Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 44 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wash, ƙara ja ta yi tana faɗin. "Shi ne ba zaka rarrasheni ba, kuma kasan na
yi fushi, amma shi ne kake kallona zan tafi baka rarrasheni ba ko? To ba kai ka
ɓata mun rai bane?".

Daga ganin idanunsa zaka fahimci yana cikin yanayi, dik jikinsa a mace, idanunsa
sun sauya sun yi ja, sai faman lumshe su yake yi, da kyar ya iya riko hannunta da
take ta faman jan dogon hancinsa da shi, can ƙasan maƙoshinsa ya furta.

"Ba zaki iya yin fushi da babynki ba ai, shiyasa na zuba maki idanu ina
kallanki, na san zaki dawo ai rigimamma kawai". Ya kai karshen maganar yana janyota
ta faɗa saman kirjinsa.
"To yanzu na bada hakuri kuma na yi rarrashi, baby ya bada hakuri ko?". Ya
sake faɗa ƙasa ƙasa yana kallan face ɗinta. "Ni wannan hakurin ya mun kaɗan, sam
ban yarda ba, sosai zaka rarrasheni". A shagwaɓe ta yi maganar.

Kamar mai raɗa ya ce. "To na yarda rarrashin ya yi kaɗan, kuma zan yi mai yawa,
amma sai kin dawo daga school, anjuma da daddare zanzo sai na yi rarrashi mai yawa
kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana ɗan shafa bayanta. Ɗago kanta daga saman
kirjin nasa ta yi. "Promise me first!". Ta yi maganar tana miƙo mashi tafin
hannunta.

Ɗaura nasa tafin hannun a saman tata ya yi, sannan ya ce. "I promised you that
zan zo da daddare in yi rarrashi mai kyau".

Siririn murmushi ta saki tare da matsawa kusa da shi ta manna mashi sumbata a
lallausan kumatunsa, ƙasa ƙasa ta ce mashi take care, sannan ta yunkura zata fice
daga cikin motar. Rikota ya yi jikinsa dik a mace, a hankali ya ɗan matseta a
jikinsa kafin ya matsar da face ɗinsa dab da ita. Sumbata ya bata a kumatu shi ma
yana mai faɗa mata ta kula da kanta sosai. Daga haka ya ɗauki ledar chocolate ɗinta
na ɗazun da taƙi karɓa ya miƙa mata yana kallanta.

Karɓa ta yi da sauri ta fito daga cikin motar, da kallo ya bita tana tafiya har sai
da ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke ajiyar zuciya tare da dawo da kallonsa ga
makunnin motar. Da kyar ya iya tasarta ya nufi gida wajen Ammo da shopping ɗin da
ya yi.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Gabaɗaya hall ɗin tsit suka nitsu saboda tsoron bomb ɗin, gabaɗaya yawan jami'an
dake wajen sun tsaya cak, kowannensu idanunsa a kan Ramish dake kasa ya kasa ɗago
kansa, saboda wani irin ɗaci da ransa ya yi mashi.

Bilal yana tsaye a kusa da Abbie, saboda ya razana shi ma ya miƙe tsaye kafin
mutanen can su yi barazana da bomb ɗin.

Wani irin tsawa mutanen suka daka a kan wai Ramish ya miƙe tsaye, har da cewa shi
kaɗai suke da buƙata a taron nan, su basu zo nan da nufin su cutar da kowa ba, shi
suke san ɗauka, in yana san cetan ran jama'arsa to dole ya tashi ya bisu. Ajiyar
zuciya Ramish ya sauke kafin ya yunkura ya miƙe tsaye.

Yana miƙewa suka sake daka mashi tsawa a kan ya sauko kasan stage ɗin ya ƙariso
gabansu ya zube gwiwowinsa a ƙasa..... Babban magana!!.

Ko kaɗan bai damu da abin da suke faɗe ba, hankalinsa bai tashi ba. Slowly ya kai
kallansa a kan Leesharh dake kwance jininta na zuba tamkar an buɗe hanyar ruwa. Ta
wutsiyar idanunsa ya kai kallansa a kan Bilal wanda shi ma shi yake kallo.

Blinking eyes ɗinsa Ramish ya yi sau biyu, da alama magana ce tasu ta jami'ai, dan
kunsan suna karɓar irin wannan horo ta magana da gaɓɓan jikinsu saboda shiga
matsala irin wannan sai su yi magana ba tare da sanin kowa ba su fahimci junansu.

