Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 13 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara gyara kwanciyarsa
a saman laps ɗin nata.
Daidai lokacin King ya fito sanye da jallabiya ruwan hoda a jikinsa, sai tashin
kamshi yake yi.

Ganin Guyson nasa a saman bed ɗin ga kuma hawaye a face ɗinsa yasa ya kariso da
sauri yana tambayar ba'asin meyake faruwa?.

Yana ganin King ya kara rushewa da kuka mai ɗan sauti, kukan shagwaɓa har da
shessheƙa.

Hankalin King ne ya kara tashi, dama shi bai wani san halinsa sosai ba, dan in baku
manta ba girman Dubai ne shi, Momma ce tasan kayanta tsab, dan haka bata wani
rikice sosai ba, dan tasan a kan ɗan buge hannu a jikin bangoma guyson kuka yake yi
bare azo ga ciwon kai ko ciki, ai sai ya wuni yana kuka!. Sakalene.........😅

A hanzarce King ya haye saman bed ɗin yana kara tambayarsa me yake faruwa?. Ya yi
maganar tare da kai hannu yana ɗan ɗagosa daga jikin momma.

Ai tin bai gama kai hannu jikinsa ba ya miƙe ya faɗo jikin daddyn nasa yana kara
tsara kukan shagwaɓar tasa da kyau, har da hawayen iyashege!.

Kallon momma da bata wani damu sosai ba King ya yi. "Rahilarh lafiya? Me kika
yi mashi?". A rikice ya yi tambayar.

"Wai jikinsa ne yake yi mashi ciwo shi ne yake kuka".............. Ta bada amsa
tana kai hannu zata taɓa gaban goshinsa.

Zaro idanu King ya yi, ya kara shiga damuwa. Muryarsa har tana ɗan sarkewa saboda
saurin wajen furta magana ya ce. "Miko mun wayata bari in kira Dr ya zo".

Ganin yadda ya rikice ya tashi hankalinsa haka abin ya ɗan bawa momma mamaki, dan
ita tasan halin kayanta, a ganinta yanzu haka idan aka bincika ba wani ƙwaƙƙwaran
ciwon da yake damunsa.

"A'a dare ya yi, ka bari sai zuwa da safe se mu kai shi hos........"
Wani irin cin burki ta yi a maganar tata bata karisar ba, ba komai ya ja hakan
ba kuma face zaro mata idanu da King ɗin ya yi.

Cike da mamaki ya ce. "Rahilarh kin san me kike faɗa kuwa? Mu bari sai da safe fa
kika ce?".

Kai ta jinjina mashi alamar tabbatarwa da yes hakan ta ce.

"Amma lallai Rahilarh baki san me bakinki yake faɗe ba, kinfa san Omar tun yana
karamin yake fama da ciwon ciki, kuma kin san yanayin tsananin azabar da yake sha
idan ciwon nan ta tashi, ba godiya zaki yi wa Allah ba da yasa yau ciwon ta tashi
har yake iya yin magana? Ai hamdala zaki yi ki kuma yi gaggauwar taimakawa wajen
kiran Dr dan sauki ya fara samuwa, amma sai ki ce mu barshi sai da safe, Omar ɗin
nawa?".

Momma dai bata wani damu ba, ta miƙa hannunta ta ɗauko wayarsa dake saman bedside
drawer ta miƙo mashi tana ce mashi.

"Allah ya huci zuciyarka ranka ya daɗe, ga wayar".

Karɓa ya yi da sauri, yana rarrashin guyson, number Dr ya shigar dan ya kirasa ya
zo ya duba mashi ɗan lelensa.

Sai binsu da kallo Momma take yi, guyson yana kara narkewa haɗe da kukan shagwaɓa.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



Babban Dr na hospital ɗinsa King ya kira, cike da bada umarni ya ce dik abin da
yake yi ya bari ya yi maza ya zo gida Omar ɗinsa bashi da lafiya.

Cikin girmamawa Dr ya amsa da In Sha Allah ga shi nan zuwa yanzu.

Katse kira King ya yi ya hau rarrashin guyson babu kama hannun yaro, kun san irin
wannan yanayi da zasu ga mutum ya yi kasa gane me yake yi mashi daɗi irin hakan sam
babu daɗi, sai ka ji a takure kake a duniya.

