Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 63 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda ya yi wannan
rantsuwa yake magana a fusace haka ya tabbata iya gaskiyarsa yake faɗe, and kome
zasu yi ba zasu taɓa canza mashi ra'ayi, dan haka sai ya ce. "Okey dad, na yarda da
maganarka, na yarda Zunaira ba zata auri Hoorain ba, but ina san ka saki Hoorain ya
koma yadda yake rayuwa kamar da". Ya kai karshen maganar tare da ɗago idanunsa,
unexpect ya yi arba da fuskar Auta tsaye a bakin kofar balconyn tana kallansa tana
hawaye, bai yi zatan tana kusa ba, yanzu ta ji dik abin da suka faɗa da King.

Daga cikin wayar King ya ce. "Already ni na saki Hoorain, yanzu haka yana hospital
yana jinya, idan ya samu sauki zai koma bakin aikinsa, dan mun yi yarjejeniyar
hakan da mahaifinsa, ya mun alkawari Hoorain zai rabu da Zunaira har abada, shiyasa
ma na sakesa".

Jinjina kai Smart ya yi zuciyarsa na ƙoƙarin pushing na fushinsa ya bayyana, shi
kuwa yana ƙoƙarin danne zuciyar tasa saboda kada ya yi jayayya da mahaifin nasa,
yana da ilmin addini sosai, so yasan rabo tana kisa, idan ya tsaya ya ce zai ja da
dad ɗin nasu in Allah ya ƙaddara za'ayi wannan aure to suna iya rasa King ɗin,
hakan ne kuma baya so, shiyasa ya sassauta zuciyarsa ya aminta da haka, gara mashi
su bi wata hanya su saka King ɗin kaffara kawai a kan su yi ja in ja da shi su rasa
shi na har abada, a kan batun aure da batun yara ba'a jayayya, idan ma'aurata sun
rabu ba'a gardama a kan ƴaƴa, misali ace uwa ta ce ita zata rike uba ya ce abasa
kayansa, irin haka ma Allah yana ɗauke ƴaƴan kowa ya raba faɗa, so a kan aure da
yara ba'a ja in ja.

"Dad zamu yi magana anjuma". Yana kai karshen maganar ya katse kiran diff ba tare
da ya jira amsarsu ba. Alama ya yi wa Auta da hannu a kan ta zo. Da ƴar gudunta ta
tafi ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai tsuma zuciya. Rarrashinta ya fara yi cike
da so da kauna. Cikin kuka ta fara faɗin. "Shikenan Yah Omerish kai ma yanzu baka
goyan bayana? Yanzu ka koma bayan dad? Kai ma baka san my Hero?".

Hannu yasa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ya ce. "Kin
yarda da ni?"....... Kai ta gyaɗa mashi alamar e ta yarda da shi. "To i promised
you that In Sha Allah zaki zama mallakin muradin ranki, burinki zai cika wannan
alkawarina ne, alkawari kuma kaya ne". Cike da gaskiyarsa ya yi maganar, babu wasa
ko golaya dan ta yi shiru yasa ya faɗa mata haka.

A ruɗe ta ce. "Yah Omerish how? Ta yaya zan mallaki Hoorain bayan daddy baya sansa,
kuma ya yi rantsuwa da girman Allah ba zai bashi ni ba, sannan kowa a gida baya
sansa, har Akka bata sansa, and nan da one week dad ya ce zai aura mun Yah
Abdussalam". Tana magana zafafan hawaye suna bin kuncinta.
Ɗan jinjina kai ya ɗan yi kafin ya ce. "Haka ne dik abin da kika faɗa,
and nasan abu ne mai wahala yiwuwar aurenku, amma In Sha Allah daddy da kansa zai
sanya maku albarka a ranar aurenku, darasi zan bawa gabaɗaya familynmu ta yadda
gobe ko da kuɗi aka basu ba zasu taɓa sake kyamar talaka ko na kasa da su ba".

