Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 39 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uncle Jahiz yake ji da shi bai isa ya karewa albarkatun
jikinta kallo haka ba.

A yanzu haka zuciyarta ta raya mata uncle Jahiz ɗan iska ne, kada ta yarda
da shi ya je ya cuceta ya yi mata ciki kamar Khadijah, wannan shi ne babban dalilin
da zuciyarta ya rike yasa ta yi baya sosai da shi, ta ji bata san sake haɗa inuwa
da shi, amma kuma tana san ganin Khadija, kuma kun san dole sai ta hannunsa zata
samu damar ganinta.

Ta kai 30 mins da kammala shiri, amma ta samu waje saman ɗaya daga cikin drawers
dake cikin ta yi zamanta tana tinanin mafita a gareta, dan wlh bata ga abin da zai
sa ta sake bari ya kalli surar jikinta har haka ba. Shi kuwa zama ya yi yana
jiranta, tunanin kyan surarta da kwaɗaituwa da shi yasa bai ga tsawon lokacin da ta
ɗauka bata fito ba, sai yake ganin kamar yanzu ta shige.

Sai da suka kara wani 20 mins a kan wancan 30, nan ma sai da yaga kiran Dr
sannan ya miƙe tsaye ya nufi dressing room ɗin cike da mamakin me ya hanata fitowa?
Shi bai san cewa mu ƴan Nigeria muna da alkunya ba, dan shi bashi da shi sai yaga
kamar kowa ma bashi da, a'a mu Nigerians muna da shi sosaima.

Ya sha madarar mamaki na ganinta zaune shiru ta buga uban tagumi, tinanin
Khadijah da ta afka yasa bata ji shigowarsa bama, sai jin sautin muryarsa ta yi
yana faɗin. "Zee lafiya kika zauna a nan?".

A ɗan razane ta ɗago ta kallesa. Kallo ɗaya ta yi mashi ta yi saurin kawar da kai,
ta tsani maza dama idan baku manta ba, da shi kaɗai ta ɗan saki jiki ashe shi ma
ɗan iska ne, wani tsanarsa ce ta ratsa zuciyarta, sai ta ji kamar ta gudu ta bar
gidan, amma ina zata je to idan ta gudu?.

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da babu komai. Ko kaɗan bai kawo aransa da wata
matsala ba, dan shi yana ganin ai normal ne kallan da ya yi mata.

"To tashi muje Dr na jiranmu". Ya faɗa idanunsa a kan kirjinta dik da ta sanya
kaya.

Da yake bata ma san fita zasu yi ba sai ta ji zancen wani irin, a ranta ta
furta yanzu haka zata jera da wannan ɗan iskan? Sannan su shiga mota ɗaya a gidan
baya, bayan haka su je hospital? Wlh ba dan Khadijah ba bata ga abin da zai sa ta
sake ɗaga idanu ta kalli mutumin nan har ta jera a tare da shi ba.

Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufo shi, a maimakon ya wuce gaba sai ya ce mata ta
yi gaba zai rufa mata baya, aikuwa nan fa ta ce babu wannan magana, kar ta fito ta
ce mashi ita a'a sai dai ya wuce gaba ko ta fasa zuwa ta hakura da ganin Khadijah
ɗin. Jin hakan yasa bai yi mamaki ba ya wuce gaba, da harara ta bishi tana jin
kamar ta dallah mashi mari amma babu dama, zai wani ce ta wuce gaba dan ya ji daɗin
kalle mata baya tana tafiya, to wlh ba zata yiwu ba, ta faɗa a cikin ranta tana
harararsa.

Sai da ma ya ɗan yi nisa sannan ta rufa mashi baya. Ko da suka shiga mota taki
ɗagowa ta kalli in da yake, shi kuwa a da idan sun shiga mota latse latsen wayarsa
yake yi baya wani kallanta, yau kuwa zura wayar a aljihunsa ya yi yana cigaba da
kare mata kallo da kyau kamar wanda ya samu tv. Dannewa ta yi kamar zata yi kuka,
amma haka ta hakura har suka isa hospital ɗin.
Kai tsaye ɗakin da Khadijah take suka nufa, special room ne da aka ware mata ita
kaɗai dan kula da ita sosai, a gaskiya ba karya ta samu kulawar da ta dace matuƙa.
Tana kwance shiru idanunta biyu tana kallan sama, da yake ta yi ta shan drip sai
bata wani rame ba, har wani haske ta kara yi sosai, ta kusa kamo Zee hasken fata,
jikinta ya yi fresh sosai.

