Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 76 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ya gyara
tsayuwarsa a jikin door ɗin, ya harɗe hannunsa a saman kirjinsa da kyau ya cigaba
da binta da kallon dan gane ina ta dosa. Gabaɗaya sai ta tsargu, ita kaɗai sai ta
rinƙa sauke ajiyar zuciya tana ɗan dafe kirjinta, sai kuma ta rinƙa satar kallonsa
ta kasan ido wanda dik yana kallonta, alamar rashin gaskiya dai ya tabbata kamar
yadda yake zargi.
"Aesh". Ya faɗa ba tare da ya kawar da kallonsa daga kanta ba. Kin amsawa ta
yi, dan tana ganin ko magana ta yi zai gane bata da gaskiya. Nisawa ya ɗan yi kafin
ya juya, kamar bai gane komai ba ya ce. "Tin da ba zaki yi mun magana ba to na
tafi, zan fita nan da 30 mins, zan dawo da wuri, pray for me". Ya kai karshen
maganar tare da barin wajen ba tare da ya sake ɗaure idanunsa a kanta ba.

Wani irin daɗi ta ji da ya tafi, da gudu ta diro kasan bed ɗin tana sauke ajiyar
zuciya, bukatarta kenan. Kai tsaye kofar ɗakin ta nufo domin ta leƙa shi, ya yi
matuƙar kyau cikin wanna dressing ɗin, dama daurewa kawai ta yi ta ki kallansa, tin
da ya tafi shi ne bari ta leƙa ta kallesa.

Sai dai kash, tana leƙowa suka yi four eyes, dan kuwa ba tafiya ya yi ba, ya
ɗan yi baya ne ya tsaya a wajen tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana bin
kofar ɗakin nata da kallo, kamar yasan zata zo leƙa shi. Ai suna haɗa ido bata san
time da ta kurma ihu ba, saboda ya mugun bata tsoro, bata yi zaton zata gansa a
haka ba, ga shi ya ɗan saki manyan idanun nan nasa sai ya yi kama da ya zarosu,
hakan ya kara razanata. Abin gwanin birgewa gwanin ban dariya.

Da gudu ta juya ta koma cikin ɗakin tana cigaba da kurma ihu. Har da turo kofa
zata murza key kamar wata mai aljanu. Hannu ɗaya yasa ya tare kofar ya hanata
rufewa. Ai a miliyan ta saki kofar ta koma ciki, ta ji haushin da ya kamata zata
leƙa shi, sam bata so haka ba.... Oh su Leesharh ana so ana kai wa kasuwa, wai ita
mai amana, ta zage ba zata ci amanar Sharifat ba, to da alama soyayyar Ramish ne
zai kasheta........ Suna yi ina shan maltina and exotic mai sanyi......🥱

Turo kofar ya yi ya dawo ciki. Tana tsaye a tsakiyar ɗakin ta yi ƙasa da kai tana
kuka. Ko me na kukan kuma?. Oho mata dai. Tsayuwa ya ɗan yi na sakanni a bakin door
ɗin, sannan ya taka izuwa ciki, mamakin kukan nata yake yi, amma kuma ya ji daɗi
yadda ya gane cewa tana san kallon shi, in bata san shi ba zata rinƙa leƙosa tana
san kallonsa idan yana waje ba. A gabanta ya tsaya kafin ya kai hannu ya riƙo
hannayenta cikin nasa. Wani irin shock da ta ji ne yasa ta yi saurin ɗago kanta,
while kukan nata ma ta ji ya tsaya cak.

Ƙasa sosai ya yi da murya kamar mai raɗa, cike da class haɗe da sigar rarrashi
ya ce. "Aesh menene abin kuka kuma? Na yi maki wani laifi ne yanzu kuma?". Ya
subhanallah, ai yadda ya yi magana yasa bata san lokacin da ta ji gabaɗaya ya
kwance mata notikan ƙwaƙwalwa ba, ta ji tamkar ba'a duniya take ba.

