Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 7 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi da securitys ɗin na tsawon 10 mins, bai bawa kowa damar jin
maganar da suka tattauna ba, daga karshe ya rufe masu zancen da yau zai wuce
Tunisia.

Yana gama magana suka amsa umarninsa cikin girmamawa, suna ta jiran ya miƙa masu
baby sai suka ga akasin haka, dan kuwa yana gama magana ya sanya aka rufe mashi
kofar mota, basu yi gangancin cewa ya basu babyn ba, saboda sun san ba mancewa ya
yi da shi a hannunsa ba, saboda dik maganganun da ya yi da su ma idanunsa a kan
babyn, so yana sane da shi.

Wucewa suka yi suka koma cikin hospital ɗin, shi kuma ya kama hanyar tafiya
izuwa hotel ɗin da suka sauƙa.

Yana sako kafarsa a cikin room ɗinsu ɗauke da babyn nan Jaish yana farkawa daga
doguwar sumar da ya yi tin jiya da rana.

A hankali ya fara motsawa yana ɗan kwaɓe fuska, tsayuwa a tsakiyar ɗakin uncle
Jahiz ya yi yana kallonsa.

Ganin da gaske farkawa yake son yi yasa ya zaga ta ɗayan gefen bed ɗin domin ya
kwantar da babyn ya dawo wajen Jaish.

Sai dai ina, yana kwantar da babyn ya fara ihu wanda sanadiyar hakan yasa Jaish ya
waro idanunsa waje babu shiri. A hanzarce uncle Jahiz ya ɗauki babyn ya rungume
haɗe da fara ɗan jijjiga shi ya dawo ta kusa da Jaish da ya gama waro idanunsa waje
yana bin saman p.o.p da kallo.

A hankali Jaish ya juyo da kallonsa a kan uncle Jahiz dake ta faman ɗan bubbuga
jikin baby.

Kara zaro idanunsa waje ya yi, bai iya motsa bakinsa ba, dan ko'ina na jikinsa ya
yi mashi nauyi, tongue ɗinsa ta yi mashi nauyin da ba zata iya yin magana ba, amma
tabbas yana son yin magana, kuma ga dikkan alamu ya dawo cikin hankalinsa, kallon
sanayya yake yi wa uncle Jahiz ba kallon bakunta ba.

"My son brk da tashi". Uncle Jahiz ya faɗa yana kallonsa shi ma.

Bai yi wani motsi ba, bai kuma yi wani yunkuri ba, shiru kamar wanda ruwa ta
cinye.

"Kana san wani abin ne?". Uncle Jahiz ya sake jefa mashi tambaya.

Ido kawai ya kafe shi da shi babu ko kyaftawa. Ganin hakan yasa uncle Jahiz ya ɗan
matsa daga in da yake tsaye dan ya ga da gaske Jaish ya farfaɗo ne ko dai ya sake
suma idanunsa a buɗe ne, yaga irin kallon da yake yi mashi babu ko kyafawa tamkar
in aka zare ran mutum yana kallon wani wajen.

Yana matsawa Jaish ya bishi da ido, wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da yin
hamdala ga Allah, sannan ya matso ya zauna kusa da jaish ɗin.

"Akwai abin da kake so ne my son?".

Da kyar ya iya girgiza kai, a hankali ya fara ƙoƙarin motsa laɓɓansa dan ya yi
magana. Idanun uncle Jahiz a kansa.

Rigasa uncle Jahiz ya yi da cewa. "Zaka yi wanka ne?".

A hankali ya gyaɗa kansa sama alamar e, dama abin da yake ƙoƙarin ya gayawa uncle
ɗin nasa kenan, amma tongue ɗinsa taki motsawa.

Miƙewa tsaye uncle Jahiz ya yi ya nufi cikin toilet, babynsa dai yaki ya kwanta,
rike da shi ya shiga cikin toilet ɗin.

Ga shi dai katafaren hotel mafi tsada suka kama, amma sai gabaɗaya uncle Jahiz ya
raina hotel ɗin, toilet nasu ko na bedroom ɗin Sarina bai kai ba, sam basu ji daɗin
sauƙa a wajen ba, amma da yake a kan hanya suke sai ba su wani tashi hankulansu ba.