Zaro idanu waje ta yi, cike da ƙaguwa na san jin abin da zai yi masu ta ce. "Me
zaka yi masu da har zai sa su koyi darasi?". Hannu yasa yana share hawayenta ya
amsa mata da. "Kada ki damu, ke dai keep praying for me". Ya kai karshen maganar
yana duba wayarsa dake ruri alamar shigowar kira. Number momma ce again, kuma yasan
dad ne, dan haka sai bai yi picking ba, saboda yana san ya ɗan yi tinani a kan irin
lesson da yakamata ya koyar da familyn nan nasu, su san cewa mutum ɗan adam ba abin
rainawa bane, da talaka da mai kuɗi dik Allah ne ya yi su..

Jama'a na ce mu jinjinawa momma, lallai ba shakka jinin momma ce yake gudana a
jikin Smart, a gabaɗaya kingdom of power momma ce kawai bata kyama ko kyarar
talaka, ita ce kawai ta ɗauki kowa dik ɗaya suke, ita ce uwar marayu irinsu
Mahnoor, Zee, Khadijah and Mahreen, lallai ba shakka momma baiwar Allah ce kuma
jininta ya fi karfi a jinin SMART!! Dan kunga shi ma baya gudun talaka bawan
Allah!.

Pretty ce ta katse masu hiransu ta hanyar miƙewa zaune a saman kujerar da take
kwance, kwata kwata Auta bata lura da ita ba tun shigowarta, dama a saman kujerar
ya kwantar da ita, sannan ya wajen ya yi mata allurar da ya ceto rayuwarta. Sai dai
kuma ya yi matuƙar mamakin ganin ta yi saurin farfaɗowa, yasan dai zata iya kai
kwana biyu a sume kam, sai kuma ga shi ko awa biyu bata yi ba ta farfaɗo, abin da
bai sani ba shi ne ita fa Pretty ko da bai yi mata wannan allura ba zata farfaɗo,
saboda poison dake cikin chemical ɗin bai yi mata lahani ba dan ita ma akwai irin
abin dake jikin Sweetie a jikinta, kuma ita ma hannunta yana iya yin magic, sau da
dama tana ɓarin abu ta hanyar magic ɗin, amma rashin sani yake sakawa ta yi zatan
kawai ɓari ta yi, bata san da shi a hannunta ba.

Da kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa a ransa yana mamakin tashinta a yanzu.
Cike da kula da so da kauna Auta ta ce. "Pretty ina kika shiga ina ta nemanki".
Tana aikin turo baki bata yi magana ba, miƙewa daga jikin Smart Auta ta yi ta koma
wajenta dan ta ji menene yake damunta. Shi kuma Smart miƙewa ya yi yana faɗawa Auta
zai je gidansu wajen mom sai kiransa take yi, yanzu ba jimawa zai dawo, daga karshe
ya ce mata kada ta sare kuma kada ta bar Hoorain cikin kewa ta rinƙa kiransa a waya
In Sha Allah kukanta zai tsaya. Da okey ta amsa mashi tana murna, har da sakin
murmushi. Kai yasa ya nufi waje a ransa yana tina ta yadda zai yi ya yi maganin
King, lallai ba zasu koma kingdom of power a yanzu ba, dole su dakatar da auren
Abdussalam, sai after one month zasu koma, dole ya yi magana da momma dan su shirya
komai a tare ta yadda ba zasu rasa King ba.

My people's kuna ganin shirin nan zai shiryu kuwa?. Auta zata mallaki Hoorain kuwa
a yadda King ya datse dik wata alaƙarsun nan?. Muje dai zuwa, zamu ga shin Smart ne
zai yi nasara ko King!.

🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬


44



🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

Tafiya take yi tana waige waige ta fito daga part ɗin mama ta nufi part ɗin momma
domin ta duba Zee, har yanzu uncle Jahiz bai dawo mata da babynta ba, yana can
ɓangaren Aunty MieMie suna hira, Aunty MieMie ta rike baby gam, ta ce sai dai
uwarsa ta biyo shi part ɗinta, ma'ana sai dai Khadijah ta dawo part ɗinta da zama,
dan ita ta samu yaro, dama bata da shi, uncle Jahiz ya ɗauka wasa take yi, aikuwa
ta nuna mashi da gaske take yi, dan fa ta dage Allah ba zata bada babyn nan ba,
uwarsa kawai ta dawo part ɗin da zama dan yaron ya shiga ranta.