Rasa abin faɗe yasa ta ce. "Ba kai ne kake ta kallona ba". Ita kanta tasan bata da
dalilin yin kukan nata. "Da wani idanu kika kalleni har kika san ina kallanki?". Ya
faɗa kamar mai raɗa. Irin wannan kallon nata mai kama da harara mai matukar tafiya
da imanin nasa ta bishi da shi kafin ta yi ƙoƙarin kwace hannunta daga nasa tana
faɗin. "Ni ban kalleka ba, kuma ka dai'na kallona". Ta kai karshen maganar tare da
kwace hannunta da nufin ta bar wajen, tana ɗaure fuska, kamar wata maras gaskiya ta
yi saurin kai hannu saman face ɗinta tana goge hawayenta, saboda tsabar karya na
zuciyarta har da raya mata nadamar zub da hawaye a gabansa da ta yi, a gaggauce ta
nufi toilet dan ma kada su sake haɗa ido.

Sarai yana lura da dik wani motsinta, ya tabbata yau bata da gaskiya, akwai abin da
ta ɓoye mashi, amma koma menene zai gano ne, binta da kallo ya yi yana mamakin
yadda idan tana tafiya surar jikinta yake motsawa cikin natsuwa da ɗaukar hankali.
Sai da ta kurewa ganinsa sannan ya juya ya fita zuciyarsa na saƙa mashi abubuwa
daban daban a kanta.

Shirinsa ya yi tsab cikin tsadaddun kayansa, sannan ya ɗauki car key da wayarsa ya
fice daga gidan, tana tsaye a jikin window tana kallansa har ya fita, wani irin
nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, lokaci guda ta saki cool murmushi dan ta kalli
yadda ya buɗe gate ɗin, kenan ta samu abin da take so. A gaggauce ta saki curtain
na window ta dawo cikin bedroom ɗin, echolac ɗinta ta janyo daga cikin dressing
room, jikinta na kerma saboda sauri, please call me hijab ɗinta dake saman bed ta
ɗauka, a gaggauce ta nufo stair case, ko tura kofar bedroom ɗin ta rufe bata yi ba,
kirjinta sai bugawa yake yi, fargaba kamar zai kasheta, har ta fara haɗa gumi.

Cikin sauri ta yi ƙasa, bibbiyu take tsallake stair case ɗin. Tana fitowa harabar
gidan har da haɗawa da gudunta wajen isa wajen gate, kamar yadda ta ga ya yi haka
ita ma ta yi wajen buɗewa, ta kuwa yi dai'dai, kaifin ƙwaƙwalwarta dai yana taimaka
mata wani sa'in. Ta sha madarar mamakin ganin yanayin arear a zahiri, tsayawa ta
ɗan yi wajen yin ƴan waige waige tana kallan hamshaƙan gidajen dake wajen, gaskiya
sun haɗu iya haɗuwa. Ganin zata iya shekara a wajen ba tare da ta gaji da kallan
ƙawatuwar arear da gidajen dake wajen bane yasa ta yi gaggawar jan echolac ɗinta ta
kara gaba. Tana tafiya tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Ganin yadda take
yi ne ma yasa Officers dake tsaron main gate suka tareta haɗe da tambayarta wacece
ita kuma ina zata je?.

Bata ɓoye masu wacece ita ba, har da yi masu kwatancen Ramish, ta ce masu ita ce
suka fita da shi rannan, Officers ɗin sun ganeta sosai, sai suka saussauta
muryoyinsu a kanta wajen tambayarta ina zata je da ta fito yanzu? Kuma meyasa take
tafiya take waige waige haɗi da sauri haka kamar zata faɗi? Lastly ina Ramish da ta
fito ita kaɗai?......... Yau Ramish ta north gate ya fita, bai biyo ta main ba,
shiyasa basu ga fitarsa ba. Murya na rawa ta hau basu excuse ɗin cewa Ramish yana
gida ita kuma zata je gidan Abu Abdussalam ne duba ƴar uwarta Sharifat, ta yi
maganar cike da fargabar kada ace sun ga fitarsa su gano karya ta yi masu su mayar
da ita gida ko su kirasa a waya, jin cewa sun tambayi ina yake neman yasa ta yi
zatan kila basu ga fitarsa ba, tin da tasan gate uku ne arear take da shi.

