Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 38 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai da kariyarsa".

Ƙasa ƙasa ya amsa da amin tare da miƙewa yana faɗin. "Zauna kici ko? Kinga tun
ɗazun kika ce kina jin yunwa". "To kai ina zaka je ba zaka zauna mu ci ba?". A
shagwaɓe ta yi maganar. "Ba zan jima ba, yanzu zan zo". Ya faɗa cike da san ya
tafi.

Bata san sake jefa mashi wata tambayar, dan tasan halinsa sam bai cika san tambaya
ba, tana kaucewa abin da baya so, sai kawai ta amsa da okey tare da komawa ta zauna
suka fara ciye ciyensu ita da Pretty.

After some minutes. Hannunsa ɗauke da wasu itatuwa ya dawo wajen, wuta ya zo ya
kunna masu sannan ya matsa gaba ya ɗauro alwalarsa a wajen ruwan gudun dake kusa da
su. Sallar mangariba da isha'i ya haɗa dikka ya yi, saboda matafiyi ne shi wanda
babu abin ganin lokacin a tattare da shi, hasalima bai iya gane gabas ba sai dai ya
kintata ya yi sallar kawai.

Bayan ya idar ya yi addu'a sosai, dik Zunaira tana ta aikin kallan motsinsa, a
yanzu basa iya ganin face ɗin juna saboda duhu, sai sun matsa kusa da wutar da ya
kunna suke iya ganin juna.

Bayan ya kammala ya matsa kusa da wutar ya zauna tare da lankwashe kafafunsa yana
kara wasu itatuwa a ciki dan wutar ta cigaba da ci har wayewan gari kada ta mutu.
Auta and pretty kuma suka tashi suka gabatar da sallar isha'i bayan sun gama cin
abin da suka ga zasu iya ci.

Shiru ya zauna yana tinanin irin kalubalen da zai fuskanta a kan soyayyarta, sai
dai ya kudurta a ransa ko mutuwa zai yi ba zai janye ba tin da ya rigada ya sanar
da ita cewa yana santa, sun kuma yi wa juna alkawarin ba gudu ba ja da baya.

Ya zurfafa cikin tinanin da yake yi, kamar daga sama ya ji saukar hannayenta a
saman shoulders ɗinsa, ta zarosu ta gabansa ita kuma tana ta bayansa, tana
durkushen a saman gwiwowinta, ta ɗan manna kirjinta da bayansa kaɗan, hannunta na
rike da fresh apple jajir mai kyau da zaƙi.

Saitin ɗan bakinsa ta kawo mashi apple ɗin, a daidai saitin kunnensa ta tsayar da
laɓɓanta, silent talk ta yi wajen furta mashi............ "My Hero kai fa baka ci
komai ba, ni kwata kwata ban ga kaci wani abin na fa, ka karɓi wannan ka ci". Ta
kai karshen maganar tare da kara matsar mashi da apple ɗin a dab bakinsa.

Rasa me zai yi ya yi, ya rasa a wace duniya yake, ya rasa a wani matsayi zai ajiye
kansa, yau shi ne tare da abar da ya fi kauna sama da komai nasa, kuma ga su a
ƙeɓaɓɓen waje, har da kulawa na musamman take bashi, bayan Abbonsa babu wanda ya
taɓa damuwa da ya ci abinci ko bai ci ba sai ita, kai ba zai taɓa manta wannan rana
ba a rayuwarsa.
Alhamdulillah ya rinƙa nanatawa a cikin zuciyarsa, ya ƙasa iya buɗe bakinsa ya
karɓi kyautarta a garesa. Ƙasa sosai ta yi da murya, kamar mai raɗa ta sake cewa.
"My Hero ba zaka ci kyautar da ya fito daga hannu na bane? Ko kuma sai na yi maka
kuka ne? Da kaina fa zan baka".

Oh my god, wani irin nisawa ya yi, ajiyar zuciya mai daɗin gaske da bai taɓa sauke
irinta ba ya sauke, a hankali ya buɗe ɗan bakinsa ta sanya mashi apple ɗin, kaɗan
ya gutsira yana jin tamkar babu abin da ya kai wannan apple ɗin daɗi a
duniya....... Oh soyayya ruwan zuma.