Momma jiki dik a mace sosai, komawa ta yi ta kwanta tana tunanin meyake
faruwa da ita ne haka?.

A haka Dr ya zo part na King ya samesu, da yake kowa ya san Drn King ne sai babu
wanda ya tare mashi hanya, suka bashi dama ya shiga har tsakiyar parlon, sallama ya
yi haɗe da dakatawa a wajen.

Kallon guyson da kyau King ya yi. "Tashi mu je Dr yana parlour ya duba mun kai".

Kai ya fara girgizawa, yana kuka ya ce. "Ni daddy bana san Dr ya dubani, ya tafi
kawai".

"Meyasa to?". King ya jefa mashi tambayar.

"Bana san ya yi mun allura, ni dai gaskiya ya tafi zan ji sauki". Yana magana yana
kara tsananta kukansa.
Lumshe idanunta Momma ta yi kamar mai jin barci, dama ita tasan idan ba Dr Raj ba
babu mai iyawa guyson, Dr Raj ma sai in su Ramish suna nan ne zaku ga ya yarda ayi
mashi allura, nan ma yana kwance jikin ɗaya daga cikinsu suna ɗauke mashi hankali
sannan ake yi.

"Dr ba zai yi maka allura ba, i promised you that".

Kara ƙanƙame King ya yi yana faɗin a'a shi dai ba zai je ba. Ba yadda King bai yi
ba ya ce shi dai a'a ba zai je ba, daga ƙarshe ya hakura ya ce da Dr ya tafi abinsa
dan shi ma ya lura ba ciwon cikin guyson ɗin bane ta taso.

Haka Dr ya juya ya koma asibiti dan ya cigaba da yin aikinsa.

Guyson kuwa King ya cigaba da lallaɓa shi har barci ta ɗauke shi a nan, momma kam
miƙewa ta yi ta basu waje, ta koma room nata.

Tana shiga ta ɗauki wayarta, wata number ta kira wanda aka yi saving da my
happiness. Kwanciya ta yi a saman bed ɗin nata tare da shigewa cikin bargo.

Call ɗin ya yanke ba'a ɗauka ba, tana rike da wayar sai ga shi an biyo kiran
nata. Cikin sanyin murya ta yi sallama. Baka jin me ake faɗa ta cikin wayar sai dai
ita da ta amsa da lafiya alamar gaisuwa aka ɗaga mata.

Jim ta ɗan yi kafin ta sake cewa. "Lafiya ta lou kawai dai ina jin jikina dik a
mace ne yasa voice ɗina ta yi haka".

Shiru ta ɗan sake yi alamar tana sauraran abin da ake faɗe, can sai ta ce.
"No ba barci nike ji ba".

Shi ma King ganin guyson ya yi barci yasa ya kwantar da shi haɗe da ja mashi bargo
ya miƙe ya sauko kasa daga saman bed ɗin.

Waje ya nufa. Bai zame ko'ina ba sai room ɗin Auta, dama kunsan baya yin barci har
sai ya yi mata addu'a.

Ya sha madarar mamakin ganin bata can, har ya mance da ana dinner, fitowa ya yi zai
nufi ɗakin mommarta ya dubata a can sai ya tina da ai ana dinner su Jawad, dan haka
tana can, bai so ya kwanta ba tare da ya yi mata addu'a ba, amma ba yadda ya iya,
sai kawai ya juya ya nufi part ɗin Akka domin ya ganta kafin ya kwanta.

Already yar tsohuwa ta yi barci, dama in baku manta ba ba koshin lafiya ne da ita
ba tin ɓacewar Spender.

Ganin already ta yi barci yasa ya matso a hankali ya tofa mata addu'a tare
da rage mata gudun A.c, sannan ya fito ya koma room ɗinsa.

Ya sha madarar mamaki a lokacin da ya shiga bedroom ɗin nasa, kara waro idanunsa
waje ya yi domin ya tabbatar wa kansa abin da yake gani gaskiya ce ko karya.

Babu guyson babu labarinsa, mutumin da aka bari yana barci, da sauri King ya karisa
gaban bed ɗin dan ya tabbatar.

