Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 43 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita.

Dawo da kallanta a kan su Chuchu ta yi, ku shirya mu je wajen daddynku ko?. Ta yi
maganar tare da wucewa dressing room ɗinta. Tana shiga mama Haulat ta shigo ya
kawowa Mahnoor alkyabbarta, ita kuma Chuchu ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsu dan ta
shirya da wuri.
After some minutes, gabaɗaya sun hallara a gaban King, wato da Chuchu, Jawad, Jaish
and Mahnoor. A nan ne momma ta sanar da Jaish wacece Mahnoor, ta kuma ce mashi ta
bashi ita amana, ya sani marainiyace, kada ya yi abu domin ita mommar, dik abin da
zai yi ya yi domin Allah y kuma duba maraicin yarinyar nan.

Kunsan mutumin da kunya, dik abin da momma take faɗa yana jinta amma ya sunkuyar da
kansa kasa kamar babu shi a cikin ɗakin. Haɗesu ta yi ta yi masu nasiha mai ratsa
zuciya, ta tunatar dasu girman Allah, ta kuma tunatar da su cewa aure sunana ne na
manzan Allah wanda ya fi kowani sunna girma da kima, ta kara jaddawa Jaish da ya
kula da Mahnoor tsakaninsa da Allah, daga karshe ta rufe da cewa su wuce bedroom
ɗinsu da matansu.

Sai da ta gama maganarta tsab sannan King ya ɗaura nasa shi ma, cikin nitsuwa
ya yi masu nasiha shi ma haɗe da karfafa masu gwiwa ya kuma ja kunnen Chuchu da
Mahnoor a kan su yi wa mazansu biyayya, daga karshe shi ma ya rufe da su tashi su
wuce bedroom ɗinsu.

Miƙewa Jawad da Jaish suka yi a tare, suka wuce gaba Chuchu da Mahnoor suka
rufa masu baya. Suna tafiya King ya dubi momma dake zaune a bakin bed ɗinsa. "Na
bawa matar Jaish kwautan kujerun makka guda biyar, idan kin je Jimeta ki sanar da
iyayenta da wanda ta zaɓa su shirya bana su je Makkah, sannan ina da special kyauta
a gareta a matsayina na mahaifi a gareta, akwai kyautar gaisheni da ta zo ta yi zan
bata sai kun dawo daga Jimeta".

Matsawa momma ta yi jikinsa, ta kwantosa tana zuba mashi godiya, kamar jira dama
yake yi haba ai sai ya fara al'amura.

🔥🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥🔥

Cike da tashin hankali Abbie ya bi bayan Ummie dan ya dakatar da ita daga aikata
kudurinta. Sai dai ina kafin ya fito parlourn har ta fice. Cikin zafa ya taka da
sauri sauri ya bi bayanta. Tana cab zata shiga part ɗin su Ramish ya kwala kiran
sunanta. Tana jin ya kirata ta yi saurin rugawa ta afaka cikin part ɗin su Ramish.
Allah sarki dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, sai ya ji kamar in da
yake tsaye ta yi wani irin juyawa da karfi, nan take ya ji kamar zai faɗi.

Dafe bango ya yi ya fara bin jikinta ya juya izuwa part ɗinsa. Ita kuwa Ummie, sai
da ta shiga cikin part ɗinsu sai ta rasa me zata ce masu ne ma, ta ce su zo suga ta
kama Abbie da wata mace nan kuma Ramish ya dallah mata mari kafin ya yi yunƙurin
zuwa, dan tasan halinsu sarai, to ya zata yi ta ja su izuwa part ɗin Abbie su
ganewa kansu? Ta jefawa kanta tambayar.

Tana tsaye a tsakiyar parlourn tana tunane tunane sai ga Ramish and Bilal sun fito
a lokaci guda, suna shirye cikin arabs jallabiya zasu tafi musque. Sun ɗan yi
mamakin ganinta a part ɗinsu da asuba haka, Ramish dai ya yi kamar bai ganta ba ya
zo zai wuceta, Bilal ne ya tsaya tambayarta me take yi a nan?.

