Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 31 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah sarki taga duniya, ta rasa da
wanne zata fara, yunwa take ji over, dan ma Allah yasa ita ba wawiya bace, da ɗan
wayewarta, amma dik da haka sai da ta yi kauyanci a ɓoye, dan kuma kun san zaren ba
kalar yadin bane.

Dikkansu babu wanda fuskarsa bai nuna alamar mamaki ba a lokacin da uncle Jahiz ya
gama basu wannan labari da ya ɗauko ɗan sanar da su su wacece Zee, a fili momma ta
furta.
"Dikka wannan zalincin su kaɗai?".

Jinjina masu kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Aunty MieMie da ranta ya gama
ɓaci har idanunta sun kaɗa sun yi jajir ne ta ce. "Gaskiya ba zata saƙu ba, dole mu
kwatar masu ƴancinsu".

Jinjina kai momma ta yi alamar tabbas kuwa. Shi ma jinjina kai ya yi alamar haka
ne. Da alama labarin tarihin su Zee ɗin ya basu, dan tabbas ya lallaɓa Zee a
asibiti, ya gwada mata fifikon shekaru a in da ya yi mata dabara har ta yarda ta
bashi tarihin rayuwarsu.

Amm kuma sai dai akwai wani abin da ya sanar da su momma bayan tarihin su Khadija
ɗin, dan yanayin mamakin da ya bayyana a kan fuskokinsu abu ne mai girma da ya fi
tarihin su Zee suka ji, dole akwai wani sirri da ya sanar da su wanda baya buƙatar
a ji........... Ni kam nace koma dai me ka sanar da su idan lokaci ya yi ruwan ta
yi tsami ni da my people's ai zamu ji ko? Sai kwan ta fashe In Sha Allah mun ji
komai ato, mu je dai zuwa.

"Gaskiya akwai azzalumai a duniya, yanzu ko ta ina zalinci kawai ake yi, ya ilahi
ya lillahi, wannan musifa dame ta yi kama". Cewar Momma da alamar jikinta a
sanyayye.

Ita ma Aunty MieMie ta yi laushi, kamar wanda ya sheka masu ruwan sanyi, dik da
alamar karyewar zuciya da tausayi a tattare da su.

"Uncle Jahiz taki cin abincin fa, ko zaka je ka yi mata dabara ta ci tun da kun
saba da ita". Cewar Aunty MieMie da ta farga da Zee bata cin abinci.

Miƙewa tsaye ya yi, ya nufi table ɗin yana faɗin. "Dama kullum sai mun kai ruwa
rana da ita take yarda ta ɗan tsakuri abincin ai, bari na gwada yanzu ma".

Momma ce ta karɓi zance da cewa. "Ai dole ne ta shiga damuwa Jahiz, amma In Sha
Allah damuwarta ya zo karshe, bari daddunsu ya sarara da musifar da muke ciki na
ɓatar Zunaira, tabbas za'a biwa yaran nan hakkinsu, sai mun tsaya masu In Sha
Allah".

Jinjina kai Aunty MieMie ta yi, kun san tana san jinin ƴan Nigeria ita, saboda
jinin mummynsu ne, dan haka ta kudurta a ranta wlh ba zata sarara ba a kan wannan
case na su Zee, sai ta ɗaukar masu fansa, kai jama'a jinin modarawa ake magana, su
da basa yafe ko harararsu ka yi........😅

Saman table chair dake kusa da ita ya zauna, su momma kuma suka miƙe izuwa cikin
bedroom ɗin momma dan su tattauna wani sirri nasu, momma tana mugun shiri da Aunty
MieMie sosai, ta su ta zo ɗaya, kun san sai hali ya zo ɗaya ake abota, batu na
Allah aunty MieMie mutuniyar kirkice number ɗaya.

Chinese fried rice ya zubawa Zee, sai kallan face ɗinta yake yi, ta yi ƙasa da kai
tana ɗan murza ƴan ƴatsun hannunta. Cikin harshen turanci ya ce da ita. "Bari in
baki abincin a baki to tin da ba zaki iya ci ba".

Da sauri ta girgiza mashi kai alamar bata buƙata.

