Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 87 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi kafin ta ce. "Akwai dalili, akwai
abin da nike san kammalawa ne". "Sisterrrrrrrr". Ya faɗa yana ɗan jan sunan alamar
kamar warning yake yi mata. "Don't worry ba zan yi abin da zai kawo mana problem
ba". "Are you sure?". Sure ta bashi amsa tana wucewa gaba!. "To please kada ki yi
magana sosai, and komai zaki gani ki yi shiru kin ji?". Jinjina kai ta yi alamar ta
yarda.

Ɗan gudu ya yi ya kamota tare da rike hannunta suka wuce suka nufi gym ɗinsu. Yana
zuwa ya hau motsa jiki, a hankali ya fara cigaba da koya mata, push up ya fara yi,
a nan Black Tiger ya zo ya samesu suna yi, bai bi ta kansu ba ya fara nasa gym ɗin,
tin da ya shigo wajen ta tsaresa da kallo, ya yi masifar kyau cikin wasu shegu kuma
tsadaddun gym wears, shi kuma sam bai kalli in da take ba ya fara aikinsa.

After some minutes Ronnie ya ce mata ta zo su fara faɗar takobi da ya fara koya
mata last week, cike da murna ta fara tsalle tare da tasowa ta nufesa. Wani
keɓanɓɓen waje suka shiga can ɗan gefe da gym ɗin, wajen tamkar duniyar mafarki
yake, ga ruwa yana zuba ta sama kaɗan kaɗan kamar shower haka. Dai'dai tsakiyar da
ruwan yake zuwa ta zo ta tsaya yana jiƙata, shi kuma zaro takobi marasa tsawo da
nauyi sosai guda biyu ya yi, ya miƙa mata guda ɗaya ya riki ɗaya a hannunsa, sannan
ya ciro hulunar faɗa masu kariya ga kan mutum, ya bata ɗaya ya ɗauki ɗaya, gabaɗaya
wajen shake yake da kayan yaki kala kala.

Faɗar wuƙa suka fara yi ruwan nan na zubowa a kansu yana cigaba da jiƙasu, yanzu ta
ɗan fara iyawa ya fara yi mata manya manya, da a hankali hankali yake yi mata. Ita
ma ta zage tana san ta ko yi abubuwan, dan suna burgeta, yana ɗaya daga cikin
dalilin da yasa take san Ronnie, saboda iya faɗarsa ga shi ɗan wrestling, bugu da
kari yana da horon mayaƙa, abin ƙayatarwa kuma ɗan wasa ne, kwallon kafa, basket
ball, kai dik wasanni yana bugawa har snooker bai bari ba, ga su skater dikka,
shiyasa ta ce ya koya mata ita ma ta zama kamarsa.

Cigaba da wasan takobinsu suka yi gwanin birgewa, tana ɗan tsoro tsoro sai da ya ce
mata kada ta damu, ta kawo mashi kowani irin hari ne ba zai ji ciwo ba, zai iya
tarewa, ita kuma ta ce kada ya zo bai tare ba ya ji ciwo, kai ya girgiza mata
alamar kada ta damu, shi fa da yayansa yake wannan training ɗin, dan haka zai iya
tarewa, kuma idan har bata kawo hari kowacce iriya ce ai ba zata taɓa iya yaki ba,
dan haka dole ta kawo hari. Jin abin da ya ce yasa ta ɗaga takobin hannunta da
karfi ta nufesa zata sara mashi a wuya.

Ɗan juyawa gefe ya yi a in da ta wuce ita da takobin nata gabaɗaya ta tafi zata
kifa, hannunsa ɗaya da bai rike takobi ba yasa ya tallabo flat tummynta, dama
tafiya ta yi zata kifa, sai ya tarota ta gaba gaba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da
ɗagowa cikin zafa, wai irin ita ma yanzu zata fara yi mashi da zafa tin da ta ga
yana tarewa, ashe da gaske zai iya tarewa ba zai ji komai ba!!. KAI SWEETIE WANI
LOKACI AKWAI SHIRIRITA, TO MEMA TA IYA DA HAR TAKE GANIN IDAN TA KAWO MASHI HARI BA
ZAI IYA KAREWA BA?! WAI ITA A TINANINTA TA ƊAN IYA WANI ABIN.......😅