Tana ɗaura idanunta a kan su ta wani zabura ta miƙe zaune, idanunta a kan uncle
Jahiz ba a kan Zee ba, ita kuwa Zee tana ganin ta farfaɗo ta tafi da gudu ta
rungumeta tana ambatar sunanta. Tamkar ba Khadijah bace a wajen, ta kafe uncle
Jahiz da kallo mai wuyar fassaruwa, lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka fara
wanke kata fuska.

Hankali a tsakanin tashe ta furta. "Zee a ina kika samo wannan
mutumin............". Sai kuma ta dakata da yin maganar, a hanzarce ta kai hannu ta
fara goge hawayenta da suka fara zubowa, a take ta shanye kukan nata.

Jin furucinta yasa Zee ta yi saurin raba jikinsu da juna, a tsananin matse da san
jin kan zance Zee ta ce. "Khadijah kenan da gaske shi ne a jikin wancan hoton ko?
Dama na ce maki shi ne kika ce ba shi bane, kullun sai na kalli hoton nan in kuma
kallesa idan mun haɗu da shi, har yau ban taɓa ganin banbancinsa da na cikin hoton
ba, amma kuma kin ki ki faɗa mun gaskiya".

Da Hausa suke maganar, hakan yasa uncle Jahiz sam bai fahimci me suke faɗe ba.

Murya a raunace, da alamar karyewar zuciya a tattare da ita, da kyar ta iya cewa.
"Zee kada ki sake yin magana a kan wannan hoto kamar yadda na faɗa maki a baya, na
faɗa maki ba shi bane ya tsaya a iya hakan!! Idan kuma ɓacin rai'na kike so to
bismilla ki cigaba, and in kuma ban isa in yi maki magana bane nan ma ki cigaba
kasa ki dai'na".

Kalaman Khadijah sun taɓa zuciyarta, haka zalika wannan abin da ya faru yaja ta
kara jin tsanar uncle Jahiz, lallai ba shakka a yanzu ta yarda Khadijah ta ɓoye
mata babban al'amari fiye da wanda ya faru da ita abaya, tabbas akwai wata a ƙasa,
wlh ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba uncle Jahiz ne a cikin wannan hoto,
kuma tana kan bakarta babu gudu ba ja da baya. Tashin sense, wai wani irin ruɗanine
wannan? Mekuke tinani? To dai ku kwantar da hankulanku, komai bala'in ruɗani da
zaku shiga alkalamina zai warware maku gaskiya, zan zaƙulo maku meyake tsakanin
uncle Jahiz da Khadijah and meyasa Zee ta ce shi ne a jikin hoton, shi kuma ya nuna
kamar ba hakan bane? To mu dai je zuwa, lokaci ne zai warware mana.

Saman chair dake kusa da bed ɗin ya zauna, a tinaninsa kukan da Khadijah take yi na
murnar ganin Zee ne, dan ya ga ita ma Zee ɗin tana ruwan hawaye, sai ya zuba masu
idanu yana kallansu.

Massage ne ya shigo wayarsa, hakan yasa wayar ta ɗan yi ƴar ƙara. Zarota daga
aljihunsa ya yi kallansa a kan Khadijah, shi dai yasan wlh ya taɓa kallan wannan
fuska, kuma shi bai taɓa zuwa Nigeria ba sai wannan zuwan nasu, to a ina ya taɓa
kallanta kenan? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta.

"Ka samemu a meeting room". Shi ne sakon da ya shigo wayarsa, uncle Abbas ne
kuma ya turo mashi wannan sako. Yana gama karantawa ya miƙe tsaye, cikin sanyin
murya ya ce masu su kasance a tare da yamma zai dawo ya ɗauki Zee. Dik cikinsu babu
wadda ta iya amsa mafi, basu da bakin magana.

Bai wani damu ba yasa kai ya fice da sauri, yana fita Khadijah ta hau jerawa Zee
tambayoyin a ina ta haɗu da wannan mutumi? Yadda take jera mata tambayoyi zaku
fahimci hankalinta a tashe yake.

