Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya
ƙoƙarinta wajen motsa ɗan hannun.

Tana motsa shi ma wanna wuƙa ya motsa, dik in da hasken hannun nata ya bi wanna
wuƙa ma yana bi, a hankali ta fara matsar da hannunta daga wuyarta, hakan yasa shi
ma wukar ya matsa daga saitin wuyar tata da ya yi.

Abin al'ajabi ya bata matuƙa, sai kuma kamar wata zararriya ta saki murmushi wanda
sai da yasa dimple ɗinta bayyana, ko me abin murmushi a wajen?.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin tana da hanyar cetan kanta, fara ƙoƙarin tabbatarwa da
kanta hakan ta yi ta hanyar juya hannunta ta in da takeso.
Dik yadda ta juya wukarma sai ya juya ta nan, wani irin dariya ta fashe da shi
kamar wata zararriya.

Yi take yi babu kakkautawa idanunta a kan wukar.

========================💔

Lokacin guda kuma ta tsayar da dariyar tata cak, kome ta tuna? Sai kuma idanunta
suka ciko da kwallah, a hankali ta furta.

"Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil, ya
Allah.........."

Bata kai karshen maganar da take son amayarwa ba kenan taga wanna wuƙa ya faɗi a
ƙasa, faɗuwarsa ke da wuya ya haifar da wani irin sauti mai ban tsoro, a take
guguwar dake ɗakin ta kara karfafa kamar an watsawa aljanu ruwan addu'a yana
konasu.

Ba ƙaramin kara razana ta yi ba, da karfi ta furta. "Wayyo Allahna ka kawo mun
ɗauki......"

Ai bata gama rufe bakinta ba kofar ɗakin ya ɓalle ya buɗe kansa da kansa. A miliyan
ɗari ta kwasa ta nufi waje, ta kasa gane cewa sunan Allah da ta ambata a wajen ya
rikita dik wani tsafi dake waje, shiyasa take jin wanna guguwa ta kara karfafa wai
dan su kare kansu daga kalamanta shi ne suka kara karfin iko.

Kai tsaye parlourn ƙasa ta nufo tana ihu, bata tsaya electric stair case ɗin
ya yi kasa da ita ba ma, da kanta ta tattake shi ta yi ƙasa.

A wanna lokaci ta kasa iya sake ambatar sunan Allah, abin ku da shaiɗan da kuma
shirka.

Bayanta Black Tiger ya biyo cikin wanna iska, dan ransa ta kara bakanta na sunan
Allah da ta kira ta jijjiga mashi hankulan ruhohin tsafinsa. Ya sha alwashin yau
zata gane kurenta.

Wanna iska ne yasa gabaɗaya kofofi da windows ɗin parlourn kasa suka rufe kansu,
fara ƙoƙarin kamata Black Tiger ya yi, ihu take kurmawa tana neman hanyar tsira.

A wannan lokacin ne ya riƙiɗa ya zama mutum, da ainahin face ɗinsa ya bayyana, yana
sanye da pj a jikinsa.
Like wow, kamar wani kafani, kaman ba mutum ba, ga shi ya juya idanunsa izuwa na
magic, sai ya kara riƙiɗewa kamar ba mutum ba, zallar madarar kyau.

Cak ta dakata da neman hanya da take yi, bata yi zaton shi bane da ba zata gudu
ba a cewarta, ita da take son ganin face ɗinsa daman! Ai da tsayawa zata yi kome
zai faru ya faru.

His first time kasakcewarsa a cikin wanna parlon, bayan ɗakin Ronnie da yake kai
ziyara ta hanyar magic bai taɓa fita ko ina ba, yau karo na farko Sweetie ta sanya
shi fitowa.

Ita ce mutun ta farko da ta fara ganin face ɗinsa bayan babansa, and ita ce mutun
ta farko da ta fara sanya shi fitowa har parlon ƙasa, lallai ya tabbata idan bai
tsaya ya bada himma ba zata iya cin nasara fa a kansada gaske.

Zuba mashi idanu ta yi tana kallonsa, face ɗinsa babu alamar mutumci ko
kaɗan, zallar mugunta ce a samanta, in ka gansa sai ka razana, amma yarinyar nan
Sweetie ko a jikinta, bata ji tsoron ganin cikin idonsa ba.

