Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 17 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da shi
ashe tin lokacin yake a sume, yanzu haka yana hospital ɗin cikin kingdom ɗin ana
duba lafiyarsa, ita ma Chuchun an bata gado.

So King ya ce a ɓoyewa Momma da Jaish hakan kada a bari su sani, sannan a ɓoyewa
Jaish batun ɓatar Zunaira, a ce mashi tana Dubai, dan in ba haka na za'a samu
gagarumin matsala, kun dai san bai jima da dawowa cikin hayyacinsa ba, so a cewar
King kafin Jaish ya damu ya fara nemanta har ya ce zai bita Dubai to su kuma sun yi
gaggauwar gano in da take!........... My people's shin kuna ganin hakan zata yiwu
kuwa?!.

Miƙewa momma ta yi, dik sai ta ji jikinta ya kara mutuwa sosai, Allah sarki
ciwon Guyson ne yake ratsa jininta ba tare da ta sani ba.

Alkyabbarta ta ɗauko ta ɗaura kan kayan jikinta, ta nufi parlourn.

Ba karamar mamaki ta sha ba ganin uncle Jahiz rike da jariri a hannu, yaron ya
kwanta luf a jikinsa, idanunsa kuma a buɗe sai dai bai yi kuka ba, yana ta faman
buɗe baki alamar yana jin yunwa sosai.

Tsuma da san jin daga ina ya samo jajiriri yasa momma ta kasa iya zama kafin ta
tambayesa, cike da mamaki ta ce.

"Jahiz....... Ina kuma ka samo baby?".

Zama ya yi saman mai zaman mutum ɗaya sofa kafin ya bata amsa da. "Zauna mama sai
ma baki labari, dama kuma hakance ta kawoni wajenki".

Idanunta a kansa ta samu waje ta zauna saman two seater.

Dik a ƙage take da san jin in da wannan yaro ya fito, ta tsare yaron da kallo,
lokaci guda ya shiga ranta, dama ta jima rabonta da jariri a hannu, shekaru wajen
14 fa yanzu, tin kan Zunaira, ai kunga zata so jariri sosai a yanzu.
Miƙa mata babyn ya yi. Ba musu ta yi saurin karɓa tana kallon babyn cike da
kauna, har da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Dawo da kallonta a kan uncle Jahiz ta yi tana jiran ta ji bayanai.

Ɗan gyaran murya ya yi kafin ya fara bata labarin haɗuwarsa da su Khadija, yadda
suka bugesu da mota da kuma halin da suke ciki a yanzu.

A ɗan hanzarce ta ce. "To yanzu ina suke?".

"Suna hospital na cikin Kingdom ɗin nan, naga a Abuja ba wani kula da su sosai
za'ayi ba, kuma kinga dik wani abin da ya samesu alhakin a wuyarmu zai rataya,
shiyasa na nemi takarda daga hospital ɗin can dan mu samu damar zuwa da su nan a
dubasu da kyau".

Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas haka ne, dik abin da ya faru da su Khadija a
wuyarsu ya rataya, sannan ta dawo da kallonta a kan babyn dake ta faman buɗe baki.

"Jahiz yaron nan ai yunwa yake ji". Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe mashi fuska da kyau
ta yadda zai samu damar ganin haske da kyau!.

"Yeah tun jiya babu abin da aka bashi, mahaifiyarsa tana kwance bamu da tabbacin
tana raye ma".

Sosai momma ta ji tausayi ya kamata, sai ta ji tana san zuwa ta gansu, amma babu
hali, bata da damar fita, dan haka sai ta ce da shi.

"Ba damuwa, zan kula da yaron, kai kuma ka kula da marasa lafiyan har zuwa su
samu sauki".

Miƙewa tsaye ya yi, cikin nitsuwa ya ce. "Yauwa momma ina godiya, dan Allah ki kula
da yaron nan sosai, saboda ina kaunarsa, ya shiga rai'na da kallon farko, yanzu dai
bari in je hospital ɗin ma in duba su, dan tun da muka miƙasu ga likitoci ban sake
komawa ba".

