Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 60 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na a kan mirrorn. A gefenta ta ajiye bowl and
towel ɗin, sannan ta hau cire botiran sauran kayan ciki, tas ta cire kafin ta sa
almakashin zata tsaga farar singlet ɗin ciki. Tana kan yankawa sai ta ji mirror ta
yi wani irin kara. A tsorace ta kai kallanta kansa jikinta na kermar kirjinta ya
bada bugun dum dum lokaci guda.

Sai dai ko da ta kai kallanta a kai bata iya gane komai ba, domin wannan kara da ya
yi alama ce da akwai matsala a birnin, so ba aikinta bane ba zata gane ba, dawo da
kallonta a kan abin da take yi ta yi. Wani irin zabura ta yi a lokacin da ta kalli
ta yanke jikin Black Tiger da almakashin da ta kai kallanta a kan mirrorsa, karar
mirrorn ne ya razata har ta yankesa bata sani ba.

Sosai ta tsorata tsikar jikinta na tashi ganin jininsa jajir kamar wuta. Sai
dai kuma jininsa na fita gabaɗaya ɗakin sai da ya amsa, a take wani irin haske mai
karfin gaske ya gauraye ɗakin, zuciyar Duniyar shaiɗanu ta buga alamar autansu ya
samu wani ɗan matsala kenan, take suka hau kururuwa mai karfin gaske, sai dai ita
bata ji saboda ɗakinsa babansa ya tsareta, idan baku manta ba sai da ya fita main
parlour ne ma Duniyar shaiɗanu ta iya gane cewa yana raye ko? To basa iya gane
komai idan yana ɗakinsa, yanzu ma saboda jininsa da ya zuba ne yasa suka ji
zuciyarsu ta girgiza. Da alama Sweetie zata shiga komarsu, dan kuwa wanda ya
fitarwa da Black Tiger jini wlh ba zasu taɓa kyalesa ya rayu ba, sai sun ga
bayansa! Wannan alkawari ne, a kan autansu babu abin da ba zasu yi ba!!.

Hmmm akwai matsala fa, Sweetie ita ta fara ganin Black Tiger ido da ido, ita ta
fara sa ya fita fada har duniya tasan face ɗinsa, yanzu kuma ita ta fara fitar
mashi da jini a jiki!!.

A gaggauce tasa wannan towel ɗin ta hau goge mashi jinin jikinta na kerma. Ko
kaɗan jinin yaki tsayawa, hakan ba karamin ɗaga mata hankali ya yi ba, da gudu ta
diro kasan bed ɗin ta nufi waje dan ta je ta kira Ronnie ya zo ya kawo mata agaji,
dan abubuwan is getting out of hand a gareta. Sun fi karfinta!.

A tsakiyar main parlour suka ci karo da Ronnie, karo suka yi ta yi baya zata
faɗi tana jan numfashi da sauri sauri. Rikota da hannu ɗaya ya yi yana faɗin lafiya
kuwa take irin wannan gudun?. Ƙasa yin magana ta yi tana sauke numfashi da ɗan
sauri sauri.

Allah sarki Ronnie, haka kawai ya ji jikinsa ta bashi ba lafiya ba, saboda har
cikin ransa ya ji wannan fitar jini na Black Tiger, shiyasa ya ce bari ya zo ya
duba. Da hannu ta nuna mashi sama ta ƙasa yin magana. Hannunta ya ja da gudu suka
haura sama ɗin yana jin gabansa na faɗuwa.

A yadda ta bar Black Tiger haka suka shigo suka same shi. Da gudu Ronnie ya haye
bed ɗin yana tambayarta me yake faruwa?. Bata ɓoye mashi ba ta faɗa mashi dik abin
da yake faruwa. Zaro idanu sosai ya yi kafin ya ce mata.
"In kalli kafan naki da ya gani ya suma" a hanzarce ta fito da kafar tata ta
nuna mashi. Yana ganin yatsunta shidda ne wani irin zabura ya yi zai miƙe tsaye,
sai kuma ya daure ya koma ya zauna.