Wani irin ihu mai sauti na ruhohin tsafinsa ne ya fara karaɗe ko'ina a cikin
parlon, hakan ya ja dikkansu biyu suka ɗan yi shock, abin ya bashi mamaki jin wanna
ihu.

Cigaba da kura mashi kallo Sweetie ta yi tana mamakin hali irin nasa, ga shi
kyakkyawa amma kyan ɗan maciji ne, ɗan kunama!. Shi kuma gabaɗaya hankalinsa ya
koma a kan sautikan da yake ji wanda ita Sweetie bata iya jiyo hakan, da yake ta
ɓangaren tsafinsa ne, shi kaɗai yake ji.

Can kamar saukar aradu haka ya tsinkayo wata iriyar murya mai tashin kai, mai kuma
karfin gaske cikin guguwa da kuwa, tamkar muryan kartin maza ya ce.

"Autan duniyoyi ya bayyana, Autan ruhohi ya bayyana".
Shi ne abin da yake fita daga wanna sauti.

Jin haka yasa ya tuna wasiyar babansa na karshe a idan yake ce mashi.

"Wasiyata a gareka shi ne, kada ka yarda ya fita waje dik rintsi dik kuma
wuya, kai ba kamar kowani mutum kake ba, kai ruhin ruhohine, autan duniyoyi ne,
jagoran rundunoni ne, gatan manya manya ruhohi ne, nemanka suke yi kamar hauka, kai
ɗan baiwa ne, da baiwa aka haifa mun kai, wanna dalilin yasa suka mayar da kai
autansu, ni kuma ban yarda da hakan ba, saboda nasan me hakan yake nufi, wanna
dalilin yasa na baro duniyar shaiɗanu da kai tin kana karami baka wuci 5 years ba,
wannan dalilin yasa ban taɓa barinka kaje wani waje ba, saboda fitarka zai sa
DUNIYAR SHAIƊANU su shaida in da kake, bana son su rabani da kai! Kada ka fita daga
Black world har sai ka tara karfi sosai wanda zaka iya sanya barazana da tsoro a
cikin zuƙatan DUNIYAR SHAIƊANU, wanda karfin ikonka zai iya sanyawa ka kwaci kanka
daga ɗaukarka da zasu zo yi...............".

"Ka tara karfin iko mai karfin gaske ɗana, na jima ina karɓar yaya maza daga
hannun matan garin nan ina sanyawa ana basu horo dik dan na yi maka tanadi ɗana, ka
cigaba da horar da su dan su zame maka bayi masu bada rayukansu a kanka!!".

A lokacin da babansa yake yi mashi wanna bayanai hankalinsa baya'a jikinsa, a
lokacin yana tunanin rashin lafiyar baban ne kawai, bai ɗauki zancen da wani
muhimmanci ba, and bayar ɓacewar baban daga fuskar duniya bai sake tunawa da zancen
ba sai yanzu.

============💘🔥===========
FOREST NE. Wajen yana cikin tsakiyar dokar daji mai cike da bishiyoyi masu girma,
wadanda ganyensu suna rufe hasken rana. Akwai hayaniya mai ban tsoro kamar kuka na
tsuntsaye da dabbar da ba a iya ganinta.

Duwatsu da Tsaunika. Duwatsu sun kewaye wajen, suna ɗauke da layuka masu kama da
alamomin tsafi, suna haskawa da ɗan wuta mai launin kore. Tsaunukan suna da tsayi,
kuma akwai tsallake-tsallake na ruwa mai fitowa daga saman tsauni yana ƙara
tsoratarwa.

Babban kogon dutse shi ne cibiyar wajen matsafan. An yi ƙofofinsa da baƙin duwatsu
mai siffar fuskokin aljannu. Jikin kogon yana ɗauke da rubutun tsafi a harshe da ba
a fahimta. A ƙofar akwai fitila masu kunne da harshen wuta mai ruwan zuma da
jajaye.


======CIKIN KOGON DUTSE=======

Ɗakuna Tsafi. Babban ɗaki ne da ke tsakiyar kogon, yana da stage mai ɗauke da kayan
tsafi, kayan al'ajabi, kwalabe masu kunshe da ruwa mai launi, ƙananan gumaka, da
wukake masu ban tsoro.

