Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 18 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya lura da kumburin da idanunta suka
yi, da kuma shi kansa face ɗinta.

Da yake Dr ne shi ɗin sai ya yi tinanin barcin da ta yi ta zubawa ne yasa idanunta
suka ɗan yi ja suka kumbura, bai dai yi tinani maras kyau ba.

Ganin ta kafe shi da kallo ne yasa ya ɗaga mata gera guda irin ɗan duniyar
nan. Bata san lokacin da ta ɗan wurga mashi hararar wasa ba sai ji ta yi ya ce.

"Laifin me kuma na yi yau kike hararata?".

Blinking eyes ɗinta ta ɗan yi tare da kawar da kallonta daga kansa, cike da
takaicin abubuwan da yake yi wanda suka saɓawa Allah amma a wajen mutanen birnin
Black world hakan normal ne, ranta yana ɓaci a dik time da taga Ronnie zai aikata
saɓon Allah, saboda tana san shi da rahama tana san ya tsira daga azabar lahira.

Ranta ya sosu sosai na ganin ya kara zana zanen tattoo a gefen wuyansa na dama,
sannan wannan uban ɗankunnaye da yake sakawa sam bata san ganinsu.

Cikin takaicin hakan ta ce. "Ronnie meyasa kake san aikata ba dai'dai bane?".

Idanunsa a kanta ya amsa da. "Menene kuma ba dai'dai ɗin da na aikata ba?".

Dawo da kallonta kansa ta yi, kamar ta kama kunnen nan nasa ta ja da karfi take ji,
bashi da aiki sai zane jiki ya kuma bi fuska da karafuna kaman wanda bashi da
mafaɗi, ko da yake kusan bashi da mafaɗin ne ai, tin da dik abin da yake so shi
yayansa yake yi mashi, kunga kuwa ai babu mafaɗi.

"Meyasa kake zane a jikinka kuma kake san saka waɗan nan karafuna a face
ɗinka?".

Fuskarsa ce ta sauya izuwa na mamaki, shi bai taɓa sanin hakan wani abin azo a gani
bane, ya ɗauki hakan a matsayin kwalliya ne kawai, bai ɗauki hakan wata tsiya ba,
dan haka with full of surprise ya ce.

"Hakan yana da aibi ne?"..............

Jinjina mashi kai sosai ta yi, kafin ta amsa da. "Babban aibi ma kuwa, kuma yana
ɗaya daga cikin kananun alamomi na tashi alkiyama!".
Ɗan jinjina kai ya yi tare da maimaita kalmar tashin alkiyama, kara rikiɗa face
ɗinsa ta yi izuwa na mamaki sosai, shi dai bai san wani tashin alkiyama ba.

"Menene kuma tashin alkiyama?". Ya yi tambayar kamar ba shi ya yi ta ba, irin
mutum ya yi magana unexpext haka.

"Ranar girban abin da ka shuka, ranar da kowa zai karɓi sakamakonsa..........".

"Dama akwai ranar da kowa zai karɓi sakamakonsa ne?"................... Kai ta
jinjina mashi alamar tabbatarwa, tabbas akwai ranar da kowa zai karɓi sakamakon
aikinsa da ya aikata a duniya.

Girgiza kai ya yi............... "Impossible, gaskiya ban yarda ba, ta ya za'ayi ki
ce mun dikka mutanen dake duniyar nan kowa zai karɓi sakamakonsa? Waye zai basu
sakamakon kuma a ina zai gansu har ya basu? Ke kin san adadin mutanen dake duniya
kuwa?!".................. Da ɗan kaifi a voice ɗinsa yayin da ya kai karshen
maganar.

Dama tasan da wuya ya yarda da hakan, amma da yake tana da kaifin ƙwaƙwalwa sosai,
ta iya bin mutun dik ta yadda ya zo mata, tasan irin kalamai da hujojin da zata yi
amfani da su wajen sanya mutum ya yarda da ita ko yaki ko ya so, sai bata ji komai
da jin kalamansa ba, bata wani damu ba, cikin sanyin murya ta ce.

"Ronnie ku nawa ne a school ɗinku?".

Kai tsaye ya amsa mata da. "Muna da yawa ba zan iya kirgawa ba!".