Da farko sun so su ɗan yi kokwanto a kan fitarta, amma da suka tina wanenen Ramish
sai suka ji ba zasu iya ja da ita ba, kada yazamana shi ya ce ta tafi su kuma su
kutsa cikin lamarinsa su ja wa kansu, dan haka sai suka bata hanya cikin mutumci
har ma da ɗaga hannu su sara mata, ta ci albarkacin Ramish.

A hanzarce ta wuce, bata sake waigosu ba har ta yi nisa, dan tana tsoron waigowa
su sake jefanta da wani tuhuma. Tafiya take yi ba tare da ta san ina ta nufa ba,
har da saurinta gudun kada ruwan sama ya jiƙata, ta ga garin nata kara narkewa da
hadari.

Tsawon good two hours tana tafiya, idan ta gaji sai ta zauna ta huta, ta yi
tafiya mai nisan da har ta dai'na jiyo ƙamshin arear tasu. Daga karshe da wahala ta
yi wahala kafafunta dik sun yi mata tsami sai ta nemi waje saman wani kujera da ake
shiryawa a bakin hanya dan jiran ƙananan jiragen ƙasa masu kama da bus ɗin nan, a
nan ta zauna tana mayar da numfashi, ga wani irin kishirwa da take ji, saboda
tafiyar da ta yi.

Tinawa ta yi a ranta yau saura sati a fara azumi, lokaci guda ta ji zuciyarta ta
buƙaci da sanin ina zata samu mafaka? Afkawa ta yi duniyar tinani dan nemanwa kanta
mafita, bata yi aune ba sai ji ta yi ruwan sama mai karfin gaske ya kece kamar da
bakin kwarya, juyawa ta yi gabas da yamma, kudu da arewa babu mafaka a wajen, sai
dogayen bishiyoyi dake can nesa da ita, wani irin tsoro ne ya dira a ranta lokaci
guda, sai ta ji tamkar ta koma, sai dai kuma ita kanta bata san ta wani hanya ta bi
ta zo nan ba, tafiya kawai ta yi ta yi.

Wasa wasa ruwa na kara yawaita while gari na kara tsananta duhu, bata da mafitar da
ya wuce ta zauna a wajen, dan babu mafaka a kusa. Tana ji tana gani train na farko
ya zo ya tsaya a gabanta har tsawon mintuna biyu, a zaton drivern shiga zata yi,
suna cika mintuna biyu kamar yadda yake a dokansu drive ya tasheta ya kara gaba.
Kazalika train na biyu ma ya zo ya tsaya, nan ma bata iya miƙewa ta je ta shiga ba,
dan bata da wajen zuwa. A haka tana zaune a wajen har train huɗu suka wuce, ruwan
sama ya yi mata dukan gaske, ga shi ko kaɗan ruwan yaki tsagaitawa, bata san lokaci
ba, dan babu abin duba time a hannunta.

Ganin ruwan nan bashi da niyar tsayawa kuma cigaba da zamanta a wajen nan ba zai
haifar mata da ɗa mai ido bane yasa ta miƙe tare da jan echolac ɗinta ta fara
tafiya tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tin tana iya ganin dai'dai har jiri ya
fara ɗibarta, har lokacin ruwan sama bai dakata ba, nisa sosai ta yi daga in da
take, a daddafe take tafiya kamar mai gocewar kashin kafa.

After some hours. Almost 6 hours ana zuba ruwan sama, daga bisani ruwan ta rage
zuba amma bata ɗauke dikka ba, irin yap yap yap mai ratsa jiki ya sanya mura ɗin
nan shi ne yake cigaba da zuba. Tin daga farkon ruwan nan har karshensa a kanta ya
kare, a yanzu an kai gaɓar da ba zata iya cigaba da jurewa ba, tafiya cikin duhun
kai yasa har ta fita cikin jama'a bata sani ba. A dai'dai wannan gaɓa ta kasa iya
cigaba da tafiya, kanta yana yi mata wani irin azabbabben ciwo mai tsanani, sai
kakkarwa take yi, hakwaranta sai ba da sauti mai karfi suke yi, gabaɗaya ta takure
ilahirin jikinta waje guda, ga wani irin jiri dake fisgarta da karfi karfi. Dai'dai
kasan wani dogon karfen sadarwa wato internet, tana ƙoƙarin ɗaga kafafunta dan ta
cigaba da tafiya, sai dai ina, ta kasa, tana ɗaga kafa bata san time da jiri ya
fisgeta da karfi har ta saki echolac ɗin hannunta ta tafi gabaɗayanta zata kifa
ƙasa ba.