Jinjina kansa Bilal ya yi tare da dunkule hannunsa sai ya sake warewa. Yana
warewa Ramish yasa hannu cikin zafa a aljihun Suit ɗin jikinsa kafin kowa ya ankara
ya zaro pistol gun, a tare suka zaro shi da Bilal.

Mutanen suna ganin haka sai suka yi ƙoƙarin danna bomb ɗin su kunna, sai dai kafin
su yi motsi Bilal da Ramish suka harbesu a tare lokaci guda, Ramish ya harbi ɗaya
Bilal ma ya harbi ɗaya a goshinsu. Tare suka zube ƙasa, ashe kallan da Ramish ya yi
wa Bilal maganar da suka yi kenan, abin da yasa suka yi haka kuma shi ne idan
Ramish shi kaɗai ya ce zai harbesu kafin ya harbi ɗaya ya sake harbin ɗayan to
ɗayan zai kunna bomb ɗin, dole a tare za'a harbesu idan ana san kowa ya tsira.

Suna harbinsu gabaɗaya jami'an dake wajen suka yi kansu da gudu dan su duba bomb
ɗin a kunne yake ko a kashe yake. Mayar da gun ɗinsa cikin aljihunsa Ramish ya yi,
juyawa ya yi ya da nufin ya isa ga Leesharh kamar walkiya haka Bilal ya rigasa isa
gareta. Bata numfashi kamar rai ya yi halinsa ne.

Cak Bilal ya ɗauketa jami'ai uku suka rufa mashi baya izuwa wajen motocinsu, shi
kuma Ramish ya haɗa kan family sannan ya bawa jami'an su umarni da su wuce mashi da
waɗan nan mutane h-q zai bi ta kansu amma ba yanzu ba, bari ya gama da case dake
gabansa na Leesharh tukun nan, zuwa anjuma idan ya tabbatar da Leesharh bata mutu
ta dalilinsa ba zai zo ya binciki mutanen.

Hankalinsa ya tashi sosai, ya kuma yi mamakin yadda aka yi Leesharh tasan za'a
harbesa har ta sadaukar da nata ran a kansa! Dik yadda aka yi tasan wani abin, dan
haka in dai bata mutu ba zai tsaya ta samu lafiya ko dan ya samu wasu amsoshi daga
bakinta.

Kunsan dik taurin zuciyar mutum in dai aka yi mashi irin sadaukarwar da Leesharh ta
yi mashi wlh dole zuciyarsa ta raunata ta kuma sassauta, to shi ma hakan ne, sai da
ya ji wani iri a ransa, tambaya ɗaya yake yi wa kansa shi ne meyasa Leesharh ta
bada ranta ta ceci shi?. Wannan ne babban damuwarsa.

Haɗa kan family ya yi suka nufi gida. Da gudun gaske motocinsu suka danna cikin
gida, sai kuka Sharifat take yi kamar ranta zai fita, ta shiga damuwa da tashin
hankali sosai. Ummie kuwa addu'a kawai take yi Allah yasa Leesharh ta mutu.

Suna shiga gida tun motocin basu gama yin parking ba Bilal ya fito da gudu ya
buɗe gidan baya ya ɗauko Leesharh a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa Ramish da Dr
Raj suka rufa mashi baya, dan su dubata. Da sauri shima Abbie and Sharifat suka
fito suka rufa masu baya.

Kai tsaye a&e ɗinsu suka nufa da Leesharh. Hankalin Bilal idan ua kai miliyan a
tashe yake a zahiri, amma bamu san me yake a cikin ransa ba, shin tashin hankalin
me ma yake yi, yana damuwa Leesharh ta mutu ne ko kuma yana damuwar ta bada ranta
ta ceci Ramish? To wannan dai dik bamu sani ba.

A tare Dr Raj da Ramish suka shigo cikin room ɗin. Bilal yana ƙoƙarin sanya
karfi ya yage rigar jikin Leesharh Ramish ya dakatar da shi. Da mamaki suka dawo da
kallonsu a kan Ramish ɗin. Dr Raj ya yi mamakin ganin yadda Bilal ya tashi
hankalinsa sosai har ya rasa control saboda Leesharh, sai kace wata tasa ta jini ko
da akwai wata alaƙa a tsakaninsu! Abin da mamaki, tabbas yasan Bilal mutum ne mai
tausayi, amma ya nuna san Leesharh sosai wanda sun san ba halinsu bane.

