Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 84 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiyasa ya
cire kamar yadda a baya Jaish ya cire ya canza mata.

"Allah ya yi maka albarka". Shi ne abin da ta faɗa kafin ta miƙe ta nufi waje. Da
kallo ya bita yana jin wani irin kaunarta tana kara narka zuciyarsa, yana san
mahaifiyar nan tasa over!.

Komawa ya yi ya kwanta shiru yana cigaba da kallon hotonta. Kamar daga sama ta
witsiyar ido ya ga alamar mutum a tsaye a tsakiyar ɗakin. A hanzarce ya juyo da
kallansa. Ɗan binta da kallo ya yi kafin gently ya ce. "Wai ke baki iya sallama
bane?". Ya yi maganar kallansa a kanta cak. Turo mashi baki ta yi. "A ina zan ajiye
maka abinci ya yi mun nauyi sosai a hannu". A maimakon ta bashi amsa sai ta faɗi
abin da take da buƙata.

"Ina Jaish da nace ya kawo mun abincin?". Ya tambaya yana wurga mata harara......
Shiru bata amsa mashi ba, dan tana ganin bata da alaƙa da wannan tambayar tin da
ita bata ma san wanene Jaish ɗin ba, kawai momma ta shiryata ta ce ta kawo mashi
abinci.... Ganin ta yi shiru yasa ya fahimci nufinta, yanzu yana iya karantar
shirunta sosai. Kai Pretty duniya, wato tana bawa Smart sabon karatu. Bin kayan
jikinta da kallo ya yi, a ransa ya ce dik yadda aka yi momma ta sanyata saka wannan
kaya, arabian abaya ce mai shegen kyau launin dark purple, ta yi masifar kyau
sosai, sai dai kan nan dai babu ɗankwali, ta saki gashi har baya. A ransa ya ce
shegen kyan bala'i ne da ita, kowani irin dressing ta yi kyau yake yi mata tamkar
dan ita aka yi kayan! Ya zauna a jijinta zam zama har sai ka ji sha'awar irin
dressing ɗin a ranka.

Ganin ya yi shiru yana bin jikinta da kallo ne yasa ta dongwarar mashi da try ɗin
abincin a tsakiyar bedroom ɗin, a cewarta tin da ba zai faɗi in da za'a ajiye mashi
ba ai tana da damar ajiyewa a ko'ina tin da ba shi ya bata hannun nata ba da zata
tsaya tana rike da abincinsa tsawon lokaci, ga shegen nauyin tsiya, dama da kyar ta
ɗauko shi, ba dan Momma da Allah ba zata ɗauko ba!.

"Ke zonan!". Ya faɗa with harsh voice, wai irin ta san ba da wasa yake yi ba, ta
tsorata ta zo. Banza da shi ta yi tana cigaba da tafiyarta zata fita. Dab zata fita
sai ji ta yi an damko gashin kanta ta baya. Wani irin kara ta saka mashi saboda
zafi tare da juyowa da sauri. Angry face ɗinsa a ɗaure tamau, in a harsh voice ya
ce. "Ina kiranki kina tafiya ni sha'anki ne?". Ya yi maganar ba tare da ya saki
gashin nata ba.

Tana turo baki tana yamutse fuska saboda zafin damkar gashin nata da ya yi ta ce.
"Ai ke na ji ka ce ta zo ba ni ba, ni sunana Pretty, da Pretty ka ce da na tsaya ko
ban zo ba". Kam bala'i, lallai Pretty ƴar duniya ce......... 😅

Rasa abin faɗe ya yi, dan wlh idan ya biyewa yarinyar nan mari ɗaya zai yi mata ta
mutu........... "Ni ka sake mun gashi kada ka cire mun su, zafi yake mun".
Shagwaɓaɓɓiyar voice ɗinta ta daki dodan kunnensa. Ɗan sauko da kallonsa a kanta ya
yi, da karfi ya sake jan gashin nata baya dan mugunta. Hakan yasa ta ɗaga kanta
sama dan dole. Ɗago kanta yasa ya kalli face ɗinta a kurkusa, har cikin zuciyarsa
ya ji wani iri na ganin kwayar idanunta, ga idanun fari tas tamkar audiga, kwayar
olive ɗin kuma ya tura kala sosai, pink lips ɗinta ya tura sosai shi ma, dik yadda
aka yi bata jima da yin wanka ba, soft skin ɗinta sai sheki yake yi yana wani
glowing. Yaran nan Sweetie and Pretty sun mori jiki sosai, shape ɗinsu tamkar su
suka yi wa kansu!

