Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 12 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne Allah yake kareta, amma ta
sha bakar wahalar da ba zaku so ku ji tarihin ba, yawo a kan bola ne kawai bata yi
ba, amma wlh haka kawai zata zauna ta yi ta ihu babu abin da aka yi mata, sai ta
rinƙa jin namar jikinta yana wani irin masifar tauna tamkar an ɗaurata saman wuta.

Dik wannan azaba ta jure, dan gara mata gidan Arɗon a kan gidan kanin baban nata,
ga shi ita marainiya ce ba uwa ba ba uba ba, dik ta shanye wannan har Allah ya bata
cikin mamar Mahnoor, nan ma ta ci wahala kamar ta mutu, da kyar ta sha maman
Mahnoor ta zo duniya.

Ita ma tin zuwanta duniya take shan wahala har ta koma ga Allah, aurenta da bappa
kullum cikin ƙunci da kuka take, ya wahalar da ita har Allah yasa ita ma ta haifi
Mahnoor.

Ita ma Mahnoor tun farkon zuwanta duniya take shan wahala har zuwan Jaish cikin
rayuwarta, ta ɗan samo sassauci kuma ace zata sake komawa cikin wahala? Abin da
taɓa zuciya matuƙa.

Sosai hawaye ya wanke fuskar Inna. Tsabar bakinciki da karayar zuciya har ta kusa
furta saɓon Allah, saura kaɗan ta ce Allah baya sansu ne yake ta haɗasu da bala'i.

Sai ta yi saurin kame bakinta tana furta istigifari. Allah sarki Allah baya
jarabtar wanda baya so, dik wanda ya tsinci kansa cikin jarabawa ya ɗaga hannu ya
godewa Allah ya kuma roki Allah da ya bashi ikon cin jarabawar, shi ne kawai ya
dace da mumini, idan kaga baka shiga kalubalen rayuwa ma to wlh ka binciki imaninka
da saura!.

Ganin Inna ta shige ciki yasa bappa ya kama hannun ƴaƴan nasa suka nufi hanyar
gida yana jin raɗaɗi a ransa.

A hanya suka ci karo da Mairo zata shiga gidansu da yake kusa da gidansu Arɗon ne.

Har kasa ta tsugunna ta ɗaga mashi gaisuwa. Cikin ba daɗi ya amsa. Sarai ta kula da
babu farinciki a tattare da shi ko miskala zarratin, ga kuma su Mahnoor suna kuka,
dan haka sai ta ce dan Allah in ba damuwa tana san yin magana da Mahnoor and
Mahreen.

Bai musa mata ba ya sake hannunsu ya ce su je wajenta. Da yake Mahnoor kam ta
saba da ita kanwar mahaifiyarta ce sai bata yi gardama ba, tana zuwa ma ta rike
hannunta tana cigaba da kuka.

Cikin gida Mairo ta wuce da su, shi kuma bappa ya samu waje a karkashin wata
bishiyar kuka ya zauna yana jiransu.

Sun shafi good 30 mins a cikin gidan ka fin su fito, dikkaninsu sun daina kuka,
fuska ba yabo ba fallasa, da alama Mairo ta iya kula da yara, tuni ta yi masu
dabara sun yi shiru.

Ba karamin daɗi bappa ya ji ba, bawan Allah har da sauke nannauyar ajiyar zuciya,
ya ji ya kara samun kwarin gwiwa a kan aurenta, sai ya ji ma bai ga abin ɓata
lokaci ba, gobe dole ya kamo shanu ɗaya ya kawowa Arɗo a kai gidansu matsayin
sadaki, tin da ta sanya mashi yar marainiyarsa farinciki ai dole ta sanyaya mashi
rai.

Dole ayi wanna aure da wuri ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji.

Ita ma ta lura da tabbas ya ji daɗi, sosai ta ji ta yi farinciki da Allah yasa
ta sanya shi jin daɗi, da alama ita ma tana son shi sosai.

Sallama suka yi mata ya riko hannun su Mahnoor suka wuce gida. Ya so su tsaya hira
da Mairo ko shi ma zai samu sassaucin zogin da zuciyarsa take yi mashi, amma kash,
saboda su Mahnoor da suke a tare da shi yasa ya ce mata sai dare yana zuwa.

Daga haka suka wuce gida.

