Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 71 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya iya rarrashi tun da yana rarrashin Auta, sai dai Autar kawai yake
yi wa ban da kowa, gara ma guyson idan yana ciwo yana bi ta kansa. Matsawa ya yi da
ita ya zauna a saman side bed, sannan ya rabata da jikinsa ya zaunar da ita a
gefen, in a low voice sosai ya ce. "Wait for me here bari in je in kawo maki
abincin". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye.

A miliyan ta riko hannunsa cikin nata, tana kuka sosai, cikin shessheƙa ta ce. "Ni
dai sai dai mu tafi a tare, ba zan iya zama ba, dan ina tsoron waɗan nan Tiger ɗin
naka".


Wai my people's bakwa tinanin meyasa Pretty bata maganar su Sweetie? Ko sau ɗaya
bata yi maganarsu ba, tamkar babu su a babin rayuwarta fa, kada ku manta kuma ita
da Sweetie suna bala'in san junansu over to over fa, basu da magana da ya wuci na
juna!.

Dan dole ba yadda ya iya ya riko hannunta a kan ta miƙe su tafi, sai dai kuma ina,
make kafaɗa ta yi alamar ba hakan take so ba, da kallon mamaki ya bita yana jiran
jin karin bayani. "Ni dai sai dai ka goyeni". Ta faɗa tana kara fashe mashi da
kuka. Shin kun tuna cewa dik in da zasu je goyonta Kamran yake yi saboda shegen
tsoronta? Ko kun manta?. To ita babu ruwanta da banbancin dake tsakanin Kamran and
Smart, ita dai a goyeta, dik su suka sani, waye ya lura jinin sarauta ya fi karfi a
jikin Pretty ba Sweetie ba? Sweetie tana da saukin hali, ita kuwa Pretty sai shirin
Allah, idan ta yi magana ba canzawa, ga shegen shariya da izza, wai a haka ma fa
bata san kanta ba, idan ta waye ta girma me kuke tinanin zai faru? Tab ina ga su
Jaish sai sun sarara mata a izza da isa. Dik yadda aka yi babansu Sweetie hegen
kwaro ne.... 😅

Shiru Smart ya yi yama rasa abin faɗe, wai ya goyata, to shi ko da yake kaunar
Auta sau biyu ya taɓa goyonta a bayansa. Ga idanun yaran da shegen kaifi, komai
zafin da ka ɗebo da ka haɗa idanu da su sai ka ji sun yi maka wani irin gwarjini ka
kasa amayar da abin da ka ɗebo masu, shiyasa Sweetie take sha a hannun Black Tiger
take cin galaba a kansa, da zarar sun haɗa ido sai ya nemi dik wata zafansa ya
rasa, abin har yana bashi mamaki, shi ma dai Smart mamaki abin ya fara bashi, sai
dai ko kaɗan bai kawowa ransa cewa suna da wata baiwa bace, kawai yana ganin kamar
dan yarinya ce, and kuma ta taimaki Auta, shiyasa yake raga mata.
Kuka ta sa mashi tare da zama a ƙasa zata fara birgima, yadda dai take yi wa
Kamran. Ai bashi da zaɓin da ya wuce dole ya goyata, dan kuwa ya ƙasa ɗaukar zafi a
kanta, sai dai har zai goyata kuma sai ya fasa, zama ya yi a side bed ɗinsa tare da
ɗauko laptop ɗinsa, umarni ya bawa mai aikin nasa a kan ya kawowa wannan kararar
yarinyar abin da zata ci ya huta da jarabarta. Yana gama aikawa ya juya zai cigaba
da aikinsa, sai kuma ya gagara iya shareta ya barta zaune a kasan, abu kamar ba
lafiya ba, dik zafinsa dai ya gagara ɗauka a kanta, kuma ya gagara iya shareta.

To menene dalili kenan?.

