Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 66 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

throughout basu haɗu ba, ya je school, bayan ya dawo kuma yana
tare da uncle Jahiz, yana san uncle ɗin nasa sosai dan yana da ra'ayi a kan kwallan
kafa sosai, so ita zai je gani, har yau wajen da kunama ta harbesa tana ɗan yi
mashi zafi kaɗan kaɗan. Amma ya rufawa su Omaid asiri bai sanar da kowa abin da ya
faru ba.

Ai yana ga abin da yake kafuwa a miliyan ya kariso wajen, yana zuwa bai yi wata
wata ba yasa hannu ya ɗagata cak ya sauketa daga kan Sarina. Kun san faɗarta baya
karewa, da gudu ta yunƙura zata sake haye Sarina ya yi gaggawar ƙanƙameta yana
tambayar me yake faruwa?. Ƙoƙarin kwatar kanta ta yi da ta cigaba da jibgar Sarina
tana wani huci kamar wadda ita aka jibga, sai dai ina ta ƙasa kwace kanta, kuma da
hannu ɗaya ya riketa, hakan zai tabbatar maku ba wai karfi ne bashi da shi ba, shi
dai kawai goyon kaka ne.

"Lafiya meya haɗaki faɗa da Aunty Sarina a cikin wannan dare kuma?". Cikin
wannan sanyin nasa ya yi maganar. Ganin ta kasa kwace kanta ne yasa ta ce. "Ni ka
sakeni in gamasa cin ubanta". Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin kalamanta, ya ma
rasa me zai ce.
Ita kuwa Sarina lallaɓawa ta yi ta miƙe tsaye, har wani tangal tangal take yi
kamar zata faɗi. Hular da Mahreen ta tiɗɗa mata a cikin bakinta ta zaro shi tare da
harbin Mahreen ɗin da shi, a fusace ta ce. "Yau sai na ga waye gatanki, sai naga
waye ubanki a ƙasar nan, sai kin yabawa aya zaƙinta........".

Ai Sarina bata gama rufe baki ba ta wani daka sufa zata yi kanta tana faɗin. "Sai
dai ubanki ba nawa ba, shegiya mai kama da akuyoyin Nenne, kuma tun da kika zagi
bappana wlh sai na cire maki hakwaran sama". Wato dai kowa yana san iyayesa kuma
babu daɗi idan aka zagan makasu, amma kuma kai a lokacin da zaka zagi wani ba zaka
ji rashin daɗin yin hakan ba sai an rama ne zaka san iyaye suna da daraja kuma kana
sansu, ita fa ta fara zagin uban Sarina, amma yanzu kun ji da Sarina ta rama
shikenan abu yazama laifi an zagi bappanta ba zata bari ba, har da zubar da
hakwaran Sarina zata yi, kai Mahreen duniya.

Ƙanƙameta da kyau guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Ki natsu mun in ji me ya
haɗaku faɗa".
Juyo da idanunta kansa ta yi, cike da rashin kunya ta yi mashi kallan uku saura
kwata kafin ta ce. "Ji yadda yake magana kamar wani babban mutun bayan kai mai
kukan ciwo ne kawai, kai da rarrashinka ake yi kamar karamin yaro ne zaka ce zaka
raba faɗa? Kai fa zan iya zaneka ka yi kuka". Babbar magana!!.

Bawan Allah a maimakon ya ji zafin kalamanta sai ma ya saki cool murmushi kafin ya
ce. "To na ji zaki iya zaneni, yanzu dai muje part ɗin momma sai ki zaneni a can".

Sarina kuwa hannu ta kai zata kai mata capka ya yi saurin janyeta daga tsakaninsu
shi ya shiga tsakanin nasu yana rike da hannunta, a natse ya ce. "Aunty Sarina dan
Allah kiyi hakuri, kada ki biye mata, baki ga yarinya bace?". ..... Ai bai gama
rufe baki ba ta sake yin tsalle ta dire haɗe da cewa. "Wlh ni ba yarinya bace, kuma
ma ai na fika tun da ni bana kukan ciwo".