"Baki san zuwa ki kalli Khadija ne?". Da sauri ta buɗi baki ta amsa da tana so. "To
in dai kina san zuwa wajen Khadija lallai ki ci abincin nan, idan kika ƙoshi sai in
kira Fanan ta kaiki ɗaki ki yi wanka sai in kai ki wajen Khadija".

Kamar zata yi kuka ta ce. "Zan ci ko dan in ga ƴar uwata, amma dan Allah ka faɗa
mun kasan Khadija ne? Ya kai sati kenan ina yi maka wannan tambayar sai ka ce mun
ni kaɗai ka sani baka san ta ba, nace maka a ina kasanni ni ɗin ka ce mun a
Nigeria, ka fayyace mun komai yadda zan fahimta kuma kaki". Da kyar ta iya karisa
maganar, saboda wani irin kwarjini da yake yi mata, kuma ita gaskiya abin yana
cinta a rai tana san samun amsa, tabbas ita hotonsa ta gani a hannun Khadija, wlh
ko ratsuwa ta yi ba zaga yi kaffara ba shi ne, sannan shi ma da ya ganta ya ce ta
yi mashi kama da wata da ya taɓa gani sai dai ya manta a ina, to da waye zata yi
kama idan ba Khadija ba?.

Bugu da kari shi da bakinsa ya ce babyn Khadija yana kama da shi, ga shi likitoci
sun hanasu ganin Khadija saboda condition da take ciki, an yi mata aiki a ciki
baiwar Allah, ashe matar nan da ta basu wajen zama a gidata a Abuja ita ta cucesu
lokacin haihuwar Khadija bai yi ba ta bata maganin tasar da naƙuda, dalilin haka
mahaifar Khadija ya tsage, sai da aka yi mata aiki yanzu, Allah ma yasa tana da
rabon shan ruwa a gaba, ai da ta jima da mutuwa saboda irin jinin da ta rasa, amma
Allah ya ƙaddara zata rayu.
"Zee ni har yau ban ga face ɗin Khadija ba bare in san nasanta ko ban santa
ba, sannan kuma na faɗa maki ke na sani kawai, ki ci abinci, likitoci sun ce mun
zuwa yamma zan samu damar ganin Khadija, idan muka je sai in ga ko na santa".

Shiru Zee ta ɗan yi, ita dai wlh tasan shi ne na jikin hoton nan, sai ma da ta
gansa a zahiri yanzu ta kara yarda, amma bari Khadija ta farfaɗo komai zai bayyana
ai.

Tana can tana duniyar tinani sai gani ta yi ya kawo mata abinci saitin ɗan bakinta.
Kai ta girgiza mashi alamar bata so, ta kai hannu ta karɓi spoon ɗin tana sunkuyar
da kai. Ta ƙasan ido take satar kallansa, Arabs jallabiya tana yi mashi mugun kyau.

A hankali ta fara cin abincin kamar tana tsoron taunawa kada hakwaranta su
karye, shi kuma ya zuba mata idanu yana kallanta, ji yake yi tamkar ya santa.

My people's me kuke tinani a wannan al'amari, wacece mai kama da Zee da ya sani?
Meyasa ya yi kama da babyn Khadija? Kada ku manta babyn Khadija korean ne, ko da
yake fa idan akwai jini wlh ba ta yadda ba zaka ga mutum ba, fata na dai Allah ya
tashi kafaɗun Akka, dan idan zarginmu ya tabbata babu wadda ta dace da yi mashi
hukunci sai Akka. (Ni ina da tantanama, anya uncle Jahiz ko ya gane Khadija zai
yarda ya nuna ya ganeta kuwa?🤔 Ya kuke tinanin wannan al'amari?)

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Luv Bird

Shi da ya sami abin da yake so, ai bai saki Chuchu ba sai da ita da kanta ta kwace
bakinta, a lokacin kuma ta gama kai shi ƙololuwa, dik ya rasa nitsuwarsa, idanunsa
a lumshe, jinsa a sama kawai yake yi, yana ƙoƙarin dakewa ya capki tula tulanta ta
yi saurin kwatar bakinta ta yunkura zata bar jikinsa.

Cikin magaggin soyayya da sha'awarta ya riƙota, kamar wani ɗan shaye shaye da kyar
ya furta. "My Jannawad ina zaki je?".