"Good......... Amma kuma dik yawankun nan ya aka yi mai school ɗin naku yasan
adadinku da har yake iya shirya maku jarabawa, idan kunci ya bawa kowa marking na
adadin amsar da ya bada, sannan waɗan da suka faɗi a sanya masu sun faɗi, har ya
rubutawa kowa result ɗinsa ya bashi da sakamakon abin da ya ci dai'dai wa dai'dai
babu zalunci?".

Shiru Ronnie ya yi dan ta buga mashi misali da hujja mai karfi, shi kansa ya
fahimci maganganunta abin dubawa ne, amma da yake shaiɗan la'anannen Allah ne sai
ya zuga shi a in da ya ce mata.

"To ai mai makarantar makarantarsa ne, dik wanda zai shiga school ɗin dole
yasan shi, kuma dole sai ya bada sunansa an rubuta, wannan dalilin yasa ya san
sunan kowa".

Wani irin daɗi ta ji ya ratsa zuciyarta, haƙiƙa ta ji daɗin wannan amsa nasa,
Ronnie ya ɗaure kansa da kansa, ai ko ta ina aka bi da mumini bayyana Allah a
wajensa ba abu bane mai wahala, har ta ji ta samu confidence a tattare da ita, dik
wani ciwo da take ji gaɓoɓɓinta suna yi mata sai ta ji dik sun ware, cike da murna
ta ce.

"Mai makaranta sai ya san sunan kowa idan za'a shigar da shi makaranta ko?".

Kai ya gyaɗa mata alamar e haka ya ce, yana nan with his full confidence, shi yana
jin ya kureta ai.

"And dik wanda zai shiga makaranta dole mai makaranta yasan da zamansa ko?".

Nan ma jinjina mata kai ya yi idanunsa a kan face ɗinta.

"Good.......... Na ji daɗin wannan bayanai ɗin naka, a nan duniya ma mutun ɗan
adam ma dan ya gina makaranta sai ya san da zaman kowa wanda yake cikin makarantar,
sannan sai ya san sunan kowa kafin ya shiga makarantar bare kuma Allah da ya
halicci dikkan duniya da abin da yake cikinta?".

Da ɗan mamaki ya ce. "Me kike nufi kenan, ban gane ba".

"Girma na Ubangiji ya wuci tinaninka Ronnie, ina san ka sani cewa dai'dai da
kwayar zarra a duniyar nan Allah ya san da zamansa, malaman makaranta sai an kawo
masu yara ake faɗa masu sunansu har su rike sunan su san da yaran ko?".

Jinjina mata kai ya yi alamar e.

"To shi Ubangiji shi ne da kansa yake sanyawa bawa suna! Kowani yaro da kake gani
da sunansa yake zuwa duniya, iyaye kawai suna isar da sakon sunan ne ga al'umma
cewa ga sunan ɗansu".

"Ban gane ba, ki mun bayani yadda zan gane"......... Yadda ya yi maganar da
alama ransa ya ɗan sosu kaɗan.

Tuni ta ji karfi ya zo mata, an taɓo addininta ana bukatar hujoji, ita ai dama abin
da take so kenan, su taɓota su ce ta kawo hujoji, dan dole kuma su gamsu, dan kafa
hujoji take yi da malamullah wato Alqur'ani mai girma, maganar Allah wasa ce? Idan
ka samu mutum mai daɗin baki ya yi maka magana ma ji zaka yi tamkar baka duniya
bare kuma ace maganar Allah? Ai ta wuci tinanin mutum.

Jingina bayanta da jikin headboard na gadon ta yi, cike da kwarin gwiwa ta fara
magana kamar haka.

"A cikin Alƙur'ani da hadisi. Allah ya bayyana cewa yana sane da dukkan halittunsa
tun kafin su zo duniya. Wannan ya fito fili a cikin Suratul Maryam, Sura ta 19 a
cikin Alqur'ani, Aya ta 7, lokacin da Allah ya yi magana game da annabcin da
haihuwar Annabi Yahaya A.S".

"Yaa Zakariyyaa innaa nubashshiruka bighulaaminismuhuu Yahyaa lam naj'al lahoo min
qablu samiyyaa."................

"Ya Zakariyya! Lalle ne, ina yi maka bushara da wani yaro, sunansa Yahaya, ban
taɓa sanya wa wani suna kamar shi ba a gabani wato kafin zuwan Annabi yahaya kenan,
ba'a taɓa samun mai suna irin nasa ba, shi ne farkon sunan yaya a duniya, zaka iya
duba wannan sura da wannan aya dan ka gani"

"A wannan aya, Allah ya bayyana cewa ya ba wa Annabi Yahaya suna tun kafin a
haife shi. Wannan yana nuna cewa Allah yana sane da mutum, ya kuma ƙaddara duk abin
da zai faru da shi, har da sunansa".

