Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 35 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a yanzu". Cikin faɗa da ɗaga murya ta kai karshen maganar. Tana kaiwa karshe
kuma ta nufosa gadan gadan.

Ƙasa magana Abbie ya yi, ya ji bala'in da ta fi karfinsa a yau, sai ya ji abin
tamkar a mafarki.

Yana can yana tinanin sai gani ya yi ta yaye duv da ya lulluɓe Leesharh da shi
tana zazzaga masifar.
"Shegiya matsiyaciya, yanzu zaki fita daga gidan nan dan ubanki, karuwa kawai, dama
ai na jima ina zargin akwai wata a tsakaninku, ashe kuwa zargina gaskiya
ce........." Ƙasa karisa maganar ta yi sakamakon ganin Leesharh tsirara da ta yi
bayan ta yaye duv ɗin kenan.

Wani irin ihu ta kurma tare da ja baya. "Shikenan zancena ya tabbata, shikenan wlh
ya tabbata, da gaske ne zina suka aikata". Kamar wata zararriya haka take maganar,
ga shi cikin ɗaga murya.

Ganin zata tara masu family yasa ya daka mata tsawar ta yi mashi shiru. A
tinaninsa tana jin maganarsa tin da bai taɓa yin magana ta ce a'a ba, sai ya yi
tinani in ya yi tsawa zata yi shiru, bai san cewa a irin wannan point ɗin mata basu
da saiti sam sam ba.

Aikuwa yana daka mata tsawa ta daka uban tsalle kamar wata mahaukaciya sabon kamu,
ihu ta yi tare da wurgi da duv dake hannunta wanda ya rufe Leesharh, sannan ta haye
saman bed ɗin kan Leesharh, hannu tasa ta fara kaiwa Leesharh bugu babu tausayi ba
imani, tana dukanta tana aika mata da muggan zagi kala kala.

Leesharh da tuni dama ta sume ai bata jiyo komai, sai zaginta take yi a kan ta
tashi ta fita mata daga gida, har da ikirarin yau sai ta kasheta.

Da Abbie yaga abin is getting out of hand, zata iya cutar da Leesharh, sai ya yi
yunƙurin dakatar da ita. Ai ina kin sauraransa ta yi, ta ko'ina take kaiwa Leesharh
duka babu kakkautawa. Ransa ne ya yi mummunar ɓaci, zuciya ta ɗebesa ya dalla mata
wani irin mari mai gigitarwa.

Ihu mai sauti ta zunduma tare da dirowa ƙasa daga kan Leesharh, ta nufi waje tana
faɗin bari ta kira su Ramish sai sun zo sun fitar mata da wannan shegiyar yarinyar
daga cikin gidanta, kuma kowa ya zo yaga abin da suke aikatawa, har ƴan aiki sai ta
kira.

Tashin hankali, my people's me kuke tinani zai faru kuma? Kuna tunanin ya rayuwar
Leesharh zata kaya a gaba?. Anya zamanta a gidan zai yiwu kuwa? Abu Abdussalam zai
iya wanke kansa a kan babu abin da suke aikatawa da Leesharh kuwa? Kada ku manta a
irin yanayin da yake shi da Leesharh gabaɗaya, ni dai a gaskiya ban ga ta hanyar da
zai iya wanke kansa a kan wannan ƙazafi da Ummie ta yi mashi ba, dan kuwa ga
Leesharh tsirara, ga jini a jikinsa shi da ita, gata a ɗakinsa a kan bed ɗinsa,
meya kawota ɗakinsa nasan shi ne tambayar da kowa zai fara yi idan ya zo kan wannan
case ɗin, Abbie dattijon arziki, ya kuke tinanin zai ji idan Ummie ta kira su
Ramish suka zo suka ji halin da ake ciki? Akwai babban cakwakiya da tashin hankali,
part na Dubai ta kama da wuta, bari mu rarrafa wani part ɗin domin mu duba meke
wakana.