Yunkurin sake kai mashi sara ta yi, ina ai sai ya fara wasa da ita tamkar wata ƴar
tsana, ya cigaba da bata wahala har sai da ta gaji ta ce. "Lovely bro am tied, ka
barni haka, ko sau ɗaya ban yi nasara ba fa". Jefar da takobin ya yi tare da jawota
jikinsa yana faɗin. "Ai in dai a kai'na ne ba zaki taɓa yin nasara ba, muje ki yi
wanka". Turo baki ta yi. "Soon zan yi nasara". Jinjina kai ya yi. "Zan yi fatan
hakan, zan so gani lovely sis ɗita ta yi nasara". Raba jikinta da nasa ta yi tana
jefar da takobin kasa kafin su nufi cikin gida. Wanka ta fara yi kafin ta bashi
waje ya shiga, shi ma wanka ya yi.

Shiryawa ta yi cikin wani haɗaɗɗen gown fari irin mai breast cuf ɗin nan, so kana
iya ganin tudun matasan tula tulanta da suke gwanin birgewa, ta yi masifar kyau
matuƙa, ga kayan ya fitar mata da coca cola shape ɗin jikinta sosai, dan irin
malesian gown ɗin nan ne, ya bi surar jikinta and rigar bai kai mata har ƙasa ba,
da kaɗan ya rufe mata cinyoyinta, ta sanya wani high heel, yadda kuka san wacce
zata tafi club party, ta zuba chewing gum masu balai'n kamshi a bakinta tana wani
tauna, da alama yau da rashin mutumci take ji. Fitowa ta yi ta nufi sama kololuwa
tana gyara headband ɗin kanta, wai hoto zata je ɗauka a saman, ɗazun taga wayar
Ronnie a wajen.

Tana haurowa shi kuma yana saukowa sanye da pj's dress a jikinsa, ya yi fitina a
cikin kayan. Wuceta ya yi tamkar bai ganta ba, ita ma wucewa ta yi kamar bata gansa
ba. Har ta ɗan yi nisa sai kuma ta ɗan ɗaga hannunta sama kamar mai neman wani abin
a sama, a hankali ta juyo tare da cewa oh irin ta gane magana take san yin mashi
ɗin nan. Gently ta ce. "Hi big bro! One minute please!". Ta faɗa tana sauke
hannunta izuwa saman waist ɗinta.

Dakatawa ya yi da tafiyar ba tare da ya juyo ba, alamar dai ya bada one minute da
aka tambayar. Cike da yanga ta tako ta nufosa, dik Ronnie ya koya mata wannan
iskanci, shi ya yi mata wayo ya ce ta rinƙa yiwa Black Tiger haka zasu yi nasara,
bata san wayo ya yi mata dan yasa su rufta da san juna ba, shi a nasa tinanin idan
ba soyayya ba akwai matuƙar wahala Black Tiger ya iya canzawa, sannan ba zai taɓa
musulunta ba idan ba ya kamu da soyayyar musulma ba, Sweetie ta faɗa mashi babu
aure a tsakanin namiji krista da mace musulma, to shi ne yake san Black Tiger ya
rufta kogin sonta, idan ya yi zurfi sai ace ba zai mallaketa ba sai ya musulunta,
wannan ne shirin Ronnie, amma bai sanar da kowa ba, ko ita Sweetie ya ɓoye mata,
shi dai burinsa yayansa ya dawo hanyar tsira, shi ai ya ɗanɗani daɗin musulunci har
sha'awa yake yi wa wani, Allahu Akbar, musulunci duniya!! Musulunci ya yi, wanda
baya musulunci wlh an barsa a wahalarce, ya kuma bonu ya lallace!! Yanzu dai Ronnie
ma ya shirya na shi plant ɗin, zai baza capacitynsa ba tare da saninsu ba. Sai dai
shi kuma Ronnie ɗin abin da bai sani ba shi ne, DUNIYAR SHAIƊANU ba zasu taɓa barin
Black Tiger ya yi aure ko ya yi soyayya ba sai dai wani ikon Allah, amma wlh babu
batun so ko aure a tsarin da suka tsara mashi da sihirinsu tin yana yaro, sai dai
mu musulmai mun san suna nasu ne Allah kuma shi ne the best planner, ya gama
tsarawa Black Tiger dik wani abin da zai yi a rayuwarsa. A tsarin DUNIYAR SHAIƊANU
manyan malamansu ma masu takewa mahaifin Black Tiger baya basu da ikon yin soyayya
ko aure, dan sun ce mata rauni ne, su ba zasu taɓa yarda da abin da zai raunata
zuƙatansu ba, mahaifin Black Tiger shi ne kaɗai aka amincewa da ya rinƙa tarewa da
mace, shi ma ɗin kuma idan ya tare da mace har ta samu ciki ta haihu, to tana
haihuwa za'a kashe uwar su ɗauki ɗan, dan a cewarsu uwa mace barinta haɗari ne, dan
mata suna da zuciya mai rauni da tausayi sosai, so zata iya koyawa yaron rauni da
tausayi. Ga dikkan alamu ita ma mahaifiyar Black Tiger kasheta suka yi. (Ni kam ma
anya ba gawarta bane suka yi mutun mutuminta a cikin fadarsu na in da na ce maku
sun cakawa mace wani dogon karfe tin dafa bakinta har ya fito ta gabanta? Kun tina
wajen? Da alama tin da aka yi gunkinta ita ce matar shugaban nasu wato uban Black
Tiger kenan)

