Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 73 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan haka sai ya kwace rabin ya kai ɗan bakinsa.

Ai a miliyan ta ɗago da kallanta a kansa, kawar da kansa ya yi tamkar bai aikata
komai ba, harara ta dallah mashi kafin ta sake daukar wani kankanan. Sarai ya
kalleta, amma ya yi kamar bai ganta ba, shi dai burinsa ya ga ta dawo da walwalarta
tamkar da, ya ga ta koma fara'a tana murmushi ta saki jiki, shiyasa yake tsokanarta
dan ta saki jiki da shi. Amma ita kuma sai wani dojewa take yi tana nuna halin
bosawa, irin ita fa ba zata sauko ɗin nan ba.

Haka ya cigaba da tsokanarta har ta sha fruits ɗin mai ɗan yawa, sannan ta ɗauki
tissue dake wajen ta goge bakinta. Tana cire tissuen daga bakin nata ya miƙo mata
hannu alamar ta bashi, ba musu ta miƙa mashi, a tinaninta zai jefar ne, sai kuma
taga akasin haka, domin kuwa bakinsa ya goge shi ma kafin ya jefar. Mamakinsa ne
sosai yakamata, bata yi zatan hakan ba, shi kuwa ido ya bita da shi yana karewa
jikinta kallo, lokaci guda tinanin abin da ya faru a tsakaninsu ya dawo mashi cikin
kwakwalwarsa, a wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ya tsinci kansa, ya kasa iya
zare idanunsa daga kanta.

"Yah Ramish please ka mayar da ni gida ka ji? Kaga fa har karfe 9 na dare ya yi, a
waje fa muka yi sallar azahar ga shi har dare bamu koma ba, Allah barci nike ji".
Ta kai karshen maganar tana ɗan ɗaure fuska, wai irin yasan ba da wasa take yin nan
ba......... A cikin zuciyarsa ya furta. "Why Aesh take mun kama da royal family?
Meyasa ko magana take yi sai in rinƙa ganin kamar Zash ne yake magana?". A fili
kuma sai ya ce. "Kina san mu koma?"............. Kai ta gyaɗa da sauri alamar e.
Jinjina kai ya yi kafin ya ce to ta tashi su tafi. Wani irin sanyayyar ajiyar
zuciya ta sauke tana ta faman buga hamma, miƙewa ta yi cikin natsuwa, sai dai tana
ɗaga kafa da nufin su tafi kafa ya ce baki isa ba.

Wani irin murɗa mata da cikinta ya yi ne yasa dan dole kafarta ta dakata, abin
kamar wasa, da farko dai sai ta daure, a karo na biyu tana sake yunkurwa zata ɗaga
kafa cikin ya sake murɗa mata da karfi, ƴar kara ta saki wadda bata ma san ta saki
ba, a gaggauce ta sanya hannu ta dafe cikin nata, wasa wasa ta sake sakin ihu mai
ɗan sauti wanda dik bata san ta yi ba. Da farko shi ma ya zaci wasa take yi, sai da
ta yi kara na biyu ne ya fahimci da gaske take yi, cikin natsuwa ya miƙe ya iso in
da take, hannunsa yasa ya tallabota yana faɗin. "Aesh are you okey?".

Kai ta shiga girgiza mashi cikin azaba tana datse idanunta gam da karfi, ganin da
gaske take yi kuma hankalin jama'a ya fara dawowa kansu yasa bai tsaya ɓata lokaci
ba ya yi gaggawar ɗaukarta cak suka nufi cikin motarsu. Ta ƙanƙame shi sosai tana
datse lips ɗinta alamar azaba take sha. Gidan gaba ya sanyata tare da zagowa ta
ɗayan side ɗin ya shiga. Kifa kanta da gwiwonta ta yi tana cigaba da datse lips
ɗinta tana ɗan murkusoso tamkar wadda take shirin yin ɓarin ƙaramin ciki. Hannunsa
yasa ya janyota jikinsa, cike da tashin hankali yake tambayarta menene yake
damunta? Bai taɓa sanin zai damu da ita dan ta shiga damuwa ba sai yau, ya shiga
tashin hankalin da bai san ya shiga ba.