Tabbas da gaske ne Omar baya cikin ɗakin, to ina yake? King ya jefa kansa wannan
tambaya.

A hanzarce ya juya ya nufi part ɗin Momma dan ya duba ko ya koma can, a
tunaninsa kila da ya shiga ɓangaren Akka ne guyson ya wuce ba tare da sun haɗu ba.

Shi kuwa guyson yana tsaka da barci ne ya ji ana ta ambatar sunansa, tin yana jin
abin da ɗan nesa nesa har ya fara jin hakan a kunnensa, abin kamar a mafarki kamar
kuma a gaske, ba muryar kowa yake ji ba kuma face muryar Auta, tana kuka tana kiran
sunansa.

Hakan yasa ya farka a firgice, har zufa sai da ta wanke mashi face ɗinsa, ya
tsorata sosai na hakan. Kamar zai yi kuka ya fara goge zufar dake face ɗinsa da
tafukan hannunsa.

Kamar daga sama ya sake jin sautin muryar Auta a kunnensa tana kuka tana kiran
sunansa.

Ba ƙaramar razana ya sake yi ba, sai a lokacin ya tuna yau fa tun da rana bai sake
haɗu da ita ba, tin da suka haɗu wajen ɗakin da Chuchu take ana mata ƙunshi, tuna
hakan yasa ya yi saurin saukowa kasa daga saman bed ɗin.

Kai tsaye ya nufi waje da nufin ya je room ɗinta ya dubata. Dai'dai zai gifta ta
wajen part ɗin maman su Yah Ramish sai ya tuna ai ana dinner, dan haka Auta tana
can.

Kamar walkiya haka ya hango wani inuwar mutum kamar na Auta ya fito daga part ɗin
maman Yah Ramish ya nufi hanyar dake wajen na fita waje.

Da sauri ya bi bayanta yana kwala kiran sunanta. Yana zuwa wajen kofar ya yi
mamakin ganin a buɗe, yasan wannan kofa ba'a buɗeta fa.

Amma sai ya danne ya fito waje ta side ɗin. Wayam babu kowa, tsayawa ya yi yana ƴan
waige waige a wajen, babu ko alamar motsin wani halitta, ya ɗan yi mamaki, amma sai
ya ce gizo ne kawai saboda ita ce a ransa yasa yaga kamar inuwarta ne.

A fili ya furta. "Tun da na fito waje kawai bari in bi ta nan in je wajen dinner
ɗin in ga Auta kafin in dawo in cigaba da barcina".

Na'am ya yi da wannan shawara dan haka sai ya nufi wata cikakkiyar hanya da take
wajen dan ya ƙarisa wajen dinner. Yana tafiya babu tsoro cikin nutsuwa da kamala.

Dai'dai zai gifta ta wajen wasu flowers dake shuke kusa da part ɗin uncle Abbas
kwatsam ya hango mutum a tsaye a wajen. Ko tsorata bai yi ba, kamar zai wuce ma sai
kuma ya tsaya ya ce.

"Wanene a nan?".

Shiru ba'a amsa mashi ba, ga kuma mutum a tsaye kamar dai macece, wajen da ɗan duhu
duhu.

Hannu ya zura cikin aljihun jallabiyar jikinsa da nufin ya fito da wayarsa ya kunna
light ɗinta domin ya samu damar ganin wacece a wajen!.

Kash babu wayar a aljihunsa, hakan yasa ya ji babu daɗi, cikin ɗan ɗaga murya ya
sake tambayar wacece a wannan wajen?.

A karo na biyu ma ba'a kula shi ba. Ransa ya ɗan sosu a kan hakan, ya ji babu daɗi
sosai.

Amma sai ya danne tun da bashi da light a hannunsa sai yasa kai ya wuce kawai.
Bawan Allah mai hakuri.

Cikin nutsuwa yake takawa, ba zaka yi zaton yana taka ƙasa ba saboda yanayin
yadda yake tafiya babu wata sauti dake fita. A hankali daga bayansa ya ji takun
mutum alamar ana biyo bayansa kenan.
Kamar ba zai juya ba sai kuma ya juya domin ya ga wanenen?.