"Bro lafiya?". Ta jefa mashi tambaya. Kai ya girgiza mata alamar babu komai. Shiru
ta yi tana tinanin lallai akwai matsala wanda Ronnie ya sani kawai faɗa mata ne ba
zai yi ba, amma tana fatan Allah yasa alkari ce a garesu bakiɗaya. Ronnie a
matsayinsa na likita A-box ya ɗauko domin taimakawa yayan nasa, ga shi a kusa da
kirji ta yankesa.

Tsab ya gyare komai, sannan ya ce ta ɗebo wani ruwa su sanyayawa Black Tiger jiki
saboda zafin da jikin ta yi. Tana ƙoƙarin sauka daga bed ɗin mirror ta kara yin
kara a karo na biyu. A miliyan Ronnie ya kai kallansa a wajen. Ai bai san lokacin
da ya diro kasa daga saman bed ɗin ba, kamar walkiya ya isa gaban mirror ya tsaya.

"Sis zo ki ga wani abin". Ya faɗa yana zaro idanu waje sosai. Da sauri ta
kariso wajen tana faɗin. "Meyake faruwa ne? Ɗazun ma mirror ya yi kara lafiya
kuwa?". Tamkar idanunsa zasu faɗi ƙasa saboda zarosu da ya yi ya ce. "Ina fa
lafiya, muna cikin tashin hankali, birnin nan babu lafiya ga yaya ya suma yanzu ya
zamu yi?".

A kusa da shi ta tsaya kafin ta ce. "Meyake faruwa da birnin?". .......... Yatsansa
yasa ya yi mata pointing na wani ɓangare daga jikin mirror kafin ya ce. "Kinga nan
wajen birnin nan ne, kinga mutanen da suke wajen nan to yaki suka kawo mana, dama
jiya yaya ya faɗa mun akwai waɗan da suke haransa dan su kwace birnin nan daga
hannunsa bayan kowa yasan birnin nan nasa ne, to ga shi yanzu sun dinfaro cikin
birnin nan da shirinsu yaya kuma babu shi yanzu ya zamu yi". Cike da tashin hankali
da fargaba ya yi maganar!!.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Ka taɓa ganin wanda ya rike Allah ya rasa
mafita?"........................ Kai ya girgiza mata alamar a'a...... "To ka yarda
dani zamu yi nasara ko da big bro ko babu shi, trust me ba zamu taɓa faɗuwa ba dan
mun rike Allah, Allah ina mai rantsuwa ina kuma mai imani da Allah Allah ba zai
taɓa kunyata mu ba, ka yarda dani". Ta kai karshen maganar tare da ware mashi tafin
hannunta. Ba tare da shayin komai ba ya ɗaura nasa tafin hannun a kan hannunta
alamar ya yarda da ita. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Mu je wajen mayakan da
suke birnin nan ka ji?".

Hannunta ya damke sosai yana faɗin. "That's why I love u my sis, kina da basirar
saurin warware mana matsala, lets go to". Ya kai karshen maganar yana sakin
hannunta. Haɗa hannun suka sake yi alamar zasu yi aiki a tare kuma zasu yi nasara
In Sha Allah. A tare suka nufi wajen Black Tiger, sannan a tare suka ja bargo suka
rufesa tare da yi mashi fatan farkawa cikin gaggawa kafin abubuwa su fi karfinsu su
caɓe masu.

Da gudu Ronnie ya ja hannnunta suka nufi waje Sweetie tana ta ƙoƙarin sanya
ƙwaƙwalwarta a chaji wajen san gano menene ya janyowa Black Tiger wannan matsalar?.
A gurguje suka fito kofar empeir ɗin, akwai wani stairs case mai bala'in tsawo a
bakin empeir ɗin wanda ya kai step 30 haka, a gurguje suka tattakasa suka sauko
ƙasa.