"Haka kuma, a cikin Suratul A’araf Sura ta 7 a cikin Alqur'ani mai girma, Aya ta
172 da 173, Allah ya ambaci cewa ya ɗauki alkawari da ƴaƴan Adam tun lokacin da
suke cikin tsatson iyayensu, yana tabbatar da cewa ya san dukkan halittunsa tun
farkon wanzuwarsu. Duk wannan na nuni cewa sunan mutum, tare da ƙaddararsa, yana
cikin ilimin Allah tun kafin haihuwarsa".

Tsit Ronnie ya nitsu yana sauraronta, shi ma fa yanzu yana san ya ji tana gaya
mashi girma da niimomi haɗe da isar Ubangiji, hakan na sanyaya mashi rai.

Cigaba ta yi da bashi hujoji, dan tana ganin kamar iya haka basu wadace shi ba,
bari ta kara mashi ko kaɗan ne dan narkar mashi da zuciya sosai!.

"Cikin hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama wanda Abdullah ibn Mas'ud
R.A ya ruwaito shi, Manzon Allah (SAW) ya ce. Lallai hakika kowane ɗayanku ana haɗa
halittarsa cikin mahaifar mahaifiyarsa tsawon kwanaki arba'in (a matsayin maniyyi
kenan) sannan ya zama ɗigon jini har tsawon kwanaki arba'in, sannan ya zama tsoka
tsawon kwanaki arba'in, sai mala'ika ya zo ya hura masa rai, to a wannan gaɓar ne
ake rubuta masa abubuwa guda huɗu. Na farko arzikinsa, ajalinsa, aikinsa, da kuma
ko zai kasance mai farinciki ko mai baƙinciki, dan haka kada wani bawa ya takura
kansa a kan abin duniya, already Ubangiji ya rubuta arzikinsa tin kafin zuwansa
duniya"

"Ingantaccen hadisi ne cikin Sahihul al-Bukhari, Hadisi mai lamba 3208. Sai Sahihul
Muslim, Hadisi mai lamba 2643 dik zaka iya nemo littafan ka duba lambobin dan ka
tabbatar!!".

"Wannan hadisi ya nuna cewa Allah yana sane da mutum da duk abin da zai kasance tun
kafin a haife shi, ciki har da ƙaddararsa da sunansa. Wannan shi ne alamar cewa
Allah mai ilimi ne da kuma iko akan dukkan halitta, dan haka Allah yasan komai dake
duniya, in takaice maka ma babu wani abin da ya isa ya motsa ba tare da izinin
Allah ba, dan haka dik abin da kake yi a duniya Mala'iku suna nan suna rubuta maka,
so akwai ranar da zaka girbi sakamako kamar yadda ka aikata ko in ce ka shuka"..

(Kai my people's ku tafawa Sweetie!! wani irin fata zaku yi wa Sweetie tamu ta
amana? Kun ji wata iriyar basira na misali da ta yi wa Ronnie da makarantarsu
kuwa?. To dik wanda ya karanta littafina ya samu karin ilimi da darusa ina rokon da
ya ɗaga hannu ya mun addu'a ni da iyayena da ƴan uwana, addu'a kowacce iriyace in
dai ta alkhairi ce a gareni wlh ina so, ba abin da zaku biyani da shi face wannan
addu'ar, ku mun ita ni da iyayena da ƴan uwana, Allah ya bar kauna 💘)

Dik jikin Ronnie ta yi la'asar kai har ma da mangariba, kamar ba shi ba, tabbas ya
yarda da maganganunta, musamman ma yadda ta kafa mashi hujoji da malaman makaranta
ma, tabbas su da suke mutane kamar kowa ma har suna iya sanin wanda ya shiga
makarantarsu da sunansa, su rubuta mashi jarabawa su kuma bashi sakamako bare wanda
ya halicci dikkan duniya?! Tabbas babban kuskure ne ma bawa ya yi tinanin Ubangiji
baya ganinsa a kan dik abin da yake yi, kuskure ne bawa ya yi tinanin ba za'a je
lahira ayi hisabi ba!!.