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, wata iriyar halittar macece halitta na matsafa,
gata doguwa mai mummunar fuska, baki kamar waga, batada kyan gani bata kuma da
fasali ko kaɗan, ga ban tsoro a fuskarta.

Sai dai ko kaɗan guyson bai tsorata ba, ko a jikinsa, sai ma kallon ƙasƙanci da ya
wurga mata, cike da confidence ya ce. "Ke kuma daga ina?".

Wani irin lankwasa ta yi haɗe da murɗe wuya, ita nan shegiya, ranta ya ɓaci ne
dan bai tsorata ba.

Ganin tana wannan lankwashe lankwashe bata da niyar yin magana zata ɓata mashi
lokaci barci yake ji ne yasa ya sanya kansa ya cigaba da tafiya abinsa, ko ɗigon
tsoro babu a ransa, kaman wanda ya saba ganin aljanu, har da jan ɗan siririn tsaki.

Cikin wata iriyar kakkausar murya wannan aljana ko ace matsafiya ta furta.
"Kai bil'adama maza ka zo nan".

Yadda kuka san bai san Allah ya yi ruwan halittarta a wajen ba, ya cigaba da
tafiyarsa yana kara jan tsaki.

"Kai bil'adama ba nace kazo nan ba? Kada ka kuskura ka kara koda taku ɗaya
ne, zaka mutu idan ka yi hakan!".................Ta yi maganar cikin murya mara
daɗin ji, kamar muryar ƴan shaye shaye yanzu kuma. Ta yi maganar tare da ɓacewa
kamar walkiya ta fito a gabansa.

Dakatawa ya yi da tafiyar da yake yi, a hankali ya ɗago da kallonsa a kanta, sai da
ya bita da kallon up and down kafin cikin sanyin murya ya ce.

"Awww ke nan wai a haka aljana ce ko fatalwa ko? Dallah ni bani hanya na wuce hai,
da wani shegen ido kamar kuliya ta faɗa tarko, ji wani muzurai da kike yi tamkar
kwarton da soja ya kama a gidansa, kina wani taunan hakwara kamar wadda ta yi
shekaru ashirin bata ci nama ba, na zabga maki mari naga karshen iskanci, kina wani
huro hanci kamar ana hura balo balo kenan wai hegiya ko?"............... Ya kai
karshen masifar tasa yana raɓawa gefenta zai wuce.

Riko wuyar rigarsa ta yi ta baya a in da ta yi sama da shi sannan ta wurgar da shi
gefe tana wani taunan hakwara, ga wani lanƙwashe kasusuwan gaɓɓanta da take yi, sai
wani murɗe wuya take yi tamkar taliya ƴar murji.

Haƙiƙa ya ji zafin wurgi da ta yi da shi, abin ya taɓa shi sosai, dan haka sai
ya ciza laɓɓansa da karfi, kamar zai yi kuka ya daure ya miƙe tsaye.

A fusace ya ce. "Ke mushirika kuma shaiɗaniya! Zaki bani hanya na wuce ne ko kuma
sai raina ya ɓaci na gwada maki karfin ikon Allah?".

Kamar wata walkiya sai gata ta bayyana a gabansa. Wani irin lankwashe wuya ta yi
tana muzurai kamar wata kuliyar da ta shiga tarko, laɓɓanta ta shiga taunawa da
karfi tana wani bubbuga kafafunta a ƙasa.

Guyson da babu alamar zai ji tsoronta ne ya ce. "Wannan hauka da kike yi kuma
fa? Ke ni ina da abin yi, zaki bani hanya ne ko sai na gwada maki yadda ake murɗe
kashin wuya, na murɗe taki na karye shege na jefar?".

Ta lura fa guyson bashi da tsoro ta wannan ɓangaren, dama kowa da abin da yake
tsoro a rayuwarsa, kun dai ga shi rago ne ta fannin ciwo, amma ba haka yake
gabaɗaya ba, baya tsoron ire-iren waɗan nan mushirikan.
Da manuniyar yatsarsa ya nunata. Cikin fusata ya ce. "Bani hanya na wuce
shashasha kawai!!".
Ya fara fusata ne, ransa ya fara ɓaci, zuciyarsa tana tafasa, so yake ya je ya
ga Auta ya dawo ya kwanta!.