Sai waige waige take yi dan bata gama sanin hanya ba, hanyoyin akwai sarƙakiya,
idan ba ka san cikin family part sosai ba zaka iya ɓacewa, shiyasa take ta waige
waige, taga hanyar shiga part ɗin King and Akkas part, sai ta ruɗe ta rasa ina zata
bi.

Unexpect suka ci karo da mutum, ya fito daga bedroom ɗin King, King ne ya kirasa a
yazo a kan batun Spender, so shi ne dalilin zuwansa. Karo suka yi ta ɗan yi baya
tana goge goshinta da ta buge da kirjinsa, da yake ita ta fi Zee ladabi da kuma
hankali sai ta durkusa kasa tare da ɗaga mashi gaisuwa.

Ido uncle Abbas ya zuba mata yana mamakin ganinta, dan shi bai san ta a kingdom ɗin
ba. Jin bai amsa mata bane yasa ta ce. "Kayi hakuri ban ganka bane shiyasa"......
Jin kalamanta yasa ya yi saurin ce mata. "Babu komai tashi ki je abinki".

Miƙewa ta yi tana yi mashi godiya tare da satar kallansa ta ƙasa ido, gaba ta yi ba
tare da tasan ina ta dosa ba, dan bata gane hanyar part ɗin momma ba. Da kallo
uncle Abbas ya bita baya san kawar da kallansa daga kanta. Har ta ɗan yi nisa ta
tsinkayo muryarsa yana faɗin. "Zo ina da tambaya"........ Juyowa ta yi ta dawo
gabansa, tana ƙoƙarin tsugunnawa ya yi saurin cewa. "A'a ba sai kin durkusa ba,
magana zamu yi a tsayen ma is okey".

Ƙasa ta yi da kanta tana amsa mashi da okey cikin harshen turanci. "Zan iya sanin
wacece ke?". Ya jefa mata tambayar yana ɗan sunkuyo da kansa ya kalli face ɗinta.
Lokaci guda ta ji gabanta ya faɗi, sai ta ji wani irin fargaba mai razanarwa,
tsoronta ɗaya kada yasa a hukuntata dan bata da wata alaƙa da masarautar, kada ya
ce waye ya kawosu? To waye zata ce mashi tun da ita ko sunan uncle Jahiz bata sani
ba bare ta faɗa mashi sunan wanda ya kawosu.

Ganin ta yi shiru ta rasa abin faɗe yasa ya ce. "Zaki iya tafiya". Dan ya lura
tambayarsa ya saka ta a cikin damuwa, lokaci guda hakan ya bayyana a face ɗinta. Ai
yana cewa ta tafi ta yi gaggawar juyawa har kamar zata yi tuntuɓe, da kallo ya bita
yana jin kamar wani abin a ransa, mamakinsa ɗaya shi ne a ina aka samo waɗan nan
black beautys ɗin?.... Ni kam na ce to dama mu Nigerians ai shegen shiga rai ne da
mu ato, dik in da muka je sai mun ratsa zuciyar mutane, bare ma mu arewacin
Najeriya ai daban muke.

Har sai da ta kurewa ganinsa sannan ya ja dogon numfashi tare da wucewa ya nufi
elvator domin ya yi ƙasa ya koma part ɗinsa, mammie na can tana jiransa ya dawo ta
zazzage mashi jajjagen masifar da ta jajjaga ta ajiye mashi. Shi kuwa yana nan
zuciyarsa ta shiga wani yanayi. Babbar magana, muje zuwa my people's, ba'a fara
komai ba, RAWANIN ZALINCI zai baku mamaki gaba kaɗan, fatana dai Allah ya ara mana
lokaci!!.

Sai da Khadijah ta shiga almost part uku a cikin amma bata iya gane part ɗin
momma ba, daga karshe ta lallaɓa ta koma part na mama ta yi kwanciyarta zuciyarta
cike da tunanin ina Zee? Bata damu da tunanin ina babynta kamar yadda ta damu da
tunanin ina Zee ba?. Dan ta san halin yar uwar tata da shegen zuciya bata ɗaukar
raini.