Ɗakin Hada Magani. A cikin babban ɗakin yake shi ma ta gefe guda. Cike yake da
tukwane masu hayaƙi, ganye iri-iri, da fararen ƙasusuwa. Akwai ƙanshi mai kaɗaici
da hayaki mai ɗan duhu yana tashi daga cikin tukwanen.

Ɗakin Ajiya. Wannan ɗaki yana da duwatsu masu haske kamar gold, manyan littattafai
na tsafi da aka ɗaure da sarƙoƙi, da wasu abubuwan al'ajabi kamar ƙwayoyin ido da
ƙananan gumaka.

Ɗakin Ƙulle-ƙulle. Wannan ɗakin yana da tagwayen layukan duhu a kasa, fitilu masu
koren wuta, da gumaka masu kama da halittun ban tsoro suna kewaye.

Tsarin Haske. Hasken daga fitila ko wutar tsafi shi kadai yake cike kogon,
kuma wutar tana ja da baya idan mutum ya matso kusa.

Sautuka. Akwai sautin iska mai ban tsoro, kuka na dabba mara ganuwa, da muryoyin
mata suna magana a hankali kamar suna yin tsafi.

Halittun Ban Tsoro. Akwai dodanni da halittun matsafa masu kama da inuwa suna yawo
a wajen.

Daga cikin wani keɓaɓɓen ɗaki dake gefe wanna murya take fitowa, sai faɗi ake yi
autan ruhohi ya bayyana, lokacin girgiza duniya ta yi.

Ɗaki ne mai cike da ababen al'ajabi da ban tsoro, sai dai akwai tarin takardun
tsafi cike a cikin ɗakin, wasu irin dogayen mutane ne su goma tsaye a cikin ɗakin
saman stage, dikkansu suna cikin shigar wani irin dogayen kaya har yana jan kasa
launin ruwan zuma, sai suka ɗaura fara kal a sama, gashin kansu ya kasance white
hair ne, ga shi sun saki gashi dogo har bayansu, dikkansu riƙe suke da litattafan
tsafinsu, ga dikkan alamu su ne manya manyan malaman duniyar shaiɗanu.

Wani irin mutun mutumi na wata mata dake a cikin ɗakin sai ya tashi hankalin dik
wanda ya ɗaura idanunsa a kanta, macece tsirara aka ginata, ga wani sanda wanda
daga gani zaka san na tsafi ne wanda aka zira mata shi daga gabanta har ya fito ta
bakinta, dik yadda aka yi ta haka suke aiwatar da tsafe tsafensu, shiyasa suka bar
alama a wannan waje.

Burin waɗan nan azzaluman su cure duniya ta zama abu guda, ya zamana babu wata ƙasa
ko gari, dik a zama abu guda ne, su ruguje ɗakin kaba dake kasar Makka su gina
fadarsu a wajen, ya zamana gabaɗaya duniya shugaban kasa kuda ɗaya ne wato su
kenan, sun shafe tsawon lokaci suna yin wanna shirye shiryen ta hanyar tsaface
tsaface dan samun karfin iko.. KOWA DAI BURINSA MULKI, WAI SHIN BASU SAN AKWAI
MUTUWA BANE? BURINSU SU MULKI DUNIYA KAMAR SU SUKA HALICCI DUNIYAR?.

Bacewar Black Tiger daga cikinsu ya dakatar da su da yin dik wani shirye shiryen da
su ke yi domin nufar ɗakin kaba. My people's kun gane cewa ikirarin Black Tiger na
mallake duniya a jikinsa abin yake ko?.

Mahaifin Black Tiger shi ne shugaban malamai ko in ce bokayen DUNIYAR SHAIƊANU,
yanzu da kuka gansu su goma a wanna ɗaki to mahaifinsa shi ne sarkinsu, shi ne
shugabansu, shi ne kuma cikon na sha ɗayansu, shi ne mai faɗa aji, rana ɗaya ya
ɗauki Black Tiger suka bar DUNIYAR SHAIƊANU, ya je ya sari daji ya kafa birnin
BLACK WORLD, ko me dalilinsa na yin hakan?. Kada ku manta fa shi ne sarki a wanna
daula, amma ya gudu ya bar wajen, to me dalili?.