••••••• KINGDOM OF POWER••••••••🔥🔥🔥

A wayewar garin yau tawagar Auntynsu Jawad zasu koma in da suka fito, ƴan England
zasu koma haka ƴan Saudiyya ma, dik cikinsu babu wanda ya san da batun ɓatan Auta,
King ya ce a ɓoye maganar a matsayin sirri, saboda fitar maganar zai zamana
gazawace a garesu, kuma abokan gaba zasu ji daɗin anyi nasarar yi masu wani abin da
bashi da daɗi, za'a rai'na yanayin tsaronsu tun da za'a iya shiga har cikin gida a
saci yarinya, and bugu da ƙari fitar maganar zai sa a ce ga hanya mafi sauki na
ladabtar da king wato a kwashe ƴaƴansa kenan.

A takaice dai fitar bayanin ɓatar Auta babban abu ne a garesu, dan zai sa su Jaish
da ake ɓoyewa su sani, Akka zata ji labari, zai haifar da munanan abubuwa da dama,
dan haka sirrinta shi shi ne ya fi komai a garesu, hakan yasa King ya sirrinta
hakan.
Auntysu Jawad tayi farinciki sosai na jin aure ya koma kan Jawad, dan dik bata da
matsala da su. Sai dai ta so haɗuwa da Rizwan kafin ta koma, amma ina bata samu
dama ba, Rizwan yaki yin waya da kowa, yama kashe wayansa ne mai gabaɗaya.

A yau ranar da zata koma gabaɗaya fam sai da suka taru a main parlour na King dan a
yi sallama da juna. A nan ne Mammie take samun labaran Jannat Jawad ya aura ba
Rizwan ne ya aureta ba. Idan hankalinta ya kai dubu to sai da ya tashi, sai ta ji
tamkar ta mutu saboda bakinciki, burinta bai cika ba, har kasa iya zama a cikn
parlourn ta yi, hankalinta a tashe ta zame jiki ta yi waje babu wanda ya lura da
ita.

Shi kam uncle Abbas godiya sosai ya rinƙa yi wa Auntynsu Jawad, sam momma bata kawo
masu batun auren Jaish ba, ta ɓoye tamkar yadda suka yi da su Aunty MieMie.

Sai dai kuma wani abin guda, dole ta tilastawa su commander Zafar yakar Daular
Qahtaniyawa dik da a lokacin da suka dinfari wajen King Al-Mustapah ya sanar da su
shi bai ɗauki gimbiya Zunaira ba, kin yarda da shi suka yi dik da commander Zafar
yasan gaskiya King Al-Mustapah ya faɗa.

Commander ya jima a fagen yaki, idan gaskiya ake faɗe ya sani, haka zalika idan
karya ne ma ya sani, amma haka ya take wannan sanin dan basu da wata mafita da ya
wuce su yakesu, a kan umarnin King Zuhair suke yanzu, dik wata hanya da Aunty
MieMie ta buƙaci da su bi dan nemo Zunaira sun bi amma babu nasara, hakan ya
tilasta masu dawowa kan umarnin King suka aiwatar da yakin.

Sai dai kuma kash, ko da suka yaƙi Daular Qahtaniyawa babu Zunaira babu alamarta a
ciki, sun dai yi masu ɓarna na King karawa, King Al-Mustapah ya yi mubaya'a har ya
gaji amma sam babu alamar King Zuhair zai karɓi nadamarsa ya kuma yafe mashi,
kafiyar bala'i King Zuhair yake da shi wlh, idan ya tambara magana babu mai iya
sanya shi ya canza ya yi ta kenan.

A ranar da Auntynsu Jawad da tawagarta suka bar Kingdom of power a ranar su
commander Zafar suka kaddamar da wannan yaƙin tare da dawo da labari maras daɗi
wanda sam King bai so ji ba shi ne babu gimbiya Zunaira a Daular Qahtaniyawa.

Sosai ran King ya sake sosuwa, hankalinsa ya tashi, yau shi da yake kwantarwa da
Momma hankali a kan wannan case ɗin, sai yazamana ita ta juyo take kwantar mashi da
hankali saboda bala'in ya kai mashi bala'i, ga ɓatar Hoorain assistant commander
su, abin sai ya haɗe mashi biyu.

A can ɓangare kuma, wannan dai sadauki mai ɗauke da fuska kamar ta Hoorain namu ko
ma muce Hoorain namu shi ya jagoranci tawagar mayakan Queen Zarina izuwa kingdom of
power.