Sarina kuwa, dama zata yi magana da ya yi magana ne, amma jin Mahreen ta capki
zancen tana jajjaga mashi masifa yasa ta haɗiye maganarta tana huci. Shi dai har
yanzu ko kaɗan kalamanta basu wani taɓa shi ba bare har su ɓata mashi rai, kara
burgesa ma take daɗa yi, dan haka bai kulata ba ya sake duban Sarina ya ce. "Aunty
Sarina dan Allah ki yi hakuri kin ji?".

Sarina na ƙoƙarin cewa ya kyaleta ta taka Mahreen yadda yakamata ko zuciyarta ya
huce, sai Mahreen ɗin ta rigata da cewa. "Kada ta yi hakuri, ta zo ta lililili ta
likeni ta zurani ta bakin allura ta sake fitarwa karshen kenan idan ta isah"......
Yau dai guyson yaga ta kansa, ana ƙoƙarin kashe wuta ita kuma tana kara hurata.
Sake kaimata wawura Sarina ta yi ya yi saurin janyeta, ita kuma ana janyeta tana
wani matsowa zata kaiwa Sarina duka har da wani dunkule hannu wai ita nan jaruma,
sai wani kyafta idanu take yi.

Guyson dai da yaga wannan abin fa ba karewa zai yi ba sai ya shammaceta ya ɗauketa
cak yana bawa Sarina hakuri ya nufi part ɗin Momma, rai a ɓace Sarina ta ce wlh ba
zata kyaleta ba, sai dai kada su haɗu, in suka haɗu sai ta fasa mata baki, ita kuwa
Mahreen ya ɗauketa ma bakin bai mutu ba, faɗi take. "Wooooo ƙatuwar banza ta sha
duka, kuma na daki banza ba yadda zaki yi".

Kai Mahreen sai shirin Allah.

Bai sauketa a ko'ina ba sai a tsakiyar bedroom na momma, babu kowa a ɗakin sai
Mahnoor dake kwance saman bed tana barci, momma taki yarda ta matsa ko nan da can,
ta ce a gadanta zata rinƙa kwana tun da ba a nan King yake kwana idan yana ɗakinta
ba, gadanta ne ita kaɗai, so Mahnoor zata iya kwana a kai, tun Mahnoor na noƙewa
har ya saki jiki ta ɗauki momma matsayin uwa kawai.

Yana sauketa ta riko waist ɗinta da hannu dikka biyu tana binsa da wani irin kallo.
Ɗan sunkuyar da kansa ƙasa ya yi alamar kunya da kamala kafin ya ce. "To sarkin
faɗa kallan me ni kuma kike mun? Ko dai kina duba ta in da zaki ɗauki fansa a
jikina ne dan na hanaki yin faɗa?"....... Kai ta ɗan girgiza mashi alamar a'a,
sannan ta ce. "Ina mamaki ne". Ɗago da kallansa a kanta ya yi kafin ya ce. "Mamakin
menene kuma?". Ɗan nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Ashe kana da karfa fa? Ban yi
zatan kana da karfi ba ai, kuma da kake maganar ɗaukar fansa ai ko zan ɗauki fansa
a kan kowa ban da Hammana (Jaish) da mai kama da shi, kana kama da Hamma shiyasa
idan ka rabamu faɗa da mutane bana komawa kanka da faɗar".

Siririn murmushi ya saki har sai da dimple ɗinsa suka lotsa, sannan ya ce. "To
nagode da nike cin darajar kamannina da Yah Jaish nike tsira daga dukanki, amma in
tambayeki mana?"........... Tsaresa da ido ta yi alamar tana jinsa ba tare da ta yi
magana ba........ "Meyasa kike san yin faɗa ne?". Shi ne tambayar da ya jefa mata.
Kai ta ɗan ɗaga sama kamar mai tunanin wani abin, can ta sauko da kallanta a
kansa, ya yi shiru yana jiran amsa..... "Idan aka taɓoni ne bana iya bari, yanzu ma
ban yafewa wannan mai kama da akuyoyin Nenne ɗin ba, dik ranar da muka sake haɗuwa
sai na cire mata hakwaran sama dikka".