"Knocking na door fa na ji ana yi". Ta faɗa tana kallan zakarar wuyarsa, wato
wannan kashi nasu na maza, kashin ta miƙe sosai tana ɗan harbawa.

Sai da ta yi magana kunnuwansa suka tsinkayo mashi knocking da ake yi. Sake ta ya
yi ba dan ya so ba, da alama da mai buga wannan kofar ya ɗan kara masu ƴan mintuna
da Jawad ya yi disvirjin ɗinta, saboda ya luluƙa duniyar chaskale dayawa.

Da kyar ya iya miƙewa. Ƙasan bed ɗin ya sauko, jikinsa dik wani iri. Door ya nufa
yana ɗan layi. Ya ƙasa iya tambayar wanene saboda nauyi da tongue ɗinsa ya yi
mashi.

Da kallo Jannawad ta bisa tana jin wani irin kaunarsa a ranta yana kara ratsata.

Yana zuwa ya buɗe kofar babu tambaya. Duka Jaish ya kai mashi a kirji daga
buɗewarsa. Har sai da ya yi layi kamar zai faɗi, da kyar ya kama kansa tare da waro
idanunsa da kyau.

"Wani irin iskanci ne wannan? Na kai 5 mins tsaye ina dukan kofar nan, mema na
rufe kofar..........?". Bai kai karshen faɗar tasa ba idanunsa suka hango mashi
cikin ɗakin, Chuchu dake zaune a saman bed tana binsu da kallo.

Idan baku manta ba shi Jaish bai san Jawad ya yi aure ba, ya ɗebo zafin kansa kawai
zai zo ya sauke a kansu, ransa ne a matuƙar ɓace saboda momma ta same shi da safen
nan a kan batun Mahnoor matarsa ce, shi ne fa ransa yake ɓace, ya zo wajen Jawad
dan su tattauna wannan bala'in in jisa, shiyasa ya rinƙa dukar kofar da karfi.
Cike da mamaki ya dawo da kallonsa a kan Jawad ɗin, zaro idanu ya yi, shi da farko
ma bai lura da yanayin da ɗan uwan nasa yake a ciki ba, sai da yaga Chuchu zaune a
tsakiyar bed ne ya fahimci Jawad fa a cikin mayen sha'awa yake.

Wani irin bugawa ya ji kirjinsa ta yi, da karfi ya bugi kirjin Jawad har sai da
Jawad ya ji ya wastsake, cikin zafa ya danko wuyar rigarsa haɗe da daka mashi
tsawa.

"Me Jannat take yi a cikin ɗakinka har saman bed ɗinka da sanyin safiyar nan?
And wani irin shiga ce a jikinku?". Cikin lokaci ƙanƙani Jaish ya rikiɗe tamkar ba
shi ba, har wani huci yake yi, a tinaninsa sheke aya Jawad yake yi da kanwarsa, ga
shi ya gansu a wani irin yanayi.

Gyaran murya da uncle Abbas ya yi ta bayansu ne yasa suka yi saurin kai kallansu
a wajen. Da sauri Jaish ya ɗauke kansa daga kan kallan uncle ɗin nasa, domin kuwa
in dai abin da yake zargi Jawad yake aikatawa babu abin da zai ana shi yi mashi
hukunci mai tsanani yau, dama su a dokarsu dik wanda ya yi zina dandaƙa ake yi
mashi.

Chuchu da dama bala'in tsoron Jaish take yi tuni ya sha jinin jikinta, ta takure
waje guda jiki na kerma.

"My son sake shi, ba abin da kake zargi bane, Jannat matarsa ce, kai ne baka sani
ba". Cewar uncle Abbas da ya ji komai da Jaish ya faɗa, dan tun time da Jawad ya
buɗe kofar ya shigo cikin parlourn shi ma.

A miliyan Jaish ya juyo da kallansa a kan uncle Abbas. Jinjina kai uncle Abbas ya
yi alamar tabbatar da abin da ya faɗa. Kara zaro idanu Jaish ya yi. Da sauri ya
juyo ga Jawad.