Sau uku Sweetie tana ambatar sunan Ronnie, amma ina bai jita ba, ya afka duniyar
tinanin maganganunta. Har sai da ta kai hannu ta ɗan taɓa shi, a ɗan zabure ya
sauke ajiyar zuciya.

Lafiya Ronnie?"........... Ta faɗa kamar bata san tinanin me yake yi ba.

"Sweetie gaskiya na ji kamar na yarda da addininki........." ......... To fah,
babbar magana.

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Na tabbata da zaka ji ko ka daure ka
koya daga addinina, to da hakika zaka gasgata cewa babu wani addini da ya kaishi,
ka daure ka ji kuma ka koya ka ji?".

Yau Black Tiger ya shiga fada, ana can anata hidimar shigarsa fada su kuma suna
nan, mutane sai shiɗewa suke yi na ganin bayyanarsa, shi kam Ronnie bashi da
labari.

Kuma hakan ba karamar nasara bace a garesu, dan kuwa wlh da Black Tiger yana nan
yana jinsu ba zai taɓa bari Sweetie ta yi waɗan nan jawabin dangane da Addinin
Musulunci har ta kawowa Ronnie hujoji cikin hikima wanda zasu ratsa shi har ya ce
ya fara yarda da addininta ba, da tuni zai katse masu hiran koma ya rabasu na har
abada, kunga kuwa shigarsa fada mu gaba ta kaimu, ko ba komai al'umma dayawa sun
samu karin ilimi a kan addininmu.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Sweetie na ji kuma na yarda da tashin alkiyama, amma ki faɗa mun menene
alamominta?".................. Cewar Ronnie.

Haba wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta, hamdala ta yi wa Allah da Ronnie ya
fara yi mata irin waɗan nan tambayoyi, Allah abin godiya, da ta samu nasara Ronnie
ya musulunta tana da tabbacin dayawa zasu musulunta ta dalilinsa, sai dai suna da
babban kalubale da barazana a gabansu wanda sai ta tsaya da addu'a matuƙa.

"Ronnie alamomin tashin alkiyama suna da yawa, akwai ƙananan alamomi akwai
kuma manya manya wanne kake san in fara faɗa maka?".

Kai tsaye ya amsa da. "Dikka nike so"........... Ya yi maganar cike da matsuwar san
jin wannan bayani, yana san bayananta, saboda komai dallah dallah take yi kuma a
nitse yadda komai jahilci da toshewar ƙwaƙwalwar mutun zai fahimceta.

Gyaran murya ta yi haɗe da kara gyara zamanta kafin ta fara bayanai kamar haka.

"Alamomin tashin alkiyama sun kasu kashi biyu. Alamomin kanana wato al-alamat
al-sughra kenan, sai kuma alamomin manya wato al-alamat al-kubra, gasu kamar haka".

"Alamomin Kanana sun haɗa da. Mutane za su ga lokaci yana tafiya da sauri, da
rana ya yi dare zata yi, kamar kyaftawa da Bismillah, alama ta farko kenan. Ta
biyu. Rashin sanin addini. Mutane za su bar koyon addini, ilimin shari’a zai ragu,
zasu koma san jin gulmace gulmace da karairayi haɗe da abin da bai shafi addini ba.
Na uku. Yawaitar zunubi. Zina, shaye-shaye, da rashin kunya, rashin kamun kai,
rashin darana iyaye da magabata, a ci mutuncin malamai da masu faɗar Allah, dik
wannan za su yawaita a doron ƙasa. Na huɗu Yawaitar yaƙe-yaƙe, jama'a zasu yi ta
yakar junansu, su yi ta kashe kawunansu ba tare da wata dalili ba, su kansu idan ka
tambayi meyasa suke kashe juna ba zasu faɗe shi ba!. Na biyan. Matsalolin
shugabanci. Shugabannin azzalumai zasu yawaita, zai zamana shuwagabannin basa
tsoron Allah, basu da tausayi, suna aikata ɓarna, suna zaluntar waɗan da suke
mulka, suna take hakkokin bayin Allah da shi kansa Allahn ba tare da suna nadama ko
kwayar zarra ba. Na shida. Kuma na karshe a ƙananan alamumi shi ne. Zama ababen
al’ajabi. Mutane za su gina manyan gine-gine suna takama da shi, su rinƙa gasa a
gine gine masu girma da tsawo".