"Zo ki zauna a saman bed bari a kawo maki abincin". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a
kanta. Gabaɗaya sai ya ji tsikar jikinsa tana tashi, sai ya ji wani irin yanayi ya
sauka a jikinsa. Gata kamar wata ƴar tsana a gabansa, haka ta miƙe tana turo baki
ta koma kusa da shi ta zauna.
Cigaba da aikinsa ya yi yana jin wani irin a zuciyarsa, ya kuma kasa
gane me yake ji. Yana tsaka da aiki yana tinane tinane sai ji ya yi ta kwanto saman
damatsan hannunsa ta gefen wide chest ɗinsa. Sai da kirjinsa ta amsa, amma ya daure
ya cigaba da aikinsa, kun san mutuniyar da shegen san jiki dama, ta kwanta a jikin
nasa ma bai yi mata ba sai da ta sa hannunta a jikin nasa tana yawo da shi tana
tattaɓa mashi jiki, kamar wadda ta tafi duniyar tinani, sai shafe mashi jiki take
yi tana turo baki, yadda take yi wa Kamran, abin a jininta yake.
Gabaɗaya sai jin tsikar jikinsa na kara mimmikewa yake yi, yana ƙoƙarin
rasa natsuwarsa. Dannewa ya yi ya cigaba da aikinsa, kamar daga sama ya ji saukar
hannunta a saman flat tummynsa tana murje ƴan yatsunta a wajen. Wani irin dogon
numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, Auta tana yawan yi mashi dik irin
kwanciyar da ta ga dama a jikinsa, amma bai taɓa jin wani abin ba sai a kan wannan
ƴar rigimar. Ita kuwa cigaba da shafe jikin nasa ta yi tana yawo da hannunta ta
ko'ina. Smart dai ya daure iya daurewarsa, amma abin tana neman ta ci tira.
_____________ A wani irin miliyan ya kaiwa hannunta capka, dan ta yi ƙasa da shi
tana ƙoƙarin taɓa mashi duniyar mercurynsa. Ai a miliyan ya capki ƴan hannayen
nata. Yana capketa ta yi gaggawar ɗago da idanunta a kansa, while shi ma ya ɗan
juyo da kallansa a kanta. Suna haɗa idanu ya ji gabaɗaya ya nemi abin faɗe ya rasa,
yarinya kamar wata aljana, dik sai ya ji kamar an shafe mashi komai a brain ɗinsa,
bai ma san lokacin da ya saki hannun nata ba, ya mace da kallonta bai ji time ɗin
da ta ce mashi. "Meyasa ka rike mun hannuna ba"..... Kai kun ji mun iskanci wajen
Pretty, ita bata ji me take yi mashi ba, tambayar dalilin rike mata hannu ma take
yi!!.

Malam Smart dai da alama ya afka duniyar mercury abinsa, dan sam baya jin abin da
take faɗe, tana magana tana turo mashi baki, hakan ba karamin tafiya da shi yake
kara yi ba. Shigowar mai aikin nasa ne ya katsesu, a hanzarce Smart ya kawar da
kallonsa daga kanta tare da cigaba da aikinsa..... A saman table ya shirya masu
abinci, a tinaninsa har da Smart ɗin zai ci abincin, sai ya kawo masu wadatacce. Ai
tin mai aikin bai kammala gere abincin ba ta yi gaggawar barin jikin Smart ta nufi
table ɗin, ba wasa da abinci. Da ido Smart ya bita da kallo yana mamakin me yake
damunsa a kan yarinyar nan? Shi idan ya haɗa idanu da ita ma idanun nata suna sa ya
ji faɗuwar gaba. Ita kuwa abincinta ta je ta fara ci ba tare da wata damuwa ba,
kuma bata sake bi ta kansa ba abinta, ta barshi da tinanin wacece ita?.

A lokacin ita kuwa Auta ta gama shirin barcinta, ta haye gado tana ta
mamakin ina Pretty ta shiga ita da ta ce ba zata sake fita waje ba? Yanzu kuma me
ya fitar da ita?. Wayarta ta jawo domin ta fara aikin da suka saba. Number my hero
ta fara kira, sai dai wayar ta yi ringing har ta katse ba a ɗaga ba, hakan yasa ta
sake kira, nan ma shiru, sai a karo na uku ne aka ɗaga. Ana picking ta sanya mashi
kuka shagwaɓa haɗe da tuhumarsa meyasa bai ɗauki kiranta tun call na farko ba.