Shiga ya yi ya haɗa mashi ruwan wanka mai ɗan ɗumi, sannan ya fito, a lokacin
babyn nasa ya yi barci, cikin dabara ya kwantar da shi a saman bed ɗin, tamkar ya
iya reno, sannan ya matso domin taimakawa Jaish ya miƙe tsaye.

Ga dikkan alamu Jaish ya dawo dai'dai sosai, dan tambayoyi uku ne yanzu a cikin
ransa, ina Momma da dad? Ina Jawad? Ina Auta? Waɗan nan su ne kawai damuwarsa, ya
yi kewarsu.

Taimaka mashi uncle Jahiz ya yi, da kyar ya iya tashi zaune, har yanzu yana ganin
jiri jiri, sanna kansa yana ɗan sara mashi kaɗan kaɗan.

Hakika ya sha madarar mamaki na ganin irin yanayin kayan da yake a jikinsa, ko a
mafarki bai taɓa ganin irin kayan ba, domin kaya ne na gargajiya wato shadda jampa
da wando, shi dai yasan ba irin kayansu bane wannan, bai ma taɓa ganin irin kayan a
zahiri ba sai dai idan a waya ya ci karo da videos na Hausawa, amma yau shi ne
sanye da irin wannan kaya, to a ina ya samo su? Ya jefawa kansa tambayar da bashi
da amsa, kuma bai iya magana bare ya tambayi uncle Jahiz.

Taimaka mashi uncle ɗin nasa ya yi izuwa cikin toilet, ya fito ya bashi waje, ya
dawo cikin ɗakin domin haɗa masu kayansu jirginsu ya kusa ɗagawa, dik abin da yake
yi idanunsa na'a kan babyn nan na Khadija, da alamu ya kamu da kaunar yaron sosai
sosai, kun san fa kyawawan koreans akwai madarar kyau ba kaɗan ba, dole su shi ga
ran mutum ko baya so.

After some minutes. Like wow Jaish ya fito da kafafunsa ɗaure da towel a
kunkuminsa, ya samu kwarin jiki na wanka da ya yi, a take har ya fara komawa yaron
mommarsa, dama ya ɗan yi duhu zamansa a Yola.

Kayansa uncle Jahiz ya fitar three-piece suit ya miƙa mashi, sannan ya janyo zip
ɗin echolac ɗin nasu ya rufeta.

Ba musu Jaish ya karɓi kayan domin ya shirya, uncle Jahiz ya fito waje dan ya sanar
da securitys ɗinsu su juya kan motocin zasu wuce airport dan su koma ƙasar Tunisia
yanzu.

Kafin ya dawo cikin ɗakin Jaish ya kammala shiryawa, like wow ya yi masifar kyau
sosai, sai dai gashin kansa a jiƙe yake, bai busar da ita ba, ya zubawa babyn
Khadija idanu yana mamakin a ina uncle ɗinsu ya samo wannan kyakkyawan yaro haka?.

"Jaish yaron ya yi maka kyau ko?". Uncle Jahiz da ya shigo a yanzu ne ya jefa
mashi wanna tambaya.

To kun dai san halin yaron Mommarsa, ba sai na sake faɗa ba, dan haka yana jin
uncle Jahiz amma bai amsa ba, ya yi banza da shi, sai ma ya wuce ya zauna a bakin
bed tare da yin kasa da kai kamar mai nazarin wani abin, da alama kunyarsa da ya
rasa a garin Jimeta yau ta dawo, halinsa dai sak ya dawo, an koma gidan jiya malam.

Da yake uncle Jahiz ya san halinsa sai bai wani damu dan bai amsa shi ba, ya ce.
"Zamu iya tafiya a yanzu ko akwai wani abin da kake son yi?".

Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya iya gamana ba, alamar zasu iya tafiya kenan,
maganar ce kawai ba zai yi ba, yana son tambayar uncle ɗin nasa a ina suke kuma me
ya kawosu nan? Amma ina baya son yin magana yasa ya yi biris da zancen, da alama ma
ya karo walaƙanci kaman ba shi ne ya gama shanyewa Mahnoor baki jiya ba, dik ya
mance wanna!. Tashin sense, me kuke tunanin zai faru?.