Bala'i can, akwai cakwakiyar na gasken gaske. Amma my people's ya kuke gani idan
Allah yasa Black Tiger ya musulunta, kuma yasan daɗin uwa ya fara neman uwarsa? Me
zai faru?.

Uhm gaskiya musuluntar Black Tiger yana da matuƙar wahala, saboda ko da ya so su ba
zasu kyalesa ba, dan ma dai yana cikin killacewar da babansa ya yi mashi ne, amma
dik ranar da ya fito shikenan ya koma cikinsu, yanzu haka sai shirin yadda zasu
samu su ɗaukesa suke yi, akwai kalubale mai girman gaske a gaban Ronnie da Sweetie,
amma da yake Sweetie ba haka ta zauna ba, tana kai kukanta ga Allah tana faɗa mashi
sunan Black Tiger a kowacce Sallah nata idan ta yi, da izinin Allah kuma Allah ba
zai basu kunya ba!!.

Kai my people's kun ji Ronnie ko? Zai jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, wai ya yi wa
Black Tiger and Sweetie wayo su kamu da san juna! shi ma fa ɗan duniya ne wasa
wasa!!.

Yana tsaye ta iso in da yake, zagowa ta yi ta gabansa ta tsaya!. "Shi ne zaka ganni
kamar baka ganni ba ka wuce ko?". Ta jefa mashi tambayar kamar zata saka mashi
kuka. Shiru bai tankata ba, sai ma da ya ɗan kara ɗaure angry face ɗinsa. "Kasan
me? Kome ka yi kyau yake maka, da ka ɗaure fuskarma ka kara kyau ne"..........
KALAMAN RONNIE TAKE YI MASHI, DIK SHI YA KOYA MATA!!

Idanunsa a kan kirjinta bai ce ko uppan ba, kunga yanayin rigar tata, so yana iya
kallan tudun tula tulanta. Yatsun hannunta ta kyasta mashi a saman face ɗinsa,
nisawa ya ɗan yi tare da cewa.

"Ke wai bakya jin tsoro ne a rayuwarki?". Zazzakar muryarsa ya daki dodan
kunnuwanta.
Ɗan siririn murmushi ta saki wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana.
"Menene kuma tsoro?". Ta yi maganar tare da gyara rigar jikinta da kyau. Sai ka
ce dole aka sakata ta sanya rigar, ta biyewa Ronnie zai yi mata wayo bata sani ba,
wato fa dik iliminka idan mutum ya rigaka zuwa duniya to fa wani abin sai ka sarara
mashi! Yanzu dai ya nuna mata fifikon shekaru!.

Kasa yin magana ya yi ya tsareta da idanu yana kallon tula tulanta da suke tsole
mashi idanu a maimakon face ɗinta.
Ƴan yatsun hannunta guda biyu ta sake kyasta mashi a saitin face ɗinsa tare da
hura chewing gum da take tauna ta yi balo balo kenan.
Kamar wani maras gaskiya da sauri ya dawo da kallonsa a kan face ɗinta yana
wani ɗaure fuska irin ya basar ta kamashi yana kallonsu ɗin nan.