Shi dai yarintarta da shiriritarta dik yana burgesa, ga shegen san kwalliyar nan
nata yasa ya kara jinta a ransa, dan shi ma kamar yadda yake ɗan wanka haka yake
san ƴan gayu, bare ita da take caras cas, ga kyau da kirar jiki mai kyau, dik kalar
wankar da zata ɗauka kyau take yi sosai.

"Please ki dai'na faɗar nan haka ya isa kin ji?". Cikin sigar rarrashi ya yi
maganar yana kallan janbakinta da ya ɓata mata gefe gefen baki saboda faɗar da suka
gwabza.

"Ni ba zan dai'na yin faɗa ba matsawar za'a rinƙa shiga gonata". Cikin tsiwa ta
yi maganar......... Girgiza kai kawai ya yi, sannan ya matsa kusa da ita dab, ya
kai hannunsa saman lips ɗinta domin ya gyara mata jan bakin ba...... A miliyan ta
ja baya kaɗan tana faɗin. "Kai ma na lura ɗan iska ne mai san taɓa jikin mata,
yanzu ka ɗaukeni ban yi maka wata magana ba na yafe maka shi ne har ka samu damar
taɓa mun baki ko?".

Nisawa ya ɗan yi kafin ya kallenta from up to down, sannan ya ce. "To ai ke ba za'a
kiraki da ƴan'mata ba, baki wuce munzalin ɗaukarki da nike yi ba, ke yarinya
ce"........ Ai rike waist ɗinta da hannu dikka biyu ta yi, cikin tsiwa ta ce. "Wlh
ni ba yarinya bace, me banbancina da ƴanmatan?"........ Kai Mahreen akwai shegen
san girma...... Shi kuwa matsawa kusa da ita kaɗan ya yi tare da kai hannunsa saman
ƴan kirgan danginta da ta fara, sannan ya ce. "Wannan shi ne abu na farko da ya
fara banbantaki da ƴan'mata, ke baki da breast ai, kin gansu fa yanzu suke fitowa
ƴan ƙananan da su, ki bari sai sun girma sai ki fara haɗa kanki da manyan
mata"....... INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, KAI ANA WANI SHA'ANI A KINGDOM OF
POWER, AMMA GUYSON MA ƊAN DUNIYA NE.

Tsit Mahreen ta yi ta rasa abin faɗe, ga shi yasa hannu ya taɓa mata su, yau dai
bakin ya mutu. Shi kuwa cigaba ya yi da cewa. "Akwai banbancinki da ƴan'mata dayawa
bayan breast ɗinki, juyo in nuna maki sauran". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin
riko hannunta ya juyar da ita. Ai a miliyan ta fisge hannunta tare da saka mashi
kukan shagwaɓa da take yi wa bappa a kauye, ta faɗi ƙasa kamar dai yadda take yi a
kauye, birgima ta fara yi tana faɗin sai ya biyata taɓa mata kirji da ya yi.

Ganin Mahnoor tana motsawa zata farka ne yasa ya yi gaggawar yin ƙasa shi ma,
bakinta ya sanya hannunsa ya toshe yana faɗin ta yi hakuri zai biyata taɓawa da ya
yi.... NI KAM INA FATAN ALLAH YA KAWO MAI SANYA BAKIN MAHREEH YA MUTU! MASU FATAN
GANIN MAHREEN A LABOUR ROOM SU ƊAGA HANNU.

Rungumota ya yi ya hau rarrashi, nan ma ashe wani laifi ya kara ya taɓata, kwace
kanta ta yi tana cigaba da kukan ta miƙe ta nufo waje, wai zata je ta faɗawa Momma
ya taɓa mata breast ɗinta ya kuma rungumeta ashe ɗan iska ne shi ɗin. Bayanta ya bi
da sauri dan ya bata hakuri, sai da suka zo dab da bedroom ɗinsa ya capketa, tana
ƙoƙarin kwace kanta ya turata cikin bedroom ɗin, shiga ya yi ya rufo kofa har da
murza key.......... To ko me zai yi mata?.