Jinjina kai ta yi kafin ta amsa da. "In ka fita ka turo mun Haulat, dan wannan
yaron ɗanyen jariri ne da ko wanka ba'ayi mashi ba".

Da okey ya amsa mata, sannan ya nufi waje.

Kurawa yaron idanu ta yi yana ta kallonsa, kyakkyawa kamar a bata shi kyauta, ga
idanunsa a buɗe dara dara.

Da fitarsa bai fi minti ɗaya ba sai ga mama Haulat ta shigo cikin hanzari. A gaban
momma ta zube gwiwowinta.

Miƙa mata babyn momma ta yi tare da miƙewa tsaye.
"Ki yi mashi wanka, sabon haihuwa ne, sannan ki bashi madara mai ɗumi, ki
yi mashi dik abin da ya dace".
Tana kai karshen maganar ta wuce izuwa bedroom ɗinta, dan jikinta babu kwari,
alamar zazzaɓi mai zafi ma take ji.

Wucewa da babyn izuwa ɗakinta mama Haulat ta yi, ita ma sai kallon yaron take yi,
da alama babyn Khadija yana da farin jini matuƙa, dan kowa ya kallesa sai ya kama
zuciyarsa da kauna.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
A can cikin fada kuwa, ran King ya gama ɗacaca matuƙa, hankalinsa a tashe, ga
guyson da Chuchu rai a hannun Allah, ga Zunaira ba labari, Hoorain ya gudu, dan
haka sai ya yanke hukunci cikin fushi, ya ce da commander Zafar a je a yaki Daular
Qahtaniyawa, a kashe dik wanda ya gwada gardama, a tattaro mashi mata da maza yara
da manya dik a gurfanar mashi da su a gabansa, daga yau sun zama bayi a kingdom of
power..... Tashin hankali. Cikin fushi ya yanke hukunci fa.

A dai'dai wannan lokacin da King yake umartan commander Zafar da a ruguje Daular
Qahtaniyawa, ya yi dai'dai da lokacin da Queen Zarina take tsaye a saman kafafunta
cikin wani irin ƙasaitacciyar shiga na ban mamaki, gaba da bayanta dikka dakakkun
warriors ne da suke gadin lafiyarta ta yadda ko guda ba zasu bashi damar taɓata ba.

A saman wani stage take tsaye wanda ƙasan stage ɗin wasu irin mahaukatan manya
manyan warriors ɗinta wanda ta gina masu jikinsu da tsafi ne, ganinsu da ido kawai
sai yasa zuciyar mutum ta buga ya mutu, basu da kyan gani ga bakar mugunta a
fuskokinsu, babu rahma ko ɗigo a tattare da su.

Sai dai dikkansu dik da wannan horo da suka samu ga kuma tsafi suna tsaye ne a
bayan wani dakakken warriors guda ɗaya wanda shi ne a gaba da su yake jagorantar
wannan runduna.

Ko baka san fuskar Hoorain ba idan kaga wannan mayaka tabbas zaka iya alakanta shi
da Hoorain assistant commander na kingdom of power......... Tashun hankali.
Dan daga yanayin tsayuwarsa cikin jarumta da daki zai iya tabbatar maka da
basu da banbanci da Hoorain...... Tashin hankali.

Kai Hoorain ne ma, dan wannan irin abu haka ba zai taɓa zama waninsa bane, shi ɗin
ne!! Tab akwai matsala, kenan Hoorain dama Queen Zarina yake yi wa aiki? Menene
yasa ya ci amanar kingdom of power har da mahaifinsa haka? Kenan ya zaɓi wasu a kan
mahaifinsa? Ya aka yi Zarina ta san Hoorain? Tin yaushe ya fara yi mata aiki? Aiya
mahaifinsa ma zai iya kasancewa abin yarda kuwa? Anya shi ma ba maciyi amana bane
kuwa? Kada ku manta a baya alkalamin princess Teema taku ta amana na gaya maku cewa
bayan mammiensu Sarina akwai waɗan da suke cin amanar Kingdom of power suke aiki da
Queen Zarina, kuma mutane da suke da kusanci sosai da King Zuhair, yardaddunsa ne,
in baku manta ba na taɓa faɗa maku zaku sha mamaki a lokacin da gaskiyar zata
bayyana, zaku sha mamaki idan kuka gane maciya amanar kingdom of power, ku dai muje
zuwa, akwai tashin kai a gaba.