On the other side commander ya amsa mata da. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe, barci
jarumin naki yake yi"........ Subhanallah tamkar Auta zata natse a kasa saboda wani
irin kunya, bata yi zatan commander bane ta hau zuba mashi sakalci da shagwaɓa.
Kasa ta yi da kai tamkar tana a gabansa, har da sa hannu ta rufe idanunta kafin
dai'dai ta natsuwarta sanna ta amsa mashi da. "Ina wuni Abbo"....... Ajiyar zuciya
ya sauke idanunsa a kan ɗan nasa dake ta sharara barci ya amsa mata da. "Lafiya lou
gimbiya, ya kike ya yayan naki?"..... Alhdulillah ta amsa mashi, cike da yarinta ta
yi gaggawar katse kiran tana kwanciya, cikin pillow ta tura kanta tana murmushi ita
kaɗai, kuruciya da daɗi, a maimakon ta tsaya su yi gaisuwa mai kyau a matsayinsa na
sirikinta, sai ta katse kiran tana murmushi, yanzu Abbo ya zama wani abin kuma a
wajenta.

So take ta turawa Hoorain ɗin sakon dik time da ya tashi ya kirata, amma tana
tsoron kada Abbo ya karanta zata ji kunya, sai kawai ta fasa turawa ta kwanta tana
tinanin rayuwa. Wayar tata ce ta fara ringing alamar shigowar kira. A gaggauce ta
duba number, dan a tinaninta jarumin nata ne ya tashi. Sai dai kash, new number ta
gani. Kamar ba zata ɗaga ba, sai ta tina su Yah Omaid zasu iya kiranta, ga su Yah
Jawad, Yah Rizwan dan haka she have to take a new number.

Picking ta yi tare da kara wayar a kunnenta tana yin sallama cikin natsuwa. Other
side cikin natsuwa ya amsa mata da. "My wife kin manta da ni ko?"...... Siririn
murmushi ta saki kafin ta ce. "Yah Abdussalam ni na isa in mance da kai ne? Kana
rai'na, kawai dai bana cikin natsuwa ne yasa ban kiraku ba"....... Sanyayyar ajiyar
zuciya ya sauke wanda sai da ta jiyo shi.
"To na ji daɗi tin da ba'a manta da ni ba, fatan wife ɗina tana nan
lafiya?".... Da alhamdulillah ta amsa mashi tana jin wani irin fargaba yana ratsa
mata zuciya, dan tana jin kamar call ɗinsa ba alkhairi bane a gareta, abokin wasan
ta ne tin da ɗan kawunta ne sun saba wasa sosai, sai dai yau tana jin wani irin da
take magana da shi.

"Wife kin kusa tabbata da gaske a matsayin wife ɗin nawa". Ya faɗa cike da
murnan hakan. Ita kuwa zaro idanu waje ta yi a hanzarce ta ce. "Yah Abdussalam me
kake nufi?"....... Ya ɗan yi mamakin jin tambayar tata, sai dai kuma ya yi tinanin
ko bata san shirin da ake yi bane, dan haka sai ya ce. "Daddy bai sanar dake cewa
ya bani ke bane? Kinga ya tabbata da gaske zaki zama wife na, abin da na jima ina
mafarki kenan, burina ya kusa cika!". Cike da fara'a sosai a saman face ɗinsa ya yi
maganar, yana kwance a saman bed ɗin kakansa the most powerful King, wato
mahaifinsu momma King Badeen kenan, ya tada kai da laps na kakan nasa ne yake
wannan surutu, sai shafa arab hairnsa King Badeen yake yi yana siririn murmushi
irin nasu na manya, da alama shi ma ya ji daɗin wannan haɗi da za'ayi, dan sai
albarka yake ta zubawa abin.,........ Tab magana ya je wajen manya, akwai matsala
kuwa, dan ni dai na duba banga hanyar ruguje wannan magana ba, dan King ba zai iya
kallan idan sirirkinsa King Badeen ya ce ya fasa bawa Abdussalam na gida Zunaira ya
ɗauka ya baiwa bare ba, akwai case kuwa, shin Smart zai yi nasara kuwa? Shirin su
momma zai yi aiki kuwa? King zai yi azumin kaffarar nan kuwa? Rantsuwa dai ya riga
da ya yi, uhm Allah sarki assistant commander Hoorain sorry, alkalamina bai yi maka
adalci ba ko? Ba laifina bane, laifin King ne!!.