••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥

Kwace Dr Raj ya isko Jaish saman sofa yana ɗan juyi a hankali hankali, cike da
kauna ya tambayesa menene yake damunsa haka, miƙewa zaune ya yi yana wanu nuku
nuku, kun san shi da kunya sosai, dan haka ya ƙasa iya sanar da Dr ga abin da yake
damuwansa, sai kawai ya ce babu komai barci yake ji. Dr ya fahimci tabbas akwai
abin da kanin nasa yake ɓoye mashi, amma tin da ya nuna baya san faɗa mashi sai
kawai ya kyalesa ya ce to ya tashi ya shiga ciki mana.

Ba musu ya miƙe ya nufi ciki, a lokacin ya kai kololuwan da ba zai iya cigaba da
rike kansa ba, har ya nufi bedroom ɗinsa sai kuma ya fasa ya juyo ya nufi na momma,
a cewarsa zai je gaisheta ne kawai..... GAISUWA TSAKIYAR DARE KUMA? WAI BA SHI NE
MA YAKE KIRANTA A WAYA DA SAFE BA? TO ME NA GAISUWAR DARE TUN DA NA SAFE MA A WAYA
AKE YINTA? TO MU DAI MUNA NAN DAI'DAI DA KAI ƊAN RAININ SENSE.

A sama farkon page ɗin nan na yi magana a kan kashe rai ba bisa haqqi ba da Sweetie
ta faɗawa Black Tiger, to waɗan ne rayuka ne suka kalatta a kashe su wato bisa
haqqi kenan, zan kawo maku su a jere domin ku sani.

A Musulunce, an haramta kashe rai ba bisa hakki ba, amma akwai wasu nau’ikan
laifuka da shari’a ta halatta a yankewa hukuncin kisa, ga sunan kamar haka, na
farko, idan mutum ya kashe wani da gangan ba tare da dalili ba, shari’a ta yarda a
kashe shi a matsayin ramuwar gayya. Wannan hukunci yana nan cikin Alqur’ani,
suratul baqara sura ta 2 aya ta 178, Ya ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku
hukuncin ramuwar gayya a kan kisanku.

Duk da haka, iyalan wanda aka kashe na da damar yafiya ko karɓar diyya kuɗin fansa
kenan, maimakon a kashe wanda ya aikata kisan.

Abu na biyu zinacewar mutumin da ya taɓa aure. Mutum da ya taɓa yin aure wato
baligi ne, yana da hankali, idan ya aikata zina, to hukuncinsa kisa ne ta hanyar
jifa da duwatsu. Wannan ya tabbata a cikin hadisai, cikin muslim lamba ta 1690 da
bukhari lamba 6814, Idan namiji da mace sun aikata zina kuma sun taɓa yin aure, to
a jefe kowannensu da duwatsu har su mutu. Sai dai, dole ne a samu shaidu huɗu ko
kuma mai laifi ya furta da kansa.

Laifi na uku riddah ficewa daga addinin musulunci. Mutumin da ya musulunta, daga
baya ya fita daga addinin Musulunci shari’a ta yarda a yi masa hukuncin kisa.
Annabi (SAW) a cikin Bukhari hadisi mai lamba 6922 ya ce. Duk wanda ya canza
addininsa ya fita daga Musulunci, ku kashe shi.
Sai dai, malamai sun yi bayani cewa dole a fara ba wa mutum dama ya tuba kafin
a aiwatar da hukunci.

Na huɗu fasad a kasa. Fasad fil-Ardh Wato Fashi, Ta’addanci, da cin zarafi.

Mutane da suka aikata manyan laifuka irin su fashi da makami, ta’addanci, ko cin
zarafin mutane a ƙasa, shari’a ta yarda a yanke musu hukuncin kisa. Allah cikin
suratul ma'ida ya ce. Lalle ne sakamakon waɗanda suke yaƙi da Allah da Manzonsa
kuma suke yin ɓarna a ƙasa shi ne a kashe su ko a gicciye su ko a yanke hannuwansu
da ƙafafunsu, ko kuma a kore su daga ƙasarsu. Wannan wani kaskanci ne a gare su a
duniya, kuma a Lahira suna da azaba mai girma da tsanani.
Wannan hukunci yana kan barayin da suka aikata fashi da makami, masu tayar da
fitina, da waɗanda suka haddasa ruɗani a cikin al’umma.
Na biyar luwaɗi da maɗigo. Homosexuality. A shari’ar musulunci, idan an samu
mutum yana yin luwaɗi (homosexuality), hukuncinsa kisa ne, kamar yadda wasu hadisai
suka nuna, a cikin tirmidhi hadisi mai lamba 1456 da Abu Dawud lamba ta 4462. Idan
kuka kama mutum yana aikata aikin mutanen Lut, to ku kashe shi da wanda ake aikata
da shi. Sai dai, malamai sun yi saɓani kan yadda za a aiwatar da wannan hukunci.

