Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 83 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata ce ba zata bi Abdussalam ba, ta bisa, suna shirye cikin
tsadaddun shirinsu na jikokin the most powerful King Badeen, alkyabbar da Auta ta
sanya ma da lu'ulu'u aka yi duwatsun masu hasken bala'in dake jikinsu, cover shoes
dake kafafunsu daga ita har Abdussalam dik sun kasance da duwatsun lu'ulu'u aka
kawata kwalliyarsu wanda hakan yasa suke ta zuba kyalli suna ɗaukar ido.

Bayan gaisuwar sarauta sun gudanar da raye-raye na gargajiya wanda ƴan'matan family
ne suke gudanarwa bisa al'adar. Sun yi rawa irin su Ardah. Maza na sarauta sukan
tsaya da takubba suna wakar girmamawa da rawar alfarma ana buga daff da tabl, kayan
kiɗa na gargajiya. Sai dai fa Jawad ya yi, amma Jaish dik yadda yake san Auta yaki
yi, dan ya ce shi fa bai ga amfanin yin al'adar nan ba, King kuwa ya ce auran
Autarsa ce dole ayi dik al'adun da suke yi, kunga haɗuwar da guyson ya yi cikin
warriors wears ɗin nan kuwa? Ya yi bala'in kyau sosai, ya riko takobi a hannunsa, a
tsakiyar hall na gidan aka gudanar da wannan biki, Omaid and Obaid dik sun yi,
Jaish ne dai ya ki yi, shi kuwa Smart ko in da suke bai leƙo ba, yana cikin bedroom
ɗinsa. Shi ma Abdussalam ya yi, kuma dik sun yi masifar kyau sosai, uncle Taheer,
Uncle Jahiz dik sun yi, su Ramish kam ko bikinma basu zo ba, sun ce sai bikin ta
dawo Dubai kawai, idan an gama a kingdom of power aka miƙe masu amaryar su zasu
tarbeta a Dubai, tin da abin dik family ne sai suka kasa kansu gida biyu

A daren ranar da aka gama wannan bikin raye-rayen sai suka gudanar da Gidauniyar
Alkhairi. Wasu sarakuna na amfani da bikin aurar da ƴaƴansu dan buɗe asusun
tallafi, bayar da gudummawa ga marasa galihu ko yin aikin alkhairi da sunan amarya,
sai dai shi King ita kanta Auta daga cikin ɗinbin dukiyarta ta buɗe wannan, shi ya
jagoranta ta buɗe wannan gidauniya, shi kuma ya yi kyautar motoci, gidaje da kuma
kujerun makka, Jaish ma ya yi kyaututtuka da sunan Auta tamkar dukiyarsa zata kare,
sai dai ko kaɗan bai girgiza ba, shi ma uncle Abbas ya yi kyaututtuka, ya taka ya
je prison da kansa ya yi freeying masu ƙananan laifuka, ya yi belinsu sannan ya
basu kuɗi dan nemawa kansu aikin yi, baya ga haka yasa anyi girke girke da dama aka
kai gidan prison ɗin dan ciyar da waɗan da suke ciki. Shi kuma uncle Jahiz gidan
marayu ya je, nan ya bada millions dan tallafa masu, dik da sunan Auta suka yi suna
fatan Allah ya bata farinciki da kwanciyar hankali mai ɗorewa a gidan aurenta, su
kansu sun san zama da wanda baka so ba kara mun abu bane, shiyasa dik suke wannan,
kowannensu da abin da ya yi, Dr Raj ma yana nan, ya yi kyaututtuka da dama, Ramish,
Bilal and Yah Rizwan suma sun yi mata kyaututtukan da baki ba zai iya faɗa ba.
Abubuwa dai sai wanda ya gani, sai dai wacce ake yi dominta ko kaɗan bata a tare da
su, umarnin daddynta kawai take bi yasa ta ja bakinta ta yi shiru.