Master Devil suka fara nema, dan shi ne master ɗin warriors ɗinsu, dan haka sai
suka nufi ɓangaren mayakan Daular, hannunsu rike cikin na juna, Allah sarki abin da
basu sani ba shi ne master Devil ya haɗa hannu da mutanen can, ya ci amanarsu dik
saboda dukan da Ronnie ya yi mashi ranar. Amma fa shi Black Tiger yasan da cewa
master ya haɗa hannu da mutanen, kuma master ɗin ne ma ya nuna masu hanyar da zasu
bi su shigo Daular a saukake su ci su da yaki. Dik Black Tiger yasan komai, sai dai
a yanzu babu amfanin sanin da ya yi, bai tina hakan zata faru da shi ba shiyasa ya
yi shirin yakarsu shi kaɗai, sai dai kana naka Allah yana nasa, ga shi dai yanzu ya
shiga wani hali.

A can part na warriors suka isko master Devil yana zaune saman chairs kamar bai
san komai ba. Suna shiga wajen tin kafin su ƙarisa in da yake suka fara faɗin.
"Master ka haɗa kan warriors ɗin nan yaki ya tinkaromu a kurarren lokaci".........
Master dake zaune ko a jikinsa ya ce. "Babu wani mayaki da zai shirya yaki har sai
King Lucian (Black Tiger) ya bada umarnin hakan".
Cak Ronnie ya tsaya jin amsar master, ransa a ɗan ɓace ya ce. "Ni na bada
wannan umarni dan haka ka haɗa kansu".

Miƙewa tsaye daga saman kujarar da yake zaune ya yi, cikin kakkausar murya ya ce.
"To ba zan yi ba! Ba zan bi umarnin naka ba!!". A fusace Ronnien ya nufesa da nufin
sake dakasa kamar a baya. Yana tsaye bai yi wani motsi ba irin alamar akwai abin da
ya taka haka. Da sauri Sweetie ta rike hannun Ronnien tana faɗin. "Bro don't mind
him, ka manta muna da abubuwa a gabanmu ne?".

Ciza laɓɓansa master ya yi, ya so ne dama Ronnie ya zo da nufin su kaure da faɗa ya
janye masu hankali har gungun matanen can su yi wa Daular zobe su rufesu da yaki ba
tare da sun farga sun shirya ba, amma sai Sweetie ta hana shi, ya ji zafin hakan
kuma ya kara tsanar Sweetie sosai.

"Bro kai da kanka ka bawa warriors ɗin umarnin da su shiryawa yaki kada ka daka
ta wannan kazamin mutumin". Cewar Sweetie, tana bala'in tsoron master Devil idan
baku manta ba tun farkon zuwanta birnin, sai dai kuma yanzu wutar tsanansa ne yake
ruruwa a cikin zuciyarta saboda lalatar da yake yi, and tana tare da Ronnie, dan
haka tana jin kwarin gwiwar zaginsa dan Ronnie ya fisa karfi kuma zai tsaya mata.

"Babu wanda ya isa ya bawa warriors ɗin nan umarni a nan sai ni". Cewar master,
dik abin da yake yi fa yana so ne ya ɗauke masu hankali har a cin masu. Ronnie zai
yi mashi martani Sweetie ta hana shi, daga karshe ta ja hannunsa suka haye saman
dogon stage dake wajen domin su yi magana da warrios ɗin. Jikinta har kerma yake yi
ta ɗauko wani katan laspeaker ta miƙa mashi domin ya yi magana. Karɓa ya yi kafin
yasa hannu ya buga belt ɗin dake wajen mai sautin gaske domin ya samu attention na
warriors ɗin.

Aikuwa yana bugawa gabaɗayansu suka juyo a kansa, kan kace me dik sun haɗu a gaban
stage ɗin, da gudu master ya hauro sama shi ma da nufin ya dakatar dasu, shirinsa
shi ne ya capke Ronnie da kokawa ya dakatar da su.

Ronnie ya fahimci hakan, dan haka sai da ya bari ya hauro yasa kafa da karfi ya
takesa a kirji da karfi a in da ya yi baya baya ya ganganra kasan stage ɗin, ya
faɗi ƙasa a gaban warriors, cike da bada umarni ta cikin laspeaker Ronnie ya ce da
mayakansu na Robbot guda biyu da su kama master su jefa mashi shi a cikin prison na
empeir ɗin. Tsalle Sweetie ta buga tare da cewa. "Good my bro".