Shi ma kai ya jinjina mashi alamar e haka. A wani irin slow Jaish ya zame hannunsa
daga wuyar rigar Jawad, like wow he was so surprised.

Uncle Abbas ne ya ce. "Jawad P.a ɗinka ne ya kirani wai yana ta kiranka baka
picking time na tashin jirginku ya kusa".

Da sauri Jawad ya juyar da kallansa izuwa cikin ɗakin, kan wayarsa ya sauke
kallansa, lallai kuwa soyayya ta yi daɗi, har ma anyi sallar asuba shi yana nan ya
afka wata duniyar.

Ɗan dafe kansa ya yi, babu ko kunyan daddyn nasa ya ce. "Sorry daddy, Jannat tasa
ban ji kiran ba, amma yanzu zamu shirya mu fito".

Jaish dai kamar ruwa ya cinyesa a wajen, faɗi yake yi a cikin ransa shikenan Jawad
ya gama yi mashi fata fata da mutumci a idanun kannensu, Jawad ya gama da shi ya ja
mashi kima a kan titi, yanzu shikenan Jannat tasan komai, gaskiya idan ya kyale
Jawad bai yi mashi hukunci ba ya cuce shi dayawa.

Uncle Abbas kuwa cewa ya yi. "Ina zaku je ne dama?".

Ɗan sunkuyar da kai na munafinci Jawad ya yi, sannan ya ce. "Daddy wai dama Jannat
ce ta ƙasa samun nitsuwa a nan, sai kuka take yi mun ta ƙasa barci, shi ne fa dama
zan ɗauketa mu je honeymoon a Dubai".

Da yake uncle Abbas ma ɗan zamani ne sai ya ce. "Yanzu kai Jawad ba zaka iya
kwantar mata da hankali a nan ba sai kun je Dubai?".

Shiru ya ɗan yi yana ƴan kame kame.
"Anya kai namiji ne kuwa?". Uncle Abbas ya sake jefa mashi tambaya. Nan ma dai
shiru ya yi.
"To ni ban yarda ku je ko'ina ba, ku na nan, idan baka iya kwantar mata da
hankali a nan na ga ɗan uwanka ya koya maka". Yana kai karshen maganar ya juya ya
fice abinsa.

Jaish ya gama zuwa har wuya, ɓacin rai kan ɓacin rai, sarai Jawad ya lura da shi,
shiyasa ya yi readyn guduwa, dan yasa saboda uncle Abbas yana wajen ne yasa Jaish
ɗin ya daure bai aiwatar da abin da ya yi niyya ba.

Tsabar tsakiyanci irin na Jawad, uncle Abbas na tafi ya dawo da kallansa a kan
Jaish, cike da neman tsokana ya ce. "Babban abokin ango kuma yaya babba zo mu je ka
gaisa da amarya, dama tana kewarka ai.........." Bai kai karshen maganar ba ya
yanka a miliyan ya fito waje saboda wani irin capka da Jaish ya kai masa a wuya,
Allah ya taimakesa ya zulle ya yo waje.

Da gudun gaske Jaish ya biyo bayansa, dan yau wlh ba zai kyalesa ba, ya zubar mashi
da mutunci, wannan ai iskanci ne, dama ga zafin ɓacin ran anki ƴar kauye Mahnoor
matsayin matarsa, sai ya haɗa dikka zai sauke a kan Jawad.................

Wayyo abubuwa sun haɗewa Jaish fa😅

Bari mu leƙa wani part mu dawo.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥 DUBAI🔥🔥🔥🔥

AFTER SOME WEEKS.

Zaune Sharifat take a saman bed, Leesharh na tsaye a wajen dressing mirror tana ɗan
gyara face ɗinta, har ta mayar da jikinta ta yi ɓulɓul abinta saboda kulawa na
musamman da ta samu daga Abbie, Yah Bilal, and Sharifat, sai ta yi saurin recovery.

Sanye take da riga da wando Pakistan mai bala'in kyau launin purple color. Ta gyara
gashin kanta, sai dai hannunta har yanzu bai gama warkewa sosai ba, sun koma kamar
yadda suke a da ita da Sharifat, suna kula da juna haɗe da nunawa juna soyayya.