Ɗaukan baby uncle Jahiz ya yi ya nufi waje, yana fita yasa securitys da su shigo su
kwasan masu echolacs ɗinsu, zasu fara zuwa asibiti su mayar da babyn Khadija sannan
su jandadawa Dr da ya kula da su kafin su tafi.

Haka kuwa aka yi, karfe ɗaya na rana dai'dai jirginsu ya ɗaga sai kasar Tunisia
cikin amincin........ Safe journey our Jaish and uncle Jahiz.


=====KINGDOM OF POWER======

Zaune take a saman sofa a part ɗin Mammienta, daga ita sai wani figaggiyr simi,
wani riga ne mai siririn hannu wanda ya tsaya mata a iya gwiwowinta, fararen
kafafunta suna cikin wani katan bowl mai ɗauke da ruwa launin orange color, skin
ɗin Sarina kullum cikin samun gyara yake, ta iya kula da shi matuƙa.

Wata kuyanga ce durkushe a saman gwiwowinta a gaban Sarina tana aikin wanke mata
kafafunta dake cikin ruwan.

Mammie na zaune a saman sofa kusa da ita, Sarina tana riƙe da wasu hotuna tana
kallo tana sakin ƙayatattcen murmushi, da alama yau suna cikin matsanancin
farinciki daga ita har Mammie ɗin tata, sai hira suke zubawa suna fara'a.

Ita kuwa wannan kuyanga kanta a kasa tana aikinta cikin girmamawa, ga dikkan alamu
tana bala'in tsoron Sarina.

Fanan ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama. Babu wanda ya amsa
sallamar a cikinsu face kuyangar nan, ita ma a cikin zuciya ta amsa, saboda tana
tsoron Sarina ta hukuntata, zasu ce ai ba ita aka yi wa sallamar ba.

Wata kuyanga ce ta sake shigowa baki ɗauke da ladabebben sallama.

Kusan a tare suka kariso ciki ita da Fanan, ita tana zuwa ta fara aikin shafawa
Sarina kayan gyaran jiki a dik wasu sassa na jikinta, ita kuma Fanan saman sofa ta
zauna tana haɗe rai kamar hadari.

"Lafiya kike wani kwaɓe fuska haka?". Cewar Sarina, ta yi maganar tana wani bin
Fanan da kallo mai kama da harara.

"Ke Aunty Sarina baki san me yake faruwa ba ko?".

Ɗan taɓe baki ta yi kafin ta ce. "Me kuma yake faruwa?".

Mammie ma kasa kunne ta yi dan ta ji me yake faruwa.
Kara haɗe rai Fanan ta yi haɗe da alamar tausayawa a saman face ɗinta ta fara
magana.
"Baki san Yah Jawad yana can kamar zai mutu saboda an aurawa Yah Rizwan Chuchu
ba ko?".

Siririn tsaki ta ja. "To ni me ya dameni da su?".

"Kai Aunty Sarina kin san fa Yah Jawad ne yake son Chuchu ba Yah Rizwan ba, ke baki
ji tausayinsu bane?".

Yamutse fuska ta yi tare da haɗe rai. "Su mutu ma dikkansu idan suka ga dama, ni
kinga in abin da ya kawo ki nan kenan tashi ki bamu waje".

Ɗan zaro idanu Fanan ta yi like surprise haka. "Aunty Sarina su Yah Jawad ne
fa!".

"To sai aka yi yaya idan su ne? Nace su mutu idan suka ga dama! Ni ki rabu dani da
abin da nima yake rai'na".

Da sauri ta dawo da kallonta a kan Mammie. "Mammie kin ji abin da Aunty Sarina take
faɗe ko? Su Yah Jawad take cewa su mutu fa".

Ta yi maganar cike da yakini da sa ran Mammie zata yi wa Sarina faɗa kuma ita ma ta
ji babu daɗi a kan maganar, ina ai sai ta ga saɓanin tunaninta, dan kuwa ɗaure
fuska sosai mammie ta yi kafin ta ce.