Burin DUNIYAR SHAIƊANU shi ne su fara ruguje musulunci a idon duniya, burinsu su
shafe babin addinin musulunci, su ruguje ɗakin kaba, su gina fadar mulkinsu a filin
na ɗakin kaba, su cure duniya waje guda domin su cigaba da juyata ta yadda zasu
samu dama su shafe addinin musulunci da gasken gaske, a yanzu haka sai yaki suke yi
da musulunci amma ta karkashin ƙasa, ba zaka gane suna yin hakan ba in ba'a faɗa
maka ba, kwantan ɓauna suke yi a yanzu, ta ƙarƙashin ƙasa suke aiwatar da komai.

Suna ta ƙoƙarin kawo rarrabuwar kai a cikin musulmi, suna ta sanyawa musulmi suna
kashe kawunansu, suna ta hasasa gaba a tsakanin musulmi ba tare da musulmai sun
gane ba!.

(LABARIN EVIL WORLD WATO DUNIYAR SHAIƊANU FA KU KALLE SHI A MATSAYIN LABARIN
GASKIYAR ABIN DA YAKE FARUWA A DUNIYA NE, DA KARFI DA YAJI SO AKE YI A YAKI ADDININ
MUSULUNCI TA KOWACCE HANYA, DAN HAKA KU TSAYA DA ADDU'A SOSAI, NASAN WASU ZASU GA
ABIN KAMAR TATSUNIYA, TO WLH YA WUCI HAKA, YA ZARCE TUNANINKU, KU TSAYA DA ADDU'A
KAWAI.)

Su waye ne a DAULAR DUNIYAR SHAIƊANU?. Wasu gungun kafurai da yahudawa ne da suka
haɗa kawunansu, suka cure a wanna waje domin ganin sun cinwa burinsu a kan musulmai
da Musulunci, suna da yawa a wajen, shararrun gima giman matsafansu ko in ce
bokayensu su ne waɗan nan mutum 11 ɗin, sannan suna da Jiga jigan TITANS waɗan da
suka zarce tunaninku a horarwa.

Kusan da tsafi suka yi amfani wajen haɓaka waɗan nan TITANS ɗin, burinsu a nan shi
ne idan suka ci addinin musulunci da yaki ta karkashin kasa sosai, idan ya rage
masu saura kaɗan, sai waɗan nan TITANS ɗin su karisa yakin su je su ruguje masu
ɗakin gaba, tsawon lokaci suka ɗauka suna bawa waɗan nan TITANS ɗin horo na ban
mamaki, burinsu shi ne bayyanar TITANS a duniya ya girgiza kowa, ya zamana babu
wani makami da zai iya yaƙarsu, sannan babu wani ɗan adam da zai iya tinkararsu,
ganinsu kawai yasa hantar duniya ta kaɗa...... Tashin hankali.

Ƴaƴan mutane suke satowa su mayar da su TITANS dan gudanar da wannan aiki, a kallah
yanzu suna da TITANS mugaye masu zuƙatan shaiɗanu sun kai TITANS 10000, kuma har
yanzu ba su daina sato wasu yaran ba.

Su waye TITANS? Wasu irin karfafa jaruman da suka jiku da horo ne, wuƙa ko bullet
baya iya huda fatar jikinsu, tamkar ba mutane ba haka suke, suna da tsawo da faɗi
sosai, sun zarce tunanin dik yadda kuke tunani!!. Da su za'ayi amfani wajen ruguje
ɗakin kaba ɗakin Allah.

Ya Ubangiji ka kare musulmi da musulunci a dik in da suke, kada ku kalli
wanna a iya labari kawai, ku dai ku yi addu'a kawai, Allah ya cigaba da ɗaukaka
musulunci!!.

======================

Ganin ya yi shiru kaman mai sauraran wani abin ne yasa Sweetie ta lallaɓa a sace ta
bar parlon, bai ankara da ita ba, ta gudu izuwa sama.

Shi kuwa ya tsunduma a kogin tunanin waɗan nan zantuka da ya jiyo ne, yana kuma
tariyo zantukan babansa.

Amma ku me kuke tunanin yasa mahaifin Black Tiger ya bar DUNIYAR SHAIƊANU? bayan
kuma shi ne shugabansu a wajen?.