Sosai ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta na ganin ya gutsira, har ajiyar
zuciya ta sauke, wannan ajiyar zuciya da ta sauke ji ya yi tamkar ta kara lulluɓe
zuciyarsa da bargon farinciki ne. Ita dai Pretty sai sanya kananan itatuwa take ta
yi a cikin wuta, sam hankalinta baya ma kansu baiwar Allah.

Sake matsar mashi da apple ɗin kusa da bakinsa ta yi, dan farinciki haka ya rinƙa
gutsira yana ci har ya cinye ba tare da ya sani ba, cike da zumuɗi ta zame
hannayenta daga shoulders ɗinsa, tana ƙoƙarin barin wajen tana faɗin. "Bari in karo
maka wani my Hero".

A hanzarce ya ɗan juyo ya rike hannunta a cikin nasa. "Please ba sai kin karo
mun ba, wanda kika bani ya wadatar, na ƙoshi sosai saboda albarkan dake tattare da
hannunki".

Ƙayatattcen murmushi ta sakar mashi, wutar tana haskasu gwanin ban sha'awa, bata yi
musu da shi ba ta yi na'am da zancensa, sannan ya saketa. A hankali ta dawo gefen
damansa ta zauna suna fuskantar wutar, kanta ta kwanto da shi a saman damatsan
hannunsa tare da kamo hannunsa guda ɗaya.

Sillent talk ya yi wajen ce mata. "Baki jin tsoron dajin nan?"........ Ƙara yin
lamo a jikin hannun nasa ta yi. "Ni da nike tare da kai kuma my Hero tsoron me zan
ji?". Ɗayan hannunsa ya kai saman hannunta da ta riƙo nasa.
"Kina ƙara mun kwarin gwiwa sosai my Hoonaira".
A ɗan shagwaɓe ta yi magana ƙasa kasa ta yadda ita kanta tasan ba zai ji me ta
faɗa ba. "Ban ji me kika ce ba". Ya tambaya yana ɗan juyo da face ɗinsa saitin
tata, irin mutum ya juyo ya kalli gefen shoulder ɗinsa haka.

Sake yin maganar ƙasa ƙasa sosai ta yi, still dai bai ji me ta ce ba, hakan
yasa ya ɗan kwanto da kansa kusa da nata kaɗan ya kara tambayar me ta ce.

"Barci nike ji kuma san yi nike ji". Shi ne abin da ta faɗa. Tabbas akwai
sanyi sosai a wajen, shiyasa ma ya kunna masu wannan wutar dan wajen ya ɗan ɗumama.

"Tashi in ɗauko maki rigan sanyina na ɗazun ko?". ............ Make kafaɗa ta
yi. "Ni dai a'a, ba zan iya tashi ba". Kallan Pretty dake ta doka hamma ya yi, da
yake ita ta saba yin barci da wuri baiwar Allah, har idanunta sun yi ja alamar
barci.

"Pretty ɗauko mun rigan sanyina a wajen kayanmu, daga nan sai ki je ki kwanta dan
naga kamar barci kike ji"............ Da okey ta amsa mashi tare da miƙewa ta isa
ga kayansu.

"ko kema zaki je wajen da na tanada maku ki kwanta ne?". Ya jefa mata tambaya
yana zame hannunsa daga kan nata....... "A'a ni dai zan kwanta kusa da wutar nan
dan in rage jin sanyi". .......... Jinjina kansa ya yi alamar to. Kawo mashi rigan
sanyin Pretty ta yi, karɓa ya yi ta wuce ya je ya kwanta a wajen nasu tana yi masu
good night.
Cikin sanyin murya haɗe da tausasawa da lallaɓawa ya ce. "Ɗaga in saka maki rigan
kin ji?".
Jiki dik kasalar barci ta ɗan ɗaga shi tana turo baki. Sorry ya ce mata kafin ya
ware rigar ya sanya mata, sannan ta sanya shi dole ya miƙe mata kafafunsa ta tada
kai da laps ɗinsa tana daka hamma, lamo ta kwanta a laps ɗin nasa, wutan yana ɗan
ratsata kafin wani ɗan lokaci barci mai daɗin gaske ya yi awon gaba da ita.