Kin bashi hanya ta yi tana cigaba da tauna hakwara tana muzurai.

Hannu ya ɗaga da karfi, ya yi bismillah zai wanke shegiya da mari sai ya nemeta ya
rasa, ɓat ta ɓace. Siririn tsaki ya ja tare da wucewa ya nufi dinner hall.

Ransa a ɓace ya cigaba da jan tsaki yana tafiya. Bai yi nisa da barin wajen ba ya
ji alamun ana binsa a baya! Wani sirirn tsakin ya ja, ba tare da ya juya ba ya ce.
"Ai sauri zaki yi mu jera kafaɗa sai ya fi, shashashu kawai".

Guyson fa yana da gaskiya, wlh ko aljani ne idan ka nuna kana tsoronsa ya dinga
azabtar da kai kenan, amma idan ka nuna mashi kai ma shege ne mai ji da kanka, ka
rike ayoyin Allah wlh ta kansa zai yi, tuni zai koma yana shakkarka!!.

Guyson bai sake juyowa in da suke ba har ya kai hall ɗin nan, dai'dai zai shiga
hall ɗin ya juyo, wayam bai ga kowa ba. Tsaki ya sake ja tare da ƙoƙarin juyawa dan
ya shige ciki.

A wani irin haukace aljanar ta bayyana a gaban idonsa, gashin kanta kamar bukkar
shaiɗanu, idanunta kamar jini, bata da fasali sam, ta yi irin wannan bayyana ne dan
su tsorata shi, so suke yi ya tsorata dan ya basu kofar da zasu shiga jikinsa su
rikka sarrafa shi, aljani baya shiga jikin mutum haka kawai, sai bawa ya tsorata ya
bashi kofa.

Wannan tsorata da mutum zai yi shi zai basu damar shiga jikinsa, idan mutum ya
tsorata wannan firgita da yake yi dik wasu kofofi a jikinsa buɗewa suke yi, to
hakan yake bawa aljanu damar samun kofar shi, jama'a sai a kiyayye wannan, arinka
daurewa ban da saurin razana a kan abu, wannan razana da kuke yi yana bawa abubuwa
da dama hanyar shiga jikinku, ciki harda sihiri idan aka yi wa mutum, bayan sihiri
akwai jifa, dik suna samun kofa ce ga hanyar razana.

Ko mushirikai sun nufeka da sharri basa iya cin maka har sai sun turo wani abin da
zai razanaka, kana razana ka firgita zasu samu kofar da wannan aiki nasu zai shi.

Razana ga mutane wannan wajibi ne idan mutum yaga abin tsoro unexpect, to amma ya
zai yi ya kare kansa daga mugayen idan ya razana? Amsa a nan ita ce ambaton Allah,
idan bawa ya razana ya yi saurin furta sunan Allah, hakan zai yi matuƙar kuɓutar da
shi daga dik wata sharri, dan haka ku yi ƙoƙari sunan Allah ya kama bakinku ya
zauna, kune da cin riba, Allah ya kiyaye ya kare dikkan musulmi bakiɗaya.

A wannan karon ya ɗan tsorata kaɗan, saboda unexpect ta bayyana a gabansa, ga
yanayin yadda ta bayyana abin tsoro ne sosai.

Sai dai yana ganinta ya yi saurin furta. "A'udhu billahi mina-sh-shaitanir-rajim".
Fassara. Na nemi kariya daga Allah daga shaidan, wanda aka la'anta

Sai. Allahu la ilaha illa huwa al-Hayyul-Qayyum......... Har zuwa karshe.
Ayatun Kursiyyu ita ce mafi girman kariya daga aljanu da shaidanu.

Sai a karanta Surorin Kariyar

Suratul Falaq (Qul a'udhu bi rabbil-falaq...).

Suratun Nas (Qul a'udhu bi rabbinnas...).
Suratul Ikhlas (Qul huwallahu ahad...).

Sannan a karanta. Bismillahi alladhi la yadurru ma'asmihi shai'un fil-ardi wala
fis-sama'i wa huwa Sami'ul-Alim.

Karanta Salatin Annabi (SAW). Yawaita salati kan Annabi (SAW) yana kawo tsaro da
saukakawa bawa tsoro.