"To sai me dan ta ce hakan?".

Zaro idanun sosai Fanan ta yi, she was so surprised jin amsar Mammie tasu.

"Mammie ban gane ba!". Tana kara zaro idanu ta yi maganar.

"Ba zaki gane ba ai, mu kingan mun nan ba su Jawad bane a gabanmu, kowa ma a
cikin Kingdom ɗin nan in ya ga dama ya mutu!!". Cewar Sarina uwar rashin kunya.

Kasa yin magana Fanan ta yi, ta zuba masu ido tana mamakin jin furucinsu.

"Ke wai baki ma san dik abin da yake faruwa da su Mammie ɗin ce ta haɗa ba ko?".
Cewar Sarina.

A miliyan Fanan ta kara zaro ido waje tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa haɗe da
furta kalmar what!! Ba tare da ta san kalmar ta fita daga bakinta ba.

"Kwarai kuwa, mammie ce ta haɗa dik wanna cakwakiya, dan haka ki wuce ki bamu
waje uwar ƴan tausayi!". Cewar Sarina again.

Yadda kuka san ruwa ya cinye Fanan, tamkar babu ita a wajen ta yi shiru, al'ajabi
ya kusa kasheta.

"Tashi ki fita ki bamu waje tattaunawa muke yi uwar masu tausayi". Cewar
Mammie.

Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta mike, sumumui sumumui ta nufi kofar fita.

"Sakarya kawai wadda bata san ina yake yi mata ciwo a jikinta ba, shashasha wai ke
uwar tausayi! Zaki mutu babu wanda ya ji sautin kukanki in dai kika ce tausayi zaki
yi a rayuwarki!!" Cewar Sarina dake binta da wani matsiyacin kallo.
Sarai ta ji abin da Sarina ɗin ta faɗa, amma bata juyo ta tanka mata ba ta nufi
waje kawai tana yi masu addu'ar shiriya.

"Ya isa haka my daughter". Cewar mammie ga Sarina.

"Allah Mammie Fanan wawiya ce wacce bata san ciwon kanta ba, ni bakanta mun rai
take yi wlh".
Tana magana tana hararar kuyangar dake gabanta tana wanke mata kafa, kamar
kuyangar ce ta yi mata laifi.

Kunsan Fanan a part ɗin Momma take yawan zama dan ta sami soyayyar Jaish, da farko
ita ma zuciyarta ya fi karkata a irin halin mammiensu, amma zamanta da momma ya
canzata izuwa mutumiyar kirki, kunga kuwa ko bata auri Jaish ba ai ta sami babban
abu da zai iya zame mata makamin tsira duniya da lahira, wato halayyar kirki haɗe
da ilimin addini kenan, ai kunga ta tsira ta kuma ci ribar zamanta da Momma ko?!.

Tana barin part ɗin nasu ta wuce King part, kai tsaye ɗakin gyaran jikin su Aneesa
da su Mama Haulat suke girka su a can ta nufa, jikinta dik a sake baiwar Allah.

Ta sha madarar mamakin rashin samun Chuchu a ɗakin, Aneesa kawai ta samu, ta so
tambayarta ina Chuchu and Auta sai kuma ta sami Aneesa tana murzar kuka, shanye
tambayar ta yi a ranta tare da hayewa saman bed ɗin, cikin sanyin murya ta fara
rarrashin Aneesa tana bata baki har da gaya mata wata bata auran mijin wata.

Sam Aneesa taki kulata, dan ita kaɗai tasan me take ji a cikin zuciyar nan tata,
tana san Rizwan za'a aura mata Jawad haba dole ta ji zafi.

==========Luv Bird==========


A tsorace ta sake shi tare da komawa jefe ta tsaya haɗe da dawo da kallonta a
kansa. Dik jikinta kerma yake yi alamar tsoro, a hankali take ta satar kallon su
uncle Abbas da suka shigo cikin ɗakin.

Allah sarki shi kuwa kasa iya riƙe kansa ya yi, wani irin jiri da ta ɗebesa ne sai
da ya yi baya baya ya koma saman mattress ɗinsa ya zauna yana sauke numfashi a
hankali hankali mai zafin zazzaɓi, dama saboda ganinta yasa ya samu kwarin gwiwar
iya miƙewa.