My people's a nan zan ɗan yi tsokaci, a cikin waɗan nan alamomi na tashin alkiyama
ku faɗa mun wanenen bai bayyana ba?!! Dik wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa
yakamata yasan da cewa duniya ta zo karshe, jama'a har yanzu muna da sauran dama ta
tuba, mu tuba mu koma ga Allah dan mu rabauta, wlh babu in da duniya zata kai mutum
face halaka, mu yawaita sadaka da istigifari, mu yawaita jin kan na kasa da mu,
kada mu rinƙa duba na sama da mu, mu rinƙa duba na ƙasa ne hakan zai sa mu kyautata
lahiranmu, mu guji cin amana juna da zalintar mutane!.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

A dai'dai wannan gaɓa Ronnie jikinsa ta sanyaya, saboda yadda Sweetie ta ce jama'a
zasu rinƙa kashe junansu babu gaira babu dalili sai ya ji tamkar da mulkinsu take
yi, tabbas Black Tiger yana kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba, kuma yasan da
hakan yake kara goyawa yayan nasa baya, gaskiya wannan abin ya yi matuƙar taɓa
mashi zuciya, yasan dai ita Sweetie bata san ya suke gudanar da mulkinsu ba, dan
haka ba dan zalincinsu ta yi maganar shuwagabannin marasa adalci ba, gaskiya ne
kawai zallarta.

Ganin alamar nadama da tashin hankali a saman face ɗinsa ne yasa Sweetie ta kara
samun kwarin gwiwa, ta cigaba da cewa.

"Alamomin Manya na tashin alkiyama sun haɗa da Bayyanar Imam Mahdi. Bayyanar
Dajjal. Saukar Annabi Isa (A.S). Bayyanar dabba mai magana da mutane wato Dabbat
al-Ardh. Fitowar Yajuj wa Majuj. Fitowar rana daga yamma. Babban girgizar ƙasa. A
cikin Al-Qur'ani mai girma Allah ya yi Magana Kan tashin Alkyiyama da alamominta a
wurare daban-daban, amma ga wasu daga ciki.

"A cikin Suratul Zalzalah surata 99 a cikin Alqur'ani kenan, aya ta 1 zuwa ta 8.
Allah ya bayyana girgizar ƙasa ta tashin alkiyama. Iza zulzulatil ardu zilzalaha,
wato Idan ƙasa ta yi girgiza girgizawarta mai tsanani".

Izazullilatil ardu zilzalaha, wato Idan ƙasa ta yi girgiza girgizawarta mai
tsanani.

Sai kuma cikin Suratul Qiyamah, surata 75, aya ta 1 zuwa 40. Wannan sura tana
magana game da tsanani da al’amuran tashin alkiyama. Sai Suratul Takwir sura ta 81
aya ta 1 zuwa ta 14, An bayyana canje-canjen duniya yayin tashin alkiyama, Idan
rana ta birkice, kuma taurari suka fadi"................ WAYYO ALLAH KA HANAMU
GANIN WANNAN TASHIN HANKALI, MY PEOPLE'S KU CE AMIN, KU KANKU BAKU JI FAƊUWAR GABA
DA AKA CE IDAN RANA TA BIRKICE TAURARI SUKA FAƊI BA?..😥

"Sai cikin Suratul Inshiqaq surata 84 aya ta 1 zuwa ta 6. Allah ya bayyana yadda
duniya za ta karye"........... Ya Allah kasa mu cika da imani.

Ronnie sai da ya ji gabansa ta yi wani irin faɗuwa, kirjinsa ne ta bada dukan uku
uku, ya ji maganganu masu girman gaske daga bakin yarinya ƙanƙanuwa mai ƙananun
shekaru.

Shiru ya yi ya kasa magana tamkar wanda ruwa ya cinye shi, har sai da Sweetie ta
kai hannunta ta taɓa shi.

Firgita ya yi tare da miƙewa tsaye. "Ronnie lafiya kuwa?".

Girgiza mata kai ya yi ba tare da iya furta word ba, Allah sarki nan take zuciyarsa
ta karaya, ta yi matukar laushi, ya ji girman Allah bawan Allah, a take ya ji ya
aminta da ita ɗari bisa ɗari, ya kuma yarda da addininta, tabbas adininta shi ne
gaskiya, tabbas Ubangijin da take ambata shi ne na gaskiya.

A cikin wannan hali da suke master Devil ya yi knocking na kofar. Kallonta a kan
kofa Sweetie ta kai shi kuma Ronnie ya kai kallonsa saman tv dake kunne.