Ƙasa iya amsa mashi ta yi, tana cigaba da murkusosonta tana nishi sama sama.
Gabaɗaya sai ya rikice ya rasa meyakamata ya yi mata, sai kawai ya rungumeta a
jikinsa yana mai ce mata sorry kawai...... Ta ɗauki lokaci mai ɗan tsawo a haka
kafin cikin ya fara lafa mata, a hankali numfashinta ya fara komawa daidai. Wani
irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya duba time a diamond watch dake manne
a hannunsa. 9:40pm. Nisawa ya yi kafin ya yi ƙasa sosai da murya, cikin natsuwa ya
ce. "Aesh are you okey now?"..... Kanta na daga manne da chest ɗinsa ta gyaɗa mashi
alamar e. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Thank god, but menene yake damunki
haka?".

Kai ta girgiza alamar ita ma bata sani ba, sannan ta ɗan yunkura zata bar
jikinsa. Cikin gaggawa ya yi ƙoƙarin hanata yana faɗin. "Ba zaki fama ciwon naki ba
idan kika tashi?"....

(Kun ji mun Ramish da iskanci, kawai dai ka faɗi gaskiya, ba wani ba zata fama
ciwonta ba, dama ni tin daga yanayin sleeping dress ɗinka nike zarginka da uhm uhm
na yi shiru saboda su maman Sultan, amma da na faɗi wani abin, bazaki fama ciwonki
ba idan kika tashi, kai Ramish ɗan duniya ne, bariki da kasuwa yaseen 😅)
Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar e ba zata fama ba...... Ba tare da ya sake yin
magana ba ya saketa. Miƙewa ta yi da kyar ta koma ta jingina bayanta da jikin
kujerar motar tana jan numfashi a hankali hankali. Sorry ya yi mata kafin ya ce
bari ya tada mota su koma gida da wuri dan ta kwanta ta huta. Kai kawai ta iya
jinjinawa, dan ji take yi tamkar an ɗaure mata tongue ɗinta.... Kunna motar ya yi
idanunsa a kanta ya fara driving, dik fa wannan damuwa da ya shiga bai san ya yi ta
ba.

Kai tsaye gida ya wuce da ita yana tinanin lokacin cigaba da yin bincikensa ya yi,
yakamata ya kama masu nikaf yanzu, yakama Leesharh ta bashi haɗin kai wajen bashi
amsar waɗan nan tambayoyi da yake da buƙata da sauran evidence da suke hannunta,
sai dai ya so kaita hospital duba da family Dr ɗinsu wato Dr Raj baya nan, amma
bala'in kishinsu na jinin Modarawa yasa ba zai iya kaita ɗin ba, dama dai Dr Raj na
nan ne, dan haka ya gwammaci ya wuce da ita gida ya je ya ɗan dubata da
kansa........... Ramish namu na amana, zaka yi bayani, wlh akwai case tsakanin
Leesharh, Ramish and Sharifat, ga Abbie a gefe wanda shi already yasan yarsa na san
Ramish, sannan ya rigada ya basa, kuna tinanin su King Badeen zasu yarda Ramish ya
auri bare ya bar Sharifat? Kuna tinanin Mama zata aminta? King Zuhair zai bari? Uhm
abu ne da kamar wuya, dama dai ba'a san da batun Sharifat bane kila iya mama da
King Zuhair su zame barazana da shamaki tsakaninsa da Leesharh, amma an san da
batun Sharifat ai har su Abbie shamaki zasu zame tsakanin Leesharh da Ramish, akwai
case ba babba kuwa.

Da yake yana sharara gudu sosai sai suka isa gida cikin ƙanƙanin lokaci, yana
tsayar da motar a garaje ya juyo da kallonsa a kanta da nufin ya yi mata magana
kenan sai ya ji saukar numfashinta irin na mai barci, ƴar ƙaniya ta ji wuya har ta
yi barcin dole. Shiru ya zubawa kyakkyawar face ɗinta idanu wanda tun da yake da
ita bai taɓa kare mata kallo irin haka ba. Zuciyarsa ce ta furta wow, shi kansa ya
shaida ta haɗu, amma girman kansa ba zai bari ya yardanwa zuciyarsa da ta haɗu ɗin
ba. Sauke kallansa ya yi izuwa saman kirjinta, lokaci guda ƙwaƙwalwarsa ta tinano
mashi yadda ya ganta tsirara a wancan ranar, take ya tunano yadda yaga tula tulanta
muraran a fili.