Shiru ya zuba mata idanu yana ta kallan face ɗinta, ya ƙasa zare kallonsa daga
kanta, kamar yadda yaga rana haka ya ga dare. Tana kwance a kafarsa yana ta kallan
face ɗinta har dare ya tsala, Pretty ta jima da yin barci abinta.

Asuban fari Auta ta farka, ta sha madarar mamakin yadda ta kwnata daren jiya ta
barshi haka ta wayi gari ta same shi, cike da mamaki da tausayawa ta tambaye shi
bai yi barci bane?. Kai ya gyaɗa mata almar e bai yi ba.

"Meyasa to?". Ta jefa mashi tambayar tana kallansa. "Tashi mu je mu yi sallah mu
cigaba da tafiya, dan mu isa gida da wuri rana na ganin ido". Shi ne abin da ya
faɗa a maimakon ya bata amsar tambayarta a garesa. "Ni sai ka bani amsata zan
tashi". Kamar zata yi kuka ta faɗa.

"Kin manta jiya na faɗa maki cewa bana barcin dare? Kin kanta na faɗa maki
gadin gimbiyata kawai nike yi ne?"............... Tina maganganunsu na jiya ta yi,
abin ya kara bata mamaki, a tinaninta ya faɗa mata hakanne kawai saboda soyayya,
bata san dik kalamansa hakikanin gaskiya ce wanda babu mix ba, baya faɗar kalamai
dan jin daɗin soyayya ko kuma daɗin bakinsa, dikkan abubuwan da yake faɗa gaskiya
ne kuma yana iya aikata fiye da hakan a kanta.

Sai yanzu ta kara tabbatarwa da kanta lallai ta yi babban sa'ar da samun irinsa abu
ne wanda zai bada wahala, lallai Hoorain one in million ne. "Tashi to tin da na
baki amsa".

Ajiyar zuciya ta sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana". Da alama zuciyarta
ta yi sanyi dayawa, dan ta fara yarda son da take yi mashi wasa ne a kan wanda yake
yi mata. "Sai da aka gama jera mun tambayiyin ne za'a ce mun ina kwana?". Cikin
zolaya ya yi maganar.
Siririn murmushi ta saki tana sanya tafukan hannayenta ta rufe face
ɗinta. Wani irin daɗi ya ji na ganin murmushinta, lallai wannan safiya tasa ta fara
da kyawawan abubuwa.

Ta tafi da tinaninsa har ya sanya hannunsa ya kamo hannayenta da ta rufe, ya
buɗe dan ya ji daɗin ganin kyakkyawan murmushinta, yarinya mai kyan gani, dik wanda
ya ganta sai ya ji daɗi a ransa. Yunkurawa ta yi da sauri ta miƙe tana cigaba da
murmushi. Zama ta yi kusa da shi suna fuskantar juna, har lokacin wutar bai mutu
ba, a hankali ya saki hannayenta da ya rike yana kallan gefe.

"My Hero". Ta ambaci sunansa kallanta a kansa. Kin ɗagowa su haɗa ido ya yi,
amma ya amsa kiran. "Idan har da gaske kana sona, abu ɗaya zaka mun in tabbatar da
hakan".

Jinjina mata kai ya yi alamar to ba tare da ya yi magana ko ya yi wani motsi ba.
"Kalli cikin idona sai mu yi magana"......... Kamar ba zai yi hakan ba, sai kuma ya
daure ya ɗago da kallansa a kanta. Ya subhanallah, sarkafe juna da kallon kauna mai
tafiya da imani suka yi, gabaɗayansu sun lula wata duniya, dik sun kasa yin magana.
Sun macewa juna a kallo, ita kanta ganin cikin kwanciyar idanunsa yasa ta rasa
nitsuwarta bare kuma shi.