Tabbas ɗayan biyu ne, wannan sadauki ko dai tsafi suka yi amfani da shi wajen sanya
mashi irin face ɗin Hoorain dan su firgitar da Kingdom of power, dan kunsan sun san
komai ta hanyar mammie, so sun san bayyanar Hoorain a cikin mayaƙansu zai iya
sanyawa su yi nasara a kan Kingdom of power, dan mamakin da dangerous warriors zasu
shiga ganin Hoorain a cikin mayakan Queen Zarina shi zai iya tallafa masu su yi
nasara sosai.

Abu na biyu kuma shi ne ko kuma robbot suka sanya mai irin zubin halittar Hoorain,
ɗaya cikin biyun nan dole suka yi, dan sak Hoorain ɗinmu yake babu banbanci komai
ƙanƙantarsa.

To shi dai ya jagoranci tawagar Queen suka nufo su King wanda a lokacin King Al-
Mustapah yana ta neman ta yadda za'ayi su shirya da King Zuhair, hakan yasa dik da
King ya yakesu bai sa ya janye kudurinsa ba, sai ya haɗa sauran mayakansa da suka
rage ya fita ya tari rundunar mayakan Queen Zarina wanda already King Zuhair ya
samu labarin zuwansu, sai kuma ya samu labarin King Al-Mustapah ya tare mashi
yakin.

Abinku da jinin sarauta mai karfi, dik da ya ji hakan bai wani nuna mamaki ko kaɗan
ba, sai ma ya nuna kamar bai san suna yi ba, ya umarci commander Zafar da ya haɗa
kan wasu zataran warriors su fita su taya su King Al-Mustapah yaki dan su kaɗai ba
zasu iya da bala'in Zarina ba.

Hakan kuwa aka yi, suka fita domin tallafa masu.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Jawad bai zame ko'ina ba sai part na King da gudu, Jaish bai rabu da shi ba sai da
ya bisa har can, dan yau ya ci alwashin sai ya kuntatawa Jawad ya ji idan da daɗi
shi ma yadda ya ja mashi kima da mutuncinsa a kan titi.

Dai'dai lokacin King ya kammala shirinsa na nufar fada zai fito ya yi breakfast
kenan. A bayansa Jawad ya laɓe yana haki yana hararar Jaish da ya tsaya ta gabansa
yana bin daddyn nasu da kallo.

Abin ya yi matuƙar bawa Jaish mamaki ganin rama a tatare da King, tun da ya dawo
dama basu wani zauna sosai ba, so bai wani san halin da suke ciki ba.

"Daddy ka ce wannan tuzurun ya rabu da ni, dan kawai na yi aurena na barshi
shi ne yake jin haushina zai fasa mun baki yajawa amaryata asara". Cewar Jawad
kenan, yana magana yana kara laɓewa a bayan King.

Bakinciki ne ya ƙara lulluɓe zuciyar Jaish, lallaima Jawad ya raina mashi wayo yake
faɗe a cikin ransa. King da ya rasa abin faɗe ai binsu da ido kawai yake yi, a
ransa yake faɗin tun suna yara suke wannan tsiya, har yanzu basu dai'na ba!.

" Ko ka zo ko kuma yau sai dai mu kwana a nan". Jaish ya faɗa ransa a ɓace,
shi serious ya ɗauki abin, Jawad kuma wasa yake yi, shi fa da ace Jawad wata ya
aura ba kanwarsa ba to da da sauki abin, amma tsabar cin mutuncin ya kama ya auri
Chuchu da ya gama yi masu jan ido, yanzu haka kawai ya janyo mashi wani abin da ba
haka nan ba, wlh ba zata saɓu ba.

Amma kuma a matsayinsa na yayan Chuchu ya ji mata daɗin ta samu mutumin kirki wanda
yasan ba zata taɓa yin kuka ba a duniya, wani ɓangare na zuciyarsa ya so da ace
Auta ma Jawad ya aura, kunga masoyiyar kanwarsa ba ita ba kuka, kuma har abada in
dai tana matsayin matar Jawad shi zai cigaba da kula da ita.