"Khadijah ki faɗa mun gaskiya, dan girman Allah ki fitar da ni duhu, ni ban ce
karya kike yi mun ba, amma dan Allah ki sanar dani abin da yake a ɓoye a karkashin
zuciyarki, ki sanar dani alaƙar Jahiz da wannan hoto na cikin akwatinmu, dan girman
Allah ki faɗa mun shi ne baban baby Junior?".

Jin karshen zancen Zee yasa ta yi saurin kai hannunta saman cikinta, sai a lokacin
tasan ma babu cikin a tattare da ita, a tsorace ta kai kallanta a kan Zee. "Zeezee
ina cikina? Ina yake?".

Zama a gefenta Zee ta yi, cikin nitsuwa ta fara kora mata bayani yadda komai ya
wakana har suna tsinci kansu a wannan hospital ɗin. Shiru Khadijah ta yi tana
jinjina al'amari na ubangiji, idan Allah ya tashi amsa addu'arka sai ya haɗaka da
bayinsa da baka taɓa zatan haɗuwa da makamantansu ba, kuma su taimaka maka, lallai
ne ba shakka addu'a bata faɗuwa ƙasa banza, sai dai jinkirin amsawa, wannan
jinkirin kuma shi ake kira da jarabawa ta Ubangiji, Allah zai jarrabaka da jinkirin
amshi yaga zaka cigaba da yarda da tawakkali da shi ne ko dai imaninka bai yi karfi
ba?! Lallai ba shakka su Khadija sun yi hakuri, sun kuma ɗauki wannan jinkiri a
matsayin jarabawa wanda a yanzu Allah yake basu sakamakon hakurinsu cikin ruwan
sanyi, tun da momma ta ce sai an bi masu hakkinsu hakika ba makawa sun san ikon
Allah ne da ya amsa addu'oin da suka jima suna yi.

"Zee yanzu dai ki kyaleni na huta, idan na kara samun sauki sai mu yi magana".
Cewar Khadijah. Na'am da hakan Zee ta yi suka cigaba da jinjina girman Allah.

•••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangaren Jaish kuwa, gobe Monday zai koma bakin aikinsa, sai dai fa har yau
kudurinsa na bincike a kan wannan ma'aikata da suka tsunduma shi cikin wahala yana
nan a ransa, bai janye ba!!.

After one day. Aneesa, Fanan, Chuchu ne suka shirya cikin uniform ɗinsu na school.
Chuchu ta sha kukan rashin Auta, da farko har ta ce ita ba zata je school ɗin bama,
daga baya da Yah Jawad ya rarrasheta sai ta shirya suka tafi, da kansa ya kaisu,
sannan shi ma ya dawo ya shirya zuwa office. A tare da Jaish suka tafi kamar yadda
suka saba.

Sarina kuma bata da class,.tana guda. So gidan ya rage daga Sarina, uncle Jahiz,
uncle Taheer, uncle Abbas, su momma, King, Guyson yana nan, su twins, sai Zee da
suke asibiti. Aunty MieMie tana part ɗinta.

••••••••••••••••••••

Momma da Mama Haulat ne zaune a bedroom na monma suna tattaunawa a kan irin
dressing ɗin da yakamata su yi wa Mahnoor a lokacin da zasu kaita gaban su King.

Mama Haulat ta kawo jerin kayayyaki na alfarma masu bala'in kyau da tsada da
yakamata su shiryata a ciki domin kaita, momma tana dudduba hotunan kayan ne, dikka
cikin waɗan da ta yi oder su daga Dubai ne, tun jiya aka kawo kayayyakin kusan mota
guda.

Mammie da Sarina kuwa, suna nasu shirin dan su zo part ɗin King su kalli
Mahnoor, su kalli dame ta fi Fanan? Sun san cewa King ya ce nan da karfe 8 na safe
dai'dai a kawo mashi ita ya ganta kafin ya fita fada, shi ne suma suke sauri dan su
zo su ganta, saboda sun san idan King ya aminta da ita yadda momma ta kwallafa rai
a kan sonta ba lallai su rinƙa samun damar ganinta ba, kunga in King ya aminta da
ita zata koma part ɗin Jaish ne, to da ni da ku dai mun san dik rashin kunyar mai
rashin kunya baya tinkarar part ɗin Jaish, bayan Auta da Guyson, King and Yah
Jawad, sai momma da mama Haulat ne kawai suke iya shiga part ɗinsa, ko su Omaid
basa kaunar dosar wajen, dan kun san dalili.
So sun san tana shiga part ɗinsa ba zasu taɓa samun damar ganinta yadda yakamata
ba.