Ya shagala da kallanta sai ji ya yi ta gabza mashi cizo a hannu, wai dan ya ja mata
gashi ta ji azaba sai ta kama ɗayan hannunsa ta gabza mashi cizo da karfi kuma taki
sake fatar, sai kara datsewa take yi da hakwaranta. Zuba mata idanu ya yi yana
kallanta ba tare da ya saketa ba, tinanin abin da zai yi mata yake yi, dan dole ya
hukuntata!.

Da taga cizon kamar bai wadatar ba, bai saka shi ya sakin mata gashi ba, sai ta
sake shi haɗe da dunkule ƴan hannayenta da basu wuce ya kama ya karya ba ta fara
kai mashi duka a damatsan hannunsa. Abin ma gwanin ban dariya, wai ita nan dukansa
take yi dan ya ji zafi ya saketa, bayan hannun nata ba auki kamar sandan snooker.
Siririn tsaki ya ja kafin ya sa hannu ɗaya ya ɗagata cancak kamar ƴar tsana ya
wurga a saman bed ɗinsa kamar wata kayan wanki. Tana ƙoƙarin miƙewa ya daka mata
tsawa a kan ta zauna. Ai ina bata tsoron tsawar tasa, dan haka ta yi tashinta, yana
tsaye ta zo ta wucesa zata fita.
Juyowa ya yi yana kallan yadda take tafiya ko a jikinta, yau ta goge mashi hadda,
wai me zai yi wa yarinyar nan ne ta fara jin tsoronsa? Shi kowa a gidan nan yana
tsoronsa amma ban da yarinyar nan, ita dik wasu tsawa da hargagi game da jan ido
dik bata tsoransu. Ganin zata fice daga ɗakin ba tare da ya hukuntata bane yasa ya
ce. "Yauwa my tiger come in.......".

Ai bai gama rufe baki ba ta watso a miliyan ta juyo, ihu ta zunduma tare da ɗale
jikinsa, ta ƙanƙame shi gam tana faɗin. "Dan Allah Yah Omerish ka ce kada ya shigo,
wlh cinyeni zai yi"...... Mamaki ne ya kama shi, ashe tasan sunansa Yah Omerish
kenan, wato dama iskanci ne ya yi mata yawa a kai kenan? Wannan yarinya wlh sai
shirin Allah, shi ya rasa ma me zai ce mata, ta wani ƙanƙame shi, wato dai bata
tsoron mutane sai dabbobi, yanzu ya gane me zai rinƙa yi mata, dole ya ɗauko
abubuwan tsoro ya kawo nan dan ta rinƙa respecting ɗinsa idan tana san zaman
lafiya.

Ihun da take ta zundumawa ne ya farkar da shi daga duniyar tinanin da ya afka. A
ɗan tsawace ya ce. "Sauka mun daga jiki ki je Tiger na jiranki a bakin kofar
shigowa, ba ke bakyaji ba?". Kara ƙanƙame shi ta yi tana cusa kanta a kirjinsa ta
ce. "Yah Omerish wlh ina jin magana, dan Allah ka ce ya tafi, wlh ba zan sake ba".
Bilhakki da gaskiya take ihun nata!!.

"Kin yi alkawarin zaki rinƙa jin magana idan aka yi?". Kai ta shiga gyaɗa mashi
da sauri sauri, tana faɗin ta yi. Hannu yasa ya rungumota a jikinsa sosai ya fara
faɗin. "To ki yi shiru ihun ya isa haka kada ki tara mana jama'a, zo ki zauna mu ci
abincin a tare". Kin sake shi ta yi, sai dai ta dakata da zunduma ihun, cikin
shesshekar kuka ta ce. "To ka ce kada Tigern ya shigo ka ji?". Yadda ta yi maganar
har cikin zuciyarsa ta ratsa shi, ga shagwaɓa ga muryar kuka, abin sai ya haɗe.
Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "To ba zai shigo ba, amma idan kina ihu zai shigo ne,
sakeni mu je ki ci abinci". Wato shi ma yasan ita sarkin son abinci ne fa!.