Cikin nitsuwa Ramish ya tako ya kariso bakin bed ɗin da Bilal ya kwantar da
ita, in a cool voice ya ce. "Rai'na ta ceta ta shiga haɗari, dan haka da kai'na
nima zan cetota daga haɗari". Yana kai karshen maganar ya buɗe drawer dake kusa da
bed ɗin, cikin zafa ya kwaso kayan aikin cire bullet irin su. Irrigation Syringe,
Retractors, Suction, Machine Forceps, Scalpel, Local Anesthesia, X-ray Machine,
Sutures, Sterile Gauze Pads, Antiseptic Solution.

A gaban bed ɗin ya zo ya zubesu saman wata tables dake ta gefe dai'dai in da kanta
yake.

Su Abbie da suka shigo yanzu ne suka tsaya cirko cirko suna kallansa yana aiki
cikin zafa da kulawa.
Almakashi ya fara ɗaukowa, rigar jikinta ya yanke tin daga farko har karshe,
ya tsaga rigar biyu kenan, wani farar vest wadda ta ji jaga jaga da jini ne ta
bayyana a ciki. Saman breast ɗinta kaɗan bullet ɗin ya sameta, hakan yasa ya yanke
iya hannun vest ɗin kawai. A saman table ɗin ya mayar da almakashin ya ajiye.

X-ray Machine ya ɗauko, komai da zafa yake yi duba da halin da take ciki na zuban
jini sosai, wannan machine yasa ya fara bincikar dik wasu jijiyoyi da gaɓaɓɓan dake
kusa da in da aka harbeta ɗin, dan ya tabbatar da in da bullet ɗin yake ya kuma
tabbatar da cewa bai taɓa wata jijiya ko wani joint or kashin jikinta ba.

Da sauri Dr Raj ya nufosa domin ya taimaka mashi, hannu ya ɗagawa Dr Raj alamar
baya buƙata, shi ma zai rama cetan ransa da ta yi ne da kansa, zai yi iyaka
ƙoƙarinsa dan yaga ya ceceta. Sharifat sai shessheƙar kuka take yi tana rungume da
Abbie, Ummie dai taki biyosu nan, ta wuce part ɗinta. Abu Abdussalam yana cikin
tashin hankali, da kaga face ɗinsa zaka san yana cikin tashin hankali bawan Allah.

A hankali Ramish ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya kalli tabbas bullet ɗin
bai taɓa koɗaya daga cikin abin da yake gudun ya taɓa ba, bullet ɗin yana tsakiyar
namar kirjinta, sai dai saura kaɗan ya huda ƙashinta.

Cikin zafa ya ajiye X-ray machine ɗin. Sannan ya ɗauko Antiseptic Solution, a
hanzarce ya fara tsabtace wajen da bullet ɗin ya fasa namar ya shiga ciki. Yadda
kuka san computer haka yake yin aiki.
Tsab ya tsabtace wajen, sannan ya ɗauko Local Anesthesia don rage mata zafi.

Dik da idanunta a datse sai da ta ɗan ciza laɓɓanta a lokacin da yake gudanar da
aikinsa, alamar tana jin azaba, the way take jin azaba the way take kara datse
idanu.

Lokacin guda tausayin Leesharh ya ratsa zuciyarsa, dan yasan azabar bullet, su da
suke matsayin jami'ai, zaratan jaruman maza ma bata sauki suke iya jure azabar
bullet ba bare ita da take mace kuma yarinya, ai dole dik wani mai zuciya a
kirjinsa ya tausaya mata.

Scalpel ya ɗauko. Shi kansa sai da ya ɗan datse idanunsa a lokacin da yake buɗa
namar kirjin leesharh da wannan Scalpel ɗin dan ya samu damar iya zare bullet ɗin.
Yana aiki cikin zafa, amma kuma dik wata karfe da zai ɗaura a jikin Leesharh a
hankali yake yi mata cikin tausayawa.
Yana buɗe namar wajen jini ne ya kara bulbula da karfi tamkar ruwa ya
fasowa kansa hanya.
Da sauri ya ɗauko Irrigation Syringe da ɗayan hannunsa ya fara tsabtace jinin
yana sharesa. Sannan ya ɗauko Suction Machine ya yi amfani da shi wajen toshe
jinin dan ya samu saukin yin aikinsa. Abin ku da jami'i, ya kware a wannan fanni na
cire bullet.