Sai dai bata kai kasan ba ya yi gaggawar tarota ta faɗa saman wide chest ɗinsa.
Kamar daga sama haka ya faɗo gabanta, yana sanye da waterproof jacket mai girman da
ya wuce gwiwansa, ya sanya hular jacket ɗin a kansa, dik da yana sanye da face
mask, hakan ba zai hana ka gane angry face ɗin nan nasa a yau ta fi ta kullum
kasancewa a ɗaure ba, harta idanunsa sun yi jajir kamar bashi da lafiya, wasu
zaratan maza guda biyu ne tsaye a bayansa dikkansu rike da umbrella, ɗaya ya rike
mashi ne ya tare mashi ruwa, ɗayan kuma ya rikewa kansa a in da ya biyo bayansa dan
su bashi tsaro. Ransa ya matuƙar ɓaci sosai, with his harsh voice ya bawa matashin
dake bayansa umarnin da ya ɗauka mashi echolac ɗinta su tafi. Yana gama bada
umarnin ya ɗan duƙa ya cicciɓeta sai saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya juya da
ita.

Bata kara sanin in da kanta yake ba sai da ta farka ta ganta a cikin bedroom, ga
wani irin ɗumi mai daɗi dake ratsata, tana ƙudundune a cikin duv mai laushin gaske.
Lokaci guda ta ware hancinta ta shaki daddaɗa kuma niimanraccen kamshin dake kai
komo a cikin ɗakin, slowly ta fara bin ko'ina na cikin ɗakin da kallo, while tana
jin kamar jikinta ba mallakinta bane, dik sai ta ji gangar jikinta tamkar baya a
tare da ita. Tana ɗago idanu sai kan drip dake ɗaure a hannunta, zaro eyesball
ɗinta waje ta yi dan ta kara tabbatarwa da kanta haka ne. Lokaci guda ta ɗan nisa
tare da cigaba da jujjuya eyes ɗinta dan ta tantace a in da take. Sai dai kuma, har
ta gama iya kallanta bata iya cinkar a ina take ba, ɗan lumshe idanunta ta yi na
ƴan mintunan da ba zasu gaza biyu ba. A hankali ta sake waro idanunta. Ai a miliyan
ta zarosu waje ganin shi a tsaye a gabanta, blinking eyes ɗin nata ta yi two time
kafin ta tsayar da kallanta cak a kansa, ta tabbata ba mafarki ko gizo bane, shi
ɗin ne kenan.

Angry face ɗin nan nasa babu alamar wasa kuma babu walwala ko kaɗan, tamkar bai
taɓa sanin menene sakin fuska ba, ya sha kunu ya murtuƙe, ko sannu bai ce mata ba,
sai dai ya kai hannu ya fara ƙoƙarin cire drip dake manne a hannunta, dan ya kare.
Sosai ta sha jinin jikinta, ta tsorata da ganin yanayinsa, muryarta na ɗan kerma ta
furta. "Good afternoon Yah Ramish"...... Tamkar mutum mutuminsa ne a wajen ba shi
ba, ya yi banza da ita, kamar bai ji ba. Sake shan jinin jikinta ta yi tana zazzare
eyesball ɗinta kamar an tare ɓera a tarko. Bata yi yunkurin sake ɗaga mashi gaisuwa
ba, saboda tasan confirm ya jita, amsawa ne bai yi niyya ba.