________________________________🔥

Yana tsaye ne tamkar wanda aka sassaƙa, dik da yana cikin hular mayaƙa, hakan ba
zai hana ka fahimci babu rahama da imani a tattare da shi ba.

Cike da izza da zallar madarar zalinci Queen Zarina take basu umarnin kalar kisar
da take da buƙata zasu yi wa kingdom of power, har da cewa su ɗauko mata Jaish su
kawo mata shi, dan a duniya idan akwai wanda take so to ya biyo bayan Jaish yaro
ɗan Mommarsa, dan haka a kashe kowa a ɗauko mata Jaish, a shekaru fa ta kai ta
haifi Jaish, amma kuma zuciyarta ta kamu da kaunarsa dan tabbatar matacciyar
zuciya.

Allah sarki yaro ɗan Mommarsa, yana can yana sha'aninsa ana mutuwa a kansa bai da
labari.

Cikin girmamawa waɗan nan bakaken azzaluman mayaƙan nata suke karɓar umarninta,
zaluncin mutanen nan ya kai su iya zaro jariri daga cikin uwarsa su kashe shi su
jefar da gawar babu abin da ya damesu, basu da tausayi ko ɗigo a ransu, ko da yake
zukatan da ake sarrafawa da tsafi yaushe suka ga imani da tausayi?.

Akwai cakwakiya, King Zuhair ya bada umarni ga mayakansa da su je su ruguje
Daular Qahtaniyawa su kashe kowa su haɗo mashi kan mayakansu da bayinsu su zo su
zama bayi a kingdom of power ba tare da ya tabbatar da cewa King Al-Mustapah ne ya
ɗauki Zunaira ko ba shi bane, kawai ya yanke hukunci cikin fushi babu bincike. Ita
kuma Queen Zarina ta bada umarnin a zo a kashe mata kowa a Kingdom of power a kama
Jaish a kai mata shi su yi aure. Me kuke tinanin zai faru?.

A gefe guda kuma evil kingdom suna can suna ta gagatumin shirin da idan suka
dinfari kingdom of power dole su rugujeta su shafeta a doran duniya, wani irin
mummunar kafurin shiri suke shiryawa.

Ga shi shi kuma King Zuhair yaki yarda ya karɓi tuban King Al-Mustapah bare ma har
su haɗa kai wajen ganin bayan Queen Zarina da su King Abdul Aziz, shi kaɗai kuma ni
da ku mun san wlh ba zai iya yin faɗa da waɗan nan masarautu har ukun ba, ga ubansu
Black Tiger a gefe, wanda shi tuni ya shirya aje a durkusar mashi da kingdom of
power a kawo mashi King Zuhair gabansa ya zo ya yi mashi sujjada ya lashi
kafafunsa, batun fitarsa fada ya dakatar da shegun wayakan Robbot ɗinsa ba su afka
kingdom of power ba, amma yana nan da shirin a ransa, kuma zasu aiwatar, yanzu so
yake ya shiga fada.

Hankalinsa ta ɗan kwanta, ya nitsu, bayan haka ya ɗauki mataki a kan Sweetie, idan
ta bashi Spender sai su ruguje kingdom of power, wannan ne shirinsa a yanzu.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Yau hospital cike yake da ahalin King, Jawad da bai san Jaish ya dawo ba yana
hospital zaune kusa da gadan da aka bawa Chuchu, su uncle Taheer dik suna cikin
hospital ɗin.

Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsu a cikin asibitin, sai dai da ya tambayi me yake
faruwa? Basu faɗa mashi Zunaira ta ɓata ba, sai suka ce mashi rashin lafiya ne na
guyson da Chuchu.

Ya yarda da hakan, dan haka ya je ya duba jikin Chuchu kafin ya fito ya nufi ɗakin
da guyson yake kwance. Bawan Allah tamkar babu rai a jikinsa.

Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsa a haka, sai ya yi tunanin ko ciwonsa ne ya tashi,
dan haka sai ya yi mashi addu'a sosai tare da tofa mashi, sannan ya fito ya shiga
wajen su Khadija.