Wani irin yawu ya haɗiya yadda kuka san ba lafiya ba, da alama abar tasu ta gado ta
motsa kenan.

In faɗa maku abin da baku sani ba my people's, tin lokacin da yake jinyarta na
wannan harbi da ta kare mashi, tin lokacin tula tulanta suka zauna mashi a ransa,
dan kullum sai yaga tudunsu, daga karshe ya gansu muraran, amma bai bari kowa yasan
sun birkita mashi lissafin ƙwaƙwalwa ba, nima saboda shegen bin kwakkwafina yasa na
gano har na faɗa maku, dan haka kada ku bari yasan na faɗa maku......🥱

Ji yake yi tamkar yasa hannu ya yi kasa da zip ɗin rigarta dan ya ga koda iya
tudunsu ne ko zai ji sauki, take wani ɓangare na zuciyarsa ta tina mashi a matsayin
da suke yanzu shi da ita, kallan ɗan iska fa take yi mashi wanda kuma ba halinsa
bane, kunga idan ta kama shi ya zuge mata zip ƙasa mekuke tinanin zai faru? Ai ko
mutuwa yake yi bazata taɓa yardar ba halinsa bane. Tina hakan yasa ya hakura ya
juya haɗe da buɗe side door ɗinsa ya fito, ba dan haka ba Allah saboda rashin
kunyarsa sai ya zuge mata zip kasa ya gansu, amma yanzu neman wanke kansa a gareta
yake yi, ba zai yi wani kuskure ba kuma.
Dik a gajiye yake. Cikin takun jarumta ya zago ta side ɗinta, kofar ya buɗe,
cikin natsuwa yasa hannu ya ɗauketa cak ya fito da ita, da kafarsa ya take kofar ya
mayar ya rufe, sannan ya nufi ciki.

Bata da nauyin barci sam, amma saboda azaban ciwon da ta sha sai barcin nata ya yi
nauyi sosai, shi ma dik a gajiye yake, da kyar ya iya ɗaukarta da kyau. Bai zame da
ita ko'ina ba sai cikin bedroom ɗinsa, kwata kwata ya mance cewa ba matarsa bace,
ya mance ba ɗaki ɗaya suke ba, (saboda iskanci ba) sai da ya shinfiɗeta a saman bed
ɗinsa sannan ya tina ashe ba bedroom ɗinta ya kaita ba. Siririn tsaki ya ja tare da
cewa sai ya yi wanka zai mayar da ita nata bedroom ɗinta, a gajiye yake sosai, bari
ya yi wanka ko zai samu karfi.

Wanka ya shiga a gurguje, sai dai da kyar ya iya yi saboda barci da ya ci karfinsa
ga gajiya. A daddafe ya fito ya shirya cikin sexy sleeping dress ɗinsa masu matukar
kyau da ɗaukar hankali. Yana zuwa ya ganta kwance saman bed ɗin nasa tamkar yadda
ya barta, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kwanta a gefenta, a cewarsa bari ya ɗan
huta kaɗan sai ya tashi ya mayar da ita bedroom ɗinta, sai dai kuma yana kwanciya
barci ta yi awon gaba da shi, dan a wuya yake dama.

To my people's ya kuke ganin farkawarsu suga juna bed guda zai kasance? To ni dai
na yanki gabas, bari in leƙa wani ɓangare in dawo.


🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

A hankali take dafa bango tana kuka ta nufo kofar fita daga bedroom ɗin, lokaci
guda ta ji sansa na juyewa izuwa kiyayya, dan ya gwada mata zallar rashin imani da
tausayi, baya kula da ita sai idan buƙatarsa ta taso, gaskiya Yah Jaish ya kai
makura wajen san kansa da zalinci. Da kyar ma ta iya mayar da sleeping dress ɗinta
jikinta, yadda kuka san mai koyan tafiya haka ta zama.