Ba musu ta sakesa tana shessheƙa. In short a tare suka ci abincin, kuma wunin ranar
a bedroom ɗinsa ta wuni har dare, taki fitowa wai kada Tiger ya kamata, shi kuma
yaki zuwa ya je ya rakata, dan bashi da matsala na zamanta a bedroom ɗin, tana ma
ɗebe mashi kewa ne, da rana ta yi sanyi ma hayewa saman bed ɗinsa ta yi a kusa da
shi ta kwanta, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.

--------------------------------------🔥

A takaice tsawon sati biyu Auta tana jinya, ban da uhm da mmm babu abin da take
cewa, tana kwance shiru a wannan part ɗin, Abdussalam sai ƙoƙarin shiga ziciyarta
yake yi ta hanyar zuba mata kalamai masu sanyi da tausasawa game da kulawa, amma
dik taki kula shi, sai ma layi da ya shata mashi a kan kada ya kuskura ya matso
kusa da bed ɗinta, bai yi mamaki ba, dan yana tinanin zafin ciwo ne, shi kwata
kwata bai san da batun soyayyarta ba, wlh da ya sani ko kaɗan ba zai taɓa yarda su
yi aure ba, yana san farincikinta sosai, so bai sani ba, ya zaci kawai bata son ayi
mata aure a yanzu ne, shiyasa idan ya zo wajenta yake yawan ce mata kada ta damu
shi zai iya barinta har ta kammala karatunta kafin su yi zaman aure, dan hankalinta
ya kwnata har ce mata yake yi zai iya barinta a kingdom of power cikin ƴan uwanta
ya koma Dubai, dik dan ta samu farinciki, amma ina, ita dik ba wannan ne a gabanta
ba, hankalinta ya yi nisa, wai a haka ma bata san Hoorain ya mutu ba, ta yi
alkawarin babu wani namijin da zata mallakawa jikinta, a cewarta zata yi ta
avoiding ɗin Yah Abdussalam har ya gaji ya sawwaƙe mata ta kawo kanta ga Hoorain
ɗinta, ta ci alwashin in dai Hoorain bai sameta ba, to tabbas kashe kanta zata yi,
dan jikinta mallakinsa ne, ta yi mashi wannan alkawarin tin tana France. Ya kuke
tinanin zata ji idan ta san ya mutu? Anya ita ma zata rayu kuwa?!.

A ɓangaren Smart kuwa, wlh yadda kuka san baya gidan, kuma dik abin da yake faruwa
yana sane, amma bai shiga harkarsu ba, ya zuba ido, sai dai kuma kamar akwai abin
da yake shiryawa daddyn nasu, dan ya ɗaukarwa kansa alkawari idan King ya yi
sanadiyar mutuwar Zunaira to tabbas wlh ba zai rabu da shi ba, kuma ya san in dai
tasan Hoorain ya mutu da wuya ta tsallake ita ma. Uhm akwai cakwakiya fa!!.

Cigaba da rayuwarsa Smart ya yi, sai kiransa daddynsa yake yi yana cewa ya
dawo, amma sam babu alamar komawa, dan ya ce ba zai bar kingdom of power ba har sai
ya gyara masu zama, azumi ta iso, Momma zata je Dubai gaisuwar azumi, sai ana gobe
za'a ɗauki azumi zata dawo, to shi ne abin da Smart yake jira, so yake yi momma ta
tafi, sannan su yi uwar watsin da za'ayi, kunga bata nan bare ranta ya ɓaci ya ji
babu daɗi!!.