Idanunta ne suma ciko da zafafan kwallah sosai, cikin natsuwa ta ce. "Daddy bai
faɗa mun ba Yah Abdussalam". Da kyar ta iya ƙarisa kai karshen maganar....... "Ayya
ina ga wani abin ne ya sha gabansa, amma da zai faɗa maki, kila shirye shiryen da
suke yi ne ya ɗauke hankalinsa......".

A gaggauce ta tari numfashinsa da cewa. "Shirye shiryen me suke yi kuma?". Ta yi
tambayar cike da fargabar amsar da zai bata, kunnuwanta ba zasu iya ɗaukar cewa
shirye shiryen bikinsu ake yi ba, sai dai kuwa kash, abin da take gudunwa bata
tsira ba, dan kuwa da buɗan bakin Abdussalam cike da murna ya amsa mata da. "Shirye
shiryen bikin mu mana, baki san nan da 3 days za'a ɗaura auren ba ko? Wlh na matsu
wannan rana ta zo in mallakeki, sai naga lokaci ma ya dai'na gudu, baya sauri a
yanzu..........". Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon wani irin ihu da ta
zunduma tana faɗin. "No dad no, please don't do that to me!!".

Da farko ta yi zatan zata iya jurewa har su kammala waya da Abdussalam ba tare da
ta nuna mashi bata san shi ba tun da Smart ya ce mata ta kwantar da hankalinta in
dai yana raye sai ta auri zaɓin ranta, to amma da ta ji saura 3 days aurensu sai ta
karaya, tuni ta firgice ta fita hayyacinta, ta haukace. Wurgi da wayar ta yi ta
diro kasan bed ɗin, sai hello Abdussalam yake faɗi, amma ina bai san ta wurgar da
wayar ta yanka waje da gudu tana kuka ba.

Bata zame ko'ina ba sai bedroom na Smart, a lokacin yana aikinsa ita kuma Pretty
tana cin abinci. Babu ko sallama a haukace ta afka masu cikin ɗakin. Da gudu ta
tafi ta faɗa saman jikinsa a kan bed ɗin tana sakin kuka mai sautin gaske. Cike da
mamaki yake binta da kallo, dan shi ɗin mai natsuwa ne sosai, so komai nasa a natse
yake yi, dan haka bai wani tashi hankalinsa ba, ya bita da kallo na ƴan mintunan da
basu gaza biyu ba. Sai da ya ga kukan nata ba mai karau bane, sannan yasa hannu ya
ɗagota tare da ture laptop ɗinsa gefe guda. Daidai lokacin ita ma Pretty ta taso da
gudu ta nufo su, dan dik wannan shirmen nata tana jin kaunar Auta a ranta.

Ɗagota ya yi tare da raba jikinsu, sai ya zamana suna fuskantar juna, cikin
natsuwa ya ce. "Is okey my sweetheart, yi shiru na ji meyake faruwa kin ji ko?".
Ina kai ƙasa yin shirun nan ta yi, tamkar ranta zai fita haka take kuka, da kyar
voice ɗinta yake iya fita ta faɗa mashi abin da yake faruwa. Lallashinta ya hau yi
tare da kara tina mata alkawarin da ya ɗauka mata, ba makawa in dai yana raye
Hoorain zata aura ba kowa ba, dan haka ta kwantar da hankalinta, daga karshe ya
rufe da cewa zai karɓi wayar hannunta, ba zai sake bari ta yi magana da kowa ba,
dan kada su rinƙa kiranta suna faɗa mata wasu maganganu har su ɗaga mata hankali.

So mugun wasa, cikin sauri ta tari numfashinsa da cewa. "Yah Omerish idan ka karɓi
wayata da wani waya zan yi magana da Hoorain?"....... Ya fahimci sweetheart ɗin nan
nasa ta yi nisa, ita dai Hoorain kawai, dan haka sai ya ce mata akwai wayarsa ai,
dik time da take so ta zo ta ɗauki nasa ta kira Hoorain ɗin, amma bayan Hoorain bai
yarda ta kira kowa ba........ "Yah Omerish har da Yah Omar kada na kira?". Cike da
fargabar kada ya hanata waya da guyson ta yi tambayar. Ai kuwa kai ya jinjina mata,
harda Guyson ɗin kenan, abin ya sosa ranta sosai, dan guyson wani ɓangare na bugun
numfashinta ne, amma ya zata yi to? Dole ta bi umarnin yayan nata idan tana san
zaman lafiyarta.