A ɓangaren guda kuwa, mammie dai ta yi jigilar aikin gasawa Sarina jiki, Sarina
anji jiki, dan ma Allah ya taimaketa a ba kan tsini ta isko Smart ba, ai da bata
rage ba, amma dik da haka ta jibgu ba karya, jiki dik ya yi ruɗu ruɗu ya kumbura,
ta sha ruwan zafi kam ba karya.

Idan muka waiwaya gefe guda kuma, a can hospital ɗin Kingdom ɗin, a lokacin da King
ya saki Hoorain, kwance yake a saman bed na hospital ɗin, sai da ya yi good two
days kafin ya dawo cikin hankalinsa, amma fa har lokacin baya iya tafiya, tin da
yake a rayuwarsa ba'a taɓa yi mashi irin wannan horo mai bala'in tsananin ba,
wannan ɗakin duhu wlh karshen azaba ne, amma kuma da yake ba bawa yake sanyawa
kansa so ba, dik wannan wahala da suka bashi wlh soyayyar Auta ninkuwa ya yi a
ransa, sai ya ji ma tamkar buɗe kirjinsa suka yi suka zuba mashi santa na wannan
azaba da suka yi mashi.
A ranar da ya farfaɗo ma da sunanta ya farfaɗo a bakinsa, sai dai yana buɗe
idanunsa da Abbonsa ya fara yin tozali, ya ji matuƙar daɗin ganin mahaifin nasa,
sai dai kuma da buɗar bakinsa ya ce. "Abbo Hoonaira bata sake zuwa wajena ba ne?".
(Yana tinanin tin da ta je wajensa a ɗakin duhu kenan bata sake zuwa ba, dan tun
wannan rana da ta je wajen nasa King ya zo ya ɗauketa, zafin ɗaukarta da aka yi
yasa zuciyarsa ta tsananta ciwo, dalilin suman da ya yi kenan sai yau ya farfaɗo.)

Ɗan girgiza kai Abbo ya yi irin alamar tausayawa ɗan nasa, shi ma ya rame sosai,
dama ga tsufa, ga ciwo, ya sha wahala dattijon arziki, zuciyarsa ta rauta a kan
Hoorain da Auta sosai, sai yake jin kamar ba zai iya sanya karfi wajen rabasu ba,
ga shi kuma ya yi wa King alkawarin zai rabasu, dama a tinaninsa karfi zai sakawa
Hoorain ɗin, zai ce mashi ya zaɓa ko shi ko Auta, kowa dai yasan dole Abbonsa zai
zaɓa ko da hakan zai yi sanadiyar rayuwarsa tun da iyaye dai ba'a haɗasu da komai,
to commander ya ji jikinsa ya mutu a kan wannan mataki da yake san ɗauka.

"Abbo dan Allah ka amsa mun, Hoonaira bata zo bane?". Ya faɗa cikin
raunatacciyar murya. Jinjina mashi kai commander ya yi alamar e bata zo ba, ya kasa
iya furta word, dan ba shi da abin faɗe. Tafukan hannunsa Hoorain ya buɗe tare da
matsar da hannunsa kusa da hannun Abbon nasa, da yake commander yana zaune a saman
chair na masu jinyar majinyata. Hannun Abbon nasa ya riko cikin nasa. Cikin wata
iriyar wahalalliyar murya irin na wanda ya sha azaba, da kyar da kyar ya fara
magana cike da dakiya da jarumta, wlh ba dan assistant commander ne shi ba, ya saba
da wahala saboda irin horan da ya karɓa, Allah da ba zai iya ɗaukar wannan horo ba,
ba'a taɓa sanya mutum a ɗakin duhu ya wuce kwana uku ya fito a raye ba, kwana ɗaya
idan mutum ya yi aka fitar da shi sai ya sha jinya na satittika, kuma kafafunsa
basa iya takawa, amma shi almost week, ya fito kuma bai yi wani dogon jinya ba ya
farfaɗo, ba shakka yana da jarumta sosai, commander ya iya renon ɗan nasa, ya mayar
da shi zaki ɗaya tamkar da dubu.