Uhm Zunaira ta shafe two weeks a saman gadan jinya ba tare da sanin Hoorain baya
raye ba, tana nan tana tattalin soyayyarsa a cikin zuciyarta, ta yi mashi ginin da
babu mai iya rusa mata!! Kullum tana kan ƙoƙari kara yawan son nasa a ranta!! Ba ci
ba sha, dik ya rame ta lalace fiye da tinanin kai tinani, bata da wani walwala,
wannan ma wai dan su Chuchu sun ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali, wlh shi kansa
King tsoron zuwa dubata yake yi, saboda yadda ta rame bata a cikin hayyacinta, abin
ya yi mugu mugun taɓa shi, sai dare yake zuwa dubata, har a yanzu yana ganin kamar
idan aka ja lokaci kaɗan zata miƙa wuya ta hakura, shiyasa bai fara nadama ba, ban
ji kamar bai kyauta ba, ya cigaba da tinanin dik in da aka yi one month zata mance
da komai ta fara sabuwar rayuwa da Abdussalam. Uhm akwai cakwakiya sosai!.

Shi kuma commander har aka yi jana'izar Hoorain aka binnesa ba tare da ya gana da
shi na karshe ba, dan bai yarda da ya mutu ba, shi yana ganin ɗansa. Auta ta yi ta
yi su kaita ta ga Smart, amma sun ki, sun ce mata baya nan, dan King yasan
haɗuwarta da Smart ba zai yi mashi kyau ba, ta yi ta yi su bata waya ta yi kira nan
ma abin ya ci tura, King ya gargaɗi kowannensu da kada su kuskura su baiwa Zunaira
waya, su kyale ta har a samu ta samu lafiya ta mance da wani Hoorain, ya ce a barta
sai ta fara sabuwar rayuwa da Abdussalam ta nisa sai a faɗa mata Hoorain ya rasu a
wannan lokaci ba zata damu sosai ba. Uhm King yana ganin cewa soyayyar yarinta ce
kawai Auta take yi, bai san abin ba haka bane, ya sha gaban yarinta King!!. Mu je
dai zuwa, lokaci ne zai banbanta maka da cewa soyayyar yarinta Auta take yi ko kuwa
na gaskiya!!!.

-----------------------------------------🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥🔥

Fito da Leesharh suka yi da nufin su tafi da ita, tsabar rashin imani ma gashin
kanta suka damko suna janta da shi. Dai'dai zasu gifta shi in da yake kwance yasa
hannu ya damki kafar wanda ya riketa ɗin, da karfi ya yi wurgi da shi tare da
miƙawa tsaye a kan ƙafafunsa.

A take suka saki Leesharh suna kallonsa da mamaki, ba su yi zaton zai miƙe ba. Wlh
bibbiyu yake kallonsu saboda wani irin jiri dake ɗibarsa, ba karya sun buga mashi
karfen sosai a kai. Haka ya daure ya rike kansa yana binsu da kallo, so yake yi ya
san su waye su? Ya cire mask dake fuskokinsu ya gani.

Wanda ya rike da light ɗin ne ya ɗaure wutar a saman stair case, hakan yasa haske
sosai ya baibaye wajen, suna iya ganin juna yadda yakamata........ "Ku kashesa, dik
da baya daga cikin waɗan da aka bamu aiki a kansa, amma ya zame mana maciji a bakin
kofar wucewarmu, dan haka ku kashesa mu samu hanyar wucewa". Ogan nasu my light ne
ya yi maganar. Masu nikaf ma a yanzu basu san Ramish ne yake tare da Leesharh ba,
dan suna tinanin ita kaɗai ya zo ya ɓoye a gidan sai masu tsaronta, shiyasa suka
bada wannan aiki na a dauko Leesharh kawai, da sun san Ramish yana gidan zasu bada
aikin a kashe shi a ɗaukota ne!!

Lokaci guda wani murmmunar faɗuwar gaba ta dira zuciyar Ramish, domin kuwa voice
ɗin nan ta yi mashi kama da wanda idan shi ne lallai zuciyarsa ba zata iya ɗauka
ba.
Cike da karɓar umarni suka nufosa gadan gadan, dama su biyar ne. Dik da halin da
yake ciki haka ya daure suka fara kokawa. Kuka sosai Leesharh take yi tana tari mai
sauti saboda tashin hankali........ Suna fara faɗa ya ji wani karfi ya zo mashi,
Allah ya taimakesa ya jibgesu sosai har suka fara gudu da kafafunsu. Nan fa ya bi
su suka sauka ƙasa parlour kenan, suna gudu yana binsu, yana san kama mutum ɗaya ne
ya cire mashi mask ya ga su wanenen.