Miƙewa ya yi ya ɗauki wayarsa ya nufi waje, dan ya je ya yi waya da King, a nan ya
barota ita da Pretty yana jin zuciyarsa babu daɗi, dan wlh ya tsani abin da zai
ɓata ran Zunaira.............. Me kuke tinanin zai cewa King, kuna ganin wannan
al'amari zata canza kuwa? Uhm muje zuwa. Kwanciya ta yi a saman bed ɗin nasa tare
da tada kai da lap ɗin Pretty tana tinanin me rayuwa zai sake zuwan mata da shi,
ita kuma Pretty ta hau shafa arab hairnta!!.


Shin kun san meyasa gabaɗaya litattafaina stars ɗina mata basa taɓa haura 13 to 14
years suke aurensu? Kun san dalilina na yin hakan? Saboda a kullum burina shi ne na
yi koyi da manzan Allah (SAW) kuma kuma na kwaɗaita maku yin koyi da shi. Manzan
Allah ya ce ku aurar da ƴaƴanku mata tun suna ƙanana, su girma a ɗakin mazajensu,
bature masu jajayen kunnuwa kuma ya ce maku aurar da yara ƙanana tauye masu
hakkinsu ne, wai a barsu su girma su san ƴancin kansu, uhm Allah mai iko, akwai
wanda ya kai manzan Allah sanin hakkin ɗan adam ne? Akwai wani malami da ya isa ya
gwada mashi sani ne? Dik duniya da kuke gani da dik wani cigaba da ake samu wlh
kwaikwayo ne daga abubuwan da Allah ya halitta turawa da masu kimiya suke yi, zan
kuma tabbatar maku da haka, so dik duniya babu wanda ya kai manzan Allah ilimi, dan
kuwa masu tinƙaho da ilimin ma wato masu jajayen kunnuwa daga iliminsa da ya koyar
suke satar nasu fasahar. Sannan kuma halittun Allah suke kwaikwayo su bunƙasa shi,
to shi kuma manzon Allah Allah da kansa ya koyar da shi, kenan karatun waya fi a
nan? Dan haka shi ya fi sanin hakki mutum fiye da kowa, amma a haka ya ce ku aurar
da yaranku tun suna ƙanana, su kuma masu jajayen kunnuwa sun hure maku kunne sun
kwaɗaita maku ku bar yarinya ta yi karatu ta girma ta san ƴancin kai, Uhm aikuwa
wanda bai ji bari ba ya ji oh oh, zaku ga sanin ƴancin kai idan ta zo tana gogayyar
kafaɗa dake, kina ta bari tana faɗa maki tasan ƴancin kanta tasan me ya dace da
ita, sai ma ta tuna ta fiki sanin abin da yakamata, ga shi nan ai kuma muna gani,
yarinya ta nuna ta fi uwarta sanin abin da ya dace ta yi. Ba ace kada a bawa mata
ilimi ba, dan ilimin mace ilimin al'umma ne, amma ta samu ilimin a ɗakin mijinta,
idan anyi aure ma ai ana karatu. Babban illame garemu kin abin da manzan Allah ya
faɗa, shiyasa ga shi nan zinace zinace dik ya ishi al'umma, lesbian da sauransu,
ƴaƴa sun girma suna son aure kun ce sai sun yi karatu, da zarar yarinya ta fara
period dik wasu kofofi na sha'awarta yake buɗewa, a wannan lokaci aure kawai take
so, a nan ne idan baki yi hankali ruɗin samari haɗe da kawaye ya jefata ga halaka,
ni dai ina mai baku shawara, a kullum ku kasance masu amfani da maganar MANZAN
ALLAH, babu ruwanku da abin da duniya zata ce, kun gannin nan zancen duniya bata
gabana, a ko'ina faɗar Allah da manzonsa nike ƙoƙarin bi. To ni dai fatana kullun
na rinƙa kwaɗaita maku koyi da fiyayyen halitta, dikkan rubutuna ina yinsa besa
koyarwar manzon Allah, kuma dik idan kuka natsu kuka duba darusa ne a gareku. Allah
ya bamu ikon koyi da fiyayyen halitta. And lastly har ya gama rubuta littafi a
rayuwata star ɗita ba zata taɓa haura 15 years ba In Sha Allah, na baku satar amsar
yadda zakuna gane Stars mata na littafaina, ba zasu taɓa haura 15 years
ba........😅