DINNER NIGHT.🔥

Ango ya sha kyau cikin bisht wato kayan sarauta na maza, rawani da takalmin fata na
alfarma, dukiya ya yi mubaya'a a wanna waje, komai nasu very luxury. Su Aunty
MieMie sun shirya amarya a cikin wasu haɗaɗɗun p-k, wani shegen gown ne mai bala'in
kyau da tsada, tana jan kasa, ga alkyabba mai kwalliyar lu'ulu'u, takalmar kafanta
kawai ya isa yasa ku fahimci auren ƴar gata ake yi. Babu karya, ko makiyi yasan
Zunaira ta yi kyau sosai, sai dai ko kaɗan babu walwala a saman face ɗinta, alamar
tana cikin tsananin tashin hankali, a haka ta shigo cikin hall ɗin, mc yana ta
faman zuba kirari a gareta, Chuchu tana rike da hannunta, ɗayan side ɗin kuka
Aneesa ce ta riketa, su Khadija dik sun shirya sun halicci dinner ɗin bisa umarnin
Aunty MieMie, Pretty ce kawai taki zuwa, ta dai cewa Momma ba zata je ba dan bata
san hayaniya, shiyasa ta yi zamanta a parlourn Momma tana kallan tv.

Kiɗan larabawa mai shehen daɗin mc ya bada umarnin a saki da shigowar tauraruwar
amarya, tana shigowa wasu jakadun mata suka hau fesheta da turarruka wasu suna
watsa mata furanni. Dama sai zuba kamshin turarukan larabawa su oud, musk,
sandalwood take yi, dik wanda yake cikin hall ɗin nan sai da dandatsetsen sarkar
zinarin dake wuyarta ya ɗauke mashi hankali, kai kyau fa iya kyau Auta ta yi,
walwalar ne dai da babu shi ne matsalar. Abdussalam dake tsaye yana jiran ƙarisowa
dik ya kotsa ta iso ya ji me yake damunta da ta haɗe rai haka, shi ya rigata zuwa,
a tsarinsu ba tare suke shigowa ba, shi zai shigo da abokansa, ita ma tare da
kawayenta.

Kun san menene babban abin takaicin my people's? Hoorain yana wajen wannan dinner,
yana gab da bakin kofar shigowa, sai dai kuma zuciyarsa bata yarda mashi abin da
kunnuwansa suka ji yo a masallaci ba, yana ganin kamar bikin Aneesa ake yi bana
Auta ba, yaki yarda, shiyasa bai nuna damuwa ba, kuma King ne ya wakilta shi a kan
tsaron kofar shigowa dinner, yana tsaye yana aikinsa yana ta faman tinaninta, a
ransa yake faɗin ya yi mata uzuri na rashin ɗaukar call ɗinsa da bata yi ba, kila
saboda jama'a ne yasa busy ya yi mata yawa, amma dik a dame yake da ta ɗauki waya
su gaisa.

Suna isa bakin stage ɗin Abdussalam ya yi saurin matsawa ya riƙo hannunta a in da
ya taimaka mata ta hauro sama, dik da kanta a ƙasa, kuma tana cikin alkyabbarta sai
da gaban Hoorain ya faɗi lokacin da ya ga Abdussalam ya riƙo hannun amarya, wai a
haka ma bai san hannun waye ya riko ba, da ya san hannun Hoonairarsa ce me kuke
tinanin zai faru?....... KAI WHAT A HEART TOUCHING PAGE 😥

Saman haɗaɗɗen King seat da aka tanada masu suka zauna, suna zama mc ya yi umarni
da a juya kiɗar zuwa karatu dan a buɗe taron da addu'a. Haka kuwa aka yi, suratul
Fatiha suka sanya bisa tsarin musulunci da kuma tsarinsu, sannan aka buƙaci manya
suka gudanar da addu’a dan yi wa amarya albarka. Dik dai wani al'adunsu suka yi shi
suka gama, saura sanyawa amarya ring and kiss, sai cin abinci da abin sha kafin a
fara sake kiɗa dan yin nishaɗi.

