Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 20 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaukosa, dik ta damu tana san jin hakan, kun san mufa mata batu
na gaskiya muna da sanin yakamata ato, taga yakamata ta san daga ina yaronta ya
fito ne?.

Uncle Jahiz ne ya fayyace masu komai yadda ya kasance da yadda Ramish ya gano in
da yake har suka je suka ɗaukosa. Dik cikin parlourn wanda kowa da kowa yana cikin
except Jawad da Chuchu da har yanzu Chuchu jikinta bai warware ba, suna hospital,
sai kuka take yi taki dainawa, ita dai a dawo mata da Autarta.

A gabaɗaya parlourn nan babu wanda ya gane aibi a cikin abinda su uncle Jahiz suka
aikata, kowa sai godiya yake yi wa Allah, sai murna suke yi, shi ma Jaish yana
zaune kusa da Momma, sai satar kallonsa Fanan take yi, tana san yi mashi sannu da
dawowa, amma tana tsoronsa sosai.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
"Amma Jahiz wani irin abu ne wannan zaku je ku ɗauke shi ba tare da kun nemi waɗan
da suka rikesa kun yi masu godiya ba?".

Muryar momma ce ta dakatar da dikka wannan godiya da murna da suke yi ɗin.

Mummyn Chuchu ce ta amsa da. "Gaskiya nima naga abin bai kyautu ba sam".

Aunty MieMie dake zaune a gefen King ne ta amsa da. "Gaskiya kam ba'ayi masu adalci
ba, bai kamata ayi masu haka ba".

Miƙewa Jaish ya yi ya nufi hanyar fita daga parlon. Aunty MieMie ce ta tambaye shi
ina zai je.

Ba tare da ya dakata daga tafiyar ba ya amsa mata da nitsuwa yake so, baya san
hayaniya, zai je ne ya kwanta. Miƙewa ta yi ta bi bayansa dan tana san yi magana da
shi. A wannan lokacin ne suna fita ya wuce hospital wajen Jawad dan yau tun da rana
da ya je asibitin suka gaisa bai sake zuwa ba, Jawad kuma baya fita ko nan da can
sai masallaci, so a tare suka je da Aunty MieMie.

Sosai momma ta nuna rashin dacewan abin da suka yi, ita ma mummyn Chuchu ta nuna
hakan, mama dai bata ce ko uppan ba, ta dake a kan kujera tare da ɗaura kafa ɗaya
bisa ɗaya.

Momma ce ta nemi King da ya yarje mata zata je ta ga mutanen nan da suka rike
mata yaro, har ta ji kaunarsu ya ka mata, uwa kenan, ko yaya ka yi wa ɗanta abu
bata mantawa da kai.

King yasan condition da take ciki na rashin nitsuwa a kan ɓatar Auta, a yanzu
farincikinta suke nema ba ɓata mata ba, dan haka sai ya ce to za'a shirya mata
tafiya nan da gobe ta je ta gansu ɗin, wannan shi ne dalilin zuwanta Jimeta, bata
ma san Jaish yana da mata ba, bata san irin rayuwan da ya yi a can ba, ita dai ta
zo da kanta ne ta yi godiya na riƙe mata yaro da suka yi, to kun ji yadda aka yi,
taso su zo a tare da Jaish, amma yaki yarda, ya ce shi gaskiya babu a gajiye yake,
kuma baya san zuwa ne kawai. Yauwa ku kara tafawa mata jama'a.......

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Da gudu Mahreen ta tafi ta rungumi guyson, dan a tunaninta Jaish ne, securitys
ɗinsu sun so hana Mahreen isa gare shi, amma kafin su tareta tuni ta isa gare shi,
kun santa da iya gudu.

Ita dai Mahnoor ta san ba Jaish bane, dan suna da banbanci da guyson dik da cewa
guyson ɗin ke binsa a wajen haihuwa, amma suna da banbanci.

Momma bata yi mamakin ganin Mahreen ta rungume mata yaro ba, saboda tana
ganin Mahreen yarinya ce, sannan kuma hakan da ta yi yasa momma ta kara jin daɗi a
ranta, dan alamu sun nuna sun yi sabo da Jaish sosai shiyasa ta rungumi guyson
matsayin Jaish.