Sai da suka ɗauki good 5 mins a haka, sannan ya yi ta mazan lumshe idanunsa yana
jin wani abu na mashi yawo daga tsakiyar kansa izuwa tafin ƙafarsa. Cool voice
ɗinta ya ji a kunnuwansa tana faɗin. "Na yi fatan mu kasance ma'aurata da wuri".
Waro idanunsa a hankali ya yi ya kalleta. "Na fiki yin wannan fata my Hoonaira".
Nisawa ta yi kafin ta ce. "Yanzu misali a ce yau daddy ya ce ya mallaka maka ni ya
zaka ji?"........... Wani irin lumshe idanunsa cikin salo mai jan hankali ya yi
tare da yunkurawa ya miƙe tsaye. Binsa da kallo ta yi. Hannu ya sanya a cikin sumar
kansa, a hankali ya ɗan watsa gashin nasa haɗe da ɗan ciza laɓɓansa kaɗan, wani
irin nisawa ya yi ya ƙasa magana.

"My Hero lafiya kuwa?". Ta yi maganar tare da miƙewa tsaye ita ma........ Kai kawai
ya girgiza mata, ya ƙasa magana, wato baki ya yi kaɗan wajen zayyana irin
farincikin da zai shiga dik ranar da aka mallaka mashi ita, wow abin ba'a magana,
soyayyarsu soyayya ce kafun Allah, ba aba bace da aka ginata yau ko jiya, shekaru
ake magana, zuƙatansu sun narkewa juna dayawa da jimawa, a yadda suke ji zasu iya
aikata komai a kan junansu.

Hannunta ya riƙo cikin nasa, wajen ruwan da suka yi alwala daren jiya suka
nufa. Sai da ya duƙa gaban ruwan zai fara taɓa ruwan ne ya yi karfin halin cewa.
"Ki dai'na yi mun irin waɗan nan tambayoyi, saboda baki ba zai iya faɗar yadda
girmanki yake a rai'na ba, watarana zaki iya sanya zuciyata ta aikata wani abin da
ya saɓawa shari'a idan kina irin waɗan nan tambayoyi".

Jinjina mashi kai ta yi tare da duƙawa ita ma dan ta ɗauro alwala, kamar zai ce
mata tana bukatar yin tsarki kafin alwala, sai kuma ya yi shiru saboda kada ta yi
mashi wata mummunar fassara, yasan halinta sarai.

Yana ganinta ta yi alwala, shi kuma ya tsaya bai yi ba, har ta gama ta miƙe, baya
kaɗan ta ɗan ja ta tsaya wai tana jiransa, ganin hakan yasa ya miƙe tsaye, cikin
sanyin murya ya ce. "Jeki ki tashi Pretty, sannan ki yi sallarki ina zuwa"........
Bata yi mashi musu ba ta wuce tana waigosa, shi ma kallanta yake yi har ta kure
mashi. Sannan ya matsa daga in da yake zuwa gaba dan ya yi tsarki.

Zaune ya isko Auta kusa da wuta, ita kuma Pretty tana sallah. Matsawa ya yi kusa da
ita, a gabanta ya zube gwiwowinsa, cike da so da kauna ya miƙo mata flowers da ya
ciro mata yana kallan face ɗinta............... Ai tsabar farincikin bata san
lokacin da ta saki ɗan kara mara sauti sosai ba. Hannunta har yana kerma wajen
sanyawa ta karɓi flowers ɗin, jikinsa ta faɗo unexpect tana murmushi. Rungumeta ya
yi yana jin daɗin ta yi farinciki.

A hankali ta ɗago kanta daga saman kirjinsa, sumbatar flowers ɗin ta yi, lokaci
guda ya ji tamkar kumatunsa ta sumbata, har wani ajiyar zuciya ya sauke, shi kaɗai
yasan me yake ji a ransa, cikin ƙanƙanin lokaci ya ji ya kwaɗaitu da san
sumbatarta.

"My Hero nagode sosai, farkon kyautarka a gareni, ba zan taɓa manta wannan
rana ba, ina sanka fiye da yadda ma'aunin tunanin mutum zai iya aunawa". Tana
magana idanunta suna ciccikowa da kwallah.

Hannu ya kai saitin gemunta, hawayenta da suka cika idanunta ne suka zubo har kan
tafin hannunsa, nisawa ya yi, calmly ya furta. "Ki dai'na mun asaran hawayena,
please my Hoonaira, kada ki sake bari su zuba kin ji?".