Uncle Jahiz, uncle Abbas, King, Akka su ne zaune a cikin parlon King suna jiran
momma, King ya buƙaci da Mummyn Chuchu da Mama and Mammie dik su zo. Akka ta samu
lafiya yanzu, jikin ya yi kwari, sai dai fa masifa ya karu, yaseen kana taɓota
kaɗan yanzu ka shiga talatin, sauke haushin rashin Spender zata yi a kanku.

To King ya bata labarin Jaish ya yi aure, shi ne ta ce wlh bata yarda ba, dan haka
dole a warware wannan aure, da kyar autanta uncle Jahiz ya shawo kanta a kan ta
yarda ta kalli Mahnoor ɗin ko sau ɗaya ne, taga idan bata dace da Jaish ba sai a
warware auren, to shi ne dalilin hallararta a parlourn King, ta ɗaura kafa ɗaya
bisa ɗaya cikin shiga ta alfarma, eh mana uwa ga manyan kai ba, ta dake cikin
alkyabbar na girma, sai wani kafafa take yi, har da cewa ko ta ga Mahnoor fa ita ba
zata taɓa yarda da wannan aure ba, uncle Jahiz da yake yana bin bayan Momma dan
tana rufa mashi asiri bakinsu ɗaya, sai ya ce da Akka e dai su bari Mahnoor ɗin ta
zo aganta.

Wlh uncle Jahiz da momma bakinsu ɗaya, ita ke goya mashi baya, harta batun
tafiyarsa kwallan kafa ita ta tsaya mashi, da Akka taki yarda, amma da momma tasa
baki sai suka fi karfin Akka dole ta yarda, so in short dik abin da ya ɗebo rufewa
suke ita da shi abinsu, shiyasa kuka ga suna mugu mugun shiri da juna, ya fi santa
fiye da sauran matan King.

Saida momma ta tsaya ta hantse ta zaɓawa Mahnoor wani haɗaɗɗen gown mai kama da
weeding gown, daga ta sama daidai da ita zuwa waist ɗinta, kasa ya yi bala'in
buɗewa kamar umbrella, rigar launin pink ne da ratsin golden, ga wasu ƙayatattun
duwasun alfarma masu kyalli da suke walwali suka kara ƙawata kayan rigar, sannan ga
wasu manyan zanen flowers a jikin kayan, rigar ta haɗu, ga tsada kamar me.

Wasu half cover masu kwalliya da duwatsun lu'ulu'u momma ta zaɓa mata, takalmar
launin golden kalar kwalliyar jikin rigar, ai ku daga jin kwalliyar dutse mai
daraja wato lu'ulu'u a jikin takalmar kun san kuɗinsu ya wuci baki ya faɗa.
Dankareran alkyabbar launin golden kalar takalmarta momma ta fidda mata,
alkyabba ce wanda King Badeen wato mahaifin momma ɗin ya saya mata a lokacin da
za'a kai ta gaban King Abdul Malik mahaifin King Zuhair kenan, a lokacin ya saya
mata su guda shidda, to da guda ɗaya ta yi amfani sauran biyar ɗin sunan sabbi gal,
a lokacin da tasa wannan alkyabbar sai da kowa yasan e lallai ƴar the most powerful
King ta fito, alkyabbar ce wanda ba'a samunta a ko'ina, kwalliyar jikinta da
duwatsun lu'ulu'u aka yisu, haɗuwar alkyabbar baki ba zai iya faɗarsa ba.

Mama Haulat sai da ta sha jinin jikinta jin cewa momma zata bawa Mahnoor wannan
alkyabba mai dajara tasa, domin kuwa ita tasan darajar waɗan nan alkyabbars ɗin,
momma kuwa dama matan ƴaƴanta ta ajiyewa, sai kuma Allah yasa tana kaunar Mahnoor
ɗin, kunga kuwa fin haka ma zata iya yi mata.

