Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Bismillarrahmanin Rahim.......✍️


BLACK WORLD😥




Dik da tsananin tsoron da take a cikin ranta hakan bai hanata ɗago kai ta fara
kallonsa tun daga kan Lion chest ɗinsa har izuwa kan his beautiful full neck
attention grabber ba.

Da kyar take iya motsa idanun nata amma ta dage sai ta kalli face ɗinsa kusa da
kusa domin ta tabbatar da mutun ne ko ba mutun ba, because she had never seen a
beauty like him.

Ta ɗauki a kallah 1 mins tana kallon zanen tattoo na Black Tiger dake saman lion
chest ɗinsa, zanen ya fita sosai, ga bakar damusar ta wage baki, waɗan nan garma
garman hakwaran nata masu tada hankalin ɗan adam sun zanu da kyau, sai da ta ji
mummunar faɗuwar gaba na ganin hakwaran damusar.

A lokacin da ta sauke kallonta a kan heart-s romance pink lips ɗinsa sai da ta
dakata cak tare da kura masu idanu tana yi masu kallon ƙurillah, ko makiyi ya gansu
yasan sun kawatu sun kuma haɗu sun kai a mutu a kansu, sai wani irin shining suke
yi kamar ya saka lips balm, kai kyansu ya wuci tunaninku. Ba shakka Allah ya yi
halitta a nan sai dai muce Masha Allah, .

Tsabar karfin hali irin nata da kyar ta iya hakura da kallon laɓɓan nasa amma sai
da ta yi gaba da idanunta izuwa saman romance nose ɗinsa da yake dogo bai zut ba,
ɗan dai'dai haka gwanin birgewa, haƙiƙa skin ɗinsa ya kai a shagala da kallonsa,
wannan ya babbata da gaske bai taɓa fita rana ba, ya tabbata dai tun yana karami
ɓoyesa ɗin ake yi, ni sai yanzu ma na gane dalilin ɓoyesa da babansa yake yi, ashe
kyansa ne ya yi yawa da zai iya ja surutun jama'a a kansa da kuma hankulan mutane,
in ya fito zai hana dikkan matan da zasu ɗaura idanu a kansa yin wani aiki ya hana
zuƙatansu nutsuwa, shiyasa babansa ya ɓoyesa na tsawon shekaru, amma fa a nawa
tunanin ni princess Teema ato bamu san dalilin baban nasa ba, abin da muka sani dai
komai da dalilin yinsa, da alama nasu dalilin ma mai karfin gaske ne.

Bin wasu kyawawan black curly sajen dake gefen kumatunsa da kallo ta yi. Ya ilahi
sai ji ta yi kamar ta kai hannu ta shafa ko tsoro babu, suna kwance luf a saman
skin ɗin nasa mai kama da madubi saboda kyalli. Ya ji hutu malam.

Dik kare mashi kallon ƙurillah da take yi yana tsaye yana cigaba da abin da
yake yi tamkar bai san da wata halitta a wajen ba, kamar ba shi ne ya jawota
gabansa with his magic ba.

Cak ya tsaya daga creating wannan haske da yake ƙoƙarin yi a lokacin da ya ga
sauƙar idanunta a cikin kwayar nasa. Bai taɓa tunanin tana da zarrar iya sanya
kwayar idanunta a cikin nasa ba, dan a cewarsa zaratan maza masu rai da lafiya ma
ba zasu iya ganin face ɗinsa ba bare kwayar idanunsa, sai ga shi ita kuma ta mace
ma da kallon idanun nasa, kyansu sun ruɗeta da har ta manta in da take ta kafesu da
kallo babu ko kyaftawa.

Haƙiƙa hakan ya girgiza shi kaɗan, dole ya dakata da abin da yake yi domin ya
dawo da kallonsa a kanta ya ga zata iya su kalli juna ido cikin ido ne? Idan har ta
iya ganinsa ido cikin ido bata kawar da kallonta ba to ya zama dole ya kasheta,
domin ta cika ƴar baiwa. Babansa ya bashi labarin tabbas dik wadda zata iya
kallonsa ido cikin ido in ma mace ko namiji to ya sani tana da baiwar irin nasa,
idan ma ya yi wasa zata iya bugesa, kuma kada ya yarda ya zauna inuwa guda da wanda
zai ga cikin kwayar idanunsa babu tsoro, idan ya yi hakan tabbas ayyukansa ne zaku
koma baya........ Tashin sense.