Irin kayan jikin Leesharh shi ne a jikin Sharifat, sai dai ita nata maroon color
ne. Hira da guyson Sharifat take yi a Whatsapp a in da take faɗa mashi Obaid and
Omaid sun samu hutun karshen shekara suna gidan King Badeen, sun ki zuwa gidansu
sun ce Tunisia kawai zasu wuce.

Shi ma guyson kwance yake a saman bed ɗin momma daga shi sai Short, ya rungumo
pillow a kirjinsa yana aikin wannan sakalancin nasa da ya saba, shi kaɗai sai turo
baki yake yi.

Sun nitsa cikin hiran da suke yi wayar Leesharh dake kusa da Sharifat ya hau ƙara.

A razane Leesharh ta ɗago da kallanta a kan Sharifat ta cikin mirror, ita ma
Sharifat kai kallanta a kan wayar ta yi.

Private number ne yake kira, hakan yasa Sharifat ta dawo da kallanta a kan
Leesharh, cikin sauri kamar maras gaskiya ta kawar da kallanta tana ɗan kame kame.

"Leesharh wayarki na kara kuma private number ne". Cewar Sharifat.

Wani irin dum dum Leesharh ta ji kirjinta ya buga, domin kuwa ko bata ɗaga ba tasan
masu nikaf ne. Jiki ba kwari ta juyo ga Sharifat. Tamkar wadda kwai ya fashewa a
ciki haka ta nufo Sharifat. Wayar Sharifat ta ɗauko ta miƙa mata.

Tana karɓa wayar ya katse. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da
Sharifat ta ɗan yi mamaki. Kunna data Leesharh ta yi haɗe da shiga cikin Whatsapp
ɗinta.

Sakon Yah Bilal kawai ta gani a ciki har wajen massages guda biyar. Sake satar
kallan Sharifat ta yi, sai taga baiwar Allah ta mayar da hankalinta a kan hiran da
suke yi da guyson.

Buɗe sakon ta yi cikin sauri kamar wadda take kan gangara.

"Leesharh zaki bimu ne?". Sharifat ta katseta da jefa mata wannan tambaya. A
hanzarce ta fita daga kan mgs ɗin Bilal ta kashe wutar screen ɗin wayar, sannan ta
jingina bayanta da jinin stool.

"Ba lallai ba, amma Sharifat in tamnayeki dan Allah". Cewar Leesharh ɗin. Da
kallo ɗaya zaka yi wa idanunta kaga tsantsar rashin gaskiya da razana a cikinsu.

Dakatar da abin da take yi Sharifat ta yi, sannan ta bata hankalinta dikka.

"Sharifat dan Allah karin haske da karin ilimi zaki yi mun kin ji". Cikin raunin
murya ta yi maganar.

"Okey ba damuwa ina jinki". Ta yi maganar tare da ɗaura wayarta a saman pillow dake
kusa da ita.

"Labari zan baki sai ki yanke mun hukunci bisa ilimin addini kin ji?"..........
Jinjina kai Sharifat ta yi haɗe da cewa. "To ina sauraronki.

"Misali yanzu Shafiat wasu mata da miji masu halin kirki da dattaku ne suka
tsinci wata yarinya, tun tana jaririya cikin tsummarta suka tsinceta, suna riketa
tamkar ƴar cikinsu na tsawon shekaru biyar, matar nan ta yi mata komai na rayuwa,
haka shi ma mijin matar, ya ɗauketa tamkar ƴar cikinsa, ya nuna mata kauna fiye da
tinaninki, duniya dik ta ɗaukar ƴarsu ce, harta danginsu suna ganin matsayin yarsu,
Allah bai taɓa basu haihuwa na shiyasa suka cewa kowa ƴarsu, kuma basa kusa da
danginsu suna wata ƙasa ne, hakan yasa kowa ya yarda da ita ƴarsu ce".

Kara nitsuwa Sharifat ta yi dan jin wannan labari, kun san ta da san karance
karancen labarai.