Retractors ya ɗauko, cike da kwarewa ya fara amfani da shi wajen rage tsokar dake
ta cikin fatar in da bullet ɗin yake. Bayan ya rage sai ya ɗauko, Chlorhexidine, ya
yi mata amfani da shi dan ya kara tsabtace wajen harbi saboda da ya yanke namar
wajen an samu zubar jini.

Ajiyar zuciya ya sauke ganin cewa komai ya daidaitan mashi yadda yakamata.
Forceps. Wannan kayan aiki ne mai kama da almakashi, ana amfani da shi don kama
bullet ɗin cikin sauƙi, cikin nutsuwa da tausayawa ya sanya forceps ɗin, a hankali
ta kama bullet ɗin. A hankali hankali ya fara jan bullet ɗin yana zaro shi waje.

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ciro bullet ɗin,
cikin wani kwano mai ɗauke da ruwa mai sanyi da Dr Raj ya kawo mashi ya jefa bullet
ɗin, sannan ya yi hanzarin ɗauko sutures ya fara ƙoƙarin haɗe wajen ya ɗinke mata.

Dik cikin ɗakin sai da suka tausayawa Leesharh, harbi a kirji namiji ma yaya aka
cika bare kuma a kirjin mace, ai abin da ciwo matuƙa wlh.
Ramish bai fita daga ɗakin na sai da ya tabbatar da ya kammala komai, sannan ya
nufi waje da sauri. Cikin zafa Bilal ya rufa mashi baya, kai tsaye h-q suka nufa a
tare. Shi kuma Dr Raj ya matsa kusa da Leesharh dan ya ƙara dubata, lallai ba
shakka shi ma ya ji yana kaunarta yadda ta bada ranta ta cetan mashi ɗan uwansa, a
yadda Ramish yasa harbi ba sau ɗaya ba sau biyu ba da ace wannan harbin ta samu
zuciyarsa ai shikenan sun rasa shi, amma ta tare mashi, a gaskiya yazama nauyi a
wuyansu da su tsaya tsayin daka wajen ganin sun ceci rayuwarta ita ma.

Matsawa kusa da bed ɗin Abbie da Sharifat suka yi domin su dubata, baiwar Allah ta
ji wahala har face ɗinta ta kumbura sosai lokaci guda, ta zama kamar ba ita ba. Shi
dai Yah Rizwan baya nan, ya ɗan yi tafiya zuwa ƙasar China dan bunƙasa
kamfanoninsa.

To Leesharh sai dai mu ce Allah ya tashi kafaɗunki kawai, Allah yasa kina da rabon
shan ruwa a gaba, Ramish kai kuma Allah yasa ka kama masu nikaf mu ji dalilinsu na
bibiyar rayuwarka da suke yi mu kuma ji maciya amanar da suke cin amanarka.

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Sweetie ta samu lafiya cikin yardan Allah, sai kuma sabon walaƙanci da ta karo
yarinyar nan, sam bata da tsoro, ya battaba dai jikin sarauta ne da gaske yake gudu
a jikinta, akwai ta da karfin hali da jajircewa.

Zaune suke a saman bed ɗin Black Tiger a bedroom ɗinsa ita da Ronnie tana yi mashi
bayanin kan yadda ake gudanar da sallah dallah dallah, Black Tiger ya tafi fada,
kun san dama sun ce idan za su yi karatun addini a part ɗinsa zasu rinƙa yi dan a
nan ne ba zai iya ganin abin da suke aikatawa ba ko?

To hakan kuwa aka yi, tana ta yi wa Ronnie bayani yadda zai yi sallah, tana sanye
da doguwar riga irin shigar mutanen birnin Black world, ta yi balai'n kyau, ta saki
wannan kyakkyawan golden white hair nata sai sheki yake yi, ya sha gyara, Ronnie ya
ce kayan basu taɓa yi wa wata mace kyau irin yadda suka yi mata ba, ta ji daɗin
yaba kyanta da yake yawan yi, ranta na sanyaya sosai.

Dik abin da take koya mashi yana rikewa sosai a cikin kwakwalwarsa, saboda akwai
brain shi ma, ga shegen san karatu kamar me.