Ita kuwa ya subhanallah, sexy romance eyes ɗin nasa ta kafe da kallo ko tsoro hakan
bata ji ba, ita dai taga abu mai kyau ya tafi da imaninta, idan ka kalli idanun
nasa a fisge sai ka yi zaton design of fish ne saboda girmansu, amma ba haka bane,
romance-s-eyes ne, ga shi shikuma ba ɗan soyayya bane, amma wlh yanayin idanunsa
irin na riƙaƙƙun ƴan love ɗin nan, ga shi baya buɗesu dikka, suna ɗan lumshe.
Kaifafa dasu tamkar eagle eyes.

Idan ya kalleka da su kaifinsu da gwarjinin dake cikinsu sai ya razanaka yasa ka ji
faɗuwar gaba.

A hankali ya juyosu a kanta, suka ga juna ido cikin ido kuma kusa da kusa. Wlh
yarinyar nan ko gezau bata motsa ba, kai ko kyafta idanun nata ma bata yi ba, sai
ma ɗan kara warosu waje da ta yi na mamakin kallon cikin nata da ya yi.

Ya ɗan ji a jikinsa, ya kuma fara yarda da cewa tana da baiwa irin nasa, domin kuwa
ita ma idanunta kaifafa ne sosai, idan baku manta ba Kamran baya iya ganin cikin
kwayar idanunsu, shin kun tuna hakan? To ba Kamran kawai ba, dik wanda zai ga
Sweetie ko Pretty idan ba mai dakakkiyar zuciya ba babu wanda zai iya jure ganin
kwayar nasu gaskiya....... DA ALAMA SUNA DA WATA ƁOYAYYAR BAIWA DA GASKE NE, TO
WACE IRIYAR BAIWA KENAN? MU JE ZUWA.

Tsabar ta shahara ma har da fara ƙoƙarin motsa hannunta domin ta taɓa face ɗinsa ta
kara tabbatarwa mutum ne ko aljani. Sai dai kash bayan idanun nata babu wani abin
da yake iya motsawa a jikinta, ya daskarar mata da komai, da zata taɓa shi ta ji
karshen rashin tsoro kenan.

Kai gaskiya Sweetie akwai karfin hali, innalilahi ni narasa ma a wani point zan
ajiyeta, tab kai abin da mamaki gaskiya.

Sakin wannan madubin hannun nasa ya yi ta yi kasa kamar zata faɗi, sai kuma ta
tsaya a saman iska bata kai kasa ba, amfani ya yi da scepter ɗinsa ya yi magic
kafin kyaftawa da Bismillah ta ɓace daga gabansa ta manne da wall na ɗakin ta
ɓangaren hagu.

Dik da haka bata tsorata ba, hasalima bata kawar da kallonta daga kansa ba, shi
kuwa tuni ya zare idanunsa zaga cikin nata.

Da kyar ta kai kallonta a kan swan sofa chair dake shirye ta wajen wall glass
dressing room dake cikin ɗakin, waɗan nan swan design chiar ɗin sun haɗu matuƙa ga
shi sun ji dollof mai laushi da tsantsar kyau da tsada.

Komai na cikin bedroom ɗin nan white, gold and milk color ne, sai kuma jikin
furniture da aka tsantsarawa kwalliya da zallar madarar gold. My people's Allah ya
yi arziki ta yi mubaya'a a wannan empire ɗin, headboard na gadan Black Tiger duniya
ce guda, wall headboard ce, wato kayin gadon manne take da jikin bango, a haka aka
yita wanda tsawonta ya kai har tana taɓa saman ɗakin, sannan aka bi gefe gefenta da
wasu kwayayen fitillu masu bada sky blue ligh mai matuƙar ɗaukar hankali, yanayin
yadda aka tsara wall headboard ɗin nan sai mutun ya kwana ya wuni yana kallo ba
tare da ya sani ba, saboda haɗuwarsu.