Dik jikin mama Haulat ya yi sanyi ganin kyautar momma ga Mahnoor, amma haka ta
miƙe ta karɓi alkyabbar, nauyi sosai yake da shi, saboda duwasun lu'ulu'u da aka
kawata kyalliyarsa da shi. Haka ta nufi waje da shi, kai tsaye ta je ta ɗauko
kayanda momma ta zaɓa za'a haɗawa Mahnoor ɗin da su.

Kai tsaye ɗakin gyara ta wuce da su. Momma ma wanka ta je ta yi ta shirya, sam babu
faɗuwar gaba a tattare da ita a kan wannan matsala, domin ita ɗin macece mai
jajircewa a lamuranta, bata san faɗuwa ba, tana da yakinin zata yi nasara.

Su mummyn Chuchu dik sun hallara a parlourn King momma kawai ake jira, Sarina da
shegen gulma har da wani zuwa ta zauna kusa da uncle Abbas, ta wani kwanto a
jikinsa dik dan gulma, kamar da gaske haka take jinsa a ranta, kawai tsabar san
kallan Mahnoor ne. One funny thing kuma shi ne yau sai ga Sarina da alkyabbar,
saboda su King suna wajen, sai ta yi shigar mutunci, ni ko na ce ashe rashin kunyar
tata ta karya ce ƴar ƙaniya.

Karfe takwas yana bugawa dai'dai wani irin daddaɗar kamshin perfume mai kwantar da
hankali ya fara dukan kofofin hancin kowa dake cikin parlourn King, turaruka masu
tsadar gaske da shegen kamshi momma ta sa aka kawo mata, sai Allah yasan daga ina
ta samo waɗan nan zafafa turarukan ta feshe sirikarta da shi.

Tin su momma basu kai ga shigowa ba kamshin Mahnoor ya aiko masu sallama. Dikkansu
sai da suka shaki kamshin suka ɗan lumshe idanu. Kowa ya fara rarraba idanu a kan
hanyar shigowa, suna jiran suka ɓullowarta.

Like wow lokacin da suka sako kafafunsu a cikin parlon, gabaɗaya kallo ne ya
dawo kansu. Momma na ɗan rungume da Mahnoor ɗin suka shigo, suna takawa cikin
natsuwa.

Like wow tamkar wata tauraruwa haka Mahnoor ta haska, shigar kayan jikinta
kawai suke kallah, Sarina alkyabbar kawai take kallah ma tukun nan, bata taɓa
kallan irin wannan alkyabbar ba.

Mummyn Chuchu ce ta yi saurin miƙewa ta taro momma, dik da basu san wacece momma ta
riko ba, amma suna da haɗin kan taimakawa junansu a irin wannan yanayi. Gefen
Mahnoor ta zo ta rungumo suka karisa da ita ciki.

Mammie da tin da suka sako ƙafafunsu take ta faman leƙo fuskar Mahnoor tana san
ganinta amma ba dama, dan alkyabbar ya yi mata yawa, hularsa ya fi kanta sosai,
kunsan na faɗa maku na momma ce, dik da lokacin bikin momma ita ma da kaɗan ta
fisu, amma dai ya yi mata yawa, hakan yasa hular alkyabbar ya sauko mata sosai,
kuma ya haɗu da ta sunkuyar da kanta ƙasa, so ba'a iya ganin face ɗinta.

Ita kuwa Sarina bata kai ga batun face ɗin amarya ba, tsadaddun kayan jikinta kawai
take kallah, ta mutu da san alkyabbar, sai dai ba samu zata yi ba, dan na manyan
mata ne wannan.

A gaban King suka kawota, mama sai binsu da kallo take yi, bare Mammie da ta saki
baki ta rasa abin faɗe kamar wata gaula.

Dama King, uncle Abbas, uncle Jahiz a saman kujerar ɗaya suke zaune mai zaman mutun
uku kenan, so a gabansu Mahnoor ta zube gwiwowinta kanta a ƙasa.

King ne ya fara cewa Momma ta kaita wajen Akka tukun nan, su fara gaisawa da Akka.
Ƙara ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya da kyau Akka ta yi, Queen mother zata yanke hukunci
e mana, Akka tamu ta amana.