Kai kawai ta gyaɗa mashi, Allah mai juya dare ya zama rana, rana ya zama dare, wai
yau ita ce tare da masoyinta a nan suke zuba soyayya wa junansu?. Pretty ce ta
katsesu da cewa. "Ina jin yunwa sosai Zunaira".

Zame hannunsa Hoorain ya yi daga kusa da ita, sannan ya miƙe yana faɗin. "Ku tashi
mu fara tafiya, a gaba zan sama maku abin da za ku ci". Ya kai karshen maganar
tare da nufar in da ya ɗaure dokinsa daren jiya. Kwantota ya yi ya zo ya ɗaukesu da
dik abubuwansu, a yanzu sai ya sanya Pretty a baya Auta a gaba, shi a tsakiyarsu
kenan, saboda a jiya da ya sanyasu dikka a gaba sun haifar mashi da matsala ta
rashin gudu sosai, dole ya rabasu idan yana san su yi gudu sosai su samu damar isa
da wuri kafin rana ta faɗi.

Daga haka suka kutsa cikin daji da gudun gaske........ To Allah ya tsare hanya our
love birds.


🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

After some days. A waɗan nan ƴan kwanaki da suka wuce abubuwa sun faru wanda suka
haɗa da ganin Khadijah da su uncle Jahiz suka je, and jiya da daddare Khadijah ɗin
ta farfaɗo baiwar Allah, amma ta ji azaba ba karya, dan ma ta samu kulawar likitoci
sosai ne yasa, sai dai bata magana dik da ta farfaɗo ɗin ma.
Time da uncle Jahiz ya ganta sai da ya ɗan razana kaɗan, dan a fili ya
furta tabbas ya taɓa kallan wannan fuska, sai dai ya manta a ina ne.

(Anya ba raina mana hankali yake san yi ba kuwa?🤔 Shi da yake Tunisia a ina ya
taɓa ganinta ita da take Nigeria bata taɓa fita ko'ina ba, ko Abuja bata taɓa zuwa
ba sai sanadin Hauwa bala'i, to aina ya taɓa ganinta? Anya zarginmu a kansa ba
gaskiya bane kuwa? Mu je dai zuwa, lokaci ne zai warware mana komai.)

Abu na biyu da suka faru kuma shi ne su commander Zafar sun ci nasara a yakin da
suka tafi, sai dai kuma da kyar suka sha, saboda commander mayakan Queen Zarina
wato mai kama da Hoorain namu ya kawo masu babban barazanar da sai da dangerous
warriors suka girgiza, sun kasa iya taɓa jikinsa, saboda suna tsoron su taɓa
jikinsa a matsayinsa na assistant commandernsu. Shi kansa commander Zafar ƙasa taɓa
shi ya yi saboda kowa ya san yana kaunan ɗansa over. In short sai da commander yaga
da gaske wannan zai iya hallaka shi idan shi bai kashe shi ba to shi zai kashe shi,
sannan ne fa ya bawa warriors ɗinsu umarni da su kashe shi koda Hoorain ɗin ne tin
da kashesu shi ma yake ƙoƙarin yi.

Sosai mayakan suka yi mamakin jin furucin commander, Allah sarki basu lura ƙoƙarin
kashe commander ɗin shi ma yake yi ba, da ciwo mai kama da ciwon zuciya commander
ya dawo Kingdom of power, Allah sarki, ya ƙasa yarda Hoorain ne, sannan ya gargaɗi
mayakansu da kada su yarda su sanar da King Zuhair abin da ya faru, su rufa mashi
asiri su bashi lokacin zai binciko gaskiya, dan ya tabbatar ba Hoorain ɗinsa bane,
idan kuma shi ne to tabbas akwai wani abin da aka yi mashi, ba haka kawai ba.