Dai'dai lokacin su Dr Raj ma suka fito da sauri, suma tsayuwa suka yi dan ganinta a
nan. Tashin hankali ne ya bayyana a tattare da ita, kame kame ta fara yi masu, can
kuma wani idea ya faɗo mata, da sauri ta ce masu su je part ɗin Abbi yana nemansu
abu ne na gaggawa.

Basu tsaya tambayarta me yake faruwa ba, dan tun dq suka ganta a nan da wannan
lokaci sun san ba lafiya ba, dan haka suka yi zafin namar nufar part ɗin Abbie.
Already dama shi Ramish da bai tsaya kulata ba can ya nufa, saboda ya saba zuwa
wajen Abbie da asuba su tafi masallaci a tare, so sai ya nufi can.

Wani irin daɗi ta ji ganin sun nufi part ɗin Abbie, har da tsalle ta daka tana
murmushi, sai kuma lokaci guda ta nitsu tare da wucewa da sauri ta rufa masu baya
tana ayyana yadda zakunan samarin Abbie zasu yi kaca kaca da Leesharh, dan in dai
suka sameta a haka kasancewarsu musulmai ne kawai zai hana ba zasu cinye namarta
ɗanya ba.

Suna shigowa suka tsaya cirko cirko kamar waɗan da aka dasa, kallan Abbie suka
tsaya yi, Ramish yana rike da hannunsa yana tambayar meyasame shi jikinsa dik jini
haka?. Abbie zai yi magana ganinsu Bilal da Ummie sun shigo yasa ya yi shiru,
Ramish ya lura da Abbie baya san yin magana a gabansu dan haka sai ya ce masu su je
masallaci zasu biyosu daga baya.

Ummie kuwa hankalinta a tashe t fara bin gadan Abbie da kallo tana zaro idanu, babu
Leesharh babu alamarta a saman bed ɗin, abin ya bata mamaki. Abin da bata sani ba
shi kansa Abbie mamaki yake yi haɗe da tambayar kansa ina Leesharh ta shiga, domin
kuwa lokacin da ya bi bayan Ummie domin ya bata hakuri kada ta kira su Ramish,
kafin ya dawo ne Leesharh ta bar bedroom ɗinsa, da y dawo ɗakin bai sameta ba.

Tambaya ɗaya yake yi shi ne ina take ya aka yi kuma ta bar bedroom ɗinsa? Yana
shigowa da bai sameta a saman bed ba ya fara nemanta har cikin toilet, sai dai da
gaske babu ita babu labarinta a cikin ɗakin, hankalinsa ne ya yi mummunar tashi,
dan yana ganin kamar waɗan da suka yi ƙoƙarin cutar da ita a farko ne suka zo suka
ɗauketa, abin da zai sanar da Ramish kenan, zai sanar mashi da ya biyan Leesharh
bedroom ɗinta ya duba mashi menene ya sameta, bai kai ga yin hakan ba su Ummie suka
shigo, shiyasa ya yi shiru?.

To ina Leesharh? Waye ya ɗauketa?.

"Babu wata matsala?". Cewar Bilal. "Yeah babu zaku iy tafiya zamu biyoku daga
baya". Ramish ya faɗa idanunsa a kan Abbie yana kallan tashin hankali a cikinsu.

Dr Raj ne ya ce. "Yah Ramish jini ne fa a jikin Abbie kuma ka ce mu tafi?".
Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Juyawa suka yi suka nufi hanyar
fita, ɗakin ya rage daga Ummie da ta yi mutuwar tsaye, sai Abbie and Ramish.

Da wutsiyar ido ya wurgawa Ummie kallo, nan take ta sha jinin jikinta, tin bai yi
magana ba ta yi saurin wucewa ta fita waje tana mamakin da al'ajabin ɓacewar
Leesharh a ɗakin haɗe da bakincikin burinta bai cika ba, ta so su Bilal su yi kaca
kaca da ita, amma Allah ya tsallakar da ita, ciza laɓɓanta ta yi tare da furta
akwai gaba ai, wato bata janye kudurinta ba kenan.