Dik wata flowers da kwalliya dake jikin wannan wall headboard ɗin da ɗanyar gold
aka yi ta wanda nasan kun san da hakan, design of butterfly ce head na bed ɗin,
dai'dai tsakiyar butterfly ɗin gold ce haɗe da wani kwai mai bada haske white
light, sai ya haskaka gold ɗin tana wani irin kyalli mai jan hankalin wanda ko baka
yi niyar kallon gadon ba baza san lokacin da idanunka zasu kai wajen ba saboda
wannan kyalli na gold ɗin.
Ita kanta Sweetie bata san lokacin da ta kai kallonta saman bed ɗin tana jinjinawa
girman gadon da kuma haɗuwarsa, kamar ba'a duniya ba, kamar kuma ba za'a mutu ba,
shifiɗun alfarma dake saman bed ɗin kawai ya isa sanya mutun ya ji ya ƙoshi da
komai saboda haɗuwarsu.

Shi kuwa sarkin azzalumai wato King Black Tiger, baiwar Allah tana can yana kalle
kalle shi kuma yana sihirinsa dan ya kasheta.

Tsakar ɗakin nasa ya nuna da scepter ɗinsa, hakan yasa nan take wajen ta zurma
tamkar rami mai zurfin gaske, magic eyes ɗinsa ya juya nan take wasu irin kifiyoyi
masu kaifi da tsinin gaske suka bayyana cike a cikin ramin har baki, kasan
kifiyoyin wuta ce take ci mai tsananin azabtar da har in da suke suna jin hucinta

Wasu irin bakaken kunamu masu duhun jiki sosai manya manya da su ne suka sake
bayyana a saman kan tsinin kifiyoyin nan, sai wasu snake da suka bayyana a jikin
kifiyoyin sun fasa kai da baki, kiris suke jira su fara kai sara.

Har lokacin idanunta a kansa, da alama bata firgita ba.

Da scepter ɗinsa ya yi amfani ya janyota izuwa gaban wannan rami ta hanyar amfani
da magic ɗin nasa. Sai a lokacin ta kawar da kallonta izuwa kan ramin dake gabanta.

Wani irin tsorata ta yi na ganin zabga zabagn kunamun dake yawo a cikin ramin, abin
mamaki kuma wutar dake ci kasan ramin baya taɓa dabbobin, babban abin da ya ɗaga
hankalinta ma shi ne waɗan nan macizai da suka fasa kai suke jiran kiris su kai
sara, wannan wani irin zalinci ne? Da me bawa zai ji idan aka jefashi cikin wannan
rami? Shin da wutar dake ci a kasa zai ji ko dai da waɗan nan shegun baƙaƙen kunamu
da bakaken kumurcin macizan? Ko da kifiyoyin dake tsaitsaye masu kaifin bala'in,
hakika kuma ta wannan hanya Black Tiger ya fi yawan kashe dik wanda ya taɓa ganin
face ɗinsa, cikin wannan rami yake jefa mutun hakan yasa ko gawar mutun ba'a sake
gani, shiyasa tin farko nace maku dik wanda ya shiga cikin wannan part ɗin nasa
ba'a sake jin ɗuriyarsa, ya tafi kenan, to ga hanya ta farko da azzalumi Black
Tiger yake bi domin ɓatar da su.

Mahaukacin razana ta yi, nan take zuciyarta ya fara duka tara tara! Idanu ta zaro
tana kallon cikin ramin tamkar kwayar idanun zasu faɗo ƙasa, jikinta dik a daskare
ba damar ta yi motsi ma bare har ta ce zata gudu, yadda zuciyar tata take bugawa
tamkar ta fasa kirjinta ta fito waje.

Kwata kwata kallonsa baya a kanta, amma yana iya sarrafata, haka zalika bai motsa
daga in da yake tsaye ba, ga mirrorn da yake creating haske da shi a sage a saman
iska.

A hankali ya saitata da scepter ba tare da ya kalleta ba, baya baya gangar jikinta
ta fara yi yana nufar cikin wannan rami. Ihu take son yi amma babu dama, dan babu
wani abin da yake iya motsawa a tattare da ita face idanu, ya datse mata bakinta
baiwar Allah ba halin yin kuka sai dai azaba ya kasheta.

Saura kaɗan ta ƙarisa afkawa cikin rami azaban zafin wutar har ya fara ɗuma fata
izuwa tsokar jikinta, sai raɗaɗi take ji.