Guyson yana karanta waɗan nan addu'oi wannan mushirika ta ɓace ɓat. Guntun tsaki ya
sake ja kafin ya ce. "Hakan ma bai yi aiki ba, sai ki sake shiri".

Yana gama faɗar haka ya shige cikin ball ɗin abinsa.

===================🔥

Momma ta jima tana wayar da take yi, daga karshe ta tufe da batun Jaish, cike da
damuwa take zayyanawa wanda take waya da ita ɗin damuwar da take ciki a kan ɓacewar
Jaish.

Izuwa yanzu dik wata jarumtarta ta kare, hakurinta ya gaza, tunaninta ya tsaya,
dannewa da take yi ta kai makura, zuciyarta ya kara tsananta ciwo, ta yi kuka a
ɓoye har hawayenta sun kusa dai'na fita, zuciyarta na raya mata Jaish ya mutu ya
bar duniya.

Tas ta gama zayyanewa wadda take waya ta ita halin da take ciki. Hakuri ta rinƙa
bata tana rarrashinta har sai da ta tabbatar da ta ɗan ji sassauci.

Sannan ne suka yi sallama. Gabaɗaya barci ya kauracewa idanun momma, damuwarta ya
dawo sabo a kan ɓacewar jaish, uwa kenan, tamkar ta san yana hanyar tunkarosu, sai
tunaninta ya kara tsananta a kansa, ta kara shiga damuwa, zuciyarta ba bugawa da
sunansa.

Ganin kwanciya ba zai haifar mata da komai bane yasa ta miƙe ta je ta ɗauro alwala.

Sallah ta zo ta fara gabatarwa domin neman Ubangiji da ya sassauta mata wannan hali
da take ciki a wannan masarauta.

A ɓangaren King kuwa, lokacin da ya dawo part ɗin momma dan duba guyson sai ya
iskota tana sallah.

Ganin babu guyson a ɗakin yasa ya juya ya fita, part ɗin mummyn Chuchu ya nufa. Dan
yasan guyson yana santa kuma yana zuwa wajenta sosai.

Nan ma guyson baya wajen, kamar zai je ya tambayi momma, sai kuma ya tuna kila
shi ma ya tafi wajen dinner ɗin ne. Hakan yasa ya ɗan ji sanyi a ransa. Bedroom
ɗinsa ya koma.

Wayarsa ya ɗauko, number Abdussalam ya kira domin ya tabbatar, ana tsaka da taro
kira ya shigo.

Cikin girmamawa Abdussalam ya ɗauka.

"Omar yana wajen taron ne?".

Shi ne abin da King ya tambaya. A lokacin guyson yana tsaye a kusa da shi yana san
tamnayarsa ina Auta. Dan haka da e ya amsawa King.

Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya King ya sauke wanda har sai da Abdussalam ya ji
hakan a kunnuwansa.

Katse kiran ya yi tare da ɗaura wayar a saman drawer, ya kwanta ya janyo bargo,
hankali ya kwanta tun da Guyson yana wajen taron.

=========================🔥

Guyson kuwa, yana sako ƙafafunsa cikin hall ɗin dai'dai lokacin MC ya ce da Jawad
ya riƙe waist ɗin Chuchu ya sumbaceta.

Shiru guyson ya yi yana mamakin abin, shi ba saba zuwa wajen biki ya yi ba,
kunsan brothers ɗinsa dik gwabraye ne babu wanda ya yi aure bare ya san yadda ake
yi, so bai taɓa sanin yadda ake wasu abubuwa ba, hakan yasa ya haɗe dik waɗan da
suke cikin hall ɗin har da su Jawad ɗin da mc ya yi masu sunan ƴan
iska..............😂

Bai kare tsinkewa da mamaki bama sai da yaga da gaske Yah Jawad ɗinsa ya mannawa
Chuchu sumbata a baki, hakan yasa ya kara zaro idanu waje yana mamaki bawan Allah
ustadz.

Tabbas yasan hakan ba laifi bane tun da Jannat matar Jawad ɗin ne, shi abin da ya
bashi mamaki shi ne ko kunyar mutane basu ji suke wannan iskanci, abin da ya
kasance sirrinsu suke bayyanata ga duniya, ina laifin iya ƴan uwansu ne kawai, shi
ne har da baki...........?