Mc ya buƙaci da ango yasa wa amaryarsa zobe, sai tambayarta yake yi meyake damunta,
amma taki ta yi mashi magana, shiru tin da ta zo wajen. Ya shiga damuwa matuƙa,
amma a haka ya daure zuwa a gama taron, wani dankareren diamond ring kusan shigen
wanda ta sanyawa Hoorain a hannu daren jiya ɗaya daga cikin abokan Abdussalam ya
miƙo mashi, Ring ɗin yana cikin box ɗinsa. Unboxing ɗinsa ya yi tare buɗewa, wani
irin kyalli yake yi yana ɗaukar ido. Miƙewa tsaye ya yi tare da riƙo hannunta ya
miƙar da ita, ya tsayar da ita suna fuskantar juna, sannan ya kama ƴan yatsunta ya
zura mata ring ɗin, take hannun nata ya kara wani irin kyau na musamman. Tafi rap,
rap, rap, gabaɗaya cikin hall ɗin ya ɗauka, abin ya ƙayatar. Muryan mc suka ji yana
faɗin yanzu Ango zai sumbaci amaryarsa kamar yadda suka saba yi!.

Aikuwa kamar jira Abdussalam yake yi, Mc na bada dama ya yi saurin sanya hannunsa
ya ɗago haɓarta da tin da ta zo wajen bata ɗago kanta ta kalli kowa ba. Ɗago kanta
ya yi tare da matsar da face ɗinsa dab da ita, cikin salon nuna mata soyaya da
kauna ya kai bakinsa zai sumbaceta. Daidai lokacin ta ɗago kallonta kai tsaye sai
saman fuskar Hoorain da ya yi mutuwar tsaye yana kallanta, tin da ta miƙe
Abdussalam ya sanya mata ring ya gane ita ce, shiyasa ya yi mutuwar tsaye!!.

Dik da cewa akwai hular warriors a face ɗinsa, hakan bai hanata ta hango tashin
hankalin dake cikin idanunsa ba, kwayar idanunsa tamkar wuta saboda ja, kuma
kallanta kawai yake ko kyaftawa bai yi ba, Ansar na tsaye a gefensa ya ɗaura
hannunsa a saman takobin dake waist ɗinsa. Abdussalam yana dab da zai haɗe bakinsa
da nata sai gani ta yi Hoonaira ya tafi gabaɗaya ya yi ƙasa, take a wajen
numfashinsa ta ɗauke ɗiff.

Ai bata san lokacin da ta zunduma ihun sunansa har sai da ta razana dik abokan ango
da su Chuchu dake wajen ba, lokaci guda kuma zancen King ya dawo mata cikin
kwakwalwarta na sharaɗin da ya gindaya mata idan har tana son ya yafe mata, ya ce
to kada ya sake jin sunan Hoorain a bakinta, ko da sunan wasa kada ta sake ɗaga
idanun ta kallesa, Allah sarki da farko ta yi niyar ta zumduma a guje ta yi kansa,
amma da ta tina maganar King sai kawai ta kara zunduma wani ihun da bata kai
karshen yinsa ba ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a wajen. A miliyan Abdussalam ya yi
kanta yana ambatar sunanta, su Chuchu dik kanta suka yi kamar yadda su Ansar suka
yi kan Hoorain da suka tabbatar da baya numfashi, babu rai a jikinsa!!. Cike da
tashin hankali Ansar da Anwar suka ɗaukesa, haka ita ma Auta Abdussalam ya ɗauketa
ya sauko kasan stage ɗin da ita, da gudu su Chuchu suka rufa mashi baya, nan fa
taro ya hargitse, hankula sun tashi sosai.

Hospital suka wuce da Hoorain a in da gwajin farko Dr ya tabbatar masu da babu rai
a jikinsa, ita kuma Auta wuce suka yi da ita cikin family part, King ya umarcesu da
su kaita part na bayan fam part ɗinsa a in da babu kowa a wajen, babu hayaniya babu
ribibi, su kai ta can Dr's su zo su duba lafiyarta, sabon part ne da ba'a buɗe ba,
dama na uncle Jahiz ne in da idan ya yi aure zai zauna kamar yadda uncle Abbas yake
da part ɗinsa. Nan aka wuce da ita, a take aka kira likitoci guda uku suka dukufa a
kanta dan ceto rayuwarta, ita dai bata mutu ba, amma zuciyarta na dab da bugawa,
shi kuma Hoorain zafin kishi da soyayya yasa ya haɗi zuciya take rai ya yi halinsa!
Lallai ba shakka Hoorain ya kurɓu gabar soyayya mai zafin gaske!!. Wlh a lokacin da
Dr yake sanar da su Hoorain ya rasu Ansar yanke jiki ya yi ya faɗi sumamme, shi
kuma Anwar capko wuyar rigar Dr ya yi, kamar wanda ya rasa hankalinsa ya fara faɗin
wlh Dr ya tasan masu ɗan uwansu ko kuma ya kashe shi shima, abin dai very very
heart touching, heartbreaking.......😥