"Abbo ina san Zunaira, ina santa fiye da yadda nike san rayuwata, a da kafin
in bayyana mata soyayyata a gareta ina jin kamar zan iya dannewa in mutu da santa,
amma tin daga ranar da na bayyana mata na gane cewa tabbas ba zan iya hakuri na
danne sonta har in koma ga Allah ba, please Abbo ka taimaka mun, dik wani hukunci
da zaku yi mun ku yi mun na yarda, amma dan Allah kada ku rabani da Zunaira, ba zan
iya jurar wannan zafin ba, gara mun zafin wuta a kan wannan zafi, ban taɓa neman
wani abin a wajenka na rasaba, shiyasa a kullum nike kara yin alfahari da kai, a
yanzu ma ga buƙatata na kawo maka dik da nasan kai ma baka da iko a kan hakan". Ya
kai karshen maganar wasu zafafan hawaye da suka cika mashi idanu ne suka zubo ta
gefe da gefen kunnensa saboda yana kwance ne. Idanunsa jajir kamar wuta, kirjinsa
na suya matiƙa, yana jin zafi tamkar an ɗaura shi a saman wuta, ya rasa a ina zai
sanya ransa ya ji daɗi.

Wani irin zabura commander ya yi, dan tin da yake da Hoorain bai taɓa ganin
hawayensa (tin da ya yi wayo kenan ba tin yana jariri ba) lallai girman san da
Hoorain yake yi wa Zunaira ya wuci misali, yau saboda santa ya yi kwallah?
Innalilahi wa inna ilahir rajiun, yanzu da wani idanu commander zai kallesa da
kudurinsa na rabasu?. Take commander ya ji ko mutuwa zai yi sai dai ya mutu amma ba
zai iya cewa Hoorain ya rabu da Zunaira ba, ba shi da wannan kwarin gwiwa,
Hasbunallahu wani'imal wakil, shi ne kalaman da commander yake ta mainaitawa a
ransa.

A dai'dai wannan gaɓa guyson ya kawo mashi waya domin su yi waya da Auta, ai saboda
farinciki Hoorain bai san lokacin da ya miƙe zaune tare da tsige drip dake manne a
hannunsa ba, murna a wajensa ba'a magana. Yana magana da ita zafafan hawaye suna
bin ƙuncinsa, wlh sai da guyson ya taya shi zubar da hawaye, ya tausaya masu
matuƙa, sai yake jin tamkar ya ɗaura masu aure kawai, sai dai bashi da damar yin
hakan, sai kawai ya hau tayasu da addu'a, ga azumi ya kawo kai, sai ya yanke
shawara a cikin zuciyarsa a kan zai sanar da King zai tafi saudiya ya sauke farali,
idan ya je ya yi alkawarin tun ranar da ya dira har ya dawo sunansu ne zai kasance
a bakinsa, addu'a ba dare ba rana zai yi masu, wannan hali da suke ciki dole a yi
saudiya da sunansu, in ba haka ba akwai matsala, shi yasan idan ba Allah ba babu
wanda ya isa ya canza rantsuwar King a kansu!!.

Bayan sun gama magana da ita ko in ce wancan baturiya ta kwace wayar ne ya bawa
guyson wayarsa tare da dawo da kallansa a kan Abbonsa. "Abbo ina wayata?". Ya faɗa
yana goge hawayensa. Allah Akbar, my people's soyayya idan ba'ayi dace ba wlh
musifa ce, yau assistant commander of dangerous warriors ne yake hawaye a kan mace?
Macen ma under 15 ba wata macen azo a gani ba, innalilahi akwai matsala fa.

Kasa jurar ganin halin da yake ciki guyson ya yi, dan ya ga kamar Hoorain fa ya
samu matsala, da gudu ya juya ya bar room ɗin, dan yana da raunin zuciya bawan
Allah. Shi kansa commander ji yake yi tamkar ya taya ɗan nasa hawaye, dan wani irin
tausayinsa ne ya kama shi matuƙa. Hannu kawai ya kai yana taya shi goge hawayen
yana faɗin. "Hoorain ya isa kukan nan haka ka ji? In Sha Allah Allah yana tare da
kai, idan gimbiya matarka ce babu wanda ya isa ya zama barazana ko shamaki a
tsakaninku, ina da yakinin Zunaira matarka ce, ka yi hakuri".