Rikota mummyn Chuchu ta yi, ita ta kaita gaban Akka ta durkushe gwiwowinta.
Sannan suka koma saman sofas ɗinsu suka zauna. Ɗago idanu Akka ta yi ta karewa su
Momma kallo kamar na mintu biyu, sannan cike da izza ta ce.

"Ina Zunaira?"........ Dum dum kirjin kowa dake cikin parlon ya buga except Mammie
and Sarina, babu wanda ya taɓa expecting Akka zata nemi Auta a yanzu, nan fa parlon
ya koma kallon kallo a tsakaninsu, an rasa mai iya bawa Akka amsa, dan sun san dik
amsar da zasu bata ba zai taɓa gamsar da ita ba, babbar magana.

Tsit parlourn ya yi tamkar uwar gulma ta yi cikin shega. Can dai uncle Jahiz ya yi
ta mazan cewa. "Zunaira bata nan, sun koma school".

Shiru Akka ta yi na ƴan mintuna da zasu kai uku haka, sannan ta ce. "Amma kun san a
bisa al'ada Zunaira ce take da damar buɗe fuskar amaryar ko?".......... Jinjina
mata kai suka yi alamar tabbas sun sani. Ita dai momma shap ta mance da wannan
al'ada, tabbas tasan kanwar miji ce kawai zata buɗe fuskar mata, amma ta mance da
yake an jima ba'ayi biki ba a kingdom ɗin. Kowa kuma yasan yadda bikin Jawad ya
kasance cikin ruɗani da tashin hankali, so ba'ayi dik wasu al'adu nasu ba, dan haka
ta mance da batun.

Cike da isa Akka ta ce. "To shikenan tun da Zunaira bata nan sai ku mayar da
amaryar taku sai lokacin da kuka shirya nuna mana fuskarta Zunaira ta zo ta
buɗeta". Ta kai karshen maganar tare da yunkurawa zata miƙe.

Innalilahi, kallon juna suka shiga yi, dikkansu tinanin ta yadda zasu dakatar da
Akka ta yi hakuri ta ga Mahnoor suke yi. Uncle Jahiz ya fahimci momma ta shiga
damuwa sosai a kan hakan, sai ya yi saurin riko hannun Akka dama suka kusa, cike da
kalaman yaudara ya ce.

"Haba Akka na, to menene banbancin Sarina da Zunaira? Ai dikkansu kannen Jaish ɗin
ne, dan haka ko ba Zunaira Sarina tana nan, sai ta buɗe mana amaryar ai".

Komawa Akka ta yi ta zauna, cike da isa ta juyo garesu domin ta sanar da su
banbancin Zunaira da Sarina kwatsam idanunta suka sauka a kan uncle Abbas, aka ce
idanun iyaye suna da kaifi a wajen da ake ƙoƙarin nunawa ƴaƴansu wani banbanci ko
fifikon ko dai cin mutunci, ashe haka ne kuwa, ganin uncle Abbas yasa ta ji bata da
kwarin gwiwar iya banbanta ƴaƴansa dana ɗan uwansa bayan kansu a haɗe yake.

Bata san abin da zai kawo masu rabuwar kai, dan haka sai ta ce. "Gaskiya ne babu
banbanci, ke Sarina zo ki buɗe fuskar matan yayanku"...... Dik wanda ya ji maganar
Akka a cikin parlon nan yasan ba daga cikin zuciyarta wannan magana ta fito ba, dik
sun fahimci ganin idanun iyayen Sarina a wajen yasa ta danne bata faɗi banbancinta
da Auta ba.

Wani irin takaici ne ya lulluɓe zuciyar Sarina, yanzu ace ita zata buɗe fuskar
makiyarsu kishiyar Fanan? Gaskiya ko a iya haka an cuceta. Ita kuwa mammie ranta ne
ya yi muguwar sosuwa, wato kenan ko a ina ƴaƴanta suna da banbanci da na King?
Kenan ƴaƴanta ba koman komai bane ko a cikin dangi? Tin ba'a je ko'ina ba ana nuna
masu su ba komai bane saboda ba babansu bane a kan mulki?.