Ya ɗan jima a haka kafin ya juyo da magic eyes ɗinsa, sannan Black heart ɗinsa
ta matso kusa. Kudurtawa ya yi a ransa in dai haka ne to tabbas sai ya riga Duniyar
shaiɗanu mallakar kambun mulkar duniya, dole ya tashi tsaye, dan ba zai taɓa yarda
su rigasa ba, bai san cewa shi ne makullin mulkar duniyar da suke shirin yi ɗin ba,
dan kuwa in dai baya Duniyar shaiɗanu to tabbas da wuya su iya isar da wanna aiki
da suka ɗauko.... Hmmm akwai tashin hankali fa matuƙa.

A cikin zuciyarsa ya furta cewa. Lokacin bayyanarsa ga duniya ya yi, lokacin
kara tsananta horar da warriors ɗinsa ya yi, lokacin farautar Spender ta kowacce
hali ya yi, dole ya mulki duniya cikin kankanin lokaci, dan haka dole ya shiga
fadar birnin Black world dan fara gudanar da mulkinsa........... Sweetie ta zame
mashi silar abubuwa da dama a ɗan zuwanta birnin, dalilinta yanzu zai bayyana kansa
wa birnin Black world.

To wai ina Spender ɗin yake? Tayaya zai samo shi? Dan dai kunga dik wahalar da ya
bawa Sweetie ta ki gaya mashi in da Spender yake, ya zai yi kenan?.

Ɓacewa ya yi daga in da yake tsaye, bai bayyana a ko'ina ba sai a katafaren fadar
birnin Black world.

Fadar sarki tana da kyan gani mai matukar birgewa. Daga waje, an gina ta da duwatsu
masu daraja da aka kawata da zinari da lu'ulu'u. Babban kofar shiga tana da girma
fiye da yadda mutum zai iya hangowa, kuma an kawata ta da hotunan zaki da bakar
damisa, wanda ke nuna ƙarfin iko da jarumta.

A cikin fadar, daki-daki za ku ga hasken fitilu masu daraja da aka yi da lu’ulu’u
na musamman suna haskaka ko'ina. Rufi kuwa an kawata shi da zane mai launuka masu
kama da taurarin dare, wanda ke nuna darajar sarauta.

Kujerar Sarauta
A tsakiyar fadar, kujerar sarautar mai martaba take tsaye tamkar zuciyar duniya. An
yi ta da zinari mai tsabta, tare da kawata ta da dutse mai daraja na lu'ulu'u da
furannin jade. Kafafun kujerar sun kasance kamar zaki da suka yi alamar girmamawa
ga sarki, kuma kujerar tana haskawa tamkar rana saboda yawan kayan ado na zinariya
da azurfa da aka yi mata, sai dai ta saman kayin kujerar kan bakar damusa ce,
sannan ta bayan kujerar gabaɗaya kaifafan kifiyoyi ne da aka yi su da zallar gold,
darajar wanna kujera ta wuci tunaninku, a kaf tarihi ba'a taɓa yin kujera mai tsada
da kyanta ba.

Zauren Masarauta
Fadarsa tana da manyan ginshiƙai da aka kawata da rubuce-rubucen hikima cikin
harsuna daban-daban. Kowane bangare na fadar yana cike da hotuna masu ban sha'awa
na yaƙe-yaƙe da nasarorin da suka bayyana tarihin sarautar. Idan baku manta ba na
gaya maku sun sha gwabza yaki wajen durkusar da dik wasu masarautu da suka fisu
karfin iko sabdoa zalunci, to hotunan yakin ne na nasarorinsu a manne a bangon!.
Tsarin Sarauta

An ware wani sashe na musamman ga makullai na zinariya, inda ake adana takardun
mulki, kayan alatu, da RAWANIN ZALINCI da sarki ke amfani da su. Kamar yadda aka
saba, masu gadi sanye da kayan mayaƙa suna tsaye kowane lokaci suna tabbatar da
tsaron fadar.

Sam warrios dake gadin fada basu ga giftawar kowa ba a wajen, da magic ya yi
amfani wajen shigewa ciki ta babbar kofar shiga.

A tsakiyar fadar ya tsaya, babu kowa a cikinta, ko'ina a share fes yana kyalli,
ɗan jujjuya idanunsa ya fara yi yana bin dik wata kusurwa lunguna da saƙuna da
kallo.

A kan dangerous kujerar mulkin ya tsayar da kallonsa. Gizo idanunsa suka fara yi
mashi na lokacin da mahaifinsa yake zama a saman wanna kujera, hango babansa yake
yi yana sanye da wannan the most powerful CROWN OF INJUSTICE ɗin a kansa yana
jawabi.