Me Abbie zai sanar da Ramish? Me zai faru? Ina Leesharh? Waye ya ɗauketa? Dik a
gaba zaku ji.

Magana suka yi na tsawon 30 mins, sannan Ramish ya fita daga bedroom na Abbie ya
nufi bedroom ɗin Leesharh. Da shigarsa bai fi 10 mins ba ya fito ya koma part na
Abbie. Jim kaɗan suka fito a tare da Abbie suka nufi masallaci.

Yau saɓanin kowacce rana da suke dawowa da wuri, yau sai karfe 9 na safe Abbie da
Ramish suka dawo cikin gidan, koda suka dawo kuma part na Abbie suka wuce, nan suka
zauna suka cigaba da tattaunawa, da alama wani bincike suke yi a sirrance, ko Ummie
basu bari ta sani ba.

After some hours. Da misalin karfe 4 na yamma, katafaren hall ɗin da zasu yi
taro ya cika makil da jama'a, taro ake gudanarwa bisa ƙaida, doka da girma, dik
wasu manya masu ji da kansu a faɗin Dubai sun hallara a cikin wannan taron. Abbie
yana zaune tare da Ummie a saman wani haɗaɗɗun kujeru da aka tanadawa familyn King
Badeen, su Dr Raj dik suna gefensu except Ramish da yake saman stage yana speech
cikin harshen larabci.

Sharifat tana zaune a tare da Leesharh waje guda, sun yi shiga iri ɗaya, bakin
Leesharh ya ɗan kumbura haka zalika goshinta ma ya ɗan kumbura, tana sanye da face
mask a face ɗinta, sannan yi rolling veil ɗinga har ya rufe mata ciwon nata da aka
sanya mata white bandeji a wajen.

Waye ya yi wa Leesharh dressing na ciwukanta? Ya aka yi hakan ta faru? Me
Abbie da Yah Ramish suke shiryawa? Dik kada ku damu zan warware maku komai, ku dai
mu je zuwa.

Miƙewa Leesharh ta yi, cikin sanyin murya ta ce da Sharifat zata je toilet tana
zuwa. Da okey Sharifat ta amsa mata, sannan ta ɗaura mata da cewa ta kula. Jinjina
kai kawai ta yi.

Hall ɗin cike yake da manya manyan jami'an tsaron, securitys ta ko'ina, tsaro ya
yawaita sosai a wajen ne saboda Abbie da yake matsayin ministan tsaron sannan ga
manyan jami'ai irinsu Ramish a wajen.

Wani keɓaɓɓen waje Leesharh ta je ta samu domin amsa call ɗin masu nikaf da suke ta
kiranta tun ɗazun, dama ba wani toilet da zata je, call take san ɗagawa. Filin da
ta je a cikin wajen taron ne, amma ta baya wajen wasu ɗakuna da babu kafar mutane a
wajen.

Ciro wayarta ta yi daga cikin hand back dake hannunta kalar abayar jikinta wato
maroon color, ta yi kyau sosai. Tana ƙoƙarin yin picking na call ɗin ta tsinkayo
muryar mutane daga ɗaya daga cikin ɗakin dake bayanta suna magana kasa kasa. Fasa
ɗaukar kiran ta yi a in da ta ƙasa kunne take sauraransu.

Zaro idanu sosai ta yi a lokacin da ta ji suna shirya shirin yadda zasu harbi
Ramish, dik yadda aka yi sun riga masu taron shiga wannan hall ɗin, sosai Leesharh
ta yi mamakin jin maganganunsu, tasan dai a yadda wannan hall ɗin yake wlh idan ba
da wani na jikin family ba babu wanda ya isa ya shigo nan wajen, saboda tsaron da
aka zuba ko tsuntsuwa bata isa ta gifta a wajen ba ba tare da an harbeta ba, to ta
ina waɗan nan mutane suka shigo wajen?.