A cikin zuciyarta ta furta lallai yazame mata dole ta tsaya tsayin daka domin
mulkin kingdom of power ya dawo tsaginsu, ina ba zai taɓa yiwuwa su zama bayin wasu
ba, dole suma su ci gashin kansu, ace har kakarsu da ta haifi ubansu da King ɗin
tana ƙoƙarin ware ƴaƴan King daban dan shi ne mai rike da mulki, gaskiya ba zata
yuwu ba.

Tabbas a nan Akka ta yi kuskure, kuma dayawa mata suna aikata irin wannan kuskure,
sai kuga a gida an fi fifita ƴaƴan da ubansu ya fi abin duniya ko yake rike da wani
muƙami, wannan babban kuskure ne wanda mun san kuskure ne amma muke aikatawa, Allah
bai manta da talaka ba da ya barshi a talauci, haka zalika mai arziki ba wayau ya
yi wa Allah ba da yasa ya bashi arzikin ba, dan haka ku daina irin wannan abin da
kuke yi, wani ma zaku ga ko ubansu ne karami in dai yana da kuɗi to sai a nuna yafi
kowa a gidan, ba'a yin haka wlh, hakan yana ɗarsa gaba da kiyayya a zukata, idan
ba'a kiyaye ba sai shaiɗan ya shiga cikin lamurran, a haka ne sai ku ji ana cewa
yaya ya kashe ƙaninsa ko ƙani ya kashe ƴaƴansa saboda abin duniya, dik ire iren
wannan abin da kuke gani kamar ba matsala bane su suke hasasa waɗan nan abubuwa,
dan Allah mu daina irin hakan ba abu bane mai kyau wlh, babu mai arzirtawa sai
Allah, shi da yake talaka ai ba yin kansa bane, idan kuwa akwai mai bada arziki
bayan Allah sai ku faɗa mun in ji!!!!!.

Shi kansa uncle Abbas ransa ya ɗan sosu, amma ya danne ya nuna kamar bai fahimci in
da Akka ta nufa ba, shi ma uncle Jahiz ya ji wani irin, amma dik suka danne.

Miƙewa Sarina ta yi tana wani ɓata rai ta nufo Mahnoor. A kule ta sanya hannu ta
janye hular alkyabbar baya kamar ma da mugunta ta yi abin. Dan yadda ta ja hular
har sai da kan Mahnoor ya ɗan jinjiga.

Mummyn Chuchu ce ta ce. "Sarina menene haka? Haka ake buɗe fuska?".

Mammie ce ta tari numfashin mummy da cewa. "An kinsan bata iya bane, kinga ba'a
taɓa biki a gidan nan da wayonsu ba sai bikin Jawad wanda shi kuma ba'a nemi
kannensa na jini dan gudanar da komai ba, ina ga da yake amaryar yar gata ce
kannenta ƴan gata akasa suka yi mata komai".

Wani irin gabaɗaya parlourn suka ji na jin kalaman Mammie, mamaki abin ya bawa
King, shi kuma uncle Jahiz ya fahimci kamar abin da Akka ta yi mata ne ya bakanta
ranta, momma kam da tasan komai ko kallo basu isheta ba, maman Aneesa dik rashin
son zaman lafiyarta da izzarta sai da kalaman mammie suka ɓata mata rai, ga shi dai
ba shiri take yi da kishiyoyin nata ba, amma da aka gasawa mummy magana sai ta ji
zafi.

Dan haka sai izzar sarautar tata ta motsa. Cike da izza ta ce. "Ke saboda baki da
hankali Umaima ɗin kike yi wa martani gatsau haka? Sa'arki ce ita? Shin dake ma ta
yi magana ne? Ko kece Sarina? To maza ki bata hakuri kafin ranki ya yi mummunar
ɓaci". Mama manya, mama harkar izza ba wasa, bata ɗaukar wargi ko ba a kanta ba.

Momma ta ɗan yi mamakin faɗar da mama ta tarewa mummy, dan sun san juna kar tu kar.

Ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya Akka ta kara yi, a kadarance ta ce. "Yauwa ku cigaba, ai
na faɗa maku idan baku yi haka ba ba mata bane ku, ku cigaba da kyau".

Shi dai uncle Jahiz dariya ma abin ya so bashi, wai yau mama ce ta

Please Login or Register in order to submit comment