Nenne na zaune a tsakar gida ta baje tana cin ɗinya da addu'a suka iskota, ta yi
zaman ƴan bori a kasa tana wani cika tana batsewa.

Ko ci kanki bappa bai ce mata ba ya wuce zai shiga cikin ɗakinsa rike da hannun
ƴaƴan nasa.

"Kwairaga magana nike san yi da kai!". Cike da isa da gadara ta yi maganar, yau
babu bappan Mahreen da ake cewa, rashin mutuncin ta motso kwairaga kai tsaye aka
kira.

Ko a gefen takalmarsa, tamkar bai san da wata halitta a wajen ba ya wuce zai shi
ga ɗaki, shi fa namiji kunsan dik in da yake hakan nan dai yake hali baya canzawa,
to shi ma fa bappa namiji ne, kun san idan maza zasu kara aure har wani sabon
iskanci da waƙalanci ƙwaƙwalensu take karowa, su rinƙa jin kansu a saman iska, sai
su ji zasu iya yin komai a kan wanna aure nasu, kamar basu taɓa yi ba, ayi ta rawar
kafa ana wani kauɗi kamar angon kare, to yaseen haka suke, a jininsu abin yake.
Idan baki da wayau kika biye masu kika kulasu takaici ya sa zuciyarki ta buga, idan
kuma kina da wayo kin san in Allah ya kaddara sai an yi sai ki bawa iska ajiyar ɗan
albarka, yana kauɗinsa ki yi kamar baki san da halittarsa a cikin gidan ba, wlh da
kansa zai damu sosai, ya yi ta jin kamar ya fasa aure, zai ji kamar ba shi ba, dik
wani kauɗi zaki ga ta ragu.

Amma in kika nuna ɓacin rai yaseen kara wa zai yi dan ya shaƙa maki takaici. To kun
dai ga bappa ya karo sabon walaƙanci, da dik iskancin da Nenne take yi mashi yana
daurewa baya kin yi mata magana, amma yanzu ina ai banza yake bawa ajiyarta, bata
isheshi ya ɗaura idanunsa a kanta ba, ango na Mairo bada kanka a sare
ba............😅

Mu dai ba abin da zai hana mu zuwa wanna biki, ai ko dan mu je a kayar mana da
shanu a yanka, mu ci nama mu kora fura da nono mu godewa Allah dole fa mu
je.......... Nenne sai dai a mutu idan za'a mutu.

Ganin bai kulata ba yasa ranta ya yi matuƙar ɓaci, kamar wata aljanar ruwa ta miƙe
fuuuuuuu kafafu kamar na shamuwa sai cikin ɗakin nasa.

Daidai lokacin ya ciro kayan Jaish dake maƙale a bayan kofa ya miƙawa Mahnoor yana
ce mata ta ajiye wannan kaya a ɗakinta na mijinta ne.

Kamar wata walkiya sai ganin Nenne suka yi a tsakaninsu. Sai da Mahnoor ta tsorata
ta miƙe zata gudu, baiwar Allah ta saba shan ukubar Nenne, to a tinanina dukanta
Nenne ta zo yi shi ne zata gudu.

Wuyar rigar bappa Nemne ta riƙo, ko tsoron Allah babu bare kunya, a gaban ƴaƴansa
ta fara jajjaga mashi jajjagen masifa da bala'i kwando kwando kamar wanda ake yi
mata wahayinsu daga duniyar shaiɗanu.

Riko hannun Mahreen Mahnoor ta yi tare da ɗan cewa. "Zo mu je gidan Inna
Rabi". Mahnoor yarinya mai hankali da sanin yakamata!.

Mahreen da faɗa a jininta yake ga kuruciya a kai ne ta ce. "Ke ni babu in sa zanje
Adda Mahnoor, ki bari in taya bappa faɗa mu ci uban Nenne".

Ai daga bappan har Nenne basu san lokacin da suka dawo da kallonsu a kanta ba.
Mahnoor da tsabar zaro ido tamkar kwayar idanunta zasu faɗo kasa ne da kyar ta ce.

"Mahreen kina da hankali kuwa? Kin san me kike faɗa kuwa?".

"Nasani mana, baki ganin Nenne ta kama bappana da faɗa ne? Ni zan taya shi mu
mata shegen duka, ni kaɗai ma na isheta ba sai bappa yasa hannu ba".