Yanzu ta kara tabbatarwa tabbas da sa hannun na gida a shirin kashe Ramish, tabbas
dole da sa hannun na gida, to waye? Ta jefawa kanta wannan tambayar.

Taba tsaka da tinani ta ji ana ƙoƙarin buɗe kofar a fito. A a miliyan ta watsa ta
bar wajen ta yi baya, a bayan wasu curtains dake wajen wasu windows kusa da wajen
ta ɓuya, a hankali ta ɗan buɗe curtains ɗin tana leƙo kanta dan taga su wanene zasu
fito daga cikin ɗakin, daga in da take tana iya gano kofar ɗakin.

Wasu maza ne su biyu suka fito cikin shigar three-piece suit launin ash mai
haske, fuskokinsu dik sanye da face mask sannan hannayensu rike da sillent pistol
gun, kafafunsu na cikin cover shoes na maza, sun yi shiga irin dai shigar dik wasu
manyan baki da suka halacci wannan yaran, sun saje da mutane kenan.

Mamaki ne ya kamata ganin zanen dake wuyarsu na scorpio, shiru ta ɗan yi taba
tinanin a in da ta taɓa ganin irin wannan zane a gidan Abbie, tabbas akwai mai irin
wannan zane a gidan Abbie, to waye?.

Tana tsaka da tinani sai ta ga sun sa kai sun nufi wajen taron. A hankali ta
lallaɓa ta fito ta rufa masu baya, tana tafiya kirjinta na dukan uku uku, a dai'dai
wannan lokacin ƙwaƙwalwarta ya tunano mata tabbas wanda ya kawo mata hari daren
jiya ma yana da wannan zane a wuya! And bayan shi akwai wani mai irin wannan zanen
a gidan.

Cigaba da bin bayansu ta yi ƙwaƙwalwarta yana tinano mata abubuwa kala kala da ya
danganci abin zargi a gidan Abbie. Tabbas Hajiya two seater ma tana da wannan
zanen, hakan na nuni da zanen na kungiyarsu ce kenan? Ko dai yaya?. Sake tunawa ta
yi Ummie ta taɓa yin wani bakon matashi mai irin wannan zanen a wuya, babbar
magana.

Binsu ta yi har zuwa cikin hall ɗin, tana ganinsu suka koma can baya wajen da ba
mutane sosai, a nan suka zauna. Jikinta na rawa ta haura saman stage da Ramish
yake, dik da tana shakkarsa tana tsoronsa amma ba zata iya bari a kasheshi ba, dole
ta je ta sanar da shi, da sauri ta nufi in da yake.

Sai dai bata kai ga isa wajen ba wasu jiga jigan jami'ai guda biyu suka tareta,
dama suna saman stage ɗin suna tsaron Ramish ɗin ta both sides ɗinsa dikka, so
ganinta yasa suka bar wajen suka je suka tareta.

Sai maganarsa yake yi cikin kwanciyar hankali ba tare da ya kalli in da take ba,
yana ji dai jami'ansa suka ce ta koma ƙasa ba zata samu damar yin magana da shi ba,
ita kuwa saboda karfin hali sai ta ce masu ita dole tana san yin magana da shi
yanzu, tana yi masu magana tana kallan waɗan can mutane su biyun.

Hankalin jama'a ne gabaɗaya ya koma kanta, ta jajirce wai ba zata bar wajen ba,
kuma tsoronsu kamar ya kasheta, amma ta ce ba zata bar nan ba har sai sun barta ta
isa garesa. Zaro idanu Sharifat ta yi tana kallanta, shi ma Abbie kallanta kawai
yake yi.

Ganin hankalin jama'a dik ya koma kanta yasa waɗan can mutane suka ga sun samu
damar harbin Ramish a yanzu, dan haka sai suka ciro bindigarsu cikin dabara, ga
face mask a face ɗinsu saboda sun san akwai cameras a wajen.