Sai dai kash, tsakanin Jawad da Auta babu aure, shiyasa ma ya so Chuchu shi ma, da
akwai aure kun san dole ita zai so shi ma, ko dan ya ramawa Momma alkhairinta a
garesa, sannan kuma Auta ta fi Chuchu komai dik da ita ma Chuchun ba baya ba.

Amma babu halin ya aure Auta saboda ya sha nonon Momma a tare da Jaish, kunga babu
aure a tsakaninsu, matsayin yaya yake a wajenta, kuma fa ba wani sosai ya sha nonon
momma ba, kawai dai rabon auren ƴaƴan momman ne ya fita a ƙaddararsa.

"Malam bafa zan fito ka fasawa amaryata bakina ba, wai kai dan kana gwauro sai
ka zalinceni ne? Daddy hasada yake yi mun dan shi bashi da wadda take son shi, ka
canza wannan bakin halin naka sai ka samu koda kuyanga ce ta ce tana sonka a
lallaɓata ku shiga daga c............."

Kasa kai aya ya yi sakamakon hannu da Jaish ya kai zai yi mashi wata capka ya zille
yana harararsa. Ran Jaish ya ƙara ɓaci, lallai ma Jawad ya kai in da ya kai, shi
yake faɗawa magana dan ya yi aure? Danasanin tafiyar da ya yi ya shiga yi, dan da
yana nan wlh ba zai bari ayi wannan aure ba.

Sai yanzu na gane rabon auren Jawad da Chuchu ne ya kawar da Jaish daga kingdom of
power, kun san rabo fa har kisa tana yi, babu abin da bata sakawa, so da alama rabo
ta kawo sanadin wannan tafiya, dan kuwa tabbas da yana nan ba zai yarda ayi wannan
aure ba, sai ya hana ya zuga a bawa Rizwan ita tun da shi Dubai zai wuce da ita.

Kaucewa capka da Jaish ɗin ya kawo mashi ya yi, yana faɗin. "Daddy ka mun tsakani
da wannan gwauron, ni yanzu ba class ɗinsa bane, haka kawai zai cutar dani ya
zalunceni".

King da ya fahimci Jawad wasa yake yi Jaish kuma da gaske ya ɗauki abin sai ya
yi ƙoƙarin yi masu tsakani kada faɗar gaske ta tashi, yasan halin kowannensu, waɗan
nan kalamai na wasa da Jawad yake jifan Jaish da shi zai iya haifar masu da
gagarumin faɗa, shi kuma Jawad ɗin sam bai lura da gaske Jaish ya ɗauki abin ba.
Kuma kunsan akwai wani bakinciki a gefe na batun Mahnoor a zuciyar Jaish, sai abin
ta haɗe mashi yazama haushin kowa da komai yake ji.

"Ya isa haka, menene yake faruwa?". King ya faɗa yana kallon Jaish da har
idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kawai dan ance Mahnoor ce matarsa.

Ransa a matuƙar ɓace ya zayyanewa King dik abin da yake faruwa, daga karshe ya
rufe da cewa. "Ni daddy tun banga yarinyar ba i hate her, kuma bana san in ganta ma
a rayuwata, ka ce da momma bana so ta mayar da ita in da ta ɗaukota in ba haka ba
kome ya faru alhaki a kan wuyarku, coz i really hated her more than your
expectations".

Kalamansa cike suke tab da gaskiya, tabbas ya ji ya tsani Mahnoor kuma baya san
ganinta, kada kuga laifinsa, dik abin da zai faru bashi da laifi, ya sota ne a baya
lokacin da yake matsayin Hamma wanda ko sunansa na ainahi bai sani ba, yanzu kuma
yana amsa matsayinsa na Prince Jaish Zuhair Abdul Malik ne, kun san kuma babu ta
yadda za'ayi ace Jaish ya karɓeta haka nan tun da dani da ku dik mun san halinsa a
baya, kunga kuwa abu ne da ba zai yiwu ya yarda ba duba da yanayinta.

King yana ƙoƙarin yin magana ya katsesa da cewa. "And why daddy zaka aurawa Jawad
Jannat? Meyasa?".

A ɗan takaice King ya ce. "Coz he love her".