Parlournsa ta fito, azabar da take ji yasa ta ji ba zata iya taka kafafunta har ta
isa part na momma ba, dan haka sai ta ce gara ta shiga bedroom na mama Haulat ta
kwana a can, zuwa da safe sai ta koma wajen momma. Parlourn gabaɗaya baibaye yake
da duhu, wutar a kashe take. A haka take laluɓawa da yake tasan a in da ɗakin mama
Haulat ɗin yake, sai ta nufi can, hawaye wani na bin wani tamkar an buɗe tap......
Da kyar ta iya gano kofar ɗakin, tana ƙoƙarin laluɓar handle na kofar ta tura ta
shiga sai ji ta yi kamar daga sama an ɗauketa cak, ga shi cikin duhu ne, amma kuma
dik da ba haske ta gane shi ne, dan idan zata ƙasa gane kowa ban da sanyin
zuciyarta, shi ɗin na daban ne da ya fita daban ko a cikin duhu.

Sai dai a tinaninta abin da ya yi mata yanzu zai sake mai da ita ya yi mata dan
azzalumi ne a cewarta, dan haka sai ta fara ƙoƙarin kwatar kanta. Bai kulata ba, ya
cigaba da tafiya, sai mutsu mustu take yi, amma dik a banza, dan bata tashi sanin
in da take ba sai da ta ji kanta a cikin ruwa mai zafi sosai. Ihu ta zunduma, a
cikin duhun ta fara laluɓar abin da zata samu ta kama ta fita, ruwan ya yi mata
zafi sosai. Sai dai bata iya taɓo komai ba, har shi bata ji motsinsa ba, yana
sakata a cikin ruwan bata sake jinsa ba. Tsananta kukanta ta yi tare da fara faɗin.
"Na shiga uku, momma wlh Yah Jaish zai kashe ni, wayyo bappana, dan Allah ku mayar
da ni wajensa".

Tsabar ta birkice tana kuka haɗe da sambatu bata ji lokacin da ya janyota ya
mannata da kirjinsa ba, shi ma ya tsunduma cikin ruwan. Sai da ta ji sanyayyar
muryarsa yana faɗin. "Babu wanda zai mayar dake wajen bappan naki, kina nan tare da
ni, ya isa haka kukan"......... Sai sannan ne ta gane ashe tana jikin mutum. Cike
da tsoro ta sanya hannunta tamkar mai tsoron taɓa abu ta fara laluɓarsa cike da
fargaba. Tabbas shi ne, ƙoƙarin raba jikinta da nasa ta yi tana kara tsananta
kukanta, cikin sauri ya kara kankameta yana faɗin. "Ina zaki je kuma?". "Yah Jaish
dan Allah ka kyaleni haka, wlh ba zan iya ba, zan koma wajen momma ne in ce ta
mayar da ni wajen bappana".

Ƙara matsar da lip ɗinsa dab da kunnuwanta ya yi, cikin raɗa ya ce. "Ni na bada
izinin a mayar dake ne? Ko kin manta ni nake da iko da ke ne?".
Shiru ta yi ta rasa abin cewa. Hannunsa yasa ya kara jawota jikinsa, cikin
dabara ya ɗan yi ƙasa da hannun nasa a in da ya fara bubbuɗe mata kafafunta ruwa
yana ratsata da kyau. Kankamesa ta yi saboda zafin ruwan, tana san kurma ihu amma
tana fargaban abin da zai iya sake aikata mata, rufin asirinta dai ta yi
shiru....... Shi kuwa, sai da ya buɗe mata kafafu ruwa ya ratsata da kyau, sannan
ne ya hauro da hannunsa sama, saboda tsabar tabbatar rashin kunya sai ya sanya
hannu a saman nipple ɗinta, a hankali ya fara shafowa, a kunnenta ya fara raɗa
mata. "Wajen yana yi maki zafi ko? Na basu wahala ko?"........ Kai Jaish akwai
tsaurin ido, kunyar rashin kunya, ko da yake ba laifinsa bane, dik kunyar mutum ya
zo wannan ɓangare sai dai ace mashi karuwan master room.

