rushewa da kuka da ta yi ne ya ja ta haɗiye sauran maganganun ta kasa
amayar da su, saboda ba zata iya karisasu ba, wato yanzu ba kukan rashin Jaish ɗin
ba ma take yi, kukan raba aurenta da shi take yi, Allah sarki abin ya haɗu ya yi
mata yawa.

A lokacin kuma Faisal ya wuce ya bar gidan saboda Nenne, yana tsoron bala'inta,
sai ya kama kansa kawai ya haƙura, kuma Jumma tazo yasan zata rarrashin mashi
Mahnoor ɗinsa.

"Haba mana bappa, ina hakan ba zai yiwu ba, gaskiya kada ki yarda a raba
aurenki da hammanki, ina da tabbacin In Sha Allah zai waiwayeki, ai so ba karya
bane, tabbas dik in da yake yanzu haka yana tinaninki, ba zai taɓa jefar dake ba
komai zai faru"............ Cewar Jumma!.

Wannan magana ta Jumma ta yi dai'dai da lokacin da Jaish ya ke ƙoƙarin kwanciya a
saman katafaren bed ɗinsa, ya yi wanka yana sanye da three quter jeans white color
and white singlet masu kyau, ya yi matuƙar mamakin ganin yadda gashin kansa ya yi
yawa, sai dai bai kawo a ransa ya yi rayuwa a wani waje ne dayasa gashin ta taru
sosai saboda rashin datseta ba, ya wanke kansa kawai ya gyarata da mayukansa masu
kyau da tsada.

Sai dai fa wlh gashin da ta yi yawa ta yi masifar yi mashi kyau, shi kansa ya
shaida ta yi mashi kyau, hakan ce ma yasa bai wani damu da yawan gashin ba, sai ya
ji ma kamar zai iya barinsa ya cigaba da kashe mashi kuɗi kawai dan ya yi kyau
matuƙa.

Rage gudun Ac ya yi, ya kwanta kenan sai ya fara tunanin ina wayarsa zai kira
number Zunaira ya ce ta zo.

Kada ku manta wayar tasa tana hannnun Mahnoor. Miƙewa tsaye ya yi ya fara bincikar
ina wayar tasa take?. Ko'ina ya duba bai gani ba.

A bakin bed ɗinsa ya koma ya zauna, shiru ya yi yana tunanin in da ya jefar da
wayar tasa, ɗan lumshe idanunsa ya yi ya fara tariyo baya dan ya iya gano ina
wayarsa take?.

Dai'dai lokacin King and Momma suka shigo cikin ɗakin, uncle Jahiz yana biye da su
a baya, hakan ya dakatar da shi daga tinanin da yake ƙoƙarin yi na a in da ya jefar
da wayarsa.

Ita kuwa Jumma cigaba da karfafawa Mahnoor gwiwa ta yi a kan Jaish zai waiwayeta,
dan haka dik bala'in da za'ayi kada ta yarda a rabata da aurensa, dan shi kaɗai ne
garkuwanta kuma gatanta bayan Allah kenan.

Ta yi na'am da zancen Jumma, dan haka sai ta ɗaura ɗamarar gayawa bappa ba zata iya
rabuwa da Jaish ba, ta kuma ji daɗin zuwan Jumma, har ta ji ranta ya ɗan sanyaya.

Da kyar ta goge hawayenta ta kuma dakata da yin kukan, har da ajiyar zuciya. Jumma
ganin ta yi nasarar dakatar mata da kukan yasa ta fara ƙoƙarin kawo mata hira masu
daɗi da zai ɗebe mata kewa.
Cikin hiran nata ne ma ta sanar da ita tana da ciki har na tsawon wata biyu da sati
biyu, sosai Mahnoor ta tayata farinciki, ta ji daɗin maganar matuƙa.

Haka suka cigaba da yin hira tana bawa Mahnoor shawarwar haɗe da kara mata karfin
gwiwa a kan ta dage ta tsayawa aurenta, kada ta yarda a farraka mata shi.

Sosai Jumma ta so jin kwakkwaf a kan ko dai ita ma Mahnoor tana da cikin Jaish ne,
ko kuma sun taɓa kwanciya, amma ina Mahnoor taki yarda da faɗa mata komai, da zarar
ta kawo zancen Jaish Mahnoor zata doje taki yarda su yi ta.

Daga karshe Jumma ta fahimci Mahnoor fa ba zata faɗa mata ba, sai kawai ta hakura,
a tinaninta iya kunya ce kawai tasa Mahnoor bazata sanar da ita ba, bata san ba
haka bane, Mahnoor tasan wannan sirrin mijinta ne shiyasa taki yarda ta faɗa, sai
dai su yi hira na iya labarin da ya shafi kauyen, amma Mahnoor bata yarda a shigo
da hiran Jaish ba, da Jumma ta sako maganarsa bakin Mahnoor zai fara haila ta ki
bata amsa, sai ta yi kamar bata ji me ta ce ba, daga karshe ta kawo wani zancen ta
ɗaura a kai.