"Love". Ya maimaita kalmar yana dallawa Jawad wani irin kallon wanda idan ya yi wa
su Chuchu shi na tabbata ko yawu ba zasu iya haɗiya ba saboda azaban tsoronsa.
Izuwa yanzu Jawad ya fahimci da gaske ran ɗan uwansa a ɓace, kuma shi kansa ya ji
ɗacin cewa da aka yi wannan ƴar kauye da Momma ta dawo da su ɗin ne matar ɗan
uwansa, shi ya zaci ma wasu ƴan aikin momma ta je ta kwaso, amma kawai sai ace
matan ɗan uwansa, ina gaskiya ko shi bai aminta da wannan ba, ransa ta sosu matuƙa,
he feel he's blood brother pain, wannan ai ƙaskanci ne a ganinsa.

Lallai jikokin Akka sun rai'na capacityn Mahnoor sosai.........😅

Matsawa kusa da Jaish Jawad ɗin ya yi, wani irin tausayin ɗan uwan nasa ya ji,
ɗan rungumosa ya yi yana ƙoƙarin kwantar mashi da hankali. King kuwa, waje ya
buƙaci da su samu su zauna zasu tattauna. Da kyar Jaish ya yarda ya zauna a bakin
bed ɗin daddyn nasa, sai huci yake yi shi ransa a ɓace ancuce shi da aka dangantasa
da ita, an zubar mashi da kima.

Zama King ya yi a gefensu, sai da ya fara da rarrashin ɗan nasa, suka haɗu shi da
Jawad suka taushi wannan zazzafar zuciyar, dan idan zuciyar bata sanyayya ba babu
wata magana da zata iya shiga kunnensa har ya iya amfana da ita, hakan yasa suka
fara da tausan shi.
Sai da suka tabbatar da ya ɗan huce, sannan ne King ya fara bashi labarin yadda
Momma ta faɗa mashi komai dallah dallah da yadda aurensa da ita ya kasance, zaman
da suka yi da komai da komai.

Tin da King ya fara magana basu ce ko uppan ba, suna binsa da kallo suna sauraro
har ya dasa aya.

Da ɗan ɗaga murya Jaish ya furta. "That's not me dad! Not me! Gaskiya wannan ai sai
dai a film ne kawai zai faru, me I can't do that, kawai dai they told momma what
the want ne kawai, but isn't true, kuma ni i can't believe that, and i can't accept
this nonsense, dik zan yi maganinsu ne". Cike da gaskiyarsa yake wannan magana.

Cigaba da tausan shi suka yi, King ne ya ce. "Sorry son, ba mommarka ta ce we
should give her one week zata gabatar mana da yarinyar ba? So calm down, after one
week sai mu ce we can't agree with her idan muka ganta, that's all".

Girgiza kai ya yi tare da miƙewa tsaye. "No dad, ba zai yiwu ba, babu wani one week
da zata yi, yanzu zata bar gidan nan, for what reason zata ce matata ce? Ni nace
ina san in yi aure ne? Did I say so?". Ya kai karshen maganar tare da nufar waje.

King bai dakatar da shi ba, dan ya fahimci lallai yau ran ɗan nasa a matuƙar ɓace
yake, saboda Jaish bai taɓa yi mashi magana a irin wannan sigar ba, bai taɓa ɗaga
murya fiye da nasa haka ba, kuma ga dikkan alamu Jaish ya manta a gaban King yake
ma, dan har da ficewa tin basu gama magana ba, a bisa dokansu Jaish ya cancanci
hukunci a kan abin da ya yi yanzu na suna magana da King ya tafi, dik da yake
matsayin daddynsa sarki fa sarki ne mai cike da isa da izza a ko ina yake.