Suna zaune suna fuskantar juna, kamar wasu yaya da kanwa, gwanin birgewa, yana
sanye da hoodies milk color a jikinsa. Sai wani binta da Koreans eyes ɗinsa yake
yi.

"Sweetie ina san ki faɗa mun a in da zan samu ainahin Ingila in karanta, dan
ina san sanin ainahin saƙon da yesu ya zo da shi". Cewar Ronnie kenan, yana magana
yana ɗan murza mata ƴan yatsun hannunta dake rike cikin nasa. Sun bajewa Black
Tiger a saman bed ɗinsa kamar nasu ne. Floris dai tana can wajen Angela, yanzu
Floris ta fara yarda da zugin da master Devil yake yi mata, shiyasa ta ja baya da
su sosai, amfani yake san yi da yarintarta ya kama Ronnie, ce mata ya yi idan ta
taimaka mashi zata mallaki Ronnie, ita kuma sai ta yarda.

Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ta ce. "No need ka
karanta ingil a yanzu Ronnie".......... "But why?". Ya jefa mata tambayar da alamar
damuwa a face ɗinsa, da alama da gaske yake yi yana san sanin ainahin abin da
annabi Isa ya zo da shi.

"Saboda ingila ba zata dawo duniya ba, Annabi Isa zai dawo duniya, sai dai idan
ya dawo shi ma ba zai yi amfani da ingila ba, zai dawone yana mai bin bayan Annabi
Muhammad (S.A.W) so dik hukuncin da zai yanke a yayin dawowarsa zai yanke ne bisa
amfani da kalamul lah, wato Alqur'ani mai girma".
Ɗan zaro idanunsa ya yi, cike da mamaki ya ce. "Kenan dama yesu zai dawo
duniya?".......... Jinjina mashi kai ta yi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa.

"Tabbas zai dawo duniya, wannan magana tana da asali daga hadisan
Annabi Muhammad (SAW), wanda ya tabbatar da dawowar Annabi Isa (AS) a ƙarshen
zamani. Daga cikin hadisan da suka zo kan hakan akwai. Hadisin Abu Huraira (RA) ya
ruwaito Annabi (SAW) ya ce. Ina rantsuwa da wanda raina ke hannunsa, haƙiƙa zai
sauko maku da ɗan Maryam a cikinku a matsayin mai hukunci na adalci, zai kashe
batun cin alade, zai hana haraji, kuma kuɗi za su yawaita har ba wanda zai karɓa,
hadisin yana nan a cikin Sahih al-Bukhari hadisi mai lamba 2222, sai Sahih Muslim
hadisi mai lamba 155".

"Sannan Abu Huraira (RA) ya sake ruwaitowa. Annabi (SAW) ya ce. Ba wani annabi da
zai kasance a tsakanina da Isa, wato bayan manzan Allah babu wani annabi da za'a
sake yi sai Annabi Isa da zai dawo. Lallai Isa zai sauko duniya, kuma zai yi
hukunci da shari'ar Musulunci. A cikin Sahih Muslim hadisi mai lamba 2365. Ma'anar
Wadannan Hadisan shi ne, Annabi Isa (AS) zai dawo a ƙarshen zamani, amma ba a
matsayin sabon annabi ba, sai dai a matsayin mai bi ga shari'ar Annabi Muhammad
(SAW) Zai yi hukunci da shari'ar Alqur'ani da Musulunci, ba da Injila ba. Zai
tabbatar da adalci, ya kawar da shirka, ya karya gicciye, ya hana cin naman alade,
kuma ya hukunta duniya bisa dokokin Musulunci. Wadannan dalilai sun nuna cewa
Annabi Isa (AS) ba zai zo da sabuwar shari'a ba, ko ya yi amfani da littafin da ya
zo da ita a baya wato ingil, sai dai zai zama mai bin shari'ar Annabi Muhammad
(SAW). Wannan yana daga cikin alamomin ƙarshen duniya da kuma tabbacin cewa
Musulunci shi ne cikakken addini har zuwa ƙarshen zamani, dan haka ba sai ka wahala
wajen neman karanta Ingila ba, ka karanta Alqur'ani mai girma dan ma ka kara sanin
girman Allah ka ji ko?".