Dikkansu idanunsu a kan King da yake ta aikin binsu da dara daran idanun gadon nan
nasu.

Momma dake tsaye kusa da uncle Taheer ne ta ce.
"Jannat me kike yi a nan kuma? Ya aka yi su Haulat suka barki kika fito daga
wancan part ɗin?".

Ai tana jin maganar momma tamkar wadda aka kwaɗawa guduma a tsakiyar kai, da karfi
ta wage murya ta rushe masu da kuka babu kama hannun yaro.

Kasa da kai Jawad ya yi yana tunanin abin da yakamata su yi, dan dai shi wlh ba zai
iya hakura da ita ba!.

Uncle Taheer ne ya ce. "Haba momma, wai ni ku meyasa kuke son saka yarana kuka ne?
Yanzu dai ga shi kin sakata kuka".

Harararsa ta yi tare da cewa. "Daga tambayarta zata rushe da kuka ka ce na sakata?
To me na yi mata?".

Uncle Taheer zai sake yin magana King ya ɗaga mashi hannu hakan ya haifar da
nutsuwa tsit na gabaɗaya familyn dake biye da shi, sannan suka kara gyara
tsayuwansu tsit alamar sun bi umarni.

Uncle Abbas ne ya fara takawa ya ƙarisa cikin ɗakin kusa da Chuchu, hannunta ya
riƙo a cikin nasa, cikin sigar rarrashi haɗe da zolaya kaɗan ya furta.

"Menene kuma Jannat? Meyasameki kike kuka?".
Kamar bai san kukan me take yi ba!.

Faɗowa jikinsa ta yi tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, irin kukan
nan ne wanda zuciyan mutum yana kusa, zaku ji har wani shessheƙa take yi kamar zata
haɗiyi zuciyarta.

Cikin kuka haɗe da ɗaga murya, da kyar ta iya fara faɗin.

"Daddy wlh ni Yah Jawad nike so, shi ma ni yake so, dan Allah ka cewa dad kada
ya rabamu, ni bana son Yah Rizwan".

Yadda take magana sai ta baka tausayi, har wani shakewa voice ɗinta yake yi.

King ne ya amsa mata da cewa. "Amma ba ke kika ce mana Rizwan kike so ba?".

Sautin kukanta ta kara haɗe da faɗin. "Allah dad ni ban ce ba, ni Yah Jawad nike
so".

Momma ce ta murje idanu haɗe da shafa toka kamar bata san komai ba ta ce.

"Da bakinki kika ce Rizwan kike so ba Jawad ba, dan haka zo ki wuce ki
koma wajen su Haulat su cigaba da shiryaki anjima akwai taron dinner na musamman".

Ƙanƙame uncle Abbas da karfi ta yi tana mai cigaba da kuka tana faɗin.
"Daddy ni nasan zaka yarda da ni, tun da dad da momma basu yarda da ni ba
shikenan, nasan kai zaka fahimceni, wlh ni ban ce ina son Yah Rizwan ba, dan Allah
daddy kada ka bari dad ya kai ni wajen Yah Rizwan........"

Bai bari ta ƙarisar da maganar ba ya ɗaura manuniyar yatsarsa a saman lips ɗinta
alamar ta yi shiru, dan yadda take maganar nan tsab zata iya haɗiyar zuciya ta
mutu.

"Ya isa haka Jannat, ina nan ai babu wanda zai rabaki da Jawad ɗinki, ba wanda
zai kai ki wajen Rizwan, ki kwantar da hankalinki".

Cewar uncle Abbas da yake aikin goge mata hawayen, sai dai yana gogesu wasu
suna kara zubowa kamar ruwa ya buɗewa kansa hanya.

Cikin zolaya momma ta ce. "A'a fa matar Rizwan ce kada ka kawo mana shubuha a
cikin lamura".

Kara ƙanƙame uncle Abbas ta yi tare da cewa. "Wlh ni daddy bana son shi, Yah Jawad
nike so".
Yadda ta yi maganar a ruɗe ne yasa uncle Abbas ya yi saurin katseta, dan ya lura
su momma zasu ruɗar mashi da ita, sai ya yi maza ya ce.