Harda mai keken napep ɗin nasu dik aka taho da shi, idan baku manta ba na faɗa maku
shi ma ɗan arewa ne, ɗan Kano ne, so da su uncle Jahiz aka ce masu babu kowa nashi
da ya zo, sai suka haɗa da shi kawai suka kawo su ana jinyarsu.

Dik wannan bidiri da ake yi fa Sarina da Mammiensu suna part ɗinsu hankalinsu a
kwance suna shabgar gabansu, sai kulla wani minahincin suke ta faman yi, da alama
wannan karan mugu mugun abu Mammie take shiryawa wannan ahali!!.

Dai'dai lokacin da uncle Jahiz ya sako kafarsa cikin ɗakin dai'dai wannan lokacin
Zee ta fara motsi numfashinta yana fita da karfi karfi.

A hanzarce ya ƙariso gaban bed ɗin nata, ɗakinta daban da na Khadija, iya kaɗai ne
nan.

Ganin tana buƙatar taimakon likitoci ne yasa uncle Jahiz ya yi saurin juyawa ya je
ya kira likita.

Oxygen suka zo suka sanya mata dan numfashinta ya dai'dai, a saman kujerar da aka
tanada dan masu jinya uncle Jahiz ya zauna yana tinanin ina ahalin su Zee suke?.
Tsananin tausayinsu ne ya kama shi sosai.

Oh ta ko'ina ba sauki fa, to bari dai mu leƙa Dubai muga me ake ciki ne wai!.

•••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••••🔥

Tuni Ramish ya miƙawa jami'ansa Leesharh, dama sun jima suna neman kamata, sai yau
dubunta ya cika. Sai dai fa ni da ku dik munsan halin Leesharh da ɗan banzan taurin
kai, yadda aka rinƙa fama da ita a court ta yi magana lokacin da ta kashe mamarta
ta ki buɗe baki ta yi magana haka yanzu ma ta yi.

Dik wani azabtarwa sun yi mata amma taki ta yi magana, har ya kai ya kawo bata iya
takawa da kafafunta saboda azabtarwa Ramish, amma dik da haka taki basu haɗin kai,
daga karshe ma da suka matsa mata sai ce masu ta yi dan Allah su kasheta kawai ta
huta, dan ita dai bata ma san a kan me suke tukumarta ba.

Wannan magana ya matuƙar konawa Ramish rai da har yasa bindiga zai harbeta ɗin da
gaske, Bilal ya dakatar da shi ta hanyar kwace bindigar ya ce dan Allah Ramish ya
barshi da case ɗin a hannunsa, zai sakata ta yi bayani cikin ruwan sanyi, Ramish
zafin zuciyarsa ta yi yawa, abu kaɗan ya hasala, dan haka ya bar mashi case ɗin
kawai.

My people's kun yarda Ramish ya barwa Bilal wannan case ɗin? Kada ku manta Leesharh
ta ce ta taɓa ganin Bilal a gidan masu nikaf, sannan kada ku manta Bilal shi ya
fara nunawa Leesharh kauna da tausayawa a gidan, meyasa Bilal ya hana Ramish ya
kasheta? Kai bari dai na barku haka kada masoya Bilal su yi mun zanga zanga, amma
dai bani na faɗa ba, Leesharh ce ta ce ta taɓa ganinsa a gidan masu nikaf, dan haka
dole mu zargesa!!.

Tsabar rainin wayo irin na Leesharh ma, har da ce masu ita fa wannan ba wayarta
bace, kuma bata san a kan me ma suke magana ba.

Wato masu nijaf sai da suka yi binciken wacece Leesharh kafin su bata wannan aiki,
irin wannan taurin kai haka? Dama irinta ƴan ta'addan suke so.

Ramish bai so barinta a raye ba, amma Bilal ya ja shi suka bar ɗakin da ake
horata a ciki ɗin, sai daɗin baki da kalamai masu daɗi Bilal yake yi mashi dan
zuciyarsa ta huce ya mance da batun Leesharh.