Har suka fita wajen gidan, dik bai dai'na binsu ba, gudun cetar ransu suke yi.
Dai'dai zasu sha kwana ya kama ogan nasu ta baya, kokawa suka fara yi a in da Allah
ya bashi nasarar cire mashi mask ɗin nasa. Yana cire mashi kuma guy ɗin ya kwace
kansa yana ƙoƙarin gudu, sai dai ya juyo kafin ya gudu, kuma juyowan nasa ne yasa
Ramish ya yi mutuwar tsaye yana kallansa ya kasa iya cigaba da binsu.

Wani irin zaro idanu ya yi yana kallonsu suna gudu, muryarsa na rawa ya furta.
"RAJ". Girgiza kai ya shiga yi yana faɗin. "No ba Raj ba ne, wlh ba shi bane, kawai
idona ne, tabbas bana gani da kyau". Wani irin jiri da ya ɗebesa ne yasa ya zube
gwiwowinsa a kasa a wajen yana cigaba da sambatun cewa wannan ba Dr Raj kaninsa
bane!!!!. Tabbas Dr Raj ya gani, haƙiƙa ba karya idanunsa suke yi mashi ba!!
Innalilahi wa inna ilahir rajiun

Tashin hankali!! Wai ni Teema mafarki nike yi ne ko gaskiya? Da sanya hannu Dr Raj
a masu san ganin bayansa ko kuma dai wani dalilin yasa yake tare da sh?. Kai
kaninsa ne fa! Kenan da Dr Raj da Bilal tafiyarsu ɗaya? How? Ko dai Dr Raj ba ɗan
mama bane? Kai akwai rikitarwa wannan lamari, ya Ramish zai yi ransa? Innalilahi wa
inna ilahir rajiun!!! Wannan shi ne ainahin tashin hankali.

Special na ce yau zan baku page mai sauki sauki ko? To ga shi nan da sauki saukinsa
😅ku karanta ƙwaƙwalwa ta ƙara ɗaukar wuta, ina ga page na yau ma ya fi na jiya
tsanani 😥😅 to ina masu chorry🤓

Kada ku damu, zan baku update da zan ɗan saukaka maku a cikin satin nan.🥱 Mun iso
INTERMISSION ne, dole komai ya ɗauki zafi, akwai kwayayen da zasu fashe soon!! Ku
dai ku cigaba da bibiya, kun san bana yin abu sai da kwakkwarar dalili ko? To zaku
ji dalilin soon. By much love 💘 🔥


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️
‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S



55



Ramish ya jima a wajen sosai kafin ya iya yunƙurawa ya miƙe tsaye, jiri yana cigaba
da ɗibansa. Kasa iya juyawa ya koma ya yi, sai ya tsaya cak yana tinani, kansa ya
kulle, abubuwa sun cakuɗe mashi. Shessheƙar kuka da ya ji daga bayansa ne ya sanya
shi yin gaggawar juyowa. Tsaye take tana haki tana kuma shessheƙar kuka mai ratsa
zuciya, kasa hakuri ta zauna a cikin gidan ta yi, shi ne ta fito da gudu ta bi
bayansa, hankalinta a tsananin tashe, fargabarta ɗaya shi ne kada su ci galaba a
kansa.

Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da ya ganta, ta ɗan duƙa tana haki sama sama.
Hannayensa ya buɗe mata alamar ta zo, babu musu ta ruga da gudu ta faɗa jikinsa
tana sake fashewa da kuka, tsananin tsoro ne kwance a cikin idanunta, ya lura da
hakan shiyasa ya ce ta zo garesa ko zata ɗan sassauta.

Tattara dik sauran karfin da suka rage mashi ya yi ya ɗauketa cak, dan
tsayuwarsu a waje babban haɗari ne, they have to be enter in. Ta fahimci yana cikin
tsananin damuwa, dan haka sai ta ɗago da kansa daga saman kirjinsa, ɗan zuba mashi
idanu ta yi yana tafiya kafin tasa hannunta dake ta faman kerma ta ɗan shafi face
ɗinsa. "Yah Ramish sun ji maka ciwo ne?". A ruɗe ta yi maganar. Hakan yasa ya dawo
da kallonsa a kanta. Kai ya ɗan girgiza mata alamar a'a ba tare da ya yi magana
ba!! Wani irin yawu mai wuyar wucewa ta haɗiya game da sauke ajiyar zuciya.
Da kyar ya iya nufar ciki da ita. Unguwar so sillent sosai.