"Big bro, face ɗina fa zaka kalla mu yi magana ba wani waje ba, da ni kake magana
ba da kirjina ba, wai nace ba, mema kake kallo a kirjin nawa? Ko dai............".
Dakatawa ta yi da yin maganar ta kasa ƙarisawa sakamakon zaro mata kaifafan sexy
eyes ɗin nan nasa da ya yi.
Wato wannan ƙaddarar tasa ta zama tacacciyar ƴar ikka, kuma yasan dik waye ya
ja mashi hakan, dole ya ɗauki mataki, yarinya ce ta wuci dik yadda yake tunani,
yanzu ya shiga uku tun da ta kama shi yana kalle mata tula tula, wannan zance ba
zai tsaya iya nan ba, to wai ma me ya kaisa? Shi anya ba zai ɓatar da yarinyar nan
ba kowa ya huta?.

Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da, ai ba zaka iya ɓatar da ita ba, ka
manta ita ɗin kaddarar ka ce, zama da ita dole, wannan shi ne ba saki ba karin
aure, mutu ka raba takalmin kaza in ji hausawa..............😂

Kai Hasbunallahu wani'imal wakil, wato ana wani iyashege a wannan gida.😂

Zata sake yin magana tana ƙoƙarin huro chewing gum ɗinta ya ɗan sanya mata zarra ta
hanyar matsar da face ɗinsa dab da ita yana zare mata ido. Ai a miliyan ta yi baya,
ta tsorata sosai. Ɗan gocewa high heel na kafarta ya yi saboda baya da ta ɗan yi ba
shiri, hakan yasa chewing gum da ta huro ya ɓata mata fuska, tafita ta yi ta zube
ƙasa a saman gwiwowinta!. Wuceta ya yi da sauri ya sauka ƙasa, dan tana neman kawo
mashi wani sabon al'amari.

Turo baki ta yi, a fili ta ce. "Allah ba zan barka ba, tin da ka sanya na faɗi kasa
kuma na ɓata face ɗina da chewing gum sai na ɗauki fansa, ai a yarjejeniyarmu mun
yi da kai ba zaka taɓa mun abin da bana so ba kuma ba zaka taɓa bari na cutu ba,
amma da kanka ka cutar dani yanzu". ME KUKE TINANIN ZATA YI MASHI?.

Tana ƙoƙarin miƙewa Ronnie ya hauro sama da gudu yana faɗin. "Sister come and see
our surprise, Big Bro ya yi mana surprised mai matuƙar kayatarwa, za'ayi shagali a
ranar white Happy and Sad day ɗinmu, zamu fi kowa kyau".

MEMENE WHITE HAPPY AND SAD DAY?

kalar fari shi ne fav kalar Black Tiger, wannan dalilin yasa ya sanyawa wannan
rana sunan white Happy and Sad day, sau ɗaya suke shagalin wannan rana a shekara,
rana ce da babansa ya mutu, kuma rana ce da a cikinta babansa ya karɓawa birnin
Black world takardar zama ƙasa mai cin gashin kanta, wato rana ce da suka samu
ƴancin kai! So ranar suna shagali da rana, da daddare kuma su yi kuka da jimamin
mutuwar babansa, the whole ranar white clothes suke sanyawa, komai fari
tas............ Wato babu kamar addinin musulunci fa my people's, wai ayi shagali
da rana, da daddare kuma ayi kuka na jimami, kai jama'a Allah ka dawwamar da mu a
cikin musulunci!!.