Dai'dai wannan lokacin Ronnie da ya fito daga cinema dake part na yayan nasa ya
turo kofar ya shigo, abin mamaki kuma yayan nasa ya rufe kofar fa, amma yana zuwa
ya buɗeta, dik yadda aka yi dama yasan yadda ake buɗe kofar ta koma wacce hanya
yayan nasa ya rufe, anya shi ma bashi da tsafi kuwa?. Kofar Black Tiger fa ba irin
kofofin da kuka sani bane.

Dama da ya yi fushinsa cikin cinema ya shiga ya yi zamansa saman luntsuma
luntsuman sofas dake wajen, ya kunna Tv wai dan ɓacin ran da yake ciki ta kau kada
zuciyarsa ta buga, sai dai kash ya gaza samun kwanciyar hankali, haka kawai ya
rinƙa jin gabansa na faɗuwa shi ne ya ce bari ya dawo su sasanta da yayan nasa kila
ya samu natsuwa. Shi ne dalilin dawowarsa kenan.

Innalilahi, ba karamar razana ya yi ba a lokacin da ya sauke idanunsa a kan
face ɗin Black Tiger, shi hankalinsa ma bai kai kan Sweetie ba tukun nan, saboda
ɗakin yana da balai'n girma sosai, so tsakanin in da take da in da black Tiger yake
akwai rata sosai, hakan yasa bai lura da ita ba.

Kusan mutuwar tsaye ya yi, ya zaro idanu yana ganin abin da bai taɓa gani ba. Ko
yanayin kirar jikin Black Tiger bai taɓa gani ba, abin da ya sani dai shi ne kullum
na Allah yayan nasa yana cikin wasu irin kaya mai kama da na Spider-Man, sannan
kayan tana da wata jela a bayanta kamar dai alkyabba haka, babu abin da mutum zai
iya gani a jikinsa, harta idanunsa Ronnie bai taɓa gani ba, ya dai san kullun da
sassafe yana zuwa wajen yayan nasa su yi gym a tare.................Ina fatan yanzu
kun gane dalilin da yasa Ronnie ya iya dukan master Devil dik da cewa shi ya bashi
horo?

Yana zuwa da safe kullum su yi gym a tare da Black Tiger ba tare da sanin kowa ba,
kullum sai ya tsaya a tsakiyar bayan Black Tiger da kafafunsa Black Tiger yana
press up Da shi.

Kunga kuwa mutumin da kamar Ronnien shararren ɗan Wrestling zai tsaya a tsakiyar
bayansa kuma ya yi press up da shi ai ba zaku haɗa hotonsa da kowa ba, shiyasa
Ronnie ya take master Devil a samun nagartaccen horo.

Kamar daga sama ya ji ance out!! Kuma tabbas Black Tiger bai motsa kyawawan
laɓɓansa ba, ba shi ya yi magana ba amma kuma lion voice ɗinsa ce ta furta wannan
out ɗin, shi kansa Ronnie ya shaida lion voice ɗinsa ce.

Sai dai ya ɗan tsorata dan Black Tiger bai buɗe baki ba.

Kasa motsawa daga wajen ya yi, ya shiga ruɗani sosai na ganin yayan nasa. Kamar
walkiya haka idanunsa ta wutsiya suka hango Sweetie da saura kaɗan ta karisa
shigewa cikin wannan bakin ramin azabar.

Ai a miliyan ya juyo da kallonsa mai gabaɗaya a kanta dan ya tabbatar. Ya
subhanallah ai bai san lokacin da ya ƙarisa wajen ba sai dai kawai ya ga kansa a
gaban ramin.

Ko tsoron yayan nasa bai ji ba ya kai hannu a miliyan ya riko hannunta dake sankare
kamar wadda ta zama ice block.

Da karfi ya janyota domin ya fito da ita, sai dai ina ya kasa koda motsata, tana
daskare kamar gunki.

Black Tiger dai yana tsaye kamar bai san da su a wajen ba. A hankali gangar jikin
Sweetie ya nufi karisa shigewa cikin ramin.