Banza da shi ta yi tamkar bata ji shi ba, ba wai kuma dan raini ko wani abin ba,
sai dai bata da abin faɗe, ya goge mata hadda kaf. Cigaba ya yi da shafasu abinsa,
yana raɗa masu wasu sexy word a kunne wanda bai bawa kowa damar jin abin da yake
faɗa mata ɗin ba. Ai bata san time ɗin da ta natsu tsit ba, kukan nata ma da take
yi sai daga baya ta nemesa ta rasa, bata san lokacin da ya gudu ba, kalaman mijinta
ya ɗauke kukan ba tare da ta shiryawa hakan ba, cikin ƙanƙanin lokaci yasa ta saki
jiki da shi, ta kwanta shiru a saman kirjinsa tana sauraron hot words ɗinsa, har
ɗan sakin murmushi ta fara yi. Uhm maza, maza sai shirin Allah, yanzu dai har ya yi
mata wayo ta yarda da shi, shikenan ya samu abin da yake so, da abar tasu ta motsa
hankalinsa a kwai yana da in da zai rageta.


•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A can gefe guda kuwa, tattabaru biyu suna can suna nasu aiki, sai rarrashi Jawad
yake yi dan ya karya alkawari, ance mashi iya romance ya zarce har izuwa babban
sashe, dan haka Jannawad dai taki yarda, muma team ɗinta ba zamu yarda ba, ai iya
romance kawai muka ce, me ya kaisa ga babban sashe idan ba rashin alkawari ba?
Chuchu kada ki yarda.

Bawan Allah ya ɗan ban tausayi, ya dukufa da girmansa da kimansa, da mutuncinsa a
gari, kowa daraja shi yake yi sai ga shi ya kwantar da kai yana yi mata karamar
murya, burinsa kawai ta ce ta yafe mashi, gaskiyar Jaish da ya ce Jawad ya gama jan
mashi mutunci a kan titi ya yi yaga yaga da shi, shikenan fa yanzu Chuchu tasan
abin da suke da shi, kai gaskiya Jaish kada ka yarda, idan ka yafe mu ƴan team naka
bamu yafe ba, idan kuma ka raba wannan aure King ya tsine maka kabi bola babu
ruwanmu, ko ya kuka ce my people's.......😅

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥


A ɗayan ɓangaren kuma sai dirama suke bugawa, hakuri iya hakuri guyson ya bata a
kan dan Allah kada ta sanar da momma abin da ya yi mata, dik izzar sarautar nan
tasu har dukar mata da kansa ƙasa ya yi yana bata hakuri, amma taki fir ta ce dole
ya buɗe mata kofa ta fita, shi kuma ya gargame ya ce sai ta yafe mashi.

Faɗi yake yi. "Dan Allah kada ki je ki faɗawa su momma, zan buɗe maki nawa rigar
nima ki rama ba shikenan ba?". Ya faɗa yana kallan face ɗinta. Kallon uku saura
kwata ta watsa mashi kafin ta amsa da. "To ni ce maka aka yi ƴar iska ce? Ni ina da
mutumci kuma ina da karfi, ba sakaliya irin ka bace". Ta kai karshen maganar tare
da murguɗa mashi baki.
Marairace mata murya ya yi tamkar zai yi kuka, ƙasa ya kara yi da murya
sosai kafin ya ce. "Ni dai please don't let anybody to know kin ji? Ki yafe mun ba
zan kara taɓawa ba"...... Tsalle ta yi ta dire kafin ta ce. "Okey dama kana da
niyar sake taɓawa kenan ko?".

A hanzarce ya girgiza mata kai kamar wani yaronta, bawan Allah yanzu ma fa kuskure
aka samu ya taɓa ɗin ba halinsa bane, ashe bala'i ya taɓowa kansa bai sani ba.
Harara ta dallah mashi kafin ta fara zagaye shi tana binsa da kallon up and down.
"Shekarunka nawa ne?". Ta faɗa tana dawowa ta gabansa, irin ita babban nan. ......
"19 to 20 haka". Ya bata amsa a sanyayye, shi dai damuwarsa kada ta faɗawa su
Jaish, idan zata tsaya a iya faɗawa momma shikenan bashi da wata matsala, amma idan
su Jaish suka ji me za su ce? Kuma wlh yasan idan ba lallaɓata ya yi ba kowa a
cikin kingdom ɗin nan sai yasan ya taɓa mata kirji ta ja mashi raini har wajensu
Omaid, to wai shi me ma ya kaisa ne?.