Zare drip ɗin ya yi ya ajiye gefe guda tare da juyawa ya nufi waje. Bayansa ta bi
da kallo, daga kan yanayin sleeping dress dake jikinsa ta iya fahimtar yanzu dare
ne ba rana ba, ta sha mamaki sosai na ganin cewa dare ya yi, ita da ta sume a
tsakanin azahar da la'asar, bata ma san kwana ɗaya ya wuce ba, dan tin jiya ta
sume, sai yau ta farfaɗo, dan ma Allah ya taimaketa ta samu kula daga hannun Dr Raj
da ya dawo jiya, kuma gobe zai koma kingdom of power, wani dalili ya dawo da shi,
ba dan kular da ta samu ba ai da ta ɗanɗana a jikinta. (Ina tantamar anya Leesharh
bata da kara mun ciki kuwa? Idan ma ba ciki akwai aljanu a kanta gaskiya 😅 kai
nama fi zargin cikin ne yake sakata yin abubuwa off head haka.)

Wasa wasa tsawon kwanaki biyu Ramish baya kulata, baya yi mata magana baya
kuma amsa nata maganar, alamar fa ran maza ya ɓaci sosai, tin bata wani damuwa har
abin ya fara taɓata, sai take jin tamkar a rami aka haƙa aka sanyata, dik ta fara
fita hayyacinta, tinani kala kala ne cike a cikin zuciyarta, wani lokaci ta ce bari
ta same shi ta bashi hakuri, sai ɓangare na zuciyarta ya ce mata waye nata ne shi
ɗin da har zata ce dan baya yi mata magana kuma baya amsa nata maganar zata damu?
Shin sun haɗa dangi ne? Mijinta ne? Ko ubanta ne? Uwarta ne? Ko yayanta ne? Waɗan
nan tinane tinanen su suke sanyawa ta ji ba zata iya tinkararsa ta bashi hakuri ba,
ga shi kuma zuciyarta ta kasa jurar rashin maganar nasa, tana jin kamar ta fasa
ihu. Har jikinta ya warware shi yake cigaba da kula da ita, time na shan magani da
ya yi zai zo ya bata, idan ya fita ba zata sake ganinsa ba har sai zai sake bata
wani maganin. Ko abinci ba shi yake kawo mata ba, wata dattijuwa ce take kawo mata,
kuma idan ta yi wa dattijuwar maga sam bata amsa mata, abin ya dameta sosai, ga shi
ba gidansu da ta sani ya dawo da ita ba, wannan gidan kam ma gabaɗaya ta rasa gane
kansa, ko ta leƙa ta window ba abin da take gani face pool dake ta baya da basket
ball area da gine ginen dake waje, abin ya jefata a ruɗani sosai matiƙa.

Uhm bata san cewa ita ce kawai makaminsu guda ɗaya da suke da shi dan isa ga
masu nikaf ba, tsaronta da lafiyarta abu ne mai matuƙar muhimmanci a garesu,
shiyasa ma ya canza masu gida, ya kawota waje mai tsaro sosai, damuwarsa yanzu ta
samu lafiya ya samu hujjojin dake hannunta ya fara gabatar da aikinsa.

Yau takama Friday, zaune take a saman dadduma bayan ta yi sallar isha'i, ta yi
shiru tana askar, amma tinaninta dik yana a kansa, yau ta kai har kololuwa sosai.
Good 30 mins ta ɗauka a zaune a saman daddumar tana addu'ointa kafin nan ta miƙe,
jiki dik babu kwari ta nufo bakin bed ɗinta da hijabin a jikinta, yau ko lunch bata
yi ba saboda damuwa a kansa. Dik halin da take ciki kuma sarai yana sane, dan ya
dasa mata Camera a cikin ɗakin, haƙiƙa ya ji babu daɗin kin yi lunch da ta yi, amma
ya danne ya cigaba da harkokinsa.

Tana zama a bakin bed ɗinta sai ga dattijuwan ta kawo mata abincinta kamar yadda ta
saba, haɗaɗɗen abinci mai rai da lafiya, sai tashin kamshi yake yi, tsohuwar ce mai
girka mata. Sosai ta yi mamakin ganin lunch da ta kawo Leesharh bata ko taɓa shi
ba, kamar yadda ta ajiye babu abin da ya motsa shi daga wajen, amma kasancewar
Ramish ya ce ko word ɗaya kada ta yarda ya haɗata da Leesharh ɗin yasa bata
tambayeta meyasa bata yi lunch ba? Sai kawai ta kwashi kayan abincin ta wuce ta
fita bayan ta ajiye mata dinner ɗinta kenan. Dogon tsaki Leesharh ta ja bayan fitar
tsohuwar, sannan ta dallawa kayan abincin harara tamkar su suka yi mata laifi. A
dai'dai lokacin da take wannan abin sai da ta so sanya Ramish murmushi, saboda yana
kallanta, dan dai bai iya murmushin bane da yau sai ya yi. A ransa ya ce ko me
dinner ɗin ya yi mata take harararsa kuma? Yarinya sai faɗar bala'i!.