Waɗannan su ne manyan laifukan da shari’ar musulunci ta halatta a yankewa
hukuncin kisa. Sai dai dole ne a bi ƙa’idojin shari’a sosai kafin a aiwatar da
hukunci, don kauce wa zalunci. Haka kuma, addini ya fi son yafiya da gyara fiye da
ɗaukar fansa. Fatan kun gane? Ina san ku rinƙa sanin hukuncin addini ne dan shi ne
hukunci na gaskiya, shiyasa ma nike kawo maku kwararan hojjoji faɗar Allah. Allah
kasa mu cika da imani


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin bedroom ɗin, rashin mutane a ciki yasa
ba'a amsa mashi sallamar tasa ba, kuma dama already yasan momma bata ciki, dan
ɗazun ya sameta a part na King, kawai dai ya zo ne dan ya rasa in da zai je.

A saman sofa ya zauna yana tinanin me mafita a garesa? Dan shi ya rasa abin
yi, ya yi shiru cikin tinanin da yake yi ba tare da ya lura da akwai mutun a cikin
ɗakin ba, wayarsa dake aljihunsa ce ta fara ruri alamar shigowar kira. Shiru ya ɗan
yi tamkar ba zai ɗauki kiran ba, sai da ta kusa katsewa ne ya ciro wayar.

Yah Omerish shi ne sunan da yake yawo a saman screen ɗin, jikinsa dik kasala, da
kyar ya iya yin picking tare da kara wayar a kunnensa. Kamar wanda yake cikin
magagin barci ya ce. "Hello, good evening Yah Omerish". Daga ɗayan ɓangaren Smart
dake kwance a saman rest bed dake wajen balconynsa ya amsa mashi da. "Evening how
was your day?". .........Da kyar ya amsa da Alhdulillah, idan yana magana sai ya ji
kamar yana kara jefa kansa cikin wahala ne.

(Na manta na ce ba zan sake saka turanci a cikin rubutu na ba, saboda su Sumayya
sun yi complain kuma na ji kukansu dama ba yarenmu bane bamu da gadonsa, shegen
iyayi ne kawai irin namu,🥱 yanzu idan turanci ta mutu muna da gadonsa ne? Yen yen
yen mun ishi mutane. Wai mu ba zamu tsaya mu daraja yarenmu ba, ance Hausa novel ko
uban me ya kawo turanci a ciki?🤔 Hegu masu jajayen kunnuwa sun sa wasu basa kallan
yaren iyaye da kakanni da daraja, sun gurɓata mana tinani, sai shegen iyayi da
feleƙe muka iya😅 to ni dai mutane na ƴan Niger sun kawo korafi kuma na karɓa mun
raba jaha da masu jajayen kunnuwa, Allah yasa kada na rinƙa mantawa ina rubutawa,
kun san sabo da rubuta shi ne yasa ko kace ba zaka saka ba sai ka manta ka saka,
amma zan yi ƙoƙarin dainawa!!.)


"Ina momma? I have been calling her number since isn't going". Ya faɗa yana miƙewa
zaune. Dan ya ji alamar motsi a parlourn ƙasa, dan haka sai ya miƙe zaune dan ya
saurara da kyau.
"Ka kira number dad tana tare da shi yanzu". Jaish ya faɗa yana ɗaga kansa
sama. Unexpect kallansa ya sauka a kan bed ɗin momma, ɗan zaro idanunsa waje ya yi
yana kallanta, sam bai yi zatan ganinta a cikin ɗakin ba.