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun". Shi ne kawai abin da Mahnoor ta iya sake faɗa.
Shi kam bappa ya rasa abin faɗe, wannan wace iriyar tarbiya Nenne ta bawa ƴarta? Ko
da yake maganinta kenan ai, ba ita ta lallata Mahreen ɗin da faɗa ba, tun tana
yarinya take yi mata huɗubar dik wanda ya daketa ta dage ta rama, ai ga shi yanzu
za'a daki bappanta zata rama mashi, harda uban wanda zata dake shi ɗin za'a ci wato
Arɗo kenan.

Sai yanzu Nenne ta gane Mahreen da take kauna take fifitawa fiye da komai ta fi
kaunar ubanta a kan ita. Mata kalubale gareku, ku so ƴaƴanku duniya ta kisu, kai
har Allah da manzonsa ba zasu yi alfahari da su ba, idan kika daure kika kawar da
kai kika danne kika basu tarbiya mai kyau kika kisu sai duniya ta sosu Allah da
manzonsa su so su.

Da karfi Mahnoor ta ja hannunta tare da tsawatar mata a kan ta zo su tafi. Tana
kwaɓe fuska ta bi yar uwar tata, sai mita take yi a kan ita a kyaleta su kwashi ƴan
kallo da Nenne a kan bappanta. Sai kwaɓar bakinta Mahnoor take ya faman yi har suka
fita.

Suna fita bappa ya dawo da kallonsa a kan Nenne da ta saki baki tana ganin ikon
god, waye ya ce maki Allah wasa ne, hmmmmm kaɗan ma kika gani.

"Zaki iya sakeni? Dan ina da abin yi ne!". Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga
kanta, sam yanzu baya san tashin hankali, dan baya san abin da zai mayar da shi
ruwa wajen dukan mata kamar a baya kan maman Mahnoor.

Nenne da jikinta ya yi mugun sanyi ta kasa ko motsawa ne ta tsare shi da ido ba
tare da ta sake shi ɗin ba.

Hannunsa yasa ya kwace wuyar rigar yasa, ba tare da ya sake furta uppan ba ya sa
kai ya fice waje ya kyaleta tsaye baki buɗe galala.

Nima kai nasa na wuce izuwa kingdom of power na barta baki a sake galala.

=========================🔥

••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••••

Daga ita har Jawad ɗin kyakkyawar shiga irin na ƴaƴan manya manyan sarakuna aka yi
masu.

Tsadaddun alkyabbars king da kansa ya ɓalle masu a ledarsu, dikka alkyabbar iri
guda ne, babu wani bannanci.

Sai dai da amarya da angon dik basa a cikin nutsuwa da kwanciyar hankalinsu a
lokacin da ake ƙoƙarin shirya su ɗin.

Ita Chuchu hankalinta gabaɗaya ya tashi tana neman ina Auta take? Dama a bisa ƙaida
babbar aminiyarta ce zata tsaya a gefen hannun hagunta, while gefen damanta kuma
angonta ne a wajen, shi ma ango a gefen hagunsa babban amininsa ne zai tsaya a
wajen.

Sai dai daga shi har ita basu san ina aminan nasu suke ba, shi Jawad ya rasa Jaish
a rayuwarsa wanda shi kaɗai ne amininsa kowa yasan da haka.

Ita ma Chuchu sai neman Auta take yi shiru bata ganta ba har lokaci ya kusa. Sai
gwada numberta suke yi, wayar tana shiga amma ba'a ɗauka.

Hankalinta in ya kai miliyan to a tashe yake, ta shiga damuwa matuƙa, ga shi ba
halin ta ce Auntynsu Jawad su dakata da yi mata kwalliya bari ta nemo Auta, ba zasu
dakata ba, ga momma bata wajen bare ta nemi alfarmar momma ta dubo mata Autar, ita
momma tana can tana fama da nata bakin.

Dik wannan kiran wayar Auta da Chuchu take yi Hoorain yana kwance saman bed ɗinsa
yana kallon kiran, tin bayan barinsa wajensu Ansar ya dawo room ɗinsa ya kwanta.