Yasan wanenen Ramish sarai, yasan idan ransa ya ɓaci ya ce zai yanke hukunci a kan
abu to fa sai ya yi, shiyasa yake mashi daɗin baki dan ya mance da komai.

(Ni kuwa nace da a yadda yake cikin ɓacin rai yanzun nan King ya yi mashi waya ya
ce an sace Zunaira mana😂 me kuke tunanin zai faru?😂 Tab na yi nan babu ruwana😂 🥱)

A can gefe kuwa, wuni kuka kwana kuka Sharifat take yi, ta gama shiga tashin
hankali da damuwa, Allah sarki, tana kaunar Leesharh tamkar ranta, bata taɓa zaton
cin amana daga gareta ba, yau tsawon kwana uku tana kuka a kan rashin Leesharh, har
ƴar rama ta yi.

Abu Abdussalam ya yi rarrashi har ya gaji, shi ma Leesharh ta kariyar mashi da
zuciya, ya ji baya san sake jawo wani jikinsa kuma, hakika ya shiga tashin hankali.

Ita kuwa Ummie, wlh ranta fes, sai addu'a ma take yi Allah yasa Ramish ya kashe
Leesharh kowa ma ya huta.

Ramish da kansa ya yi wa Leesharh azabar da sai da ta zaɓi mutuwa a kansa, irin
azaban da yake ganawa manyan ƴan ta'adda da jami'ansa idan suka yi laifi ya rinƙa
gana mata, amma Leesharh ta daure ta shanye wannan dukka.
Ko sa yake ai ta saba da wahala tun da ta yi zaman gidan AAJ, yarinyar da ake
tuhuma da kashe mahaifiyarta ai kunga dole ma zata yi fin hakan.

Hmmmm wato fa Dubai ma ta kama da wuta, ta ko'ina dai ba sauki, to bari dai mu leƙa
France muga ko da ɗan sauki sauki can.

•••••••••••••••••FRANCE••••••••••••••••🔥

Sosai Smart ya sha barcin na good 4 hours, sannan ya farka. Misa call ɗin mom ya
kai 10 a wayarsa, sai kiransa take yi yaki ɗagawa, da ƙoƙari irin nata wai so take
yi ya zo su yi bankwana da iyayen Heleena zasu koma England, har suka tafi ba'a
samu ya ɗaga call ba.

Robbert kuma mamaki yake ta yi a kan ya aka yi wannan nuclear da aka gwada bata
dawo ba, kada ku manta shi bako ne a wajen, yanzu yake koyan aiki. Batu na gaskiya
makamin nuclear ba'a harba shi sama kuma ya dawo, idan aka saita shi in da ake sam
ya je aka harna shi ya tafi shikenan, ba zai dawo ba, wannan shi ne nuclear na
gaskiya.

So already a cikin takekken teku Smart ya saita shi, dan haka yana tashi barci ya
je ya duba computersa dan yaga yadda makamin ta tarwatse a cikin ruwa, dama so yake
yaga karfin aikinta, idan ta yi yadda yake da buƙata sai su cigaba da haɗa irinta,
wannan shi ne gaskiya.

Robbert dai kasa hakura ya yi har sai da ya tambayi Smart ya aka yi makamin
bata dawo ba.

Iska Smart ya bawa ajiyarsa, dan bai amsa mashi ba, ya wuce ya yi wanka tare da
sauya kayan jikinsa, ya fito ya umarci yaransa da su cigaba da haɗa irin wannan
makami dan ya yi mashi yadda yake so hundred over hundred!.

Daga haka ya nufi gidansa.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




•••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••••🔥

A hankali jiki dik a mace Ronnie ya hau saman escletor domin ya haura izuwa
parlourn Black Tiger, jiya kwana suka yi suna cashewa, yanzu haka idanunsa dik
barci, kuma yana da Exams a school da zai rubuta yau, kamar wanda aka hana shi yin
barci jiya, wato shi dik in da sharholiya take yana nan wajen abinsa, bashi da wata
damuwa.