Saita saitin zuciyar Ramish suka yi, Leesharh tana ganin sun saita zasu yi harbi ta
yi kukan kura da gudu ta keta tsakiyar jami'an, cikin zafa suka rufa mata baya dan
su kamata, ita kuwa tana zuwa ta daddage da ita karfinta ta ture Ramish daga wajen
da yake tsaye bullet ɗin da wadan can suka harbo ya sameta a kirjinta pass. Shi
kuwa Ramish gefe ya yi ya faɗi kasa saboda bai wani kame jikinsa ba a lokacin da
yake tsaye a wajen.

A take Leesharh ta zube ƙasa jini na malala a kamar hanyar ruwa. A zabure Abbie ya
miƙe tsaye, jama'ar dake wajen ne suka kiɗime. Cikin abin da bai gaza second
talatin ba jami'ai suka kewaye saman stage ɗin, su kuwa waɗan can mutane biyun
jami'ai suka nufesu da nufin su kamasu, sai dai me, basu kai ga isa wajen ba
mutanen suka miƙe tsaye tare da ɓalle botirin suit ɗin jikinsu, nan take rigar bomb
ya bayyana a jikinsu.

Cike da barazana suka ce dik wanda ya motsa to zasu tashi wannan waje, so basu damu
da rayuwarsu ba, a shirye suke da su mutu, dan haka kowa ya nitsu a sauraresu a
kuma basu abin da suke so ko kuma kowa ya mutu.

To ni dai ba za'ayi wannan mace macen da ni ba, bari na haɗa kayana na je zuwa
gidan baby da Ammo in sha maltina mai sanyi a can ko na huce takaicin mutuwar
Leesharh.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




🔥🔥🔥BABYN BABY🔥🔥🔥

Safiyar yau dik jikinta a mace ta farka daga barci, kamar wadda aka jibga gaɓɓanta
gabaɗaya ciwo suke yi mata. Da kyar ma ta iya tashi daga barci, sai da Ammo ta
matsa mata, kuma tana da Exams in baku manta ba.

Saukowa kasan bed ɗin ta yi ta nufi toilet tana hararar Ammo da ta tasheta, ita a
dole ranta ya ɓaci.
Wanka ta shiga ta yi, sannan ta fito a gurguje ta hau shiryawa, a lokacin har
7:30 ya yi. Sai da ta kammala shiryawa tsab, sannan ta dawo bakin bed ɗinta ta
zauna. Sai tashin kamshi take yi.

Wayarta ta ɗauko tare da kunna wutar screen ɗin, a gaggauce ta cire password ɗin da
nufin ta yi kira, sai kuma ta ga massage da aka turo mata tin karfe 5 na asuba.
Baby shi ne sunan da aka yi saving number wanda ya turo wannan sakon. Lokacin guda
wani ƙayataccen murmushi ya kubce mata, a hankali ta danna kan massage ɗin ta buɗe
cike da matsuwar san ganin me aka rubuta.

"Good morning, my love. Waking up every day with the thought of you in my heart is
a blessing beyond words. You are the light that brightens my world, the melody that
soothes my soul, and the dream I never want to wake up from. This morning, I just
want to remind you how deeply I adore you. Your smile is my sunshine, your voice is
my favorite song, and your love is the air I breathe. May your day be as beautiful
as your heart, as radiant as your smile, and as peaceful as your embrace. I love
you more than words can say. Have a wonderful morning, my queen!". A karshen sakon
sai ya sanya mata emojin heart da na kiss guda bibbiyu. Shi ne abin da saƙon ya
ƙunsa.

Tin da ta fara karanta saƙon nan take sakin cool murmushi, wani irin sanyi ta ji
yana ratsa zuciyarta, kaunarsa yasa har ta mance da abin da ya faru daren jiya, nan
take kewarsa ya kamata. Danna kan reply ta yi domin ta mayar mashi da martani.
Rubuta sako kamar haka ta farayi tana yi tana murmushi mai ƙayatar da mai kallanta.