Wayar tana hannunsa ya kasa matsar da ita daga kan face ɗinsa, ya kai ƙololuwa
wajen shiga tashin hankali a yanzu, idanunsa sun fara rena fata, dik in ka gansa
sai ka ji gabanka ya faɗi saboda yadda yake a hargitse.

Haka Auntynsu Jawad ta tsarawa Chuchu kwalliya, amma sai dai kash dik wannan
kwalliyar da ake ta faman tsara mata idanunta ƙoƙarin cikowa da kwallah ma suke yi.

Auntynsu Jawad ta lura da hakan, dan haka sai ta shiga bata hakuri, a tunaninta
Chuchu tana san yin irin kukan da amare suke yi nan ne, bata san ita wanna ba shi
ne a ranta ba, Auta take nema yasa zata fara yi masu kuka babu gaira babu dalili.

A ɓangaren shi ma Jawad, su uncle Taheer suna yi mashi kwalliya hankalinsa yana a
kan tunanin Jaish and Yah Rizwan, yau zai yi aure Jaish baya nan, bashi da babban
aboki yanzu, shi ko ƙaramin abokin ma bashi da shi bare babba, Jaish jinin jikinsa
ne kawai, komai nasa, ga shi babu shi babu labarinsa.

Hakan yasa ya ji tamkar a fasa wanna taran dinner ɗin, yanzu in sun je ma za'a nemi
wanda zai karɓi mic ya yi bayani a kan halin ango babu, dan dik wanda zai san halin
Jawad to fa ya biyo bayan Jaish kamar yadda dik wanda zai san halin Chuchu to ya
biyo bayan Auta, haka suke!.

Karfe 11 dai'dai wajen taro ya cika makil da ƴan'mata da samari, kowacce tana
ji da kanta, abu ne na jinin sarauta da jinin sarauta suka haɗe a wajen, kowa ji da
kansa yake yi, babu mai ɗaga idanun ya kalli ɗan uwa, kowa yana jin ya wuce class
ɗin ɗaga ido ya kalli mutum a wannan waje.

Da yake su momma ba halartar wajen zasu yi ba sai basu san cewa babu Auta ba,
Fanan ita ta mayewa Chuchu gurbin Auta wanda kowa daga cikin family ya gansu sai ya
yi magana ya tamabayi ina Auta da Fanan ta maye gurbinta?.

Sai dai Chuchu ta ce masu ta shige cikin ƴan biki bata ganta ba. Sam basu kawo
komai a ransu ba, dan babu wanda ya yi tunanin faruwar wani mummunar abin a wannan
rana. So ga kuma baki dayawa, sai kowa ya ce kila tana wajen ƴan uwan mommarta da
suka zo daga Dubai ne, kila zumuɗin ganinsu yasa ta je ta manne masu!.

A ɓangaren Jawad kuma Abdussalam wato yayan Sharifat ɗa ga Abu Abdussalam na farko
shi ne ya maye gurbin Jaish wajen tsayawa a gefen Jawad suka shigo cikin hall ɗin.

Saman kujerar da aka tanadawa amarya da ango Jawad ya zauna, Abdussalam ya tsaya
a gefensa, shi ma Abdussalam ɗin ba zai wuci mate na Jawad ɗin a shekaru ba,
kyakkyawa ne sosai, da ka gansa zaka san jini ɗaya suke da su Jaish, ga shi very
gentle so silent haka.

Amma wayayyene sosai, ga ilim both sides, bai da wani fara'a kamar dai Jawad ɗin,
ya fi kama da Abu Abdussalam shiyasa akwai yanayin kama da su Jaish a tattare da
shi, dan kun san babu abin da ya rabe Momma da Abu Abdussalam.

Saman kujerar da aka tanada masu Jawad ya zauna kansa a ƙasa, sai yau sabon
kewar Jaish ya dawo cikin rayuwarsa, ji yake yi kamar ya yi ta kuka babu
kakkaunatwa, ya kasa hakuri har sai da ya ce.

"Where are you my twins brother? I really missed you a lod, I feel like I'm
not feeling well cause of u".

Dik da ƙasa ƙasa sosai ya yi maganar Abdussalam ya ji shi, kuma yasan me yake yi wa
wannan sambatu, dan haka sai bai kula shi ba, sai ma ya nemi kawar mashi da zancen
ta hanyar cewa.