"19 to 20 years? Ashe ma baka wani fini sosai ba, amma ya aka yi ni jaruma ce kai
kuma rago? Kenan girman banza ka yi?". (Allah mai iko🤔 wani abu sai Mahreeh,
shekaru 7 fa ya bata amma wai bai wani fita ba saboda shegen san girma.)

Kai ya girgiza mata a karo na biyu. "Ni ba rago bane, kawai bana iya jure rashin
lafiya ne, kuma ciwon nawa yana da tsanani sosai ba yadda kika zata ba, ban da
ɓangaren ciwo babu wani abin da ba zan iya yinsa tamkar jarumi ba". Tun da ya fara
magana idanunta a kan kyawawan roman lips ɗinsa irin na Auta........ "Kai ko lips
ma baka da shi, ji bakinka kamar babu saboda ƙanƙata". Tana magana tana binsa da
irin kallon da take yi wa su Abu a kauye.

Shiru ya yi dan bashi da abin faɗe, tun da ance bashi da baki ai dole ya yi
shiru....... "Buɗe mun rigarka nima in taɓa shikenan sai in yafe maka". Ta faɗa
tana kai kallanta ƙasa, ita kanta abin ya yi mata nauyin da ba zata iya haɗa ido da
shi ba idan zata aiwatar da hakan, amma saboda tarihin rayuwarta bata yafiya yasa
ba zata iya haƙura ba sai ta rama..... Shi kuwa, wani irin sanyi ya ji a ransa, ko
ba komai zata rufa mashi asiri idan ta rama, dan haka a hanzarce ya ɓalle butiran
rigar ya cire mata, kanta a ƙasa taki ɗagowa saboda iskanci ya cika ƙwaƙwalwarta,
kai wlh Mahreen sai kun sakata a addu'a, ni kam Princess Teema ta fi karfina!.

Zare white singlet dake ciki ya yi, ya rage daga shi sai short, sannan ya ce mata.
"To ga shi na cire maki ki rama". Tamkar zai yi kuka ya yi maganar. Slowly ta fara
kallansa daga ƙasa tana haurawa sama. Ƴar ƙaniya sai da ta ji wani irin mummunar
faɗuwar gaba, kirjinta ya bada bugun dum!!! Dum!!! Saboda kirjin nasa da ta gani, a
tinaninta bashi da karfi, sai kuma ta kalli yana da murɗaɗɗen jiki, ta yi mamaki
sosai, amma fa ta kasa iya yin sama da kallonta, a iya kirjinsa ta tsayar da
idonta, dik rashin kunyarta ta ji shakkar haɗa ido da shi at this moment.

"Taɓa ki rama to". Ya sake faɗa idanunsa a kanta, ko kaɗan bai ji burgesa da take
yi a da ya ragu a ransa ba, sai ma karuwa ya yi, yana mugun san confidence ɗinta da
tsayawa a kan maganarta idan ta yi. Babu kunya ba tsoron Allah ta ɗago hannunta na
ta kerma ta nufi kirjinsa da shi da nufin ta taɓa ita ma ta rama. The way tana
matsar da hannunta garesa, the way hannunta yana tsananta kerma, amma dik da haka
ta danne, ta nufesa. Ya zuba mata idanu kawai yana jiran ta aiwatar da nufinta ya
mayar da kayansa.

Tana gab da taɓa shi sai ta dakata tare da fashe mashi da kuka mai ɗan sauti. Ɗan
zaro idanunsa kaɗan ya yi, a rikice ya fara tambayarta lafiyarta kuwa? Me kuma ya
sake samunta?. Kin kula shi ta yi, ta cigaba da kukanta. Matsawa kusa da ita sosai
ya yi ya hau rarrashi, yarinya sai kace mai aljanu, shi yanzu to me ya yi mata da
take kuka.