To tin da suka dawo wannan yaki commander yake kwance yana jinya, ya kasa samun
kwarin zuciyar iya ɗaukar wannan balai'n bare har ya iya tashi ya binciko gaskiya,
sai zargi zuciyarsa take ɗarsa mashi, ya yi tinani ya fi dubu a kan hakan, sai faɗi
yake yi dama kenan da Hoorain ya gudu daga nan bayan Zarina ya koma ne ko
yaya?...... MY PEOPLE'S GASKIYA ABIN DA ƊAURE KAI, ALKALAMIN PRINCESS TEEMA TAKU TA
AMANA CE KAWAI ZAI IYA WARWARE MAKU WANNAN CAKWAKIYA, KU DAI MU JE ZUWA.

Abu na uku da ya faru a kingdom of power kuma shi diransu Omaid and Obaid, sun samu
hutun karshen shekara, azumi ya kawo kai, sun samu hutun dawowa gida su yi azumi,
shi kuma guyson yanzu result ɗinsu ya fito har ya yi registration, yanzu guyson
namu zai shiga hundred level, ya zama babban yaro, yanzu jami'a yake, sai sakalci
da kukan ciwo kam har yanzu tana nan.

A ɓangaren su Mammie kuwa suna can suna aikin kullace kullacensu, sai shirya ta
yadda zasu taimakawa Fanan suke yi, ita ma Fanan yanzu ta bi bayansu, a kan
soyayyar Jaish ta yarda dik abin da suka sanyata zata iya aikatawa. Babbar magana,
mu je zuwa.

Shi kuwa King, yanzu hankalinsa yana can yana kan neman Auta, tin yana ganin abin
kamar da sauki har ya fara ganin abin fa ya zarce tinani, ya baza mayakansa a
ko'ina nemanta ake yi, wasu har cikin dajin da su Hoorain suke suka shiga, amma
basu samu haɗuwa da su ba.

Mahnoor and Mahreen suna ta shan gyara, wa'adin da momma ta ɗibawa King gobe zai
cika In Sha Allah, yau sai busy momma take yi tana shirya masu oder kayayyaki na
gani na faɗa wanda zasu tashi kai. Sarina dai dik balai'nta bata samu damar ganin
Mahnoor ba, dole ta hakura suna jiran gobe a fito da ita su ga wace tsiya ce.

Wannan shi ne kaɗan daga cikin abubuwan da suka faru a ƴan kwanaki da suka shuɗe,
to mu je zuwa.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

7:30am. Agogon kingdom of power mai tsananin kara ta buga. Sanye uncle Jahiz yake
cikin shiga ta ƴan kwallo na team ɗinsu, ya ɗaura jacket a kan kayan nasa saboda
sanyi da ake yi, cikin nitsuwa yake takowa, daga part ɗin Akka ya fito izuwa part
ɗin mama wajen Aneesa kenan.

Yanzu likitoci asibin kingdom suka yi mashi waya a kan Khadijah ta farfaɗo daren
jiya, dan haka suna bukatar na kusa da ita wanda ta sani ya zo dan suka yanayin
kwakwalwarta, ta ki yin magana, ta kuma ki yin motsi ƙwaƙƙwara, to shi suke buƙatar
Zee, idan ta zo kila Khadijah zata yi magana ko wani abin da zai sa su fahimci tana
cikin hayyacinta kuma aikinsu ya yi kyau.

Wannan dalilin yasa ya fito da safiyar nan zai je wajen Zee su tafi hospital ɗin,
ga shi cikin satin nan yake san komawa Brazil, dan suna da wasa, hutun da ya ɗauka
ta kusa karewa, zai je ya shirsshirta.

Bakinsa ɗauke da sallama ya afka cikin ɗakin Aneesa, bai yi tinanin sun tashi
daga barci bama shiyasa ya afka kawai. Wani irin birki ya ja lokacin da idanunsa
suka sauka a kan Zee dake tsaye gaban mirrorn Aneesa tana shafa mai, daga ita sai
towel a ɗaure a kirji, ita kuma Aneesa ta fita izuwa kaiwa mummyn Chuchu
labari...... KO LABARIN ME ZATA KAI MATA KUMA?🤔

MU JE ZUWA ZA DAI MU JI.