Kin sakin hannun nata Ronnie ya yi yana kallon cikin kwayar idanunta ya ki motsawa
daga wajen kuma, a cewarsa sai dai su tafi cikin ramin a tare su mutu tun da
yayansa ya ki ya saketa ya samu ya janyota ta fito. Idan ran Ronnie ya kai miliyan
to yau ya ɓaci, tin tini yake neman ya sanyata a idanunsa yayansa ya hanasa dama,
ashe dama kasheta zai yi shiyasa ya ɓoyeta na tsawon lokaci? Ronnie ya tambayi
kansa!.

"Ronnie get out!". Lion voice ɗinsa ta daki kunnuwan Ronnie dake tsaye a kan
ƙafafunsa sam bashi da niyar motsawa daga in da yake ko ya saki hannun Sweetie,
idanun nan nasa sun yi jajir kamar wuta, sai wani uban zufa yake haɗawa kamar wanda
aka watsawa ruwa a fuska, saboda hucin wutar dake cikin ramin ta taɓa shi, da kallo
ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin tsananin tashin hankali na wuce misali.

Ko motsawa bai yi ba tamkar ba ƴaƴan nasa bane ya yi mashi magana, ga dikkan
alamu suman tsaye ya yi, dan bai taɓa tsammanin kamanin Black Tiger haka yake ba,
bai taɓa tsammanin ƴaƴan nasa king of beauty, handsome, gorgeous! Sexy man bane,
bugu da kari bai taɓa sanin ta haka Black Tiger yake kashe dik wanda ya keto ya
shigo cikin wannan part ɗin ba.

Magic eyes ɗinsa ya juya, idan ya juyasu kuma alamar zallar madarar rashin imani
zai aikata, Ronnie yasan da haka amma yana tsaye bai motsa ba. Wasu irin dogaye
dogayen itatuwa marasa ganye ne suka bayyana a bakin ramin suka yi mashi zobe, suma
bakinsu kamar kifiya a feke.

Still Ronnie bai tsorata ba bai kuma da niyar sakin Sweetie, daga shi har ita
azabar zafin wutar karkashin ramin yana taɓasu sosai, hakan ya haifar mashi da
wannan zufar da yake haɗawa.

Scepter Black Tiger yasa a in da ya turasu gabaɗayansu biyu cikin ramin. A
tunaninsa Ronnie zai tsorata ya saki Sweetie idan ya ga zasu faɗa ciki dikkansu
biyu, sai dai kash, Ronnie dai da alamar ɗan a mutu ne a kan kyawawan mata. Ya
tsare sweetie da ido suna kallon juna ba halin yin magana, ta zaro mashi idanu sai
ya kara jin ya samu kwarin gwiwar da zai iya mutuwa a kanta, karku manta kaifafan
idanunta suna ɗaya daga cikin abin da yasa yake kaunarta, bare kuma da ta zaro
mashi su, ai abin ba'a magana.

Ganin haka yasa Black Tiger bai bari sun ƙarisa shigewa ciki ba, ya yi saurin fitar
da su dan kada Ronniensa ya cutu.

A bakin ramin ya dakatar da su, sai huci mai zafi ne yake fita daga bakin Ronnie,
da alama ran maza ya kai ƙololuwa wajen ɓaci.

Shammatarsu Black Tiger ya yi ya raba hannun Ronnien da nata, kafin Ronnien ya yi
wani motsi tuni ya turata cikin ramin ya kuma yi amfani da magic ɗinsa ya daskarar
da Ronnien a wajen dan ma kada ya ce zai bi bayanta. Ya ɓatar da waɗan nan itatuwa
da suke bakin ramin sannan ya yi yunkurin rufe ramin a shafe babin Sweetie kenan.

Sai dai abin mamaki abin ɗaure kai shi ne, wani irin haske ne ta bayyana a
cikin ramin mai hasken gaske, kofar ramin taki komawa ta rufe. Ya yi mamakin ganin
hakan daga ta ciki, daga ta waje kuma mamakin bata bayyana ba.

Tafiyar magic ya yi kamar wani walkiya sai ga shi a gaban ramin domin ya duba
menene? Shi kuma Ronnie yana daskare ba motsi kaman gunki.

Sai da ya ji wani irin shock a jikinsa lokacin da waɗan nan magic eyes ɗin nasa
suka sauka a cikin wannan rami, hasken dake fitowa daga cikin sai da ta ɗan
dishashe mashi gani, amma dik da haka bai girgiza ba.