Miƙewa ta yi tana faɗin. "Menene white Happy and Sad day kuma?". Hannunta ya zo ya
riko yana faɗin. "Muje ki ga kayan da Big Bro yasa aka kawo mana daga kasar
England, idan kika gani zan faɗa maki menene white Happy and Sad day da irin
shagali da kuka da muke yi"...... "Shagali da kuka kuma?". Ta tambaya cike da
mamaki......... Wai shagali da kuka, dole kanta ya kulle......................
"Let's go zan yi maki bayani idan muka je bedroom". Ya kai karshen tare da jan
hannunta, bayansa kawai ta bi mamaki kamar ya kasheta!!. My people's wannan rana ta
W.H.S.D ɗin nan nasu fa ba ƙaramin gagarumin rana bane wanda kura zai tashi a
cikinsa, uhm zamu sha shagali kuma mu sha kuka, kowacce shekara da Floris ake yi,
amma wannan babu ita.............. 😥

-----------------------------------------------🔥
🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER.🔥🔥🔥

A yau jirgin momma ya ɗaga zuwa Dubai, tamkar Smart ya zuba ruwa a ƙasa ya sha haka
yake ji, ya ji daɗin tafiyanta matuƙa, ta so tafiya da Auta dan ta kaita can ko
zata huta ta ji sauki, amma King ya hana, saboda ya ƙasa samun natsuwa, yana cikin
fargaba da tashin hankali, dan yana ganin kamar zai rasata ne kawai, saboda dik
yadda kuke tinani abin ya wuci nan, Zunaira ta lallace ta rame, tamkar mai ciwon
H.I.V, abin gwanin ban tausayi, uncle Jahiz sam baya san zuwa wajenta, saboda tana
saka shi kwallah!.

Zaune take tare da Chuchu a saman bed a cikin part da aka kaita, sai ƙoƙarin janta
da hira Chuchu take yi domin su samu ta ɗan saki jiki da su, sai dai ina, dik hiran
da Chuchu take yi mata taki tofa ko uppan, kanta a ƙasa tana kallan yatsun hannunta
da suke ɓulɓul a da, yanzu sun rame sosai, kamar ba nata ba!.

Dafata Chuchu ta yi tana faɗin. "Auta dan Allah ki ce wani abin mana! Tsawon awa
biyu muna tare, ni kaɗai nike ta yin magana kinki ki amsani, kina son nima in kara
ciwo a kan wanda nike ciki ne?". Cikin raunatacciyar murya Chuchu ta yi maganar,
tamkar zata yi kuka, idanunta sun cicciko da kwallah, ta rame sosai ita ma, tamkar
ita take jinya!.

Kanta a kasa ta ɗan girgiza alamar bata san Chuchu ta yi ciwo, amma bata iya yin
magana ba. Kara matsawa kusa da ita Chuchu ta yi, ta buɗe baki zata yi magana kenan
sallamar Abdussalam ya katseta. Sanye yake da arabs jallabiya dark ash, shi ma ya
rame sosai, saboda ciwon nata. Ganinsa yasa Chuchu ta miƙe tana faɗin. "Zan dawo
zuwa anjuma". Ta kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin.

A in da Chuchu ta tashi ya ƙarisa ya zauna, a hanzarce Auta ta ɗan ja baya tamkar
wadda aka matsowa da wuta kusa da ita. Ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, cikin
sanyin murya ya ce. "Zunaira ki faɗa mun dalilinki na guduna? Na tabbata yansu kam
na ciwo bane! Dole akwai wani dalili, dan kin samu sauki"......... Kin yi mashi
magana ta yi, sai dai har cikin ranta ta ji wani irin yadda ya kira sunanta, bai
taɓa kiranta da Zunaira ba, kullum my wife yake cewa, da alama yau hakurinsa ya
kare ne!.

"Ki yi magana kin ji? Ki kalleni a matsayin yayanki ba miji ba, ki faɗa mun
damuwarki, ni kuma zan tsaya a wajen ganin na fitar dake daga damuwar"...........
"So nike kawai ka sake ni, shi ne damuwata". Abin da ta faɗa kenan ba tare da ta
ɗago da kanta ba, da kyar muryarta yake iya fita saboda kukan da ta sha. Wani irin
zaro idanu Abdussalam ya yi, a hankali ya maimaita kalmar saki kafin ya ce. "Ai ko
wata bare na aura ba zan saketa ba Zunaira bare ke da kike matsayin kanwata, ke da
nike tsananin kauna tin kina yarinya, Allah ya mallaka mun ke ya cika mun burina
kuma yanzu ki ce in sakeki? Tukun nan ma saboda me?".