STORY🔥♥️
🔥🔥KINGDOM OF JUSTICE🔥🔥

Wato RAWANIN ADALCI kenan, shi ne sunan masarautar nan na Queen Zarina, wasu suna
kiranta da kingdom of justice, sai dai kuma sunane saɓanin aiki, dan kuwa babu koda
kwayar zarra na adalci a cikin wannan masarauta, mulki suke yi mai cike da zalinci
wato mulkin kama karya, babu adalci a tafiyarsu, babu tausayawa bare jin ƙai. To
meyasa kenan sunan masarautar ta kasance na adalci?. Muje zuwa zaku ji tarihi a nan
zaku fahimci daga ina aka samo matsala ta sauyawar abubuwa.

Fadar Sarauniya wato Qeen Zarina, ita ce zuciyar masarautar zaluncin. Babban
katafaren gini ne da ya kai girman wata gari gabaɗaya.

Ga wata katanga dake ɗauke da gicciye-gicciyen bayi da aka kashe don tsoratar da
mutane birnin su yi biyayya dan dolensu, in ba haka ba su bi sahun waɗan da aka
gicciye suma. Ƙofofin fadar guda uku ne kuma gabaɗayansu suna da ƙaho na zinariya,
dik wanda baa bashi izinin shiga ba ya keta ƙofar, fatar jikinsa za ta ƙone nan
take, tsabar karfin tsafin Queen Zarina.

Gidajen bayi a cikin kingdom ɗin suna a cikin duhu, babu haske, babu kwanciyar
hankali, ana ɗaure su da sarƙoƙi, ana azabtar da su idan suka yi ba daidai ba. Ana
azabtar da mutanen da suka yi laifi a wurin, wasu ana yanka su, wasu ana narkar da
fatarsu da wani abin sihiri nata dan nuna barazana ga ƴan baya tare da tilasta masu
dole su yi biyayya ko kuma suma su riski irin wannan tsastsauran hukuncin. Qeen
Zarina tana da wani ɗakin sirri da ke ƙasa (underground) wanda ke cike da abubuwan
al’ajabi, kamar wurin bautar da jini dan ƙarfafa mulkinta da sauransu.

Suna da ƙasashe da yawa da suka mamaye, ana bautar da mutanen waɗancan ƙasashe a
matsayin bayi. Dik wata ƙasa da ta ƙi biyayya, suna kisan jama'arta gabaɗaya ko
kuma su tilasta wa yara da matan su zama bayin fadarta masu yi mata hidima. Queen
Zarina ita ce uwar zalunci, tana amfani da doka mai tsauri dan riƙe ƙarfinta. Ba
wanda zai iya yi mata ƙarya, domin tana da sihirai da sirri mafi ƙarfi da zata iya
gano karya suke yi mata, dan haka dole yake tilastawa mutanenta faɗa mata gaskiya
koda sun san kashesu zata yi.

Tana da Jagororin mabiyan sihirinta. Wata macece mai suna bokanya Ruhgara, da ke
kula da manyan bokaye da matsafa da ke fadar Queen Zarina. Su ke tabbatar da cewa
dik wanda aka kama yana tunanin cin amana, sai a hallaka shi kafin ya yi wani abin.

Ana kiran shugaban warriors ɗinsu da black scorpion, wato bakin kunama mai harbi
ɗaya sai lahira. Warriors ɗinta ba mutane ne na yau da kullum kamar yadda kuka sani
ba, a'a ita ta ƙunshi mayaƙa marasa tausayin da aka horar tun suna yara don su zama
na musamman, gabaɗa warriors ɗin renon black scorpion ne.