"Jawad where's my wife? Tin da nazo fa bamu haɗu da ita ba, taki zuwa in da
nike, kuma nasan fushi take yi dani sabida wancan zuwanta Dubai na yi mata ba
dai'dai ba, naki zuwa mu haɗu da ita har ta dawo, so nasan fushin ne har yanzu bata
huce ba".

Magana yake yi a kan Auta wadda tun tana jaririya ya ce da Momma shi fa ga matarsa,
tin suna ɗaukar abin wasa har suka fara mayar da wasa izuwa gaskiya, har yau har
gobe da my wife yake kiranta, tin bata amsawa har ta fara amsawa, yana santa sosai.

"Tana nan zata shigo a tare da Jannat". Jawad ya bashi amsa da kyar, dan har
voice ɗinsa bata fita sosai.

"Gaskiya yakamata na ganta, i really missed her fa, yanzu almost 8 to 9 month
rabon da na sakata a idanuna, this time bata je Dubai ba".

Nisawa Jawad ya ɗan yi, cikin yanayi maras daɗi da damuwa ya buɗi baki zai yi
magana kawai shararren mc da ake ji da shi a faɗin ƙasar ya yi sanarwa a kan amarya
na shigowa.

Gabaɗaya kowa kallonsa ya kai a kan kofar shigowa, kowa dama yasan kalar amaryar,
wato ƴar wanka ce, bare kuma yanzu da ya kasance ranarta ce, ai abin sai dai kawai
ka daure ka kawar da kallonta daga kanta, amma ba wai dan zaka gaji da kallan
kyanta da kwalliyarta ba.

Miƙewa tsaye Jawad ya yi a lokacin da ta sako kyawawan fararen kafafunta dake sanye
cikin Queen cover shoes masu high sosai cikin wajen.

Ba komai ya sanya Jawad miƙewa ba face abubuwa guda biyu, na farko kyan da Allah ya
zuba mata ya gaurayu da tsararren kwalliyar da ya tashi kan dik wanda zai ɗaura
idanunsa a kanta, na biyu kuma ganin Fanan a side ɗinta ba Auta ba, ya girgiza
matuƙa na ganin Fanan a gefenta, to ina Auta?. Ya jefawa kansa tambayar da bashi da
amsarta.

A take ya ji gabansa ya yanke ya faɗi, har wani sara mashi ya ji kansa ta yi!.

Dik da cikin alkyabba take kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, hakan ba zai hana kaga
tsantsar damuwa da take a ciki ba, idanunta har sun yi ja baiwar Allah.

Tin da ta shigo wajen har ta karisa kusa da ango hannunta na'a kan screen ɗin
wayarta tana ta faman gwada number Auta, taki hakura sam.

Tana ƙarisowa kusa da angon nata ya sa hannun biyu ya riko nata hannayenta da
suka sha kunshi dan ya taimaka mata wajen hawa saman stage ɗin dake wajen.

Jama'ar wajen ne gabaɗaya suka ɗauki tapi rap, rap, rap, kowa ya miƙe tsaye yana
jiran amarya da ango su zauna sannan shi ma ya zauna.

Abin ya ƙayatar da mutane yadda Jawad ya taimaka mata wajen haurowa sama. Tsakuwa
ta yi a kusa da shi kanta a ƙasa.

Kasa dannewa ya yi har sai da ya ce. "Jannat ina Auta?".

Kamar jira take yi wani ya yi mata magana ta fashe da kuka, haba ai sai ruwan
hawaye wani na bin wani.

Kowa ya ɗauka kawai kukan amarci ne.

Rikicewa Jawad ya yi, a tsorace ya ce. "Jannat Auta na tamnayeki ba fa kuka nace ki
yi ba, ina take?!".

Wayarta ta miƙa mashi tana ƙoƙarin juyawa da nufin ta bar wajen, a cewarta zata je
ta nemo Auta, dan haka kawai take jin kamar akwai wani tazara mai tsawo a
tsakaninta da Autar.

Riƙo hannunta da kyau ya yi tare da zama a saman kujerar ya zaunar da ita, sannan
ya saketa ya mayar da hankalinsa a kan wayarta, number Autar shi ma ya shiga kira
babu kakkautawa.

Mc sai cika mutane da surutu yake yi yana yabon amarya da angon da bai san yanzu
haka wutar tashin hankali ce yake ruruwa a cikin zuƙatansu ba!.