Uncle Jahiz ne ya wuce gaba wajen isa gaban Arɗo dake tsaye a kofar gida yana
kallansu, sun ga shi ne dattijo a wajen sai suka nufesa.

Sarautar nan dai tana nan, badan momma bama da su uncle Jahiz ba zasu zo nan
ba, dan haka cikin isa ya ce da Arɗo suna neman gidan da ɗan uwansu ya yi rayuwa a
ciki kafin suka zo suka ɗaukesa kwanaki shidda zuwa bakwai da suka wuce!

Arɗo ya ɗan yi mamakin jin yadda Uncle Jahiz ya yi mashi magana kamar wani ɗansa,
yana mashi magana ba girmamawa, bai san haka suke magana cike da izza ba su kam.
Da hannu ya nuna masu gidansu Mahnoor dake bayansa, dan yasan a kan bakonsu
Jaish suke magana.

Momma da guyson kuwa, sun yi tsaye suna kallan Mahreen da ta rungume guyson tana
zuba mashi surutai haɗe da ɗauki game da sambatun ta san zai dawo garesu dama, har
da cewa ta yi kewarsa, ta fara bashi labarin irin kukan da Adda Mahnoor ɗinta ta yi
a lokacin da baya nan.

Guyson da momma dik babu mai jin yarenta, dan haka basu san me take faɗe ba, sun
dai yi shiru suna sauraranta ne.

Jin basu yi mata magana bane yasa ta raba jikinta da guyson ɗin ta riko hannunsa ta
fara jansa wai ya zo su je su ga bappa, bappa ma yana can yana kewarsa. Ita dai
Mahnoor idanunta a kansu ko kyaftawa ta kasa yi, tana kuma tsaye, fuskar mijinta
kawai take gani a face ɗin guyson.

Sam bashi da kuzari a jikinsa ya dawo da kallonsa a kan Momma, Mahreen sai faman
jan mashi hannu take yi.

"Bita muje ka ji, dik yadda aka yi a gidansu yayanka ya zauna shiyasa take
janka, ga dikkan alamu kallan matsayin yayanka suke yi maka".......... Cewar Momma
kenan.

Kamar zai yi kuka ya ce. "Momma jikinta dik datti fa! Kalli yadda ta zo ta taɓani
ta ɓata mun jiki".

Kunsan guyson ɗan wanka ne, ga kayan jikinsa farare kal kal, irin Pakistan na maza
riga da wandon nan ne, ya sha rawani a kansa, kyau iya kyau, so baya shiri da datti
ko kaɗan, Allah sarki dan ma yana da saukin kai ne yasa bai yi mata faɗa ko ya
mareta ba, da su Omaid ne ai da yanzu zancen sun sumar da ita ake yi.

"Yi hakuri, ɗaukin ganin yayanka yasa ta yi maka haka, idan mun koma gida sai ka
cire kayan ka ji?"................ Cewar Momma.

"Momma ni Allah bana san dattin, kice kawai ta sakeni".

Momma da ta fahimci zai iya saka masu kuka a wajen, dan wlh ko da wasa baya san
datti, sai ta riko hannun Mahreen da take rike da shi, cikin harshen larabci ta ce
da Mahreen.

"Zo wajena kin ji?......"

Bata idasa maganar ba Mahreen ta kwace hannunta, cikin tsiwa ta ce. "Wacece ke da
zaki rikeni? Ni ki barni a wajen hamma na". Tana kai karshen maganar ta sake rike
hannun guyson.

Kasancewar da fillanci ta yi maganar sai momma bata gane me ta faɗa ba. Shi kuma
guyson tana rikesa ya fisge hannunsa da karfi haɗe da cewa........... "Kada ki sake
rikeni da hannunki dik datti".
Da larabci ya yi maganar. In baku manta ba a baya Mahreen ta fara koyar
larabci kaɗan kaɗan, dan haka ta ji wannan kalmar da guyson ya ce ta sake shi.

Sai kuma a lokacin ta lura voice ɗinsa ba iri ɗaya da Jaish ba, muryarsa na yara
ne, kuma ɗan siriri ne sosai. Fahimtar hakan yasa ta yi saurin ja da baya daga kusa
da shi.