Suna shiga ciki ya fito da wayarsa bayan ya sauketa a tsakiyar bedroom ɗinsa, kunna
wayar ya yi, emagemcy number na masu gyaran wuta ya kira tare da sanar da su
buƙatarsa, sannan ya katse kiran. Wani zuciya ce ta ce mashi ya kira Smart ya sanar
da shi halin da yake ciki ko zai samu sauki a ransa, dan gabaɗaya zuciyarsa ta
zanto tamkar an ɗaura garwashin wuta a kai. Idan har da gaske ya san Dr Raj, to ba
shakka shi ne wanda ya gani a yanzu!! Kamar zai kira Dr Raj ɗin ma, sai kuma ya
fasa, tinanika kala kala ne sosai a ransa. Ita kuma tana tsaye a kusa da shi, a
dai'dai wannan lokaci aka dawo da wutar gidan, masu gyaran wuta har sun iso sun
gyara.

Gaban mirror ya nufa, face ɗinsa ya zubawa idanu yana kallan kansa. Lokaci guda
gabansa ya yi wani irin mummunar faɗuwa sakamakon wani tinani da ya yi, wayarsa ya
kawo face ɗinsa, number mamansa ya fara kira ba tare da ya duba time ba. Bugu ɗaya
ta ɗaga, ɗan gyaran murya ya ɗan yi kafin ya yi mata sallama.

Tana daga kwance a saman katafaren bed ɗinta bata san time da ta miƙe ba jin
muryarsa wani irin, cike da tsananin tsoron kada ace wani abin ne ya same shi ta
amsa sallamar tare da tambayarsa ko lafiya yake?. Nisawa ya yi kafin ya ce.
"Lafiya lou mama, aiki na sha na gaji". Wani irin ajiyar zuciya da ta sauke sai da
ya jiyota, alhamdulillah ta furta sau uku a jere tana ɗan rintse idanu.

"Mama menene ratar dake a tsakaninmu da Raj? And Mama kada ki ɗauki tambayata da
wata manufa please ke kika haifeni da gaske?".......... Ai bata san lokacin da
numfashinta ya ɗan dakata na ƴan dakiku ba, zaro idanu sosai ta yi, lokaci guda ta
rikice. "Ramish wani irin tambaya ce wannan kuma?". Ta yi maganar word ɗinta suna
harhaɗewa........... "Mama ai dama na ce kada ki ɗauki tambayata da wata manufa,
kawai na yi ta ne ba dan wani abin ba sai dai ina san sani".

"Wallahi billahi ni na haifeka Ramish, meyasa kake tantama?!!". Daga yadda ta yi
maganar ya fahimci da iya gaskiyarta ta yi, dan haka ita ta haifesa, sai dai idan
Dr Raj ne ba ɗanta ba, dole akwai wata a ƙasa. "To mama Raj..........." Ƙasa ƙarisa
tambayar ya yi, dama zai tambayeta ita ta haifi Dr Raj ne, sai kuma ya tina yanzu
zata iya zargan wani abu, shi kuma bayan Smart baya san kowa yasan abin da yake
faruwa bare har su ɗaga hankalinsu haka, ta haka ne kawai zai iya cin nasara a
aikinsa, rufe sirrinka shi ke kaika ga nasara, and kuma ya tina yana da jinin Dr
Raj a bedroom ɗinsa a gidan Abu Abdussalam, yana nan a ma'adanarsu na gwaje-gwajen
lafiya, ya taɓa gwada shi a lokacin da ya yi wani ciwo, a lokacin sun tsorata
sosai, sai suke ga kamar yana shan miyagun kwayoyi shiyasa suka yi mashi gwaje-
gwaje sosai shi da Bilal.