Rungume Abbon nasa ya yi, cikin zafin zuciya da raɗaɗi ya ce. "Abbo dole waɗan nan
hawaye ba zasu dakata daga zuba daga idanuna ba har sai na dakatar da na
Hoonairata, saboda a cikin zuciyata na ji kuka take yi a yanzu, dan Allah ka bani
wayata domin in kirata in dakatar da nata hawaye zaka ga nawa ma sun dakata". Out
of control yake maganar. A dai'dai lokacin da ya yi wannan magana tabbas kuka Auta
take yi, dan a lokacin tana bawa Smart labarin abin da yake a tsakaninsa da my
heronta. Soyayyar gaskiya daban take, ya so ta tin tana jaririya ai dole ya iya
fahimtar halin da take ciki.

Abbo ya fahimci Hoorain fa baya cikin hayyacinsa dan haka sai ya ce. "Ka yi
shiru wayarka tana hannunsu Ansar, yanzu zan sa a karɓo maka, ya isa haka ka
ji?..........".

Commander bai gama tufe baki ba sai ga sallamar Ansar and Anwar aminan kwarai sun
shigo, da ka gansu zaka fahimci suna cikin damuwa da tashin hankali, ba jimawa suka
bar hospital ɗin, wanka suka je yi, dama suna a tare da shi suna taya commander
jinya bayin Allan, su suka yi jinyar commander ɗin ma har ya warke, yanzu kuma suna
taya shi yin na Hoorain.

Hoorain yana ganinsu ya zabura yana faɗin su bashi wayarsa. Ansar ne ya ciro
wayar daga aljihunsa tare da na Auta da yake wajensa ya miƙa mashi yana faɗin. "Our
lion lafiya kuwa?".

Ai ina bai amsa masu ba, kunna wayarsa ya yi, jikinsa har yana ɓari ya shiga
contacts, sai kuma me? Ya rasa wani number zai kira, dan bashi da numberta na
Paris, wayarta ma ai gata a hannunsa. Da karfi ya ɗaga wayar tasa ya yi wurgi da
ita dan takaici, sai dai Ansar ya yi gaggawar capke wayar bata isa kasa ba, da
tarwatsewa zata yi, ransa ne ya kara jagulewa, zuciyarsa tana tafasa ya juya ya
kifa kansa da jikin bango yana wani irin huci mai fita da karfi karfi.

Gabaɗaya sai da suka yi matuƙar tausaya mashi, take jikinsa ya kara tsananta zafi
sosai, zazzaɓi ne ta rufesa sosai. Miƙewa tsaye daga kan chair commander ya yi tare
da tallabo ɗan nasa da kyau domin ya taushesa, ya san shi da ɗan banzar zuciya,
tsoronsa kada ya je ya haɗiyi zuciya dan ɓacin rai ya mutu su shiga uku, idan
Hoorain ya mutu ina zai sanya ransa?. A gaggauce su Ansar suka matsa kusa da shi
dan su taushi zuciyar zaki kada ta buga. Sai huci yake yi bai iya cewa komai, ya
dai datse idanunsa gam alamar baya san ganin kowa. A dai'dai wannan lokacin kuma
Smart yake rarrashin Auta yana yi mata alkawarin zata mallaki Hoorain while shi ma
commander alkawari ya shiga yi wa Hoorain a wannan lokaci a kan in dai yana raye to
da izunin Allah zai mallaki Zunaira, ya yi hakuri ya daure har ya samu lafiya. Sai
dai ina, Hoorain bai iya amsawa ba, bayan wannan huci babu wani abin da zaku ji
yana fita daga garesa.