A tinanin momma tsawar da ya daka mata na ta sake shi ne yasa ta ja bayan, dan haka
sai ta yi ƙoƙari matsawa kusa da ita ta rikota. Ai ina, a miliyan Mahreen ta juya
ta bar wajen tana rushewa da kuka mai ban tausayi, Allah sarki ta gane ba Jaish
bane yanzu.

Uncle Jahiz da ya tsaya yana turɓune fuska yana binsu da kallo ne ya matso kusa da
momma............ "Ga gidan nan, ku shiga ku yi abin da zasu yi kin dai ji yaya ya
ce kada mu kwana, yau zamu juya". ....... Ya faɗa ransa a ɗan ɓace, da alama bai so
batun zuwansun nan ba sam.

Momma ta lura da baya san zuwa, dan ma saboda ita ce, wlh da mummyn Chuchu ko mama
ne ba zai zo ba, dan haka sai ta wuce gaba saboda su yi sauri su je su fito.

Cikin mutunci ta gaida Arɗo, sannan ta buƙaci da ya yi mata jagoranci izuwa ciki,
bodyguards zasu shige cikin su duba babu wani abin cutarwa kafin ta shiga, ta yi
saurin dakatar da su, ta ce su bari zata shiga kawai.

Mairo Arɗo yasa ta tarbesu hannu bibbiyu, a lokacin da suka shigo bappa baya
ɗakin, ya samu kaikayin ta sakesa saboda Arɗo ya labta mashi kashin sosai a
jikinsa.

Nenne kuma ta gudu gidan Arɗo, so Mairo ce kawai a cikin ɗakin tana ƙoƙarin gyara
komai, ta fitar da tabarman da aka kwantar da bappa, ta juye mashi wani ruwan
wankar ya shiga wanke jikinsa, da yake isaka na kaɗawa sosai ma har kashin shanun
ta bushe a jikinsa.

Tabbas momma ta ji kyamar shiga cikin gidan, amma duba irin alkhari da suka yi
mata, ɗanta sukutum, first born ɗinta suka kula mata da shi, sai ta danne kyamar ta
shiga cikin gidan.

Guyson kam ya gudu wajen uncle Jahiz sun koma cikin mota sun zauna. Time da Mairo
ta yi masu iso cikin ɗakin, Momma ta so ta ki shiga, amma kuma da ta tuna Jaish sai
ta daure ta shiga ciki.

Mahnoor kuwa ganin babu Jaish a cikin tafiyar sai ta dawo cikin gida ta wuce
ɗakinta ta kwanta, ita kuwa Mahreen bin momma ta yi har cikin ɗakin bappa dan taga
me ya kawosu gidansu?.

Arɗo ma ya shigo cikin ɗakin dan ya ji me ya kawo su Momma?. Cikin girmamawa
Mairo ta tsugunna ta ɗagawa Momma gaisuwa.

Sai dai kash babu fillanci, momma bata gane komai da suka faɗa ba, da yake Arɗo
babban malami ne yana jin larabci sai ya sanar da momma gaisuwa Mairo take yi mata.

Jinjina kai kawai momma ta yi, ta ku ma ɗan ji daɗin ansamu mai jin irin
larabcinta, dan haka sai ta faɗa mashi ita mahaifiyar bakon da suka rike ne, ta zo
ne ta yi masu godiya bisa rike mata yaro da suka yi.

Sosai Arɗo ya yi mamaki, a wani ɓangaren kuma ya ji matuƙar daɗin hakan, ko ba
komai sun nuna sun san anyi masu halarci.

"Bani na rike ɗanki ba, ɗana ne ya riƙesa, ya shiga wanka bari ya fito sai ku
gaisa".......... Cewar Arɗo.