Warriors biyu ne suka capki master suka wuce da shi, ga shi robbot ne bai isa ya
gwada masu fin karfi ba, kuma Ronnie shi ne mutum na biyu bayan Black Tiger da aka
shigar masu da su rinƙa bin umarninsa a cikin kwakwalwarsu, dan haka tin da ya ce
su kai master prison ba makawa sai sun kaisa.

Attention ɗinsa Ronnie ya bayar a kan sauran warriors da sun haura sama da 3k a
wajen, cike da bada umarni ya ce su yi maza su shiryawa yaki basu da isasshen
lokaci an kawo masu hari. Sannan ya ware wasu warriors da zasu iya kai 300 ya
umarcesu da su tattara mata, tsofaffi da yara, su tarasu waje guda, su basu karisa
kada su bari wani abin ya samesu. Daga karshe ya wari wasu warriors ɗin ya umarce
da idan yakin ya ɗauki zafi fiye da tunaninsu to fa su tashi jiragen eagle dromes
na yaki su fara ɓarin wuta daga sama. Yana kai karshen wannan magana bai gama rufe
baki ba suka fara jin rugugin tashin wuta daga cikin empeir ɗin.

Cikin ɗaga murya Ronnie ya ce ku je, daga haka ya riko hannun Sweetie da gudu suka
sauko kasan stage ɗin suka nufi cikin empeir ɗinsu wajen Black Tiger kenan.

Wato idan ka yarda da Allah wlh cikin sauki zai kare ka daga sharrin dik wanda ya
nufeka da sharri ba tare da kasan ya yi ba, kun dai ga aya a kan Floris, ta nufi
Sweetie and Ronnie bayin Allah da sharri, to da yake su Allah kawai suka rike ga
shi ya juyar mata da aniyarta a kanta, my people's me kuke tinanin yasa Black Tiger
a cikin wannan hali? Ya kuke tinanin wannan yaki zai kasance babu Black Tiger? To
mu dai bari mu je wani part ɗin mu dawo.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥

Zaune Auta take a gaban tabkeken s-p na gidanta da Smart ya mallaka mata, tana
sanye da short army trouser mai shegen kyau da ya tsaya mata a iya gwiwa, sai kuma
white shirt daga ta sama, ta yi shiru haɗe da buga uban tagumi tana tinanin
Hoorain.

Manya manyan ƙosassun dolphin fish ɗinta suna ta wasa a cikin ruwan, sai fito da
kansu waje suke yi suna taɓata dan ta zo su yi wasa amma taki kulasu, tana cikin
damuwa, kun san dolphin idan ka saba wasa da su da sun ganka za su yi gaggawar
fitowa saman ruwa, so ita a koda yaushe suka zo France ita da Jaish tana wasa da su
sosai, ita ma tasa Smart ya saka mata su ɗan wasa, amma wannan karon sai ga shi
taki kulasu, sai tsalle suke yi su fito su koma.

Hoorain kawai take tunani baiwar Allah, ta yi rama sosai, yau kwananta biyu a
gidan nan tare da Smart and Pretty, sai dai ko kaɗan bata san a wace duniya take
ba, ga shi tin da suka dawo Smart bai natsu ba bare har ya san halin da take ciki,
baya zama saboda aikinsa, wani lokaci sai cikin dare yake dawowa,lokacin kuma sun
yi barci. Ita kuma Pretty dama ba wani cika damuwa da abubuwa ta yi ba, bama zata
fahimci halin da take a ciki ba bare har ta tausaya mata ko ta bata shawara. Ji
take tamkar ta sanya hannu bisa kanta ta kurma ihu ko zata samu sauki, wayar da
Smart ya bata wanda zata rinƙa kiransa idan tana buƙatar wani abin sai ruri yake yi
ta ɗaura shi a saman kujerun dake kawayen da wajen, da alama ta yi nisan da bata ma
jiyo ringin na wayar ba.

Guyson ne kuma yake ta kiranta, dan ya gaza samun kwanciyar hankali da sukuni, jiya
ita ta kirasa da number da yake ta haddace numbersa, ta ce mashi ya dubi girman
Allah ya je ya haɗata da Hoorain a waya, da farko yaki yarda, daga baya da ya
fahimci zata iya cutuwa sai ya ce tabbas zai je koda dad zai jefashi cikin prison
ne, to shi ne yake ta kiranta yanzu bata ɗaga ba hankalinta ya yi nisa.