A ɓangare guda kuwa, Chuchu dai ta lallaɓa ta gudu ta koma part ɗin Akka da zama,
tun safe take can, har dare taki komawa part ɗinta, da yake yau Jawad ya je office
to bai dawo da wuri ba, saboda aikin King na gina wasu makarantu dan marasa galihu,
so wannan aiki ta tsayar da shi, sai ana kiran mangariba ya shigo gida. A gaggauce
ya yi wanka ya wuce musque. Bai dawo ba sai da ya yi sallar isha'i a wajen, sannan
ya dawo gida.

Part na King ya fara zuwa, sai da suka gaisa suka ɗan yi hira kaɗan kafin ya wuce
wajen momma domin su gaisa, dan tun safe basu haɗu ba. Ita ma suka ɗan taɓa hira na
kamar ten minutes, sannan ya yi mata sallama ya fito, yasan yana da mara lafiya,
hankalinsa dik yana a kanta, dan ma dai ba laifi ta samu sauki saboda wadataccen
kulawa da ta samu daga wajensa.

Bedroom ɗinsa ya nufo yana tinanin yadda zai yi da ita yau, dan gaskiya batu na
Allah a matse yake, yana hannu, ita kuwa tsoronsa take ji, jiya ya yi ya yi da ita
ta bashi haɗin kai, amma ta murje idanu ta ce bata san wannan zance ba, ko taɓata
taki yarda ya yi, da ya taɓata zata saka mashi kuka, ya rasa me zai yi mata, ga shi
su kuma jarabarsu fa ba irin wadda za'a iya dannewa ta dannu bane, shiyasa kuka ga
suke yawan san shan cappuccino, dan yana ɗan sassauta masu, kun gano su ko?.

Ya yi mamakin ganin bata a cikin bedroom ɗin, ya kuma san bata part na momma,
dan da tana can momma zata ce mashi gata nan su wuce a tare. Toilet ya nufa cike da
tinanin ina ta tafi? Wanka ya yi ya fito ya shirya cikin sleeping dress ɗinsa masu
kyau. Waje ya fito sai tashin kamshi yake yi, kai tsaye ya nufi part na Akka, dan
yasan bata wajen mummynta, bata cika zuwa can ba, in bata wajen momma to tana wajen
Akka.

A yayin da yake nemanta shi kuma Jaish yana kwance saman bed ɗinsa barci ta
gagaresa, tin ranar da wannan abin ya shiga tsakaninsa da Mahnoor bai kara yarda
sun haɗa hanya da momma ba, tsabar rashin kunya da safe idan ya tashi barci kafin
ya tafi office sai ya kirata a waya su gaisa, haka da rana da yamma ma, wai shi
kunya yake ji, ita kuwa momma ta ɗauke Mahnoor daga part ɗinsa, ta kafa mashi
tarkon da sai ya kawo kansa, shiyasa ko ya kirata a waya dan su gaisa yana ɓuyan
mata bata wani damuwa, dan ta san halin kayanta, tasan maganinsa.

Mahnoor baiwar Allah sai da ta yi kwana guda a sume, sannan ta farfaɗo, ta sha
jinya da ruwan zafi, tun tana ihu idan za'a sakata ruwan zafi har ta saba, yanzu a
duniya babu wanda take tsoro biyun Jaish, kuma tana san sa fa, amma tsoronsa ya
lulluɓe san, idan ta ji sunansa ma gabanta faɗu yake yi, bata san jin dik wani abin
da ya dangancesa, zuciya kuma da bata da ƙashi, idan ta ɗan ji shiru bata ji
ɗuriarsa ko da suna call da momma bane dik sai ta bi ta damu kanta tana san jin ko
yana lafiya, ita dai idan yana lafiya shikenan hankalinta ya kwanta, wani ɓangare
na zuciyarta yana bala'in san kallan face ɗinsa, dan tana kewarsa sosai. Wani
ɓangare kuma tsoronsa!!.

So kwance yake yana ta juyi ya kasa yin barci, tinanin yadda ya ɗanɗani zumarta ne
kawai a cikin ƙwaƙwalwarsa, yau tun safe tula tulanta suke yi mashi yawo a cikin
idanunsa, ya rasa gane wani

Please Login or Register in order to submit comment