Har sai da mangariba ta kawo kai, sannan Jumma ta tafi ita kuma Mahnoor ta fito ta
kama aikin da ta saba.

A tsakar gida ta isko Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi kamar dai ɗazun a
gona, shi kuma bappa ya wuce masallaci daga nan ya wuce gidan Arɗo dan su yi magana
a kan Mahnoor ɗin.

After some days. Bayan wasu kwanakin.

An ɗaura auren bappa da Mairo tamkar yadda aka ce, yanzu saura tarewa, kwana
uku kenan yau da ɗaura auren, babu wani biki da suka gudanar saboda na faɗa maku
ita ba budurwa bace, so iya ɗaurin aure ne kawai sai kuma wannan al'adar tasu da
suke yi nahawa dutse dan a rubuta sunan ma'aurata, wannan dole ce a wajensu, sannan
sai al'adar da suke yi na yanka shanu ayi ta gashi, a can gidansu Mairo kuma an yi
al'adar da iyaye da makota suke yi wato a tara nono da fura dayawa ayi ta sha,
kowasu makota ranar ba zasu sayar da nono da furansu ba, zasu haɗosa a kawo gidansu
Mairo, shi ne nasu gudumawar.

Dik bakin da zasu zo sai su yi ta sha babu kakkautawa.

So iya abin da aka gudanar a bikin kawai, Mahnoor dai bata je wajen bikin ba, tana
wajen Inna kakarta, Mahreen kuwa da bata ga abin da zai hanata zuwa wajen biki ta
ci uwar sabada ba ai sai da ta je, ta ci uwar kyalliyar powder gora guda ta zazzage
a face ɗinta abinta, kamar aljanar asuba, amma saboda bala'inta kowa ya ganta sai
ya ce ta yi kyau sosai, kuma karya suke yi ba wani kyan da ta yi, kawai suna tsoron
bala'inta ne yasa suke yabata ɗin munahikai. Kaki yabata ka shiga uku.

Har da su Jumma sun je bikin, sun kuma yaba kyan Mahreen ƴar amarya kenan, dan
ita ta gama shaidawa kauye yanzu ita yar Diddi Mairo ce ba ƴar Nenne ba, wato a
duniya yarinta ma fa duniya ce, ba abin da ya kai shi daɗi, ta dai ce ita ƴar Mairo
ce, ta koma tsagin amarya.

Kwanaki uku ana ta hidima, yau za'a kawo Mairo ɗakinta ko in ce zata tare a
ɗakinta, bappa bai yi mata wani ɗaki na daban ba, ya ce a ɗakinsa zata zauna, so
nan kawai ya gyara mata, yaki yi mata wani bukkar.............. Ni Princess Teema
na ce anya bappa ba ɗan duniya bane kuwa? Wato so yake bakinciki ya kashe Nenne ko?
In ba tsabar minahinci ba ita ma ya yi mata ɗakinta daban kamar Nennen mana! Me na
wani ta sauka a nasa ɗakin?.

My people's kuzo mu yi gulma, anya ba maman Mahnoor bawan Allahn nan yake gani a
tattare da Mairo ba kuwa? To mu dai yanzu zamu koma team uwar gida Nenne dan mu
taya Nenne faɗa, haba wannan wani irin bala'i ne, yar cikinta ma ta gujeta ta
komawa amarya, to mu ba zamu yi lamurje ba.🙄

To izina garemu mata, shi dai bakin hali yana raba ka da kowa, ciki harda ƴaƴan
da ka haifa a cikinka, ya rage naku ku kyautata zamanku da kowa, ku zaku ji daɗi
idan kuka iya zama, kai in fa kuka zauna da kowa lafiya wlh sai kunfi abokan zaman
nakuma cin ribar zaman, ina fatan kun ɗauki darasi?!!.

Wato akwai dirama a gidan bappa fa, dan kuwa ko da ƴan uwan Mairo suka kawota basu
kwashe ta daɗi da Nenne ba, dan kuwa irin wanna nasiha da ake yi ace an kawowa uwar
gida amana nan da suka zo zasu bawa Nenne amana ta yi masu wankin babban bargo, har
da cewa su dai kaiwa bappa amana tin da shi ya rakitimowa kansa ita kuma yake ganin
zai iya, dan haka a kai mashi ba dai ita ba!!!.