Miƙewa tsaye ya yi a hanzarce, tun daga Smart bai sallamesa ba ya katse kiran tare
da nufar in da take kwance. Like wow abin ya birgesa ya kuma bashi mamaki, ga shi
momma bata nan, so the thing sweet him over. Shiru ya ɗan yi yana tinanin me
yakamata ya yi kenan? Ya zuba mata idanun yana yi mata mayen kallo yadda ta
kudundune a cikin bargon, kallo ɗaya ya yi wa face ɗinta ya fahimci ta sha kuka
kafin ta yi wannan barci, a cikin zuciyarsa ya ji wani abin ta ɗan sokesa ganin
busassun hawayen nata, kun san akwai tsohon soyayyarta a kasar zuciyarsa, so idan
wani abin ya sameta baya jin daɗi, amma kuma yaki yardanwa kansa ya yi accepting
ɗinta hundred.

Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta ayyana mashi momma zata zo ta same shi, ai tuna
haka yasa ya yi gaggawar sanya hannunsa ya ɗauketa cak har da bargon momma ɗin dik
ya haɗa ya nufi bedroom ɗinsa da ita, buƙata ta biya, wai ita momma a nan ta ɓoyeta
sai ya kawo kansa ya bada hakuri ne, to ga shi dai ya ɗauke matarsa abinsa. MAHNOOR
SAI DAI MU CE ALLAH YA BAMU ƳAN TWINS IRIN UNCLES ƊINSU OMAID AND OBAID.....🥱

(Yauwa kun takurawa jikokin Akka fa my people's, kun saka masu idanu saboda suna da
sha'awa sosai, ku rufe mun baki shiru, kada na kara jin wata ta takurawa jikokin
Akka, dik duniyar yanzu ba haka ta zama ba? Ba haka kuke ba wai? Ko kun ɗauka bamu
sani bane? Mun san komai dan haka ku dai'na takurawa jikokin Akka dik haka kuke😒
kuma ni dai bana ganin laifinku, dan dama a karshen duniya sha'awa zata yawaita
sosai shiyasa za'a samu zinace zinace, da addini nike rubuta littafina ba da ka
ba!! Na san me nike yi, wasu abubuwan sai gaba idan suka bayyana zaku ce mun
karanta a littafin Princess Teema da jimawa)

Shi kuwa Smart Jaish yana katse kiran ya kira number King tare da miƙewa ya nufo
waje domin ya duba waye mai motsi a parlourn ƙasa bayan ya san dare ya yi, yau a
gidan Auta zai kwana da su, dan jiya sun yi mashi complain a kan ba zasu iya cigaba
da kwana ba tare da shi ba, suna tsoro, shiyasa ya ce wa daddynsa ya yi tafiya,
amma yana tare da su, baya san kaisu gidansu kuma, dan baya san dad ɗinsa yasan ya
je Kingdom of power ko ya haɗu da mahaifinsa, momma ta ce ya ɓoyewa dad ɗin nasa,
dan ba ƙaramar dirama za'ayi ba, King zai ce a bashi ɗansa, shi kuma daddyn Smart
kun san aikin da suke aikatawa da Smart a ɓoye wanda idan King ya ji ba zai taɓa
yarda ba! Ko ita momma ta ji wannan aiki ba zata yarda ba!! So kun dai san daddynsa
ba zai taɓa yarda ya koma kingdom of power ba, yanzu ita momma ta rasa yadda zata
ɓullowa wannan al'amari, ita kanta yanzu tana san Smart ya dawo gareta tun da
already yanzu King yasan yana raye, to burinta ya dawo kusa da ita tana jin
ɗuminsa, ta kuwa san yayanta dai ba zai yarda ba, wlh akwai cakwakiya ba kaɗan ba,
sai ma King yasan aikin da Smart yake yi tukunan, a nan ne za'ayi yaki kam.

Bugu ɗaya King ya ɗauka, dan a lokacin yana hira da momma ne a kan dawowar Smart
ɗin, ya ce ya umarceta da ta dawo mashi da ɗansa kamar yadda ta ɗaukesa ta kai shi
can, to hiran da suke yi kenan, ta yi ƙoƙarin tausansa a kan ya bari zuwa ɗan wani
lokaci, a take ya gwada mata ɓacin ransa tare da ce mata wlh ko wata ɗaya ba zai
iya bari Smart ya kara a can ba, dole ya dawo wajensa ya ji ɗumin ɗansa da ya rasa
tsawon shekaru.