A fili kuwa cigaba ya yi da feshe jikinsa da daddaɗar perfume ɗinsa, yana shirye
cikin kayan barci, kwanciya zai yi idan ya je ya bata drugs ɗinta ya dawo. Ita
kuwa, gyrawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike da tinaninsa, tana jin tamkar ta tashi
ya je bedroom ɗinsa ta sanyasa a idanunta ko zata ji sanyi. Amma girman kanta da
rike amanar Sharifat yasa ba zata iya ba, a haka ta daure ta lumshe idanunta alamar
barci take san yi, ba zata ci dinner ɗin ba kenan. Da kwanciyarta bai fi five
minutes ba sai ga shi ya shigo bedroom ɗin bakinsa ɗauke da sallama ƙasa ƙasa. A
hanzarce ta miƙe zaune idanunta a kansa, shi kuwa ya ɗaure angry face ɗinsa sosai,
yana tafiya cikin natsuwa. Kai tsaye gaban bed ɗin ya nufo, bai ko kalli in da take
ba ya hau ɓalle drugs ɗinta yana miƙa mata a kan ta karɓa ta sha.

Ƙin karɓa ta yi ta tsare shi da kallo, ya san me take yi wa dan haka sai ya zuba
drugs ɗin a saman wani small plate dake wajen, sannan ya ɗauko ruwa ya buɗe mata
bakinsa, ya ajiye mata su ready kafin ya juya ya nufi hanyar fita abinsa, wato idan
ta ga dama ta sha, in kuma bata yi niyya ba sai ta barshi ko ohonsa, ai jikinta ne
zai gaya mata. Anya ba dan ma babynsa yasa yake damuwa da ita ba kuwa?. To mu je
dai zuwa.

Ganin fita zai yi yasa ta yi gaggawar miƙewa tsaye, muryarta na rawa ta ce. "Yah
Ramish dan Allah ka tsaya ina san yin magana da kai". A tsorace ta yi maganar, dan
tana fargabar abin da zai iya faruwa a tsayawarsa ko buɗar bakinsa. Tamkar ba da
shi ta yi magana ba, ya cigaba da tafiyarsa. Ai a miliyan ta watsa da gudu ta tare
gabansa, har sai da ya ji wani irin shock jin yadda ta yi gudun, ya ɗan ji fargabar
kada ta faɗi. Meyasa ya damu da ita haka? Meyasa kuma yake kula da ita har haka?
Meyasa baya san wani abin ya taɓata ko kaɗan ne? Akwai ayar tambaya fa a
lamarinsa!.

Ƙara ɗaure fuska sosai ya yi, ya haɗe gerar sama da ƙasa, kwata kwata yaki yarda
ya kalleta, with harsh voice ya ce. "Bani hanya in wuce!"....... Marairace fuska
sosai ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Ramish dan Allah ka yi hakuri, na san
na yi kuskure, amma na tuba ba zan sake ba!"........ Ƙara daure angry face ɗin ya
yi, murya a kausashe ya ce. "Kuskure?! Da wani abin ya same ki shi ma zaki kirasa
da kuskure ne?! Kin san risk da kika gefa kanki damu bakiɗaya a ciki kuwa? Kin san
yadda ake farautar rayuwarki kuwa? Kin san halin da kike ciki kuwa? Kin san
matsayin lafiyarki a wajena kuwa?!".