A can cikin gida kuwa, Pretty ce tsaye a gaban dressing mirror na ɗakin Smart, bata
san cewa bedroom ɗinsa bane, ta tashi daga barcinta kawai ta je ta afka cikin ɗakin
a garin neman hanyarta na san fita waje ta duba Auta, ta san Auta tana yawan zama a
wajen dolphins ɗin nan, sai dai bata iya fitar da kanta wajen ba, sai dai su je a
tare da Autar, saboda hanyar yana da sarkakiya sosai.

Ganin kanta a cikin wani bedroom ɗin yasa ta fara kewaye a ciki tana zuba
ƙauyancinta, taga bedroom ɗin ya fi nasu haɗuwa da ƙawatuwa sosai, ta ga abubuwan
da bata taɓa gani ba, Allah ya yi zata zo France, dan suna rike da hannun juna ita
da Auta a lokacin da Smart ya ja hannun Auta suka baro kingdom of power, sai Auta
bata saki hannunta ba ta jata suka tafi a tare. Time da suka je airport Smart ya
nuna ba zai tafi da ita ba, sai Auta ta ce ya kyaleta kawarta ce kuma suna san
juna, dalilin da yasa ya zo da ita kenan.

Leke leke ta shiga yi mashi kamar ya aikata, kun san ita Pretty kifin rijiya ce,
ba kamar Sweetie take ba, wayonta da sauki, ga bala'in tsoro ba confidence, sai
shegen shagwaɓa da cin abinci. Amma idan baku manta ba ita ɗin gwana ce wajen iya
fitina, bata ganin abu bata taɓa ba. Dan haka sai ta shiga yi mashi taɓe taɓe, dik
abin da ta gani sai ta taɓa.

Cikin taɓe taɓen nata ne hannunta ya kai ta buɗe drawer mirror, tsautsayi dai baya
wuce ranarsa, Smart yana rufe drawer da password, idan ya buɗe ya ɗauki abin da zai
ɗauka, da ya tura drawer zata sake shiga password, so yau da ya tura drawer sai
bata turu da kyau ba bare ta shiga password, hakan ya bata damar buɗewa.

Wasu robobi ta gani a ciki kamar na zuba magunguna haka, tsabar fitina da kiran
ajali wanda in ya kira dole a amsa sai tasa hannu ta ɗauki roba guda ɗaya, har da
ɗan saka karfinta wajen buɗe robar da ta ɗauko. Tana buɗewa wani abu ya fita kamar
hayaki haka, shakarsa ta yi a take ta saki robar ya faɗi ƙasa.
Lokacin guda jini ya fara gangaro mata daga hancinta da kuma hakinta, ji ta yi
tamkar am shake mata wuya wuya da karfi, hannunta dikka biyu ta kai ta riki wuyar
tata tana kwalalo idanu waje. Da kyar ta iya juyawa tana san barin wajen, sai dai
ko motsa kafafunta ta ƙasa bare ta iya tafiya.
A take a wajen ta yanke jiki ta faɗa saman kirjinsa, dan yana tsaye a bayanta, da
ta juyo ta fita a cikin hayyacinta ne yasa bata iya gane akwai mutun a kusa da ita
ba. Shi kuwa dama ya fito daga wanka yana cikin dressing room yana shiryawa zai
fita, to ya fito daga dressing room ɗin kenan yaga ta ɓalle marfin robar, shi ne ya
kariso wajen ya tsaya a bayanta, ta cikin mirror dake gabansu yake kallan yadda
jini ya fara zuba daga hancinta har izuwa bakinta.

Fararen kaya tas ne a jikinsa, da ta faɗa jikin nasa kaf ta ɓata shi da jini.
Allah ya cecesa yana sanye da face mask a fuskarsa, dan shirin fita ya yi, da wlh a
tare zasu mutu da ita, dan in ya shaki wannan chemical ɗin shi ma ba zai tashi ba,
dama sai sun saka face mask, hand's gloves da wasu irin riguna na leda kafin suke
buɗe chemical ɗin, kun tuna yadda suke aiki a wajen haɗa makamansa ko? To haka suke
yi kafin amfani da waɗan nan shegun chemical, kisa suke yi nan take, ita kuwa da
fitina da rashin sani ta je ta buɗe.