Ni kuwa nace guyson kenan, dan dai bai faɗa soyayya bane, yana faɗawa zumuɗi zai sa
ya mance da cewa kiss sirri ne, kila ma abin da zai yi sai ya fi nasu......😂

Ciki ya ƙarisa yana ta aikin rarraba idanu a kan ta ina zai ga Auta?. Har ya
ƙariso kusa da su Jawad bai hango Auta ba.

Kusa da Abdussalam ya tsaya, yana ƙoƙarin tambayarsa ina Auta sai ga kiran King a
lokacin ta shigo.

Shiru ya tsaya har sai da Abdussalam ya karisa call ɗin, nan ne ya ce. "Yah
Abdussalam ina Auta?".

"Kana nufin my wife?". Cewar Abdussalam.

Jinjina kai Omar ya yi kafin ya amsa da. "E ita nike nema".

"Ai tin da nazo ban haɗu da ita ba, kila tana cikin gida, bata zo nan ba, muma
nemanta muke yi".

Guyson bai kawo komai a ransa ba, ya juna ya nufi hanyar fita, dan a tunaninsa ko
tana ɓangaren Akka, dan haka zai je can ya duba ta.

Ƴan dinner sai cin uwar sabada ake yi ana sharholiya, Jawad ansami abin da ake so,
wato yiwa Jannat sumbata, ko kunyar mutane baya ji, shi ba goshinta ya sumbata
bama, bakinta ya sumbata mai gabaɗaya, buri ta cika yau. Kada ku manta wannan
ƙaramin dinner da iya ƴaƴan sarakuna da masu mulki ne kawai a ciki, akwai babbar
dinner da za'a gabatar gobe da misalin karfe 12 na dare.

===========================🔥

••••••••••• BLACK WORLD•••••••••••••🔥

A hankali idanunta suka fara buɗewa, kunnuwanta suka fara jiyo mata sautika na
kukan abubuwan da bata taɓa jin irinsu ba.
Jiri jiri ta fara gani kamar zata faɗi ƙasa. Lokaci guda ta ji wani irin sanyi ya
ratsa mata jikinta har izuwa cikin ƙashi da ɓargo, ga kafafunta babu takalma.

Dishi dishi ta fara gani haɗe da wani irin yana kamar ɗakin da ya ɗebi shekaru aru
aru babu mutane a ciki, a hankali idanun nata suka fara washewa.

Sai kuma menene? Wani irin tabkeken tekun kankara ta gani a gabanta mai shake da
ruwa mai bala'in sanyi har da ice a ciki, wannan dalilin ya haifar da uban sanyi da
ta ji ya ratsata.

A tsorace ta zaro idanunta waje sosai, ta yi iya kallonta bata iya gano karshen
wannan kogi ba, tsoron juyawa bayanta ta yi dan kada ta sake cin karon da abin da
ta gani ya makantar mata da idanu ɗazun.

Tamkar wadda aka ture haka ta tafi luuuu sai cikin wannan tapkeken teku ba
zato ba tsammani.

Wani irin ihun azaba ta saki sakamakon wani irin sanyi da ya ratsa kashin jikinta,
a tsananin razane ta fara ƙoƙarin cetan kanta, Pretty ta fita iya ruwa, dan in baku
manta ba Pretty mayyar san ruwa ce, kada ku manta kullum a wajen korama Kamran yake
iskota, ita kuma Sweetie kullum tana ɗakinsu.

So bata wani iya ruwa ba, hakan yasa ta fara shan ruwan, ita dik ba wannan bane ma
damuwarta, bala'in sanyin dake cikin ruwan ne matsalarta, sanyin ya yi mata over.

Sai fafutuka take yi tana san cetar kanta, abin mamaki kuma bata nitse kasa ba,
ruwan kuma yana da bala'in zurfi. Kamar daga sama taga bayyanarsa a bakin tekun.

Kamar wani aljani haka ya bayyana, sleeping dress launin white color ce a jikinsa,
ya yi bala'in kyau matuƙa, gashin kansa a sake, hakan yasa ya kara wani irin
bala'in kyau, da alama ya kwanta zai yi barci ne

Please Login or Register in order to submit comment