Tin da ya fara magana idanunta a kansa, bata taɓa ganin ya yi magana cikin zafa har
haka ba, hasalima baya ɗaga murya a magana sai yau, da alama ta yi babban kuskure
ne ba karama ba.
"Ka yi hakuri, wlh ba zan sake ba ko da sunan wasa?" Cikin marairacewa sosai ta
yi maganar. Nisawa ya ɗan yi, yadda ta marairace murya tasa ya ji wani irin a cikin
ransa. "Shin kin san mutanen da suka biyoki daga fitarki har izuwa in da kika je
kuwa? Kin san rayuwarki tana gab da zuwa karshe a lokacin da muka isa gareki kuwa?
Ko kin ɗauka na damu ne saboda ciwon da kika jama kanki na ruwa da ya dakeki?". Ya
kai karshen maganar tare da kai hannu ya damkar rigar jikinsa, karfi yasa wajen
tsaga rigar gida biyu, jifa ya yi da ita gefe tare da sanya hannun nasa ya yi mata
nuni wide chest ɗinsa da gabaɗaya yankar wuka ne a wajen, sai dai ya sha treatment
sosai, almost yanka 4 masu zurfi ne a wajen, ga ɗaya a saman shoulder ɗinsa wajen
damatsan hannunsa. "Diba abin da kika ja mun, ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu
wani maganar ake yi a kanki ba wannan ba, kin yi zatan saboda abin da ya faru a
tsakaninmu ne yasa na ɗaukeki daga gidan uncle? To idan ma haka kike zata kin
yaudari kanki, ina san ki san cewa a gidan uncle rayuwarki cike take da barazana,
ko kin yi zatan ban san attacking ɗinki da aka yi a ɗakinku daren ranar bane? Dik
ina sane da komai, that's the reason why na ɗauke ki daga gidan, amma dik baki yi
tinanin komai ba kika sa kafa kika fita". Cikin ƙunan rai ya yi maganar!. Ta bashi
haushi sosai!!

Wani irin zaro idanu ta yi a lokacin da ta ga yankar dake jikinsa, ta tsorata
sosai, ashe yana kan gaskiya fushin da yake yi da ita, ashe ta tabka babban kuskure
na fita da ta yi ba tare da izininsa ba, yanzu ta ja mashi ciwo, ta kuma ja dole ya
canza masu gida, ta ja mashi abubuwa da daman da bai bayyana mata ba, ciki har da
rasa abokin aikinsa da ya yi, sun kashesa, sun zo harbinza da bindiga ba tare da
saninsa bane babban yaron nasa ya tare masa, harbin ta same shi Allah ya yi mashi
cikawa, dik a bayanta da suka bi, da ita za'a kashe Allah yasa bai ajiyeta ƙara
zube ba, dik motsinta yana sane da shi, lokacin da ta fita daga gidan watch dake
hannunsa ta buga mashi alarm na an buɗe gate na gidan, Allah yasa bai yi nisa ba
shi ne ya juyo ya dawo, dan in baku manta ba yana fita ba'afi da 10 mins ba ta fita
ita ba, so bai yi nisa da ita ba, da yana nesa ma ai da ta jima da mutuwa. Shi da
farko ma bai yi zatan ita ce ta fita ba, ya yi zatan ko wasu ne suka shiga cikin
gidan, sai da ya juyo ya dawo, can ya hangota a hanya tana tafiya!.

Lokacin da ya biyo bayanta ya so ɗaukarta tin time da ta fita arearsu, amma sai ya
lura da wata black car dake biye da ita a baya, hakan yasa ya kira babban yaronsa
da ya zo da wata mota mai tinted su bi wannan mota. Mutanen dake bibiyarta sun
cigaba da binta suna san ta matsa daga idanun mutane su ɗauketa su aiwatar da
nufinsu a kanta, shi ma kuma ya cigaba da binsu dan ya kamasu, abin da yasa bai yi
gaggawar bayyana ya kamasu ba shi ne dan bai san su nawa bane, watakila bayan
wannan mota akwai wani a ɓoye bai sani ba, hakan yasa suka cigaba da binsu da taƙa
tsantsan. Lokacin da ta fita daga cikin mutane sai suka yi ƙoƙari kamata, amma sai
suka ga kamar asirinsu zai iya tonuwa, wannan dalilin yasa sai suka yi yunƙurin
harbinta daga ɗan nesa da ita kenan,

Please Login or Register in order to submit comment