Sosai ta bakanta mashi rai, domin waɗan nan chemical ɗin suna da wahalar samu,
shiyasa ma ya ɓoyesu a gida, wannan ɗan kaɗan ɗin da ta zubar mashi millions of
dollars yake, chemical ne mai haɗarin gaske na haɗa nuclear mai karfi sosai, yanzu
haka gabaɗaya ya tsastsaga mata kafa, saboda sake shi da ta yi ya faɗi ƙasa ya ɗan
taɓa ƴan kafafunta.

Jininta a kafa ne ya fara zuba, lokaci guda ta sandare kamar wadda lantarki ya
busar. Siririn tsaki ya ja ya rasa me ɗaya zai fara yi?. Daga bayansa muryar Auta
ta katse shi da cewa. "Yah Omerish kaga Pretty? Yanzu na je ɗaki ban ganta ba". Da
yake ya bawa kofar shigo baya ita kuma Pretty tana kwance a kirjinsa sai yasa Auta
bata iya gane Pretty na ɗakin ba.

Ya lura da akwai shakuwa sosai a tsakanin Auta da Pretty, dan haka sai ya ce mata.
"Jeki parlour ina zuwa". Ya yi mata hakan ne dan kada ta ga gawar Pretty hankalinta
ya tashi, dama daga jiya zuwa yau ya fahimci tana cikin damuwa, daren jiya da ya
dawo ya shiga bedroom ɗinsu, a nan ya sameta tana sambatu cikin barci, yau da safe
kuma kafin ya shiga wanka sai da ya tsaya a jikin window ɗinsa ya zuba mata idanu
tana zaune wajen dolphins, dama ya sa a ransa yau idan ya dawo daga office ya je
ainahin gidansu ya dawo zai tambayeta me yake faruwa?.

Juyawa Auta ta yi ta fita hankalinta bai kai kan jinin kafar Pretty dake malale
a kasa ba. Tana fita ya raba jikinsa da nata, da hannu ɗaya ya ɗagata izuwa
balconynsa, saman ɗaya daga cikin kujerun dake wajen ya kwantar da ita.

Ita kuwa Auta parlour ta koma ta zauna tare da buga tagumi tana jiransa. A gurguje
ya fito daga cikin bedroom ɗin nasa, rufe kofar ya yi dan ma kada ta Autar ta shiga
taga gawar Pretty, bai tsaya bi ta kanta ba ya nufi waje yana ce mata yana zuwa. Ta
yi mamakin ganin yadda yake tafiya tamkar zai haɗa da gudu, amma bata kawo wani
mummunar tinani a ranta ba, tana san tambayarsa ya ga Pretty, sai dai kafin ta buɗi
baki tuni ya sauka ƙasa.

Shiru ta yi tana tinanin ina Pretty ta shiga kuma?. Can kunnuwarta suka tsinkayo
mata wayar dake ruri a waje. Da sauri ta miƙe ta nufi waje. Filin dolphins ɗinta ta
koma, wayar natan ne dai yake ruri. Tana zuwa ta ɗauka, guyson ne yake kiranta, a
hanzarce ta yi picking tare da kara wayar a kunnenta tana faɗin.
"Hello Yah Omar". A maimakon ta ji voice ɗinsa sai jin muryar Hoorain ta yi
ya amsa mata da Hoonaira. Ai bata san lokacin da ta zube ƙasa a wajen ba, tamkar
zata kurma ihu saboda daɗi, har ta rasa abin faɗe ma.