Shiru ta yi mashi dan tasan ko zata mutu ba zai taɓa sakinta ba, aurensu ai babu
saki, su a ƙaidar familynsu ma ba'a saki, babu wacce aka aura aka saka, ko bare
suka aura nasa saki bare na gida, ai kun san wannan aure ba mai mutuwa bane!. Ganin
ta yi shiru ne yasa ya kai hannunsa ya riƙo nata. Zabura ta yi zata kwace kanta ya
yi gaggawar riketa da karfi, dan dole ta natsu bata iya kwacewa ba. Cikin taushi da
tausasawa ya ce. "Zunaira please, ki tausaya mun, ki ji kan zuciyata, wlh ina
sanki, kuma kome kike so zan yi maki, dan Allah ki faɗa mun menene yake damunki,
Zunaira kalli yadda na rame fa saboda ke, please my wife, Yah Abdussalam ɗinki ne
fa? Ko kin manta ne? Kin dai'na so na ne? Please kada ki bari zuciyar da bata san
komai ba face sonki ta cutu, bata san komai ba sai begenki, please my wife help me
and accept me as your husband, na yi maki alkawari zan sanyaki farinciki koda ni
zan kuntata". Tamkar zai yi kuka ya kai karshen maganar.

Shiru ta yi idanunta suna zub da zafafan hawaye, take kalaman Hoorain suna ratso
mata cikin brain ɗinta a in da yake ce mata. "Hoonairata kada ki yarda ki yi magana
da wani namijin a bayan idona, ki rike mun amanar kanki, ke tawace ni kaɗai". Tina
hakan yasa ta kai kallanta a kan hannunta da Abdussalam ya rike, take zuciyarta ya
buga da karfi, ba iya magana da wani ba har hannunta ta bari ya rike.

Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi tare da kwace hannunta da karfi, da
gudu ta miƙe ta fito parlour, ƙasa iya cigaba da tafiya ta yi, da ta so ne ta fita
waje, amma sai ta ƙasa saboda jiri, bata gama samun lafiya ba, a tsakiyar parlourn
ta zube gwiwowinta a kasa, rushewa ta yi da kuka mai sauti, cikin kukan ta fara
sambatu kamar haka. "Am so so sorry my Hoorain, yau na karya alkawarin da na ɗauka
maka, na bari wani namiji ya taɓani, ba zan yafewa kai'na ba har sai ka yafe mun,
ni taka ce kai kaɗai, kai kaɗai kamar yadda kake nawa ni kaɗai". Cikin fitar
hayyaci take wannan magana, sam bata lura da Chuchu dake zaune a saman sofa a cikin
parlourn ba. Allah sarki Chuchu, ta kasa komawa family part ta bar autar ne, shi ne
yasa ta zauna a parlourn tana jiran idan Abdussalam ya fita sai ta koma su cigaba
da yin hiran.

A dai'dai wannan lokacin kuma King yana can suna kai ruwa rana da smart, ga tashin
hankalin da yake ciki na ciwon Auta, ga zafafan questions da Smart ya jefesa da su.
Yana tsaye a tsakiyar bedroom na daddyn nasa, yana sanye da sleeping dress, dan
shirin kwanciya barci ya yi, while shi kuma King yaka zaune a saman bed ɗinsa, babu
ko sallama Smart ya shigo mashi cikin ɗaki, kallo ɗaya King ɗin ya yi mashi ya
kawar da kansa, a cewarsa yana fushi da Smart, a tinaninsa hakuri Smart ya zo
bashi, sai dai bai san wata fitinar ce ma ta kunno kai ba.

Wai irin ya nuna ransa ya ɓaci sosai ɗin nan kuma yana fushi da shi shi ne har da
wani cewa Smart ɗin. "Meya kawoka room ɗina?". Ya yi maganar yana wani ɗaure fuska.
Shiru Smart ya yi yana cigaba da binsa da kallo.

"Idan ba zaka yi magana ba ka fice mun daga ɗaki". Ya faɗa yana nuna mashi hanyar
fita. Man ma shiru Smart ya yi, maganganun momma na ta yi mashi yawo a kunne in da
take cewa tana san su yi magana amma tafiya Dubai ya zo da sauri, dan haka idan ta
dawo zasu tattauna a kan matar commander, kada ya kula kowa a gidan, ya kasance a
ɗaki kamar yadda yake. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Meyasa ka cika san
kanka da zalinci ne dad?". A sanyayye ya yi maganar!.