Ba zai taɓa manta lokacin da wani bawa ya yi laifi aka kawosa gaban sarki
mahaifinsa ba, yana zaune a gaban Tv a room ɗinsa yana ganin yadda babansa yake
wanzar da mulki, dan baban nasa yasan shi zai gajesa, dan haka sai ya sanya yana
ganin dik yadda ake mulki ta Tv, yana kuma koya mashi a zahiri idan ya koma cikin
gida, hakan yasa ya iya gudanar da komai cikin tsanaki.

Yana gani babansa ya sa aka ja wanna bawa, ya ce aje a tsaresa tsawon sati biyu
babu abinci babu ruwan sha, sannan a tabbatar da sauran bayi dake tsare suna cin
abinci a gaban idanun wannan bawa shi kuma yana ganinsu tsabar zalincinsa.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da yin magic walk ya isa gaban wanna kujerar. Ya ɗan
ɗauki tsawon lokaci yana kallonta kafin cikin nutsuwa ya zauna a samanta.

Yana zama nan take fadar ta bada wani irin duhu wanda ya samu sanadiyyar ɗaukewar
dik wasu fitillu dake ciki, sanna lokaci guda suka sake kawowa da hasken gaske fiye
da yadda suke.

Komai na cikin fadar sai da ya girgiza, shinfiɗun dake ƙasar wajen ne kawai basu
girgiza ba.

Dik ya ga hakan, amma sai ya yi kamar bai gani ba. Ya ɗan ɗauki lokaci a cikin
fadar kafin ya fice izuwa room ɗinsa, shap ya fita harkar Sweetie, yanzu abin da
yake a gabansa ya sha gaban tunanin mutum, dole ya mance da wata ƴar karamar
kwaruwa Sweetie.

Ta in da ya saba magana da master Devil wato ta wani ɗakin duhu, in da ko ɗan
yatsanka baka iya gani, nan ya nufa tare da kiran master Devil a kan ya zo.

Yana zuwa ba ɓata lokaci ya umarcesa da ya sanar da gabaɗaya mutanen birnin Black
world a kan gobe zai shiga fada, zai koma kan kujerar mahaifinsa.

Sosai master ya yi mamakin jin wanna magana, amma bashi da ta cewa da ya wuce ya
isar da abin da aka umarcesa kawai, dan haka sai ya karɓi umarni ya tafi.

Ita kuma Sweetie, room ɗin Ronnie ta koma ta takure waje guda, ko tsoron komawa
cikin ɗakin bata yi ba.

===========🔥🔥🔥==========

ABUJA.
Kwance suke a cikin A&E cikin katafaren hospital mafi tsada a garin Abj.

Kowannensu yana kwance saman nasa bed ɗin, jaririn Khadija yana hannun ɗaya daga
cikin securitys da suka kawosu hospital ɗin, an duba shi an yi mashi dik abin da ya
dace.




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Kwance suke a cikin A&E cikin katafaren hospital mafi tsada a garin Abj.

Kowannensu yana kwance saman nasa bed ɗin, jaririn Khadija yana hannun ɗaya daga
cikin securitys da suka kawosu hospital ɗin, an duba shi an yi mashi dik abin da ya
dace.

Sai kuka yaron yake yi yana neman abin da zai sanya a cikinsa, yunwa sosai yake ji,
ga uwarsa kuma bama a san a wani hali take ciki ba, ta mutu ne ko tana raye? Allah
masani.

Ko motsawa babu wanda ya yi a cikinsu, kamar babu rai a jikinsu. Sai kai komo wanna
security da ya rike yaron yake yi, yana ta safa da marwa ya kasa zama, sai haɗa
uban gumi yake yi, ga babyn yaki ya yi shiru saboda yunwa.
Ya rasa ya zai yi da shi, ga shi shi ba iya reno ya yi ba, haka dai suke ta
fama, idan ya gaji sai ya miƙawa wani daga cikin securitys ɗin, shi ma in ya gaji
sai ya miƙawa wani.