"Babu wanda zai kai ki wajen Rizwan, Jawad shi ne mijinki ba Rizwan ba".

Jawad da tun da suka shigo kansa na'a kasa ne ya ɗago a miliyan yanzu, idanu ya
zaro waje sosai, da kyar ya iya cewa.

"Daddy me kake nufi?".
Jinjina kai uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Kwarai kuwa abin da ka ji shi ne
gaskiya, kai ne mijin Jannat ba Rizwan ba".

A hanzarce ya miƙe tsaye, lokaci guda ya ji karfi ta zo mashi, ita ma Chuchu bata
san lokacin da ta saki uncle Abbas ta dawo da kallonta a kan flowern nata ba.

"Please dad don't play with my heart, ba wai na faɗi hakan dan raini bane, a'a,
nasan ka saba yi mun wasanni kala kala, please don't make this as a part of joke to
me, zan iya mutuwa idan ka yi hakan".

Siririn murmushi uncle Abbas ya saki, a hankali ya kamo hannun Chuchu, ya matso ya
riƙo hannun Jawad ɗaya. Ya buɗe tafin hannun Jawad ya ɗaura tafin hannun Chuchu a
saman, cike da so da kauna ya fara magana kamar haka.

"I knew that koda yaushe muna cikin wasa da kai, but this isn't a joke,
Jannat is ur wife, gata nan kuma na miƙa maka ita amana, don't let her tears to
come out dik da nasan ba zaka yi hakan ba".

Ai mutuwar tsaye ya yi, ya kasa iya sake yin magana, wasu irin zafafan hawayen
farinciki ne suka fara wanke fuskarsa, ya kasa fahimtar a wace iriyar duniya yake,
gabaɗaya ya rasa me zai sake yi.

King ne ya ce. "Eyeee my son ya girma ya yi aure, to me zaka yi mana kuka
kuma?".

Uncle Taheer ya karɓa ta cewa. "Ni yaya kada ku takurawa ɗana, ku je bari mu yi
sirri da shi".

Yana magana yana nufar Jawad.

Mom ce ta ce. "To mu dai a bamu ɗiyarmu mu tafi da ita, sai ku yi ta sirrinku ɗin".

Ta yi maganar tana miƙawa Chuchu hannu a kan ta zo. Kara ƙanƙameta Jawad ya yi, da
kyar ya iya furta.

"Please Momma ki ɗan bar mun ita a nan ko da na 10 mins ne kin ji? Long time
bana tare da ita, and...........".

Uncle Abbas ne ya katse shi da cewa. "Babu wanda zai ɗauke maka ita, ba 10 mins ba,
even one hour take is your time today".

Juyawa momma ta yi ta nufi waje tana faɗin. "Kuzo mu je kada Abbas ya koremu".

King ne ya rufa mata baya a in da ya nufi fada dan ya bada umarnin sarkin hatsi ya
fito da abinci a girka dayawa a kai gidajen marayu, sannan su tabbatar sun girka
abincin da zai kai a ciyar da gidajen prison dake garin gabaɗaya, su ɗauki tsawon
sati guda suna ciyar da gidan prison and gidanjen marayu, su rabawa talakawa
buhuhhunan abinci da kuɗi makudai dik dan murnar bikin Jawad and Chuchu, sannan su
ziyarci asibitoci dan duba waɗan da za'ayiwa aiki kuma babu kuɗin yi, su biya masu
kuɗin aikin, wanna hurumin sarkin fada ne, shi zai jagoranci zuwa asibitoci ya
tabbatar ya biya kuɗin aiki da magungunar marasa karfi.

A wajen ɗaurin aure ma ya yi kyauta da kujerun makka sun kai 50, ya kuma yi kyauta
da makuɗan kuɗaɗe ta hanyar raba check, anyi abubuwa da dama, King adalin sarki ne
mai taimako sosai.

Wai ina maganar waɗan da suka karo masu hari? Muje dai zuwa.
Uncle Taheer ma fita waje ya yi ya bar uncle Abbas, Jawad and Chuchu kawai a cikin
ɗakin.