•••••••••••••••••••••••••••••••••GUYSON💘

Kwance yake saman gadan Mommarsa, daga shi sai short, babu ko singlet a jikinsa, ya
kudundune a cikin bargo kamar mai jin sanyi, a hankali hankali yake ɗan jujjuyawa a
saman bed ɗin kamar wanda bashi da lafiya.

Tun da yamma gabansa yake faɗuwa, fargaba kamar zai kashe shi, ya kasa
halartar wajen dinner ɗin, zuciyarsa haka kawai take tsinkewa, ya shiga damuwar da
bai san dalilinta ba. Bawan Allah jini ai ba wasa ba, shaƙuwa kuma ba karya ba.

Haƙiƙa ko mu mun shaida gimbiya Zunaira wata ɓangarece ta rayuwarka Guyson, mun
shaida hakan, Allah sarki, rashinta yasa mashi ciwo ba tare da ya sani ba.

Ya shiga mawuyacin halin da bai san dalili ba, ya faɗa damuwa ba gaira babu dalili,
jikinsa dik tamkar wanda aka tsinkewa jijiyoyin jininsa.

Gajiya ya yi da juyin da yake ta faman yi babu wani sauki da ya samu dangane da
abin da yake ji a ransa, hakan yasa ya miƙe zaune.

Kafafunsa ya zuro kasa, kamar wani ɗan yaro, sai turo baki yake yi, a haka ya miƙe.
Sai dai yana da kunya dai'dai gwargwado, dan haka sai da ya ɗauki arabs jallabiya
ya sanya a jikinsa, gashin kansa dik a watse kamar wanda ya taso daga ciwo.

Waje ya nufa yana jan kafafunsa kamar baya san motsa jikinsa. Part ɗin King ya nufa
dan yana da tabbacin zai samu Mommarsa a can.

Babu wanda suka haɗu da shi a hanya har ya ƙarisa cikin part ɗin. King baya cikin
room ɗin, yana cikin toilet yana wanka. Momma tana kwance a saman bed ɗin King
kamar wadda bata da lafiya, ta yi shiru tana fuskantar sama, ita kanta tin ɗazun
gabanta yake ta faman faɗuwa, zuciyarta yana ta tsinkewa, ta rasa menene sila.

Sai addu'a take yi a kan Allah Ubangijin ya sanya dik wani abin da zai tinkarota na
masifa da yake sanyata faɗuwar gaba ya rikiɗa ya zamana alkhari.

Dik wani bawa da yake jin kamar wata musifa tana tinkaro shi, yana yawan jin
faɗuwar gaba to ga addu'ar da zai yi wanda zai sa Ubangijinmu ya juya wannan abin
zuwa alkhari, in ma kaddararsa ce ta zo a haka to Allah zai saukaka mashi abin ya
zo mashi da sauki, zan rubutu maku addu'ar da hausa dan ina samun korafi a kan
rubuta shi da larabci da nike yi, wasu basu iya karatun larabci ba, so addu'a
addu'a ce koma da wace yare ka yi ta Allah zai jika, gata kamar haka haɗe da
fasararta dik na haɗa na rubuta maku da Hausa dan ku fi fahimta da kyau, Allah yasa
mu dace.

"Hasbiyallahu laa ilaaha illa Huwa, alaihi tawakkaltu wa Huwa
Rabbul-‘Arshil-‘Azeem."
Fassara. Allah Ya ishe ni, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, a gare Shi
na dogara, kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma, shi kaɗai zai iya kareni daga
dik wata sharri.

Sai cikin Alqur'ani mai girma, Suratul Baqarah Surah ta 2 bayan Fatiha kenan, aya
ta 286. Wannan ita ce aya ta ƙarshe a cikin Suratul Baqarah, kuma tana ɗaya daga
cikin mafi girman addu'o'in Al-Qur'ani don neman gafara, rahama, da taimako daga
Allah, wannan addu'a idan kika yi ta bata da shamaki da isa ga Ubangiji, kika yi ta
da tawali'u ki kaddara addu'aki ta karɓu kawai, dan bata da shamaki kai tsaye take
wuce zuwa ga rabbil izzati, ita ce addu'a kamar haka.