"Lokacin da yarinyar ta kai shekaru biyar a duniya sai Allah ya karɓi ran wannan
mata tasa, hakan yasa ƴan uwansu suka ki tausayin wannan yarinya a in da suka ce to
ya auri kanwar wannan mata dan ya cigaba da rike ƴar ƴaruwanta kenan, haka kuwa aka
yi, wannan tsintacciyar yarinyar ta sake samu uwa a karo na biyu, to wannan uwar ce
ta riketa har yarinyar ta kai shekaru goma sha huɗu".

Sai jinjina kai Sharifat take yi labari ya fara sugar, har da cewa Leesharh ta
rinƙa rinƙa yin labarin da wuri please, dan so take ta ji komai da wuri.

Cigaba ta yi da cewa. "To dama wannan uwa ta biyu da yarinyar ta samu macece mai
masifar san kuɗi, dan haka bata zama, tana zuwa gidan larabawa ta yi masu aikatau,
suna bayanta kuɗi sosai, shi kuma wannan mijin yana sana'ar gasa nama ne a ƙasar da
suka je in da nace maki dama sun yi nisa da danginsu ɗin. Ana nan watarana wannan
mata ya ce zata fara tafiya da yarinyar nan gidan aikinta dan ta rinƙa tayata aiki,
mijin yaki yarda ya ce yarsa karatu take yi, matar ta tsayar da bala'i a kan lallai
dole wannan yarinya ta bat karatu ta rinƙa binta wajen aiki, dan yanzu kuɗi shi ne
mutum, babu abin da karatu yake tsinanawa mutum, in short wannan mata ta fi karfin
mijin ta yadda tasa dole ya yarda yar nan karatunta ya salwanta ta fara bin mamanta
neman kuɗi aikatau gidan larabawa".

"Rayuwarsu ya cigaba da tafiya a haka, suna shan wahala a gidan larabawa, amma haka
suke daurewa, sai watarana tsautsayi yasa mahaifiyar yarinyar nan ta zubawa wata
yar larabawa ruwan zafi a jiki by mistake, nan take uwar yarinyar ta fara dukan
mahaifiyar yarinyar, kuma a gaban yarinyar, sai hakuri yarinyar take bata amma taki
yarda, dukanta take yi da dik abin da ta samu, kuma wlh yarinyar ba wani konewa
sosai ta yi ba, amma haka ta rinƙa dukan uwar yarinyar, a garin ɗaukar abin duka
har ta ɗauki wuƙa ta cakawa mamar yarinyar a ciki".

Dai'dai lokacin da ta zo wannan point ɗin sai da idanunta suka ciko da kwallah, ita
kuma Sharifat wani irin zabura ta yi tare da zaro idanu, wannan wace iriyar
labarice.

Leesharh bata bata damar yin wani magana ba ta ɗaura da cewa. "Sosai wannan
balarabiya ta razana ganin ta cakawa matar wuƙa ta kuma faɗi ƙasa, hankalinta ya
tashi, ta rikice ta rasa ya zata yi, yarinyar matar kuma da ta ga komai yadda ya
faru, ita ma tashiga tashin hankali, hakan yasa ta juya zata gudu ta bar gidan ta
je ta kira mutane, haka babu tausayi babu imani wannan balarabiya ta kamata, ta
damka mata wukar da ta yi kisan a hannunta, sannan ta danneta ta saka mata wuta a
baki ta yadda yarinyar ba zata iya sake yin magana ba bare har ta faɗi ga abin da
ya faru, in takaice maki labari dai laifin kisa ya koma kan wannan yarinya a
matsayin ita ya kashe mahaifiyarta".

Idanun Sharifat ne suka ciko da kwallah, saboda labarin ya taɓa mata zuciya. Ita
kanta mai bada labarin hawaye take yi.

"A takaice haka aka kai wannan yarinya prison, an yanke mata hukuncin kisa amma
sai ta yi zaman prison ta jira lokacin da zata cika shekaru 18 kafin a kasheta. Ana
haka sai wasu mutane suka zo suka fitar da ita daga wanna gida na prison da sunan
zata yi masu wani aiki, yarinyar taki karɓar aikin saboda tana tsoron me zai je ya
dawo, sai suka ce mata ai taimako zata yi, wani za'a kashe zata taimaka mashi,
hakan yasa wannan yarinya ta yarda, ta karɓi sannan aiki".