"Good morning, my baby. Waking up to your sweet words fills my heart with
warmth and joy. You are my sunshine, my peace, and the love that completes me.
Every moment with you feels like a beautiful dream I never want to end. Knowing
that I have your love makes my world brighter and my heart lighter. I cherish you
more than words can express, and I can't wait for the day when I can wake up beside
you every morning. I love you endlessly. Have a wonderful day, my baby!" A karshen
rubutun ita ma sai ta sanya emojin heart dana kiss guda bibbiyu kamar nasa.

Kewarsa da zumuɗin daɗaɗan kalamansa ya ja ta rubuta mashi wannan reply ɗin ba tare
da ya mayar da hankalinta a kan kalaman da ta zuba, sai ya yi mata kamar sarauyinta
zata rubutawa, bata ma sake bin sakon ta karanta ba kawai ta tura mashi.

Tana turawa ko minti ɗaya ba'ayi ba sai ga call ɗinsa ya biyo baya, ta yunkura zata
tashi kenan sai ga kiran nasa ya shigo. Cike da zumuɗi ta koma ta zauna tare da yin
picking na call ɗin.

Kara wayar a kunnenta ta yi, cikin sanyin murya ta ce Hello baby. Daga cikin wayar
ta ji saukar ajiyar zuciyarsa, sai da ya ɗan yi gyaran murya saboda ɗan saisaita
voice ɗinsa da ya sarkafe saboda daɗin kalamanta kafin ya ce.

"Sai yanzu kika tash daga barci ko?". Kai ta gyaɗa kamar tana a gabansa, sannan ta
bisa da e.
"Menene ya dawo mun dake haka ne baki tashi da wuri?".

Shiru ta ɗan yi ta rasa abin faɗe. "Kin shirya tafiya school ne?". Ya katse mata
shirun. Kai ta gyaɗa tana haɗawa da e ta shirya.

"Ina zuwa yanzu in kai ki, wait for me"....... Mamaki ne ya kamata, bai taɓa kaita
school da kansa ba, to why yau ya zaɓi kaita da kansa? Ta jefawa kanta tambayar,
tana can tana tunani bata san time da ya katse kiran bama, sai kawai ta ji shiru.

Miƙewa ta yi ta fito parlon ɗauke da school back ɗinta a hannunta. Already an
shirya mata breakfast ɗinta da komai da komai, so tana fitowa ta haye saman table
ta fara cin abincinta cikin nitsuwa. Bayan ta kammala ta goge bakinta da tissue,
sannan ta nufi bedroom ɗin Ammo dan su ɗan yi hira kafin ya zo.

Bata kai ga shiga ba ta tsinkayo kamshin perfume ɗinsa alamar ya nufo parlourn
kenan. Da ƴar gudunta ta juyo ta isa bakin kofa ta laɓe tana ƙunshe dariya. Yana
sako kai unexpext ta saka ƙara wai dan ta bashi tsoro.

Ko kaɗan bai tsorata ba, sai ma binta da kallan mamaki ya yi. Turɓune fuska ta
yi shagwaɓar ta motsa, kamar zata yi kuka ta ce.

"Baby, why didn’t you get scared? Do I look like someone who wouldn’t scare you? Is
that why you refused to be scared? Well, you’ve disappointed me".
She finished her words and turned to head toward Ammo’s room.

Quickly, he grabbed her hand and said, "You’re just too dramatic. Alright, I’m
sorry. Next time you scare me, I’ll act scared. But for now, time is up, and you’ll
be late for school. There’s no time for games. Just go and inform Ammo that we’re
leaving".
He finished his statement as he released her hand.

"Do you promise that next time if I scare you, you’ll act scared?". She asked,
pouting.

He nodded in agreement. Aminta da hakan ta yi, sannan ta nufi room ɗin Ammo. Da
kallo ya bita yana jin wani irin kifiya na santa yana kara cakar kahon zuciyarsa.