Jinjina kai momma ta yi ba tare da ta yi magana ba, dik zama a cikin ɗakin ya
isheta, ji take yi kamar zata yi amai, amma haka ta daure har bappa ya fito daga
wanka, yana sanye da jampa blue, ta koɗe kam sosai, jikinsa fa dik ya ji ciwo bawan
Allah, bayansa ta ɗaye, kai Nenne muguwa ce, ta gana mashi azaba, wannan ma fa wai
yanzu aka fara zaman kishin, anya nan gaba Nenne ba zata saka masu wuta ba
kuwa.................🤔
Lokacin da su Momma suka zo bai gama dawowa cikin hayyacinsa ba, so bai san da
batun zuwan nasu ba. Da ya fito yaga jirage a saman suna shawagi kuma sai ya ce
bari ya je ya wanke jikinsa da sauri ya fito yaga menene yake faru? Shi ma dai da
kallo jiragen sau ɗaya ya raya a ransa Jaish ɗinsa ne ya dawo garesu.

Har kamar zai fita waje da ya fito daga wanka, sai kuma ga kalli sabbin Queen cover
shoes masu bala'in kyau a kofar ɗakinsa, hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, shi
ne ya ce bari ya shiga ya ga wacece a ciki.

Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Arɗo ne ya amsa mashi sallamar tasa. Yana
ɗaura idanunsa a kan momma ya gane cewa mahaifiyar Jaish ce, wani irin farinciki ne
ta lulluɓesa, Allah sarki har kasa haƙura ya yi sai da ya tambayi ina Jaish, ko
zama bai yi ba.

Sai dai da fulatanci ya tambaya, ya manta da basa jin fillanci, sai da ya ji momma
bata amsa shi bane yasa ya juya harshe izuwa larabci.

Mahreen tana ganinsa ta yi sauri ta zo ta rungumesa tare da saka mashi kuka tana
faɗa mashi hamma bai dawo ba sai dai wani mai kama da shi ne ya zo. Guyson kenan.

Nan take bappa ya ji jikinsa ta yi sanyi, gabansa har sai da ta faɗi, dik tinaninsa
Jaish ya dawo garesu ne. Arɗo ne ya ce mashi ya nemi waje ya zauna momma wajensa ta
zo.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya samu waje ya zauna yana tinanin Jaish.
Cikin mutunci da girmamawa ya ɗagawa momma gaisuwa da larabci.

A ɗan dake ta amsa mashi kafin ta ɗan yi shiru na ƴan mintuna. Sannan ta gabatar
mashi da wacece ita da kuma abin da ya kawota.

Sosai bappa ya sake jin zuciyarsa ya karaya, wato godiya suka zo yi mashi ma ba wai
sun kawo Jaish bane, sam abin bai yi mashi daɗi ba, ba haka ya so ba, shi bai yi
dan ayi mashi godiya ba, saboda Allah da kuma kaunar da yake yi wa Jaish ya yi.

Ganin ya yi shiru kaman ya shiga damuwa ne yasa Momma ta buƙaci da ya bata tarihin
a ina ya ga Jaish da har ya rikesa na tsawon watanni haka?.

Jiki ba kwari ya zayyana mata komai daga farko har karshe, bai ɓoye mata komai
ba har da gudun Jaish da ƴan kauyen suka rinƙa yi suna ce mashi aljani, dik ya
zayyane mata.

A gabaɗaya maganganunsa da ya faɗa abu ɗaya ne ya yi mata daɗi shi ne Jaish ya yi
aure, wannan magana ta yi mata daɗi sosai, har sai da ta ɗan murmusa, cike da
farinciki a ranta ta buƙaci da a nuna mata matan ɗanta.

Bappa ya yi mamakin ganin bayyanar farinciki a tattare da ita daga jin Jaish yana
da mata, ya yi zaton zata ki batun auren, ashe ba haka bane baiwar Allah. Tabbas
momma har cikin ranta ta ji daɗi, saboda ko ba komai ta kara samun ɗiya mace,
sannan kuma zata rama masu alkhairi da suka yi mata, sun cancanci hakan, sun
cancanci a rike masu ƴa da amana, dik ɗan halak ba zai manta halacci ba, dan haka
tana maraba da Mahnoor from the button of her heart. Kuma ni da ku mun san bappa ya
yi matuƙar ƙoƙari a kan Jaish, kada ku manta fa farko ko irin abincinsu Jaish baya
iya ci, amma haka bappa ya rinƙa yanka mashi nama yana ci, dik kaunar ƴan kauye da
dabobinsu haka bappa ya sadaukar da nasa dabbobin wa Jaish, ai ya yi namijin
kokari.