Shiru ya yi yana tinanin lallai ba shakka Annbi Muhammad fiyayyen halitta ɗin
ne da gaske kamar yadda Sweetie ta faɗa mashi, lallai zai yi biyayya ga Annabi
Muhammad iyaka iyawarsa, tabbas zai karanta Alqur'ani mai girma zai kuma yi
haddarta.

Ganin ya yi shiru yasa ta ce. "Baka gamsu bane in kawo maka wasu hujojin masu
karfin da dole ka gamsu Ronnie?".

Da sauri ya girgiza mata mai alamar a'a ya gamsu, sannan ya ce. "Dan Allah ki bani
tarihin Imam Mahadi ko kaɗan ne yau kam, kullum sai na tambayeki amma baki faɗa
mun".

Jinjina kanta ta yi, sannan ta fara magana kamar haka.
"Zan baka tarihin Imam Mahadi ko dan saboda yadda jama'a suka ɗaukesa, wasu sun
karyata bayyanarsa, wasu kuma sun faɗi yadda zai bayyana ba'a dai'dai ba, sun ruɗar
da mutane game da bayyanarsa".

Shiru ya nitsu yana jinta, cigaba ta yi da cewa.

"Imam Mahdi Allah ya yarda da shi, shi ne ɗaya daga cikin manyan alamomin tashin
alkiyama. Addinin Musulunci ya yi bayani a kan zuwansa, kuma ya na da mahimmanci a
fahimtar al’amuran da za su wakana kafin ranar alkiyama. Menene Ma'anar Mahdi ma
farko tukun nan?".

Shiru ta ɗan yi tana kallansa, ganin bai motsa lips ɗinsa da nufin yin magana bane
yasa ta ɗaura da cewa.
"Sunan Mahdi yana nufin wanda Allah ya shiryar zuwa gaskiya. Shi
mutum ne da Allah zai zaɓa domin ya jagoranci al’umma zuwa ga adalci da gaskiya a
lokacin da duniya ta cika da zalunci da barna. Asalinsa daga zuriyar Annabi
Muhammad (SAW) yake. Yana daga cikin zuriyar Nana Fatima, ƴar Annabi (SAW) Sunansa
da sunan Annabi iri ɗaya ne sak. Sunansa Muhammad shi ma, kuma sunan mahaifinsa
Abdullah, kamar dai Annabi Muhammad (SAW). Zai cika duniya da adalci. Zai bayyana
ne a lokacin da duniya ta cika da zalunci da fasadi, sannan zai dawo da adalci da
gaskiya. Annabi Muhammad (SAW) ya ce Al-Mahdi yana daga cikin zuriyata, daga cikin
ƴaƴan Fatima ka duba Sunan Abu Dawud, Hadisi mai lamba 4286 a nan manzan Allah ya
yi wannan magana".

"Manzon Allah ya sake cewa za a cika duniya da zalunci da danniya, sannan Allah zai
kawo wani daga cikin iyalina wanda zai cika ta da adalci da gaskiya kamar yadda aka
cika ta da zalunci da danniya ka duba cikin sunan Abu Dawud, Hadisi mai lamba 4285,
Annabi ya ce Imam Madih zai bayyana ne a Makka kusa da Ka’aba, inda mutane za su
rantsar da shi a matsayin jagoransu. Aikin da zai yi a zamansa a duniya sun haɗa
da.Yaki da zalunci. Zai jagoranci yaƙi da azzalumai da masu rushe gaskiya. Zama
jagoran musulmi. Zai haɗa al’ummar musulmi karkashin jagoranci guda. Zai taimaki
Annabi Isa (AS) A lokacin zuwansa, Annabi Isa (AS) zai sauka daga sama, sannan su
yi aiki tare wajen tabbatar da gaskiya. Ahlus-Sunnah wal-Jama’ah. Sun gaskata da
zuwan Imam Mahdi kamar yadda hadisan Annabi suka tabbatar. Suma ƴan Shi'a sun yi
imani da Imam Mahdi, suna cewa shi ne Imam na goma sha biyu daga Imaman su, wanda
yanzu yana boye kuma zai bayyana a nan gaba a cewarsu. Wannan shi ne takaitaccen
tarihin bayyanar Imam Madih".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Wani lokaci Imam Madih zai bayyana?. Shin
bayan zuwan su dijjal ne zai bayyana ko dai sai ya zo kafin su dijjal?".