Wlh page ɗin nan ya yi mugu mugun taɓa ni, Allah sarki, ashe da rabon kafin ya mutu
zai yi kissing Zunairarsa, to King yanzu dai Hoorain ya bar maku duniyar, sai ku
dafa Zunaira ku cinye, amma my people's kuna tinanin Commander Zafar zai yafe jinin
Hoorain ya tafi a banza kuwa? Baku ganin kamar commander zai juya masu baya ya
yakesu? Kada ku manta commander shine kaso sittin cikin ɗari na karfin kingdom ɗin,
warriors dik umarninsa suke bi, ya kuke gani idan ya juya masu baya?!. Wlh akwai
case ba na wasa ba, ni dai bari in je in kora Maltina ko zan samu sassaucin abin da
nike ji a cikin zuciyata!!!.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




54


Sai da kingdom of power ta tsaya cak na ƴan wasu ɗakinku a lokacin da labari ya
karaɗe kunnuwar mutane Hoorain ya mutu, shi kansa King sai da ya yi zazzafar
razana, ai Commander Zafar cewa ya yi karya ne, ba Hoorain bane ya mutu sai dai
wani, amma shi ɗansa yana raye, dik yadda aka so a fahimtar da shi Hoorain ya mutu
ya zo su gana da gawarsa ya yi mashi addu'a kafin a je a rufesa, amma commander ya
ƙaryata, ya ce wlh shi babu gawar da zai zo ya yi sallama da ita, dan shi ɗansa na
raye. Ansar ya lura lallai commander ya zaune ce, ba kuma zai taɓa fahimtarsu ba,
dan haka sai ya ce su sanar da King ko zai iya sanya commander ya fahimtar har ya
sami damar yin bankwana da ɗansa.

Haka kuwa aka yi, suka sanar da King ga abin da yake faruwa, suna san yin jana'izar
Hoorain amma commander ya ki yarda ya zo ya gansa ma bare har ya yi mashi addu'a.
Cike da alhinin abin da ya faru King yasa a kira mashi commander. Babu kunya babu
tsoron Allah King ya iya kallan commander ido cikin ido ya sanar mashi da ya ɗauki
dangana Hoorain dai ya mutu.

Murmushi commander ya yi kafin ya ce. "Allah ya kara maka tsahon rai, na tabbata ba
Hoorain ɗina ne ya mutu ba, wani Hoorain ɗin ne, Hoorain ɗina yanzu na barosa a
waje". Jin waɗan nan kalamai yasa King ya fahimci commander fa ƙwaƙwalwarsa ta
shiga cutar da ake kira da I-M-R-S, lallai ko zasu shekara suna faɗa mashi Hoorain
ya rasu ba zai taɓa yarda ba, dan shi Hoorain yana yi mashi gizo, yana kallansa da
idanun da babu mai kallansa sai shi. INNALILAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, HASBUNALLAHU
WANI'IMAL WAKIL!! KENAN YANZU COMMANDER YANA KALLAN HOORAIN KOWA BAYA KALLANSA?
YANA YI MASHI GIZO? BABBAR MAGANA!! LALLAI KUWA BA ZAI TAƁA YARDA DA HOORAIN YA
MUTU BA!!.

Yana tsaye a tsakiyar fada yana kallan King, sai kuma ya juyar da kallansa izuwa
kofar shigowa, gwanin ban tausayi ya fara faɗin. "Yauwa my lion, wai cewa suke yi
ka mutu, na ce masu baka mutu ba, zo ka gwada masu kanka!". Ya kai karshen maganar
yana riko iska a matsayin Hoorain da ya shigo fada a yanzu.

Wlh a dai'dai wannan lokacin gabaɗaya ƴan majalisar fada sai da idanunsu ya ciko da
kwallah, shi kansa King sai da zuciyarsa ta karaya, gaskiya bai taɓa ganin soyayyar
uba da ɗansa irin tsananin soyayyar dake a tsakanin Commander da Hoorain ba.