.................Ba komai ya haifar da wannan haske ba face hannun
Sweetie, da yake da magic ya turata cikin ramin so tana tafiya ne bisa
sarrafawarsa, hakan ya haifar da tafiyar tata a hankali hankali take yinsa, lokacin
da zai rufe ramin ta daina ganin komai ta faɗa cikin wuta da kifiyoyin nan sai ji
ta yi hanunta ya sake a in da ta nuna bakin ramin da tafin hannun nata tana yin
alamar Ronnie dake tsaye ya taimaketa kada ya bari ta faɗa cikin wannan bakin
azaban.

Wannan nuna tafin hannun nata da ta yi shi ya haifar da wani irin hasken gaske da
ya fito daga tsakiyar siraran jijiyoyin tafin hannun nata. Hasken kuma ya hana
ramin komawa ya rufu.

Tashin sense, me kuke tunani? Kenan Sweetie ma tana da magic ne ko me?!!.

Zantukan babansa ne kawai suka dawo mashi cikin kunnuwansa a in da yake ce
mashi. "Tabbas a duniyar neman Spender da zai yi zai haɗu da ƴar baiwa mai baiwa
irin tasa, idan ya yi wasa ita ce zata zama ajalinsa, in kuma ya bi komai bisa
tsari shi zai cinye game ɗin".

Tuna wannan magana yasa zuciyarsa ta aminta da tabbas Sweetie ce wannan ƴar baiwar,
domin tun daga kan yadda ta kurawa idanunsa kallo babu tsoro daga nan ya ji a
jikinsa tabbas tana da baiwar irin nasa, bai kara tabbatar da hakan ba sai yanzu.

A maimaikon ya yi amfani da dark magic ɗinsa ya kasheta kawai, sai ya fito da ita a
cewarsa bai ga wani halitta da ya isa ya ja da shi har ma ya yi nasara a kansa ba,
dan haka zai ƙaryata maganar babansa, a zuciyarsa ya raya zai barta a cikin empeir
ɗin ya ga ta yadda za'ayi ta zama ajalinsa, yarinyar da bata wuce ya murkusheta
bane zata zama ajalinsa? So Funny, wonder should never end in this world. A
ganinsa kenan, ya raina baiwar Sweetie, amma ku me kuke gani my people's? Me kuke
tunani? Dan ya karyata maganar babansa nacewa zata yi ajalinsa zai barta da ranta
ya ga ta ya zata yi ajalin nasa!.

Abin da yake tunani kenan fa, dan haka sai ya fitar da ita daga cikin ramin, ya
kuma mayar da ramin ya shafeta kamar bata taɓa bayyana a wajen ba, har wani kyalli
tiles na wajen yake yi kamar babu wani magic da ya taɓa wanzuwa a nan, ya saki
Ronnie dake sankare, ita ma ya sake mata gaɓɓanta.

Kamar walkiya haka ya koma saman swan chair ya zauna tare da ɗaura kafarsa ɗaya a
saman chair ɗin, ɗayan kuma yana ƙasa, ya ɗaura hannunsa ɗaya saman laps ɗinsa.

Da ido ta bishi da kallo har sai da ya zauna, sannan ta dawo da kallonta a kan
Ronnie da yake kare mata kallo, ya ga ta rame, amma kuma ta kara wani irin kyau na
musamman.

"Ronnie wannan ne yayanka ko? He's so handsome sosai, kamar ba mutum ba, ka ga
jikinsa kamar na Robbot ɗin nan da suke aiki a gidan nan, yanayin fatarsu iri ɗaya
kamar madara".
Tana magana tana zaro idanu irin like wow ɗin nan, ga mamaki sosai a saman face
ɗinta, she was so surprised.

Wato ita kwata kwata abin da ya faru da ita ma bai bata mamaki ba, bata wani
tsorata ba, hasalima kyansa yasa bata ga azabar da yake gabanta wanda har ya yi
niyar ɗanɗana mata ba.

Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke tare da ɗan lumshe idanunsa kaɗan ya sake warosu a
kanta, ya ji matuƙar mamakinta sosai, ya jinjinawa karfin halinta da rashin
tsoronta.

Kallonsa take yi tana jiran ya amsa mata wannan shi ne yayansa Black Tiger ko ba
shi bane.