Ni kuwa na ce ba a ko'ina yake ba, ina da ja a kan wannan magana, domin kuwa a
gaban momma dai baby yake zama, babu wani sarauta a wannan waje idan
yana............. To dai saboda sirirkina ne na yi shiru, amma da kwance mashi zani
a kasuwa zan yi....😅

🔥🔥🔥

Amma sanin halin ɗan nasa yasa bai ce komai dangane da hakan ba, sai ma ya ce Jawad
ya bishi ya rarrashesa kada ransa ta cigaba da ɓaci. Da sauri Jawad ya miƙe ya bi
bayansa. Shi kuma King parlournsa ya fito dan ya yi breakfast ya tafi fada, yau
sarkin hatsi zai fitar da zakka daga runbum kayan hatsi na King izuwa ga talakawan
dake cikin kingdom da kawaye.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A yau momma ta tsara Ibrahim kawun Mahnoor zai koma Nigeria, sai dai zai koma ba
tare da ya sanya Mahnoor ko Mahreen a idanunsa ba, dan kowa yasan yadda dokan
kingdom of power yake, dik da yake kawun Mahnoor yanzu matsayin matar Prince take,
bashi da damar ganinta a saukake haka, idan ba ita ta buƙaci ganinsa ba to ko ya so
ganinta ba za'a bashi dama ba har sai ta buƙata, kuma sun shiga ɗakin gyara ma
abinsu. Ko momma ɗin ma bai samu damar gani ba, ta dai turo a faɗa mashi nan da
sati ɗaya (wato idan King ya aminta da Mahnoor kenan) nan da sati ɗaya ya sanar da
bappa zasu zo da tawagarsu su kawo masu kayan lefen Mahnoor da sadaki da komai da
ake yi a biki, shi ne sarinta.

Sannan ta haɗa mashi uban tsaraba, yadika, shaddoji, atamfa, lace da arab abayas
and jallabiyas, kayan abinci da makuɗan kuɗaɗe a kan ya kaiwa bappa a rabawa ƴan
uwan Mahnoor sai sun zo nan da sati guda In Allah ya ɗorasu a kan King.

Tawagar mota guda ta ɗaga a kan a kaisa airport, ya samu gata albarkacin Mahnoor,
dan kuwa private jet aka ɗaga ta ɗaukesa zuwa har birnin Jimeta Yola.
Yana san ganawa da ƴaƴan nasa, amma babu dama, haka ya hakura dan bai ga fuskar
tambayar ina suke bama, saboda warriors da suka kai saƙon Momma garesa bai ga
fuskar ya masu magana ba, tsoro ma suma bashi, da wuri dole ya amshi komai suka
wuce airport.

Yana zuwa baifi da minti 10 ba jirginsa ya ɗaga sai Nigeria.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

UNCLE JAHIZ🔥

Sai da ya tsaya Zee ta ci abincin nan sosai ta ƙoshi, sannan ya ce ta tashi su je
ya kaita wajen ƴaƴansa ta yi wanka ta shirya anjuma su je kallan Khadijah.

Ajiyar zuciya ta sauke, haƙiƙa ta yi farinciki na jin cewa zata je kallan ƴar
uwarta, sai satar kallansa take yi, idan ya kalli face ɗinta kuma sai ta yi saurin
kawar da kallanta.

Ɗakin Aneesa ya nufa da ita, a lokacin ita kuma tana ƙoƙarin fitowa hannunta rike
da wayarta tana kallan hoton Yah Rizwan, Allah ya gani tana san bawan Allahn nan.
Sanye take da sleeping dress, yanzu ta tashi daga barci, kamar wata aljana ta samu
labarin Yah Jaish ya yi aure ne ta nufo waje, ko wanka bata tsaya yi ba zata je
kaiwa Fanan gulmar.

Kai Aneesa duniya, da alama ƴaƴan mama ma ba baya ba a kaifin ƙwaƙwalwa, ga Ramish
ga Aneesa, ko daga ina ta samo labarin Jaish ya yi aure kuma?. Maganar da iya King
and Momma ne kawai suka sani, sai kuma Yah Jawad da aka faɗawa da safen nan, ko
uncle Abbas and uncle Jahiz da suke matsayin uba a garesu ma basu sani ba, kai
gaskiya Aneesa ta fara bani tsoro.

Zata fita shi kuma zai shigo, ɗan karo suka yi, baya ta ɗan koma tana ce mashi
sorry haɗe da cewa. "Good morning my lovely second dad".