Allah sarki ni Princess Teema na ji matuƙar tausayin Fanan, tana murna Jaish ɗinta
ya dawo sai aure, ashe mata garesa, heart breaked!!.
"Mahreen jeki ki kira Mahnoor a ɗakinta". Cewar Bappa.

Cikin kunci, tana guntun kuka ga hawaye a saman face ɗinta ta miƙe ta fita, sai
gunjin kuka take yi. Godiya momma ta yi wa bappa sosai tare da nuna mashi jin
daɗinta a kan wannan aure, ta kara mashi wani godiya na daban a kan bawa ɗanta mata
da ya yi, daga karshe ta rufe mashi da zata tafi da Mahnoor.

Tashin hankali, nan fa matsalar take, dan kuwa bappa bai shirya rabuwa da Mahnoor
ba, a tinaninsa wai sai dai Jaish ya zo su yi zaman aure da ita a cikin kauyen, shi
bai yarda a ɗauketa ba, ita kuwa Momma ta ce mashi ina hakan ba zai yiwu ba,
Mahnoor matar Prince ce fa ba wai matan mutum gama gari ba, ai kuskure ne ma su
bari wani yaga face ɗinta, nan fa momma ta shiga zayyana mashi dokikin gidan
sarauta da tsarukanta da yadda matansu suke kasancewa cikin tsaro da lulluɓe kai,
daga karshe ta ce tafiya da Mahnoor dole ne!!! Idan suna da ra'ayi su tashi mutanen
da zasu bisu su ga in da suke, amma tafiya kam babu fashi............ Babbar
magana.

Bappa ya yi shiru cikin ransa yana tunanin yadda zai fara rabuwa da yarsa. Dik
tattaunawar da suke yi Ibrahim kawunta yana jinsu, dan yana zaune a tsakar gida, ba
ƙaramin daɗi ya ji ba na jin matsayin da Mahnoor ta samu, abin da basu taɓa
tsammani ba, ya ji daɗi da suka ce zasu tafi da ita, kamar ya zuba ruwa a kasa ya
sha.

A tare Mahreen da Mahnoor suka shigo cikin ɗakin, Allah sarki ashe da ta koma cikin
ɗakinta kuka ta je ta rinƙa yi, idanunta har suka kumbura. Suna shigowa bappa ya ce
da momma ga matar Jaish ɗin, ya kuma cewa Mahnoor wannan mahaifiyar mijinta ne ta
je ta gaisheta.

Matsawa ta yi kusa da momma, kanta a kasa ta tsugunna zata gaisheta. Jawota momma
ta yi ta runguma tana tsananin farinciki, dan kuwa tamkar an shiga ranta anyi
bincike kafin a bashi wannan mata, tabbas irin matar da take mashi fata take kuma
yi mashi addu'ar samu kenan, kyakkyawa san kowa kin wanda ya rasa, abin ya yi mugun
yi mata daɗi, dik wani bakincinkinta sai ta ji ya kau, tamkar zata mayar da Mahnoor
cikin cikinta saboda so da kuma murna.

Shi dai bappa dik wannan bashi bane damuwarsa ba, ya za'ayi momma ta ce, zasu tafi
da Mahnoor? Gaskiya ba dan su gidan sarauta ba a ja in ja da su ba wlh da shi dai
ba zai yarda ba, amma ba yadda ya iya.

Dai'dai lokacin Jaish ya kira Momma ta Whatsapp, voice call kuma ya kirata, dan
ya gwada number kai tsaye taki shiga.

Ganin shi ne yasa ta yi saurin ɗauka, cikin nitsuwa suka gaisa ya tambayeta ya
hanya?. Murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha ta ce mashi ai gata a cikin gidansu
tare ma da matarsa.

Ya ɗauka wasa take yi sai ya ce. "Momma kada ki ɓata lokaci please, ku dawo da wuri
dan har na damu na fara kewarki".

Ita kuwa sai ta ce mashi ga matarsa nan su gaisa.

A ɗan dakile ya ce. "Mata kuma?!".