Zaunar da Jawad a bakin bed uncle Abbas ya yi, sannan ya ja hannun Chuchu suka
zauna a tare, yana a tsakiyarsu ya fara yi masu nasiha mai ratsa zuciya.

Shiru suka yi suna sauraronsa har ya dasa aya, sannan ne Jawad ya ce.
"Daddy please tell me yadda aka yi Jannat ta zama mallakina bayan ka ce mun Yah
Rizwan dad ya bamawa?'.

Ajiyar zuciya uncle Abbas ya sauke, nan take yanayin face ɗinsa ya canza, alamar
ya shiga damuwa, hakan yasa zuciyar Jawad ta kara karaya, dan bai san dalilin
sauyawar face ɗin daddyn nasu ba.

Sun kasa kunne suna jiran jin me zai ce da su, ita kanta Chuchu ta fahimci
uncle Abbas ya shiga damuwa a wanna tambaya da Jawad ya yi mashi.

"Rizwan ne ya sami dad ɗinku ɗazun da safe ya sanar da shi a ɗaura aurenka da
Jannat ba da shi ba".

Zaro idanunsu a tare suka yi, they will not expect that at all, so they shocked.

"Dama Yah Rizwan yasan ina son Jannat ne ko dai kai ka gaya mashi daddy?".
Jawad ya yi tambayar cikin ƙaguwa da san jin an warware masu komai dallah dallah!.

Girgiza kai uncle Abbas ya yi, sannan ya ɗaura da cewa.
"Ko ɗaya babu wanda ya gayawa Rizwan kana son Jannat, shi da kansa ya san da
hakan?".

Sam Jawad bai san lokacin da ya furta. "How and when?". Ba.

"Lokacin da ya sanar da dad ɗinku ya sadaukar da soyayyarsa wa kai sai ya wuce
room ɗinsa ya je ya fara haɗa kayansa zai koma Dubai, a time ɗin dad ɗinku ya
kirani a waya ya ce dik in da nike na zo yana son ganina".

"Ban ɓata lokaci wajen zuwa in da yake ba, na same shi a room ɗinsa, I was so
surprised time da ya gaya mun furucin Rizwan a kanku, ban iya haɗiye abin a raina
ba sai da na bi Rizwan ɗakinsa dan na ji meyasa ya yi hakan".

"A lokacin da na shiga ɗakin nasa ya gama shirya echolac ɗinsa domin tafiya, ni
na dakatar da shi na kuma umarcesa da ya zauna mu yi magana. Bai yi mun musu ba, ya
zauna.
Da kallo ɗaya na yi mashi na fahimci ya sha kuka sosai, dan ga idanunsa har
sun kumbura, ban nuna mashi kamar na gane yana cikin damuwa or ya sha kuka ba, na
yi amfani da fifikon dake tsakaninmu na tambaye shi cikin hikima".

========================😥

"Rizwan meyasa kace ka barwa ɗan uwanka Jannat ya aura?".

"Babu komai daddy, naga hakan shi ne yafi dacewa da ni ne!".
Ya yi maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa, baya san su haɗa ido da uncle
Abbas, dan baya san ya gane yana cikin tashin hankalin da ba zai iya ɗauka ba a
dalilin sadaukar da soyayyar tasa da ya yi.

"Ko zaka ɓoyewa kowa Rizwan bai kamata ni ka ɓoye mun na, shin ka manta nine
daddynku ne?".

Girgi kai ya yi alamar a'a bai manta ba.
"To ka gaya mun meyasa ka sadaukar da soyayyarka ga Jawad? Shin ya ce maka yana son
Jannat ne?".

Girgiza kai ya sake yi a karo na biyu, kamar zai rushe da kuka ya ce.
"Babu wanda ya gaya mun Jawad yana san Jannat a baya, da idanuna naga hakan,
sannan kuma Auta ta tabbatar mun da hakan, har ɗakin nan ta zo ta gaya mun cewa
Jawad yana san Jannat tun tana ƙarama, ta nuna mun video da hotunansu a wayarta a
lokacin da suke

Please Login or Register in order to submit comment