Ta ci masu mutunci fes, dik da haka kuma bai isheta ba, da taga basu kulata ba sun
nufi cikin ɗakin bappa sun kai Mairo suna karisa mata jeren da basu gama na.

Sai Nenne kam ta fito da tanadin da ta ɗauki sati guda tana shirya masu, wato wuta
ta hura yana ci sosai, sai ta banka barkono mai bala'in zafi da yawa a cikin wutar,
ai ba iya ƴan kawo amarya ba, gabaɗaya unguwar rikicewa ya yi da tari mai sauti,
kun san yadda barkono yake a cikin wuta.

Haba ai ba yan kawo amarya ba, harta ita kanta amarya bata tsaya ba, tuni suka ari
kafar kare suka cikawa zannuwansu isa. Binsu da barkono da toka wanda ta daka
barkonon ta tanƙaɗe toka ta haɗe su wajen guda ta rinƙa ɗaurawa a leda, to shi ta
rinƙa binsu da shi tana harbinsu da shi, yana da bala'in zafi ga shiga hancin
mutun.

Idan ta harba shi ya faɗi kasa ya fashe sai tokan ya tashi sama da garin barkonon,
ya yi masu dai kamar guguwar turɓaya yana shiga hanci. Balai'n zafi ne da wannan
abin.

In short pata pata Nenne ta yi masu, ta zama kamar mahaukaciya, dik wasu abubuwan
da aka kawowa amarya sai da ta ta dawo ta watsa shi kaca kaca, abubuwan fashewa
dake cikin kayan kuma dik ta bi ta fashesu rugu rugu, kwaryar dama nono da su
ludayi da aka kawowa amarya masu bala'in kyau har da kwalliya a jikinsu, dik ta
takesu ta fashe, dik wasu tulu na jere sai da ta fashe shi!.

Abin dariyar kuma tana gama yin wannan aika aikan bata tsaya ba sai ta gudu gidan
Arɗo ba tare da Arɗo yasan ta zo ba, ta gudu ta je gwaggonta ta ɓoyeta a ɗaki ta
yadda ko annemeta a yau dai ba za'a ganta ba. Ashe maras kunyar karya ce ita.

Idan ran bappa ya kai dubu to ya ɓaci, yana ji da kansa an kawo mashi amarya kawai
Nenne zata wani rakasu a guje!. Wlh bata isa ba.

Cikin ɓacin rai bappa ya dawo gida domin ya ɗacaca mata kamar yadda ta ɗacaca
mashi, ta korar mashi amarya, yau Nenne ta kuresa ta kawo shi har wuya, hakan yasa
ya shigo a fusace, sai dai kash, bai sameta ba, wlh yau da ya sameta a gidan da
bakaramin duka zai yi mata ba, saboda ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci.

Cikin kunan rai ya juya ya fita, kai tsaye gidan Arɗo ya nufa dan ya dubata.
Sai dai ko da ya je can Arɗo ya ce mashi bata zo ba, dan bai san tana ciki ba.

Da kyar bappa ya iya haɗiye ƙuncinsa ya koma wajen Mairo dan ya basu hakuri ya kuma
ɗauko amaryarsa su koma gida a tare.

Kai my people's Nenne ƴar duniya ce wato.
===============≠===========🔥

••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••🔥

Kwance momma take a saman bed ɗin a cikin bedroom ɗinta, ta baro room na King, da
kanta ta kaiwa Jaish abinci cikin bedroom ɗinsa, a lokacin ta isko shi yana wanka,
sai ta koma room nata dan ta ɗan huta.

Sallama mama Haulat ta yi mata a bakin kofar shigowa, tana da kwance ƙasa ƙasa ta
amsa sallamar haɗe da bata izinin shigowa.

Turo kofa ta yi ta shigo, a ƙasa gaban bed ɗin ta zube gwiwowinta, cikin
girmamawa ta ce
"Barkanki da hutawa ranki ya daɗe".

Shiru na ƴan sakanni momma ta yi kafin ta amsa da. "Akwai wani abin mai muhimmanci
ne?".

"E dama uncle Jahiz ne yake parlour yake san ganinki".

Jinjina kai ta yi ba tare da ta sake magana ba ta nunawa mama Haulat hanyar fita da
hannu alamar ta je tana zuwa.

Miƙewa ta yi ta nufi waje tana yi mata addu'ar a fito lafiya. A cikin ranta ta amsa
addu'ar da Amin, Allah sarki, damuwa ne kamar zai kasheta, shiyasa King yasa a ɓoye
mata Guyson ya suma yana gadon asibiti, ga Chuchu ma kwance rai a hannun Allah, dik
saboda tashin hankalin ɓatar Zunaira, tun fitar da su Mummyn Chuchu suka yi

Please Login or Register in order to submit comment