Allah sarki jiya Floris ta rufe mashi kofan ɗaki hakan yasa ya je ya yi rawa a
tare da Angela, kun san jiya ta yi fushi ai, ta kwana kuka Ronnie ya kwana taka
rawa abinsa, yo dama shi me ya damesa? Ai sai dai ta kashe kanta da bakinciki, shi
bai taɓa cewa yana san ta ba, infact Ronnie bai san menene soyayya bama, kunga kuwa
babu fushin wata mace da zai hana shi yin abin da yake da ra'ayi!!.

Ko Sweetie tausayinta kawai yake ji, bai taɓa cewa yana santa ba, hasalima wlh a
yanzu kam babu soyayyar kowace mace a ransa, Sweetie ma shakuwa da kauna ce irinta
kanwa da ya ɗauketa, ita kuma Floris kyanta yake burgesa, that's all.

Yanayinsa idan kuka ga yadda yake treating ƴan'mata sai ku yi zatan sansu yake yi
ko wani abin makamancin haka, ainahi zuciyarsa tana da rauni a kan halittar macece
sosai, amma kuma ai kunga jarumi ne a kan maza sosai, yana zubar da maza a wajen
Wrestling, mata ke cin riba a kansa.

Yana san zuwa room ɗinsa duba Sweetie, amma ya fi san ya fara zuwa wajen
yayansa.

Yana zuwa ya buɗe kofar ɗakin da password ya shiga ciki. Ɗan jujjuya koreans eyess
ɗinsa ya yi yana neman ta ina yayansa yake? Dan ɗakin tana da girma sosai.

Like wow he was so surprised na ganin alamar babu mutun a cikin ɗakin, shiru ya ɗan
tsaya tamkar mai nazarin wani abin, yau kwata kwata baya san zuwa school, dik san
shi da karatu yau dai baya jin zai je.

Calmly ya fara takawa dan ya ƙarisa ciki ya tabbatarwa da kansa da gaske yayansa
baya nan. A bakin bed ya zauna yana cigaba da bin ɗakin da kallo, shi ko tsoron
ɗakin ma baya ji.

Hamma ya fara dakawa alamar barcin tana san a biyata bashin da aka ci daren jiya
da ba'ayita ba, ɗan yamutse fuska ya yi tamkar guyson a gabansu Yah Ramish.

Shi da zai je ya yi shirin tafiya school sai ga shi ya gyara ya karkata ya
kwanta a saman bed ɗin abinsa............ Kafin ƴan mintina barci ta yi awon gaba
da shi.

Ita kuwa Floris ta sha kuka har kamar ranta zai fita, daga karshe barci ya yi awon
gaba da ita zaune a bakin gado, sai da ta kwala kanta da jikin headboard na bed ɗin
ne, da ta ji zafi sai ta karkata ta kwanta haɗe da rungumo pillow tana jin kunan
rai tana kuma sauke ajiyar zuciya har barci ya yi awon gaba da ita.
After some hours.

A hankali Sweetie dake kwance s saman bed ɗin Ronnie ta fara motsa idanunta da suka
yi mata bala'in nauyi, zara zaran eyelashes ɗinta a jike suke da hawaye, alamar
kafin ta yi barcin nan hawaye sun zuba daga idanunta sosai.

Jikinta dik tamkar an girka dik wasu gaɓɓai ɗinta, tsokar namar jikinta dik sun yi
mata tsami tamkar wadda aka yi wa luguden duka da sandina, harta tongue ɗinta ji ta
yi tamkar an sanya igiya an ɗaure mata shi, taci bakar wahala daren jiya a hannunsa
ne, yarinya ta ji kamshin mutuwa, Allah ma ya taimaketa yana san Spender a hannunta
yasa ya yi ƙoƙari ya yi mata magani ta tashi bata mutu ba, da jefar da ita zai yi.

Gashin kan nan nata tamkar wanda aka sanya kum aka baza mata shi, dik ya
cukurkuɗe kamar kayan wankin da aka kwato daga bakin kura, idanunta har sun kumbura
sun yi jajir da su, har ta kara hasken wahala yar ƙaniya.

Ta sha madarar mamaki matuka a lokacin da ta waro idanunta ta ganta a cikin
ɗakin Ronnie, bata yi tsammanin hakan ba, ta yi zaton ganin kanta a wata duniyar
kamar yadda ya nuna mata tun farko zata yi, ya aka yi ta dawo nan? Ta jefawa kanta
tambaya.