"Ranka ya daɗe ba ga shi nan ba! Ai dama na faɗa maka bai mutu ba, ga shi ka gani
ma da idonka". Allah sarki, daga yadda yake magana zaka fahimci sambatu ne kawai,
dik yana rikice, gwanin ban tausayi, ya yi maganar yana nunawa King iska a matsayin
Hoorain dake gabansa. Aunty MieMie dake zaune a kusa da King wacce bata jima da
shigowa bace ta miƙe tsaye, wani irin kuka ne mai karfin gaske ya kwace mata, dama
ta shigo ne ta ɗan taushi zuciyar baban nata, dan ta ga ya ɗauki zafi sosai, tana
zaune aka kawo labarin mutuwar Hoorain, ta ji hakan a ranta sosai, sai yanzu kuma
ta ga abin da ya fi mutuwar tasa zogi, ba zata iya zama ba, da gudu ta ruga cikin
gida alkyabbarta na jan ƙasa tana hawaye.

Allah sarki commander dattijon arziki, cike da damuwa ya ce. "Lafiya ranki ya daɗe
ta tafi tana kuka? Ko wani abin ne yake faruwa?". A ruɗe ya yi maganar.
Dik cikin fada babu wanda ya iya bashi amsa, sai sharan kwallah da kowa yake
yi, bare ma sarkin hatsi da tuni hawaye sharɓa sharɓa sun gama jiƙa fuskarsa har
sun jiƙa wuyar rigarsa. Da mamaki commander yake binsu da kallo, cikin ruɗu ya fara
faɗin. "Malam liman lafiya kuke kuka? Ko dai akwai abin da yake faruwa ne? My lion
ka ji labarin wani abin yana faruwa ne?". Ya yi maganar yana kallan gefensa a zuwan
yana kallan Hoorain.

A gizon da yake gani girgiza mashi kai Hoorain ɗin ya yi yana ce mashi babu wani
abin da yake faruwa, watakila kukan farinciki suke yi. Jinjina kai commander ya yi
tare da mayarwa gizon nasa amsa da. "E ina ga kukan farinciki suke yi, suma suna
murnar biki ne, to shikenan jeka abinka ni bari in zauna a nan mu gama magana kan
yakin da zamu tafi jibi". Jinjina mashi kai gizon nasa ya yi tare da juyawa ya bar
wajen ya nufi waje.

Wlh dik taurin zuciyar king sai da idanunsa suka kawo kwallanh, bai taɓa zatan zai
shiga damuwa a mutuwar Hoorain ba sai da commander ya shiga cikin wanna hali, amma
kuma fa dik da haka sam bai yi danasanin abin da ya aikata na raba masoyan ba, shi
yana ganin yana a kan dai'dai!!

-------------------------------🔥🔥🔥

Cikin ƙanƙanin lokaci likitoci suka yi nasarar shawo kan Auta har ta farfaɗo, sai
dai kuma, Dr ya sanar da in dai basu bata abin da take so ba, to wlh zuciyarta tana
gab da bugawa, yanzu haka ta samu babban rauni a zuciya. Sosai ƴan uwan suka
girgiza da jin wannan labari, a in da suka ce kada a kuskura a sanar da ita Hoorain
ya mutu, King kuma ya ja Abdussalam gefe a in da ya sanar da shi ya san dik ta
yadda zai yi ya maye gurbin Hoorain a cikin zuciyarta gudun kada su rasata, sai dai
abin da King bai sani ba shi ne, soyayyar Auta and Hoorain daga Allah ne, babu
wanda ya isa ya maye gurbin Hoorain a cikin zuciyarta kamar yadda babu wanda ya isa
ya maye gurbinta a cikin zuciyarsa!. Abdussalam ya tambayi wanenne Hoorain kuma,
sai King ya ɓoye mashi, ya ce dai ya yi ƙoƙarin janyota a jiki ya kwantar mata da
hankali, King baya san Abdussalam ya san komai!.