Kai Ronnie yana da san yawan tambaya, dama kuma dik mai ilimi kuma mai san kara
faɗaɗa iliminsa dole ne ya rinƙa tambaye tambaye. Allah sarki ita kuwa tun da tana
san ya shiryu, bata gajiya da tambayoyinsa. Gyara zama da kyau ta yi, a nitse ta
fara bashi amsarsa kamar haka.

"Bayyanar Imam Mahdi, Dajjal, da sauran manyan alamomin tashin alkiyama suna da
tsari da Allah ya tsara, kuma akwai bayani a hadisan Annabi (SAW) game da wannan. A
mahangar addinin Musulunci, Imam Mahdi zai bayyana ne kafin bayyanar Dajjal, kuma
zai taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar musulmi a lokacin wannan fitina mai girma
wato fitinat dijjal. Zuwansa ba a lokacin da aka sani ba ne. Annabi Muhammad (SAW)
ya ce, lokacin bayyanar Imam Mahdi ba wani abu ne da mutane za su iya hasashe da
cikakken tabbaci ba. Amma zai bayyana ne lokacin da musulmi suke cikin
matsananciyar bukatar jagora, sun jigata suna cikin kunci da wahala game da azabar
azzaluman shugabanni, a lokacin zai bayyana domin ruguje zalincinsu ya zama jagora
ga musulmi. Tsakanin bayyanarsa da bayyanar dijjal. A hadisan Annabi (SAW), ya nuna
cewa Imam Mahdi zai bayyana ne kafin bayyanar Dajjal, kuma zai yi wa Dajjal tawaye
tare da taimakon Annabi Isa (AS) lokacin da Dajjal ya bayyana, Imam Mahdi zai
jagoranci musulmi su yi gwagwarmaya da shi. Sai Annabi Isa (AS) ya sauka daga sama,
sannan shi ne zai kashe Dajjal a ƙarshe. Hadisin Bukhari da Muslim. An ce Annabi
Isa zai sauka a lokacin da Imam Mahdi ya riga ya kasance jagora, sannan su biyu za
su haɗa kai wajen yin maganin Dajjal. Annabi Isa zai sauka a kusa da minar Madina
mai farin haske (minaratul bayda) a Syria, Bayyanar Dajjal. Fitowarsa ita ce mafi
girman fitina ga al’umma, wanda zai zo tare da ƙarya da sihiri mai ƙarfi. Saukar
Annabi Isa. Annabi Isa zai zo domin taimakawa Mahdi wajen kawo ƙarshen Dajjal,
sannan ya jagoranci sauran al’umma. Zai zo ne bayan Mahdi ya fara gyara duniya.
Wannan shi ne ainahin cikakken bayani a kan bayyanar Imam Mahadi".

Ta kai karshen maganar tana kallansa. Shiru ya yi yana jinjina girma irin na
Ubangiji, wato Alqur'ani ya tabbata ba abin wasa bane, lallai ne ba shakka dik mai
tinani ba zai bijire maganar Allah ba.

Buɗe baki ya yi domin ya yi magana sai gani suka yi anturo kofar ɗakin an
shigo. A tare suka kai kallansu a kan kofar shigowa tana zare hannunta daga rikon
da ya yi mata. Ɗan zaro idanu Sweetie ta yi tana kallansa, shi kuwa ƙarisowa ciki
ya yi ba tare da ya kalli in da suke ba.
Gaban mirrorsa ya karisa ya tsaya, ya gama shirya komai domin cire
ƙwaƙwalwarta kamar yadda ya tsara, yau kuma yake sa rai zai yi wannan aiki, shi ne
dalilin dawowarsa yanzu kenan.

Silent talk ya yi wajen cewa Ronnie ya fita daga ɗakin ita kuma ta same shi a
wannan ɗaki da ya yi treating ɗinta last time. Kallon juna suka yi ita da Ronnie,
miƙewa Ronnie ya yi ya sauko kasan bed ɗin, sannan ya nufi kofar fita, yana san
tambayar yayan nasa me zai yi mata ko dai bata da lafiya ne? Amma sai ya ji tamkar
an ɗaure mashi tongue ɗinsa, ya kasa magana, haka ya nufi fita waje.

Ita kuma dirowa kasan bed ta yi, idanunta a kansa, shi kuma sam sam baya kallanta,
ita kyansa na musamman da ya yi ma take kallah, kowani kaya yasa kyau

Please Login or Register in order to submit comment