Jinjina mata kai ya yi haɗe da ce mata shi ne.

Wari irin kara zaro idanu waje sosai ta yi, she was so surprised na jin hakan, a
hanzarce ta mayar da kallonta kan Black Tiger, babu ko tsoro ta ce.
"Gaskiya yana da kyau sosai, kaga ɗan bakinsa ɗan karami kamar na Prettyna,
amma yana magana ne ko bayayi? Dan naga bakinsa ya yi karami sosai". A ruɗe take
maganar.
Kamar Ronnie zai ɗan yi murmushi sai kuma ya fasa tare da cewa. "Amma baki ganin
mirror ko?".

Kai ta jinjina mashi alamar e. Harɗe hannayensa a saman kirjinsa ya yi kafin ya ce.
"To ai kamar bakinki ma ya fi na yaya ƙanƙanta, jeki ga mirror a ɗakin ki ki gani".

Ya ce ta je ta ga mirror ne dan yana son ta fita daga ɗakin kada Black heard ɗin
Black Tiger ta motsa ya ce ya fasa yi mata afuwa ya gana mata wani azaban. Sai dai
kash, ita da bata san da wani izaya ba ai gaban mirror dake cikin ɗakin nasa ta
nufa domin ta duba face ɗin nata.

Sosai Black Tiger ya yi mamakinta, wai ita bata san tsoro bane? Wata ɓangare na
zuciyarsa ce ta tuna mashi cewa irin baiwarsa ke gareta fa, dan haka babu tsoro a
jininta. Tashin sense, wlh akwai kura kuwa, Sweetie like black Tiger e kam akwai
matsala, a cikinsu waye kuke tunanin zai kure wani? Shin da gaske kamar yadda
babansa ya faɗa mashi ita ce zata zama sanadiyyar kawo karshensa da shi da
zalincinsa ne ko kuma dai shi zai iya karyata maganar babansa ta hanyar barinta a
cikin kingdom ɗin kuma ya zamana ba zata iya yi mashi komai ba? Waye kuke tunanin
nasa tunanin zai zama gaskiya, baban Black Tiger ne ko kuma shi Black Tiger ɗin?!
Muje zuwa, akwai game mai zafi a gaba.

Tana isa dai'dai tsakiyar ɗakin in da yake tsaye ɗazun kenan da nufin ta nufi
gaban mirrorsa ta duba kanta. Wani irin kara ne ya fito daga jikin mirror tasa
tamkar karar shigowar sako.

Slowly ya ɗago sharp romance eyes ɗinsa kai tsaye sai saman mirror ɗin masa, while
ita kuma Sweetie ta dakata daga nufar wajen.

A hanzarce Ronnie ya kariso in da take, jikinsa har kerma yake yi saboda tsorata,
da karfi ya fisgi hannunta ya nufi waje da ita, tsoro yake kada bakar zuciyar yayan
nasa ya motso kuma.

Kamar aljani haka Black Tiger ya ɓace ɓat daga in da yake zaune, ya fito a
gaban mirrorsa, wato tsafi fa ba abin da bata sanya mutum ya yi, Allah dai yasa
mufi karfin zuƙatanmu kawai, amma matsafi abin tsoro ne.

Zubawa mirror idanu ya yi yana kallo kamar Tv, wani irin tambatsetsen jirgi ne
mai girman gaske yake landing a Black Tiger international airport dake cikin birnin
na Black world, jirgi ne har jirgi, girmansa ya wuci tunaninku, yanayin tsarin
jirgin sak yake kama da FR-55, sai dai shi kan jirgin sak fuskar bakar damisa, da
alama wanna tana ɗaya daga cikin manya manyan jiragen da Black Tiger yake alfahari
da su, dan tsarinta daban ne.

Kafin jirgin ta kammala sauka jikin tampatsetsan mirrorn nasa ya rabe kashi
biyu, rabi yana cigaba da nuna mashi landing wanna jirgi, rabi kuma ya fara nuno
mashi cikin forest in da wasu zaƙwaƙuran matasan warriors ɗinsa ke ta aikin haƙar
ɗanyar gold, kai sai dai fa muce masha Allah, amma arzikin gold kam ba'a magana,
Black Tiger yana da arzikin da ba'a taɓa yin mai irinsa

Please Login or Register in order to submit comment