Jinjina mashi kai ta yi haɗe da tabbatar mashi, bada ban ita ta ce matarsa ba da ya
ja tsaki kuma ya kashe wayarsa, amma ita ce ya zai yi? Sai ya ce.......... "Please
momma kada ki fara wannan zancen auren naki, ni kada ki ce ma zaki ga ƴar mutane ki
saka mata ran aurena, bani da lokaci a yanzu, please kada ki mun irin abin da kika
yi wa uncle Abbas, zan tabbata cikin kunci". Yana maganar fuska a ɗaure tamau
kamar hadari, alamar bada wasa yake yi ba!!.
Kunsan momma ita ta haɗa auren uncle Abbas da maman su Yah Jawad, kawai daga ziyara
ta haɗa wannan aure, to shi Jaish a tunaninsa irin taga mace kyakkyawa ne ta ce
zata zaɓa mashi, kwata kwata bai taɓa kawowa ransa matar ta gaske ce kuma
mallakinsa ce ba.

Momma da ta rasa me zata ce mashi saboda bata san tsayawa yi mashi dogon bayani ta
waya, sai ta ce mashi zasu yi waya anjuma, yanzu bari ta samu ta bar wannan kauyen
su kamo hanyar kasarsu shi zai fi.

Da okey ya amsa mata, har zai katse kiran kuma sai ya sake ce mata dan girman Allah
shi kada ta jajuɓo mashi bala'i yana zaune lafiyarsa. Bata amsa mashi ba ta katse
kiran, dan bata san biye mashi yanzu.

Bappa dik da bai san da waye take waya ba sai ya ji yana san yin magana da na cikin
wayar, dan zuciyarsa na faɗa mashi da Jaish take waya.

In short haka momma ta gama dik abin da zata yi, ta kawo makudan kuɗin da suka
canza nasu izuwa na Nigeria, miliyoyi ta bawa bappa, suka kara yi masu godiya
sosai, sannan ta ce yakamata su tafi da wani ya bisu ya ga ƙasarsu.

A nan ne Arɗo ya ce su tafi da kawu Ibrahim. Bappa ma ya aminta da hakan. Sai kuma
me?.

Momma tana rike da hannun Mahnoor taki saketa, sai da suka je zasu shiga motocinsu
Mahreen ta ce wlh basu isa ba, bata ga uban da zai rabata da ƴar uwarta ba. Ita ma
Mahnoor ɗin kuka ta saka masu, ta ce wlh ba zata iya rabuwa da Mahreen ba, infact
sai cewa ma ta yi da a rabata da Mahreen gara ta hakura da Jaish ɗin har abada.

Ganin haka yasa momma ta ce zata tafi da su dikkansu biyu kuma ta yi alkawarin
zata rikesu amana, dan ba zata iya barin Mahnoor ba, ai ita taga wa ɗanta matar da
babu rabuwa.

Nan fa bappa kuma ya ce gaskiya bai aminta a tafi da Mahreen ba, to shi wa za'a bar
mashi?. Sai da Arɗo yasa baki ya roƙesa a kan ya dubi girman Allah kada ya raba ƴan
uwan nan guda biyu, tare suka taso, tare suke komai, suna bala'in kaunar junansu,
idan ya rabasu wlh zai cutar da su ne, ya yi hakuri ya kyalesu su tafi ɗin kawai.

Kun san abin isn't easy wlh, rabuwa da yara biyu lokaci guda, yaran ma su kaɗai ka
mallaka, a rabaka da su kai akwai wuyar iya ɗauka fa. Da kyar da suɗin goshi bappa
ya aminta da su tafi a tare. Kawu Ibrahim ya yi masu rakiya suka tafi.

Nenne tana gidan Arɗo bata san abin da yake faruwa ba, daga baya ta ji maganar daga
sama, tuni ta rugo tazo dan ta ganewa idanunta, sai dai kash, suna tafiya tana
isowa, dan haka bata samu damar ganinsu ba. A lokacin kuma bata san da Mahreen aka
tafi ba, da za'ayi bala'i kam.

To our Mahnoor safe journey, daga Jimeta sai Abuja, daga Abj sai Tunisia, Allah
ya kaiku lafiya.

9:30pm. Su momma suka isa Tunisia, su Mahnoor sai kauyanci suke ta bugawa, da
yake Mahnoor tana da kunya, ta san momma surkuwarta ce, sai tana danne kauyancinta.