Yana tsaye a wajen har suka fito a tare da Ammo. Cikin mutunta juna suka gaisa
shi da Ammo, sannan ya riko hannunta yana yi wa Ammo sallama suka fice daga gidan.

Su kansu drivers da suke kaita school sun yi mamakin ganin ogan nasu zai kaita
school da kansa yau, sai dai basu ce komai ba suka bisu da fatan alkhairi. Gidan
gaba na motarsa ta shiga, ya shiga mazaunin driver, idanunsa a kanta ya tada motar,
da alama fa da gaske ta manta abin da ya faru daren jiya.

Da ɗan madaidaicin gudu ya ja motar suka nufi waje. Shiru ta kwantar da kanta a
jikin kujerar motar tana tinanin Exams da take da shi, bata ankara ba sai ji ta yi
ya kashe motar.

Da sauri ta ɗago kanta ta kalli hanya, tabbas basu iso school ba, bakin wani
katafaren super market suka tsaya. Dawo da kallanta a kansa ta yi. Ita yake kallan
shi ma, ta buɗi baki zata yi magana ya rigata da cewa. "Wait for me am coming". Ya
kai karshen maganar tare da buɗe kofar motar zai fita.

Da sauri ta riko hannunsa, hakan yasa ya juyo gareta. "Baby ka saya mun chocolate
ga ji? Kullum idan na ce ka saya mun baya saya mun sai ka ce cikina zai yi ciwo, ba
zan sha dayawa bafa".

Lips ɗinta kawai ya zubawa idanu yana kallan yadda take magana, bai san ko da ya
furta. "Ni da kayana amma am mun shamaki da shi". Bai san ya faɗi hakan ba sai da
ya ga ta zaro mashi idanu, nan ne ya fara tinanin wai shin me ma ya faɗa ne?. Gudun
kada ta jefa mashi wata tambayar yasa ya yi saurin janye hannunsa daga riƙon da ta
yi mashi ya fice waje.
Yana ji tana ambatar sunansa yaki dakatawa, dan ya yi suɓul da baka. Turo baki
ta yi a fili ta ce na yi fushi da kai, ba zan sake yi maka magana ba.

Mai da kanta jikin kujerar ta yi ya kwanta tana turɓune fuska. Good 20 mins ya
ɗauka a cikin wajen kafin ya fito, tana ganin ya doso motar ta kara turɓune fuska
tana harararsa.

Bayan mota ya zo ya buɗewa yaran super market ɗin suka jibge mashi niki nikin kayan
da ya saya, sannan ya dawo ya shiga gidan gaba. Kunna motar ya yi da gudun gaske
suka nufi school, dan ta yi latti. Dik bayan minti sai ya juyo ya kalleta, tabbas
ya fahimci fushi take yi da shi, amma bai kulata ba saboda saurin da suke yi.

Bai dakata a ko'ina ba sai a cikin katafaren parking space na school ɗinsu,
yana yin parking ya sanya hannu a gidan baya ya ɗauki ƙaramin lada daga cikin
shopping da ya yi ya miƙa mata. Kin karɓa ta yi a in da ta sanya hannu zata buɗe
kofar motar ta fita, ita dai ta yi fushi da shi.

Zuba mata ido ya yi yana kallanta har ta buɗe kofar ta fita, bai hanata ba kuma
bai yi magana ba, cikin nitsuwa ta fara takawa ta nufi barin parking space ɗin, ko
kyafta idanu daga kanta ta gagara yi, kallanta kawai yake yi.

Sai da ta ɗan yi nisa, sai kuma ta dakata cak da tafiyar tata, da sauri ta juyo
garesa, ganin ita yake kallo yasa ta yi saurin dawowa garesa. Yana dai kallanta bai
motsa ba, ta side ɗin da yake ta zo ta buɗe kofar motar tana huci irin na shagwaɓa.

A saman laps ɗinsa ta zauna, hannu tasa ta ja dogon hancinsa da karfi har sai da ya
furta

Please Login or Register in order to submit comment