Yana can yana tinanin me ya yi mata sai jin voice ɗinta ya yi tana cewa. "Saboda
kasan ba zan iya ramawa bane yasa ka ce in taɓa nima, wlh to Allah ya isana kuma
ban yafe ba.........". Cikin ɗaga murya ta yi maganar. Gudun kada tasa a gane halin
da suke ciki yasa ya yi gaggawar janyota jikinsa ya rungumeta, muryarsa har tana
kerma wajen cewa. "Please kiyi shiru, zan yi dik abin da kike so, amma please ki yi
shiru kin ji?". Kin kula shi ta yi tana cigaba da kukanta. Damuwa da tashin hankali
yasa ya yi gaggawar kamo hannun nata ya ɗaura a saman kirjin nasa dai'dai nipple
ɗinsa, a rikice ya ce. "To ga shi nan yanzu ai kin taɓa kin rama, dan Allah ki
yi.......".

Kasa iya kai karshen maganar ya yi sakamakon idanu da ta wurgo mashi, ga shi suna
kusa kusa da juna, ta bushe mashi tamkar wadda aka zarewa ruhi, ƴar ƙaniya ta ji ta
taɓa kirjin maza, tuni bakin nata ya mutu, kukan ma ta nemesa ta rasa. Ya ɗan
tsorata ganin yadda ta kafesa da ido bata wani motsi, a rikice ya kai hannu ya fara
jijjiga kumatunta yana ambatar sunanta. Ina bata motsa ba, a nan ya fahimci sume
mashi a jiki ta yi, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya rage tsawonsa ya
ɗauketa zuwa saman bed ɗinsa, sai faman nisawa yake yi. Ya tsira daga bala'inta!!

Yana kwantar da ita aka fara knocking na door ɗin nasa, wani irin fargaba ya ji,
gabansa ne ya yanke ya faɗi, murya na rawa ya tambayi wanenen? Daga waje Omaid ya
amsa mashi da shi ne. Ai sake rikicewa ya yi, abin da yake gudu ne yake shirin
faruwa, wato kannensa su kama shi da ita shikenan girmansa ya zube. Rasa me zai
cewa Omaid ya yi, ga shi bai isa ya hana shi shigowa cikin ɗakin ba.

My people's ko kuna da wani abin cewa? Ko kuna da dabarar da zaku faɗawa guyson ya
yi dan ya tsira daga Omaid ya gane suna tare da Mahreen?. To idan kuna da shawara
ku yi gaggawar bashi kafin in dawo daga Black world.


🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥

Washegari da safe, sanye take cikin jelly dreass launin pink, ta yi masifar kyau,
ta ɗaure haɗaɗɗen gashin kanta, da karfi da ya ji Sweetie ta koyi yawo babu
ɗankwali, aka ce zama da maɗauki kanwa shi ke kawo farin Kai.

Tsaye take a tsakiyar bedroom na Ronnie, kyawawan kafafunta na sanye cikin flip
floor launin white color, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm sosai, sai wani sheki
yake yana wani ɗaukar hankali, sai launin dark purple lips ɗin nata ya kara turuwa
sosai, idanunta sun kara kyau tamkar ta sanya kwalli alamar tana cikin farinciki
sosai kenan. Ronnie dake zaune a tsakiyar bed ɗinsa sanye da pj's dress a jikinsa
ne ya harbeta da wani ɗan ƙaramin throw pillow yana faɗin. "Ba zan barki ba, sai
kin faɗa mun shirinki".

Yana jefo mata pillown ta yi gaggawar juyowa haɗe da buɗe tafin hannunta, take
magic ɗinta ya fita ya daki pillown, kai tsaye ya koma ya daki face ɗin Ronnien.
Ƙayataccen murmushi ta saki kafin ta ce. "Alhaki cuicuyo, yanzu dai pillownka ya
koma kanka". Tana magana tana kara faɗaɗa murmushinta, wlh sai ka ji ba zaka taɓa
gajiya da kallanta ba matuƙar tana wannan sanyayyar murmushin nata. Shi kansa Black
Tiger bai san ɗauke idanunsa daga kanta idan tana yi, shi ma dai Ronnie yana
kyatsawa sosai, tana bashi a jikinsa.

Cikin zafa ya miƙe tare da dirowa kasan bed ɗin. Da gudu ta watsa ta nufi waje tana
faɗin. "Idan ka isa ka kamani, in ka kamani zan baka satar amsa"....... Tsayawa ya
ɗan yi tare da riko waist ɗinsa da hannayensa dikka biyu, a ɗan kule ya ce. "Is
better for you da

Please Login or Register in order to submit comment