Ganin master ne a bakin kofar yasa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya
matso dab da Sweetie, jikinsa dik ya mutu, kamar zai rungumeta, ya fita tsawo nesa
ba kusa ba.

Dan haka sai ya rankwafo kanta, kamar zai sumbaci kumatunta, sai kuma ya mayar da
bakinsa saitin kunnenta. Har ta zaro idanu tana jiran jin saukar kyawawan lips
ɗinsa a saman bakinta, sai kuma ta ji yana yi mata raɗa a kunne.

Wani irin ƙayatatcen murmushi ta saki, da alama ta ji daɗin abin da yake faɗa mata,
cikin sanyin murya ta ce.

"Amma dai sai............"

Katseta ya yi ta hanyar zuro hannunsa ta saman shoulder ɗinta ya ɗaura yatsarsa
ɗaya a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru. Ba musu ta haɗiye maganar ta cigaba da
sauraron abin da yake faɗa mata.

Ya ɗauki a kallah 2 mins yana yi mata raɗa kafin daga bisa ya furta. "Anjuma da
daddare zaki kara mun bayani a kan Annbi Isa da kuma Imam Madih? Ina san jin
tarihinsu sosai, ina tsananin san Annabi Isa sosai".

Jinjina mashi kai ta yi alamar to ba tare da ta yi magana ba.
Shiru ya yi yana kallan gurun wuyarta, ya dakata da yin dik wata magana ya mace da
kallanta. Jin ya yi shiru baya magana, kuma bai ɗago kansa daga gareta ba, sai ta
ɗan juyo domin ta kalli me yake yi.

Tana juyowa fuskokinsu ya haɗe waje guda, bai ɓata lokaci wajen manna mata sumbata
a ɗan bakinta yana sakar mata cool murmushi ba.

Gabanta ne ya faɗi sosai lokacin da ta ji saukar lips ɗinsa a saman tata, lokaci
guda ta ji wani abu ya tsoki zuciyarta, bata san time da ta sakar mashi murmushi
ba, kun san fa murmushin Ronnie idan ya yi wa mutun ko baka so sai ka mayar mashi
da martani, sai ka murmusa kai ma.

Ƙasa ƙasa cikin salo mai jan hankali kamar mai raɗa ya ce. "Meyasa kike
murmushi? Sumbatar ta yi maki daɗi ne?".

Bata san time ɗin da ta gyaɗa mashi kai alamar e ba. Sai ji ta yi ya ce. "In kara
ɗaya?".

Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a. Yadda ta yi saurin dojewa yasa shi kara
faɗaɗa murmushinsa.

"Gaskiya kyakkyawa ce ke Sweetie". A kunne ya yi mata wannan raɗan.

"Kafini kyau ai........." Bata ƙarisa maganar ba ya yi sauri ɗaura babban
yatsarsa a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru.

"Your lips is so very very soft and sweet like your name Sweetie". Da muryarsa
kaman na ƴan maye ya yi maganar.

Master Devil ne ya sake yi masu knocking a karo na uku. Ƙoƙarin zullewa ta yi daga
kusa da shi dan tana tsoron master ya shigo ya gansu a haka. Ina cikin sauri ya
capko waist ɗinta tare da kara matso da ita kusa da shi.

"Meyasa kika ce kada na kara sumbatarki?".

Ƙasa sosai ta yi da murya wai dan kada master Devil ya jiyota......... "Saboda a
addinina hakan bai dace ba, sai idan matarka ce zaka yi mata hakan".

"To meyasa?". Ya jefa mata tambaya yana ɗan shafa lips ɗinta da yatsarsa, hannunsa
ɗaya yana saman waist ɗinta.

"Addinina yana da tsabta sosai, kai kanka ba zaka so ace kowani namiji zai iya
taɓa kowace macen da kuke tare wadda ba mallakinsa ba, misali yanzu kaddara ni
matarka ce, kenan kowani namiji zai yi mun kiss kamar yadda zaka yi mun, zaka yarda
da hakan?".

Ai a miliyan ya girgiza kai haɗe da cewa. "A'a ba zan yarda ba, sai dai ni kaɗai
zan taɓa matata".

"Good...... To kaga addinina akwai hikima da tsabta a cikinsa, shiyasa ya saka
dokar matan mutun shi kaɗai zai iya amfani da ita, addinina bai yarda kowa ya taɓa
matar wani ba".