Kanta ya ɗan shafa yana amsa gaisuwar tata cike da kauna, Allah sarki koma dai me
Aneesa macece mai fara'a ga iya ƴan uwanta kawai banda bare, a waje kana ganinta
zaka san jinin sarauta ya ratsa jinin modarawa dake gudana a jikinta, kuma suna
shiri da uncle Jahiz sosai.

"Daughter ga friend na kawo maki, ki tayata ta yi wanka ki bata kayanki ta
sanya". Ya faɗa yana satar kallan Zee ta witsiyar idanunsa.

Da wani irin kallo mai kama da na ƙaskanci ta ɗan bi Zee da shi, ba dan uncle Jahiz
ne ya kawota ba da bata ga dalilin da zai sa wannan ƙazamiya ta shigo mata room ba,
sai wari ma take yi, ta faɗi hakan a cikin ranta, a fili kuma sai ta ɗan kwaɓe
fuska, cike da izza ta ce. "Second dad wacece ita ɗin?".

Ya fahimci kyamar Zee take ji duba da yadda ta kwaɓe fuska, amma bai ga laifinta
ba, dan haka suke, suna da tsabta basa san datti komai ƙanƙantarsa.

"Daughter tana da mahimmanci sosai ga rayuwata, ba kamar yadda kike tinani ba, ta
wuce nan, ki kula mun da ita sosai, kada ki ji kamar ba ƴar uwarki bace, ki kalleta
a matsayina kin ji?".

Ya yi mata hakan ne dan kada Zee ta fiskanci kyara da kyama a wajensu, yasansu
sarai, idan ba haka ya bi da su ba wlh Zee zata yi kuka kasancewarta da su.

"Second dad ka ganta fa, a hakan ne take da mahimmanci a wajenka?". Cike da
mamaki ta yi maganar. Tana yi tana ɗan hararar Zee da wannan idanun nasu na
gado.................................... Jinjina kansa ya yi alamar tabbas tana da
mahimmanci a wajensa.

"To amma second dad meyasa bata yin wanka, ka ji fa wari take yi". Ta sake
jefa mashi tambaya.

Da yake da larabci suke yin magana, kuma sun zurfafa sosai sai yazamana Zee bata ji
sosai, dama sama sama take ji, shi ma dan islamiyyar da suka yi kafin babanta ya
rasu ne yasa take ɗan ji. So bata ji irin cin mutuncin da Aneesa take yi mata ba.

Satar kallan Zee ya yi kafin ya dawo da kallansa a kan Aneesa da ta turɓune fuska
sosai.
"Daughter bata da lafiya ne fa, daga hospital ta tawo yanzu, please take
good care of her, ni zaki yi wa kin ji my lovely daughter?".

Kai ta gyaɗa mashi amma rai bai so ba, dan yadda ta ɓata ran nan babu alamar zata
yi na'am da Zee, ta yi mugu mugun rai'na class ɗin Zee, a cewarta ma ko a ƴar aiki
ba zata ɗauki Zee ba, gaskiya kuma dik kuyangunsu mata ne masu tsabtar gaske.

"Allah ya yi maki albarka Daughter, anjima da yamma zan zo in ɗauketa kin ji?".
Sake jinjina kanta ta yi tana cigaba da ɓata fuska.

Juyowa ga Zee ya yi, cikin harshen turanci ya ce. "Zee zan dawo da yamma in
ɗaukeki, ki zauna tare da Daughter kin ji?".

Kanta a ƙasa tana ɗan satar kallansa ta amsa da okey sai ya dawo. Kamar ba zai tafi
ba, alamar baya san rabuwa da ita, amma sai ya daure ya juya ya fita. Yana juyawa
ta bi bayansa da kallo.

Kura mata idanu Aneesa ta yi tana kallan yadda take binsa da kallo har ya kurewa
ganinta, sannan ta katseta da cewa. "Kyakkyawa ne uncle ɗina ko?".

Aneesa akwai iya shege wlh, cikin harshen turanci ta yi maganar ganin uncle Jahiz
ya yi wa Zee ɗin magana da turanci, sai ta yi tinanin ko bata jin larabci ne yasa,
kuma ta ganta bakar fata sai ta kara rai'na class ɗinta.

Jinjina mata kai Zee ta yi

Please Login or Register in order to submit comment