Da okey kawai ta amsa mashi, amma ta sha jinin jikinta, dan bata san da wani ido
zata iya fuskantar mommyn Smart da sunan zata ɗauki ɗanta ba, Allah sarki, babban
damuwarta ma shi ne su daddyn Smart ɗin Allah bai basu haihuwa ba har suka tsufa,
sun ɗauki son duniyar nan dik sun ɗaura a kansa, kuna dai ganin yadda suke rayuwa,
idan baka sani ba ba zaka taɓa cewa ba su suka haifesa ba.

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

"Good evening dad". Ya faɗa yana tako stair case a hankali cikin natsuwa. "Evening
my love how was your day?". Da Alhamdulillah ya amsa kafin ya ɗan yi shiru yana
cigaba da tafiya a natse.

"Dad where's momma?". Ya faɗa yana warware igiyar rigar barcin dake jikinsa,
dan ya ji igiyar ta ɗan kama shi sosai, shi ne zai sukurkutata. "My son kowani
lokaci mommarka kawai baka san yin hira da ni ne?". Cikin murya mai rauni King ya
yi maganar, Allah ya gani yana bala'in san Smart fiye da tunanin mutum.

"No dad, ina san yin hira da kai mana, in the morning zamu yi hira sosai, but
now give momma the phone I want to ask her something". Jinjina kai ya yi tare da
miƙawa momma wayar ya miƙe ya nufi toilet, dama wanka zai shiga suka tsaya hira da
mommar.

Kasa shi kuma Smart ya sauko parlourn akwai duhu babu haske, kai tsaye ya nufi
switch dan ya kunna wutar...... "Hello momma". Ya faɗa. Ajiyar zuciya ta sauke
kafin ta amsa da. "Son how was your day?". "Alhamdulillahi what of you?". .... Da
Alhdulillah ita ma ta amsa mashi. Dai'dai lokacin ya kunna wutar parlourn haske ya
gauraye ko'ina.

Zaune take saman sofa mai zaman mutun biyu, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, hannunta
rike da cup da mai aikinsa ya haɗa mata hot tea mai kauri. Sanye take da sleeping
dress, gown ne zuwa kyawawan cinyoyinta kusa da gwiwa, sai yar pant daga ta ciki,
launin kayan pink color hakan yasa ta yi kyau sosai cikinsu, ga skin ɗinta luwai
luwai, ta zubo gashin nan nata ta gaban saman shoulder ɗinta, kun dai san Pretty
bata shiri da yunwa, shiyasa ta fito cin abinci abinta, ita kuwa Auta tana ɗaki sai
gwada number Hoorain take yi baya ɗauka saboda ya karɓi alluran barci ɗazun, ya
birkicewa commander a kan ta ne yasa commander ɗin ya ce a watsa mashi alluran
barci ko kwakwalwarsa ta huta, shiyasa take ta kira ba'a ɗaga ba, har kuka ta yi.

Zuba mata idanu Smart ya yi yana kallan yadda take shan tea ɗinta a natse, bata
ko ɗago kai ta kallesa ba, abincinta kawai take ci, wlh Pretty akwai miskilanci
fiye da tunaninku, ba komai take ɗaga idanu ta kalla ba sai abinci ne bata yi mashi
hakan. Wani irin faɗuwar gaba ya ji ganinta a cikin wannan shiga.

"Son baka jina ne?". Momma ta faɗi hakan har sau uku, amma bai ji ko ɗaya ba,
saboda hankalinsa yana a kan Pretty, yarinya kamar wata aljana. Har momma ta katse
kiran ta sake kiransa, jin karar wayar yasa ta ɗan ankara tare da sauke ajiyar
zuciya, sannan ya katse kiran ya kirata, har lokacin bai zare kallansa daga kanta
ba, ita kuma tamkar bata san da mutum a wajen ba, tea ɗinta kawai take sha, ko irin
ta ɗago kanta ɗin nan, ya ɗan yi

Please Login or Register in order to submit comment