A haka har gari ya waye, babu wanda ya nufosu domin ya taimaka masu ya sa yaron ya
yi shiru, saboda kowa a cikin hospital ɗin tsoronsu yake ji, sun ga jiga jigan
jami'ai ai dole su tsorata kowa ya kama kansa, so kwanan tsaye waɗan nan securitys
suka yi. Ba halin su koma hotel da suka sauƙa, dan kafin tafiyar Ramish ya ce su
kula da case ɗin har komai ya warware, ma'ana su kula da waɗan da aka buge har su
sami lafiya.

Washegari da safe haka babyn nan ya rinƙa kuka, Allah sarki bawan Allah yunwa
yake ji sosai. Waɗan nan securitys ɗin dikkansu har sai da suka ji sun tsani yara
saboda kukansa, sai dai kuma wanna baby na Khadija fa ya shiga ransu ba kaɗan ba.

Sai misalin karfe 12 uncle Jahiz da wasu securitys ɗin suka nufo hospital ɗin, so
yake su wuce Tunisia, shi ne ya biyo sahunsu ya ga shin zasu iya tafiya ne ko
yaya?.

Har yanzu Jaish yana sume bai farka ba, Ramish ya ce su barshi ya farka da kansa.

Tun daga nesa da securitys ɗin nan suka hango uncle Jahiz suka yi saurin
nufarsa, har lokacin baby bai yi shiru ba.

Tun da suka doso in da yake idanunsa na'a kan babyn hannunsu, mamaki yake yi a in
da suka samo baby, dan shi a daren jiya bai ga wani baby ba.

Suna ƙarisawa wajen suka fara yi mashi sannu da zuwa haɗe da barka da safiya.

Bai iya amsa masu ba, idanunsa na'a kan babyn. Sai da ɗaya daga cikin securitys ɗin
ya ce.
"Sir mu ƙarisa ko?"

Jinjina kai ya yi, sannan ya wuce gaba, har ya yi taku step biyu sai kuma ya juyo,
ga mamakinsu sai suka ga ya miƙa hannu a kan su bashi babyn.

A hanzarce securityn ya miƙa mashi, basu taɓa ganinsa rike da yaro ba, bama su yi
zaton ya iya riƙewa ba. Ga mamakinsu kuma sai suka ga ya iya riƙe jariri ɗanyan
haihuwa da kyau.

Yana karɓar yaron kuma ya yi shiru kamar wanda ya ji ɗumin jikin uwarsa ko ubansa.
A saman kaffaɗar kirjinsa da ya ji training saboda football ya ɗaura yaron, ya
janyo towel da suke riƙe shu da shi dama ya ɗan lulluɓe shi da shi, ya zubawa babyn
idanu sosai yana ta kallonsa, haka kawai ya ji kaunar yaron tana ratsa shi.

Gaba ya wuce securitys cike da mamaki suka rufa mashi baya, a maimakon ya kalli
hanya sai gabaɗaya idanunsa suna a kan babyn har suka ƙarisa ɗakin da su Khadija
suke kwance.

Dr ya buƙaci gani domin yasan me yake damunsu, saboda yana san yau zai wuce
kasar Tunisia, ya ƙosa ya mayarwa da King Jaish ɗinsa su ga juna, rashin sanin ya
fi dare duhu, bai san yanzu ne ma zasu shiga ainahin tashin hankalin na mutuwa da
kuma ɓacewar gawar Gimbiya Zunaira ba, ko shi kansa Jaish ɗin sai ya ji a jikinsa.

Buƙatar su haɗu a office babban Dr ya yi, bai ja ko ya yi wata magana ba, yana
rungume da baby kamar wani ɗansa ya bi Dr izuwa cikin office ɗinsa.

Su kuma securitys suna ta going up and down a cikin ɗakin. Ya ɗauki a kallah 30
mins suna tattaunawa da Dr kafin ya fito fuskar nan tasa babu annuri sam, kamar Dr
ya gaya mashi wata magana mara daɗin ji.

Motarsa ya nufa ɗauke da baby, bayansa securitys uku daga cikin waɗan da ke
gadinsu Khadija suka bi. A tunaninsu tun da zai tafi zai basu babyn, sai suka ga
akasin haka, dan kuwa ya manne babyn nan da jikinsa kam, babu alamar zai iya
ɓanɓarosa ya basu shi.

Yaronma da gulma ji kake yi tsit kamar wanda aka mukkawa nono uwa, har barci ya
fara yi.

Magana

Please Login or Register in order to submit comment