"Rabbanaa laa tu’aakhidhnaa in nasinaa aw akhṭa’naa. Rabbanaa wa laa taḥmil
‘alainaa iṣran kamaa ḥamaltahu ‘ala-l-ladheena min qablinaa. Rabbanaa wa laa
tuḥammilnaa maa laa ṭaaqata lanaa bihi wa’fu ‘annaa waghfir lanaa warḥamnaa anta
Mawlaanaa fanṣurnaa ‘ala-l-qawmi-l-kaafireen."
Fassara. Ya Ubangijinmu! Kada Ka kama mu idan mun manta ko mun yi kuskure. Ya
Ubangijinmu! Kada Ka dora mana nauyi kamar yadda Ka dora wa waɗanda suka gabace mu.
Ya Ubangijinmu! Kada Ka dora mana abin da ba za mu iya ɗauka ba. Ka yafe mana, Ka
gafarta mana, Ka jiƙanmu. Kai ne Majiɓincinmu, Ka taimake mu kan mutanen da suka
kafirta suke binmu da sharri.

Addu'a ta uku a kan Allah ya kareki daga dik wata masifa da kike jin kamar tana
tinkaro ki shi ne.
"A‘oozu bikalimaatillahi-ttammaati min sharri ma khalaq."
Fassara. Ina neman tsari da kalmomin Allah masu cike da kamala daga sharrin duk
abin da Ya halitta.

Manzon Allah (SAW) ya koyar da wannan addu'ar don neman kariya daga kowanne irin
sharri, so addu'a ce mai karfin gaske, idan kika riketa wlh wane mutum sai dai
ubangijin mutum!!!.

Addu'a ta huɗu kuma mafi tsada, wannan addu'a idan kika yi ta da safe kafa uku,
Manzon Allah ya yi rantsuwa a kan babu wata sharri da zata sameki, safe da yamma
ake yi, in kika yi ta uku da safe wlh a wannan wunin ranarkam babu wani sharri da
ya isa ya kusantoki, dik balai'n mutum nan zai ganki kuma yarbi, Allah zai saukar
da Mala'iku daga sama domin baki kariya wunin wannan rana har zuwa yamma, in kika
sake yin kafa uku da yamma to fa har zuwa washegari da asuba kina cikin kariyar
Ubangiji. Sai dai ki sani addu'a babu cikakkiyar Tauhidi fa Allah baya karɓarta,
sirrin addu'a ita ce idan zaki roƙa ki sanya a ranki cewa Allah ya gama biya maki
buƙatar ma kawai, ki sa a ranki dama babu wanda zai biya maki sai shi!!.

Ga addu'ar kamar haka.

"Bismillahil-ladhi la yadurru ma’asmihi shai’un fil-ardi wa la fis-sama’i wa
Huwa-s-Sami‘ul-‘Alim."
Fassara. Da sunan Allah wanda ba zai yiwu wani abu ya cutar da mai ambatonsa ba a
sama ko a ƙasa, kuma Shi ne Mai ji, mai sani a kan komai.

A karanta sau uku safe da yamma, domin samun tsari daga sharrin duniya gabaɗaya!.
Allah ya cigaba da karemu daga dik wata sharri!.

Waɗan nan addu'oi Momma take ta karantawa dan ta samu saukin abin da take ji, hakan
ne ma yasa mutuwar Zunaira bai yi mata wani tsananin tasiri ba, Allah ya dafa mata
zuciyarta ya ɗan sanyaya dalilin wannan adduoi.

Guyson na shigowa ya haye saman gadon, kusa da ita ya matso, tana kwance idanunta a
sama, jin motsinsa yasa ta ɗan yi kasa da kallonta izuwa kansa.

"Lafiya Omar?". Ta yi maganar da kyar.

"Momma jikina ne dik yake mani some how na kasa ganewa, and kaina yana ɗan sara
mun, kamar bani da lafiya".
Tin da ya fara magana idanunsa suka cicciko da kwallah, dama kun san halinsa
mai kukan ciwo ne, da zarar ya fara ciwo zai fara kuka. Allah sarki babu juriya!.

Yana kai karshen maganar kuma ya kwantar da kansa a saman laps ɗinta yana shirin
fara yin kuka mai gabaɗaya.

Miƙewa ta yi zaune a tsakiyar bed ɗin, hakan ya bashi damar

Please Login or Register in order to submit comment