A hanzarce King ya zaro idanu yana kallansa. "Omerish ni kake cewa ina da san
kai'na da kuma zalunci? Ni kam anya baka shan wani abin kuwa?"....... Idanunsa kar
kan dad ɗin nasa ya ce. "Dama shi mara gaskiya a kullum cikin hargagi yake, dad
baka da gaskiya, kana da zalinci da son kai, baka san zaluncinka ya tonunwa duniya
shiyasa kake ƙoƙarin hahhaura abubuwa a kan wasu".

A zabure King ya zuro kafafunsa kasan bed ɗinsa, yana zaro ido kamar an tare ɓera a
tarko ya ce. "Zaluncin me na yi Omerish? Dan na aurawa Zunaira wanda ya dace da
rayuwarta shi ne na yi zalunci?". Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye, yana
wani furkaki!.

"Dad ni fa ba ɗaya nike da sauran ƴaƴanka ba, kai kanka kasan da hakan, kasan cewa
yaran momma gifted ne, shiyasa kake jansu a jikinka fiye da ƴaƴan kowa saboda baka
san su ja baya da kai har su fara tinanin akwai abin da kake binnewa, kasan da cewa
ko da iya Omaid and Obaid aka barka sai sun tona ɓarnar da kake yi cikin ƙanƙanin
lokaci bare kuma ni".

Kara firgita King ya yi yana zazzare idanu. "Omerish ya tabbata yanzu kam da gaske
akwai abin da kake sha!". Ya faɗa yana nufosa. "Dad babu wani abin da nike sha,
yanzu ni ba wannan ne ya kawoni ba"..... "Batun Zunaira ne ya kawoka ko? To Zunaira
matar aute ce, sai ka zare bakinka a cikin maganar ta". Cewar King!!

Kai Smart ya ɗan girgiza. "Ba'a banza makiya suke kirana da Smart ba, tun da har
makiyana suka yarda ni Smart ne yakamata kai ma daddy kasan ni ba irin saura bane,
ba shakka batun Zunaira yana daga cikin abin da ya kawoni, amma bashi ne the best
ba, the best shi ne so nike ka faɗa mun wacece uwar Ramish?! Dan dai kasan Aleezarh
(Mama kenan) ba ita ta haifeshi ba!!".

Tamkar kwayar idanun King zasu fito su faɗi ƙasa, lokaci guda wani irin gumi ya
wanke mashi fuska, a rikice word ɗinsa suna harhaɗewa ya ce. "Idan ba Aleezarh ce
ta haifesa ba kai ne uwarsa? Wai Omerish anya kana da hankali kuwa? Lallai ba
shakka Rahilarh ta mun cuta da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ta mayar da kai mara
hankali ma.......". Ƙasa ƙarisa maganar ya yi saboda tsawa da Smart ya daka mashi.
"Ya isheka haka dad! Kowani lokaci sai ka zagi momma a kai'na for what reason? Ka
zageta kuma ka zaganmun iyayena, dik saboda kana san ɓoye laifukanka, just tell me
wacece uwar Ramish kuma meyasa ka yaudari Aleezarh da shi? Me ya yi maka da ka ja
mashi irin wannan bala'i da dik in da ya yi neman rayuwarsa ake yi? Laifin me ya
aikata a gareka? Ka faɗa mun sannan ka bani amsar menene a tsakaninka da mahaifiyar
Hoorain da har ka zage ka rabasa da Zunaira". Ɗan dakatawa ya yi yana mayar da
numfashi kafin ya sake cewa.

"Dad kai azzalumi ne sosai, ka faɗa mun su waye suke bibiyar rayuwar Ramish, dan
nasan tin da har ka iya yaudarar Aleezarh da Ramish a matsayin ɗanta to ba shakka
kasan su waye suke neman kashesa, Raj shi ne kawai ɗan Aleezarh namiji sai Aneesa,
Ramish ba ɗanta bane, kuma kai ka san uwarsa, dole kuma ka faɗa mun ɗan waye".

Yau ake yinta, Ramish ba ɗan mama ba, how comes to? Ya aka yi ita kanta bata san ba
ɗanta bane?

Please Login or Register in order to submit comment