Shi kuwa yana kwance a kan gadan jinya, da shi da Abbonsa dik suna gadan jinya,
gara Abbonsa ma ya ɗan samu lafiya, ya farfaɗo yana iya gane waɗan da suke kansa.
Shi kuwa Hoorain yana gab da mutuwa King ya samu labarin daga bakin masu tsaronsa
cewa Hoorain zai iya rasa ransa a kowani lokaci daga yanzu, hakan yasa King ya ce a
fitar da shi a kaisa hospital. Time da aka fitar da shi ranga ranga aka wuce da shi
hospital, baya iya taka kafafunsa ma, sai ɗaga shi warriors suka yi. Jiya aka fitar
da shi, yanzu a can guyson ya je ya kai mashi waya ba tare da sanin King ba.

Wai me ya faru a kingdom of power bayan tafiyar Smart ne?.

Cikin bedroom ɗinsa King ya nufa hankalinsa a tashe. Shi kuma Smart kai tsaye
babban gate na kingdom ɗin ya nufa. Sun zo dai'dai wani waje dake kusa da fadar
King ta biyu, idan baku manta ba na faɗa a baya fada gudu biyu ne a kingdom of
power, so King baya amfani da ɗayan, saboda ainahi na mahaifinsa King Abdul Malik
ne, to fadoji a da suna haɗe ne, sai ka shiga ta cikin ɗaya zaka je ɗaya, bayan
hauwar King Zuhair mulki sai ya rabasu, aka toshe kofar tsakiyar aka buɗewa
kowanne nasa kofar yana cin gashin kansa.

So sun zo giftawa ta dai'dai wannan fada na King Abdul Malik wani irin haske ne ya
bayyana daga cikin fadar ya shiga cikin motar tasu, sarai Smart ya ga hakan, amma
hankalinsa ta yi gaba wajen tuƙi, bai wani bi ta kan hasken ba, ita kuma Auta dama
ta kifa kanta a kan gwiwowinta tana kuka, Pretty dake zaune kusa da ita a kanta
wannan haske ya sauƙa, dama saboda ita ya fito, saboda Spender dake tattare da ita,
dik yadda aka yi da akwai alakar Spender da wannan fada, ina ga yana daga cikin
dalilin dayasa King Zuhair ya rufe fadar ƙin faɗawa mutane gaskiya ya yi, dik yadda
aka yi akwai abin da ake ɓoyewa, amma lokaci zai warware mana komai.

Ba iya haske ne kawai ya fita daga cikin wannan fada ba, akwai abubuwa da dama da
suka nuna alamar bayyanar Spender a wajen. Sai dai da yake Smart da gudu suka gifta
wajen sai basu ga komai ba bayan wannan haske.

Akka dake cikin bedroom ɗinta tana kwance sai da ta zabura ta miƙe zaune a lokacin
da su Pretty suka gifta wannan fada, a jikinta ta ji hakan, take ta ji jiri na
ɗibarta, jikinta ne ya fara tsuma. A lokacin su uncle Abbas sun koma part ɗinsu.
Wayarta Akka ta ɗauko, number King Zuhair ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a lokacin
suna tsaye a tsakiyar bedroom shi da momma suna ƙoƙari neman Smart dan ya dawo.

Muryar Akka na kermar ta ce. "Zuhair dik yadda aka yi Spender ya dawo cikin
Masarautar nan, ku yi gaggawar gano in da yake". Yadda take magana ya yi matuƙar
ɗaga hankalin King, a hanzarce ya ce mata. "Ki kwantar da hankalinki Akka dole nema
mu nemosa, gani nan zuwa kin ji?".
Da okey ta amsa mashi kafin ta katse kiran, hankalinta ya yi matuƙar tashi, dik
yadda aka yi Spender abu ne mai tsananin haɗarin gaske kuma barazana ne ga al'umma
shiyasa take shiga damuwa sosai,!.

Kingdom of power dai ya rikice.

A ɓangaren su Mammie kuwa, kuri da cika baki ta rinƙa yi a kan wlh ba zata kyale
Smart ba, sai ta ɗauki mummunar mataki a kansa, dan haka dole su fara gagarumin
shiri, ta yi rantsuwa da Allah ba zai daki Sarina a banza ba, uncle Abbas dai shiru
ya yi yana jin surutan nata ba tare da ya ce uppan ba.

Ɓangaren su Khadija kuwa, ita dai Khadijah tana cigaba da kula da babynta babu wani
damuwa abinta, yaro

Please Login or Register in order to submit comment