Zee har ta goge ta yi kyau, sai dai ko kaɗan bata jin daɗin zama da su Aneesa, suna
tsangwamanta, bare ma Sarina da in dai ta shigo sai ta ci mata mutuncin da kare ma
ba zai sinsina ba, amma tana hakuri tana dannewa dan gidansu ta zo, kuma ko ba
komai sun taimaka mata, ita burinta Khadijah ta samu lafita su koma Nigeria abinsu.

Da yake uncle Jahiz ɗan duniya ne girma cikin turawa, sai ya fara binta da kallo
tun daga kafafunta har izuwa kirjinta, sai da ya ɗan tsai da idanunsa a kan
kirjinta ma kafin ya kai kallansa a kan face ɗinta. Ta yi ƙasa da kai ta takure
jikinta waje guda, tana jin kunyar motsawa daga in da take, jin sallamarsa dama
yasa ta juyo, ta yi danasanin ɗaura towel bata sanya hijabi kamar yadda take yi a
gida ba, kuma saboda taga babu wanda yake shigowa ɗakin ne yasa bata saka hijabin
ba.

Ko kaɗan babu kunya a idanunsa ya sake dawo da kallansa a kan kirjinta da suke
cike fam, a hankali ya kalli santala santalan cinyoyinta da yanzu suka murje suka
yi kyau saboda wanka da sabulai masu rai da lafiya na Aneesa da take yi.

Ya kasa motsawa ya kuma kasa kawar da kallonsa daga kanta, sai ma ƙara kurawa
kirjinta ido ya yi, ita kuma ta kasa gudu ta bar wajen, to me kuke tinani zai faru?
Shi dai uncle Jahiz ba kunya ne da shi ba, ni dai na tafi shan maltina idan na dawo
zan ga shi da ita waye zai ɗagawa ɗan uwa kafa, shin zai hakura ya ja da baya ya
koma ne? Ko kuma ita zata danne zuciya ta gudu? Su dai suka sani, ni na yi ta
nan...............🥱
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Cigaba da karewa albarkatun jikinta kallo yayi, kwata kwata babu alamar zai ja da
baya ko ya kawar da kansa, ta gaji da tsayuwa taga alamar bafa dai'na kallanta zai
yi ba, dan haka sai ta daure ta fara takawa a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a
ciki ta nufi dressing room na Aneesa.

Dik wani step ɗinta ɗaya a kan idanunsa take yi har ta kurewa ganinsa,
nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan dukar da kansa ƙasa, shi kaɗai ya fara
ayyana yadda kyanta yake a cikin ransa, saman sofa ya zauna yana kara jinjina kyan
abin da ya gani, to da alama dai ransa ya biya.

Shi da bashi da fara'a ko kaɗan, sai ga shi yau ya sanya hannu saman arabs hairnsa,
yana ɗan watsa gashin yana murmushi kamar wani sabon kamu......... My people's ni
wai ba uncle Jahiz ba ne ya ce ba zai taɓa san mace ba sai ya kai 40 years? Sannan
har da wani ce mana babu abin da zai yi da yar yarinya, shi mace daga mai 25 years
ya yi sama yake so? Anyi haka ko ba'ayi ba? To inaruwansa da Zee ɗinmu? Zee dai 17
years take da shi, ko Khadijah bata kai 20 ba bare Zee bare kuma a kai ga 25 years,
me uncle Jahiz yake nufi? Kada ma ya kuskura ya fara ce mana ya janye kalamansa,
dan ba zamu lamunta ba, amma guy ɗin nan ya sha damu dama, to wai an faɗa mashi
mata wasa ne?......…....🤔

Shiri Zee ta yi cikin abaya again, kunsan su Aneesa kaso 80 cikin ɗari na kayansu
abayas ne, saura kaso 20 ɗin kuma irinsu riga da wando, riga da sket and gown ne.
Abaya mai kyau da tsada launin purple color ta sanya, ta yi rolling mayafin a
kanta, sai kuma ta ƙasa fitowa waje, saboda bata san haɗa idanu da shi, zuciyarta
ta ja baya matuƙa da shi, dama kun san halin Zee ai, yanzu ma saboda Khadijah ta
samu lafiya yasa ta yi sanyi take jure komai da ake yi mata, banda haka ai wlh ba
sarauta ba, ko uban me

Please Login or Register in order to submit comment