Sosai ya kara samun kwanciyar hankali da addinin nan nata, saboda kyawawan ayyuka,
ga tsabta da cikar dik wani abin da ake so.

Master da gajen hakuri sake yi masu knocking ya yi. Ronnie tamkar bai ji shi ba, ya
bawa banza ajiyarsa.
A hankali yasa hannu ya janye mata dogon gashinta da ya zubo wajen wuyarta, slowly
ya kai ɗan bakinsa saman wuyarta, sumbata ya manna mata kafin ya saketa yana lumshe
idanu kamar wanda yake duniyar sama jannati, ita kuma murmushi ta ɗan saki kafin ta
juya da sauri ta nufi toilet.

Shi kuma ya bita da kallo yana ganin yadda round butt ɗinta suke motsawa cikin
kayan barcin Floris, gabaɗaya sai ya ji kasalarsa ta kara karuwa mashi, ya ji kamar
ya sake janyota jikinsa.

Har ta kai bakin toilet zata shiga sai ta juyo, a take idanunsu suka sarkafe cikin
na juna. Wani irin abu ya ji yana taso mashi a cikin zuciyarsa, ga wani abu dake
tsikararsa a tsakiyar kansa kamar wanda ake tsirawa allura.

"Ronnie bari in yi wanka, kuma ina jin yunwa sosai, ko sallan ban yi ba". A
ɗan shagwaɓe ta yi maganar.

Banda kallo babu abin da yake binta da shi, tamkar wanda ya ga bakon halitta daga
wata duniyar.

"Ronnie lafiya?". Cike da mamaki ta yi tambayar, tana magana tana ɗan tsuke fuska
tana ɗan ɗaure fuska.

In a low voice sosai, a kasale kamar wanda yake cikin maye ya ce. "Zallar madarar
kyau ne ya hanani yin magana"........... Har cikin ranta ta ji wannan magana, tana
matuƙar jin daɗi idan ya yabeta.

Ɗan juya idanunta sama kaɗan ta yi, kafin ta ce. "To ni dai kam yunwa nike ji".

A hankali ya motsa lips ɗinsa, voice ɗinsa bai fita ba irin magana mai alama da
bakin nan ya yi mata wajen furta. "Jeki kiyi wanka ina kawo maki abinci".

Jinjina mashi kai ta yi, har zata juya sai ta tuna wani love story da ta fara
karantawa a cikin littafinsa da ta gani a ɗakin nasa, dan haka sai ta tsaya ta
mannawa tafin hannunta sumbata, sannan ta huro mashi.

Wani irin lumshe idanu ya yi dai'dai lokacin master ya sake yi mashi knocking.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya motsa lips ɗinsa ya yi mata raɗa da. "Shige ciki".

Juyawa ta yi da sauri ta shige, shi kuma ya nufi kofar. Yana buɗewa master ya
tsaresa da kallo yana mamakin meyasa idanunsa ta rikiɗe haka? Anya yana da gaskiya
kuwa?. Ya jefawa kansa tambaya.

Shi kuwa ɗaure fuska ya yi tamkar bai taɓa yin dariya ba, a ɗan takaice ya tambayi
master da lafiya kuwa?.

"Babban yaya yana fada yana jiranka". Cewar master.

Sosai Ronnie ya yi mamakin jin furucin master, amma sai ya danne mamakin nasa ya
nuna kamar yasan da yayan nasa ya shiga fada. Rufu kofar ɗakin nasa ya yi sannan ya
wuce ya nufi escalator ba tare da ya sake bi ta kan master ba. A hanzarce master ya
rufa mashi baya, yana tafiya yana waiwayi ɗakin Ronnien, hankalinsa bai kwanta da
ɗakin ba, bai yarda da shi ba, yana ganin kamar akwai abin da Ronnie ya ɓoye a
ciki, kunsan master da shegen gulma.

=============================🔥

••••••••••••••••••JIMETA•••••••••••••••••🔥
Dirama iya dirama ake bugawa a wannan gida, Nenne dai tin da ta gudu gidan Arɗo a
ranar bata dawo ba, dan haka amarya Mairo dai ƴan uwanta suka sake hakura suka
rakota gidan bappa.

Da daddare bappa ya kwana da amaryarsa ita kuma Nenne tana gidan Arɗo ta yi

Please Login or Register in order to submit comment