Allah sarki, ta yi zaton ta yi bankwana da su Ronnie kenan, ashe ba haka abin yake
ba, gata ta dawo garesu.

"Good morning sarkin barci"............ Kamar daga sama ta jiyo sautin muryar
Ronnie ta bayanta.

Da sauri ta juyo da kallonta ta wajen. Yana tsaye gaban mirrorsa, sanye yake da
wando three quter jeans sky blue, da round neck polo shirts black color, ya yi
masifar kyau cikin bakin rigar, tamkar ka sace shi ka gudu.

Yana tsaye yana ƙoƙarin sanya ɗan kunne a kunnuwansa, ta cikin mirror ya hango ta
farka yasa ya yi mata magana. All his though since yesternight da suka rabu take
barci up till now, shiyasa ya ce mata sarkin barci, bai san ita ɗin ma dik kanwar
ja bace, ai kusan a tare suka yi barci wato da safe kenan, and ita daga suma ne ta
farfaɗo ta zarce da barci.

Ajiyar zuciya a bayyane ta sauke mai matuƙar sanyin gaske wanda yasa Ronnie
juyowa gareta da kyau. A yau dai ƙaƙalo murmushin dole ta yi ta sakar mashi, dan
bata taɓa tinanin zata rayu ba, ta sha bakar wahala, so babu walwala a tattare da
ita, infact bata ma jin daɗin jikinta, dik wani sassa na jikinta kamar na nata ba.

Bayansa ta kurawa kallo sosai kafin ya juyo, idan ka gansa a yanayin yadda yake
tsaye ɗin nan sai ka ji gabanka ya faɗi, ko ta baya ka gansa kasan ya cika cikar
halitta sosai, ga faɗin baya sosai saboda wrestling ɗin da yake yi, sexy body kamar
na yayansa.

Gashin dake kwance a bayan wuyarsa ta zubawa idanu tana kallo, sai a lokacin ta
lura gashin kan Ronnie fa kamar combination ne na two colors ba zallar white bane,
dan daga tushen gashin nasa zaku ga kamar ruwan toka toka mai haske haka.

Ɗan runtse idanunta ta yi tana ƙoƙarin tunani ina ta taɓa ganin irin wannan gashin?
Tabbas kafin idanuwanta su dai'na gani a lokacin da take forest wlh ta taɓa kallan
mai irin wannan gashi.

Wani irin juyawa da wani sadaukin warriors ya yi da karfi ne yasa gashin
kansa ya pyaɗeta a wuyarta, da sauri mum ɗinsu ta ɗauketa daga
wajen................... Da karfi ta sauke ajiyar zuciya, tabbas ta tuna in da ta
taɓa ganin sak irin wannan gashi, tun mum ɗinsu tana a tare da su a forest, akwai
wani lokaci da wasu warriors suka kai masu hari zasu ɗauki mum ɗinsu, tabbas a nan
cikinsu ta taɓa ganin mai irin wannan gashi, to ko waye shi? Kuma a yanayin girman
jiki da kira ba zai wuci kamar Ronnie ɗin ba!.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Ɗan ciza laɓɓanta ta ɗanyi kafin ta motsa jikinta zata miƙe zaune. Sai dai kash, ta
ƙasa iya motsawa bare har ta miƙe zaune, gaɓɓanta tamkar an ɗaure mata su.

Ronnie ya lura da ita kamar ba lafiya take ba, dan tin daga kan yanayin yadda ta
sakar mashi murmushi ya fahimci lallai akwai matsala, dan wannan ba ƙayatattcen
murmushin da ta saba sakar mashi bane.

"Sweetie are you okey?"................. Da mamaki sosai a saman face ɗinsa ya
yi maganar.

Ita kuma kyan da ya yi mata a lokacin da ya juyo gareta kawai take kallah.

Cikin kasala da nitsuwa ya tako zuwa in da take, jikinsa dik a mace. A gefen bed
ɗin ya zauna yana kallon fuskarta, sai a yanzu

Please Login or Register in order to submit comment