Ƙara matsowa bakin bed Sharifat ta yi tana sharar kwallah, dik da bata san labarin
na gaske ne ko kirkirowa Leesharh ta yi ba abin ya yi mugun bata tausayi.

"In takaice maki labari dai sai wannan yarinya ta zo ta fara wannan aiki,
kwatsam sai ta fahimci amfani da ita ake yi a cutar da mutane bayin Allah, shi ne
sai ta yi ƙoƙarin bijirewa waɗan da suka sakata a aiki, ba zato ba tsammani suka yi
mata barazana da sun kama babanta da yake sana'ar gasa namarsa a bakin kasuwa, suka
ce dole ta yi wannan aiki idan bata yi ba kuma zasu kashe babanta, ni yanzu abin da
nike so ki faɗa mun a nan shi ne meyakamata wannan yarinya ta yi? Kada ki manta
babanta da ya yi mata komai a rayuwa, ya inganta rayuwarta ya zama gatanta shi ne
za'a kashe idan bata yi wannan aiki ba, sannan kuma aikin da zata yi cutar da
mutane zata yi, kai in taƙaice maki kashe mutum ma za'ayi amfani da ita ayi, me
kike tinanin yakamata ta yi?". Ta kai karshen maganar wani irin kuka mai tsuma
zuciya yana ƙoƙarin kubce mata.

Babbar magana, dik wanda ya fahimci wannan labari da Leesharh ta bayar a kan take
magana ya sarawa yarinyar nan, lallai ba shakka an cuci Leesharh sosai, ta sha
wahalar rayuwa, ashe ba da hakkinta aka kaita gidan AAJ ba ma, innalilahi wa inna
ilahir rajiun, kenan ba iyayenta na gaskiya bane ma take san taimakawa, to wacece
ita kenan? Ina iyayenta na gaskiya kuma suke? Meyasa aka jefar da ita har waɗan nan
suka tsinceta? Wani irin shawara kuke tinani Sharifat zata bata? Wani irin makoma
kuke yi mata tinani? Shin zata cigaba da yi wa masu nikaf aiki ko akasin hakan?
Tayaya zata kuɓuta daga sharrinsu? Kenan iyayenta cirani suka jo yi a Dubai wannan
iftilai ya afka mata? Lallai yakamata mu san labarin Leesharh dallah dallah da kuma
in da aka tsinceta! Akwai cakwakiya babba kuwa. Amma ba shakka anyi wasa da rayuwar
baiwar Allahn nan.

Haka kawai Sharifat ta tsinci kanta da jin cewa wannan labari da Leesharh ta bayar
gaske ne kuma kamar dai labarin yana da alaƙa da ita Leesharh ɗin duba da yadda
take kuka kamar ranta zai fita..... Ba dole ta yi kuka ba, an kashe mahaifiyarta a
gabanta, sannan an ɗaura mata laifi, bugu da kari ana sanya mata wuta a baki ta
yadda ba zata iya magana ba, lallai akwai zalinci matuƙa a wannan lamari, ancutar
da ita kwarai. Wai ya aka yi masu nikaf ma suka santa? Shi ma wannan babbar abin
tambaya ne. To koma dai me lokaci zai yi mana alkalanci.

Princess Teema taku ta amana bani da lafiya, da kyar na iya yi maku wannan update
ɗin dan kada na barku a cikin kewa, ku mun addu'a, idan kun samu typing errors ma
amin afuwa, zazzaɓi da ciwon kai ya sa na kasa iya ƙarisa editing ɗin.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




20



Ganin Sharifat tana hawaye kuma tana kallanta yasa ta ɗan yi iyaka ƙoƙarinta wajen
ganin ta dakatar da kukan nan da take yi, cikin raunin murya da kyar ta iya cewa.
"Labarin ya taɓa mun zuciya sosai Sharifat".
Sharifat zargi zuciyarta ya fara yi, dik san da take yi wa Leesharh hakan bai hana
ta fara ƙoƙarin gane gaskiya ba. Leesharh tana da kwakwalwa sosai, so ta fahimci
kamar kallan zargi Sharifat take yi mata, gudun kada asirinta ya tunu sai ta yi
saurin shanyewa, sannan ta kwarara zuciyarta.



Please Login or Register in order to submit comment