Tina yana da jinin yasa ya fasa yi mata tambayar tare da kawar da zancen zuwa
zancen gidan da abubuwan da suke faruwa, a zuwan zai je gobe ya ɗauko jinin ya zo
ya gwada ya gwada nasa sai ya tabbatar, ya so ma da ya samu jinin mamar tasu, dan
ya kara samun tabbaci, lallai da wuya ne idan Dr Raj ɗanta ne, akwai dai wata a
ƙasa.

Zama a gefen bed Leesharh ta yi tana ta kallansa yadda yake waya da mamarsa a
natse. Bayan ya kammala ya katse kiran, zubawa kansa ido ya yi yana tinanin kalaman
yayansu, wato Smart, a kullum yana faɗa mashi kada ya yi saurin yanke hukunci a
aiki, ya koyi hakuri da danne abubuwa game da zurfafa bincike, ya zamana mai
tsananta bincike da rufe sirrin dik abin da yake yi, shiru ita ce babban makaminsu
a matsayinsu na jami'ai, idan yana zargin na kusa da shi, kada ya kuskura ya bari
su iya gane yana zarginsu, ya yi masu sillent walk wajen kamasu, ya barsu su cigaba
da rayuwa da shi kamar yadda suke a baya, amma shi yasan irin takunsa a kansu, yana
lallaɓawa wajen bincike a natse ta yadda zai haɗa hujjojin da idan ya yi masu kamu
ɗaya ba zasu sake dawowa ba!!.

Tuna waɗan nan kalamai na Smart yasa shi sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da
furta alhamdulillah. Yana furta hakan ya ji sanyi ta ratsa zuciyarsa, a hankali ya
ɗago da kallansa a kanta ta cikin mirror, while ita ma shi take kallah, zubawa juna
idanu na ƴan mintuna suka yi, ta shagala da kallan kyansa sai jin sexy voice ɗinsa
ta yi ya ce. "Zaki iya bani haɗin kai a yanzu dan mu iya kamasu?".

Kai ta gyaɗa mashi alamar e, dan yanzu ta fara tsorata da al'amarin mutanen nan,
kuma ita suke hari sosai, dan sun san ta iya ganesu, idan basu gaggauta kawar da
ita ba zata tona asirinsu, ai kun san da suna ganin kamar bata da hujjar nunasu ko
da an kamata ne, shiyasa suka saki jiki, amma sai suka ga ba haka bane, kuma ita ma
Leesharh ta yi babban kuskure! Domin ba'a nunawa mutane irin wannan cewa ansan wani
abu a kansu ko kuma za'a iya fito na fito da su, kun tuna lokacin da suka kirata
tana gidan Abbie?. Ba ta ce masu tana da hujoji a kansu har da recoding ba? To
wannan shi ne babban kuskuren da ta tabka, da ta yi shiru bata sanar da su cewa
tasan wani abin ba, da wlh ba zasu nemi rayuwarta har haka ba....... Ku ɗauki
darasi a nan, kuskure ne faɗawa wani abokin faɗa naka cewa kasan wani abin a
tattare da shi wai dan ka yi mashi barazana, idan har baya san wannan abin ya fita
a duniya to tabbas zai iya cutar da kai koma ya yi ƙoƙarin kawar da kai wa duniya,
ba a iya labari ba, a gaske ma ya fi faruwa! Kowa ya iya harshensa, sai dai a ga
komai a aikace kamar yadda Smart ya bawa Ramish shawara! Kuma kamar yadda Smart ɗin
yake yi! Kun taɓa jin ya faɗi shirinsa wa wani ne? Ai sai dai ku gansa a aikace
kawai!!.

"Bari in yi wanka in zo sai mu fara aiki ko?". Ya faɗa yana kallanta. Jinjina
mashi kai ta yi. Toilet ya nufa, har zai shiga kuma sai ya tina da dattijuwar dake
gidan, wani zuciya ce ya ce mashi ya je ya dubata, wani kuma ya ce to ya bari sai
ya yi wanka, hakan kuwa aka yi, ya ce bari ya yi wanka ya fito. Yana shiga toilet
Leesharh ta miƙe ita ma, dik da a tsananin tsorace da gidan take hakan bai hana ta
daure

Please Login or Register in order to submit comment