Mai tsaron dukiyarta. Wanda ke kula da taskar zinariya, azurfa, da kayan sihiri da
aka kwace daga ƙasashe da suka mamaye, wani bakin mutum ne, mai hudun launin fata
sosai, ga shi shirgege gwanin ban tsoro, mummunar gaske, fuska babu alamar annuri
ko ɗigo, in ya yi maka duka ɗaya sai mutuwa, yana da faɗi sosai.
Sannan warriors ɗinta mutane ne da suka haɗa da, mayaƙan Jini wato mutanen da
aka yi wa wani sihiri mai karfin gaske, suna jin karfi da lafiya ta yadda suke
ganin babu wani bala'i da zai iya shafan su, kuma idan aka sare su, jinsu na iya
dawowa su cigaba da yaƙi, wato saboda da tsafi suke amfani ko an saresu suna iya
tashi su koma normal yadda suke su cigaba da yaƙi, waɗan nan mayaƙa ne masu haɗari
wanda har yanzu tana kan sihircesu ne, bata fara amfani da su ba, sune mayaƙanta na
rukunin farko a ɓangaren haɗari. Wlh ba dan kingdom of power masarauta ce ta Allah
sun riki addini ba da ba zasu taɓa sha a hannun wannan azzalumar mata ba!
Makircinta ya zarce yadda kuke tinani!!.
Akwai masu take masu baya, wato su kuma mutane ne da aka horar tun suna ƙanana dan
su zama tamkar dawakai a fagen karfi dik dan su zama masu saurin kashe mutane babu
imani babu tausayi. Maza da mata da ke ɓoye suna satar sirrin wasu ƙasashe domin
tabbatar da babu wanda zai iya yin juyin mulki, shiyasa kuka ga har cikin kingdom
of power suna da ƴan leken asirinsu waɗan da suke binciko masu menene ke wakana a
manyan masarautu.

Magana ta gaskiya babu wanda ya isa ya yi masu tawaye. Mutane basu da ƴanci. Dik
wanda aka samu da yunkurin yin tawaye, daga shi har danginsa dikka sai an hallaka
su. Basa son wata daula ta yi ƙarfi ko kwatansu. Dik wata ƙasa da take kokarin
girma ko samun ƴanci, warriors na masarauta suna zuwa su mamayesu su kuma kwace
komai. Yadda kuka san Queen Zarina renon BLACK TIGER ce, wlh zalincinsu kusan ɗaya,
sai dai Black Tiger ya fita haɗari ne da karfin tsafi.

Sannan tana sihirce mutane. Idan aka samu wani yana tunanin cin amana, mayakan
sihiri suna iya hango hakan kafin ma mutum ya furta shi, sai ta sa a sihirce sa, a
mayar da shi wani gunki ko kare ko dai wata ƙasƙantacciyar dabba a ajiye shi a
kofar gate ɗin farko na shigowa masarautar dan ya zama ya kare a kaskance kuma ya
zama izina ga masu tasowa. Wanna ba dalilin yasa ƴan birnin suke yi mata biyayyar
dole!.

Masarautar tana da zinariya fiye da kowacce ƙasa except birnin BLACK WORLD. Sannan
a tsarin Queen Zarina babu wata ƙasa da za ta iya yin ciniki ko kasuwanci ba tare
da izinin ta ba, muna magana a kan kasashen da ta mamaye, kasuwancin dik waɗan da
suke kewaye da ita a karkashin sarrafawarta suke yi. Bayin basu da wata ƙima da
daraja, a haka kuma wai sun fi talakawar da ake mulka kima, idan ka zama bawa a
wannan kingdom ɗin, to ka san rayuwar ka ba taka bace. Wannan kingdom da fadar
Sarauniya tana da ƙarfi fiye da sauran ƙasashe. Za su iya mamaye kowace ƙasa, kuma
babu mai iya taka masu birki sai KING ZUHAIR, wato KINGDOM OF POWER sune kawai suke
zama babbar barazana ga ZARINA! Black Tiger kam bai ma san da wanzuwan Zarina a
doran duniya ba!.

Doka mai tsauri, dik wanda yayi gaban kansa ko ya yi magana kan zalunci, ana
hukunta shi da azaba mai tsanani. Masu iko sunfi kowa

Please Login or Register in order to submit comment