-----------------------------🔥🔥

Tin da momma ta samu labarin mutuwar Hoorain ta shiga tantama da tashin hankali,
zuciyarta na ayyana mata akwai wata babbar dalilin da yasa King ya gwammaci gara
Hoorain ya mutu a kan ya auri Zunaira, sosai momma take zargi da biyu ma King ya
saka Hoorain ɗin gadin hall ɗin dinner dan zuciyarsa ta buga a lokacin da zai ga
Auta da wani, abin ya tsayawa momma a rai, shiru ta nutsa cikin tinaninta tana
tariyo rayuwar baya, ɗauko tinanin ta yi tin daga kan lokacin da matar commander
take raye, ita dai tasan ma tin kafin commander ya aureta kamar ita ce kuyangarsu
ba kuyanga Zubaida ba, wato ita ce wacce King ya amincewa da ta rinƙa zuba mashi
abinci tana kuma girkawa kamar yadda ya aminta da kuyanga Zubaida a yanzu!

Take ƙwaƙwalwar momma ya fara shiga ruɗani, sai a lokacin kuma ta tina ita fa bata
taɓa kallan face ɗin Hoorain ba a tsawon rayuwarta! Wani irin mummunar faɗuwar gaba
ta ji a lokacin da ta tina bata san face ɗinsa ba! Saura kaɗan kwakwalwarta ya kama
da wuta a lokacin da tinanin dalilin mutuwar mahaifiyar Hoorain ya ratso cikin
kwakwalwarta, yanzu ta fara tantama a kan mutuwarta, anya kuwa ba kasheta kawai aka
yi da gangan ba? Meyasa da ta ɓace babu wanda ya sake yin maganarta bare ma har ya
nemota? Meyasa King bai tsaya tsayin daka sun nemota ba tin da amintacciyarsa ce a
lokacin?.

Kai ganin ƙwaƙwalwarta yana ƙoƙarin tarwatsewa ne yasa ta miƙe ta nufi wajen Smart,
dan wannan tinani ya fi karfin kwakwalwarta. A ɓangaren su mummyn Chuchu dik
tinanin da suke yi kenan, wato meyasa King zai tsani Hoorain har haka ne wai?.

Gida ya rikice da koke koke, gidan biki ya koma gidan mutuwa!.

Kwance momma ta isko Smart, ya ja bargo har zuwa saman chest ɗinsa, hannunsa rike
da phone ɗinsa yana latsawa. Ya yi nisa cikin abin da yake yi, har momma ta shigo
bai ji shigowarta ba, a kusa da shi ta zauna, ganin hankalinsa ya yi nisa a taɓa
waya yasa ta kai hannu ya karɓi wayar. Sosai ta ji mamakin ganin yadda ya zabura
zai kwace wayar, sam bai yi tunanin ita bace. Yana ganinta sai ya kara ɗaure fuska
tare da komawa ya kwanta yana ɗan kawar da kansa gefe.

Bata yi magana ba, amma ta sha jinin jikinta ganin yadda ya ɗaure fuska, alamar
ransa a ɓace har yanzu kenan. Juyo da screen ɗin wayarsa ta yi dan taga me yake
gani da ya zabura dan an kwace wayar haka. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallan screen
ɗin, sai kuma ta dawo da kallonta a kansa, lokaci guda ta ji wani irin sanyi ya
ratsa zuciyarta, cike da zolaya ta ce. "Wannan ita ce sirikar tawa ne?".

Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma gyara kwanciyarsa da ya yi zai ja bargo ya
rufe har face ɗinsa. Rike bargon ta yi, cikin sigar tausasawa ta ce. "Ɓacin rai ne
ya sanya ni yin wancan furicin, ba wai dan wani abin ba".

A ɗan takaice ya ce. "Amma dai ke kanki kinsa daddy ba'a a kan dai'dai yake ba ko?
Meyasa ba zaki yi ƙoƙarin mai da shi hanyar dai'dai ba!"........ "Omerish wannan
sarauta ce ba siyasa ba, sarauta da siyasa akwai banbanci matuƙa, kai siyasa ka
sani baka san sarauta ba, karfin izza da isa a sarauta yake ba'a siyasa ba, ba
komai ake juyawa da karfi a sarauta ba, dik abin da ka gani sai dai ka bishi a haka
yadda yake a dokance.........".

Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Babu wata dalili da zata sanya in yi
shiru in bar iyayena a kan hanyar halaka, and babu wata dalilin da zai sa in yi
shiru a kan saɓon Allah ana aikata ɓarna ba dai'dai ba!!". Ya kai karshen maganar
yana sake mata bargon. Ɗan matsawa kusa da shi ta yi. "Zaka iya dawowa nan?". Ta yi
maganar tana nuna mashi saman laps ɗinta da hannu. Shiru ya yi mata kamar bai ji ta
ba. "Zan faɗa maka wata magana ne"......... "Momma zaki fara ko? Please ki barni in
more ɓacin rai'na".

Kai ta ɗan girgiza. "Naki gaskiya, zo ka ji wani magana". Ta yi maganar tana jan
dogon hancinsa............. Ajiyar zuciya ya sauke... "Momma dayawan mata sun iya
kalaman yaudara, shiyasa bana haɗa hanyata da mace, haka mom take mun irin wannan
abin, idan dad ya ɓata mun rai bata barina in more ɓacin rai'na bare in yi fushi in
ki kula dad, sai ta zo ta mun kalaman yaudara tasa na manta, shi ne kema zaki mun
abin da take mun ko?".

(Malam Smart mu dai mata ba kalaman yaudara muka iya ba, tausasawa da tausayi muka
😇
iya, ko ya kuka ce my people's?)

Da hannu ta kara nuna mashi saman laps ɗinta ba tare da ta yi magana ba, dan dole
ya dawo da kansa samansu ya kwanta yana kallanta. Kyakkyawar dark black curly
hairnsa ta fara shafawa, ta lura ransa ya ɓaci sosai, sai ta nemi kawar da zancen
da suke yi ta hanyar cewa. "Wannan ce sirikar tawa?".

Ɗayan hannunta ya riko cikin nasa, yana ɗan rarrabe yatsun hannun nata ta amsa
da. "A'a kawai dai na ajiye hotonta ne, amma bamu da wata alƙa".

Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Ka tabbata kawai ka ajiye hoton ne?". Kai
ya gyaɗa mata alamar e. "To meyasa ka ajiye shi kuma meyasa kake ta
kallanta?"...... "Kai momma zaki fara ko? Ni kam ma dake da mom ban san wace ta fi
wani ba, ni fa ba kallanta nike yi ba"......... Kallan gefen ido ta wurga mashi, da
sauri ya sake cewa. "Da gaske momma ba kallanta nike yi ba"..................
"Omerish har na shigo ɗakin nan fa baka san na shigo ba saboda ka shagala da
kallonta, in baka faɗa mun gaskiyar wacece ita ba wace zaka faɗawa?". Cikin sigar
tausasawa ta yi maganar.

Yatsanta na tsakiya ya riko, ring da Jaish ya sanya mata ranar ya fara ƙoƙarin
zaresa daga hannun nata, sannan ya ce. "Momma kawai kyau take mun, and ina san wasu
ɗabi'u nata, that's all". Ya kai karshen maganar tare da cire ring ɗin. "Kana sonta
ne?". Ta jefa mashi tambayar. Da sauri ya girgiza mata kai kamar wani baby. "Momma
ni fa ki rabani da sharrin mata, kina ganinsu ƴan yaudara ne, ya na kare dake da
mom ma, bare in karawa kai'na wata".

Ita momma sam bata damuwa da yanayin maganarsa without a respect, saboda tasan ya
yake tin yana karami, a koda yaushe tana bibiyarsa, to tasan ba wai raini bane,
haka ya iya magana.

"To shikenan na ji baka sonta, yanzu dai ta shi ka yi lunch ka ji? Zuwa dare zan zo
mu yi magana, ina da magana mai mahimmanci da kai". Ta faɗa tana bin hoton dake
saman screen ɗin nasa da kallo, saboda ita kanta ta yi matuƙar burgeta, ta fita
sosai a hoton, sai murmushi take yi dimples ɗinta sun lotsa, ga eyesball ɗinta su
tura olive sosa, kamar ka saceta ka gudu!.

Jinjina mata kai ya yi haɗe da sakin hannunta ya karɓi wayarsa. "Ki sa Jaish ya
kawo mun lunch ɗin a yanzu". Ya faɗa yana miƙewa daga saman laps ɗin nata, dama
yunwa yake ji, kawai baya san kulasu ne yasa bai bi ta kan lunch ɗin ba. Ya kuma
cire mata ring ɗinta, dan ya ɗan kama hannunta har ya yi mata shaida,

Please Login or Register in order to submit comment