Ita kuwa Mahreen da suka zo shiga cikin kingdom of power, idan baku manta ba dama
akwai wasu gumaka na zakuna a bakin gate ɗin, sannan akwai kungin Aunty MieMie. Ai
kuwa tana ganinsu ta fara yi wa su Momma hauka wai taga mugun abu.

Da kyar Ibrahim ya rarrasheta, haka a wajen shiga jirgi ma ta rinƙa yi masu hauka,
ta ki hawa sai da Ibrahim ya ɗagata, Mahnoor dai dik da a tsorace take ta danne
bata fito fili ta yi haukar ba, sai dai zuciyarta cike yake tab da tashin hankali,
ta gama tsorata. Dama da pr jet ɗin King Zuhair suka zo.

Ai Mahreen bata gama yi masu hauka bama sai dai suka nufi family part, a lokacin ne
suka ga hauka, ta rinƙa yi masu kuka a kan ita a mayar da ita wajen bappanta, ai
nan ba duniya aka kawota ba, kasheta za'ayi. Ta ƙanƙame Ibrahim tana ihu.

Ita ma Mahnoor kukan nan take san yi, amma ta danne, idanunta sun ciko da kwallah
sun yi jajir. Ta kofar baya motocin su momma suka tsaya, dik da dare ne basu tsaya
ta gaba ba, dan in baku manta ba doka ce ba'a ganin matan sarki.

Momma tana rike da hannun Mahnoor gam suka nufi cikin gidan, sai ta ce Ibrahim ya
jirata a wajen zata turo wanda zai kaisa masaukinsa. To shi Ibrahim ya saba yawace
yawace bai wani tsorata sosai ba, amma dai ya ɗan tsorata shi ma, saboda bai taɓa
ganin Daula haka ba.

Mahreen ta ƙanƙame Mahnoor sai kuka take yi, momma ta yi ta yi tayi shiru amma
taki, ita dai a mayar da ita wajen bappanta kada a kasheta, so su da yake basa jin
fillanci sai basu san me take faɗe ba, guyson dai ya wuce part ɗin mummyn Chuchu
abinsa, ya ce sai su Mahreen sun yi wanka zai dawo wajen mommarsa, sai ɓata rai
yake yi momma ta kawo masu ƴan datti, bai ma san cewa Mahnoor matar Jaish bace.

Suna sako kafarsu a parlourn momma Jaish dake zaune saman sofa shi da Jawad da aka
sallamesu daga asibiti ɗasun ya miƙe tsaye da nufin zai bar part ɗin, dama tun
ɗazun suke zaman jiran momma a wajen, so yaga kamar ba zata iso da wuri bane yasa
ya miƙe da nufin ya je part ɗinsa ya kwanta.

Ai Mahreen tana ganinsa ta dagata da yin haukar da take yi masu, tuni ta manta da
in da take, ai a miliyan ta watsa a guje ta je ta faɗa a jikinsa.

Mahnoor ma wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta sauke, ta kasa kawar da idanunta
daga kansa, ya canza sosai cikin kwanaki bakwai, ya koma sak yadda yake da, hasken
fatarsa ta dawo yadda take, ga gashin kansa da ya tara a kauye yanzu ta sha gyara,
ba ƙaramin kyau ya kara ba, yana sanye da sleeping dress launin up white, shi ma
Jawad kayan barci launin up white ce a jikinsa, dama su fa kayansu iri ɗaya suke
sakawa, komai nasu kusan ɗaya kamar tagwaye.

Cikin zafa Jaish ya finciketa daga jikinsa, da karfi ya wurgata gefe guda, ransa
ta yi mummunar ɓaci, kallan ƙazamiya ƙasƙantacciya ya yi mata, bai santa ba ta zo
ta wani rungumesa.

Ƙoƙarin dalla mata mari ma ya yi cikin fushi, da sauri Jawad ya riƙesa yana
faɗin......... "Haba mutumin meyayi zafi haka?".

Momma dai turus ta tsaya tana kallonsu, sam bata yi mamakin hakan ba, dan tasan
dikka ƴaƴanta

Please Login or Register in order to submit comment